Cutar Da Kai – Chapter Two
by Aysha A Bagudo*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*
“A hankali ta furta “Ya Allah ka bani karfin zuciya akan bawanka Aliyu , ya fahimceni ya duba lamarina , ya tausayawa rayuwata , Allah ka bani ikon yi masa abinda zuciyarsa zata kusanto zuwa gareni ,ka bani ikon yin nasara akanshi na mallakesa na mallaki zuciyarsa cikin sauki ,cike da sanyi jiki ta kai hannu jikin handle din kofar d’akin ba dan tana tunanin a bude kofar take ba sai dan tabbatar da hakan, abun mamaki ji tayi kofar ta buɗe .
ta tura a tsanake ta shiga , hangosa tayi kwance akan bargo a kasa ya rungume pillow a qirjinsa wanda hakan kusan al’adar sa ce, yana ganin shigowarta ya juya d’ayan bangaren rungume da pillow , dan baya qaunar kallon fuskarta ,ta k’arasa inda yake kwance ta durkusa a gabansa “nasan nayi maka laifi kuma na roki afuwarka ya kamata ka tausaya ka yafe min haka bana son na cigaba da zama makiyayarka kamar yadda ka ɗauka saboda mu samu damar inganta rayuwar ya…..
“dan Allah malama bana son takura bacci nake ji kije kawai bana son kusancimu tare .
“ammmm to dan Allah ka tashi ka koma saman gado ka kwanta ni sai na kwanta a kasa ” kije ki kwanta kawai bana bukatar haka ya k’arasa maganar yana runtse idanunshi gam , mikewa tayi jiki a sanyaye kamar zata yi kuka ta hau saman gadon ta kwanta ta janyo bargo ta lullu’be rabin jikinta ta jingina bayanta da abun gado sai dai ta kasa runtsawa sai faman tunanin yadda zata shawo kanshi take ..”
Matsowa tayi ta dawo bakin gadon ta tsura masa kyawawan idanunta tana kallon yadda yake sauke numfashi ,a hankali qirjinta ke dokawa, ta dinga jin kamar zuciyarta zata fito daga qirjinta , tuni hawayen suka wanke mata fuska tausayin kanta ya kamata “daman tasan dole sai ta fuskanci irin wannan matsalar atare dashi , gashi ita yanzu babu abinda tafi bukata kamar kulawarsa da samun zaman lafiya a tsakaninsu “
“wallahi bazan taɓa yarda ba sai nayi galaba akanka , sai na mallaki zuciyarka kamar yadda ka mallaki tawa cikin sauki batare dana shiryawa hakan ba tayi maganar a kasan ranta tana cigaba kallon fuskarsa bata san sanda gigin soyayya ya sauko daita daga saman gadon ba , ta ra’ba ta kwanta a gabansa ta zare pillow dake manne a qirjinshi ta maye gurbin pillow dake qirjinshi ,cikin rashin sani ya rungumeta tsam ajikinsa yana sauke numfashi , cikin sanyayyiyar muryarta tace “dan Allah ya Aliyu kayi hakuri ka barni na rayu a karkashin ka “ta k’arasa maganar gabanta na tsananin fad’uwa , tasan bancin kuskurenta na baya da babu abinda zai hana aliyu sonta …”
Sake shige masa tayi ta zuba masa kyawawan idanunta tun daga kan kwantaccen sumar kanshi take bi da wani mayataccen kallo ,
Sosai ta fuskartashi tare da kai fuskarta daidai nashi tana zuko numfashinsa ,wani irin sanyi taji yana ratsa sansar jikinta , laulausan tafin hannunta ta kai cikin rigar baccinsa ta kife hannunta akan qirjinsa dake kwance da gashi tamkar na jarirai ,a hankali ta soma murza kan nipple’s d’insa wani irin yanayi ya tsinci kansa cikin bacci ,ya shige jikinta batare daya san yayi hakan ba, lumshe ido tayi dan dadi” ina ma idonsa biyu yake rungumeta daita cikin kulawa da farinciki ?”Ina ma zai bata dama daya sha mamakinta , dan kuwa sai tayi nasarar dasa soyayyarta a cikin zuciyarsa batare daya shiryawa hakan ba “
lip’s dinta ta d’aura akan lip’s d’insa ta kamo tana tsotsa a hankali tamkar ta samu sweet tana murza kan nipple’s d’insa , wani irin zirrrrrrrrr yaji a gabad’aya ilahirin jikinsa mai kama da shocking , wani irin zabura yayi saboda sakonta yaje masa har cikin ‘kwa’kwaluwarsa ,a hankali ya bude idanunshi ya zuba mata fuskarsa dauke da damuwa mai tattare da miskilanci, sake shige masa tayi tana sauke numfashi dan gabad’aya yanayinta ya fara sauyawa “ba tsaya ‘batawa kanshi lokaci ba ya fizgeta a jikinsa yayi jifa daita kamar wata ƙaramar yarinya.”
qara ta saki mai sauti tare da rike daidai kugunta da hannuta ɗaya tana ciza lip’s dinta “kina hauka ne ? “ko ance miki nima ɗan iska ne irinki da zaki wani kawo min wasan iskanci”?runtse idanunta tayi sai ga hawaye sharrrrrrr daga idanunta sun zubo “wallahi idan baki kiyayeni ba zan ‘bata miki rayuwa , zan karyaki kuma na karya banza dan ko gurin mai d’auri bazan kaki ba wawa wawiyar bazan kawai da bata san ciwon kanta ba “
Yana gama fadar haka ya koma ya kwanta tare da juya mata baya.
a hankali sautin kukanta ya dinga tashi a d’akin kusan minti goma ta ɗauka tana zaune tana kuka rike da gefen kugunta “wayyo kuguna wayyo dady , wayyo mummy , wayyo aryan ,wayyo arif zan mutu ……”
duk yan gidansu babu wanda bata kira ba , yana jinta yayi mata banza a ransa yace” baki ga komai ba tukunna, ba dai takamarki naci ba ? “sai na maida rayuwarki abun kwantaccen ,sai canza miki kamani , sai miki illa a rayuwarki ta yadda mutane idan sun ganki zasu kasa ganeki , sai data ci kuka mai isarta sannan ta rarrafo ta dawo inda yake kwance ta zauna tana sake girka sabon kuka da kiran zan mutu ,mutuwa zanyi ka kira min babana da mamana mutuwa zanyi ya Aliyu “ya tashi zaune a matukar fusace “ooooooooo wai meye haka ne da zaki hanani bacci ? “Kuguna ke ciwo mutuwa ma zanyi ka daina min ihu idan na mutu ai ka huta “
“sosai kuwa wallahi na huta da jaraba da naci ” ta tsurawa kwayar idanunshi ido tana kallonsa cike da mamaki, “laila a illalla muhammadur rasulullah Sallallahu alaihi wasallam ta shiga furtawa tana runtse idanunta numfashinta na sama da kasa ” “ke ……..” yayi magana tare da girgiza kanta cikin tashin hankali, fuskarta ta sake narkewa tana ƙoƙarin zu’bewa a kasa “ke ki bude idonki mana, kin budewa tayi ta tsaya batare da ta kai kasa ba , ta ɗan kanne idonta ɗaya daman bawani ciwon kirki taji ba so take ya bata kulawa, numfashi ya sauke yana furzar da iska ,yayinda idanunshi ke kanta yana karanta yanayinta gabad’aya ya gama fahimtarta dan haka ya mike tsaye da hanzari .
” Maza ki tashi tsaye”
“ai bazan iya tashi ba “what ? ya furta a fusace. “bazan iya tashi ba ta sake furtawa a shagwa’be idonta na tsiyayan ruwan hawaye”
” ki tashi tsaye nace, wallahi idan baki tashi ba zanyi kwallo dake sai kanki ya bugu da bangon d’akin nan shegiyar kwalmashashiya kawai mai fuskar alade ,zaki tashi ko kuwa sai na fara kwallo dake ?
zumbur ta mike jikinta na kyarma tana mamakin jin furuncisa sam batayi zaton haka halinsa yake ba asanin data masa shi mutun shiru shiru , bata taɓa jin furucin zagi daga bakinsa bare kalmar kwalmashashshiya .
“yar iska yarinya kawai kin ɗauka nima ɗan iska ne irinki? ” maza ki kama gabanki mara zuciya ”
Tafiya ta soma yi a hankali tana waigensa har ta karaso bakin kago ta hau kan katifa ta kwanta lamo tana mamakinsa yaja tsaki tare da komawa ya kwanta ruf da ciki ..”
Da misalin ƙarfe biyar na asuba ya tashi domin gabatar da sallar , bai tasheta ba yaje yayi alwala ya fito, motsinsa ya tayar daita ta tashi ta shiga bayi ta d’auro alwala ta fito ta gabatar da sallah “bayan ya idar yayi addu’oinsa wanda ya zame masa jiki ,ita kan duk adduarta akan shi ne , ya koma ya kwanta akan doguwar kujera itama gado ta haye ta koma bacci , gari na wayewa ta rigashi tashi ta shiga bayi tayi wanka ta shirya sannan ta haɗa masa ruwan wanka ta fito ta tsuguna a gabansa ta kai bakinta daidai saitin kunneshi tana hura masa iskar bakinta, a hankali ya buɗe idanunshi tana durkushe kusa da jikinsa , wannan abu ya ‘bata masa rai “jaraba……” ya furta a fili sam taki zuciya ,ya mike tsaye batare da yayi mata magana ba, itama mikewa tayi ta tsaya a gefensa tana wasa da zara zaran yatsun hannunta “uhmm na haɗa maka ruwan wanka ka shiga kayi wanka “na saki ? yayi mata tambayar yana jefanta da wani mugun kallo , ta girgiza masa kai tace “uhmm naga hakina ne ba sai ka sani ba “to karki sake bana so okay”
ya wuce ya barta tsaye ya shiga bayin , yana shiga ya zubar da ruwan data haɗa masa ya haɗa wani yayi wanka ya fito kugunsa d’aure da farin towel tana ganin fitowarsa ta juya masa baya sakamakon ganin qirjinshi a buɗe dan hakan nasata jin wani iri ajikinta , tsaki ja a ranshi yace “munafuka kawai kalleta kamar ta Allah nan kuwa kasurgumar yar ta’adda ce “
Lotion ya mulka a tafukan hannunsa ya soma bin jikinsa yana shafawa , ya fesa turare, cumb ya ɗauka ya gyara sumar kansh ya karasa jikin wordrobe gefen daya ga ta jera kayansa ya buɗe ya dauki suit ash colour da vest fari da boxcer fari ya karaso gaban mirrow ya tsaya ya ajiye kayan akan ƙaramin stood yana sanya boxcer da vest , ta ɗan juyo ta gani ko ya gama shirin , ganin ya saka vest da boxcer yasa ta juyo gabadaya ta tsura masa ido kawai batare da tace komai ba .
a natse ta soma takowa zuwa inda yake tsaye yana ƙoƙarin saka dogon wandon suit ta ɗauki farar rigar suit zata saka masa, a hankali taji sautin muryarsa ta doki kunneta wanda ya haddasa mata jin mummunar faduwar gaba “ajiye min riga wai ke wata irin jarababbiyar yarinya ce mara zuciya ? Ta numfasa kana tace “ta ya zanyi zuciya da lamarin mijina ? “aljannata nake so kaga kuwa samunta da wuya da wahala ,wata uwar harara ya watsa mata ya fixge rigar daga hannunta ya saka ya tura cikin wandonsa ya soke belt ,ya da’ura yar saman suit d’insa ya sakawa kafafunsa safa tare da takalmi ash , ganin ya gama shirinsa tsaf jaka aikinsa kawai ya rage ya ɗauka ta karasa da sauri inda taga ya ajiye
ta dauko, wani kallon raini yayi mata yana kallonta a wulakance , sai lokaci yayi mata kallon tsaf tun daga samanta har kasa sanye take cikin jar riga doguwa wacce bata kai kasa ba mai kama jiki sosai dan sunyi bushing brest d’inta kasancewarta mai wadatattun dukiyar fulanin ,kanta sanye da hula mai kalar riga, kafarta sanye da jan takalmi silifas, fuskatar kwance da murmushi wanda bai san ko na meye ba amman yafi kama dana iskanci .”
“ka barni na rike jakar dan Allah iya kasan gida nan kawai zan rakaka fa “ki fita hanyata ance miki barinki zanyi a d’akin nan ai wucewa zakiyi ki komai parlour’n kasa na kulle d’akina ” ya fixge jakarsa da karfi tare da juyawa , hannusa rike da jaka ya buɗe kofa ya tsaya a bakin kofa yana jiran fitowarta ..”
Da sauri ta shege bayi ta danna key “wallahi bazan zauna a parlou’n kasa irin na jiya ba , tayi maganar muryarta cike da shagwa’ba , cike da sanyi jiki ya dawo cikin d’akin ya k’arasa bakin kofar bayi “a she zaki sha wahalar data fi na jiya dan kulleki zanyi a bayi kuma na kulle d’akin sannan na kulle ko’ina a gidan nan , tunda kika zabi rayuwa dani kin zabarwar kanki tashin hankali da matsalar rayuwa iri iri, bazan taɓa saurara miki ba , dan kece mace ta farko dana tsana a rayuwata yana gama fadar haka ya juya zai bar d’akin da niyyar kulleta ciki ta bude kofar bayin ta fito da gudu ta matso kusa dashi fuskarta a shagwa’be ta tsaya tana kallonsa cike da matsanancin sonshi “ina sonka ya Aliyu me yasa bazaka soni ko dan darajan su ar…….?
” Shot up bazaki taɓa cin wannan darajan ba har abada yayi saurin katseta ta hanyar fadar haka ,sake matsoshi tayi kamar zata shige jikinsa tana busa masa iskar bakinta, yayi saurin matsawa baya yana watsa mata wani banza kallo “kina son shige min ,okay nasan dalili saboda yanzu idanunki sun buɗe kin gane wanene aliyu , Kinga aliyu ya dawo had’ad’d’en gaye fiyye da yadda kika sanshi ga kyau ga kudi ga ilimi ko ” ?
tayi tsam da ranta tana cigaba da kallonsa qirjinta na dokawa da karfin gaske a hankali ta shiga girgiza masa kai alamun ba haka bane “karki ‘bata min lokaci da iskanciki na banza da wofi fitar min a d’aki na kulle “zuciyarta na cigaba da bugawa da karfi ta ra’ba ta gefensa ta fita daga d’akin tafiya take kamar wacce bata da isasshen lafiya tana zance zuci har ta karaso parlou’n kasa taja ta tsaya tana jiran fitowarsa, ta gabanta ya wuce ya hau wani ƙaramin table zai kashe wutar gidan “dan girman Allah karka kashe wutan ka barshi karka barni cikin duhu “wannan ne kuma baki isa ba yarinya da yunwa da rayuwar duhu zan miki izaya har sai kin mutu ta turo masa ƙaramin bakinta a ranta tace “ya cika taurin kai da shegen jaraba kamar mutanen farko ai sai ka kashe tunda kayi niyya “
“me kika ce? ya juyo yana kallonta , tayi saurin daidaita natsuwarta tana girgiza masa kai alamun babu komai” na ɗauka wata maganar banza kika yi na sauko na ci ubanki na kara miki da dukan mutuwa , tasan tunda ya furta , zai aika dan haka ta shiga hankalinta ya sauko ya juya yana taku daya bayan daya ,sautin takun takalminsa ne kawai ke tashi a parlou’n ta zubawa bayansa ido har bata son kiftawa ya fice daga parlou’n ya kulle kamar jiya ….
Naunayen ajiyar zuciya ta sauke ta zauna a hannu kujera tana mamakinsa a hankali ta mike ta nufi gurin changeover ta hau kan kujera daya hau dan canza abun wuta amman tsawonta bai kai ba “wato dan yasan tsawonta bazai kai ba ne yake kashe wutar gidan saukowa tayi tana tunanin yadda zatayi idanunta ya sauka abakin kofar kitchen wani irin tsalle tayi sakamakon ganinsa a buɗe da tayi ,sauri lekawa tayi ko’ina duhu bata iya hango komai saboda kofafin window a rufe suke parlou’n ta sake dawo ta tsaya can ta matso gurin center table ta durkusa ta soma turawa , wani irin karfi taji har sai da tafin hannunta yayi zafi ta kalli hannunta tana yarfewa sannan ta kara kai wa jikin table ta dinga turawa har ta kawo gurin abun canza wuta ta d’aura kujerar daya hau akan Center table ta hau da kyar kamar zata fadi tana girgidi har ta samu nasarar canzawa take gidan yayi haske ta sauko tana sauke numfashi ta shiga kitchen ta kunna wutar kitchen ta kunne ac sannan ta soma bubbude kitchen cabinet, babu komai acikin ta bude frizer shima babu komai dan akashe ma yake , kawai ta daura hannuwanta duka aka ta rushe da kuka “shike nan ya aliyu zai kasheni da yunwa ” jikin window kitchen din ta koma ta bude hawaye shabe Shabe a kwance a fuskarta mai gadi ta hango zaune ta sauke numfashi tana kallonsa ta rasa abinda zata faɗa, masa ita ba yaren garin take ji ba bare ta kirashi, hakan jikin mai gadi ya bashi ana kallonsa , ya waigo idanunsa ya sauka akanta yayi shiru yana kallonta har sanda tayi masa alamar yazo da hannuta da sauri ya karaso ta lumshe idanunta na second daya sannan tayi masa alamar tana bukatar abinci .
hannu ya kai bakinsa shima tayi saurin gyada masa kai, da hannu yayi mata alamar yana zuwa ta juya da sauri ko cikakken minti goma bai ɗauka ba ya dawo hannusa rike da takeway ya mika mata ta amsa tana godiya ta zauna akan kujera data gani a kitchen din ta bude soyayyiyar shikafa ce da soyayyiyar kaza da ruwa ta soma cin abinci kafin kace me ta tashi da abinci tas har wani gumi ne ya rufeta , ta rufe takeway ta maida cikin ladar ta sake dawowa bakin window bata ganshi ba dan haka ta tura tasan idan ya dawo zai gani ya ɗauke , ta nufi sama da niyyar gyaranwa sai tunawa datai ya rufe dakin , ta dawo kasa ta soma gyarawa sai data gyara ko’ina tsaf sannan ta mike a saman doguwar kujera ta kwanta tana tunanin rayuwa “wai ita ta Aliyu yake wulakanta ? wannan abu ya tsaya mata a rai lallai duniya juyi juyi ne abinda kafi karfi wata rana shi zai fi karfinka “
Misalin karfe uku na rana ya shigo parlou’n gidan bayan ya bude cike da matsanancin mamaki yake bin parlou’n da kallo kafin idanunsa ya sauka akanta kwance akan doguwar kujera tana sauke numfashi a hankali iskar parlou’n sai faman kada gashin kanta yake a saman kafad’unta yana neman rufe mata fuska take wata irin tsanarta ta kuma sakko masa cike da takaici yake dubanta .a hankali ya dinga takowa har ya karaso inda take kwance bai tsaya wata wata ba ya sauke mata mari har biyu a fuska…..
*Domin bukatar karanta novel dina kyauta a sauke manhajar Aysha a bagudo ta hanyar shiga wannan link din dake kasa* 👇🏻
https://play.google.com/store/apps/details?id=aysha.a.bagudo.all.books.pro
Mmn Sudais
💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗