Turken Gida – Chapter Fifty-six
by Janafty*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*
Rawan jiki da ɓare-ɓare kam Yallaɓai na yin shi a kan cikin Rabi’atu ga shi cikin na ta ya zo da laulayi ga shi ba ta son cin abinci in ku ka ga yadda Yallaɓai ke lalacewa a gaban yarinyar sai kun yi mamaki. Ni kuma duk abin da ta ce tana so haka zai marairace yana roƙo na domin na samar mata, ni kuma tausayi take ba ni ko bakomai nima uwa ce, wani lokacin kuma Baby yake sawa dafe-dafe nan Gimbiya dai ya san ko giwan wake ya sha ba zai tunkareta ba domin ba ma yi za ta yi ba iyakarta da Rabi’atu sannu Allah ya ƙara lafiya.
Kwanciyarta asibiti biyu sannan ta ɗan samu kanta sai da ta koma gida ta yi satuttuka. Antynta ta ɗauke ta ganin wahalan da take sha, Yallaɓai ya so ya hana na dakatar da shi da cewa ya barta a gidansu a kula da ita. Ya bari ɗin amma fa can yake tarewa in ya dawo daga aiki sannan ya dawo gida ya zaunar da ni yana bani labarin in na ga Rabi’atu sai na yi mata kuka ta rame kaza kaza, ni har gajiya na ke yi kamar a kanta aka fara samun ciki su ‘ƴaƴan gidan ba a gaban sa aka samu cikinsu ba daga sama ya gan su, duk dauriyata sai da ya riƙa motsa mini zuciya. Tana gidansu sau biyu yana sakani muna zuwa duba ta ni da yara Gimbiya dai an tashi zuwa sai ta ce ba ta da lafiya duk da ya san ƙaryanta ne ba ya matsa mata sai ni. Ni dai na yi sakacin da gabaɗaya Yallaɓai ya gama raina ni in dai akan lamarin matansa ne ko abu ne ba zai tunkari Gimbiya ba sai ni. Saboda ina yi masa kara shi kuma hakan sai ya bashi damar ya rika cin ko wata kasuwa a saman kaina , yanzu kuma lokaci ya kure mini na yi sakacin da ba zan gyara komai ba tun farko da ban bashi fuska zan iya ɗauka ba da wataƙila nima zai shakkar tunkarata da sha’anin matarsa kamar yadda ya ke jin shakkar tunkaran Gimbiya.
Ba ni kaɗai ba dangin shi ma sun ta sintirin zuwa duba ta zuwan mu na ƙarshe can na ga Halima ta yi baje-baje kamar a falon Nene ban yi mamaki tun fa yanzu ai Rabi’atu uwar ɗakin ta ce. Gimbiya ta ɗauka bayan ita ba wata macen da Yallaɓai da dangin sa za su yi ma rawan jiki saboda samun ciki sai ta ga ma suna abin da ya fi wanda suka yi mata a baya. Sai ta sha mamaki domin tun cikin na ƙaramin sa Yallaɓai ya gama tsara in mace ne ga sunan da zai saka Aisha in namiji ne kuma Alhajinmu zai yi ma takwara zai yi zai yi kaza har na haddace su a kaina.
Gimbiya ta yi ta ƙunci in an yi wani abu da ya bata haushi ta same ni da mganar na gani ko? Na ce na gani mana amma ban nuna na ji ko na gani ba itama in ta yi haka sai ta zauna lafiya. Amma ba ta ji shawarata ba kafin Rabi’atu ta dawo gida sai da suka yi tsiya akan ranar girkinta yana kai wa dare a can. Ta ga fa nima har ranar da yake ɗakina abin da yake yi kenan amma ta na gani ban ma na nuna na gane abin da yake yi ba, amma ita da shegen kishi ta yi masa mgana har tana saka ni a ciki wai na faɗa masa gaskiya ba ya adalci tunda yana jin mgana ta.
“Tana gidan nan ma rashin adalci yake yi mana Maman Jidda. Ba ta gidan ma ba zai daina ba.”
Ina zaman zamana a bangarena ta kira ni a waya sha ɗaya saura na dare. Na ji dawowarsa ba daɗewa ni na ma ɗauka wani abu ne ya same shi amma sai na iske shi zaune fuskar nan kamar hadari ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya a saman kujera yana karkaɗawa alamun yau fa akwai masifa in Gimbiya ta cigaba da zungurin sa. > Janaftybaby: Kallonta na yi, Baiwar Allah ta yi masa kwalliya da fa zafi ka zauna jiran miji har sai ka siƙe sannan zai dawo. Amma yanzu in na ce bai kyauta ba daga ni har ita zai iya cewa mu bar masa a gidansa a yadda dai yake zaman taƙama nan yana kaɗa kafa ji yake yi yana daidai da koma wacece.
“Fisabillahi yana kyautawa? Sai ya je ya shantake? Tun ƙarfe nawa na gama shirina ina jiran shi? Ni ban hana shi zuwa ba amma sai ya yi abin na shi da tunani a ciki.’
“Ok wato kina so ki ce ba ni da tunani ko Saudatu?
Ya faɗa yana daga zaune, a ɗan kuma fusace domin ni fa na daɗe ban ji yana kiran ta da Daughter da ya saba ba itama tuni Daddy ya kama kan shi Babansu Jidda ne ko Abban Khalipa.
“Ni ban ce ba amma dai na ce ba ka yin tunani in za ka yi wani abu.”
Kawai sai ya yi wani mirmishi na san in ya tashi magana ba zai faɗi mai daɗi ba ita kuma ta harzuƙa za a iya yin abu mara kyau.
“To ke kiyi haƙuri don Allah. Zuwa gobe in hankula sun kwanta cikin tsanaki sai ki nuna masa in da bai yi daidai ba sai ya gyara.”
“Ba zan gyara ba.”
Ya katseni a fusace na yi jage ina kallon shi sai kawai ya miƙe kamar zaki ya fara nuna Gimbiya da yatsa kafin ya ce” Ke wai me ya sa kin raina ni ne! Komai abin kishi ne a wajen ki? Rabi’atu ba ta da lafiya na je gidansu na dubata na shigo kin yi tunanin ki ce mini ya mai jiki.? Matata ce fa ke kuma y’ar uwan ki ce fa?
“Aa ni wallahi ba yar uwata ba ce. Ta tsaya iya dai matsayin matarka dai.”
Ta faɗa har tana ɗaga masa hannu sai ya yi wani slow kafin ya cigaba da faɗin”Ok yanzu na ma gano ki. Duk wannan ihun da kike yi cikin ne baki so ta samu ba ko?
Ta buɗe baki za ta yi mgana ya hanata ya ɗaga mata hannu yana cigaba da faɗin” Ba sai kin yi magana ba na gano ki baƙinciki ne da hassada dankare a zuciyarki. To bari ki ji na faɗa miki haihuwa yanzu Rabi’atu ta fara sai dai ki mutu wallahi”
“Haba Yallaɓai.”
Na faɗa saboda na ga kalaman na shi sun yi tsauri amma sai ya juyo ya balla mini harara kafin ya ce” Ki yi mini shuru kema ai zan iso kan ki.”
“Topha”
Na faɗa a zuciyata me kuma na yi?
Gimbiya ta ba ni tausayi ta jawo ma kanta cin mutumci Yallaɓai haka yake ta jifanta da manganganu wai ita kaɗai ce matarsa! Ni me ya sa ban taɓa masa ƙorafi ba sai ita daga dawowarsa ta san abubuwan da suka faru da shi yau? Ta san wani hali ya yini a ciki ba tarba ba kalamai ma su daɗi kawai ta zaunar da shi tana challanging ɗin sa a kan mganar banza! To wallahi in ya ga dama sai ya kwana a duk in da ya ga dama kuma ba wacce ta isa ta hana shi.
“Allah ya ba ka sa’a ka koma gidan su Rabi’atu a ba ku ɗaki sai ka riƙa kwana “
Gimbiya ta faɗa tana tsane hawayen baƙin ciki. Ba ita ba ni kaina wallahi na ji zafin mganganunsa haba wai kamar Yallaɓai ya fara haukacewa.
Ni ina ta tsoro ma kar su Khalipa su ta so.
“Ina ruwan ki? In ma a hotel zan ɗauke ta mu je mu kwana wannan duk ba damuwarki ba ce. Matata ce.”
Da na so ba zan ƙara mgana ba amma ganin lamarin ya fara lalacewa shi ya sa na sake mgana.
“Don Allah Yallaɓai ka yi haƙiru ke ma Gimbiya ki yi hakuri ku bar mganar nan. Dare ne kar ku ta shi su Khalipa.”
Ita dai Gimbiyar ta yi shuru tana ta jan majinar kuka shi ko uban gayyar komawa ya yi ya zauna yana huci shi kaɗai da man ina tsaye ne ban zauna ba sai na ce” Sai da safe”
“Dawo nan kema”
Ya kira ni a ɗan zafafe, ni fa ban san me na yi masa ba amma na fahimci ba mganar Gimbiya ba da man yau a fusace ya shigo ita kuma kishi ya rufe mata ido ba ta gane ba ta je ta taɓo shi.
“Na’am kana kirana ne?
Wajen zama ya nuna mini a kujeran da ke gefen shi ta zaman mutum ɗaya sai na zauna ina jiran na ji ni kuma me za a sauke mini?
Gimbiya ya kallah kafin ya ce” Da kika kira Sadiya ita ɗin uwa ce ita! ?
Daga ni har Gimbiya sai da muka kalli juna sannan muka dawo muna kallon shi saboda mamaki.
“Zugwai-zigwai kin ɗaga waya kin kirata na ce ita din Nene ce?
Dukkan mu mun kasa mgana daga ni har ita saboda ba mu da abin cewa.
“Sadiya ke aurena ko ni nake auran ta? Ni ne shugaba a gidan nan a cikin ku ba wacce ta isa na faɗa muku.”
“Ikon Allah”
Na iya faɗa a saman leɓena kamar an turo fa Yallaɓai. > Janaftybaby: “Kar ki ƙara mini wannan sakarci muna mgana ki je ki kira mini wata wallahi in kika ƙara ranki sai ya ɓaci na ma faɗa miki.”
Ya faɗa yana nuna Gimbiya da yatsa, ni ta kalla sai na gyaɗa mata kai alamun ta ba shi haƙuri.
“Ka yi haƙuri.”
Ko sauraranta bai yi ba ya juyo kaina ai ni na yi suman zaune tun da yau Yallaɓai ya ke kirana da wata ai na san kuma sai abin da ya manta.
“Ke kuma ki daina ganin ina jin mganarki ki ɗauka ko wani abu na rayuwata sai kin shiga. Ba ruwan ki da tsakani da kowacce a cikin matana. Ki tsaya in da na saka ki, ni ne mijinki ba ke ce mijina da za a ce komai ya faru ki tasani kina yi mini faɗa kamar wani ɗan ki ba. Ba na so na faɗa miki bana so”
“Ka yi haƙuri “
Na faɗa cikin sanyin murya.
“Ban yi ba.”
Shima ya ma yar mini a fusace.
“Allah ya huci zuciyarka.”
“Amin.”
Ya faɗa a ƙufule kafin ya tashi ya shige bedroom har yana bango mana ƙofa.
Gimbiya ta kalleni kafin ta riƙe baki tana faɗin” Kin gani ko Maman Jidda? Wallahi ba ƙalau yake ba”
Miƙewa na yi tsaye kafin na ce” Lafiyar sa ƙalau. Da a ce kin ji shawara da duk ba ki jawo ma kan ki tozarci ba, nima da ba ki jawo mini wannan jan kunnen da ya yi mini ba. Don Allah Gimbiya ki daina sakani cikin rigimarki. Ba zan iya da Yallaɓai ba nima kina dai ji ya ce ni ba Nene ba ce ina yi masa shisshigi, in dai kin san ba za ki dinga haƙuri da wasu abubuwan ba nima to ki yi ma Allah ki daina saka ni a ciki.”
“Ki yi hakuri.”
.
Ta faɗa a sanyaye to itama ai ta gani yadda ya zauna yana ta yaɓa mana mganganu.
“Na ce miki ki riƙa kauda kan ki. Ba fa komai ne sai ka yi mgana ba. Ki bar shi ya yi ta kai wa daran mana in kin ga za ki iya jiran shi ki jira shi in ba za ki iya ba ki yi kwanciyarki. Ke in ya ga dama duk ranar girkinta ya je can ya kwana me ye na ki? Gidan shi abin da ya dama shi za mu sha, kuma Allah ai yana sama yana kallon shi cikin mu duk wacce ya danne ma haƙƙi sai Allah ya tambaye shi.
Duk tsiyar shi ba zai kwana can ba zai dawo kuma yau da gobe ba ta bar komai ba in kika yi haƙuri itama ai wata rana za ta zama ɗaya da mu. Ai mace ce haihuwa za ta fara. Kamar yadda ya ganta ya auro wata rana haka zai ga wata ya auro itama a fara gwagwarmaya da ita ba, ai Namiji ne shi a rayuwar namiji mai ya yi ne da kuma ɗauka da ajiyewa ke dai ki zura ido kawai ki daina ma tanka shi, ki nuna ma kamar ba ki san abin da yake yi ba shi da kan shi zai shiga taitayinsa.”
“In sha Allahu ba zan ƙara mgana ba.”
Ta faɗa tana miƙewa itama.
“Ya dai kamata gaskiya.”
Ba mu ji ko ƙaran buɗe kofa ba sai ganin shi muka yi kawai a kan mu a falon, ban san ko ya ji manganganun mu ba ko kallon mu bai yi ba ashe ya manta wayarsa a saman kujeran da ya tashi ita ya ɗauka a fusace ya koma ciki ina ganin haka na kama hanyar fita ina yi ma Gimbiya sai da safe, mganganun sa ba su wani dame ni ba Gimbiya ce washegari ta ce ba ta iya barci ba a raina na ce ba za ki yi ba kam nima haka na kwana kuka a ranar da Yallaɓai ya ce ina baƙin ciki da su Khalipa. A cikin zuciyata na ce Gimbiya Welcome to the Game.
Wannan tsiyar da Gimbiya ta jawo ta aka yi ita ta ja mana Yallaɓai sati ya yi daga ni har ita yana yi mana cin mgani
ko abincin mu ba ya ci da gani har ita, sai ma bangaren shi da ya turo ma’aikata suka fara ida sa gyarawa ko gaya mana bai yi ba, ni in ranar kwana na ba yan gaisawa ba ma mgana sai dai ya yi ta aikinsa a kan system ko kuma ya yi wasannin shi da ƴa’ƴan shi, nima ko ganin haka na kama kaina ban ga abin da na yi masa na bashi haƙuri tun a falon Gimbiya ban san kuma me ya ke so ba ko so ya ke yi na kwanta masa saboda yana fushi da ni, ni ko na ce a cigaba da tafiya gabar nan ce ya san ni na fi shi kwarewa. Da na fahimci ba ya cin abincina sai na daina ma yi masa ta yi, Gimbiya ta ce itama haka ba ya mata mgana in ta yi masa mgana da kyar yake amsawa. Ita duk ta damu kamta ni fa na faɗa mata an riga an zo matakin da ɗan zaki ya riga ya girma ni Yallaɓai ai ya daina hana ni sukuni da takaicinsa tuni na ke tattara shi na watsar na kama sabgogin gabana. > Janaftybaby: Balle da na dawo da sana’ar hijabai na gadan-gadan ina na gama ta lokacin shi, da man hatsiyar tariyar da bukukuwa ne suka saka na yi sanyi ganin ina so ma na taba jarin kuma ga mutane na so shi ya sa kawai na saka aka ɗinko mini da yawa aka aiko mini da shi.
Gimbiya ko ga shagonta ga aiki amma duk da haka ta zauna Yallaɓai na neman kasheta da haushi. Wai tana faɗin ya fara gyaran bangaren shi bai sanar damu ba na ce ina ruwan ki? Shi da gidan shi da kudin shi? Ni ko a gefen gyalena to da Rabi’atu za ta dawo bai sanar da mu ba ranar ni ba na nan na je gidan Ma’u na duba ta tun da ta haihu ɗin ba ta ƙara lafiya ba lafai lafai ce, Gimbiya kuma tana shago yara suna makaranta danginta suka zo suka yi mata gyaran bangarenta sannan da daddare suka dawo da ita. Ni ina muka sani ba sai dai muka gan su ba kawai ni dai na shiga bangaren Rabi’atun na yi musu sannu da zuwa itama na yi mata sannu duk ta yi wani fari ta rame.
“Ai mun zo ɗazu gyaran bangaren Rabia megadi ya ce duk ba ku gidan”
Kai tsaye na ce ni na je dubiya ne Gimbiya kuma daga wajen aiki ta wuce shago. Kuma ba mu san yau za su dawo da ita ba.
“Ai ko dai tun jiya ma Megidan ya so ta dawo Allah bai yi ba sai yau.”
Wato kenan yana sane mu ne dai bai ga damar sanar damu ba ya yi ma kansa ruwa na kawo musu ba su ma sha ba.
“To ga Rabi’atu nan mun san ana ƙoƙari kula da ita Allah ya ba da lada.”
Na amsa da Amin Gimbiya sai da suka fito haraba ta leƙo suka gaisa direban da ya kawo su ya kwashe su ya ma yar. Na koma na sake duba Rabi’atun muna ɗan yi hira kaɗan ta ji sauki sai dai ta rame. Ni dai na ga abin mamaki yarinyar nan tana jin diran shigowar mota ni ko ina zaune na ce ina jin Yallaɓai ne ai sai da na yi suman zaune saboda barikin da na gani ganin idanuwa. Yarinyar nan tana zaune amma sai ga ta kwance ta narke kamar ruwa, yana shigowa da man bangarenta ya nufo, yadda ya ganta kwance tana wani lumshe ido ko lura da ni bai yi ba ya nufeta duk ya rufe ya tarairayota jikinsa yana tattaɓa goshin ta.
“Baby me ya faru jikin ne?
Kan ki ke ciwo? Ko zazzaɓin ne?
Ya ke faɗa yana taɓa kanta da cikinta ita ko ta narke masa tana shagwaɓa kamar wata jaririya.
“Abba uhm”
Ta ke faɗa har da gutun hawaye, shi kuma gabaɗaya ya ruɗe.
“Me Abba ya yi? Uhm faɗa mini.”
“Ba kai ne ba’
Kawai sai ta fashe masa da kuka cikin rawan jiki ya ƙamƙameta yana faɗin”Abba ne ko? To Abba ba zai ƙara ba kin ji ko?
Ɗankari!
Haka na faɗa a zuciyata. Gimbiya ta daɗe tana ce mini yarinyar nan muguwar yar bariki ne ban sani ba, sai yau da ta nuna mini Umma na ke ita kuma Rabi’atu ina zaune tana abin da ta ga dama in shi bai ganni ba ita ai ta san da ni. Zuciyata ta motsa amma ban bari na zubar dakaina a gaban su ba sai na miƙe ina mirmishin ƙarfin hali.
“Mu kwana lafiya Rabi’atu.”
Sai a lokacin shi ya farga da ni, ya ɗan yi shock tun da har ya ɗan sake ta, ta bar cinyarsa ta zauna da ɗuwawunta a saman kujera.
“Umma to sai da safe.”
Ta faɗa cikin sanyin murya ji na yi kamar ma juya na kamata na yi bugu. Ban taɓa jin kishinta da haushinta irin na yau ba.
“Sadiya da man kina nan zaune?
“Sannu da dawowa.”
Na faɗa ban jira amsar shi na bar musu falon, duhu duhu hazo hazo na ke gani kafin na kai bangarena. Na yi shuru zaune ina tunani,ko ma me ya faru yarinyar nan da gangan ta yi, tun da ai ni da ita ne zaune muna hira, raina ya ɓaci kenan ta shirya mini wulakanci ne? Daga abin arziƙi duk abin da ta ga ina yi mata darajan Yallaɓai ne da sauke haƙƙoƙin zaman tare amna ni ai ba ta isa na koma bayan ta ba. Amma tun da ta ce haka mu zuba mu gani, ni ko zan nuna mata na riga ta zuwa duniya ita yarinya ce har yanzu. Ranar raina a bace na kwana ko Jidda ta kira ni a waya ban wani saurareta ba na ce ina jin barci washegari da safe sai ga Yallaɓai ya shigo yana yi mini kame kame ya ɗauka zan nuna masa wani abu ne ya ga bayan gaisuwa kallon musulumci ni ban yi masa ba ma shima ai munafukin ne. > Janaftybaby: Ko kunya bai ji ba yana faɗa mini Rabi’atu na son tuwo, na ɗauka zai ce ne ni na yi mata wallahi da in na fara faɗa masa mgana sai abin da na manta sai ya taimaaki kan shi ya kira Baby ya saka ta. Asabar ne ba makaranta Tahfiz kuma suna ajin bita ne yau ba ta je ba. Tun da y’arsa ya saka ban yi magana ba na yi shuru kamar zan ce ta je can bangaren nata ta yi mata sai na fasa ganin gogan yana can ya tare. Ranar ko fita bai yi ba har su Adnan gida suka zo suka same shi Gimbiya ko tun safe ta wuce Rano an yi musu rasuwa sai gobe za ta dawo shima Yallaɓai in dacewa zai yi ai ya dace ya je tun da yaron ƙanin Hajiya ce ya rasu saurayi ne ma Gimbiyar take faɗa mini to yarinya ƙarama ta saka shi a gaba har lahadi bai fita ba Baby ya samu tana yi mata wahala ranar ma da na ce ta wuce ta je Tahfiz hanawa ya yi wai ta bari wani sati kawai.
Ban yi magana ba saboda na shirya mafita na. Ranar litini da safe ya fita ya ce mini za su je Rano gaisuwa. Na ce Allah ya tsare ni da man mun tsara da ni da su Munnira Gimbiya gobe za ta dawo ranar bakwai za mu koma tare da ita amma na kira ta a waaya ta haɗa ni da Hajiya na yi mata gaisuwa. Tun ranar nan da na kama shi yana wannan ɓare ɓare jikin ya daina sha mini ƙamshi, ni ko na yi kamar ban ma gane shi ba tare suka fita da Rabi’atun ya sauke ta a makaranta ai ko ta gane ba ta da wayau sai yamma ta dawo gida ban yi kuma abinci da ita ba. Sai ga ta shigo shashena ta zauna ta ɗauka irin baya ne in ce ta shiga kitchen ga abincin ta ga na yi mata kiri ƙiri.
“Umma ba ki yi sauran abinci ba?
Kai tsaye na ce mata yau ban yi girki ba indomie ce Baby ta dafa da suka dawo makaranta. Ba su nan kuma sun tafi islamiya na samu an saka su wata islamiya anan anguwar da muka dawo ba nisa. Su Khalipa da man wajena Gimbiya ta bar su da za ta fi.
“Ki je ko yar indomoe ki sulala ki ci.’
Ta ce mini to, ta tashi ta wuce na rakata da harara ba wai haushin abin da ta yi mini ba ne a’a haushin yadda ba ta raga mini ko don karan da na ke yi mata ba.
Na yi kyafci na ce za ki gane ba ki da wayau yarinya.
Tun daga ranar na daina ije mata abinci sau biyu tana zuwa tambaya na ce yara sun cinye daga nan ta fahimci dai ba zan ba ta ba ta kama kanta. Sai Yallaɓai ya ce ba ta da lafiya ba ita iya komai amma ranar girkinta su kule ba ka jin motsin su to da man ni ce na ɗaukar ma kaina kuma na yaye Gimbiya da man yar gaskiya ce ba za ta yi ba shi ya sa bai taɓa saka ta ba.
Da Gimbiya ta dawo kamar zan faɗa mata sai na fasa kawai na share saboda kowa ya ji sai ya yi mini Allah ya ƙara. Munnira ta zo ranar jumma’a mganar tafiyar mu Gobe muka shiga wajen Rabi’atu ta duba ta. Da ya ke muna ta knoking shuru ni kuma na ɗauka ko tana salla me tun da bayan mangariba ne sai muka tura kofar tun da a buɗe yake muka shiga abin mamaki ta gyara ɗakin nan tas yana tashin ƙamshi sai na tuna ashe yau gogan yana ɗakin ta ne, sai muka zauna saman kujera muna jiran ta ba ta ji shigowarmu ba sai ga ta fito da wata shigewar riga marabanta da tsirara kaɗan ne. Ko ta yi tunanin shi ne ya dawo ko da man dai haka take yawon ta a ɗakin ta ban mu sani ba da ta gan mu ta ji kunya da gudu ta koma ɗaki ta ɗauko hijabi ta saka ta fito muka gaisa tana rufe fuska muna fita haraba Munnira ta kalleni kafin ta ce.
“Ke na taɓo ki da mgana. Wai yarinyar nan ne ta kile haka?
Ina dariya na ce” Ras. Ai Namiji ya kilar da ita.”
Munnira ta riƙe baki kafin ta ce” Wallahi in ka ganta kamar ka saka mata yatsa a baki ba za ta iya cizawa ba.’
Uhm kawai na ce saboda Rabi’atu ta sauya idanuwanta sun buɗe ko na ce yanzu ta san daɗin namiji shi ya sa.
“Kin ga idanuwanta ƙif ƙif na marasa kunya yanzu.”
Mirmishi kawai na yi ban yi mgana ba.
“Ba shakka Tafida ya ba ta zuma ta ɗanɗana. Sadiya sai ku shirya za ta haɗa kafaɗa da ku yanzu.”
“Me ya rage? Ai tama fara haɗawa.”
Na fada ina danne abin da ke ta so mini, yarinyar da Yallaɓai ya ce kwana take yi da zazzaɓi ne haka shi ya sa da man ya ce ita ba za ta je Rano ba ni da man na yi masa mgana ne kar daga baya ya ce an ware ta tun da yanzu ba ya so wani abu ya same ta. > Janaftybaby: Washegari su kaɗai muka bar ma gida da yara kaf muka tafi ya ba mu mota Sadi ya kwashe mu, su kuma su Hauwa suna motar gidan Mimisco har da su Anty Bahijja aka yi tafiyar da Mubeenan Musbahu da tsohon ciki har ina ta faɗa na ce kamar dole ta zauna a gida mana tun da cikin ta ya tsufa.
Can muka yini sai dare, Amma mun je gidan Marwa an haɗu ana ta hiran duniya mun haɗu da Sameena ta ce mini gobe ma za ta koma tana dariya ta ce ya ta gan mu da mutuniyar nima ina dariya na ce ta ji wuya ne ta dawo muka haɗa kai don Allah, Sameena na ta dariya ina ta ya ta. Sai bayan isha’i muka koma gida muna mota Jidda ta kirani tana faɗa mini wai Abban su ya kirata ya ce in sun samu break ta zo gida ta duba Anty Rabi:atu ba ta da lafiya sosai.
Kamar Jidda ce Yallabai na rufe ta da faɗa ta in da na ke shiga ba ta nan na ke fita ba.
“Ko hutu kuka samu ki tafi gidan Ya Hamza ma ji kin kamo hanya kin dawo sai na ci uban ki Jidda. Saboda kawai duba Rabi’atu sai ya ce ki bar karatun ki taho! Gaskiya Yallabai ya fara samun matsala.”
Ita dai da ba ta san mafari ba hakuri ta ba ni ta ce wai ta faɗa masa suna ma test ne, bayan mun gama wayar na kalli Gimbiya ina faɗin” Kin ji mijin ki ko Gimbiya?
Ta yi uhm kafin ta ce” Wallahi ni dai ina tunanin ba haka nan ta bar sa. Ba ki ganin yadda ya ke fita hayyaci a kanta ne?
Wai Jidda ta zo dawo makaranta kawai saboda ta duba yar gold? Da wani abun ne ya taso tsaye zai yi ya ce ba za ta zo ba amma da ya ke yar gold ce ya ce a zo a duba ta mana.”
Ni takaici ma ya hana ni mgana, ko da muka isa gidan yana bangarenta shi dai ya zo ya yi mana bangajiya ban da ita ni Gimbiya ta ma ce mini ko gaisuwa ba ta yi mata ba da a ce da ne zan yi mata mgana yanzu ko kiɗa ya sauya shi ya sa rawa ma ya sauya. Shi kuma gogan bai nuna mata abin da ya kamata ba. Yadda bai nuna mini ya kira Jidda ba nima ban nuna masa na ji aikin da ya yi ba. Sai da kan shi ya zo yana ce mini Jidda ta so ta zo gida amma tace suna test a raina na ce ta so ko ka so, ya na neman ya riƙa kashe ma Baby karatu saboda matarsa kawai sai ya ce ta zauna ta yi ma Rabi’a girki ne ga an yi sau ɗaya sau biyu ana uku na ce ba zai yuyu ba.
“Ba zai yuyu ba kika ce Sadiya?
Ya faɗa da safiyar lahadi sun shirya Sadi na jiran su zai kai su Tahfiz wai Baby ta zauna ta je bangaren Rabi’atu ta yi mata shara sannan ta tambayeta abin da take so ta dafa mata yarinya ta ce hadda za ta je tana bita yau amma ya ce ta haƙura ai jiya ta je.
“E gaskiya ba ta yuyuwa ka kashe ma yarinya karatu kawai saboda bukatar matarka. Yallabai ta ɗauko wata daga can garin su ko ka samo mata wacce za ta kula da ita fakat kenan.”
Sai ya kasa mgana ni ko na yi masa mai gabaɗaya sai na ce” Kuma ni ban ga aikin da zai gagareta ba ai ba ta ciwo tun da ta iya ji da hidimarka to za ta iya ji da hidimar kanta da gidan ta ma”
Tun da ya ji na faɗi haka ya kiyayi tsayar mini da karatun yarinya ban san ko maganar da na yi masa ba ne, ko da man sun tsara hakan sai ga wata yarinya an kawo kamar za ta ɗan girmi Baby ƙanwar Antyn ce ta yi candy aka kawo ta taimaka ma Rabi’atun ta bakin Gimbiya ta ce da man akwai wacce za ta taimaka man aka bar shi yana ta faman wahala. Tun da ga lokacin kowa ya samu lafiya ta warke tun da yanzu laulayin ya bi jiki amma tun da makira ce a ko da yaushe nuna masa take yi tana cikin ciwo saboda ya lalace a kanta.
Mubeena ta haihu amma aiki aka yi mata da nagudan ya taso mata ni Musbahu ya kira uku na dare na ce ya zo gida ya ɗaukeni tun da ba zan iya driving ba. Yallaɓai na ɗakin Gimbiya a waya na kira shi sai ga shi ya fito, da man ina haraba ina jiran Musbahu yana zuwa bayan sun gaisa kawai ya ɗauke ni muka tafi, muna asibitin har safe ba ta haihu ba kan yaro ya jirkice suka ce aiki za a yi mata Musbahu ya saka hannu. Bawan Allah duk ya ruɗe sai da Adnan ya zo yana bashi baki. > Janaftybaby: Da safen Yallaɓai ya zo shi ya biya ma kudin aikin da aka yi mata an samu nasaran fito mata da yaron ta namiji ƙato mai kama da uban shi. Ba ni na koma gida ba sai da na ga ta farfaɗo y’anuwanta sun zo suna ta mini godiya domin ni ce na tsaya a tare da ita har ta samu kanta na ce ba komai Musbahu da Mubeena sun ɗaukeni da daraja shi ya sa nima nake daraja duk abin da ya shafe su. tun da kuma aka yi haihuwar bana zaune kullum sai na je asibitin kwanan ta huɗu suka koma gida to can ma gidan haka nake sintiri , suna an ɗaga sai sati biyu kan lokacin maijego ta ji sauki. Y’anuwanta sun ce za su dauketa bayan suna da Musbabu ya nemi shawara ta na ce ya barta ta je gidan kamar gobe ne.
An yi suna yarinya ta ci sunan Hajiya iya Hafsat. Musbahu ya yi ƙoƙari ya yi abin da kowani uba zai yi raguna biyu aka yanka mata Ya Usman ya siya ragunan sunan. Mun sha suna har Nafisan katsina ta zo da Safiiya ni da man mune yan gaba gaba Gimbiya da wuri ta zo har yara da suka dawo makaranta na saka Sadi ya kawo su, Amaryan Yallaɓai sai yamma ta zo daga makaranta saboda kuma tuƙo kanta ta yi ba ta yi dare ba da dokar megidan ban da tukin dare. Wannan kan gaskiya ne daga ni har Gimbiya in muka fita da mota muka kai dare ba mu dawo ba haka zai yi ta kira yana mana faɗa. An yi suna lafiya an watse bayan suna da kwana huɗu yanuwanta suka ɗauketa zuwa gida sai dai ya riƙa zuwa yana ganin ta.
Ni dai na yi mata atamfa da kayan Baby iya karfina. Sai da ta gama wanka za ta dawo ne Musbahu ya zo da kanshi ya ke faɗa mini abin arzikin da Yallaɓai ya yi masa ni ban ma sani ba cewa ya yi ya tashi daga gidan shi ya yi ƙarami ya bashi gidan da na taso ya zauna a ciki ya bar masa na wajen na shi sai ya saka haya a ciki. Kai na yi masa murna kuma na san Yallaɓai ya yi haka saboda ni, domin ko kwanaki da ya ce zai saka haya magiya na fara yi masa ina son gidan nan bana so na ga an bama wani can bare gwara na gida.
Da na yi ma Yallaɓai godiya hararata ya yi kafin ya ce” To ya zan yi? Gidan nan ji kike yi da shi kamar me. In na ce zan siyar ki ji haushina in na ce haya ma kice aa. Shi ya sa sai na yi tunanin gwara na ba ma Musbahu shi sai ya bar mini na shi, tun da na ga in shi ne zaki ji daɗi yaron ɗakin ki ne”
Ina ta dariya ban yi magana ba wai zan ji daɗi yaron ɗaki na ne kuma na ji daɗi sosai. An je an yi ma gidan fenti da gyare-gyare Mubeena ta dawo, ta kuma zo har gida ta yi mini yini ita da Anna(Hafsat) daga baya nima na je gidan na da wuri sai na ke ganin kamar zan waiwaiya na gan ni ina shiga ina fita a gidan wasu shuɗaɗdun al’amura ba za su taɓa shuɗewa ba, saboda a gidan nan abubuwa da dama sun faru sai dai godiya tun da yanzu mun samu cigaba ne.
Kowa ya ji labari sai ya yi ma Musbahu murna tun da ya samu cigaba gidan shi kuma Yallaɓai ya saka yan haya.
An gama gyara shashen Yallabai falo ɗaya ne da bedroom uku. Ni har mamaki yawan bedroom ɗin na yi da na tambaye shi cewa ya yi ba ruwana na jira mana na gani. Sai na kama bakina. Ya yi shirin shi har kayan funitures ya siya ya gyara bangaren shi tas kuma kowani ɗaki ya saka gado, wato dai wulaƙanci Yallaɓai ya ƙaro ashe wai kowacce ranar girkinta da ɗakinta in kin fita ki rufe ranar da kike da miji ki zo ki gyara ku kwana da miji in kin fita kina da key dinki ki rufe.
Ranar da ya ta ramu yana faɗa mana na kasa haƙuri sai da na yi dariya.
“Na zama abin dariya ne?
Ya tambaya a daƙune ganin ya ji haushi ya sa na ce” Ni tsarin ne ya ba ni dariya wai ranar girkin ki da key ɗin turaka ki je ki gyara in kin fita ki rufe”
Shima sai da ya yi dariya kafin ya ce” Maganin ƙorafi na yi. Kowa da turakanta magana ta ƙare.”
To ni dai ko rawan jiki ban yi ba tun asali na tsani turakan miji wallahi, Shi ke nan Yallaɓai ya fara buɗa jiki in kina da girki sai dai ki bi shi har dining ya saka a bangaren na shi duniya sabuwa. Ni fa ranar girkina mantawa na yi na yi barci a bangarena da safe na tuna tsarin har abinci a can za ki haɗa masa ke fa can za ko tare sai kin fita girki ni ko na ce ba zan iya ba ya’yana fa. > Janaftybaby: Yallaɓai ya ce to na yi ta kwana a bangarem nawa shi dai ya gama bin kowacce daƙinta tana yi masa yanga.
Ina gani Rabi’atu da Gimbiya ana gogawa. In suna da turaka aka kasa zaune aka tsaye. Rabi’atu in ranar ta ce ƙamshi turare har haraba. Ita da Salima kanwar Antyn tasu su zage a yi ta girke-girke. A sauya zanin gado a yi wannan a yi wannan haka itama Gimbiya sai suka koma suna gasa shi ko Yallaɓai na jin daɗi sun zaɓi dakunan su ni na karshe suka bar mini, na san dai in dai ranar girkina ne da safe zan je na gyara ko na saka Baby ta gyara na kuma shiga ɗakin na gyara na wanke tiolet a bangarena na ke yi abinci na kwasa na je na jera masa bana yin wannan rawan jikin na su to Allah na tuba wani kuma dare ne jemage bai gani ba ai sai daran mutuwarsa? In muka kwana da asuba nake gudawa bangarena sai dai in zai fita ya biyo ni ranar har ce mini ya yi in bana son kwanan nan ne na faɗa masa.
“Aa kawai dai ban saba ba ne wallahi ina jin wani iri.”
Wani kallo ya yi mini kafin ya ce” Gwara ma ki saba malama turaka yanzu kika fara zuwa.”
Shuru kawai na yi, ni bai san ban wani damu ba ta kaina na ke yi, duk da wannan rabawan da ya yi bai hana an samu matsala ba Gimbiya ta ce Rabi’atu tana ɓata kitchen da falo ba ta gyarawa haka take fita tun da can take girki, saboda da daga Rabi’atu sai ni ne daga baya abin ya birkice ni na dawo farko, sai Rabi’atu sai Gimbiya, rigima sosai sai da ya tsawarta musu da cewa zai kori kowa a turakan na shi sannan aka zauna lafiya bayan an yace kowcce ta zo ta ɓata waje ta gyara kafin ta fita ni ina gefe ban shiga ba ina ruwana na yi magana ya ce ina yi masa shissshigi. Na koma gefe na zama yar kallo tsakanin Rabi’atu da Gimbiya ne suke ƙwama film acikin gidan nan wani abun ma kamar ka yi ta dariya wani abun kuma hauahi ka ji kamar ka yi ta dukan su.
Cikin Rabi’atu har ya fito wata biyar amma ya yi girma sosai. Har ni kaina ina mamaki, sai da ta yi scan Yallabai ya zo bakin shi kamar zai kai kunne yana faɗa mini an ce yan biyu ne a cikin Rabi’atu mace da namiji. Sai a lokacin ya ke faɗa mini wai maman Rabi’atu yan biyu ne namijinta ya rasu ne. Labarin yan biyu Rabi’atu za ta haifa kusfa kusfa Yallaɓai ya kai labarin nan da man fa yana da shegen surutu da faɗi ba a tambayeka ba. Gimbiya ko ta ce ya dai bar murna domin likita ba Allah ba ne, shi ko ina ruwan shi yana ta shirin haihuwa kamar an ce gobe ne ballanta yanzu da kuɗi suke huda shi ai komai ma zai yi.
Haka nan muke zaune muna gungura rayuwar mu, ba a sati Gimbiya da Rabi’atu ba su yi tsiya ba, kuma duk fa kan turaka da miji, ni wallahi har na gaji da baa su haƙuri na saka musu ido, kuma in dai aka yi sai Gimbiya ta zama mara gaskiya saboda ta cika ƙorafi da mgana ita kuma Rabi’atu wayau da bariki da haka take cutar da ita ba ta sani. Ni dai ba mai yi da ni Yallaɓan ma kan shi isata yake yi na tattara shi na bar musu ranar har mgana ya kwaɓa mini wai ya fahimci na koma gefe yanzu na yaye shi kamar ba mijina ba, ba na damuwa da al’amuran shi.
“Ba haka ba ne. Gani na yi bayan ni kana da biyu irina masu kula da kai.”
Hararata ya yi kafin ya ce” Wato ina da biyu! Ai ko goma ne ina nan a matsayin mijin ki kuma dole a ce ma mijin iya Baba.”
“Dole ne wannan”
Na faɗa ina masa dariya ganin ya shaƙa sai kawai ya jinjina kai yana faɗin”Na gano ki wato kin gama cin moriyar gangan za ki yada ƙwaron ta ko?
Dariya har ina faɗowa daga kan kujera.
“To wallahi ba ki isa ba.”
Yallaɓai da karfi hali shi wai a dole ban shiga ana kishin sa da ni ba a raina na ce ba kuma zan tusa kaina ba, ai ni tun da na yi karatun namiji na daina ta yar da hankalina a kan shi.
Ya gaji da mitan shi ya haƙura domin ni kam ta kaina na ke yi, haƙkin shi dai ina ba shi ina iya bakin kokarina amma ba na rawan jiki da na ƙafa a kan shi. Na gama yin wannan tun a baya yanzu duk abin ma ya fita kaina. To jiya ai ba yau ba. > Janaftybaby: Siyayyya kayan haihuwa komai biyu aka siya dangin Yallaɓai kowa uwar biyu yake kiran Rabi’atu da shi har Nene fa in ta kira waya sai ta ce ina uwar biyu? Na ce lalle duniya juyi juyi yanzu uwar biyu ce a layi ba mai farar haihuwa ba. Cikin Rabi’atu na wata bakwai ya yi ƙasa ga shi ya girma yana rinjayan ta, ba ta aiki komai da man daga kwanciya sai in za ta shiga makaranta ya ma hana ta driving shi ya ke kaita ko Sadi, Salima na nan tare da ita tana kula da ita amma da wannan ƙaton ciki ba ta fasa zuwa turaka ba tana ganin ƙya shin ta haƙura har sai ta haihuwa na ce yar wahala kawai in dai namiji ne ke ce a baya ba shi ba. Danginta sun yi maganar a al’adansu gida za ta koma ta haihu megidan ya ce bai amince ba da kan shi ya zo yana faɗa mini na ce Allah ya kyauta ban san yadda suka ƙare ba daga baya ya ce mini in ta haihu an yi suna za ta je can Maiduguri ta yi wanka tun da sun matsa a raina na ce to ni ina ruwana? In na yi magana ya ce ina yi masa shisshigi ni dai iyakata Allah ya kyauta da Allah ya raba lafiya.
Ciki na kai wata tara ta daina fita ko’ina saboda ta yi nauyi ba sai an faɗa maka ba kana ganinta sai ka ce amma dai yan biyu ne acikin nan ko? Saboda girman shi ya yi yawa gaskiya Rabi’atu ta zama ɓukekiya ciki ya ma yar da ita babban mace. Edd ɗinta bai gama cika da kwana goma ba aka yi mata aiki ta haihu a wani daran jumma’a. Da ya kama 13 Nov. 2023
Ni Yallaɓai ya taso ina barci lokacin da ta fara naguda da man cikinta na shiga wata tana ya tara mu ni da Gimbiya ya ce zai riƙa kwana a bangaeen Rabi’atu saboda cikinta ya shiga watan haihuwan shi, ni dai ko a jikina na ce Allah ya ba da sa’a. Gimbiya ce ta ɗan nuna ba ta yadda ba ya shi ba yardanta yake bukata ba shi ya sa ba ma amfanin mganar tun da abin da ya yi niyya ba zai fasa ba.
Ta kasa haihuwa da kanta sai da aka yi mata C.S an fito da jarirai biyu mace da namiji. Kwana muka yi zaume a asibitin nan ni da Yallabai da Salima sai da safe aka fito da ita sannan ya kikkira jama’a ya sanar da su. Da safen na koma gida ni na ke ma faɗa ma Gimbiya da yara Rabi’atu ta sauka an samu yan biyu. Su Baby suna ta murna, Sai da huta can da yamma na koma asibitin Gimbiya ta ce mini sai gobe za ta je shago za ta leka.
Ko da na je asibiti ta cika makil da dangin Rabi’atu da na Yallaɓai su Anty Bahijja ana bakin gadon mejogo ana ta yi ma jarirai hotuna. Faɗi take yi an yi haihuwan da ba a taba yi a gidan Tafida ba haka ta yi posting ma a status. Shi kan shi angon ƙarnin ya kasa sukuni ina jin all contact ya yi wajen tura sakon an yi masa haihuwa saboda yadda yake yini amsa wayoyin yan barka.
Washegari tare muka koma da Gimbiya da yamma da yara ai ko ta sha mamakin ganin su Anty Maimuna ana ta rawan ƙafa a gabanta ma sun sake faɗa an yi ma Tafida haihuwan da ba a taɓa yi masa ba ta cika ta yi fam har tana ba su amsa da cewa sai dai a kira su da ƙannen su Khalipa Anty Maimuna ta ce ta yi mata rashin kunya ba aure gare ta ba ta san ita kanwarta ce dukan tsiya za ta yi mata suka bar Gimbiya da tura baki tana ƙwalla ni dai ban tofa ba amma da man na san wata rana itama za ta ji irin abin da na ke ji a can baya.
Kwanan Rabi’atu shidda a asibiti aka sallamota suka dawo gida. Yayenta biyu sun taho daga Maiduguri da kanwar babansu Yakumbo ita za ta zauna da ita har bayan suna. Gida fa sai kamshin masu jego, an shirya suna gagarumi tun da haihuwa ce da ba a taɓa yi ba. Kuma mun ga haka mukan mu kowaccen mu 100k Yallaɓai ya ba mu ni da Gimbiya na fitar kayan suna. Jidda ma ta zo gida lokacin ai dole ta zo Yallaɓai fa haka ya dinga kiranta wai ta zo gida ta ga k’annenta yan biyu. Kuma yara sun ci sunan Sulaiman da Aisha. Ya cika alƙawari ya yi ma Alhajinmu takwara. Alhajinmu ko har gida ya taho barka ya kuma turo Gwaggo. Tun da an yi ma ubana takwara ai dole na ware kudi na yi hidima cikin kuɗin da ya ba ni ne na siya ma yaran riga da pampers uwar kuma atamfa na yi mata. > Janaftybaby: Gimbiya dai kayan jarirai kawai ta yi ni kuma ba ni da da man zillewa Yallabai ya gama yaɗa ma Duniya Alhajinmu ya yi ma takwara shi ma can Alhajimmu ya gama yaɗawa shi ya sa kaf yan gidanmu sai da suka zo barka na nesa su Amina suka kira waya.
Sa guda Yallaɓai ya gada da raguna biyu, shagalin suna abinci ma daga reataurant aka dafo shi. An yi kayan rabo su robobi jaka memo da hotunan yara, Jidda dai ta yi kayan fulawa su cake da donut uban kuma ya ba da kuɗi ta yi har da cake, Rabi’atu kuma ta shiga ta fita da kayan alfarma. Ni dai kala biyu na saka da man ina da su Gimbiya ko da man tana da sutura ina tunanin ba ta yi ma sabon ɗinki ba. Yan uwansu na Maiduguri ba su zo da yawa ba gaskiya saboda nisa sai dai dangin Yallaɓai ne suka cika gidan har da mai kiɗan kwarya su Halima suka kira suka cashe, wata zabiya cikin masu kiɗan ƙwarya tana waƙe mai jego.
“Ina mai jegon ta ke ne? Rabi’atul badawiyya farar mace alkyabban mata. Farar mace fitilar gida. Amaryan Yusuf mai yan dubu dubu kin iya haihuwa da kika tashi biyu kika haifa ki shigo fili ki taka domin yau ranar ki ce”
Anty Maimuna ta fito da maijego suna ta mata barin kuɗi sai ga Yallaɓai ya zo gidan zabiya na ganin shi hau yi masa kirari.
“Ga ni ga Alhajin Naira. Alhaji yusuf angon Rabi’atu mijin fara baban farare. Mijin mai kyau daga Maiguduri, uban biyu kake dole dai a ce da mijin iya Baba.”
Nan fa Alhajin naira ya zaro bandir ɗin yan dubu dubu yana ta ɓari waje ya ruɗe da murna da ihu. An yi hotuna mai hoto kam ya haska ya fi kala ɗari, mu dai muna gefe muna mirmishi in ka yi baya ace kana bakinciki Gimbiya tana bangarenta ma ba ta fito ba. Su Anty Bahijja sun kuma haɗa ma Rabi’an kayan suna ya kai atamfa goma ga kayan jarirai ga kuɗi, Mimisco kanta da ba ta kasar suna spain ita da megidanta super ta aiko Naja da shi da less mai tsada. Ana ta ɗagawa ana yabawa, Baban biyu ma ai ya yi wasa da naira yana da shi yanzu komai ma zai yi ba ya ƙya shi.
An yi suna lafiya an gama an yo soye soye kuma duk sun ba mu domin lokacin ma da suka gama sai da suka kirani na ce su dibar ma mejego da mijinta sai na bangaren su da namu bangarem mu dai yan gida gabaɗaya suka dibar mana da yara na dangin Yallaɓai Gwammaja akai tare da yaji mai yawa da turaruka. Na Yallaɓai kam har naman sai da ya kai ma Alhajinmu da kan shi na sunan takwaran shi kuma Alhaji shima za a riƙa ce masa. Alhajinmu haka ya zaunar da ni da na je yana yi mini faɗan na zauna lafiya kar ya ji kar ya gani na zama silar tashin hankalin mijina ai ba ni da ta cewa. Yallaɓai ya gama kama Alhajinmu a hannu da makircin su na maza
Macen kuma Ayush za a riƙa kiranta. Tariq ya zo ya ga jarirai ya yi barka haka ma Kawu. Abokan aikin Yallabai duk sun zo barka shi ya sa sai bayan suna da wajen kwana goma Rabi’atu da y’anuwanta biyu da Yakumbo suka bi jirgi zuwa Maiduguri sauran kuma suka bi motar haya da kaya. Sun yi mana sallama da za su tafi muka rabu da faɗin Allah ya sa mu gana.
Tun da Rabi’atu ta tafi sai da ta yi wata biyu a gida sannan Yallabai ya je ya kwana biyu suka dawo tare. Su Alhaji sun yi kiɓa ɓulɓul kamar Yumna tana ƙarama sai dai su farare ne irin su uwar su, bayan ta dawo kuma ta fara ɗan zaga gidajen dangin miji ga shi kuma da man karatunta ma ya tsaya na ji Yallaɓai na faɗin diparing za ta yi. Rabi’atu ta dawo da sarkan ƙafa na kwalliyar mata da hudun hanci Yallaɓai kuma ya ce ya yi mata kyau ta yi kiba ta ƙara yin kyau sannan ta dawo s da wata yarinya Zafira ɗiyar yayarta ce wata kila a wajenta za ta zauna megidan dai bai ce mana komai ba.
Satin da ta karɓi girki Yallaɓai kamar zai yi hauka saboda rawan ƙafa, har zuwa ya yi ya same ni wai tun da ta daɗe ba ta nan mai zai hana mu bata sati ɗaya na ce ni na bata sati biyu ma sai dai Gimbiya. Itama ban san Aljanun sukunin da suka shiga kanta ba ta ce su yi ma wata ba ta damu ba ina ga itama ta fara dawowa daga rakiyan Yallaɓan ne shi ya sa aiko ya ji daɗi suka yivta gwangwazan amarci, daɗin da ya ji ne a watan ya sauya ma Gimbiya sabuwar mota balle ma mun shiga sabuwar shekaran 2024 harkoki suna ta budewa. > Janaftybaby: Yallaɓai yanzu sai godiya ya samu kwangila ginin wani kamfani a zaria zai je ya yi kwana biyu ba kwana kwana ya ce Rabi’atu ta raka shi muka ce Allah ya tsare baban biyu da uwar biyu sun fi kwana huɗu sannan suka dawo Jidda ta ce sun kawo mata ziyara ita yanzu ajin ta uku a Jami’a Baby ce ke SS3 Yumna da Ammar tuni an saka su a makaranta.
Watan su Ayush shidda Gimbiya ta fara laulayi da azumin watan ramadana ashe ciki ne. Bawan Allah ya yi ta murna domin Yallaɓai na son yara a rayuwan shi. Nima yana ta mini dan biki wai ban gama sai na ƙara ko ɗaya ne, ba ni da sanin gaibu amma sai na ke jin kamar na gama haihuwa tun daga kan Yumna. Itama Gimbiya cikin na ba ta wahala kuma tabbas itama ya kula da ita amma fa uwar biyu da biyunta dabam suke, su ke shan sharafinsu na ɗauka son da yake yi ma su Khalipa na daban ne sai da biyu suka zo na gane su Khalipa ba su ga komai ba in dai gata ne.
*Janafty*