Turken Gida – Chapter Fifty-two
by JanaftyFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Gkzmhd0zmnFChYrdONLFYp
Bedroom ɗina na koma na yi zama na ban san lokacin da suka tafi ba, har ga Allah ba ina murna da ƙarin auren Yallaɓai ba ne saboda kishiya ai sunan ta kishiya nima a zaman matar mijina take. Na so Gimbiya ta ji maganata ta kwantar da hankalinta saboda ta tsira da sauran mutumcinta amma taƙi jin maganata tana biye ma su Anty Bahijja. Wanda na tabbata in aka juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe, dole akwai bangaren da za ta nuna mata Yallaɓai ne jininta na kusa ba ita ba.
Abin da nake yi ita a ganinta ina bin bayan auran Yallaɓai ne saboda ita, abin da ba ta sani ba da na bi baya da ban bi baya ba ban ga dalilin da zai saka Yallaɓai ya fasa wannan auran ba, yau ko Nene ce ta hana shi na tabbata zai yini yana yi mata karatun da za ta gane har ta amince domin bai ɗauko maganar auran nan don ya fasa ba. Shi ya sa gwara ta kwantar da hankalinta domin ba abin da za a fasa.
Rasa wanda zan kira na tseguminta masa zuwan Gimbiya da Anty Bahijja sai Munnira ina faɗa mata ta yi dariya da shewa kafin ta ce.
“Sai yanzu suka san ana haɗa kai? Wato sai yanzu da suke neman mafitar su.”
“Wallahi, ni kaina zuwan su ya ba ni mamaki. Har Anty Bahijja na faɗin wai mu haɗa kai ko ba mu rusa auran ba mu hana su zaman lafiya har sai ya gaji ya sake ta”
Na faɗa, ina riƙe baki domin sai a lokacin na ke jin ma ƙarin mamakin zuwan su da magangansu.
“Lalle. Ni ban yi mamaki da man na san za a zo wajen. To ke me kika faɗa musu?
“Na ce ni ba zan haɗa kai domin a yi tashin hankali da ni ba itama ina na faɗa mata gaskiyan ta bar ma komai ta kwantar da hankalinta. Amma ba ta ji ba ita a ganinta ina goyon bayan Yallaɓai saboda ita ne, ni kuma wallahi ba haka ba ne Munnira. Kin sanni ba ni da wanman muguntar, ina tausaya mata ne domin a irin rawan kafan da Yallaɓai ya ke yi a kan auran nan ni ko ita wallahi ba mu da darajan da za mu iya dakatar da shi, shi ya sa na koma gefe na zama yar kallo na shafa ma kaina lafiya.”
“Haba na sani wallahi. Kin huta da man a irin wannan lokacin in baku sauke
a kai ba sai a samu matsala. Kuma su Anty Bahijja ne za su ɗora ta akan keken ɓera su kaita su baro ta.”
Na amsa da wallahi, domin in ta kwaɓe su kan su ba za su iya ba. Wai maimakon su ce ta yi haƙuri ta ma yar da lamarin ta ga Allah, amma suna zugata ta yi tashin hankali da miji. Har muka gama waya da Munnira ita kanta ta ce da Gimbiya ta kwantar da hankalinta da zai fi mata alherin akan wannan haukan kishin da ta ke yi, nima abin da na hango mata kenan. Bayan Munnira ban faɗa ma kowa zuwan su Gimbiya ko Hauwa ba mu yi taɗin da ita ba, a satin na je Ɗorayi gai da su Alhajinmu ina faɗa masa ƙarin auran Yallaɓai, sai ga magana tiryan tiryan a bakin Alhaji.
“Har nan falona in da kike zaune nan megidanki ya zauna ya sanar da ni zai ƙara aure, ya kuma dawo ya roƙeni na shirya aje nema masa aure da ni sai kuma aka yi rashin sa’a ranar zan je Yashe shi ya sa ban samu zuwa ba amma na yi masa alƙawarin zuwa masa ɗaurin aure.”
“Maidugurin Alhajinmu.?
Na faɗa ina zare ido saboda mamaki.
Sai kawai Alhajinmu ya yi dariyar su na manya kafin ya ce” In sha Allahu in dai muna raye zan je. Ai ya girmama ni matuƙa nima zan ma yar masa da girmamawan sa.”
Uhm kawai na ce na ma kasa magana saboda mamakin Alhajinmu wai zai je har Maiduguri ɗaurin auran Yallaɓai, ni bai ma taɓa nuna mini ya zo ba ashe ya zagayo sai da na koma gida da Yallaɓai ya zo yi mana sallama a daran nake masa mganar aahe ya wanke kafafunsa ya je ya faɗa ma Alhajinmu maganar aurensa.
“Ya ba zan faɗa masa ba! Me kike nufi? Alhaji ai uba ne dole na je na same shi na faɗa masa komai dangane da aurena. Bai ma samu zuwa maganar auren ba amma ya yi mini alƙawarin zuwa ɗaurin aure har can maiduguri “
Kallon Yallaɓai kawai na ke yi, a fatar baki na ce Allah ya kaimu da rai da lafiya. > Janaftybaby: Tun da Alhaji ya yi niyya wa ya isa ya hana shi, ni ma kafin na fito sai da ya sake yi mini nasiha sosai akan haƙuri na zauna kuma da kowa tsakani ga Allah, ina jin daɗin manganganun Alhajinmu shi dai har na zama mai ɗaga ma mijina hankali. Na zama mace mai samar masa da zaman lafiya a cikin gidan shi, haƙurin da na yi a farko yanzu na ninka shi, nan gaba kaɗan zan ga riban haƙurina ko ya ce zan ƙara gani domin ribar haƙuri na gan shi tun da har gobe mijina ya yaba mini da hallaya masu kyau.
Tun da aka sanya lokaci Yallaɓai bai zauna ba shiri kawai yake yi kamar zai yi auran farko. Ko da yake budurwa zai ɗauka dole ya yi rawan jiki, ranar sati na zuwa Yallaɓai ya ce na shirya yara za su je su gaida Gimbiya. Shi ya sa ya ƙi ma yar da su Khalipa gida, ni na ma manta da zencen amma shi yana sane bai manta ba faɗa mini yake yi ai ta riga ta gama shirin tarɓansu tun da ya faɗa mata za su zo, Jidda na saka ta shirya yaran suma na ce su shirya sun ci gayun su ni dai ba ni da komai Hijabi da mayafi na ba ma Jidda na ce ta kai ma Antyn na su. Yallaɓai kamar bakin shi zai yage saboda farinciki shima ya ci gayu yana rawan jiki har sai da na yi masa magana.
“Yallaɓai wai ba can za ka bar yaran ka wuce office ba?
“E ina tunanin haka akwai baƙin da zan gani.”
Sai na yi shuru domin na ga yana rawan kafa ne har ya wuce misali, har yana yi mini godiyan saƙon da na ba da akaikace na ce bakomai yiwa kai ne.
Shi ya ɗauke su a motar shi, tun wajem sha ɗaya na safe, ina jira na ga Yallaɓai ya dawo mini da yara amma shru har la’asar shi kuma na kira wayarsa bai ɗauka ba sai na kira Jidda ina mata faɗan zaman me suke yi ne har yanzu ba su dawo ba.
“Umma Abba ya ce mu jira shi zai dawo ya ɗauke mu.”
“Kenan shi kuke jira?
Na faɗa ina mai kama baki, kafin ta yi magana sai na ji an yi mini sallama cikin sanyin murya ina jin murya na gane na Rabi’atu ne
Gaishe ni ta yi na amsa nima cikin sakewa kafin na ce” Yau an kawo miki gidan gabaɗaya hayaniya ya dame ki ko?
Tana mirmishi ta ce” A’a ni da man su kwana Anty”
Sai nima na yi dariya kafin na ce”Haba dai. Ba yanzu ba ki jira saura ƙiris wata rana ma sai kin kore su saboda gajiya.”
“Ni ba zan kore su ba. “
Ta faɗa tana yar dariya, godiya ta yi mini na saƙo na ce mata haba yi wa kai ne. Na ce su kira Yallaɓai in ba zai samu komawa ya ɗauke su ba Jidda ta yi jagoranci su samu a daidaita su dawo gida yamma ta yi.
“Ya ce zai dawo ya ɗauke su. Na san yana hanya.”
Ai ni sai na kasa magana tun da ga abin da ya ce. Ni dai ban ga yara ba sai bayan sallar isha’i, Yallaɓai bai isa can ba sai bayan mangariba can suka ci abinci sannan ya tarkato yara suka taho. Baby ke faɗa mini a mota suka jima Abban su na cikin falo da Antyn na su. Ni fa tsoron rawan jikin Yallaɓai na ke yi a kan yarinyar nan har ta haukata shi, sun dawo da kayan zaki kaya guda kamar za a buɗe shago su bickit ne da su katan ɗin boo na yara. Yallaɓai yana faɗa mini ya ce ta bar shi amma ta fara fushin yana nuna mata su Jidda ba ya’yanta ba ne, ni dai ban yi magana ba saboda ba ni da ta cewa
Godiya ma shi ya yi mini na ci sai na kirata na yi mata godiya kamar wani laifi ne in ban yi mata ba haka nan na ce Jidda ta kira ta a wayarta tun da sun karɓi lambar wayar juna. Shi ne na samu na yi mata godiya tana ta jin kunya da man iyayin Yallaɓai ne amma ni na san har tsaraban ma duk shi ya siya ba wai ita ba, in ita ta siya ma da kuɗin shi ne.
Washegari Lahadi Gimbiya ta aiko aka tafi da su Khalipa. Da man ko ba ta aiko ba ina shirin na roƙi Yallaɓai ya ma yar da su to sai ga shi bayan fitan shi, ta aiko Salisu ya zo ya tafi da su. Da ya dawo a daran da man yana gida ne, ya ga bai gan su ba ya tambaya na ce sun koma gida.
Sai ya fara faɗan wai ba na jin maganarsa me ya sa zan ma yar da su ba tare da izinin shi ba.
“Ah ni fa ba ni na ma yar da su ba kana fita mamansu ta aiko Salisu ya tafi da su.” > Janaftybaby: Sai ya yi shuru bai yi magana ba amma ya yi ƙyafci alamun ran shi ya ɓaci ni ko a raina na ce can ku ƙarata ba ruwana. Sai da muka zauna ne Baby ke ba ni labarin da suka je gidan su Antyn ta su haka ake ta zuwa ganin su, a raina na ce dole a zo a gan ku Jidda ba ta magana ita da man Baby ce da man yar surutu amma faɗa mini take yi Antynsu na da kirki gidan ta za ta koma na ce Allah ya ba da sa’a.
Jidda ce mini kawai ta yi She is young Umma, ko ba ta faɗa ba na san ƙaramar yarinya ce Yallaɓai zai aura. Kuma yadda yake rawan kafa wannan in aka yi auran sai Allah kawai kar Yallaɓai ya lalace a gindin yarinya ƙarama. Ni ban san a in da Gimbiya ta ji labarin su Khalipa sun je wajen Antyn ta su ba amma na fi tunanin a bakin Khalipa ta ji tun da yana da magana shima. Kawai bugo mini waya ta yi da man tun zuwan su gidana na ce ba na tare da su ba mu ƙara magana ba.
Ni wai Gimbiya ta buga ma warning akan me ya sa zan yanke hukunci kan ya’yanta? Me ya sa na tura su gidan wata banza ba tare da sanin ta ba.
Ni ko cikin mamaki na ce’ Umarnin megidan ne amma ba ni na tura su ba “
Sai ta fara masifa tana faɗar manganganu wai da sanina aka yi komai da ban ba da goyon baya da ba a tura mata yara gaida wata banza ba tare da sanin ta ba.
“To ki yi haƙuri.”
Haka kawai na ce mata ganin kamar ni ce take jin haushi yanzu ba mijinta da zai ƙara aure ba.
“Ahto ni dai a kiyayeni. Ya’yan dai nawa ne ba wani ya haifa mini ba, in kina son neman sunan ki aika na ki ƴa’ƴan amma ban da nawa.”
“To in sha Allahu hakan ba za ta ƙara faruwa ba’
Kawai sai ta yi mini tsaki mai girma har ina jin sa a cikin kunnuwana sannan ta kashe wayarta ta bar ni sake da baki. Ni zan fita? Ina ruwana a wannan maganar da abun zai dawo kaina? Raina ya ɓaci amma sai na danne zuciyata na ɗau girma na yi haƙuri shi ya sa ko zencen ban yi ma Yallaɓai ba. Nima bai yi mini ba. Mun shiga tsakiyar watan December, Yallaɓai na ta shirin shi na gida ina ga ma an gama gyara bangaren da Rabi’ar za ta zauna sai maganar lefe ya fara yi mini. Da cewa ya yi magana da Mimisco ta ba shi shawaran kawai ya ba ma ita Rabi’an kuɗi ta siya komai da kanta. Nima da ya faɗa mini na ce hakan ya yi, tun da Mimisco ita ce kaɗai ke supporting ɗin sa sai su Suwaiba amma su Anty Bahijja sun ja tunga shi ko ya ce uwarsa ba ta hana shi ba ba wacce ta isa ba.
A bakin Suwaiba na ke jin wasu mangaganun, sun ce ni ce ke zuga shi saboda na ga ba ni za a yi ma kishiya ba ni in suna faɗar haka har mamakinsu nake yi mijina ne fa zai ƙara aure? Ni ba mace ba ce ba zan yi kishi ba? Ba dangin Yallaɓai kaɗai na ke shan zagi ba hadda na su Giimbiya a can Rano. Sameena ta kira ni a waya tana faɗa mini mganganun da ta ji a kaina marasa daɗi.
Wai na ki yadda mu haɗa kai da Gimbiya na koma gefe ina munafutarta wai tun kafin Amaryan ta shigo na ke ta tusa kaina a wajen yar cikina. Mangaganu dai marasa daɗi, ni ko na yi mata rantsuwan duk abin da ta ji ƙarya ne na yi mata cikaken bayanin abin da ya faru da wanda ke faruwa.
“Sameena na isa na hana Yallaɓai aure? Ni ban isa ba shi ya sa na koma gefe na zama yar kalllo. Itama shawaran da na bata kenan ba ta ɗauka ba, ta biye ma su Anty Bahijja suna faɗa mata cewa ni ina jin daɗin auren da Yallaɓai zai yi sabo da ita. Sun manta nima ɗin mijina ne kuma mace ce ni, ina da kishi sai da na saka haƙuri kuma na roƙi Allah ya cire mini zafin kishi. Kuma ya cire mini shi ya sa na ke zaume lafiya su kuma shi ne ba su so, sun so ne yadda take hauka nima na biye mata duk mu zama mahaukata.”
Sameena ta ce “wannan gaskiya ne. To kuma ba a kishiya ke kika bari aka auro ta,? Duk ta manta baya? Wallahi tana ta rigima domin jiya ma mun yi waya da Hajiyar mu take faɗa mini case ɗin gida ma ake yi “
“Gida?
Na furta cikin mamaki domin ni ban ma san da maganar ba
Sai da ta yi mini bayani ashe Gimbiya ta yi tsalle ta ce Amarya ba ta isa ta fara tarewa a gidan ba kafin ita ba.
“Ikon Allah.”
Na faɗa ina jinjina kaina.
“Wallahi an ce magana har Baba Tafida ya shiga ciki. “
“To ya ake ciki yanzu? > Janaftybaby: “Ban sani ba. Amma dai an ce Ya Tafida ya ce in har ta ga ta tarewa a gidan nan to kema kin tare ne amma tun da ta saka tsiya sai ya gani ɗin.”
Ni ma kasa magana har muka yi sallama da Sameena. Kenan da gaske Gimbiya take yi? Illau ko kwana biyu da maganar mu da Sameena Yallaɓai ya shigo mini gida da rana kamar kabubuwa ranar a gidan Gimbiya ya kwana ban san kuma me ya faru ba kawai ya ce nima na shirya za mu tare a sabon gida a ƙarshen wata bai ma ba ni damar magana ba ya fita ya shiga mota ya ta fi. Hankalina ya tashi saboda ban shirya komai ba ina ni ina tariya ni da Yallaɓai ya yi ma manyan falo uku da bedroom huɗu na su Gimbiya ne falo Biyu bedroom biyu. Ina na ga kayan da zan yi wannan tariya ai ba tariyan sauri ba ne sai na natsa.
Na rasa yadda zan yi, a yadda Yallaɓai ya zuciya ban isa na kawo wata magana ba. Domin a daran ma da ya dawo ina fara magana ya dakatar da ni.
“In dai maganar tariyan gida ne bana son jin komai. Ki shirya ki tare a ƙarshen wata nan.”
Tun da na ji haka na san akwai matsala na rasa wa zan tun kara, na yi niyyar na yi sabbin labulaya. Da Zannuwan gado da ɗan abin da baa rasa ba sauran abubuwan daga baya in Allah ya hore mini sai na yi. Ni kwata kwata ban shirya ba, har ya faɗa ma yara suna ta Murna su Jidda har sun fara parking ɗin kayan su har Yumna tsalle take yi za su koma sabon gida.
Ganin ya ƙi saurarena ya sa na kira Mimisco na sauke murya ina faɗa mata uzirina.
“Ke ma kin yi magana Sadiya. Amma kin sani ki yi shuru kar ki yi masa mgana a yanzu yana cikin tsini ne, ki bari nan da sati ɗaya in ya huce sai na yi masa mgana.”
Sai na ce mata to, ban tambayeta ba da kanta ta fara faɗa mini matsalan da aka samu. Gimbiya ta matsa sai ta fara tarewa magana har magabanta ta sun shiga. Hajiyar Tafida ta goyo bayan yarta har tana cewa Tafida bai yi adalci ba ta ya ya wata can za ta fara tarewa ba mu ba, in ni ba zan tare ba amma ya zama dole ita Gimbiya ta fara tarewa. Shi kuma ya ce ba za ta taren ba, ya ɗauka ta gama fahimtarsa ashe ba haka ba ya cije ya yi taurin kai sai da magana ta kai wajen Nene ita ta tursaashi ya amince amma da sharaɗin sai dai mu tare ni da Gimbiya amma ba ita kaɗai ba. Ni dai Gimbiya ce ta kusa ja mini bala’i ina zaman zamana amma tun da Mimiaco ta ce za ta saka baki na san za ta yi mini iya ƙoƙarinta illai kuma ta yi domin sai ga Yallaɓai da kan shi ya zo mini da maganar.
“Me kika ce ma Mimisco?
Sai na gyara zama ina faɗin” Na fada mata ta roƙar mini kai. Ka yi mini alfarman tariyana sai bayan bikin ka sai na tare a tsanake.”
Kallona ya yi amma bai yi magana ba ganin haka yasa na gyara zama ina sake faɗa masa hujojina, bai wai ya gamsu ba ne kawai dai ya dakatar dani da cewa” Shike nan tun da kowa abin da ya ga dama ya ke yi. Ni dai Allah na gani ina iya bakin ƙoƙarin sauke nayin da ke kaina. Wacce acikin ku take ganin ina cutar da ita Allah ai yana sama yana kallo.”
Sai na ji wani iri a cikin zuciayata da maganaganunsa.
“Ka yi haƙuri. Bari kawai sai na tare tun da haka kafi so.”
“Kar ki damu, ki yi na ki tsarin itama can ta tare a lokacin da ta so ba shike nan ba.”
Sai na kasa magana saboda a daƙune ya yi maganar kuma tun daga lokacin bai sake ɗaga maganar ba sai na fahimci Gimbiyar ta gama ɓata ma Yallaɓai rai kan mganar gidan nan ba ma ya son maganar kwata-kwata amma ni tun da na samu ya amince shike nan na kama kaina ban shiga abin da ba ruwana ba. Ya faɗa mini ya fara ba ma Rabi’a wasu kuɗi na lefe tun da farkon wata mai kama za ta koma can maiduguri sai an ɗaura aure kamar wasa na ce ya ba ni kwangilan hijabai da iners na Amarya ban ɗauka zai amince mun yi maganar yau washegari ya zo mini da maganar na yi list ɗin komai amma mu yi magana da Rabi’atun na ji size ɗin ta. Jin zan samu nawa a sama ya sa da gudu na amince, na neme ta a wayar Jidda muka yi magana ta tura mini size ɗin bra ɗin ta pant, sai na hijabi adadim yadin da take sawa duk ta tura mini da kalolin da take so. > Janaftybaby: Nan take na tura bangaren Hijabai, inears ɗin kuma na shirya da kaina Jidda ta rakani muka shiga kasuwa a rana ɗaya muka siyo komai. Na ci riba domin Yallaɓai bai yi mini ƙauron kuɗi ba isassu ya ba ni. Kuma da ya dawo ya ga kayan shi kan shi ya yaba. Sai da aka kawo hijaban sannan ya kwasa ya kai mata ta haɗa da sauran kayan, abin da aka yi daga ni sai Yallaɓai sai Rabi’atu sai ga magana na yawo a dangin Yallaɓai wai saboda neman gindin zama ni ce na haɗa ma Amarya lefe. Hauwa ta kyanƙyaa mini maganar ta ce a bakin Halima ta ji, sai ga shi na je barka gidan Jamila da ta haihu muka haɗu da Anty Bahijja ta shaguɓa mini magana da cewa na dai na murna na sani duk abin ka yi shi za a yi maka.
Ni ko na amsa da cewa haƙƙun kuma in ka shuka alheri ka ga alheri in sharri ne ma shi za ka gani. Na kuma ƙara mata da cewa a wannan zamanin ma abin ba ka yi ba shi ake yi maka ballanta ka yi.
Abin da ke ba ni mamaki a ina maganar ta fita? Sannan ma ba za a faɗi gaskiya ba sai an ƙara da sharri. Ni su Hauwa kawai na faɗa ma gaskiyan magana sauran ban damu ba su cigaba da yaɗa duk abin da suka ga dama. Sai da na yi ma Yallaɓai magana na ce ko shi ya yi maganar da wani a can Gwammaja? Sai ya ce ya faɗa ma Nene ina jin haka na ce wata ƙila ita ce ta yi zencen da ya’yanta su kuma da man suna adawa suka ƙara ma labarin gishiri da maggi tun da ba sa son zaman lafiya. Tuni na fita batun su na kama harkan gabana fafutaka na samu yan kudaɗen da zan rage siyayyan tariyan sabon gida. Na samu na labule sauran cafet da zannuwan gado cikin riban siyayyan Amarya Yallaɓai sauran kuɗin da ke hannuna duka zan haɗe su waje ɗaya mu ga abin da Allah zai yi. Shi ya sa duk na faɗa ma su Ya Hamza za mu tare a sabon gida kuma akwai falo ɗaya da bedroom biyu ban san me zan saka ba.
Ya Auwal ya ce na saka karikitai mana, ina laifi Ya Hamza kuma ya ce ni na ma samu duniya tun da har falo huɗu Yallaɓai ya yi mini. To ya cika ladan shi ya yi kayan ɗakin mana ni dai na yi dariya ban yi magana ba. Na san ba domin hidiman auren da ya ɗauko ba Yallabai zai iya yi mini abin da ma ya fi haka in dai bai fi ƙarfin shi ba. Amma dai yanzu kan bam ma saka rai ba shi ya sa nake ta fafutakana na samu na rufa ma kaina asiri. Har a raina ban saka rai da samun wasu kuɗi daga Yallaɓai ba, sai ga shi ya ba ni 200k ya ce ba yawa yara kuma 100k na yi musu siyayyan kayan fitar biki na yi ta godiya domin ban yi tsammani ba. Atamfa kawai na siya mana sai leshi sauran kuɗin na adana, da gayya da Munnira ta yi mini maganar Anko na ce a fitar mana da shi, nan take ta fitar mana da kamfala mai ja da ruwan madara mai kyau, kuma ni na tura ta a group ɗin gidan su Yallaɓai na ce ankon bikin Yallaɓai, kalilan ne suka fito suka yi magana amma su Anty Bahijja gum, na san kuma na sha zagi da man kuma ina kan sha ne.
Ai wannan ankon da na fidda kamar za su saka ni a cikin wuta. Yallaɓai ko da ya ji labari daɗi ya ji nan take ya sake tura mini 50k namu ni da yara har da Gimbiya da aka kawo na aiki Jidda ta kai mata sai ta dawo mini da shi da cewa Allah ya kyauta ita ba ta so, da ya dawo na faɗa masa tsaki kawai ya yi kawai ya ce na yi kyauta da shi. Ho ho ina shan zagi, Mimisco ta ce abin da na yi ya yi dai dai, hankalinta ya ɗauke ba ta yi tunanin haka ba, ba takura wanda ya ga dama ya yi wanda ba zai yi ba, ba takura. Su a cewarsu miye na fidda anko? Ai sai a jira a fidda a bikin Adnan na ce kowa da ranar auran shi saboda haka mu dai mun fidda wanda ya ga dama ya yi, wanda bai ga dama ba ya bar shi.
Su Suwaiba ce kawai suka siya sai su Jawahir, Halima kuma Jamila ta kirani a waya tana faɗa mini irin zagin da ta zo gidanta tana yi mini wai ba na kishi ina ta murna har ina fidda anko. Kamar zan kirata na ja mata kunne sai na fasa na ce bari na jira bikin na ga ni in ta isa ta hana abin da Allah ya tsara. Ni dai da tawagata muna gefe muna shirin mu Ankon Gimbiya kuma Rahila na ba ma ta ɗinka har Amina ta siya za ta zo mini biki. > Janaftybaby: Gimbiya ba ta gayyace ni tariya ba, ban kuma san za ta tare ba sai a bakin Hauwa na ke ji ta tare a sabon gida a ranar 31 ga watan December, na ce Allah ya sa rai ya mora, ba ta gaya mini ba ban kuma je ba shima uban gayyar bai sanar da ni ba.
Hauwa dai ta je amma Munnira ba ta je ba, ita ta zo mini da labarin ina shan zagi wajen su Anty Bahijja na ce sai su yi ta yi, ni kam ba sa gabana. Sun ce wai tarewaar ma saboda ina da mugun nufi na ce sai daga baya to tun da na nuna haka shike nan sai mu zuba su gani. Na rasa me na tare musu suka ɗora mini karan tsana, ga Ɗan uwan su da zai yi aure ba su yi masa haka ba sai ni? Miye nawa saboda nima ban yi haukar da Gimbiya ke yi ba? To in dai haka ne sai dai su yi ta tsana ta amma ni ba zan yi wannan haukar ba a baya ma ban yi ba, ballatana yanzu da girma ya kamani ba ruwana. Su je su yi faɗa da Yallaɓai shi da ya ɗauko auren ni dai ba ruwana shirin auren sa baya gabana, a gefe ɗaya ina ta shirin tariyata da zan yi bayan auren Yallaɓai amma na ce sai ya gama cin amarcinsa sannan zan koma, ba zan iya juran ganin shi yana rawan ƙafa kan wata mace ce. Ita Gimbiya da ba ta gane ba ta kai kanta. Hausawa suka ce ai ƙazantar da baka gani ba sunanta tsabta amma ita kazantar ta je gani Allah kuma ya ba ta sa’a ina nan ina zaman zamana na san za ta yi nadaman abin da ta yi.
*
Biki ya ƙarato tun da mun shiga sabuwar shekaran 2023 Jidda na shirin komawa makaranta amma za ta je ta biya kuɗin makaranta da na hostel, sai ta dawo tun da karatu bai kamkama ba sai bayan bikin babanta za ta koma, amma ko a yanzu ba zaman banza take yi ba kullum cikin cin kayan fulawa muke yi a gidan nan Cake kam har kyauta nake yi da shi. Donut kuma sai ya yi sati tun da shi ba ya lalacewa da wuri.
Jidda ta gayyato kawarta Ummu Salma Hamza. Baby ce uwar gayya har da yan haddar su, su ba ruwansu murna kawai suke yi, a na saura sati biyu da wani abu biki Yallaɓai ya ce Rabi’atu a ranar ta koma Maiduguri na ce lalle za ta sha tafiya. Sai ya ke ce mini ai jirgi ta bi amma daga nan gida sati na sama za su tafi da sauran kayan a mota. Ban ma tambaye shi ba shi da kan shi yake faɗa mini suma a jirgi za su je ɗaurin aure. A raina na ce ai kana da shi ko birnin sin ne za ka biya domin ku je, yana yi mini list ɗin da waɗanda za a je ɗaurin aure Alhajinmu na sahun gaba shi da Tafidan Rano. Sai shi da aminan shi, sai Ya Usman da a can za su haɗu sai Musbahu.
“Kuma duk kai za ka biya kuɗin jirgin?
Yana dariya ya ce” Kawun ki ya ce zai ɗau nauyi”
Na jinjina kai zai iya tun da shima ya ta da kai. Har anko ya siya ma Marwa kuma da kan shi ya zo ya karɓan mata da ya shigo garin. Tariq ne da man bai kamo su ba amma shima yana da rufin asirin shi.
Yallaɓai bai faɗa mini ya yi kashe kashe kuɗi ba amma ni na san ya yi auran yar maiduguri ba wasa ba, ya faɗa mini an yi masa maganar kuɗin gyaran jiki na ce ai su can kamar al’ada ne.
Amma shi fa bai damu ba murna kawai yake yi ba ya damuwa da kashe kuɗin. Ni ce ma na gaji na tambaye shi gidan da Gimbiya ta tashi ya zai yi da shi? Ya ce mini bai yi tunani ba yanzu an rufe shi in ya yi shawara zuwa gaba zai san yadda zai yi da shi. Wallahi har raina nake son gidana ba na son tashi, amma tunda cigaba ne ya samu ba ni da mafita amma ina son gidan nan kuma ina da tarihi mai ɗimbin yawa a cikin shi.
Yallaɓai ya tsara tun da ban riga na tare ba a gidana za a yi taron biki ba Gwamnaja ko sabon gida ba. Ni da man ban ce kowa ya zo ba iya ni da yan uwana da wanda ya ga zai zo. Gimbiya da man ta ce ita ba biki za ta yi ba gidan matar de za ta zo, saboda haka mukkarabanta can za su sameta a sabon gida. Ni kuma ina gidana da jama’ata.
Tun satin biki Yallaɓai ya fara ƙyallin amarci ni kuma sunan shi ya tashi daga Yallaɓai ya koma Ango da ko na ce Ango zai washe baki yana jin daɗi..komai na buƙata ba abin da Yallaɓai bai kawo ba. Ya ba ni kudin kunshi da gyaran kai ni da yara kuma mun yi, mai kunshi ta zo har gida ta yi mana na yi gayya domin kaf yan gidanmu ban ce na ɗauke ma kowa daga su har yaran su. > Janaftybaby: Ana jibi biki Amina ta diro daga Kaduna. Faridan Tariq tazo aamma ita sai ana gobe biki. A kuma ranar su Yallaɓai suka daga maiduguri tun da in an ɗaura aure kuma za su juyo da amarya amma akwai sauran kayan da wasu za a kawo su ta mota. Jere kuma a ranar jumma’an da man daga nan Kano dangin su suka zo suka yi, ni ce na yi musu abincin tarba domin Gimbiya ta ce ba za ta yi ba Yallaɓai ya kirani ya ce na dafa na aika akai musu. To ba ma ni na dafa ba su Mubeena ne su kuma suka kai musu abincin can gidan shinkafa da miya da pepe chicken, sai kunin aya da zoɓo. Suka dawo suna faɗa mana irin dukiyar da aka sanya ma Amarya a shashenta da tsaruwan sabon gida.
Da man Mubeena da Marwa ne suka je kai musu. Suka ce Gimbiya na bangarenta ana ta shewa ta shirya rashin mutumci na ce ya ƙare mata can ni ba ruwana da ita. Wannan abin da na yi haka Yallaɓai ya kirani yana ta yi mini godiya sai da na ji wani abu ya motsa a cikin tsokar ƙirjina. Me na yi masa? Komai shi ya kawo kawai nawa na ba da umarni an dafa kuma na aika da shi.
Washegari 30 Jan ranar asabar ƙarfe sha daya na safe aka ɗaura auran Yallabai da Rabi’atu kuma sha sha ɗaya da mintina ni ya fara kira ya sanar mawa.
“Alhamdulillah. Ma sha Allah Allah ya ba mu zaman lafiya ya kaɗe dukkan fitina.”
“Amin na gode Sadiyata. Na gode ƙwarai da girmamawan ki.”
Ya faɗa cikin farinciki ina jin ta hayaniya ta wayar sai ya kashe. Sai da na ji tahowar ƙwalla amma sai na yi saurin yar da ita. Na yi kwalliya tun da har mai kwalliya na kira na gayyaci su Maijidda da samira duk sun taho mini biki. Waina aka yi da shinkafa sai alele sai zoɓo ga ruwan gora da lemuka sai wanda ka zaɓa. Na diba abincin tun da aka gama na aika da shi Gwammaja. Su Suwaiba ne suka zo mini bioi sai su Jawahir, sai su Hauwa da yan gidanmu duk wanda bai zo ba yana gidan Gimbiya. Na ce duk abin ta dai ga shi ba a fasa ba. Sai ga Ummu Salma da mahaifiyarta sun zo mana biki kuma wallahi na ji daɗi har da su turarenka wuta ta kawo mini da mayukan gyaran jiki ba su kwana ba, bayam la’asar suka juya ta ce sai za mu koma sabon gida za su dawo in sha Allahu. Haka na yi taron biki lafiya aka gama lafiya mun shan ankuna mun sha hotuna kuma duk na tura ma Yallaɓai shima ya turo mini na su da su Kawu sai na shi shi da Amary ta sha lafaya yar maiduguri sak ba ta yi makeup ba fuskarta sak ta bayyana.
Mimisco ta watsa hotunan a can group ɗin su na gida Musbahu ma dake can ya riƙa turowa ma su jin haushi suna gefe suna ji ba su da yadda za su yi. Tun kafin su Yallabai su ta so ya kirani ya faɗa mini, ya ce akwai ma wasu y’an uwa Rabi’atu da tun jiya suka taho. A yi abimci na tarban Amarya na ce ma to. Su Munnira na bar ma aikin,shinkafa suka dafa priderice, sai ferfesun nama da pepe chickenn da kuɗin hannuna na yi amfani ya ce in ya dawo zai ma yar mini. Ba a samu kunin aya ba amma an yi zoɓo sannan ga lemuka da ruwa
Da aikawa na so na yi amma Yallaɓai ya kirani da kan shi ya ce na je gidan na tarban masa Amarya.
“Sai na je? Ba ga Gimbiya da su Anty Bahijja?
“Na san da su na ce ke. In kuma ba za ka yi mini ba ne sai na ji.”
Ina jin haka na ce masa ya yi haƙuri zan je, ina ma gidan Mimisco ta biyo ɗaukata ita ta yi tsire ne mai yawa na tarban Amarya nima da su Hauwa da Munnira da Farida muka fara yin gaba sauran kuma na ce su hawo adaidaita. Motata kuma Amina ta tuƙo yan gidanmu zuwa cam. Mun iske bangaren Gimbiya cike da su Halima itama bangaren Amaryam akwai yan uwata a ciki masu jiran tarban ta. Saboda dai a zauna lafiya sai Mimisco ta ce mu fara sauka a bangaren Gimbiya amma na san ita kanta ta yi nadama. Wulakanci suka yi mana, kamar ba su taɓa sanin mu ba, Naja ba ta gaisheni ba amma ta gaishe da uwarta Anty Bahijja ba ta gidan sai Anty Maimuna kamar ta kashe nu in tana da iko. Sai Gimbiyar da ƙawayenta sai yanuwanta daga can Rano. Haka suka yi mana kallon banza wai ni Halima ke yi ma habaicin a yi dai mu gani in tusa za ta hura wuta. > Janaftybaby: Da Mimisco ta ce in Amarya ta zo a fita gabaɗaya a yi tarba shuru suka yi wallahi da ta iso ƙin fotiwa suka yi, Adnan ne ya ɗauko ta da ita da ƙawarta da kanwar mamanta daga filin jirgi, dagqani sai tawagata sai Mimisco muka yi tarban amarya. Mimisco ta yi tarba da Turaman zannuwa uku da 50k. Nima na yi da 20k da cimgam da su minti kuma wallahi sun ji daɗi, Rabi’atun tana cikin lafaya fara ne a rufe amma tana ganina sai da ta gane ni ta riƙe mini hannu.
.”Barka da zuwa Amarya.”
Bi sa al’ada bangaren Gimbiya muka fara yi musu jagora. Kanwar mamanta ta tambaya an ce tana da abokan zama guda biyu. Mimisco ta nuna ni ta ce ni ce uwargida ban riga na tare ba ne amma na taho tarban Amarya sai Gimbiya. Wacce ba ta ma fito falon ba duk da ko Mimisco da kanta ta kirata amma wallahi ta kunya ta mu a gaban mutane abin gudun ban takaici. Kanwar maman Rabi,a ta ɗan fahimci wani abu sai ta yi ta cewa a yi haƙuri da juna a zauna lafiya. Rabi’a ƙanwa ce a gare mu mu tsawarta mata in ta yi ba dai dai ba, haka nan muka kwashi sanyin jikin mu muka raka su bangaren Amarya. Ni na ɗauka a gidan Nene za tafara sauka Mimisco ta ce sai gobe za a kaita. Itama ranta ya ɓaci na ga ta kira Naja da Maimuna tana yi musu faɗa ni dai ba mu zauna ba, muna danƙama dangin Amarya abinci muka yi ta kan mu bayan na sanar da ita in tana bukatar wani abu ko ta kirani ko ta kira Yallaɓai za a kawo mata ta ce to.
A daran ma Yallaɓai ba a gida ya kwana shi da su Kawu a hotel suka kwana sai washegari da safe na gan shi da suka shigo gidan. Yallaɓai ana ta baza baban riga yana washe baki da an kira shi Ango ya yi dariya har tana fidda sauti.