Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    ~TRUE LIFE STORY~

    *PAID BOOK*

    *AYSHA A BAGUDO*

    *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*

    A matukar harzuke ta shiga dakin zuciyarta kamar ta kama da wuta , tana k’arasa shiga cikin filin d’akin idanunta ya sauka akanshi tsaye a tsakiyar d’akin ya zuba hannunwansa duka a cikin aljihun wandonsa yayinda idanunshi ke runtse yana ciza gefen lip’s dinsa na kasa a hankali , duk da bai bude idanunsa ba yasan itace ta shigo dakin duba ga yanayin da yaji bugun zuciyarsa ya qaru.”

    kallon second biyu tayi masa ta ɗauke idanunta akan shi ta k’arasa da sauri ta bude wardrobe ta dauko akwatin kayanta data zo dashi kasar ta ajiye akan gado ta bude ta soma dibo kayanta ɗaya bayan ɗaya tana zuba aciki ,still bai bude idanunshi ya kalleta ba bare ya dakatar daita daga abinda take ƙoƙarin yi ya cigaba da ciza lip’s dinsa , hakan yasa taji sabon ɓacin rai ya mamaye zuciyarta taji muddin bata bar masa gidan a lokacin ba zata iya mutuwa..”

    Aunty zee ta shigo dakin cikin tsananin tashin hankali ta k’arasa gareta ta rike hannuta batare da ta kalli inda Aliyu ke tsaye ba hankalinta a matukar tashe ta soma magana “mai kike ƙoƙarin yin saboda Allah ? “Kiyi hakuri mana
    duk fa abun bai kai haka ba, idan fa rai ya ɓaci hankali baya bata kisna , ki dawo hankali ki natsu dan girman Allah Karki yi abinda zai janyo bacin rai fiyye da wanda muke ciki yanzu “.Tun da aunty zee ta soma magana kisan bata furta komai ba ta cigaba da zuba kayanta cikin akwati zuciyar na wani irin zafi da ciwo , haka shima Aliyu bai ce komai ba sai sake juya musu bayansa yayi yana furzar da iska mai tattare da bakin ciki “.

    Kisna na shirya kaya aunty zee na dauka tana maida wa cikin wordrobe tana bata hakuri , wani sabon kuka ne ya kufce mata , hawaye sai turereniyar zubowa suke daga cikin kwarnin idanunta “mai kike son nayi aunty zee shine fa da kanshi yace na bar masa gida “? Tayi maganar cikin tsananin kuka wanda da kyar muryarta ta fito “nasani amman dan girman Allah kiyi hakuri ko zaki tafi ba yanzu ba saboda tashin hankalin da mommy zata shiga Sam Sam mommy ba zataji dadi faruwar haka ba. tayi maganar tare da juyowa ta kalli inda Aliyu ke tsaye har lokacin tamkar babu wani halitta dake motsi agurin, ya aliyu ka bata hakuri dan Allah sannan ka dakatar daita dan gaskiya kayi kuskure abinda kayi sam bai dace “. Bazan yayi daita qirjinshi na wani irin dokawa da karfin gaske “saboda me zai bata hakuri bayan bai ga abinda yayi mata ba ,idan zata zauna ta zauna idan zata tafi ta dade shi dai bazai wani dakatar daita ba yayi maganar aransa yana furzar da iska mai zafi ….

    kisna ta sake rushewa da wani sabon kuka mai matukar cin rai ganin ko kallonsu Aliyu bai yi ba bare ya kula aunty zee dake masa magana ,ta d’aura kanta a kafad’arta aunty zee numfashinta na barazanar daukewa saboda kukan da yaci karfinta “kisna !kisna!! Aunty zee ta ta kira sunanta a rude tare da rungumeta a jikinta suka zauna a bakin gado tana cigaba da kiran sunanta , da kyar kisna ta janyo numfashi ta sauke zuciyar na mata wani irin azababben zafi da ciwo , aunty zee ta mike ta tsiyaya mata ruwa a glass cup ta mika mata “ki sha ruwa kisna ko zaki ji sanyi babu mutsu kisna ta amsa cup din ta kai bakinta ta kurbi kadan ta mikawa aunty zee sauran ,aunty zee ta amsa ta ajiye ta cigaba da bata baki .
    cikin haka aryan ya shigo dakin yana kuka aliyu ya juyo a hankali yayi taku daya yana ƙoƙarin kamoshi zuwa garesa , amman tuni yaron ya karasa gurin uwarsa dake kuka tamkar ranta zai bar gangar jikinta , ya haura saman gadon ya rungumeta ta baya yana furta mata kalmar “sori mommy , papa ne ya saki kuka kou ?” Ki yi shiru Ki daina kuka zan rama miki kinji “.
    kukanta ne ya qara akan wanda take tabbas ya’ya rahma ta juyo ta rungumeshi ajikinsa tana sheshekan kuka tamkar ranta zai fita,hawaye tausayinsu ne ya shiga gangarowa aunty zee Aryan ya soma ƙoƙarin raba jikinsa dana kisna “,mumy bari naje na rama miki “a hankali ta shiga girgiza masa kai tana kuka gumi na tsatsafo mata ta ko’ina ajikinka matse aryan tayi gam saboda kokarin fixgewa da yake kokarin yi ajikinta yadda take kuka haka arayan da aunty zee ke kuka gaba-daya an rasa wanda zai rarashi wani .”

    Sautin kukansu ne ya soma damun Aliyu a natse ya fita daga d’akin yana jan dogon tsaki ya shiga d’akin da areef yake kwance ya zauna a gefensa tare da tsura masa idanunshi yana kallonsa, ganin yadda numafashinsa ke sauka a hankali yasa shi sauke numfashi da ajiyar zuciya a tare ya d’aura hannunsa akan sumar yaron yana shafawa a hankali yana jin wani irin sanyi mara misaltuwa a zuciyarsa , dan da wani abu ya samu d’ansa da sai yayi distroye rayuwarta ,sai yayi mata abinda har ta koma ga Allah bazata mantawa dashi ba taimakonta daya d’ansa yana numfashi kuma ko yanzu bazai barta ba har sai yaga mikewar d’ansa tukunan zai saurara mata …”

    “Idan kika ji ancewa mutun yayi hakuri bisa wani abu daya faru to an cucesa ne ,ki qara hakuri kisna idan kika bar gidan Aliyu da sunan yaji ko rabuwa dashi ina zaki “?”kin san dai baki da inda zaki sannan baki da masauki a gidan dady idan kin manta abinda dady yace bari na tuna miki “cewa yayi matukar ba ziyarar arziki ce zata kowaki gidansa ba baya son ganinki da suna matsala dan baki a masauki a gidansa, kuma duk ranar da kika kashe aurenki da Aliyu sai dai ki nemi wani uban amman ba shi ba, zan rokeki da ki kara hakuri kisna ki zauna a d’akinki kada ki ɗauki maganar Aliyu da mahimmcin da zai sa ki bar gidan nan “. wani sabon kuka ta rushe mata dashi tare da zubewa kasa bisa gwiwowinta ta kamkame Aryan dake rungume ajikinta “shikenan haka zan kare rayuwata cikin kunci da maseefa da tashin hankali “? “mai yasa dady da mommy suka kasa fahimtata akan ya Aliyu “?
    “Mai yasa suka fi son shi akan ni da suka yi silar zuwana duniya “?
    aunty zee ta mike tsaye cikin tsananin tashin hankali ta amshi aryan a hannunta sannan kamota ta zaunar daita tace ” wannan soyayya daga Allah ce kisna da kuma kyautatawar da yayi musu, kin sani na sani kowa ma ya sani a cikin yan’uwa Aliyu mutumin kirki ne ,ni yanzu babu abinda zan ce miki daya wuce kiyi hakuri sannan kiyi ƙoƙarin ki adana damuwarki kafin mommy ta dawo gidan nan ta fahimci wani abu , sannan waɗan nan kayan suma ki karasa maidasu cikin wardrobe zanje muyi magana da ya Aliyu ta k’arasa maganar tana fita daga.”

    kai tsaye parlou’n kasa ta zarce domin yin magana da Aliyu sai dai bata samesa anan ba sai nasir da Samir da Safiyya ta samu zaune shiru tamkar waɗan da aka turo musu da sakon mutuwa , ta Kallesu daya bayan daya sannan tace “ina ya Aliyu ko ya fita ne “?Safiyya da nasir ne suka hada baki gurin ta bata amsa da bai sauko ba yana sama ,
    yayinda har lokacin samir ya kasa furta komai sannan ya kasa aiwatar da komai dan jin zuciyarsa yake kamar zata kama da wuta yau da wani ne ba Aliyu ba yayiwa kisna irin wannan wulakanci Allah ne kadai zai rabusu amman akan Aliyu babu abinda zai iya yi ko dady yaji yayi magana akan lamarin sai ya bata masa rai bare matsayin Aliyu ya zarta komai a zuciyarsa …”

    Har aunty zee ta juya zata koma sama ta tsaya batare data juyo ba tace “dan Allah abban Junior ka dawo daidai kar mommy ta dawo ta fahimci wani abu ,wannan matsalar tsakaninsu ne kuma inshallahu komai zai dawo normal yanzu batare da bata lokaci ba , tsakanin miji da mata sai Allah ko mutun ya shiga faɗansu kunya zai ji tayi masa hannunka mai sanda saboda lura da tayi gaba-daya yanayinsa ya sauya tana gama fadar haka ta hau sama da sauri ta shiga dakin mommy ,nan ta samesa zaune ya tasa areef gaba yana kallonsa hawaye na tsiyayo wa daga idanunshi jin motsin shigowar mutun yasa yayi saurin ɗauke hawayensa da hannunsa , sai dai ya makaro dan ta rigada ta gani .
    girgiza kai aunty zee tayi sannan ta samu guri ta zauna akan kujera tana kallonsa sai data numfasa sannan ta kira sunansa a natse ” ya Aliyu …. Bai amsa mata ba haka zalika bai waigo inda take ba ,sanin datayi yana sauraranta yasa ta cigaba da magana “dan Allah ya Aliyu ka canza ,a zahirin gaskiya ban ji dadin abinda kayi wa kisna ba , kuma nasan ko mommy tana nan kai zata bawa rashin gaskiya akan abinda ya faru “.”ina dalilina nayi haka , barinta gidan nan shine abinda zuciyata ta yanke akanta idan taga zata iya ta cigaba da zama a gidan idan bazata iya ba ga hanya nan dan Allah Karki sake bata hakuri akan lallai sai ta zauna ki bari ta wuce duk inda zata dan nima nafi bukatar haka “.”Uhmmm Aliyu ka kuwa masan abinda kake faɗa kama ajiye batun aurattayar dake tsakaninku kai da kisna yan’uwa ne na na jini kasawa ranka kisna Aliyu suna tare muddin rai mutuwa ce kawai zata rabasu “stop saying that zainab I don’t like what you are doing Ina nugun ganin girma da mutuncinki saboda ke din mai mutunci ce kowa ya sani …… “.

    “bazan daina fadar haka ba ya aliyu saboda bayan jinin na y’an’uwanta akwai wani jini na musamman dake gauraye acikin jininku ko kaki ko kaso kisna da Aliyu abu guda ne “dan Allah ki daina faɗar haka kina maseefar taba min rai wallahi “”,Babu wani ɓacin rai hakuri ma ya kamata kaje ka bata saboda kayi mata ba dade ba . “wannan maganar ma ba mai yiwa ba ne dan Allah ki daina fadar haka banaso ina ganin girmanki zainab saboda me zan bata hakuri “? “Laifin mai nayi da zan bada wani hakuri “? yayi mata tambayar ajere ransa na sake ɓaci sannan ya cigaba da magana cikin zafin zuciya “bana tunanin abinda nayi ya sa’bawa Shari’a to saboda me kike tunanin zan bata hakuri “? yayi maganar yana rike hannun areef yana jin yadda hannunsa yayi sanyi “yanzu kana son fahimtar dani cewar ba kayi kuskure ba Kenan “?”Yes of course ban yi komai ba wallahi ,kin kasa dai fahimtata ne kawai saboda kina ganin kamar nayi kuskure alhalin ni Kuma nasan babu kuskure dana akan za’a kashe min da…. …..”…..
    yayi shiru ya kasa karasa maganarsa yana kallon kofar d’akin ,itama aunty zee kofar tabi da kallo ganin kisna ta gani tsaye idanunta na tsiyayar da ruwan hawaye muryarta cikin kuka tace “ki yarda aunty zee bai yi min laifin komai ba ,ni kuma daman na ɗauki laifina ya dai kasa min uzuri ne amman nasan nice da laifi wallahi tunda nasan halinsu aryan basa zama guri daya “. ta runtse idanunta wasu hawaye masu zafi da ciwo suka sake gangaro mata .
    “ni kaina a yanzu zanso rabuwa dashi
    sai dai bazan iya kallon idanunshi nace na tsaneshi ko nace bana bukatar rayuwata dashi ba saboda darajan ya’yana, bazan iya kallon idanun uban ya’yana nace banason shi bana bukatarsa arayuwata ko bana bukatar had’uwa dashi a lahira ba kamar yadda ya fada min “.

    A matukar fusace yace “kinji ba kinji abinda wannan wawiyar take cewa ko zainab wato ma darajan ƴaƴanta takewa komai ? “ai daman nasan abinda ke zuciyarki kenan shi yasa nake son rabaki da su gaba-daya na canza musu wa……….”tayi saurin katse masa hanzari ta hanyar cewa ” duk abinda zaka faɗa ya Aliyu ka fada amman bazaka taba canzani agurinsu arayan ba saboda nice nan na dauki cikinsu na tsawon wata tara da kwanaki kuma nayi na kudarsu ….” Ni yanzu Abinda zaka min tunda baka bukatar zamana da kai ka taimaka ka wankeni agurin mahaifina tunda nayi iyakar ƙoƙarina naga mun sasantar kanmu muyi zaman lafiya da juna amman kaki ,” ba dai baka son zama da kisna ba ? yayi shiru tare da jan tsaki “to ka taimakawa rayuwata ka wankeni agurin iyayena kafin ka sawakemin aurenka dake kaina wallahil azim ina bukatar takardar saki daga gareka ,ka sake ni ka huta rayuwarka nima na huta ” .

    tunda ta fara magana ya dauke kanshi akanta sai dai jin maganarta ta karshe yasa Ya d’agowa idanunshi a hankali yayi mata wani kallon banza sannan ya ɗauke kanshi ya cigaba da kallon areef zuciyarsa na masa wani irin tuttukin bakincikin, sosai aunty zee ta tausayawa halin da kisna take ciki gashi dai a shirye take data sadaukar masa da rayuwarta amman ya kasa fahimtar kisnar da data yanzu akwai bambamci “ya Aliyu karka biyewa zuciyarka kayi hakuri dan Allah, karka biyewa maganar kisna tana cikin ɓacin rai ne , karkayiwa rayuwar aurenku nakasu alhalin kuna bukatar juna ,ka tsaya ka duba rayuwar ƴaƴansu uwar wani da ɗan wani sai Allah babu wanda zai iya kula dasu Aryan kamar kisna, ka barta a gindin ƴaƴanta da ita kadai suka saba sannan ina kake tunanin zata idan ka saketa tunda kasan abinda dady yace mata kayi hakuri dan Allah ta tarkashe maganar kamar zata yi kuka ….”

    d’akin ya dauki shiru na wani lokaci sannan sautin muryar kisna ya karade dakin ” aunty zee ki daina bashi hakuri dan girman Allah ki bar shi yayi duk abinda zuciyarsa ta yanke masa akaina ko dady da mommy sun ki amsata amatsayinsu na iyayena zan bi duniya ,zan kwashe yarana mubi duniya tare dan bazan bar ko daya ba ya sake d’agowa a matukar fusace yana kallonta da jajayen idanunshi da suka canza kala “da wasu yaran zaki bi duniya ? Yayi maganar kamar zai cinye ta “idan zaki bi duniya ki bi duniya ke kadai kar ma ki tsaya a iya duniyar mutane ki zarce zuwa wata duniyar daban i dont fucking care amman ban da ya’ya na ….” ya karasa maganar a zuciye yana baro inda yake ya iso gabanta ya tsaya suna fuskantar juna “idan kin shirya yawon duniya ki tafi ke kadai karki sake ambato ya’yana a ciki okay idan ba haka ba zan kasheki da kai kaina ya karashe maganar yana nuna mata yadda zai yi daita “.

    a hassale tace “lokacin dana yi d’awainiyya da cikinsu kana ina “? ta kai hannuta qirjinshi tana nuna shi jijiyon wuyanta na mikewa sabida tsananin tashin hankali da jin dacin maganarsa ” kana ina nace ? ” kana ina na ɗauki tsawon kwanaki ina nakudarsu sannan na haifeshi kana ina “? “kasan yadda ake daukar ciki ko kasan yadda ake nakuda bare ka faɗa min magana akan ya’yana ka bani amsa tambayarka nake ? ta dinga zuba masa magana tana nuna qirjinsa tare da turesa tamkar mahaukaciya sabuwar kamu shi kuma yana ja baya ganin kamar ta soma fita haiyacinta yasa a zuciye ya damki kafad’unta ya haɗeta da bango dakin “shut up kisna !!!! I said shut up or else I will get you lost on second are you insane ? ya cigaba da magana cikin zafin rai “ko kina hauka ne kike ture ni ” ?”Ko kin soma shaye shaye ne ko kuma tsohon haukan rashin mutuncinki ne ya motsa “? ” alright ai nasan bazaki taba canzawa ba dan idan kayi shekara dari baka haɗu da mutun ba duk ranar daka haɗu dashi karka tambayi halinsa dan halinsa na nan bai canza ba , da wannan halin kike tunani zaki mallaki zuciyar Aliyu never in history? ” Aliyu yafi karfinki yayi miki nisa da…..

    “Papa Me yasa kake sa mommy Kuka ? Suka jiyo sautin Muryar aryan yana kuka har da shesheka ” kullum kana sa mommy kuka bana sonka tunda kana sa mommy kuka daga yau kai ba papa dina bane, babu ni babu kai “.ya riko hannun aryan da niyyar rungumeshi yaron ya fixge hannunsa ya karasa jikin kisna yana goge mata hawaye “stop crying mommy ,I will tell Grandma to punish him wasu hawaye suka zobo mata ya sake goge mata ta karasa ta dauki areef ta saba shi a kafad’anta ta rike hannun aryan suka bar d’akin .”

    “kaga abinda kake kokarin haddasawa ko ?” wannan karamin yaron da bai san meye damuwa ba amman yau saboda ganin uwarsa cikin damu………..
    “ya damu ko kuma ana son gurbata min tunanin yaro ya dauka ni din mugu ne “dan girman Allah kayi hakuri ya Aliyu komai ya wuce karka sake tada maganar nan plz numfashi ya sauke jikinsa yayi matukar yin sanyi saboda ganin yadda aryan ya nuna reaction dinsa akan kisna ya juya ya fita zuwa haraban gidan kanshi kamar zai kama da wuta nasir ya dake zaune ya kalli samir “tashi mu bishi mu shawo kanshi , Samir ya masa banza ganin haka yasa nasir ya mike ya fita,Aliyu yana tsaye hannunsa daya dafe da goshinsa dayan hannunsa yana cikin aljihunsa nasir ya karaso ya rike hannunsa ya nufi lambun gidan dashi batare da yace masa uffan ba shima ya bishi a baya har suka shiga ya zaunar dashi ya koma ya dauko ruwa mai dan sanyi ya ɓalle murfi ya mika masa “ka sha kaji sanyi a hankali ya amsa ya kafa bakinsa a bakin goran bai sauke ba sai daya shanye tasssss .
    Yana ajiye goron nasir ya fara magana cikin fushi ta inda yake shiga bata nan yake fita ba “karka ɗauka ko na shigarwa kisna ne a’a ina fada maka gaskiya ne a matsayina na d’anuwanka kuma abokinka saboda bai dace ba ko wata kayiwa haka ba kisna ba zan tsaya tsayin daka naga na faɗa maka gaskiya shima Samir sam bai ji dadin abinda kayi ba ya dai kasa saka bakinsa ne bisa wani dalili nashi ,ko baka duba darajan kowa ba ka duba Samir mutumin da rayuwarsa ne kawai bazai iya baka ba ,mutumin da kai da kanka ka sha fada min yadda kuka yi rayuwa tare haba muradi ai ko mutuwa tana jin kunyar idon iyaye ,ya’yan nan fa ƴaƴanta ne bazata so abinda zai cutar dasu ba sannan duk sonka dasu bazaka Kai ta ba, nasir ya dade yana masa magana jikin Aliyu ya sake yin sanyi sai lokacin ya fara tunanin yanayin da Samir ya shiga a lokacin da yake wa kisna tujara “kenan haushinsa Samir yaji ko me ..”? Yayiwa kansa tmbayar yana duban nasir ƙwaƙwalwarsa na sake shiga caji “Idan kuwa haushinsa Samir yaji lallai jini ba karya ba “amman har an zo lokacin da samir zai yi fushi atsakaninsa da kisna ? sun dade zaune a lambu nasir na nusar da Aliyu gaskiya bai dai kula sa ba haka bai ce masa ya hakura ba illa iskan da yake furzarwa ..”

    Misalin ƙarfe biyar mommy ta shigo parloun aunty zee ce da safiyya suna zaune ” assalamu alaikum ta furta a hankali tana karasa shigowa gabad’aya suka maida hankalinsu gareta “wa’alaiki salam tare da mikewa suka amshi laidodi dake rike a hannunta ta zauna akan kujera “ya Allah ta furta a hankali ina waɗan sojojin suke ban ji motsinsu ba”?
    Safiyya da aunty zee suka kalli juna sannan aunty zee tace “suna sama tare da mammansu bari na kawo miki ruwa ki sha sai naje na dauko miki su ta karasa maganar tana shiga Kitchen bayan kamar second biyar ta fito hannuta rike da jug da glass cup ta tsiyaya ruwa ta mika mata ta ajiye sauran a saman table sannan ta juya ta hau sama mommy ta kalli safiyya “ina nasir ko suna bangaren Samir ne ko suna lambu “?
    “Eh suna lambu “ta bata amsa da haka suna zaune aunty Zee ta dawo “mumy bacci suke daga su har mammansu ta fadi haka ne dan kar mommy ta d’ago komai “bacci a daidai wannan lokacin ki koma ki tasota ga waya nan na siyo mata ta bude ladar data shigo dashi ta mikawa aunty zee wayar “gashi nan ki tasheta ki bata “kai mommy gaskiya ta gode kisna zata dawo online kenan ? “Gaskiya wayar tayi kyau sosai ” dubu ɗari biyar kenan a kudinmu na nigeria zaro ido aunty zee tayi “haka waya yake da tsada anan ?”sosai kuwa ai wayoyi sunfi sauki a Nigeria nan dai aunty zee ta dinga jan mumy da hira daga karshe nasir ya kira safiyya a waya tayi musu sallama ta wuce aunty zeey ta shiga Kitchen domin daura abincin dare ..”

    Haka nan jikin mommy ya dinga bata akwai abinda ya faru a gidan da bata nan dan har kusan takwas din dare bata ga yaran ba haka bata ga kisna ba hankalinta yaki kwanciya gashi ita ta kalli abincin da aunty zee ta kawo mata bata jin zata iya sanyawa cikin komai batare da ta daura idanunta akan jikokinta mafi soyuwa acikin ranta ba ,ta mike ta sanya silifas ta fito daga d’akin ta karasa bakin kofar dakinsu har zata tura sai tayi tunanin watakilla Aliyu yana ciki tayi knowking tare da sallama ……”

    Aliyu ne ya taso sanye da jallabiya dan maroko kalar dark blue jallabiyar tayi masa kyau sosai abunka ga fari sol ya bude kofar ganin mommy tsaye ya sha jinin jikinsa sai dai yayi kokarin sanyawa jikinsa jarunta cike da girmamawa yace “barka da dare mommy , kina bukatar wani abu ne “?Girgiza masa kai tayi kana tace “yaran nan nazo dubawa tunda na dawo daga kasuwa ban sanya idanuna akansu ba daga su har uwarsu shiru yayi dan shi kansa baya son mommy tasan abinda ya faru ,idan ya hanata ganinsu zata fahimci wani abu idan ya barta ta ga hannun areef hankalinta zai iya tashi fiyye dana yanzu duk da bawani ciwo bane ,hannu dai yayi sanyi ne saboda shock din daya samu , matsawa yayi gefe ya bata hanya ta shigo d’akin akan gado ta hago su kwance lullu’be cikin bargo kisna na zaune a gefensu jingine da gado ta tafka tagumi tana ganin mommy ta sauko tana wayancewa “,mommy kiyi hakuri kin jini shiru ko wallahi tunda kika fita kaina ke ciwo shine na kwanta har yanzu ma ban daina jin ciwon kan ba momy ta zuba mata ido tana nazarinta sannan ta karasa gurin yaran ta shafa kansu tayi kasa da hannuwanta zuwa kirjinsu taji numfashinsu na sauka yadda ya kamata ta rankwafo ta sunbuci goshinsu ta dawo ga kisna “kiyi kokari kiga likita kada ki tsaya gida shan magani a tare kisna da Aliyu suka d’ago suka kalli juna qirjinsu na mahaukacin bugawa da wani sauri mommy kuwa tana gama magana tayi musu sai da safe ta fita Aliyu ya kulle kofar ya hau saman katifa ya yi rigingine rungume da hannuwansa duka a qirji yana tunanin maganar mumy da alamun ta dauka ko ciki ke ga kisna ..?

    Har kusan dayan dare kisna bata runtsa ba tana kwance kusa da ya’yanta shima ba runtsawa yayi ba tunani ne ya sha kanshi ta kai hannu ta janyo laidar da aunty zee ta shigo mata dashi d’azu tana dubawa wasu zafafan hawaye ne suka zo mata “uwa kenan “hakika duk wanda ya rasa uwa yayi kuka tasan ta siya mata wayar ne a matsayinta na yarta da kuma kwantar mata da hankali dan ta zauna da Aliyu gashi wanda ake wa dan shi yaki kwantar da kai su zauna lafiya ta mike dan saka wayar a caji motsin laidar ya tadda areef ya Mike zaune Aliyu yayi saurin kamoshi jikinsa ya rungume shi “zaka ci abinci ne?Yaron ya girgiza masa kai yana cewa “,papa tea “
    da sauri ya sauko yana ƙoƙarin fita kisna ta rigashi fita dole ya dawo ya zauna rike dashi bata dade ba ta dawo hannunta rike da cup din tea ta amshesa a hannun Aliyu ta soma bashi can shima Aryan ya farka ta dauko shi ta bashi sauran tea din da areef ya sha ta kwantar dashi ta shiga bayi dan bata jin zata iya runtsawa ta d’auro alwala ta fito wanda zuwa lokacin ya kwantar da areef a kusa da aryan sai dai idanunsu biyu yana lallabasu dan su koma bacci ..”

    Tana zaune byn ta idar da sallah ta fashe da kuka yaranta dake kwance suka sauko a gigice suka karaso gareta suka rungumeta kuka take suma suna kuka kamar ana zarar ransu kuka yaran suke sosai saboda ganin halin da take ciki gashi dai basu da cikakken wayon da zasu ce ga dalilin kukanta sai dai suna jin zafin halin kunci da mahaifiyarsu take ciki a hankali ta rungumesu ajikinta tana ci-gaba da kuka “Allah kasa papa ya daina saka mommy kuka kasa ya bata farinciki , ki daina kuka kinji mommy duk aryan yake magana shi areef ganin mamansa da d’an’uwansa na kuka ne yasashi kuka “na gode d’ana na daina kuka kaji babana Allah yayi muku albarka na gode muku ,kuma na godewa Allah daya azurtani da samu ya’ya irinku masu tausayi Allah yayi muku albarka ta karasa maganar tana shafa kansu …..”

    Mmn sudais
    💗💗💗💗💗💗
    CUTAR DA KAI
    💖💖💖💖
    💗💗💗💗💗💗

    ~TRUE LIFE STORY~

    Note
    error: Content is protected !!