Turken Gida – Chapter Fifty-four
by Janafty*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*
Bikin Datti ya taho gadan-gadan mu mun ɗauka ma za a ɗaga bikin ne ganin ba a yi shirye-shiryen komai ba amma su Ya Hamza suka ce ba za a ɗaga ba tun da Datti ya kusa gama haɗa lefensa ta hannun Anty Laila a can Abuja. Gidan da za su zauna kuma haya ya kama anan garin Kaduna kusa da ma’aikatansu.
Ya Hamza ya turo da kuɗi Ya Abubakar da Ya Muntari sun yi ja gaba an yi fentin gidanmu ciki da bai. Sannan an gyara ɗakin Mama an yi waje da wasu kariki tai an rufe shi saboda nan Amarya za ta sauka sai sun yi sati sannan za su wuce Kaduna ita da angonta. Duk da can za a yi mata jere amma Kano za a fara kawo ta in ji Datti. Kuma y’an uwansa suka yi naam da haka mu da man namu kawai to ne da bi, saboda ƙurewar lokaci shi ya sa ba mu tara kuɗi masu yawa ba amma kowa ya yi abin da zai iya dai’dai ƙarfin sa mun damƙa ma Datti, amma ni da Amina mun ƙara masa da leshi guda biyu da atamfa aka ƙara cikin lefen shi. Gida da man su Ya Hamza sun ɗauke komai hatta da abincin da za a ci har a gama biki, balle kuma Alhajinmu na da hatsi a store sai abubuwa suka taho mana da sauƙi.
Ana saura kwana huɗu aka kai lefe. Daga Abuja Laila suka kawo shi Zaria bayan duk mun gama ganiwashegari ni da Ya Murja da Ya Aina da Inna Mariya muka tafi da su Kaduna muka haɗu da Amina a gidanta sannan direban mijinta ya tuƙamu zuwa gidan su Amaryan mai suna Badariya. Mun samu kyakyawan tarba sai godiya akwati bakwai muka kai kuma mun yi daidai abin da ya kamata wanda ba za a raina ba. Kuma ba su raina ba ɗin mun ci mun sha har da guzuri sannan sun bamu tuƙwaici muka ce ma ba za mu karɓa ba suka matsa mana. A gidan Amina muka kwana sai washegari har da ita da yara muka tattaro Kano gabaɗaya. Muna zuwa muka iske mutanen Zaria sun iso da mutanen Yashe gida ya fara ɗaukan harama. Dangin Mama na gandun albasa da man ni ce na sanar da su bikin suna ta faɗa domin ba a faɗa musu da wuri ba amma duk da haka sun haɗa kudaɗe sun aiko mana da shi, har gobe ba su yada wannan zumuncin ba.
Jidda ta kira ni a waya har tana mini shagwaɓa wai na bar ta tazo bikin Uncle Datti na ce mata ni ba ruwana ta kira babanta, ita kanta ta san ɓata ma kanta lokaci ne ba zai bar ta ba, nan da nan ya ce ta zauna makaranta ta yi karatunta ga bikin Adnan nan in ya ga cancantar ta taho zai tura aje a ɗaukota. Ta kirani kamar ta yi kuka tana faɗa mini ina yi mata dariya. Sai a lokacin ma take faɗa mini har Rabi’atu ta saka ta yi ma baban na su magiya amma bai amince ba ni ta so na saka baki ni kuma na ce ba ruwana ta zauna ta yi karatunta kamar yadda ya ce ba a gama ba, ga bikin Adnan nan tsakaninsu sati uku ne su har sun fidda anko ma, mu dai na Datti ba mu fitar ba lokaci ya kure kowa na shi zai saka.
Ban raba cinghan ɗin gayyata ba amma na sanar da baki. Kaf dangin Yallaɓai suna da labarin ƙanina zai yi aure. Balle ma na san Yallaɓai zai sanar a group ɗin su na gida nima kuma Munnira ta sanar a wanda muke ciki ta ce muna gayyatar kowa da kowa. Rabi’atu da Gimbiya ko kowacce har shashenta na kai mata kati na sanar da ita. Rabi’atu ce ke murna ita da Baby amma Gimbiya ce mini ta yi itama ranar tana da biki a Rano can ma za ta kwana. Ni kuma sai na ce in ta yi ma addu’a ya wadatar. Yallaɓai kuma ya ce mini zai je ɗaurin aure sannan Datti ya kirani ya ce na taya shi godiya 100k Yallaɓai ya tura mai da na yi masa godiya sai ya shafa kumatuna yana faɗin” Nima ai Datti ƙanina ne.”
Sai na jinjina masa kai amma duk da hakan dai na yi masa godiya. > Janaftybaby: Ana gobe biki acan na kwana ni da Yumna kaya ma Baby ce da safe suka taho mini da shi ita da Rabi’atu. Na ga kara sosai su Munnira tun safe suka zo mini biki su Suwaiba duk sun leƙe min har Mimisco ta zo, ta ba ma Gwaggo 10k. Gimbiya dai da safe ta leƙo ko minti talatin ba ta yi ba ta ce mini za ta wuce Rano na yi mata godiya na rakata har waje. Da yake ɗaurin auren na safe ne zuwa la’asar tuni har yan ɗaurin aure tun kamo hanya da Amarya. Yallabai da Kawu sun je ɗaurin aure Tariq da dake can ya samu zuwa, mu kuma muna gida muna shirin tarban su, sun iso wajen biyar na yamma kai tsaye gida suka taho da ita muka tarbeta a ɗakin Mama aka sauke su ita da y’an uwanta da ƙawayenta abinci da komai ba su da matsala duk mun tanada.
Marwa tun jiya itama ta na nan, Mubeena ce kawai ba ta zo mini biki ba tana gidansu ba ta da lafiya laulayi. Ta samu ciki sau biyu yana zubewa sai yanzu ta sake samu. Ma’u ma sai fama da tsohon ciki, riki riki ita abokan zamanta sun zo mata biki, ni kam da man Rabi’atu tana gidan nan tun safe sai dare sannan Yallaɓai ya zo ya ɗauketa suka koma gida. Ni da yara duk nan gida muka sake kwana. Dangi an haɗu gabaɗaya kamar kar a rabu yan gandun albasa ma sai ranar lahadi suka koma, mu kam sai litini sai da aka ci aka suɗe a ranar duk su Ya Hamza suka koma da matan su, a bikin ne muka ji an saka ranar auren Anti ɗiyar Ya Murja, Ya Balki ma ta ce mai son Firdausi an turo, ina tunanin bikin nan zai yi mana rudgudu, yanzu dai sai dai in Ma’u ta haihu za mu sake haɗuwa. Muka baro gida da Amarya sai Gwaggo da Baaba amma dangin ta sun kawo kayan fulawa da kololi, da sauran kayan al’ada kuma duk an rarraba mana har dangin Mama suma an ɗibar musu na su kason
Ranar litini gidan ya watse. Ni kaina sai dare na koma gida ni da yara. Sadi ne ya je da mota ya ɗauko mu Rabi’atu har ranar lahadi ta dawo sai mangariba ta tafi, litini kuma da man tana da makaranta ko a hakan ma na gode. A bikin ma su Suwaiba na ji suna taɗin su Anty Bahijja sun ce wai na haɗa kai da ƙaramar yarinya saboda na ƙuntata ma Gimbiya maganganu dai gasu nan ni ban biye musu ba, saboda in da sabo na saba da ire-iren mganganun su a kaina. Ni ban haɗa kai da Rabi’atu ba amma dai na san daga ita har Rabi’atu ina da zaune da su tsakani ga Allah, ita ce kawai yarinyar take darajani ta kuma ɗauke ni da ƙima fiye da yadda ita Gimbiyar ta ɗauke ni,sai a ga laifina don ina kula mai kulawa da ni? In fa tana gida a shashena take rabin yini na in ba ni ce na ce ta koma bangarenta ba, barin ma in Yallaɓai na ɗakinta sai na ce su je Baby ta ta ya ta ayyuka shine fa za ta tafi, amma in dai yana bangarena ne, ko bangaren Gimbiya sai dare sannan zai rakata ta koma shashenta ita da Baby dake tayata kwana nan take cin abincin ta yi koman ta ta zauna da yara su yi ta hira, barin ma Yumna da har ta saba da ita, da ta ganta za ta dafe mata. Sannan ko y’anuwanta wallahi suna darajani in dai suka zo gidan nan sai ta fara kawo su bangarena mun gaisa sannan su ke wucewa shashenta. Kuma in za su tafi za su yi mini sallama Gimbiya ko sai mu kwana uku ba mu ga juna ba muna gida cikin gida ɗaya kofar bangarenta ma yana rufe ne, ba ta neme ni ba ni ko ai ba zan lalace a kanta ba. Ni dai ba na gaba da ita in muka haɗu ko ba ta gaisheni ba zan gaisheta. Yallaɓai ba ya yini yake yi a gida ba ni kuma ba ni da halin ƙorafi balle na sanar da shi wasu abubuwan. Shi dai tun da bai taɓa jin an samu wata matsala bq sai hankalin shi ya kwanta. Ba ruwana da sanin tsakanin matan shi kamar yadda nima ba sab tsakanin mu ba. Na kama kaina gefe sai kuma na samu zaman lafiya.
Kafin tafiyar su Datti Kaduna ya kawo mini Amarya har gida ta gaishe ni, ba ni ba kaf ɗin mu haka bi da ita gida gida ta gaishemu. Ranar sati na zagayowa suka wuce Kaduna. Ni kuma anan Gwammaja muka shiga hidimar bikin Adnan, abin da ya sa na shiga sha’anin Adnan nawa ne kamar Musbahu ne, mun yi anko gabaɗayanmu Yallaɓai ya siya mana har da su Jidda da ya amince za a ɗaukota ta yi biki ta koma. > Janaftybaby: Adnan anan Kano zai ɗauko matarsa a can tarauni, shima ya haɗa lefensa na gani na faɗa da taimakon yanuwan shi, sai da bikin ya matso na ji labarin Adnan a gidan da Gimbiya ta tashi zai zauna Yallaɓai bai faɗa mini ba amma sai na yi masa uzuri ayyuka sun yi masa yawa wataƙila ya manta ne. Gida an ce an yi mass fenti tas ya dawo kamar sabo a bakin ni Hauwa na fara ji tace itama Mutaƙƙa ya faɗa mata sai da na koma gida a daran Yallaɓai na shashena na tambaye shi sai ya ce mini haka ne. Ganin ba shi da gida zai kama haya shi kuma tun da yana da gidajen sai kawai ya ce bari ya bashi guda ɗaya ya zauna. Na ce tabbas ya yi tunani Allah ya bar zumunci. A satin bikin aka kai lefe ni kaɗai na je Gimbiya ba ta je ba Rabi’atu tana makaranta su Anty Bahijja ne yan gaba gaba da yayarsa Ummu salma da su Nasara. Mu dai muna gefe ba mu yi baya ba kuma ba mu tusa kan mu ba.
Sai da muka haɗu a sha’anin bikin Adnan ne sannan Anty Maimuna ke yi mini Allah ya sanya alherin auran Datti na amsa amma sai da na yi musu tsiya da gayya kuma Anty Bahijja na wajen na yi musu jirwaye mai kamar wanka na ce na tare kowa ya zo ya ga waje ya saka albarka ita da Anty Bahijja ban gan su ba.
“Sai mun sake komawa? Ai ina ce in mutun ya yi zuwa ɗaya shike nan.”
In ji Anty Maimuna.
“Shi na gani. Duk ba gida ɗaya ba ne. Mun je lokacin tariyan Gimbiya kuma da auren Tafida da yarinyar nan”
Haka Anty Bahijja ta faɗa Allah ya sa Rabi’atun ba ta nan da ta ji wani iri kamar ba ta san sunanta ba.
“Bisa adalci kun je ma Gimbiya. Kun je domin Rabi’atu ni kuma sai ku kasa zuwa saboda ni? An ya kun yi adalci kuwa?
Sai suka kasa mgana ganin na daure su da mgana. Anty Maimuna tace shike nan bayan bikin za su zo in sha Allah. Nene na wajen ta ce ba su kyauta ba ya kamata su je su saka albarka. Anty Bahijja ta yi muƙus ba ta yi magana ba ni ko na gama faɗin abin da ke raina na kama harkan gabana.
Har su Anty Zabba sun taho sha’anin bikin Adnan, ranar jumma’a Sadi ya je ya ɗauko Jidda sai murna take yi a bikin nan na sha surutu kau da kai kawai na yi, ganin har da Dangin Rabi’atu da suka zo ni suka fara nema na kuma yi musu jagora falon Nene na sanar da ita iyayen Rabi’atu ne sannan ganin ta tana tare da su Jidda, in wani abu take ɓukata za ta zo ta ce mini Umma kaza shike nan aka saka mini ido a gidan bikin nan da nan su Anty Bahijja suka fara yawo da ni da cewa na haɗa kai da yar cikina saboda neman suna. Gimbiya kam tana gefe da man ko a sha’ani ba ma zama bangare ɗaya amma na san ba haka ta so ba, ta so ne wata ƙila itama Rabi’ar ta fi ma rashin ganin darajata hauahi take ji ta bakin Munnira ganin yarinyar ta ɗauke ni da daraja. Anty Zabba ta ce mun ba ta sha’awa na riƙe Rabi’atu ta gam bisa Amana hausawa sun ce kai ma ka gaida mai gaishe ka.
Nan Gwammaja aka fara kawo Amarya bayan isha’i. Muka tarbeta gabaɗaya bayan an shisshiga da ita ko’ina. Dangin mahaifiyar Adnan ma suna gefe sai dai in an kira su amma dai an sauke ta a farko a shashen mahaifiyar Adnan ɗin ne. Misalin wajen tara na dare za su koma da ita sai aka ce mu yi mata rakiya gabaɗayanmu za mu je c a motocin gida tun da ga abokan Adnan nan duk da motocin su, har mun shiga mota sai na ga ban ga Rabi’atu ba, ban ga Jidda ba sai Baby ta ce mini ta bi motar Uncle Musbahu. Rabi’atun ne tana shashen Hajiya Iya tana salla in ji Jawaheer. Ni kuma jin haka sai na ce don Allah a ɗan jira ta.
Kawai sai Anty Bahijja ta fara faɗa wai ba ta son sanabe in ta idar da salla ga motoci nan su kawo ta mana. Da man Mimisco ce ta ce a tafi gabaɗaya kar ace za a raba tafiyar.
“Baƙuwa ce fa bai kamata mu tafi mu barta ba.”
Na faɗa har a cikin zuciyata.”
“Gaskiya ne kuma”
In ji Anty Zabba.
Gimbiya na cikin mota ita da Naja da Halima sai ga sun fito suna tambayan ba a si.
“Uwar iya ce ta ce ba za a tafi ba sai an jira Amaryan ku.”
In ji Anty Maimuna.
Kawai sai Gimbiya ta yamutsa fuska kafin ta ce” To sabon salo tusa a lasifika.”
“Ni fa ban ce ku tsaya jiran mu ba ku yi gaba za mu taho daga baya.” > Janaftybaby: Na faɗa ganin suna neman su taso mini har su Hauwa na ce su yi gaba cikin gida na koma sai ma muka haɗu da su a tsakar gida ita da Nafisan Kabir sun ɗauko kololin abinci Mimisco na bin bayan su. Sai take ce mini an manta ba a tafin musy da abinci ba, sai na ce Rabi’atu ta kawo kulan amma taƙi ba ni. Ko da muka fito sun tafi sai da muka jira Musbahu ya dawo ya ɗauke mu zuwa can gidan mun iske gida cike da dangin amarya da mu kanmu da man ashe akwai wasu masu ganin gidan Amarya da ba su zo nan Gwammaja ba.
Har ga Allah ban san abin da aka dafa ma yan kawo Amarya ba ni dai na ga Mimisco ta saka su Naja sun yi abinci ashe shinkafa ce jalop da kaza sai alele sai pepe chicken, amma ita Rabi’atu ta gani muna zaune a falo tare da su Hauwa ta zo gefena ta yi mini raɗa wai za ta ci alale amma tana jin kunyar tambaya sai na miƙe ina fadin bari na je na samo mata. Anty Zabba na gefe tace mene da ba za a faɗa a fili kowa ya ji ba.
“Sirri ne”
Na faɗa ina dariya ita kuma sai ta sunkuyar da kanta akwai kunya ita, Munnira na yi mata tsiyan ko Yallabai ne ya yi kira sai ta saka kanta cikin mayafi tana dariya. Nan da nan suka bushe mata da dariya.
“Amaryan Tafidanmu akwai kunya.”
In ji Jamila kuma ba ganin ido ba tana da kunya, ba ta iya haɗa ido da wanda ya girmeta.
Duk sai hankula ya dawo kan mu, Rabi’atu kanta na ƙasa sai mirmishi amma ba ta mgana. Hauwa na ce ma ga amana nan bar mata zan je na dawo sai ta ce ta karɓa ta dawo kusa da Rabi’atu tana faɗin” ƙyalesu ƙanwarmu.”
Munnira ta daddage ta saki guɗa tana dariya, ni ma dariyan na ke yi, Gimbiya na gefe ita da Halima kamar su mutu saboda baƙin ciki. Amma ba halin mgana.
Ciki na shiga in da dangin Amarya suke na ga suna ma zuba abincin wata cikin su na yi ma mgana ina son alele, sai ta ce mini haba bakomai ta samu filet ta saka mini guda huɗu sai da na ce ta rage za ta sanya mini nama na ce wallahi ta bar shi, wannan ɗin ma sha’awa ce wata ƙanwata ke so.
“Allah sarki hala kwaɗayin ƙaramin ciki ne?
Sai na yi dariya kafin na ce” Muna dai saka ran haka”
Sai itama ta rakani da dariya sai da ta faɗa sai na yi jim a zuciyata ina tunanin ko dai an samu rabon ne? Amma kuma ban ga alamun ciki a wajen Rabi’atu ba da man na san ta akwai son alale ko ni in na yi har ajiyewa take yi. Itama tana yawan yin shi sai na cire tunanin haka a raina. Na fito falon dai dai ana cewa mu ta shi mu tafi, tun da mun rako amarya gida fa kamar ba shi da yake sun yi jeren su da wuri Gimbiya kafa ɗaya kan ɗaya kamar falonta ta manta ya tashi daga falonta yanzu ya koma na wata.
Kowa ya ganni da alele bai yi nagana ba sai Anty Maimuna tana tambaya ta ni kuma kai tsaye na ce” Rabi’atu ke so shi ya sa na samo mata.”.
Matar nan ba sai ta fara faɗa ba.
“Miye haka? Ta son tana so tun a can ba ta yi magana ba sai da muka zo nan?
“Renin wayau ne “
In ji Halima.
Anty Bahijja na can gefe tana waya tana gamawa itana ta zo aka faɗa mata ba ta bi ba a si bq sai ta ara ta yafa wai wulaƙanci mu zo da abinci daga gida amma mu koma muna roƙo saboda zubar da kai.
Sai Rabi’atu ta ba ni tausayi sun ta so mata, cikin rawan murya ta ce” Ban san an yi alelen ba ne sai yanzu na gani raina ya biya. Ku yi haƙuri “
Ta faɗa kamar ta fashe da kuka har ta ma fara hawaye. Sai Anty Maimuna ta fara faɗin”To daga mgana sai kuka?
Ta faɗa cikin mele baki ni kasa ma mgana na yi, na ba ta alalan baiwar Allah ta ce na ma yar ba za ta ci ba.
“Karɓi abin ki me zai hana ki ci?
Sai ta yi shuru. Suwaiba ta ce na samu leda na saka mata in mun je gida ta ci amma yadda aka taso mata yanzu za ta ji ya fita ranta ne.
Sai na yi haka na koma na tambayo leda a ciki aka bani mai girma na juye mata alalan ina fitowa da karfi Anty Bahijja ta kira sunana gaban mutane har da waɗanda ba ahalin mu ba. Na amsa mata duk da na san kiran ba na arziƙi ba ne.
“Ke wai ba za ki kama girman ki ba ne, ji yadda kike rawan jiki a ƙan ƙaramar yarinya?
Sai na buɗe baki amma na ma kasa mgana. > Janaftybaby: “Ai ba da ita ya kamata ki haɗa kai ba. Gimbiya ce dai da ke sai ita data ke ƙarama ta bi bayan ku amma abin da takaici ji yadda kika ma y’ar da kan ki baya a kan yar cikin ki, domin ko za ta girme ma Jidda da kaɗan ne.”
Na ji na muzanta amma ban bari ta fahimta ba sai na yi mirnishi kafin na ce” Ai kema kin ce sa’ar y’ata ce. Shi ya sa sai nake yi mata kallon ƙanwa. Kuma maganar na ma yar da kaina baya ba haka ba ne, ni ina daraja wanda ya san ina da daraja, da Rabi’atu da Gimbiya duk ɗaya suke a wajena. Tun da matan Yallaɓai ne, abin da za ki fahimta wanda ba ya yi da kai ba za ka takura shi sai ya yi da kai dole ba. Wanda kuma yake yi da kai kar ka kwabe masa ƙokarinsa ka ta ya sa nuna girman karramawan da ya yi maka.”
Sai na dakata ina kallon Anty Bahijja kafin na sake yin mirmishi na ce” In dai wannan shi ne kike kira na zubar da kaina na yarda ki yi ta ɗauka a hakan.”
Jamila ta kada baki ta ce” Ni ban ga abin ceceku ce a kan wannan maganar ba wallahi ina laifin yarinyar nan? Duk in da Sadiya ta yi tana biye da ita sai kawai ta wulakanta ta! Haba Anty Bahijja kuma ai ba komai za ku rika mgana ba “
Jin kowa ya taso yana mgana yasa sai ta yi shuru. Baiwar Allah har sun saka ta kuka. Yumna ce ta je wajen ta hau jikinta ta ɗauketa shi ne ma ta daina sharan ƙwalla duk sai na ji ban ji daɗi ba. Gimbiya sai taɓe taben baki da fuska take yi amma ba ta yi magana ba, daga nan Gwamaja muka koma, Sadi na kira ya zo ya kai mu gida Yallaɓai na can tare da su Kawu, Gimbiya sai daga baya ta dawo kamar Direban Naja ne ya mai do ta.
Na yi ta ba ma Rabi’atu haƙuri da ta ce ba za ta ci alalen ba.
“Karɓi abin ki ki ci, haka suke kin san kowani dangi suna da na su matsalan. Sai kin kauda kai akan maganganun Anty Bahijja ko Anty Maimuna. Gimbiya kuma tana gaba dake so karki ɗauka da wani abu. A hankali za ki saba.”
Sannan ne ta karɓa, kuma na ga hankalinta tun da har kwana biyu da faruwan abun ban ji Yallaɓai ya yi magana sai na tabbatar ba ta faɗa masa ba. Jidda ranar laraba ta koma makaranta laraban ma da ta kai ni ce na saka baki da litini tun safe Yallaɓai ya ce ta koma na ce ya barta ta ɗan yi wanki da sauran shiri, sannan ya amince. Tun bayan bikin Adnan kuma sai na natsa a gida ba in da nake zuwa. Gimbiya tana fita shago ko wajen aiki Rabi’atu kuma makaranta ita da yara ni kaɗai ce ake bari ina gadin wannan wargajejen gidan.
Su Inna Mariya da iyalan Gandun albasa sun zo mini ganin gida gabaɗayansu sun saka albarka kuma wallahi na ji daɗi. Suma dai nasihan su na yi haƙuri na zauna lafiya da abokan zamana domin samar ma da mijin mu kwanciyar hankali na ce In sha Allahu.
Gimbiya ce ta fito da tsarin kwana ɗaya amma daga baya sai ta ce wai ba ta ganewa mu ma yar da shi kwana bibbiyu.
Har falona ta zo ta sameni wata ranar asabar da safe. Baby da su Khalipa sun tafi Tahfez Yumna ce kawai ita kuma tana shashen Rabi’atu wajen Yallaɓai da safe da ya shigo mu gaisa ta dafe shi.
Kallonta na yi cikin mamaki ni da man na san tun da na gan ta a falona na san banza ba ta kai zomo kasuwa.
“Kwana ɗaya nan gaskiya bana gane mishi. Mu koma biyun kawai Maman Jidda.”
Ta sake faɗa sai na yi dariya kafin na ce” Ba matsala da man ni biyun na ce ke ce a baya kika ce mu ma yar da shi ɗaya.”
“Gaskiya mu dawo biyu nan ɗayan nan bana gane mishi.”
Sai da na sake murmusawa sannan na ce mata shike nan.
“Za ki faɗa ma Baban su Khalipa ne? Yau ba Daddy su Yallaɓai an koma Baban su Khalipa na fahimci tunda ya yi auren nan ta daina kiran shi da Daddy sai da Baban su Khalipa.”
“Ina ruwan shi? In dai duka mun amince shi ba shi da matsala kin sani “
Sai ta gyaɗa kafin ta miƙe tana faɗin” To sai ki faɗa ma ita Rabin”
Sai na amsa mata da cewa zan faɗa mata har ta bar falona ina mamakinta. Ranar Yallaɓai sai Yamma ya fita, Rabi’atun da ta shigo na faɗa mata mun sauya tsari ta ce to, Yallaɓai kuma na manta ban faɗa masa da ya bar ɗakin Rabi’atu ɗaki na ya dawo ya yi kwana ɗaya ya koma ɗakin Gimbiya ya yi kwana ɗaya, ashe ita a tunanin na sanar da shi ni kuma na sha’afa saboda a ranar da yake wajena aka yi ma Ma’u C.S An ciro mata jariri ba rai ta zubar da jini > Janaftybaby: sosai hankulan mu duk sun tashi mun ɗauka ma ba za ta yi rai ba. Ba gidan nake yini shi ya sa ban ma yar da kaina na sanar da shi ba.
Ina gidan Ma’u tun da an dawo da ita gida. Baaba ke kwana da ita can muka kai dare tare da su Ya Aina Yallaɓai ya kira wayata ni na ɗauka zai yi mini faɗan na kai dare alhalin ya hana ni yin dare in dai na fita da mota. Sai na ji muryansa a kausashe sannan ina jin tashin mgana amma ban san ko ta wace ce ba.
“Kin taho ne?
Lokacin takwas ne da wani abu na dare kenan yau ya dawo gidan da wuri.
“A”a zan dai ta so. Ban san ma lokaci ya tafi ba ka yi haƙuri “
“Ki taho yanzu ina jiran ki”
“Me ya faru?
“In kin zo za ki ji “
Ya faɗa sannan ya kwashe wayar ina jin haka na san ba lafiya, ina jin haka ban tsaya ba na yi musu sallama tare muka fita da su Ya Aina na ajiye su a juction na wuto gida.
Abin da ya ba ni mamaki Yallaɓai na haraba yana jirana shi da Gimbiya kamar yaƙi.
Ina gama parking ɗin motana na fito Gimbiya ta taroni da cewa” Maman Jidda baki faɗa ma Baban su Khalipa mun sauya tsarin kwanaki kwana ba ne?
“Ban faɗa masa ba me ya faru?
Na faɗa ina kallonta saboda mamakin abin da ke faruwa.
Yallabai na kalla kawai sai na ga ya juya zai shiga shashen Rabiatu Gimbiya ta bishi tana faɗin”Ai ka ji sai ka dawo bangarena sai gobe ne za ka koma mata.”
“Ba zan koma ba. Wannan tsarin ku ne ba nawa ba, nawa wanda na sani jiya na shiga ɗakin ki, yau da daddare na fita zan kwana a bangaren Rabi’atu.”
“Wallahi ba ka isa ba”
Gimbiya ta faɗa cikin ɗaga murya ta juya zai shiga ta sha gaban shi har tana riƙe masa riga.
Ni dai sai na yi tsaye kawai ina ganin ikon Allah.
“Ba ni hanya in wuce.”
“Ba fa za ka koma shashenta ba sai gobe wallahi “
“To ni kuma yau a nan zan kwana in kin isa ki hana ni “
“Ni kuma wallahi in har ka kwana a ɗakin yarinyar nan Da haƙƙin kwana na Allah ya isa ban yafe ba”
Gimbiya ta faɗa har tana shan wallahi. Shi kuma Yallaɓai ya fizge rigar shi ya tureta gefe ya shiga yana faɗin” Da sauki tun da ba tsine mini za ki yi ba “
Ta kwashi kururuwa za ta bi shi ciki, shi ko yana shiga ya rufo ƙofar ta ciki sai ta fara bugu tana kiran sunan shi.
“Yusuf ni za ka wulaƙanta? Wallahi in har dai ka kwana a ɗakin nan ban yafe maka ba tun da dai haƙkina ne yau “
Kawai sai ta fashe da kuka ni wallabi ban saba ganin haka ba yasa sai jikina ya yi sanyin da na kasa motsi. Ganin maigadi na gefe yana kallon komai ita kuma tana ta kuka tana buga ƙofa tana Allah ya isa ba ta yafe ba. Yau ba Baban Khalipa Yusuf ne kai tsaye.
Ƙarisawa na yi ina mai saɓe da yumna da ta fara barci a mota na ƙarisa wajen Gimbiya ina kiran sunanta amma ba ta ji na.
“Haba don Allah wannan ba girman ki ba ne. Ki zo mu tafi bangaren ki.”
Amna bata saurareni ba, ganin kamar ba ta cikin hayyacinta yasa na saka hannu ɗaya na rike ta ina fadin” Megadi na ji fa kar ki jawo mana mutane don Allah.”
“Gwara ya ji. kowa ya ji cewa ba ya adalci. Maman Jidda yau fa yana dawowa shashen yarinyar nan ya tare na shiga na yi masa mgana a bangarena yake ya fara masifa shi bai san da haka ba. Ita kanta ta ce masa kin faɗa mata amma bai yarda ba ya kira ɗin ma ya tabbatar daga bakin ki amma ki duba fa a gabanki ya shige ciki saboda zalunci har yana rufe mini ƙofa saboda tozarci?
Ta faɗa tana kuka, abin da Yallaɓai ya yi bai kyauta ba amma ita ta ja ma kanta, da ƙyar na lallasheta na ja ta bangarenta. In da Allah ya taimaka yara suna bangarena tare da Baby. Haka na zauna ina ba ma Gimbiya haƙuri amma tana ta kara shan wallahi in dai ya kwana a bangaren Rabi’atu ba ta yafe masa ba
“Ki yi hakuri mana. Ki yi masa uziri tun da bai sani ba.”
“Da bai sani ba amma ai yanzu ya sani.”
Ta faɗa tana jan majina.
“Ki yi haƙuri zuwa da safe sai mu yi magana gabaɗaya “
“In yana so na saurare shi to ya fiti daga ɗakin yarinyar nan in kuma ya kwana wallahi ba zan saurari kowa ba “
Jin haka yasa na ɗaga waya na kira Yallaɓai sai da ta katse na sake kira ya ɗaga ko mgana bai yi ba daga gani ranshi na ɓace ne.
“Yallaɓai don Allah ka fito mu yi magana.”
“Ba zan fito ba. Ke ma ina mai ba ki shawara karki dame ni in ba haka ranki ya ɓaci.” > Janaftybaby: Ya faɗa a fusace.
“Ka yi haƙuri ka fito don Allah.”
“Ta ce Allah ya isa to zan kwana Allah ya bi mata haƙƙin ta kamar yadda ta ce.”
“Ba za a yi haka ba. Ka dai yi haƙuri “
Da ƙyar na samu ya anince zai fito mu yi magana da ya fiton ma cewa ya yi ba zai shiga bangaren Gimbiya ba jan shi na yi zuwa bangarena mu ka yi magana, ina ba ma Yallaɓai haƙuri yana yi mini tsawa.
“Ina ruwan ki? Ki ƙyaleni kar ki dane ni “
“Kar ka yi haka. Ka je ka kwana ba gobe ba ne shike nan!
“Ba zan kwana ba “
Ya katse ni, sannan ya cigaba da faɗin” Kina faɗa mini wai ta fada za a dawo kwana biyu ni kun faɗa mini ne? Kuma ma haka za ta zo tana mgana da ni gaban Rabi’atu tana yi mini rashin kunya?
“Ka yi haƙuri ai ta fada mini laifina ne da ban faɗa maka ba”
“To kema ki fita idanuwana. Ke ce ke aurana da za ki riƙa yanke hukunci a gidana ba tare da sanina ba?
Ai ina jin haka sai na yi shuru, ya riƙa masifa har da rantsuwan zai gyara bangaren shi da yanzu sai dai bishi can in ya ga dama ya kori kowa ya kwanta shi kaɗai.
“Ka yi haƙuri ‘
Nawa kenan ban haƙuri, dakyar na samu ya amince zai kwana a ɗakin Gimbiya.
“Ka yafe mata Allah ya isa da ta yi sheɗan ne “
“Ke ina ruwanki da abin da zan yi mata? Sadiya kina mini abin ba na so wai nan gidan gidan ki ne ko gidana?
Ina dariya na ce”Gidanmu dai Ranka ya daɗe “
Sai da na saka shi dariya. Na samu dai ya shige ban san yadda suka ƙare ba, yara ma a bangarena suka kwana da safiyar Allah Gimbiya ta bugo mini waya tana sharban majina wai da na sani na ƙyale Yallaɓai ya yi kwanciyarsa a in da yake so.
“Tun da ya shigo ya ke faɗa sai abin da ya manta bai faɗa mini ba. A falo ya kwana a kan kujera da asuba da na gaishe shi wai in na ma sake gaishe shi zai yi mini Allah ya isa.”
Ni gabaɗaya ma sun sakani a tsakiya. Yallabai tun bakwai na safe ya fita na kira shi a waya
Yace kar na dame shi kamar ya san maganar Gimbiya ne ya taka mini burki.
“Sadiya in dai ba ke kika auro mini Saudatu ba to ki fita a mganata da ita. Tsakanimmu ne ba ruwanki.”
“To ta zo tana mini ƙorafin kai ma kace in ta sake gaisheka Allah ya isa.”
Kawai sai ya yi tsaki kafin ya ce” in ta sake zuwa ki kore ta. Ki faɗa mata ni na ce ba ruwanki”
Zan yi magana ya tare ni da cewa”Wallahi kema zan yi miki Allah ya isa in baki ƙyaleni ba haba.”
Ai ina jin haka na kama kaina daga ƙarshe ya ce in na sake yi masa magana wallahi zai yi mana yaji kuma in ya tafi ba zai dawo ba sai ya ga dama.”
“Abin har ya kai haka? To Allah ya huci zuciyarka “
Ya ce Amin a fusace ya kashe wayarsa tun da na ji haka na cire kaina a ciki. Da Gimbiya ta dawo tana faɗa mini wai ita Baban su Khalifa zai wulakanta saboda wata zaunar da ita na yi na faɗa mata gaskiya da cewa ta yi haƙuri ta kauda kanta a kan Yallabai da Rabi’atu in ba haka ba wata rana komai zai iya faruwa. Ta koma gefe ta zama yar kallo amma ba ta ji ba.
A cikin kwanakin ma sun sake wata rigima wai in ya shiga ɗakin Rabi’atu da daddaee zai yi mata sallama yana ɓata lokaci, rigima suka yi sosai Gimbiya ta sake masa Allah ya isa a kan haƙkinta shi kuma ya ce ya gaji ya ɗaga waya ya kira Nene ya faɗa mata. Sai da Nenen ta zo gidan sulhu ne na ji labari gabaɗaya ta taramu ta yi mana faɗa shi dai ta jadadda masa ya yi adalci ne.
“Nene ina iya bakin ƙoƙarina. Saudatu ta cika ƙorafi sannan ba ta da hakuri tun da na yi auren nan ba ta bar mu mun zauna lafiya bq”
Ita kuma tace me ya sa yake mata rashin adalci in yana da gaskiya ai ba za ta riƙa mgana ba.
Rabi’atu dai shuru bata mgana, Yallaɓai ya rantse ya ƙara rantsewa in Gimbiya ta sake masa Allah ya isa zai dauƙi mummunan mataki a kanta Nene ta yi mata faɗa ta kuma sakata ta bashi haƙuri nima ta yi mini faɗa da nariƙa nuna ma Gimbiya wani kuskureta in ta yi wani abun
“Ko ta nuna mata wannan zata ji ta ne? Wallahi Nene Sadiya ba ta taba ɗaga mini hankali da zan auero Saudatu ba a wannan auren ma bata ɗaga mini ba. Amma kin ga wannan y’ar taki? Haƙuri na ne ya ƙare amma ta yi mini diɓar albarka ba adadi ina shanyewa.” > Janaftybaby: Nene dai ba ta bar gidan ba sai da ta yi musu sulhu. Kwana biyu kamar an samu canji. Rabi’atun ma na nuna mata ta riƙa bin Gimbiyae har ɗaki tana gaisheta. To na ga tana shiga, amma fa kishi Gimbiya take yi da ita kamar hauka kishin da take yi da ni ne ya koma kan Rabi’atu tun da ta ga Yallabai a gaban mu ma yana nuna mata rawan jiki.
Rigima ta lafa sama da wata ɗaya kawai a wani dare muna kwance da Yallaɓai yake faɗa mini ya siya ma Rabi’atu mota saboda zirga-zirgan makaranta cikin satin nan za a kawo motar. Kamar zan yi masa mgana na ce ya manta da Gimbiya! Domin ko kwanaki ta yi masa mganar ya sauya mata mota ko ciko ne ya yi mata ta saida tata ta siya wata ya ce sai zuwa gaba.
Kar yace ina baƙin ciki ya sa ban ce komai ba. Mun yi maagana da kwana biyu mota ta iso, Musbahu ya tuƙo ta ya kawo ta gidan Corolla ce Gimbiya ta ɗauka motarta ce har ta fara murna sai gogan ya ce na Rabi’atu ne.
Gimbiya ta cika ta yi fam Rabi’atu ta yi ta santin mota tana murna nima dai na fito na gani na taya murna lafiya lau muka kwanta da mota amma ko da garin Allah ya waye gabaɗaya an yi ma gilashen motar nan rugu rugu.