Cutar Da Kai – Chapter One
by Aysha A Bagudo~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
Free page
*AYSHA A BAGUDO*
*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*
bismillahirrahmanirrahim
EGYPT
*Reehab* unguwa ce dake cikin babban birnin kasar cairo , unguwa ce data tattare kan manya attajiran masu kudi , zagaye da had’ad’dun gidaje masu kyau da tsari kamar yadda gidan
muhammad realwan yake d’aya daga cikin jerin gidajen unguwar .
Babban katanfarin fili ne wanda aka gina madaidaicin gidajen sama guda uku a cikinsa mai hawa ɗay d’ay, tun daga bakin get din gidan har zuwa babban parlou’n gidajen ciki zaka fahimce yadda had’uwar gidan yake , babban parlou’n ne wanda ya kunshi duk wani nau’i abubuwa na more rayuwa da qawata muhalli , idan mutun yana parlou’n zai ɗauka a wata duniyar yake ba’a wannan duniyar tamu yake ba.”
makakeken tv bango ne manne da bango kowani parlour dake cikin gidan, ga wani katon wutan lantarki a saman parlou’n mai jere da fitilu masu matukar haske riras ,ga masuburbud’an sanyi , ga makaken dining table zagaye da kujeru na alfarma , yayinda parlou’n yake zagaye da fararen kujeru masu ratsin baki ajiki , banda kitchen da bayi kwaya daya tal da landury , babu d’aki ko daya a cikin parlou’n .”
yayinda sama gidajen ke ɗauke da dakuna guda biyu da parlour d’aya Alhaji realwan ya gina wannan katafarin gidan ne saboda ya’yansa Aliyu da samir da shi kansa idan ya kawowa kasar ziyara , yadda tsarin ginin Samir yake haka na Aliyu yake babu wani bambamci , komai iri ɗaya aka zuba acikinsa “.
Wata matashiya mace ce raku’be a akan kujera a matukar tsorace take a parlou’n saboda girmansa, ta takure jikinta guri ɗaya saboda duhun parlou’n ga yunwa dake tattare daita , tun jiya da suka sauka a kasar bata ci wani wadataccen abinci ba ,tunanin yadda tahowarsu ta wakana take , tun da suka shiga jirgi yake cicccin magani wanda a idanun iyayenta ba haka ya nuna ba, cikin sakin fuska da farinciki suka rabu da iyayensu , jirgin na gama mikewa a sararin samaniya ta nemi murmushin dake kwance akan fuskarsa ta rasa, fuskar ta dawo tamkar hadari ko ta wani mayunwacin zaki ,a hankali ta d’aura kanta a kafad’ansa ta ɗan d’aga idanunta kaɗan ta kalleshi , bai motsa ba , hasalima wani bangaren yake kallo yana danne danne a wayarsa tamkar babu wata halitta atare dashi ,a hankali hancinta ya dinga zuko mata dad’ad’d’an kamshin turaren jikinsa dake gauraye da kamshin skin dinsa , a natse ta sauke numfashi kamshinsa na sake mata dadi ,duk wannan shiru da yayi a lokacin tasan zuciyarsa cike take fal da jin haushinta ..”
Jin bai yi magana ba har lokacin yasa taki buɗe idanunta , tayi lamo tana cigaba da shakar kamshinsa a haka bata san lokacin da bacci ya ɗauketa kanta na kan kafad’ansa ba.
ji kanta ya bugu da kujera yasa tayi firgigib tare da bude idanunta da sauri ta furta “oooooo ta dafe gefen kanta tana kallonsa , ko kallon inda take bai yi ba , bama zakace shine yayi muguntar ba, Allah Allah ya dinga yi su isa dan baya sonta a kusa dashi ,yayinda bangarenta kuwa babu abinda tafi qauna da muradi kamar kusancinsu tare ..”
Suna sauka a kasar cairo motar campanie dana escout dinsa na tsaye zaman jiran karasowarsu , kai tsaye Aliyu Muhammed realwan ya wuceta ,
cikin sauri itama ta gyara zaman handbag d’inta ta biyo bayansa dan tasan ba karamin aikinsa ya barta agurin ba , escout dinsa na hangosa suka hanzarta k’arasowa inda yake cikin girmamawa tare da buɗe masa gidan bayan ,ya shiga ya zauna yana gyara zaman rigar suit din jikinsa , cikin hanzari itama ta shiga inda taga an buɗe masa ta zauna gabanta na faduwa ,
gama saka jakunkunan kayansu ke da wuya direba yaja motar suka bar gurin escout dinsa na biye da motar da yake ciki a baya .
Koda suka iso gidan ko’ina a gyara yake tsab kasancewar Companie club ɗinsa man United sun san dawowarsa dan haka suka sanarwar masu aikin gyara gida ,
tsayawa tayi a parloun gidan , shi kuma cike da kuzari ya hayewarsa sama , ganin haka yasa ta biyo bayansa da sauri tana shiga d’akin da ta gani a bude wayarsa ta ɗauki qara ,hannunsa rike da kugunsa ya k’arasa jikin window ya zuge labule window yana kallon haraban gidan, maganar minti goma yayi yace “gani nan zuwa ya maida wayarsa cikin aljihun wandonsa ya juyo inda take tsaye “fitar min a d’aki ” ya furta a fusace .
jiki a sanyaye ta fito ta tsaya daga bakin kofar d’akin ya fito ya kulle ya sauko zuwa parloun bayansa ta biyo ta tsaya, tana tsaye mai gadi ya shigo da manya jakunkunansu ya juya ta kasa zama tana kallonsa ya kashe wutan gidan gabadaya sannan ya fita tare da kulle kofar parloun bai dawo gidan ba sai tsakar dare lokacin tuni bacci yayi awon gaba daita akan doguwar kujera .
idanunshi ya tsura mata cike da takaicin ganin yadda take bacci ya balain bata masa rai ya shiga kitchen ya buɗe fridge ya d’auko roban ruwa mai sanyi ya fito ya tsaya akanta ya shiga tsiyaya mata tun daga tsakiyar kanta har sansar jikinta ta farka a matukar firgice , yana ganin ta buɗe idanunta ya ɗauke idanunshi akanta tare da cilla mata roban ruwan da yayi saura ajikinta ya haura step ,da sauri ta mike ta biyo bayansa tana masa magana yayi mata banza , bakin gado ta samu ta zauna tana kallon jikinta dake jike , ta zabga tagumi tana kallonsa ya buɗe bakar jakarsa ya fito da takeway , snaks da cake ne aciki sai driks ya zauna kan doguwar kujera ya mike kafafunsa ya cinye tasssss ya da’ura driks akai sannan ya mike ya shiga bayi ya watsa ruwa ya fito , haka suka kwana batare da yayi mata magana ba ko damuwa da bata abinci ba .”
To yau ma tun safe daya bar gidan bai dawo ba har gashi shabiyu da rabi na dare ta buga , tana cikin wannan tunani taji motsin shigowar motarsa ba’a fi second biyu da shigowar motarsa ba taji yana ƙoƙarin buɗe kofar parlou’n naunayen ajiyar zuciya ta sauke , haske wayarsa ne ya gwauraye parlou’n, idanunsa ne suka sauka akanta takure guri daya , a natse ta d’ago kyawawan idanunta ta sauke su akanshi yana tsaye kikam kamar wani soja rashin wadataccen hasken parloun bai hanata karewa kyawawar fuskarshi kallon tsab ba , ita ba dawowarsa bace abin daga hankali da fad’uwar gaba irin yadda gaba-daya siffarsa ta sauya ,idanunsa dake kanta cike suke da bala’i iri iri ,fuskarsa nan nashi tamkar ba’a taba saukar da rahma akanta ba , tana kallonsa ya nufi gurin meter yayi changeover yana jan tsaki , a yadda ta lura babu abinda ya tsani gani kamarta ..”
Ya waigo bangaren da take zaune ,yayi mata kallon second biyu sannan ya ɗauke idanunshi akanta yana sake jan tsaki ya nufi sama ya tsaya tare da tura hannu cikin aljihunsa ya ciro key ya bude kofar d’akinsa ya shiga ya tsaya gaban mirrow yana sausauta tie d’insa tare da cire yar saman suit d’insa ya ajiye wayoyinsa akan dres mirrow ya kwance agogon dake d’aure daa tsintsiyar hannunsa ,ya kife jikinsa bisa gadonsa tare da talla’be kansa da duka hannuwansa, yayinda kafafuwansa ke kasan tayis yana girgizawa a hankali cikin jin kai .”
a hankali ta turo kofar d’akin ta shigo bakinta dauke da sallama tana d’aga kafafunta da kyar tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki ta karaso inda yake ta durkusa a gabansa “sannu da zuwa ta furta cikin kasalalliyar muryarta mai sanyi da shiga jiki sannan ta soma ƙoƙarin kwance masa igiyar takalmin dake sanye a kafafunsa ta kai inda taga jerin takalmansa suke , ta dawo zata taɓa masa kafa domin cire masa safarshi ,yayi saurin janye kafafunsa yana jan tsaki “tana son kusancinta dani mayyar yarinyar kawai yayi maganar a kasan ranshi yana jan tsaki shiru tayi jikinta na rawa muryarta a raunane tace “yunwa nake ji ya Aliyu tun abinci jiya ne a cikina ,ka fita ka kulle ko’ina a gidan nan daidai da ruwan sha sai na bayi na sha ka taimaka min da abinci yunwa nake ji tayi maganar hawaye na gangaro mata “
“ina ruwana da jin yunwarki ,da rayuwarki da mutuwarki duk daya ne agurin Aliyu ,da zaki mutu ma wallahi sai Aliyu yafi kowa farinciki a duniya ,har mafarkin nayi kin mutu an zo zaman makoki nace bana bukata kowa ya kama gabansa .. ….”
“saboda me ya Aliyu kake min irin wannan fatan “? tayi maganar tana mikewa tsaye jikinta na rawa “saboda bana sonki , baki da amfani komai agurina , banci zuciyar muslunci da darajan iyaye wallahi da a kasar zan kasheki da hannuna ki mutu ,dan gara mutuwarki dana yi rayuwa dake ….”
mutuwar tsaye tayi cikin tsananin tashin hankali da matsanancin gigita jin furucinsa yayinda hawayen idanunta ya karu suka shiga kokuwa da juna gurin silalowa ga wani irin kyarma da jikinta ke yi , sai dai rawar da jikinta ke yi ya sanyata saurin durkushewa a gabansa domin kafafunta sun tabbatar mata bazasu iya cigaba da ɗaukar gangar jikinta ba, baya ga haka ma ga wani iri jirin yunwa dake d’awainiyya daita .
Wani irin bugawa kanta ke yi tamkar zai rabe gida goma , a hankali muryarta ta fito “idan ka cigaba da tunanin abinda ya rigada ya wuce bazaka taɓa daina tsanata ba a cikin zuciyarka “. “bazan ta’ba dainawa ba Kinga kuwa bazan taɓa daina tsanarki ba ,”shi fa so halitta ne da …….
” bar dakin nan stupid tun kafin nayi losing control , dan ina jin bakinciki kasancewata dake yayi maganar a zuciye cikin tsananin fushi da tashin hankali mara misaltuwa “
Bata bar d’akin ba kamar yadda ya furta sai rarrafawa tayi ta koma gefen doguwar kujerar kushin kwaya daya dake d’akin ta rakube , tana kallonsa ya mike ya shiga bayi batare daya cire kayan jikinsa ba saukar ruwa a bayin yasa ta fahimci wanka yake a hankali yunwa ta dinga nukurkusanta , ta rike gefen cikinta tana had’iyar miyo da kyar tare da share hawayen dake tsiyoyo mata, tasan mugunta yake mata saboda baya qaunarta .
wasa wasa sai da yayi kusan awa ɗaya a bayi bai fito ba ,sake rarrafawa tayi ta k’arasa inda jakarsa take saboda tunanin jiya a ciki taga ya fito da cake yaci ya da’ura lemu ya kwanta yayi banza daita, ta buɗe jakar aiko nan idanunta suka sauka akan cake da ruwan roba da driks , jikinta na rawa ta ciro farar laida ta fito waje ,tun daga kan step ta soma cin cake din kamar wata mahaukaciya ..”
A natse ya fito daga bayi kugunsa d’aure da farin towel Wanda kad’an ya zarta gwiwarsa yaga wayam babu alamun ta , numfashi ya sauke” crazy girl kawai da yunwa kadai zan iya azabtar da rayuwarki , tsawon awa guda yana shirin bacci ya gama tsab ya karaso gaban jakarsa ya buɗe da niyyar ɗaukar cake dinsa ya ga wayam ya sake dubawa bai gani ba , shiru yayi na second biyu ,can ya nufo parloun kasa a zuciye kafafunsa sanye da silifas masu matukar kyau waɗan da suka dace da zara zaran yatsun kafafunsa “ke uban wa yace ki ɗauki cake din can “? dan ke na siyo ko da kudinki na siyo “?
tayi shiru tana sauke numfashi da ajiyar zuciya dan tuni ta cinye cake din neman kari ma take “idan kika sake kuskuren taɓa duk wani abu nawa a cikin gidan zan ci uban. ……..
Shiru yayi ya kasa karasawa , ta mike daga zaunen da take ta soma takowa a hankali har ta karaso gabansa ta tsaya qirjinta na bugawa da matsanamcin karfin gaske “ka k’arasa mana , ka zagi mutumin daya inganta rayuwarka fiyye da ya’yan cikinsa ka zageshi mana ,me nene idan ka zageshi “.?
juyawa yayi zai bar gurin tayi saurin riko laulausan tafin hannunsa cikin nata tana murzawa a hankali “a ina zan kwanta bacci nake ji sosai “fixge hannunsa yayi da karfi ” ban sani ba ya haye sama ya shige d’aki .
Ajiyar zuciya ta sauke bayan barinsa gurin jikinta a sanyaye ta biyosa zuciyarta na rawa, kai tsaye bayi ta shiga ta watsawa jikinta ruwa ta d’auro alwala ta fito d’aure da towel ta karasa inda jakar kayansu yake a tun jiya da suka zo bai barta ta samu damar jera kayansu cikin wordrobe ba , ta buɗe ta ciro doguwar rigar mara sharara ta zira ajikinta kallo inda yake tayi a daidai lokacin daya waigo idanunsu suka tsarke cikin juna wani abu yaji ya tsarga masa , boyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke yana jan tsaki a zuciyarsa cike da jin sabuwar tsanarta , ta ja masa kwana da yunwa tunda ya fita bayan coffe da cake babu abinda ya ci gyara kwanciya yayi ya juya mata baya yana furta kalmar “yar iska yarinyar kawai ..”
Turare ta d’auko mai sanyi kamshi ta feshe ilahirin jikinta ta ciro hajib ta zira ta kalleshi “ina ne gabas zan yi sallah ? da hannu ya nuna mata ta juya ta kalli inda ya nuna mata sannan ta tada sallah raka’a biyu tayi ta zauna tai addu’a akan Allah ya karkato mata da hankalinsa ya fahimceta bayan ta gama ta mike ta janyo jakunkunan kayansu ta karasa gaban wordrobe ta buɗe ta soma jira nata sannan ta jira nashi ta bude wani bangare da babu komai ta sanya jakunkunan ta juyo ta saci kallonsa idanunshi na runtse yayi pillow da hannunwansa ta hawa kan gadon ta kwanta, tana gama kwantawa ya mike kamar wanda aka tsinkara ya dauki pillow ya koma kan doguwar kujera ya kwanta ta tsura masa ido daga inda take tana masa kallon mamaki, a hankali tun tana jin motsinsa har ta daina ta sauko daga kan gadon ta tsaya a gabansa tana karewa masa ..
Dogo ne sosai sai dai bashi da jiki can sannan ba irin siraren mazan nan bane , yana da faffadan qirji da wadatar kafad’u , doguwar fuskarsa mai ɗauke da dogon hancinsa zarrr tamkar biro ,bakinsa dan karami ɗauke da pinky lip’s , girar idanunsa kuwa garza garza ne yayinda kirjinsa da sansar jikinsa ke kwance da kwantaccen gashi tamkar ta jinjirin da’aka haifa yau , fari ne tasssss shiyasa pinky lip’s d’insa ya sake fito da ainihi kyawun da Allah yayi masa , a hankali ta tsuguna bisa gwiwowinta tana cigaba da kallon kyakkyawar fuskarsa, sai wannan lokacin ta lura da irin baiwar da Allah yayi masa, hannu ta kai tana shafa gefen fuskarshi zuwa kan lip’s dinsa tana lumshe ido a hankali ya buɗe idanunshi ya ganta durkushe a gabansa tana shafa fuskarsa , saurin zaro ido yayi waje yana buge mata hannun tare da tashi zaune yana kallonta “kina hauka ne” ? ta girgiza masa kai alamun a’a “kifa shiga hankalinki dani banason wannan iskanci naki dan lura kina son shishige min,sai dai duk abinda zakiyi bazai sa na saurareki ba “karka sake kiran ta’bawar da nayi maka da kalmar iskanci dan kai mijina ne na sunnah ni matarka ce meye abun iskanci anan “?. ta karasa maganar tana shafo qirjinshi yayi wata irin zabura ya mike tsaye tare da damkar tsintsiyar hannunta ya buɗe kofar ya tura waje da iyakacin karfinsa ya maida kofar ya rufe garam da karfi yana jan dogon tsaki “dakikiya kawai mara kamun kai “. tayi shiru tana kallon kofar d’akin zuciyarta na rawa .. ….”
Mmn Sudais
💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
Free page