Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    ~TRUE LIFE STORY~

    *PAID BOOK*

    *AYSHA A BAGUDO*

    *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*

    ….Numfashin juna suka cigaba da zuka da kamshin jikinsu , ta lumshe idanunta tana jin wani irin yanayi da bata taɓa jin irinsa ba sai akanshi , a hankali taji ya soma taɓa wani bangaren na jikinta cikin wani irin salo da shi kaɗai ya iya , ta narke sosai tana kallon idanunshi dake rufe tare da amsar sakoninsa masu tsuma zuciya da tsantsar jiki , hannun rigarta yake ƙoƙarin zamewa har yayi nasarar zamewa batare daya sani ba brest d’inta ɗaya ya bayyana, numfashinta dake sama da kasa ne ya nemi tsayawa , gabad’aya ta tsorata ,ta zaro idanu jikinta na ɗaukar rawa cikin tsananin tsoronsa ta kai hannuta zata maida hannun rigarta ya sake yin wani yuyi sai ga hannusa akan dukiyar fulaninta ya kife, wata irin razananniyar ƙara ta saki da karfi aiko ya farka a firgice daga baccinsa suka haɗa ido ta saki ihu , shima tsorata yayi da ganinsa kwance a jikinta ya zabura ya tashi ya zauna dafe da qirjinsa , ita kuma ta duro daga kan gadon da sauri ta tsaya tana haki jikinta na wani irin kad’awa tamkar mazari ta dinga sauke numafashin sama sama “.

    Ransa a matukar ‘bace yace ” Ki faɗa min abida kike anan kafin na sauko na fasa miki kai yanzu ? ” muryarta cike da in ina tace “ni ni na kwanta ne saboda na kasa bacci dan ban saba kwamciya a kasa ba ,kuma ina kwantawa kusa da kai , kawai naji ka rungumeni ajikinka ka soma wa .. …..
    Mugun kallon da yayi mata ne yasa ta kasa k’arasa maganarta , ta qame guri daya ta buge da wasa da yatsun hannunta ,sai dai idnnunta na kanshi tana kallon sansar jikinsa, dan gabad’aya yanayinsa ya sauya a cikin lokaci kankani, ya zuba mata idanunsa kamar zai cinyeta dan bakinciki “me kika ce yanzu ? tayi shiru tana ci-gaba da wasa da yatsun hannunta qirjinta na dokawa da matsanancin karfi ” what do yau say ? ya sake aiko mata da tambaya jikinsa na tsuma “have you lost your mind ?” ya fad’a a fusace cikin tsananin ɓacin rai tayi shiru tana dubansa cikin tsoro sai dai kamar tayi dariya amman ta danne dan tasan abinda dariyar nata zai jawo mata ” .

    “kawai ki fito ki faɗa min ba zaki iya kwanciya a kasa ba saboda kina son ki ra’bi sansar jikina ,”shikenna bari ni na bar miki gadon na koma kasa na kwanta dan bazan iya da jarabanki ba “ya yaye bargon daya lullube rabin jikinsa dashi yana kokarin saukowa tace “no no kayi kwanciyarka kawai ni zan kwanta a kasa ta ɗauki pillow da bargonta ta wuce ta ajiye pillow da karfi akan shimfid’arta ranta a jagule ta zauna “you can be comfortable there ta faɗa tana kwanciya tare da d’aura kanta akan pillow ta lullube jikinta banda kanta ta rungume hannuwanta a qriji tare da juya masa baya ,tayi shiru tana kallon bangaren kofa .”

    Pillow ya janyo ya makale ajikinsa gam yana fidda numfashi sama sama yana kallonta ,a hankali ya matsa baya ya jingina bayansa da abun gado yana furzar da numfashi mai zafi “wawiyar yarinya kawai mara kamun kai , duk yadda nake gudunta taki tayi hankali bare ta fahimci bana bukatarta a rayuwata , i have to take care of my self before she rape me ” ya fada yana sake kamkame pillow ajikinsa tare da runtse idanunshi saboda kanshi bai daina masa ciwo ba har lokacin gashi damuwarta tasa ciwon ya karu .”

    a natse ta ɗan d’ago kanta ta gani ko ya koma bacci idanunshi biyu ta gani tayi saurin maida kanta ta runtse idanunta , dukkaninsu kankame pillow suka yi ajikinsu suna jin wani irin sauyi na dabam a sansar jikinsu sakamakon had’uwar da jikinsu yayi “my goodness why am feeling about him koda yake ai ni ba itace bace kuma ba ruwa ne ajikina ba ya kamata zuwa yanzu naji fiyye da haka ajikina, dumin jikinsa mai laushi kaɗai ya isa ya haddasawa mutun jin tsananin sha’awarsa ” duk yadda kake guduna aliyu dole kayi rayuwa dani dan zan zame maka karfen kafa duk inda kake zan kasance tare da kai , zan hana zuciyarka sukuni , zan ruguza duk wani shirinka akaina ya zamo zuciyarka bata da hutu da yancin kanta har sai kasance tare dani , kusan karfe ukun dare tana kwance tana tunani abinda zata yi domin mallakashi da komai nashi , a hankali ta tashi tana sauke ajiyar zuciya ta koma saman gado ta kai hannu kan hannunsa taji jikinsa yayi sanyi wannan karon bacci mai nauyi fiyye dana d’azu ne ya daukeshi ta yaye bargon jikinsa ta soma balbale botiran gaban rigarsa ta kwanta a saman fad’ad’d’en qirjinshi dake kwance da kwantaccen gashi sai kamshi yake ta zame rigarsa gabadaya fuskarta na fuskantarshi bakinta ta kai daidai gefen wuyansa tana shinshinawa kafin daga bisa ta kai cikin kunneshi tare da haɗe hannunwansu guri daya tana cigaba da tsotsar kunnenshi ,wani irin numfashi yake fitarwa yana ware kafafunsa, ta cire bakinta cikin kunnenshi ta kai bakinsa sai data tsotsi bakinsa sosai kafin ta cire bakinta ta kamkameshi tana maida numfashi ,ta lullubesu da bargo a hankali bacci ya ɗauketa kwance a saman jikinsa .

    har gari ya waye tana kwance a saman qirjinsa tana sharar bacci a hankali ta fara motsa hannunta da fuskarta har ta buɗe idanunta taganta kwance ajikinsa , sama tayi da idanunta tana kallon fuskarshi kana ta mike zaune hannunta ɗaya a saman qirjinsa shiru tayi tana cigaba da kallon kyawawar fuskarshi dake zagake da kasumba kaɗan baki mai sheki da ɗaukar hankali, shi kuwa bacci yake hankalinsa kwance “duk bala’inka sai da muka kwana a guri daya ta fada a kasan ranta murmushi ne ya bayyana akan fuskarta ta matso ta kai bakinta goshinsa ta sumbata tana murmushin jin dadi sannan ta juya bayanta ta fito daga cikin bargo ta zuro da kafafunta da niyyar saukowa daga kan gadon taji kamar an riketa ,dan dakata tayi ta juyo a hankali ashe kasan rigarta ne ya malake a karkashin hannunsa, ta kai hannu ta ɗan daga hannunsa a hankali ta zare rigarta ta lalla’ba ta ajiye hannunsa dan kar ya farka ya ganta ta gyara masa bargon fuskarta ɗauke da murmushi sannan ta sauko ta tsaya bisa kafafunta idanunta na kanshi ,a natse ta k’arasa jikin window ta zuge labulen window ta rufe sosai saboda sanyin da d’akin ya ɗauka ta juyo ta tsaya tana kare masa kallo daga inda take tsaye ,a hankali ta soma takowa qirjinta na bugawa da matsanancin karfi ,ta ɗauke Idanunta akanshi ta nufi kofar bayi ta buɗe ta shiga tana sauke numfashi da kyar, ta d’auro alwala ta fito ta dauki hijab d’inta ta zira ta shimfida sallaya ta tada sallah koda ta idar ma bata tashi ba zama tayi tana addu’a akan Allah ka karkato mata da hankalinsa ….”

    A hankali ya bude idanunshi tare da yin mika da salati ,ya yaye bargon jikinsa ya mike ya shiga bathroom yayi wanka da ruwan dumi ya fito,tsaye yake a tsakiyar dakin bayan ya fito daga wanka ya shirya cikin riga dark blue mai gutun hannu da bakin wondo jeans yayinda hannunsa ke rike da Kayan daya cire yana ƙoƙarin tattarasu dan kaisu laundry ta shigo d’akin bakinta ɗauke da sallama jikinta sanye cikin riga da siket na tamfa super holland dinki yayi matukar tsayawa ajikinta haka ma siket din ya zauna mata sosai duk da bai wani matseta ba amman dai ya zauna sosai ajikinta sai kamshi turaren humura da wasu turarukan take , da kyar ya iya amsa sallamar da tayi a ciki ,shima dan yasan mahimmancin sallamar ne bancin haka babu abinda zai sa ya amsa mata .”ta karaso ta tsaya gabansa “good morning Mr A yana jinta yayi mata banza ,zata amshi kayan hannunsa ya fixge yana d’ago kanshi “wai mahaukaciyar ina ce ke ? ” zan lalata miki fuska fa matukar baki kiyayeni ba” ya fad’a cikin zufin zuciya . “

    “Saboda baka sona ba “.
    “exactly kamar kin sani, kuma tun da kin san da haka sai ki daina shiga rayuwata ko kusantar duk inda nake dan bana bukatarki kusa dani .
    “Wannan zancen naka ina da ja, ka dai san dalilin da yasa kake guduna ,ba komai bane sai dan na zama wani bangare na rayuwarka shiyasa kake gudun duk wani abu da zai had’amu guri daya saboda yanayinka na sauya wa ? tayi maganar tana murmushin mugunta
    Shiru yayi mata yaki cewa komai dan wani iri tuttukin bakincikin sosai yake ji akan furucinta ,shiru itama tayi tana sakar masa murmushinta mai matukar kyau wanda ke sake bayyanar da ainihi kyawunta ” wai ma me nayi maka da har kake min irin wannan tsanar ? ” Kana treat dina Kamar baka san daga inda na fito ba ? Kana kokarin kasheni dan ka yiwa iyayena hasara , dan nasan kai baka da hasara ko mutuwa nayi”.

    Tayi kasa da muryarta sosai ” nasan nayi maka kuskure a baya na kuma roki ka yafe min abinda nayi maka “ai abinda bazan taba miki ba kenan yafe miki ba ? ” ya fada yana mata kallon sama da kasa, “babu abinda baki min ba na shanye na had’iye na danne zuciyata nayi hakuri ” you treat me the way you like I can’t forgive what you did to my life , I cant forgive you kisna Kuma bazan taba mika miki ragamar rayuwata ba ,kin kashe min gudan jinina kisna …….”
    “ɗan da zan fara samu a duniya abinda nafi so nafi qauna abinda nake ji duk duniya shine gatana kuma yan’uwana ko zan iya yafe miki akwai abubuwa dayawa da kika min arayuwa wanda bazan iya yafe miki ba , na sha yafe miki a duk sanda kika min wani abu saboda nasan duk randa hakina ya tashi tambayarki bazaki ji dadi n rayuwarki ba, na yafe miki abubuwan da kika min amman ban da zubar min da cikina da kikayi ,a yanzu bana bukatar komai daga gareki illa ki fita rayuwata dan bana son ganinki a duk inda nake kiyi rayuwarki nayi tawa simple as that “
    “Duk abinda kace nasan haka ne amman kuma ai na baka abinda kafi so da bukata a rayuwarka sannan duk yadda ka kai da kina bazaka taɓa kankareni daga rayuwarka ba dan ba’a canzawa tuwo suna..” banza yayi mata tamkar bai jita ba dan ya fahimci inda maganarta ta dosa yadda ta tsura masa ido ko kiftawa bata son yi yasa ya dinga jin wani abu acikin zuciyarsa yana shawagi ” idanunta ta lumshe tare da matsoshi sosai kamar zata shige jikinsa ” maganar had’uwa ko kusanci mr A tuni an wuce gurin dan samun su aryan da arif ma wani ….”
    “Enough kisna banason jin komai Karki sake danganta min ya’yana dake” ..

    Ajiyar zuciya ta sauke tana sake gyara tsayuwarta “shikenan bazan sake ba amman ka tausaya min dan Allah ka manta da abinda ya faru ina sonka aliyu ina son komai naka most especially kyawawan halaiyenka ,kana da kyakkyawan zuciya, zan baka mabudin zuciyata Aliyu ka bude ka shiga duk inda kake so ba dai bakincikinka kiyayyar dana nuna maka bane ? “Yau ga kisna agabanka tana rokonka tana furta maka kalmar so da bakinta “.

    Ya d’ago idanunshi da suka wadatu da zara zaran gashin ido ya zuba mata kana ya maida kanshi kasa yana cewa “ba fahimtar abinda kike faɗa nake ba ,zai fi dacewa kiyi shiru da bakinki ko ki kama gabanki “
    “dan Allah ka fahimceni zuciyata ta cika da dimbin soyayyarka tare da qaunarka gabad’aya so nake ka bude kofofin zuciyaka sannan ka amince na shiga, ka soni tamkar yadda nake sonka yanzu ….”

    Da sauri ya sake d’agowa yana dubanta duba mai cike da matsanamcin mamaki ya kada kai yana tabe baki “ban yi mamaki ba ta yadda kike da careless din bude zuciyarki ga duk namijin
    daya ga dama zai shiga batare da shamki ba,Koda yake ba abun mamaki bane sbd dama haka kike , idan ya kasance zuciyarki a buɗe take ,to ni tawa Zuciyar a datse take bana tunanin har wata mace zata samu shiga ,babu soyayya kowace mace a zuciyata bazan iya saka kaina a sawun mashirmanta ba yayi gaba abunsa yana dafe da kanshi dake sarawa ta biyosa tana ƙoƙarin kamo hannunsa ya fixge tare da juyowa ya sauke mata mari guda daya mai kyau a fuskarta irin marin da akewa lakabi da ‘barin makauniya ya damki makoshinta yana huci , “zaki sake kuskuren kai hannunki jikina ?”
    “Nace bana so i don’t like it ,live me alone ya k’arasa Maganar a fusace ,take ganin kisna ya dauke sakamakon marin da yayi mata ga wuyanta daya shake da kyar numfashi yake fita gaba-daya bata wani ganin kirki duk ta dimauce ta gigice bata ganin komai bata jin komai har sanda ya saki wuyanta tare da tureta yasa kafa ya shureta “daga yau kika sake gangancin kai hannunki jikina zan lalata miki rayuwa zan ‘bata wannan kyakkywar fuskar da kike takama dashi ya karasa maganar yana kwafa da kyar ta samu ta sauke ajiyar zuciya da karfi ta rike wuyanta da har lokacin take jin rad’ad’i wani sanyi taji yana tsiyoyawa daga hancinta ta kai hannu ta tabo tana dubawa jini ta gani “kaɗan kika gani muddin bazaki fita daga rayuwata kiyi rayuwarki ba irin wannan izayar sune hukuncinki ,kiyi rayuwarki nayi rayuwata shine zaman lafiyarki a cikin gidan sabanin haka kuma kinsani “. yana gama magana yayi parlou’n kasa ya kwanta yayi pillow da hannunwansa duka ya daura ƙafarsa daya akan daya yana girgizawa baya jin zai iya fita zuwa ko’ina saboda zazzaɓi da yake ji itama kwanciya tayi akan gado wasu zafafan hawaye na bin kuncinta “na *cutar da kaina* me yasa nayi masa abinda nayi ?”Me yasa banji maganar Samir ba a lokacin da yake nuna min illar abinda nake ? me yasa baji maganar aunty Aysha ba “? yar’uwata ta fada min gaskiya tayi min nasiha ta fada min wata rana zanyi dana sani gashi ina yi …”
    ” mai yasa na biyewa aunty Afra gashi ta Kai ni ta baro ta barni Ina girban abinda na shukawa zuciyarsa ni ɗaya , kuka take sosai har da shesheka ta mike zaune tana tunanin abinda zai ci “ko kinyi masa tayin abinci bai zama lallai yaci ba zuciyarta ta faɗa mata haka “amman ai bashi da lafiya ? ta yiwa zuciyarta tambaya “ki rabu dashi har zuwa sanda zai huce umarnin zuciyarta tabi ta koma ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya tana tunanin kalmamin daya faɗa a sakwanin da suka gaba “babu soyayyar kowa a cikin zuciyarsa kenan itama nawal din ba sonta yake ba ? ba sonta yake ba zai aureta yana duk sonta “ina ma zai zamo da gaske babu soyayyar kowa a zuciyarsa kamar yadda ya fada haka ta dai dinga saka da warwara a hankali har bacci ya ɗauketa .”

    sai kusan karfe ɗaya na rana ta farka ,taji fuskarta tayi mata nauyi ta zuro kafafunta ta sauko ta tsaya gaban mirrow gabanta ya fadi ganin bakinta da hancinta sun kumbura har ma da idanunta girgiza kai tayi ta shige bayi tayi wanka ta d’auro alwala ta fito ta sauya kaya zuwa doguwar riga pinky colour tayi sallah ta sauko kasa dan shiga Kitchen mamaki ganinsa kwance tayi hannunsa daya da abun qarin ruwa yayinda likita ke gabansa yana ƙoƙarin bashi kulawa daga gefe guda kuma nasir ne zaune yana kallonsa sam hankalinta bai kai ga nasir ba har ta karasa saukowa idanunta na kanshi kunnensa manne da waya daga jin yadda yake wayan tasan da Samir ne ,da sauri ta karasa zuwa inda yake kwance jikinta na rawa “sannu a she zazzaɓi yayi karfi haka ?” sannu Allah ya baka lafiya ina ke maka ciwo ? “Ya tsani jin sautin muryarta duniya da lahira ” kai hannunta daidai saitin wuyansa tai ,ta shafa zafi taji ya ratsa tafin hannunta shi kuwa saurin runtse idanunshi yayi yana jan tsaki sai dai ya kasa dakatar daita saboda ya badamasi daya amshi wayar a hannun Samir , kanshi ta d’aga ta d’aura a saman cinyarta tana shafa sumar kanshi “doctor meke damunsa plz “?”Fever ne amman nan da zuwa wani lokaci zai ji sauki tunda anyi masa allura ta cigaba da shafa sumar kanshi tana sauke numfashi”sannu Allah ya baka lafiya gaba-daya duk ta rud’e shi kuwa wani tuttukin bakincikin ne ya tokare masa kahon zuciya, yana gama wayar yace ” ke maza ki tashi ki bar nan..” yayi maganar a dan zafafe , babu mutsu ta d’aga kansa ta maida kan pillow ta Mike tsaye sai lokacin taga nasir dake zaune , jiki a sanyaye ta gaishesa ya amsa mata cikin sakin fuska “ya gida kisna ? “Lafiya ta furta masa a hankali tana tambayarsa safiyya yace” tana gida zuwa anjima zata zo, ta gyada masa kai sannan ta nufi hanyar Kitchen har ta kusan shiga likita yace “madam akawo masa abinci ya ci ya sha magani ..”

    “No likita ba sai naci komai ba ka bari na sha maganin kawai “ba zai yiwu ba ,idan ma bazaka ci ci abinci ba kasha ko ruwan zafi ne , ki kawo masa tea “okay ta faɗa tana karasa shigewa kitchen ,bayan kamar second biyar ta fito hannunta rike da cup ta karaso gabansa ta durkusa wanda zuwa lokacin ya mike zaune “ga tea “ki ajiye a kaina mana ” ya fada a zafafe yana nuna kansa “ban taɓa ganin sakariyar dakikiyar mace irinki ba komai baki iya ba “. ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ajiye cup din akan table din dake gabansa ta sake juyawa ta koma kitchen zuciyarta na wani irin zafi ..”

    A tsanake ta fara haɗa priderice tana cikin aikin safiyya ta shigo bayan ta gaishe da Aliyu tare da yi masa ya jiki ta shiga Kitchen saboda jin motsin kisna da tai “har kin karaso? Kisna tayi magana tana kawar da fuskarta gefe dan bata son safiyya ta fahimci wani abu amman sai data fahimta ,ta dawo gabanta ta tsaya tana kare mata kallo fuskarta dauke da tambaya sake kawar da fuska kisna tayi tana juyawa gurin wanke wanke Safiyya ta biyota tare da juyo daita suka fuskanci juna “me ya samu fuskarki haka naga ta kumbura ?”
    “babu komai ta bata amsa atakaice” babu komai fa kikace ko dai uncle Aliyu ne ya ‘bata miki fuska haka “? tayi saurin girgiza mata kai “ko daya faduwa dai nayi a bayi d’azu da safe ta bar gurin ta karasa jiki frizer ta buɗe ta dauko naman kaza tana juyowa taga safiyya a gabanta tana kallonta idanunta sun cicciko da ruwan hawaye kafin kace me har sun fara zubowa “meye abun kuka babu komai fa faduwa nayi “babu wani faduwa da kikayi wallahi kina dai boye min ne kawai, amman dagani fuskarki mari ne” ta karasa maganar cikin rawar murya , “tam shikenan kije parloun ki jirani ina zuwa ta faɗa tare da ra’bawa ta gefenta ta wuce duk yadda safiyya take son su tautauna akan lamarin zamanta da aliyu kisna taki, aikinta kawai take tana dauko mata wani zance dabam , daman kuma ita ba mai yawon magana bace .”

    A parlour ma magana nasir yake wa Aliyu “kayi hakuri Aliyu hakuri ake da mata haka kowa yake fama dan Allah ka manta komai sannan ka daina dukanta, da iyayenta sunsan irin wannan zaman zakayi daita da basu sake baka ita a karo na biyu ba , ka saka wa zuciyarka damuwa, kullum kana cikin damuwa da zubar da hawaye nasan kana son kisna duk da baka taɓa furta min hakan ba amman wallahi ko rantsuwa nayi bazan yi karfafa ba kana sonta kuma so mai tsanani laifinta ne ya hana soyayyar tasiri “.

    “zaka yi kaffara kuwa abdul-nasir saboda ban taba sonta a cikin zuciyata ba ,muyi zama ne ba irin zaman da zamu so juna daita ba, nasir ya karaso inda Aliyu yake zaune ya dafa kafad’ansa “naji amman kayi hakuri dan Allah taci darajan iyayenta ka saukaka mata ba dole sai ka sota ba amman ka daina wulakantata kana dukanta akan abinda bai kai ya kawo ba ,kalli yadda ka mayar mata da kyakkyawar fuskarta akan ta rike hannuka kawai …..”
    Aliyu ya ja tsaki kaɗan yace “gaskiya nasir ka cika min ido dayawa ,nasir yayi dariya mai nuna cin nasara akansa yace “na gode duk abinda zatayi ka barta dan Allah ka daina dukanta kisna da safiyya suka karaso parlour’n hannunsu rike da manya manyan kuloli suka ajiye akan dining tare da plet kisna ta karaso gaban Aliyu ta na cewa “ranka shi dade abinci yayi ready nasir yayi dariya yace “an gaishe da uwar gidan Aliyu sannu da ƙoƙarin zubo masa kawai ki kawo masa nan “murmushin jin dadi tayi taje ta zubo masa ta dawo ta ajiye a saman table din gabansa taje ta dauko masa lemunsa na gado da ruwa ta dawo nasir ya mike ya koma mazauninsa “sannu yaya kake jin jikin naka yanzu”? Yayi mata banza tamkar ba dashi take magana ba , ta dauki plet din abinci ta dibo had’ad’d’en priderice ta kai bakinsa “kallon cikin kwayar idanunta yayi yana jin zallar ɓacin rai “ka bude baki kaji , kaga baka da lafiya rashin cin abinci yana bari ciwo ya samu matsuguni ajikin mutun”.tayi maganar tana lumshe masa idanuwanta , fuskarta data dan kumbura yake kallo ta dan bashi tausayi kadan “ka bude baki ” ta sake maimaitawa “jikinsa a sanyaye ya buɗe ba dan yaso ba ta soma bashi abinci abaki spoon uku yayi ya kawar da kanshi, ta ajiye plet ta tsiyaya masa lemun ta kai bakinsa ya buɗe ya sha ta jiye cup din, kallonsa tayi taga gumi ya ɗan tsatsafo masa a fuska tasan gumin abinci mai zafin daya ci ne, tasa gefen rigarta ta soma goge masa “ba muna da towel ba “? Yayi maganar muryarsa can kasa kamar baya son magana , ta gyada masa kai sannan ta mike cikin sauri ta hau sama.”

    bayanta safiyya tabi da kallo dan gabad’aya dawowa tayi kamar wata wawiya ta kasa zubawa mijinta abinci tana kallon kisna dake rawar jiki akan mutumin da bai san darajanta ba ,ko cikakken minti biyu batai ba ta dauko towel ta dawo ta zauna kusa dashi zata goge masa ya amsa “zanyi da kai numfashi ta sauke ta cigaba da kallonsa ,yadda safiyya ke Kallonsu haka nasir ke Kallonsu kisna ta bala’in burgeshi kuma yaji dadin yadda ta sauya ta rusunar da kanta ta zubar da makan yakinta domin kyautatawa mijinta sai gurin yamma su nasir suka bar gidan .”

    A cikin mota safiyya ta waigo inda nasir yake zaune yana tuki “sweet heart Wai me ka fahimta yau ne a gidan aliyu “? “Kamar me kenan ?shima ya tambayeta yana sake maida hankalinsa ga tukin da yake “kamar duka yayiwa yarinyar mutune fa , wallahi ban taɓa tunanin haka daga Aliyu ,ban san haka halin aliyu yake ba ,mutumin da nake ganin ya fika kyawawan halaiya ,mutumin da nake ganin babu kamarsa a fadin duniyar nan ,mutumin da nake kismawa a raina duk matar data sameshi a matsayin miji tayi sa’a duniya da lahira, mutumin da nayiwa kanwata kwadayin aurensa saboda kyawawan halaiyensa yau shine yake musgunawa matar aurensa kuma uwar ya’yansa why nasir “?

    “Duk abinda kika lissafa akan Aliyu gaskiya ne domin kuwa Aliyu mutumin arziki ne mutumin Karki ne ,muyi karatu dashi a kasar nan tunda muka zauna bamu taɓa samun matsala dashi ba, mutun ne na gari bai taɓa aikata laifin komai ba ,mutun ne shiru shiru wanda yasan darajan dan adam da duk wani hukunci da’aka tanada domin mu’amula .”
    “ita kuma kisna da kike ganinta yar ta’adda ce kamar yadda duk wani dake cikin danginsu ya san da haka ,duk wannan tashin hankalin da take fuskanta ita tajawa kanta da taimakon Afra ,wannan halin da yake nuna mata tayi masa fiyye dashi , wallahi idan na faɗa miki abinda tayi masa har duniya ta nade bazaki sake ganin kima da girmanta ba yanzu ma wannan ladab din da kikaga tayi na wuya ne , saboda taga babu wanda zai iya rufawa rayuwarta asiri sai shi …..
    ” dan haka ki daina magangun bazan akan abinda baki sani ba ,naki kiyi kokarin kwantar mata da hankali tunda yanzu tayi nadama ki nuna mata ta cigaba da hakuri wata rana zai dawo mata yadda take so . numfashi Safiyya ta sauke tace “kenan shiyasa bata son ana fadar laifinsa saboda tasan itace bata da gaskiya? “eh ya bata amsa a takaice dan duk ya gaji da tammayoyinta “shikenan zan tayata da addu’a Allah ya daidaita tsakaninsu “ameen addu’a mai kyau kenan .”

    Mmn Sudais
    💗💗💗💗💗💗
    CUTAR DA KAI
    💖💖💖💖
    💗💗💗💗💗💗

    Note
    error: Content is protected !!