Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    *EID MUBARAK FANMILY. ALLAH YA MAIMAITA MANA. SON SO.

    Da ma Amina ce da Faridan Tariq sai Marwa suka kwana a gidan. Yallaɓai yana ganin Amina ya washe baki yana ce mata ashe ta zo?
    Ita ko saboda ta kunna shi sai ta ce ai zuwa bikin nan ya zame mata dole. Ba kunya ya ce ya ji daɗin zuwanta. Megidanta ya tambaya da yara tace suna nan lafiya.

    Faridan Tariq kuma tsiya ta fara yi masa wai ya yi biyu ba zai haƙura ba sai ya haura uku.
    Yallaɓai na dariyan nishaɗi ya ce” Ta in da za ki gane ni gwarzo ne ba. Ba matsaroci irin mijin ki ba.”
    Ya faɗa yana nuna Tariq wanda ke gefe yana magana a waya ne tun shigowarsu gidan
    Kawu Abba kuma muna gaisawa da shi ne.

    Shewa Farida ta yi kafin ta ce” In dai tsoro ne to Allah kar ya cire masa wannan tsoron har abada.”
    “Muguwa kike Farida?
    In ji Yallaɓai yana dariya.
    “Sadiya kina jin kawarki ko!
    Ya faɗa yana kallona ina dariya na ce” Bar ta sai dai in bai gano wata yar faka faka kamar yadda ka gano ba.”

    “Wallahi da man na ga a can yana bin yan mata gidan su Rabi’atu da kallo ko ya ga ni yana so ne?

    Ya faɗa yana dafa kafaɗan Tariq daidai lokacin da ya gama wayar.

    “Nima na lura da munafukin yana ta kallon wata yar fara nan ƙasa ƙasa.”

    Kawu ya faɗa yana shafa sajen sa, Farida ta ce ba su gani da kyau ba tana kare ma mijinta.

    “To ke ina ruwan ki? Ba shi da bakin mgana ne?

    Yallaɓai ya faɗa yana dariya.
    Kawu ya ce ina zai yi magana ya san gaskiya.

    “Ko dai kai ne ka ƙyallo wata kana son ka yi mini kage Kawu?

    Tariq ya faɗa yana kallon Kawu shi kuma sai ya buɗe baki amma ya kasa mgana ni da Farida muka fashe da dariya.

    “Ina matarsa? Ina marwatun? To ta shirya wata ƙila za mu koma Maiduguri karshen shekara.”

    “Tariq haka ka zama?

    Kawu ya faɗa yana rike baki.

    “Ƙarya na yi? Kai Tafida ba ka gan shi a ranar ɗaurin aure da muka je gaisuwan surukai yana tambayan sunan wata budurwa ba?

    “Kamar fa na gan shi.”

    Yallaɓai ya faɗa yana danne dariya.
    Kawu ya jinjina kai kafin ya ce” Yaran nan abin tsoro ne. Mu ɗan bangaji juna ne lokacin da za mu shiga za ta fita ita kuma, sai ta ba ni haƙuri na ce ba komai amma saboda ku magulmata ne har kun hango wai ina tambayan sunan ta ba?

    “Ashe dai ka yi magana da ita.”

    “Na yi sai ka hana ni Ubana.”

    Kawu ya faɗa sannan ya kalleni yana faɗin” Surukata ni fa ban ga matata ba ban ga yayana ba.”
    Ina dariya na ce suna ciki bari na yi mata mgana.
    Sai ya koma ya zauna saman kujeran falon yana faɗin” Yauwa Uwargida ran gida. Ke ce ke da gidan gabaɗaya. A ɓata miki rai mu yi tawaye wallahi “

    Ya faɗa yana hararan Yallaɓai kamar ya san da shi ake yi ya ɗaga sannu alaman sarander kafin ya ce” Ba ma mai ɓata mata. Ni kaina in na ɓata mata abin a yi mini hukunci ne “
    Kawai ba zato zan wuce na ji Yallaɓai ya rumgumeni ta baya ina ƙoƙarin ƙwace kaina ya sumbace ni a gefen fuska yana faɗin.

    “Na gode Abar ƙaunata. Ubangiji ya ruɓanya miki a ranar lahira.”

    Farida da su Tariq suka amsa da Amin har da Kawu.

    “Gaskiya Sadiya tana da kawaici. Wallahi ni ba zan iya abin da ta yi ba har ga Allah. Tun auran Gimbiya na san ita jaruma ce to ga wannam ma. Gaskiya na jinjina mata.”

    “Gaskiya abin a jinjina mata ne.”

    In ji Tariq.

    “Shi ya sa nake ƙara jadaddaa ma Tafida cewa ya riƙe ta da kyau. Domin kaf cikin matansa ba mata kamar Sadiya. Domin a wannan zamanin ka samu macen da ka yi mata abubuwa da dama ta kauda kai, ta yi maka kara ta mutumta rigarka a idanuwan danginka da danginta ba abar tozartawa ba ce.”

    “Gaskiya ne.”

    Tariq ya sake faɗa, ni kunya ma suka kamani na ƙwace kaina ina faɗin” Ka bari mana Yallaɓai.
    “Wai ina miki godiya?
    Ya faɗa yana kallona da ka gan shi za ka san yana cikin farinciki.

    “Ni me na yi? Ai umarnin Allah ne ban isa na ja da hakan ba.”

    “Duk da haka Na gode miki.”

    Ya faɗa yana mai kallona tare da yi mini mirmishi.

    “Muna godiya Madam”

    Tariq ya faɗa sai na amsa shi da cewa” Kai dai kana tsoro ko? Ko ƙawata ta bake ko’ina ne?
    Na faɗa ina dariya, ita kuma Faridan tana cewa ita ba ruwanta ya yo mana ai ba kanta za ta zauna ba.

    “Ba wani cika baki. Ba ke kika hana shi ya ƙara ba.”

    In ji Yallabai.

    “Kuma wallahi tsoron ta yake ji.” > Janaftybaby: In ji Kawu nan suka haɗe mata kai suna ta caccankanta da cewa kamar fitilar besfa Tariq dai ya ƙi kara aure sai ita kaɗai haba ai gwara dai ya ƙara ko ɗaya ne. Shi dai Tariq na gefe yana dariya.

    “To ku ba shi matar ya ƙara mana? Wallahi ko a jikina tun da ba kaina za ta zauna ba amma gaskiyan mgana ba zan iya abin da Sadiya ta yi ba wallahi.”

    “Ka ji ba “

    Kawu ya faɗa yana dariya kafin ya cigaba da faɗin” Za ko mu ba shi mata mu ga karyan cika baki. Kai ka zo Rano na duba maka cikin dangi.”

    “An gama Kawun mu.”

    Tariq ya faɗa yana dariya.

    “Amma tare da shi za ku ƙara ko?

    Yallabai ya tare shi.

    “Me?

    “Auran mana.”

    “Ah ni kam ai na tsufa, na fara furfurta matata Marwatu ta ishe ni.”

    “Kai ma tsoron matar taka kake yi kenan?

    Farida ta faɗa, sai ya sosa keya kafin ya ce” Ki fahimta mana “
    Tariq ya shuri kafar Kawu yana faɗin”Ka iya addabata da maganar aure kai ma fa? Me ya hana ka ƙarawan?
    Ga tafida har ya yi ta uku?

    “Na ce muku matata ta isheni kar ku tsananta bincike”

    “Sai mun tsananta.”

    In Tariq.

    “Ko ba ka da lafiya ne?

    Yallaɓai ya kwaɓo magana ni da Farida muka tafa muna sunne kai.

    “Ba shi da lafiya ya haifi su Abdallah munafuki lafiyan sa ƙalau”

    Tariq ya faɗa yana dariya da Kawu ya ga sun dame shi kawai sai ya kalle su kafin ya ce” Ba ni da karfin mazukutan da zan tara mata shike nan kuke son ji?
    Sai suka yi shuru suna kallon shi, ni da Farida saboda kunya sai muka kama hanyar barin falon saboda kunya.

    “Matata ma haƙuri take yi da ni. Ta ina zan jajiɓo wata?

    Kawu ya faɗa a maganarsa ba alamun wasa.

    “Wallahi ƙarya kake yi munafuki.”

    Tariq da Yallabai suka haɗa baki wajen faɗa ni da Farida muka bar falon muna dariya in dai su ne in suka fara to sai kowa ya yi shuru ya bar su.
    Marwa na ce ma ta je mijinta na kira ta ce to da man ta tsaya yi ma su Abdallah wanka ne.
    Jidda na tura da kayan kari falon iyayenta sai ma ta dawo da shi ta ce sun ce a sun yi beakfast daga hotel ɗin da suka kwana, sun jima a gidan sama da awa sannan suka fita. Tariq da Kawu duk a ranar za su koma. Sun ce ma matan su su shirya kafin su dawo. Marwa ke son zuwa gida sai na ce ta yi sauri ta je ta dawo kafin su dawo. Amma ba ta tafi ba sai da suka ta ya ni muka gyara gidan sannan muka yi abincin rana Allah ya sa ba mu dafa da yawa ba tun da sai da na kira Yallaɓai a waya na yi masa maganar bangaren Amarya da danginta ya ce kar na damu Mimisco ta kira shi ta ce za ta yi direba zai kai sai na ce shike nan ta hutattashe ni.

    Farida na ta mamaki wai kuma sai na dafa na kai! Na ce me ye a ciki? Ita kam ta ce ba za ta iya ba.
    “Ba zan ta yar da hankalina balle na zama abin tattaunawa a dangi ba amma wallahi ba zan yi ba.”
    Ina ta dariya ita ko tana shan wallahi. Shi ne har muka gangaro maganar Gimbiya ina ba ta labarin duk abubuwan da suka faru kafin auran nan.

    “Ba irin shawaran da ban ba ma Gimbiya ba ta ƙi jin maganata. Ni yanzu haka makiyayarta ce. Su Anty Bahijja ne masoyanta su ta rike suna zugata tana yi ma mijinta rashin kunya. Jiya fa a gaban dangin Rabi’a ta kunyata ni da Mimisco abin ba daɗi wallahi.”

    “Ai ga shi nan ta bar ma kanta abun faɗa. Sai yi da ita ake da cewa mijinta zai ƙara aure tana ta hauka. Gaskiya abin da ta yi ba aji ba ne, ni kaina ba ta wani yi da ni tun ma kafin auranta da Tafida. Bayan auran su kuma ganin muna tare ba ta shigo ni ba.”

    Ina dariya na ce” Ko yau kika je Allah ya sa ma ta kalle ki. Za ta ce kina murna tun da kika zo biki kika kwana a gidana.”

    Farida ta ce to sai dai ta ce amma ita ina ruwanta? Tun kafin auran ta da Tafida ya ke aminin mijinta kuma ko shi yayan nata ai ya je ɗaurin auran

    “Allah na tuba su maza ina ruwan su?

    “Ai shi kan shi ya yi ta faɗa da ya ji labari kin san Tafidan bai sanar da shi ba sai Hajiya ce ta kira shi tana faɗa mai akan na gida ne ma. Kai tsaye ya kira shi ya ce in ta sake yi masa gaddama ya kora ta gida.” > Janaftybaby: Na riƙe baki ina faɗin” Lamarin har ya kai haka? To Allah ya kyauta.”
    “Ni in na je zan yi mata faɗa ruwanta ne ta ji ko kar ta ji ta gyara “
    Ni dai da man ba komawa zan yi ba, zuwa la’asar suka barni ni kaɗai a gida har su Jidda sun tafi Gwammaja. Farida tun wajen biyun na rana ta wuce Gwammaja daga can za ta ƙarisa sabon gida. Amina da Marwa tare suka fita zuwa Ɗorayi, har Yumna da ita Baby suka tafi suka bar ni kaɗai.
    Zuwa can Yallaɓai ya kira ni ya ce yan uwan Rabi’a za su kawo ta nan gidana na ce sai sun zo. Na tashi na ɗan ƙara gyara gidan na saka turaren ƙamshi
    Ganin ba kowa a gidan har zan kira Munnira na ce ba za su dawo ba ne! Sai ga su ita da Hauwa sun shigo, na ce wayar dake hannuna su nake shirin kira na ce za a kawo mini amarya babu yan tawagata suna ta dariya.

    Sai gabda mangariba suka zo. Musbahu ne ya kawo su a motar Yallaɓai, daga Gwamnaja suke an kai ta wajen Nene da su Maman Farko. A can kuma sun fara kai ta shashen Gimbiya. Hauwa ke faɗa mana Mimisco ce ta yi mata fata fata shine da aka kai mata Amaryan ta fito ta karɓa. Ni ma sun kawo min ita suka kuma damƙata amana a hannuna a matsayina na babba na kuma riƙe hannunta na ce na karɓa Allah ya zaunar damu lafiya.

    Matar Baffan Rabi’atun na Kano da take zaune a gidan su ce ta kalle ni tana mai faɗin”Rabi’atu ƙarama ce a cikin ku don Allah a kula da ita. In ta kauce a karkato da ita, duk da ba kwa gida ɗaya tun da ke ce babba ki taya mu riƙe wannan Amanar don Allah”
    “In sha Allahu. Da yake ba daɗewa nima zan koma can ba matsala Allah ya ba mu zaman lafiya.”
    Aka amsa da Amin gabaɗaya sannan aka yi addu’o’i sun kawo mini kayan su fulawa har da su dakuwa da nakiya sai tarurukan kamshi na ɗaki da na kaya sai atamfa da kololi sai filantai da kofuna har da kayan kwalliya kaya fa himiɗi ni na ce ma su rage kayan sun yi yawa suka ce ina tuwon girma a miyan shi nama. Sun kai ma surukanta da ɗayar abokiyar zaman nata. Muka karɓa su Munnira suka taya ni godiya nan na tsayar da su suka yi salla sannan suka tafi bayan sun sake yi mini sallama tun da sun ce suna ma yar da ita gida suma za su wuce. Baƙin Maiduguri kuma asuban cin gobe za su ɗau hanya

    A bakin Musbahu nake jin suma su Nene haka aka kai musu himilin kayan arziƙin nan ita da su Maman Farko, har da na yayyen miji.
    Ina ta mamaki daga baya kuma sai na cire shakku suna da al’adu sannan daga gani suna da hali da rufin asiri. Sannan kamar yadda suka ce ne Tuwon girma miyan shi nama shima Yallaɓai ya yi harkan girma in sun yi masa kara babu laifi a ciki. Ban bari su Muniira sun tafi ba na ce su tsaya mu raba kayan nan suka ce bai kamata ba na bari in Yallaɓai ya zo ya gani sannan sai da suka faɗa na yi wannan tunanin. Dare ya yi sosai shi ya sa ban kai su gida ba tun da Yallaɓai ya hana ni tukin dare tun da na faɗa rami wata rana na dawo daga ɗorayi ni da Baby da Yumna mota ta maƙale na kira Yallaɓai a waya. Ƙarshen ta dai nan motar ta kwana sai washegari aka ciro ta daga ramin.

    Mun yi waya da Marwa sun wuce. Farida ce ta ce mini tana Gwammaja can za ta kwana sai a safe za su ɗau hanya. Ni da kaina na faɗa mata kayan da dangin Rabi’atu suka kawo mini sai itama take ce mini.
    “Haka suka kai ma Gimbiya. Sannan nan ma bayan na su Nene har da na yayyen miji, har maza suna da kula. Waliyi kuma Baba Tafida na da shadda.”
    Na riƙe baki ina faɗin” Haka Musbahu ya ce. Ma sha Allah. Allah ya saka da alheri ya ba mu zaman lafiya.”
    Ta amsa da Amin ta cigaba da faɗin” Ai Gimbiyar da kyar ta fito fuskar nan ta kumbura saboda kuka na ce sakarya zauna ki kashe kanki saboda namiji. Shi kin ga bai fasa ba, ba kuma zai fasa ba ko da mutuwa za ki yi”

    “Wallahi..”

    Na faɗa ina jinjina kaina.

    “Da zai fasa tun boren da ta yi a farko da ya fasa ɗin.”

    “Ai ba zai fasa ba wallahi. Ko don ya ga karshenta ma sai ya ce sai ya yi. Ai an ce da safe Mimisco ta je ta yi mata faɗa akan abin da ta yi jiya. Nene ma an ce ta kira ta a waya shi ne har yau ta ɗan saki jiki kaɗan.”

    “Allah ya kyauta ” > Janaftybaby: Na faɗa ta amsa da Amin sannan muka katse wayar.
    Su Jidda sai wajejen goman dare Adanan ya dawo da su ina ta ma kiran wayarta ba ta ɗauka ba suna shigowa na fara masifa sun barni ni kaɗai a gida ta je sun yi zaman su.

    “Ki yi hakuri Umma. Ba mu samu me dawo da mu ba ne. Uncle Musbabu ne kuma Anty Mubeena ba lafiya ya tafi gida. Sai Uncle Adnan ne shima bai daɗe da dawowa ba.”

    “Ba sai ki fito ki jagoranci ƙannen ki ku samu adaidaitasahu ku dawo gida ba? Sannan ina kika saka wayarki ina ta kira ba ki ɗauka ba?

    “Ban ji kiran ba Umma tana jaka “

    Hararanta na yi ta wuce tana dariya. Adnan da man bai shigo ba yana ajiye su ya juya. Baby ce ta fara mini surutu wai Amaryan Abba an kawo ta Gwammaja, kaf labarin abin da ya faru sai da ta ba ni Yumna saboda Gajiya a can ta fara barci ko da suka shigo tana saɓe a kafaɗan Jidda. Sai na ce ta shigar mini da ita ciki.
    Sai da duk ta gama surutunta sannan ta ce mini wai yunwa take ji.

    “To ni ce zan ta shi na dafa miki abin da za ki ci kenan uwata Maimuna?

    Na faɗa ina hararanta sai ta miƙe tana dariya ta wuce na rakata da tsaki. Kayan da man su Munnira suka kama mini na kai shi ɗayan bedroom ɗin da niyyar sai Yallabai ya gani sannan zan yi kasafin shi. Na ɗauka zai shigo yi mini sallama ne amma tun da na ga sha ɗaya ta yi na cire rai. Ni kaɗai a falo su Jidda sun gama duduman su sun shige ciki.
    Nima dole na tashi na kashe komai na shiga ciki. Tiolet na shiga na kama ruwa ina fitowa na ga wayata na haske kafin na ƙarisa wayar ta katse.

    Yallabai ne, ina shirin bin bayan kiran shi sai ga saƙon shi ya shigo.

    “Ku kwanta sai da Safe Sadiya ta. Tariq ya rako ni yanzu haka ma muna ƙofar gidan.”

    Sai na ji jim ina sake bin saƙon sa da kallo, to mi ye na sai ya wani faɗa mini za a raka shi ɗakin Amarya. Duk da na so kar na ji zuciyata ta motsa sai da kishi ya taso mini. Shi ya hana ni mayar masa da amsa, ganin kamar zuciyata ta ɓaçi sai na juya na koma tiolet na ɗauro alwala na zo na yi shafa’i da wuturi na yi addu”o’ina da Allah ya cire mini damuwa a wannan daran ya sanyaya mini zuciya.
    Na yi ta maimaita LA’ILAHAILLAH ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZ ZALIMIN.
    Sau arba’in har sai da na ji zuciyata ta yi sanyi.
    Ina idarwa na yi shirin barci Yumna da man tuni ta kai england. Gefenta na kwanta bayan na yi mana addu’an barci na shafe mu gabaɗaya wutar ɗakin na rage sannan na kunna suratul Maryam a wayana na ɗan rage ƙara na saka shi gefena na rumgume y’ata muka shige bargo.

    Da farko sheɗan ya fara hasko mini abubuwan da ba su kamata ba na yi ta ta’awizi a cikin zuciyata cikin ikon Allah sai barci ya fara fizgata ban daɗe ba barci ya sace ni, ba ni na farka ba sai asuba na kuma ta shi wasai kamar ba ni ba. Na ɗauka zan ga Yallaɓai a ranar shima haka aka yi har dare ba shi ba wayarsa da Amina ta zo yi mini sallama ma nuna mata kayan sannan na diɓa mata kayan fulawan da kayan kwalliya na ce ta kai ma su Afra sai filet da kula guda ɗaya. Tun da gogan yana can yana cin amarci bai samu fitowa ba, aka sake kwana ba Yallaɓai ba wayarsa ni kuma ban neme sa ba na riƙe mutumcina amma in na ce zuciyata ba ta motsa ba wallahi na yi ƙarya daurewa kawai na ke yi. Amma ni kaina na san Yallaɓai ya samu chajiin Lambu ba zai yi wasa da ban ruwa ba.

    Da na ga ba shi da niyyar zuwa ranar laraba da yamma Rahila da Ma’u da ke da tsohon ciki suka sake leƙoni da man ina da niyar kiran Hauwa ko Munnira ne su taya ni na raba kayan sai ga su Rahila. Su suka taya ni muka zauna na kasa shi, har Gwaggo sai da na dibar ma turaren wuta da kayan fulawa haka su Ya Aina. Hauwa da Munnira ma daidai da nawa na ɗibar mana saboda a sha’anina ko ya’nuwana albarka yadda suke tsaya mini. Kayan kwalliyan kuma suka ce na bar ma yara tunda ƴaran mata gare ni, Alhajinmu ma zaɓa masa yar kula mai kyau na ce zan kai masa Atamfar kuma suka ce na ɗinka tunda ni suka ba mawa. Su suka tafi da y’an gidanmu har na Gwaggo da Alhajinmu tun da Dorayi suka ce za su fara sauka kafin su wuce gidajen su, jin haka yasa na diɓi kayan fulawan da turare na ce Ma’u ta kai ma Baaba, duk da ta daɗe a can Yashe sai a satin nan ta dawo Kano. > Janaftybaby: Sun fita ba daɗewa aka kira mangariba ina cikin yin salla na ji ana ta kiran wayata sai da na idar na duba na ga Yallaɓai ne sai bayan kwana biyu ya tuna damu. Jidda ma sai jiran shi take yi tana so ta komawa makaranta ranar lahadi. Ta ce mini ta kira shi bai ɗauka ba, na ce kar ta sake kiran shi ai ya san da komawar na ta.
    Sau biyu yana kirana ina salla sai da na idar ya sake kira wayar na hannuna na ƙi ɗauka haka kurum na ji ina jin haushin shi. Har kwana biyu muna gari ɗaya amma Yallaɓai bai neme ni ba! Gwara Gimbiya suna gida ɗaya na tabbata ba zai kwana su tashi ba ta gan shi ba.

    Sai da ya kara kira na huɗu sannan na ɗaga tana ma gabda katsewa.

    “Umma Sadiya.”

    Ya faɗa yana ɗariya. Sai na ji zuciyata ta ƙuntata, wai Umma Sadiya sai yau na ji kamar da gayya ya faɗi sunan e mana na zama Umma shi ko yanzu ai sabuwa gare shi.

    “Uhm Ango.”

    Na faɗa ina ƙoƙarin daidaita yanayina.

    “Uwargidata.”

    Yallaɓai ya iya bariki da ban sani ba sai da ya auri Gimbiya na san ko lauya ya karanta sai haka in dai wajem lauya zence ne.

    “Ina yini? Ya amarci?

    Na faɗa ina ƙoƙarin sakin fuska kamar yana gabana.

    “Lafiya lau. Ya yarana ya gidan? Sai kuma kika manta da ni Abar ƙaunata?

    Kamar na yi masa ashar sai kuma na fasa.
    Cije baki na yi kafin na ce” Ah na bar ka ne ka ci amarcinka. Ina Amarya?
    “Ga ta nan tana jin ki.”
    Ya faɗa yana yar dariya.
    “Ayya ka gaisheta. Ina fatan ba ta yi baƙunta ba?
    “Ta yi fa, ta na ma kan yi, ga ta nan ma kwance sai rakin tsiya.”

    Kasa magana na yi saboda na ma rasa me zan ce. Hakan bai sa Yallabai ya yi shuru ba ina jin sa yana dariya yana mata magana a ƙasa ƙasa wai ga ni ina son magana da ita ni yaushe muka yi haka da shi? Ina hamgame da baki ban rufe ba na ji muryanta tana yi mini Sallama.

    “Umma ina yini”

    Shike nan daga Anty na koma Umma, Yallaɓai ya gama da ni.
    Sai na danne na saki fuska kamar tana ganina na amsa mata gaisuwar ina tambayanta baƙunta ta yi mirmishi.
    “Ki saki jikin ki kin ji ko? Ai gidan ki ne”
    “Yaushe su Jidda za su zo mini?
    Ina riƙe baki na ce” Ba yanzu ba. Sau nan gaba Jidda ma ranar lahadi za ta koma makaranta in sha Allahu.”
    Sai ta ce Allah ya nuna mana, sai ya karɓi wayar yana ce mini gwara dai na yi mata faɗa taki sakin jiki.

    “Ka yi haƙuri za ta saki na ɗan lokaci ne. Kuma ka san haka ke faruwa da kowacce amarya.”

    “Wallahi na tuna kema haka kika yi ta mini. Da na matso kusa dake ki fara mini kuka kina faɗin don Allah kar ka taɓa ni ba na so.”

    Ya ƙarishe faɗa yana kwaikwayin muryata wai, baƙinciki da takaici suka yi mini rufdugu kamar Yallaɓai ya ruɗe, ni na ma kasa mgana ina shirin ma na kashe wayata ne na ji yana faɗin” To itama haka take yi mini, in na kalleta ke kawai na ke tunawa a wancan zamanin Sadiya ta.”

    “Uhm”

    To me zan ce? Ko na ce wani abu ba zai gane ba giyar amarci ne ke ɗiban sa.

    “Maganar komawar Jidda makaranta ranar lahadi ne.”

    Na faɗa da ƙoƙarin na kaudar da maganarsa.

    “E wallahi na sha’afa sai da na ga kiranta jiya. Zan tura mata kudi ta yi siyayya kafin na shigo gidan.’

    Wato ba ma yanzu ba? Duniya sabuwa a wajen Yallaɓai.

    Ban ce masa yaushe zai zo ba? Na ce Allah ya kaimu. Yumna ya tambaya na ce masa tana falo na ɗauka ya kirani ne mu gaisa amma sai na ji yana faɗa mini kwana daya daga gidan Mimisco aka kawo musu abinci jiya ko da yau ma duk takeway ya yi musu.

    “Gaskiya. Ga Gimbiya a kusa ai ita ya kamata ta baku abinci har sai Rabi’atu ta yi bakwai.”

    Sai ya yi shuru maimakon ya amsa maganata sai kawai ya ce” Ina neman alfarman daga gobe ki dan riƙa dafawa damu, sabon direba zai riƙa zuwa yana ɗauka.”
    Na buɗe baki kamar yana ganina kafin na ce” Har sai an zo nan? Miye amfanin matarka dake gidan?

    “Ai na san da ita na kira ki Sadiya.”

    “To me ya sa sai ni? Kana da tabbacin zan amsa alfarman taka ne?

    Sai ya yi mirmishi kafin ya ce” Nima ban san me ya sa a komai nawa in ya taso ke nake son kira ba. In wata bujata ce wajen ki nake son fara zuwa. Ina da yaƙinin ko ba ki yi mini abin da na ke so ba in na faɗa miki kina bani mafita.”

    Kalamansa suka kashe mini jiki da na kasa mgana. > Janaftybaby: “Ita ta ce ba za ta yi ba Sadiya ba zan kuma taɓa matsa mata ba. Ke ce na ke da yaƙinin kina yi ma zaman auren mu kara na kuma san wannan karan ma ba za ki ƙi yi mini karan da kika saba ba.”

    “Uhm”

    Na faɗa a ƙasan makoshi.

    “Ba zan takura ba, in kina ganin ba zai yuyu ba sai mu bar shi na cigaba da oder. Amma kamar bai kyautu ina da matan aure har biyu na riƙa siyan abinci a waje ba, sannan ita kanta ya za ta fassara lamarin?

    Sai na ga kuma gaskiya ya faɗa duk da wata zuciyar na ce mini na ce ya cigaba da siya amma na kasa. Sai da na tuna da kalaman Alhajinmu da ya ce na yi ma abokan zamama alheri da ƙarfina da jikina da aljihuna. Ruwan su ne su ma yar da alheri da alheri ko su ma yar da alheri da sharri. Ni dai in dai na yi don Allah ladana na wajem Ubangiji kuma ya gani na sauke haƙƙi da nauyin zaman tare. Sai kawai na ce masa to shike nan da yaushe da yaushe za a riƙa zuwa karɓan abincin?

    Cikin murna ya ce” Ko sai ɗaya a rana is ok.”

    “Shike nan Allah ya ba ni iko.”

    “Na gode Abar ƙaunata. Allah ya kare mini ke.”
    Na amsa da Amin a ƙasan maƙoshi, ban wani ja mgana ba muka yi sallama bayan ya ce mini za a kawo cefane a raina na ce tunda hidimar amarya ya tashi ba. A washegari aka kawo cefane har da su Nama da kaji, Sadi ne ya kawo sabon Direba Salisu Yallaɓai ya ɗauke shi ya koma direban kamfani. Sai Salisun ya kawo Sadin a matsayin madadin shi anan gida tun kafin ma bikin ga shi shima har an saba ya fara zama ɗan gida ya kai yara makaranta ya dawo da su sannan ya yi aike aike da kawo cefane.

    Ban faɗa ma kowa ba, ni na ke yi abincin Sadi na kai ma Yallaɓai da Amarya. Kuma a satin na je gidajen su Hauwa na kai musu sakon su amma ban amince na yi musu ma zencen ba, dalilina shi ne ba komai ne na aure ya ke buƙatar fallasa ba na bar ma cikina. Kuɗi Yallaɓai ya tura ma Jidda ita da direba suka tafi kasuwa ta yi siyayya. Kayan abinci da man daga gida take ɗiba kayan kwalama ne su bickit sai mayuka da su pad da kayan tea ta je ta siyo. Anan gida ta yi miyanta ta yi cincin da Donut za ta tafi da shi, tun ina sa ran zuwan Yallaɓai har na cire ma raina, ganin ma daga wajen Amarya sai ya fara dawowa wajena kafin ya koma wajen Gimbiya shi ya saa na kira Surayya Dee ta aiko mini da haɗin kazar sababi na uwargida. +234 803
    Sai kuma a gida ina ta cin ganye da kayan marmari, ba domin wai na gyara ma Yallaɓai ba aa sai domin nima macece ina bukatar na gyara kaina. Ko da na ba ma arba’in baya ban tsufa ba akwai ruwa a jikina har yanzu kuma ko gobe ai ruwa na mganin dauɗa nima asabuwar Yallabai ya aure ni muka gurji juna har ta kawo mu ga yau, saboda haka in ma ya manta mafari zai dawo mafarin na shi dolen shi dai.

    Ba Yallaɓai ya zo gidana ba sai ranar lahadi da safe ranar da ya cika sati ɗaya a ɗakin Amarya. Kun gan shi da wata bakar jallabiya ya yi kiɓa ya yi haske ga tumbi ya ƙara tasawa. Shima dalilin zuwan saboda tafiyar Jidda ne. Adnan ne zai ma yar da ita. Ita ta kira shi ta ce za ta tafi ba su yi sallama sai ga shi da jallabiya iriin ma fitowar na dole ne.
    Baby da Jidda suna ta murna ganinsa suka dafe shi suna ihun ga Abba ni ko kallon su ban yi ba. Yallaɓai ya ba ni mamaki muna gari ɗaya? A wayar ma sai ya ga dama yake kira ko kuma in ta shi buƙatar ya taso shi zai kira yana rage murya yana daidaiciyar mgana.

    Jidda na tafiya kunya ce ta hana shi shima ya wuce sai ya ɗan shigo ciki. Ni ko abun kari ban yi masa ta yi ba sai ya ce wai na ware shi kamar ba ɗan gida ba.

    “Na ɗauka ka ci kai da Amarya.”

    “Ba mu tashi ba wayar Jidda ce ta tashe ni, na baro ta can tana barci.’

    Ko kunya Yallaɓai ke faɗa mini haka na tusa buredi a bakina na yi masa wani kallon renin wayau bai ma gani ba yana can yana mgana da Baby, Yumna kuma ta ishe mu da kiran sunan shi Abba sai ya amsa sai ta yi shuru sai kuma ta sake kiran shi. Tare da mu ya zauna ya karya yana hira da ya’yan shi, ni ina gamawa na shig ciki sai da zai wuce ya biyo ni yana yi mini sallama nan ne na ke nuna masa sauran kayan da dangin Rabi’atu suka kawo mini sannan na faɗa masa na yi kyauta da wasu. > Janaftybaby: “Kar ki damu kayan ki ne fa. Ke suka kawo mawa kina da damar yin abin da kika ga dama da shi, yau ko da ma nawa ne tuni na yarje miki ki aiwatar da gabaci in dai ba na nan.”

    Ban bari daɗin bakin shi ya yi tasiri a kaina ba na yi masa sallama. Har yana cewa ko rakiya babu? Na shige tiolet ina faɗin fitsari ya matse ni ya fita yana dariya shi kam shi ya san na zille ne kawai sai da na ji tashin motarsa sannan na fito ina ƙunƙuni ni kaɗai.
    A ranar na kira Alhajinmu na gaishe shi shi ne yake faɗa mini jiya Yallabai ya kawo masa Amarya ta gaishe shi Amarya ta kawo masa kyautar turare. Sai na saki baki ina jin Alhajinmu kawai ina mamakin Yallaɓai bayan daɗin baki yanzu har makirci duk ya iya.
    Kafin mu yi sallama Alhajinmu Jadadda mini yake yi na zauna lafiya da abokan zamana don Allah , na ce to ni kam ai ban isa na ƙara komawa gida na ce Yallaɓai ya yi mini wani abu ba sai Alhajinmu ya ce sharri na yi masa.

    Can da yamma sai ga kiran Yallaɓai da cewa anjuma zai kawo su Gimbiya gidana zai yi zama da mu.
    “Har sai ka tarkato su gidana ? Ka yi musu duk maganar da za ka yi acan ni in ka zo sai ka faɗa mini ba ni da matsala.”
    Na faɗa masa haka har a cikin zuciyata
    Kawai sai ya fara mini faɗa wai ni zan faɗa masa ga yadda zai yi?

    “A’a yi hakuri daga shawara.”

    “Riƙe shawaranki sai na ce ina ɓukata. Malama za mu zo anjuma nan sai ki hana ɗin.”

    Daga haka ya katse wayarsa sai na bi wayar da kallo ina riƙe da baki da man tun lokacin da ya kira wayar na ji muryansa a sama ina kyautata zaton shi da Gimbiyarsa ne aka tafka wata tsyar shi ne zai sauka akaina ƙaramin tsaki na ja ina tura baki kamar yana ganina

    Ni da Baby mu ka share gida muka goge. Tare kuma muka yi girki cous-cous da kayan lambu mai hanta sai na yi mana kunin Aya da zoɓo muna gamawa na bar mata gyaran kitchen na ce kuma ta jera komaI a saman dining ni kuma na shiga wanka. Gayuna na ci da man ni duk wanda ya sanni ya sani da ban yarda da zama haka ban gyara kaina da jikina ba. Wata doguwar rigar amfata na saka sabuwa ban ma taɓa sata ba, ɗinkin A shafe ne ta yi min ɗas a jiki na kashe ɗaurina na maryam babangida. Da man na yi kitso Maman Nana ranar asabar ta zo ta yi mana ni da yara har da Jidda tun da ana gobe za ta koma ne.

    Na idar da sallar isha’i Saude ta kirani a waya na tsaya muna gaisawa. Har suka iso ma ban sani ba sai da Yallaɓai ya shigo ciki da kansa. Ji kawai na yi an ruƙumƙumeni ta baya tunda na ji kansa a saman wuyana na san shi ne in Yumna ce kafafuwana take rumguma
    Sama sama na yi sallama da Saude ina ture Yallaɓai.

    “Ke ba ki iya zuwa tarban miji ba ko?

    Hararan shi na yi kafin na ce” Mijin wa?

    “Mijin Sadiya mana.”

    Ina dariya na ce” Ai ni na bar ma su Rabi’atu kai.”
    “Wallahi ba ki isa ba”
    Ya faɗa kai tsaye har yana wani shan mur sai ya ba ni dariya.
    “Ahto ban yarda ban kuma lumta ba. In ke za ki iya haƙuri da ni, ni ba zan iya haƙuri da ke ba My Sady”
    Ya faɗa yana ƙara rumgumomi wannan karan ban kwabe niyarsa ba nima sai na rumgumeshi ƙamƙameni ya yi yana shinshinan ƙamshina.

    “I miss you”

    “Na yi kewar dumin jikin ki.’

    Ya sake faɗa yana shafa bayana zuwa ƙuguna.

    “Na yi kewar ban ruwa a nan.”

    Hannun shi na ture ina faɗin” Wani kewa? Kai da ka samu sabon lambu ba irin nawa tsohon da ya ji tsatsa ba.”
    Kallona ya yi cikin ido kafin ya ce” Haka nan na ke son shi, ai tun yana sabon shi ni na riƙa gurzan shi har ya yi tsatsan kin ga ko dole na so shi a haka”
    Na buɗe baki zan yi magana ya matse ni ya haɗe bakin mu sai da ya tsotse jan bakina tas sannan ya sake ni ni da shi gabaɗayanmu muna sauke numfashi.

    “I miss everthing about you Sadiya ta. Har da wannan jan bakin.”

    Ya faɗa yana shafa bakin sa, baki na tura masa ina ƙunkƙuni

    “In kika sake tura mini baki wallahi zan turmushe ki sai na yi ɓarnan ruwa.”

    Ai ina jin haka da gudu na fice ina jin sa yana ƙayƙyatan dariya. > Janaftybaby: Sai da na daidaita kaina har ɗaurina ya kwance sai da na sake yin wani sannan na fita can falo, na iske Rabi’atu da su Baby, ta saka dogon hijabin ta har kasa sannan ba ta yi kwalliya ba amma da ka ganta fuskar nan ta yi fresh alamun dai ana shan amarci.
    Gimbiya ko na gefe ta kame a kan kujera mai zaman mutum ɗaya an ci gayu da mayafi a saman kafaɗa, Ammar na hannunta Amwar na gefenta Khalipa ne kawai tare da su Baby.

    Rabi’atu na ganina ta fara gaisheni cikin girmamawa na amsa ina tambayanta baƙunta ta sunkunyar da kai. Gimbiya ko ni da gidana ni ce na fara gaisheta ta amsa kamar ba ta so. Ban damu ba Yallaɓai na fitowa na ce na haɗa mana dinner mu fara da cin abinci.
    A gaban su ya ɗan rumgumo gefen kafaɗata ya sumbaceni kafin ya ce” Allah ya yi ma matata Sadiya albarlka”
    Na amsa da Amin Rabi’atu ta yi gaba ita da su Yumna Gimbiya ce a wajen amma ba ta amsa ba ina ganin ma tana hararan mu ko shi ne ya ja mini ban sani ba.

    Dukkanmu har da yaran muka zauma a dining muka ci abincin. Gimbiya kunin aya kawai ta sha ta tashi ta koma saman kujeran falon ta ce ita dai ta ƙoshi. Ni da Yallaɓai ne a wajen ke ta hira sai ni in na sako Rabi’a ciki ta ɗan yi mirmishi kuma ta ci abincin sosai ta sha kunin aya. Da ma ina cewa ta ci mana ta daina baƙunta nan ma ai gida ne.

    “Za ta ci fa, a can gida in kika aiko mana da abinci ta riƙa santin cewa gaskiya Umma ta iya girki “

    Ya faɗa yana kwaikwayonta ni da shi muna ta dariya ita ko ta sunne kai, ina son ta tana da kunya sosai. Anan ne na ke masa taɗin ashe ya kai ta wajen Alhaji.

    “To ni da babana kuma? Ko sai na tambayi izini.”

    Ina dariya na ce ba ruwana, mun tattauna mganar makaranta ya ce ai itama Rabi’atu cikin satin za ta shiga cikin makaranra ta yi risgtration suma sun koma sai ina zolayansa na ce shi zai kai ta?

    “A’a sati ɗaya ban je aiki ba gobe zan koma office. Amma ina tunanin na haɗa ta da Musbabu ko Adnan”

    Ni ko na ce sai dai Adnan din Musbahu ma ayyuka sun yi masa yawa ita ko tana gefe ta ce ai za ta iya fa ita kaɗai, sai ya ce bari dai ya gani in ba buJata sai ya haɗata da direba. Baby ta yi zencen nata makarantan ya ce gobe zai shiga makaranta ta zama cikin shiri za ta fara SS1.
    Ni ko na ce ga Yumna a saka mini ita a Ajin yara.

    “Mugunta ko? Wannan jarriyar ne zan kai makaranta to ni ba da ni za a yi haka ba “

    Ina dariya wai Yumna ce jaririya ina roƙon Yallabai ya kai ta bakinta ya buɗe da karatu ya ce sai ta kai shekara huɗu zai saka ta a makaranta wai Baby ta riƙa koya mata a gida tun da na ga ya dage na yi shuru na san ba zai amince ba.
    Muna gama cin abincin na saka Baby ta gyara wajen sannan Yallaɓai ya ce duty ɗin ta ta tattara yara su koma can falon su a zauna lafiya ban da hayaniya har Ammar sai ta karɓe shi hannun Gimbiya ta tafi da shi can falon su, saboda ya ce kar a yi hayaniya shi ya sa suka yi shuru kamar ba su a gidan.

    Farko Yallaɓai ya buɗe taro da addu’a sannan ya yi nasihohin shi, da tunasarwan cewa dukkanmu ya aure mu ne domin yana son mu ne, Gimbiya da ya aurota ni ban gaza ba haka itama Rabi’atun ya faɗa mata Gimbiya ba ta gaza ba. Duka matsayin mu ɗaya mu yi haƙuri mu zauna lafiya mu rike juna da Amana. Ya ce ni ce Babba ya san ina ƙokari to don Allah na ƙara Rabi’atu ƙarama ce a cikin mu, mu zauna da ita bisa gaskiya da Amana.
    Ya ba mu damar magana ni dai na ce in sha Allahu ba matsala daga bangarena Gimbiyar ma ta ce haka itama Rabi’antun ta ce haka sannan ya yi mata gargaɗin ko ba aure ba a shekaru mun girme mata ta yi mana biyayya in ya ji saɓanin haka zai saɓa mata ta ce hakan ba zai faru ba.

    “To na ji daɗin haka. Maganar rabon kwana mu bar shi 2dys ɗin ne ko ya ya?

    Sai na ce a bar shi a haka ɗin ai ya yi.
    Amma sai Gimbiya ta ce ba ta yarda ba sai dai a ma yar da shi kwana ɗaya.

    “Miye wani kwana ɗaya,? Da ba biyun kuke yi ke da Sadiya ba?

    “Da ka ce yanzu ko mun ƙaru gwara ɗayan saboda kar a cuci kowa.” > Janaftybaby: Gimbiya ta faɗa cikin gatsali, zai fara faɗa na dakatar da shi da cewa” Ba komai a yi kwana ɗayan ai duk ɗaya ne.”
    Bai haƙura ba yana so ya dai yi magana na ce”Ka yi haƙuri a bar shi a haka don Allah”
    Jin haka yasa sai ya yi shuru. Zaman dai haka ya shi ba wani kwarjini, shi da ya kawo su shi ya ɗauke su ya ma yar da su yafi awa da tafiya sannan ya dawo ni kuma ban tuhume shi a in da ya tsaya ba da kan shi yake faɗa mini Rabi’atu ke kuka wai tsoro ba za ta iya kwana ita kaɗai ba, shine ya tsaya yana lallashinta da nuna mata ga Gimbiya a gidan kar ta ji tsoro.

    “Allah sarki. E kafin ta saba ko a gida ta ɗauko yarinyar da za ta ɗan rika taya ta kwana in baka gidan.”

    “E mun yi wannan mganar to can gidan baffan nata ba yara fa, ni da man Baby na ce ta riƙa zuwa tana taya ta kwana kafin ta saba.”

    Na ma kasa mgana ni shike nan ya’yana Yallaɓai yana raba su tsakanin matansa ba tare da izinina ba kala ban ce masa ba.
    Mu ka yi shirin kwanciya amma bai bar mu mun kwanta ba sai da ya yi ɓarnan ruwa har yana yi mini sambatun ya yi kewar gidan ruwan shi a raina na ce ka ji da shi dai da asuba ma ya koma ruwa. Da safe kuma tun safe ya yi shiri ya tafi office da yamma da ya dawo ya biyo ta nan gidan ya ɗauki wasu kaya sannan ya wuce can gidan yana ƙara jadadda mini na fara shirin tariya, a nan ne ma ya ke faɗa mini gidan da Gimbiya ta tashi Kawu ya bashi shawaran ya saka yan haya, ni dai na ce kar ya saka yan haya a gidana don Allah.

    “To a bar miki za ki rika zuwa partime kenan?

    Na ce masa e, saboda ina son gidan ya fita yana dariya wai duk abuna sai na tashi na koma sabon gida na samu cigaba ni ina noƙewa bai san yadda na ke son gidan nan ba ne ne har raina ni kaɗai ce fa anan can ko da gayyar kishiyoyi. Ganin ya matsa ya sa dole na fara shiri Baby dai ta koma makaranta an zama manya yanzu, ni dai labulayan na samu na siya sai cafet na falo biyu sauran kuma na tattara aka kai wanki na ce na yi amfani da su. Yallaɓai na yi ma maganar falo guda ɗaya ba kujeru ban saka rai ba ya ce na yi magana nawa za a yi saffa saffa gado da kujeru da gudu na je na tambayo, can ɗan kusa da gidanmu na Dorayi ne kafinta ya ce 800k na zo na faɗa masa ya ce a yi mini ganin na samu sauƙi na ce a yi mini ƙaramin gado da wardrope na ɗayan bedroom ɗin sauran kuma kaya na kuma da su zan koma, na so tariyan ya zama bayan biki ko da wata ɗaya ne amma bai samu ba sai da ya kai wajen bayan biki da wajen wata biyu sannan saboda an ƙarisa aiki a shashena. Allah ya taimake ni bangarena na haɗe da bangaeen Yallabai ne. Na Rabi’atu ne da Gimbiya suke a haɗe.

    Ranar wata asabar ce na tare a sabon gida. Da man tun satin mota ta zo ta kwashe kayana zuwa can gidan y’an uwana suka taya ni muka gyara komai. Ban yi gayya ba daga ni sai su Munnira sai y’an gidanmu sai Marwa da ta zo, sai dangin Yallaɓai, mun dai yi girki saboda ma su zuwa. Bangarena babban bangarene kamar gidana sai dai nan na samu ƙaruwan falo da ɗakuna amma duk samfur ɗaya ne. Dining na so na yi sabo rashin kuɗi ya sa na dawo da tsoho. Amma zencen gaskiya gidan ya yi kyau Yallaɓai ya kashe kuɗi sosai masha Allah. Gimbiya tun da ta leko sau ɗaya ban ƙara ganin ta ba Rabi’atu kuma tana zuwa makaranta amma in dai ta dawo ta nan tare da mu da ita duk muka gyara ɗakuna na.

    Gaskiyan magana ba ruwanta ba ta da hayaniya ga kunya. Hatta su Munnira sai da suka yabe ta ga girmama na gaba da ita. Su Suwaiba da su Jamila duk sun zo mini amma ban ga su Anty Bahijja ba Mimisco ta zo ta ga waje ta saka albarka. Maƙotana na can anguwan da na shiga na yi musu sallama suma sun zo mini ganin gida sun saka albarka. Ga wargajejen fili, ga motata, ga na Gimbiya ga na Yallaɓai amma ko rabi ba a cika ba sannan ga maigadi, na yi hoton shashena na tura group ɗin gidanmu su Ya Hamza suka ga gaggani, suka saka albarka Amina na ta santi ta ce wallahi shashema duk ya fi kyau haka su Munnira suka ce, har fentina ya fi kyau sannan Yallaɓai ya siya mana manyan palasma guda biyu ni ɗaya Gimbiya ɗaya. > Janaftybaby: Sai na yi amfani da na tsohon na falona a falon yara na tsohon faalon Yallaɓai kuma na saka shi a falona na yanzun sabon kuma na saka shi a sabon falon Yallaɓai.

    Sai na raba abun falon farko na Yallaɓai ne na biyu kuma nawa na ukun na yara. Bedroon na farko na nawa ni da Yallaɓai na biyu kuma na yara sauran kuma sai na bar shi a na baki. Sannan kitchen ɗina na nan wargajaje har fridge dina da frizer anan na saka su disspanser ne kawai na saka a falon Yallaɓai.
    A satin kaf ban samu fita ba ana ta leƙo mini Allah ya sanya alheri, Baby da Yumna kamar an saka su a aljannah. Sun haɗe gida ɗaya da su Khalipa in sun dawo makaranta haka za su yi ta wasa a haraba.
    Rabi’atu kuma in dai tana gidan ba ta je makaranta ba tana tare da yaran
    Ni da ita zaman mu lafiya. Amma Gimbiya ta ware kanta gefe, ni da man ba ta yi da ni ballatana Rabi’atu yar baya baya. Ban san tsakanin ta da Yallaɓai ba tun da ba faɗa mini abin da ke faruwa a tsakaninsa yake yi ba.

    Ba ni na fara fita ba sai da aka shiga satin bikin Datti sannan muka fara zaryan zuwa Ɗorayi.

    Note
    error: Content is protected !!