Turken Gida – Chapter Fifty
by Janafty*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*
Shike nan faɗan mu ya ƙare ni da Yallaɓai amma lokaci bayan lokacin in muna zaune da ya yi magana zan kalle shi na ce” Ni ai Yallaɓai ka ga ƙarar mini da ruwan kaina. Ni da ka kalla ido cikin ido ka ce mini ina da mugun nufi akan matarka. Wallahi na kasa mantawa da wannan maganar”
In na faɗi haka sai ya marairaice yana lallashina shi a dole sai na manta duk kalaman da ya yi amfani da su a kaina.
“Me ya sa ba ki mantuwa ne Sadiya? Maganganun da na faɗa cikin fushi kema kin san ba a son raina ba ne. In ma na ce kina da mugun nufi ai kaina na yi mawa. Tun da tsawon shekarun da muke tare da ke ban amfana da komai ba sai alheri. Ki yi haƙuri don Allah ki daina dawo da maganar da ta wuce.”
In ya faɗi haka sai na tura masa baki na ce” Uhm, ai ka san da haka ka manta ka yi ta manganganu.”
“Ki yi mini afuwa ki yafe mini. Halin ɗan adam ne na ajizanci.”
Haka ya kan faɗi in na ta da maganar kuma ba wai ban yafe ba ne na yafe amma na kasa mantawa in na ga yana yi mini rawam ƙafa sai na kalle shi na tuna masa maganar. Tun yana lallashi da sake ban hakuri watarana ma shuru yake yi mini amma ya kan ce Allah na sama yana gani kuskure ne ya yi kuma ba wanda ya wuce ya yi kuskure.
Har cewa ya yi sharrin sheɗan ne ranar ina ta tsintsira dariya shi kuma sai ya yi fuska yana hararata.
Kwana biyu kamar na manta da maganar kawai ranar yana gidana da daddare muna falon muna kallo, Yumna ta yi barci tana ɗakin su Baby, sai za mu kwanta zan je na ɗaukota.
Wani American film muke kallo daman sune fina finan Yallaɓai ni kwata kwata ba sa burgeni sabo da shi ne ma na ke kallo, in ya ga na yi shuru sai ya yi ta mini bayani iyakata Umh da Hmm to ni bai san ba na son wannan bayanin ba, da zai ƙyale ni da na ji daɗi amma ba zai gane ba ni kuma ba na son na kushe ƙokarinsa. Yana cikin ba ni labarin film din ne ya gangaro kan karatu shi ne ma yake faɗa mini ya nemi gurbin PHD a Universty of Ibadan har ya samu.
Baki na buɗe kafin na kalle shi ina faɗin” Lalle Yallaɓai can Ibadan ɗin za ka koma?
“A’a ai online ne karatun sai in za a yi jarabawa zan je.”
“Allah ya ba da sa’a.”
Ya amsa da Amin Amin.
“Saura ni Yallaɓai maganar komawata master”
“Ina za ki je da Yumna? Ki bari ki yayeta sai ki koma.”
Na kalli Yallabai shima ya kalleni, ai yadda ya ga ina kallon shi ne ya sa ya yi dariya kafin ya ce” Wallahi da gaske na ke yi. Zan hana ki komawa makaranta ne? Ko Daughter na faɗa mata in har za ta koma ni ba ni da damuwa.”
Shuru kawai na yi masa na ma kasa mgana ina zencen makarantana yana kawo mini zencen wata matar shi, tsaki na so na yi sai na fasa kar ya ce na raina shi yana magana ina yi masa tsaki.
“Kina yayeta in sha Allahu sai ki koma. In kuma lokacin na sake yin ajiya shike nan sai ki jira ki sake haihu ki yaye sai ki koma.”
Ai ban san na kai ma kafaɗan Yallabai duka ba ya kauce yana dariya.
“Me na faɗa? Ba ki son haihuwan ne yanzu?
“Ban sani ba.”
Na faɗa ina tsumewa,
Rumgumoni ya yi yana faɗin”Sorry tsokanarki fa nake yi, ke ba ki san wasa ba?
“Ni ka ƙyale ni, ni ai na gama haihuwa da kai, ni da ka ce ina da mugun nufi a raina game da kai da matarka.”
Na faɗa ina kallon shi, da sauri ya sake ni, ni na faɗa ne a wasa amma sai na ga ya wani daure fuska.
“Yi haƙ..”
“Sadiya.”
Ya katse ni da kiran sunana a fusace kafin na amsa ya nuna mini yatsa yana faɗin” Ba na ce ki bar tado da wannan mganar ba? Me ya sa ba kya jin magana ne, ko so kike yi ki ɓata mini rai hankalin ki ya kwanta ko? To shike nan kin ɓata mini rai kin ji daɗi.” > Janaftybaby: Ya faɗa yana ture hannuna da na ɗora a kan cinyarsa. Ya mike na yi saurin kama hannun shi guda ɗaya.
“Sorry”
Na faɗa ina leƙen fuskarsa, tun da ya kauda kai ne ya ki dariya sai na jawo shi ya faɗo gefena na sumbaci ƙuncinsa ina ƙara faɗin” Am sorry Yallaɓai na.”
Lumshe ido ya yi ya buɗe kafin ya kalleni har muryan shi ta sauya.”
“Me ya sa kike haka ne Sadiya?
“Ba zan ƙara ba”
“Shike nan ni ba zan yi kuskure kuma na zo na gyara daga baya ba? Na ba ki hakuri kin ce kin hakura to dawo da maganar kuma duk na mene ne? Ni fa mijinki ne, ke matata ce da soyayya ce ta kawo mu a wannan karnin, kina yi mini laufuka, kafin ma ki roƙe ni nake yafe miki saboda ba na son mala’iku su yi fushi da ke. Amma ke me ya sa in saɓani ya shiga tsakaninmu magana kaɗan bisa kuskure sai ki ma yar da shi makami a kaina? Ko don kin ga ina lalacewa a kanki da ban baki shi ya sa kike yi mini yanga?
Sai na kasa mgana saboda maganganun shi sun sanyaya mini jiki.
“Ka yi haƙuri wasa nake yi.”
“Wannan maganar ba abar wasa ba ce. Ki bari kar ki ƙara ta yar da ita raina ba ya so. In kika ƙara zan kai karan ki wajen Alhajinmu.”
Da sauri na kalle shi gira ya ɗaga mini kafin ya ce” Da gaske na ke yi. Kin fara kular da ni da mganganun ki.”
“Yi haƙuri ni dai. So kake yi ka sa Alhajinmu ya daina misali da mu.?
“Tun yaushe? Ai kin gama karya mini wannan record ɗin a gaban Alhaji. Fisabillahi abin da kika yi ba ki kyauta mini ba.”
Na tura baki kafin na ce” To ba kai ka ja ba. Cewa ka yi na fita ba za ka hana ni ba.”
“Kuma kika juya kika tafin ko kunya?
Ya faɗa yana kallona ni kuma sai na juya masa baki, caraf ya kama bakin nawa ya ja, na yi ɗan ƙara ina buge hannun shi.
“To kar na tafin? Na nuna maka muna da gidan uba muma”
“To ai kin makara. Domin Alhajinmu ya fi sona a kan ki.”
“Na ga alama.”
Na faɗa ina rike baki shi kuma yana yi mini dariya.
“Haka fa Alhajinmu ya zaunar da ni ina faɗa masa abin da ka yi mini ina kuka amma shi yana koro mini jawabin laifina ne a fakaice yana yabon ka.”
Na karishe faɗa cikin mamaki, Yallabai ya kwashe da dariya yana mai rumgumoni cikin nishaɗi, muka yi baya shi ya jinginar da kansa a jikin kujera mai zaman mutun huɗun da muke zaune ni kuma ya yi ma kaina da jikina masauƙi a saman kirjinsa.
“Wallahi na yarda Yallaɓai Alhajinmu ya daɗe yana yin ka.”
“Tun a ranar farko da na fara ganin shi nima na ji kamar mahaifina. Ba ƙarya ba ne yana ƙaunata nima ina ƙaunarsa sosai na ke ganin girmansa saboda shi ɗin adalin Uba ne sannan dattijo ne.”
Ina ta mirmishi jin yana ta yaɓon mahaifina.
“Na je gabansa ina mai neman afuwa na yi miki laifi. Amma ni yake sake ba ma haƙuri da Amana. Ya ce Yusufa ka yi hakuri da Duhu ka cigaba da hakuri da ita akan wanda kake yi a baya. In ta yi maka laifi ka yi mata hukunci cikin natsuwa bayan ka yi bincike. Saboda shi yanke hukunci cikin fushi yana kawo dana sani. Kin ga dai afakaice ya yi mini nasihan na daina saurin yanke hukunci cikin fushi ba tare da bincike ba.”
Ya faɗa yana wasa da gashin kaina da na yi tsifa ban yi ri ga na yi kitso ba.
“Kawu ya yi ta kambama dattakon Alhaji. Na ce ai bai ga komai ba ni ne zan bashi labarin Dattakon sa.”
Sai na ɗago ina kallon shi, sumbatar lebensa na yi kafin na ce.
” Na gode.”
“See your mouth kin gode mene! Nima Alhaji mahaifina ne so ki daina yi mini godiya kuma duk abin da na faɗa akan shi kyakyawan hallayan shi ne.”
Na gyaɗa kaina ina faɗin” Gaskiya ne. Allah ya ƙara masa lafiya da tsawon kwana.”
“Amin ya yi tsawon ran da zai ga takwaran shi in sha Allahu.”
Sai na kalle shi kafin na yi magana ya rigani da cewa.
“Ina so na yi ma Alhajinmu Takwara Sadiya.”
“Uhm me ya sa ba ka yi masa a wannan haihuwan na Gimbiya ba?
Mirmushi ya yi har ina jin sautin mirmushin.
Kafin ya ce” Zan iya yi masa ba wanda ya isa ya ce don me. Amma na fi so takwaran Alhajinmu ya kasance Dubu da Yusufa ne iyayen sa. Sai ya fi soyuwa a wajen ki da wajen Alhajinmu.” > Janaftybaby: Girgiza kaina na yi kafin na ce” ba ka san Alhajin mu ba ne. Ko ni ko Gimbiya duka ba zai bambata mu ba.”
“Duk da haka dai. Hausawa suka ce abin cikin ƙwan ai ya fi ƙwan daɗi.”
Dariya na yi shima yana taya ni,na ƙara rumgume shi ina faɗin.
“I love you Yallaɓai na.”
“I really like you Sadiya ta “
Na ɗago ba zato kawai ya haɗe bakin mu, yana sumbata na. Sai nima na rumƙumƙume shi da hannayena na zagaye da su zuwa maransa ina shafawa. Hannu ɗayan kuma na saman kirjinsa ina masa wasa. Ban ɗauka za mu zarce ba sai da na ga Yallabai na sabule mini ƙaramar rigar da jikina da sauri na riƙe masa hannu ina kallon shi.
“Ina so.
“Mu yi a falo.”
Ya faɗa ararrabe saboda a lokacin ya ɗan kai sama can yana buƙatar matallafiya.
“Yara fa? Kar su shigo.”
Sai ya tashi yana layi, ya je ya rufe mana ƙofar falo ya kashe wutar amma bai kashe kallon ba. Tun yana tafe gare ni ya cire farar vest ɗin jikinsa ya yi kuma fatali da dogon wandon dake jikinsa, kaina ya ƙariso ya jawo ni a saman kujera mai zaman mutum ɗaya ya zaunar da ni a saman jikinsa muna masu kallon juna.
Ƙura mini ido ya yi da ɗan hasken Tibin da ke falon idanuwansa sun juye sun yi ja sannan sun ƙanƙance.
“Sadiya ta.”
“Uhm”
Na faɗa a ƙasan makoshi.
“Ki agaza miniiiii”
Ya faɗa cikin wani yanayi sai da tsikar jikina ya tashi da gudu na haɗe bakin mu waje ɗaya shi kuma hannayen shi na kara kaina wajen raba ni da yar ƙaramar shimin dake jikina. Ba ka jin komai sai tashin nunfashin mu sama sama.
Gaskiya Yesterday was cool. Na faɗa a cikin raina jiya nan mun yi nishaɗi da ni da Yallabai mun gamsu da juna fiye da tunanin mai tunani. Yallabai na ƙarshe ne wajen sarrafa ma mace da jan ragamar tunaninta in ta shiga hannun sa. A jiya nan haka ya ruka juyi da ni kamar waina ni ma ba a bar ni a baya ba na yi ƙoƙari sosai wajen faranta masa rai. Sai wajen ɗayan dare muka koma ɗakin mu bayan na je na ɗauko Yumna. Da asuba kuma a tiolet ya yi ɓarnan ruwan shi, ina ya bari ya bari amma bai ji ba sai ya ɗaga ni sama sai ji na yi kawai ya baƙunce shi, ban ɗauka har a tiolet lamarin zai ba da armashi ba sai da ya nuna mini hanya. Kai jama’a ni dai na faɗa muku Yallaɓai duniya ne wallahi.”
Ni dai tun da faɗan mu ya kare da Yallaɓai na manta da maganar Rahila sai da ta zo gidana na tuna na yi mata zencen me ya haɗa ta da Ya Muntari? Magana ta kawo magana na ba ta labarin artabuna da Yallaɓai, har dalilin da ya sa na ji batun su ita da Ya Muntari
Shi ne take faɗa mini kan wata budurwansa ce da ya ke kashe ma kuɗi, tana ɗauke masa hankali, ai ni na yi suman zaune kar ka raina namiji. Ya Muntari da nake gani sumu sumu kamar na Allah ashe kwallo ne..
Rahila na hawaye tana faɗa mini irin tashin hankalin da watsttatsiyar yarinyar nan ta saka ta a ciki. Ta hargitsa mata gida ba zaman lafiya ita da Ya Muntari, ta daina wanka ta daina mgana ta daina girki shine da ya gaji da magiya ya kawo ƙaranta wajen Alhaji.
“Tabdijam amma dai Ya Muntari bai da kunya.”
Rahila ta jinjina kai kafin tace” Dakyar na samu ya rabu da ita
.Kuma ba shi da ƙudin auranta amma tana cinye masa kuɗi daga waje.”
Ni dai har Rahila ta tafi ina ta kambama lamarin a ƙasan raina. Wai Ya Muntari tabdijam! Ban taɓa tunanin haka daga gare shi ba. Ai daga nan na daina raina wayan namiji. Yana fama da rayuwarsa amma yana ɗebe ma kansa aiki.
Allah dai ya kyauta. Yadda ni kaɗai na sani sai ban furta ma kowa ba amma na yi ƙoƙari sosai wajen taimakon yar uwata ta dawo cikin hayyacinta da shawarwari da jikina kuma da Aljihuna. Lokaci kaɗan kuma ta manta ta dawo kamar ba ita ba.
Maza maza mutanen mu.
***
Tun bayan abin da ya faru ba mu ƙara haɗuwa da Gimbiya ba sai da ta yi arba’in ta zo gidana kuma ina da tabbacin Yallabai ne ya matsa mata tun da shi ya kawo ta da kan shi. Da sunan an kawo mini Ammar na gan shi. Ban nuna komai ba na yi musu kyakyawan tarba, gidana ta yi yini tun safe har dare har yara da suka dawo makaranta nan Salisu ya kawo su tun da mamansu ta na gidana. > Janaftybaby: Da farko ta ɗan yi ɗari ɗari, amma daga baya da ta ga na nuna kamar ma wani abu bai faru ba sai ta saki jikinta. Amma ban ƙyaleta ba sai da na yi mata maganar da man kuma na yi alƙwarin ko ba jima in dai muka haɗu sai na fada mata gaskiya.
Ce mata na yi a duk abin da za ta yi to ta riƙe gaskiya da amana. Ta sani Allah na sama yana ganin ta, in har ta nufi wani da sharri to ta sani ƙaiƙayi na iya komawa kan masheƙiya. Sai ta fara kame-kame da cewa wai ba ita ce ta faɗa masa abin da ya faru ba kawai dai ya zo ya ganta tana kuka ga targaɗe a hannu shi ne ya fusata tana ta dai ƙoƙarin kare kanta na ƙarya ahalin ni da ita mun san ba gaskiya ta ke faɗa ba.
“Magana ai ta wuce. Da man na ce sai na faɗa miki gaskiya. Ki sani ni tsakani da Allah na ke zaune da ke ban taɓa nufin ki da wani sharhi ba. Ruwanki ne ki gyara alaqata da ke a zuciyarki ruwanki ne ki cigaba da ɗaukata tun farko. Amma ni dai ba zan fasa zama da ke tsakani da Allah ba sannan ba zan fasa mutumtataki a matsayin ki na matar mijina kuma uwar yayansa ba.”
“Na gode in sha Allahu zan gyara. Don Allah ki yi haƙuri “
“Ba komai. Ban riƙe ki ba, koma na ƙullaceki a baya na yafe miki. Ni da ke ba mu isa mu hana kan mu jin kishin juna ba tunda kishi gaskiya ne. Amma in ya taso mana mu koyi yadda za mu sarrafa shi akan mu. Allah ya ba mu zaman lafiya.”
Ta amsa Amin duk ta ji kunya ni kuma abin da ke zuciyata na faɗa mata. Tare muka yi ma tuwon shinkafar da na yi mana da daddare muna yi muna ɗan hira jefe-jefi a bakinta ma na ke jin Nene ta yi zazzabi kwana biyu na ce ban sani ba ai da na je na duba ta. Da Yallaɓai ya dawo da daddaee ya ji daɗin ganin mu tare gwanin ban sha’awa. Ranar girkina ne saboda haka na yi kwalliya yar caras da ni ina tashin ƙamshi. Tare muka yi dinner gabaɗaya har yaran cikin farinciki abin da ba mu taɓa yi ba.
Ni ban faɗa masa wani abu ba shi ne muna falon shi tare ya kallemu ni da ita yana faɗin” Na ga chanji daga gare ku na ji daɗi kwarai.”
Sai ta ce masa ai ni ce na yi mata nasiha kuma ta ji za ta gyara in sha Allahu. Ya yi ta washe baki yana jin daɗi ya taso ya rumgumeni yana sumbatana a ƙuncina na ture shi ina hararan shi.
“Ke ce jagoran mata na ko a gidan Aljanna Sadiya ta. Ni da duk abin da na mallaka duka na ki ne.”
“Har wannan gidan?
Na faɗa ina dariya.
Sai ya gyara zama a hannun kujeran da nake zaune ya ce” Wannan gidan da abin da ke cikin shi ai ya zama na ki, yau ba fata nake yi ko mutuwa ko rabuwa ba wanda ya isa ya fidda ke daga cikin sa. Sai dai ni ki kore ni ma domin kin cancanta.”
Ina dariya na ture shi ina faɗin”Bana son daɗin baki.”
“Wallahi da gaske na ke yi “
Ya faɗa yana ƙoƙarin ya dawo ya zauna kusa da ni sai na tashi na koma kusa da Gimbiya na zauna.
” Ni za ku haɗe ma kai?
Ya faɗa yana kama baki ni da ita muka haɗa baki wajen fadin” E ɗin.”
Muka faɗa a tare muna dariya sai ya koma ya zauna akan kujeran da na tashi yana faɗin” Za ku neme ni yara “
“Yara?
Na faɗa ina kallon shi sai ya zare mini ido yana faɗin” E yara ko kun girme ni ne?
Sai na yi shuru tun da na fahimci yana jin magana ne.
Saboda jin daɗi sai wajen goma ya tafi kai su gida da ya dawo bayan mun kwanta sai da ya yi mini maganar.
“Na gode Sadiyata. Don Allah ki cigaba da haƙuri. Ba ki ji farincikin da na ji ba lokacin da na gan ku tare da Daughter ba”
“Uhm”
Kawai na iya cewa domin sai na ga kamar Yallaɓai na sane a duk wasu iskancin da Gimbiya ke yi. Me ya sa ba zai mata faɗa ba? Sai ni ce zai yi ta nanata ma in yi haƙuri da ita, ita ba zai ce ta yi haƙurin ba.
Ni dai na yi masa yaƙe kawai ban nuna komai ba, sabo da kauda maganar sai na yi masa maganar zazzabin da aka ce Nene ta yi kwana biyu. Sai ya ce mini ta ji sauƙi ne shi ya sa bai faɗa mini ba amma na bari weekend sai na shirya mu je da yara mu gaishe ta na amsa masa.
Haka ko aka yi ranar lahadi muka je Gwammaja tun safe muka yini. Da man su Baby sun yi hutun Tahfez saboda gabatowar azumi, Nene ta ji sauki amma jikinta ba karfi ina gidan sai ga Halima wataƙila saboda idanuwan Nene ne ya sa ta gaishe ni, nima saboda mahaifiyarta na amsa. > Janaftybaby: Ni saboda ita a bangaren Maman farko na yi yini na, sabo da ba na son abin da zai haɗa ni da yarinya. In ta neme kawo mini wargi ba zan ɗauka ba. Muna gidan har dare tun da Yallabai ne ya kawo mu sannan shi ya ce zai biyo ya ɗauke mu. Motata a gida na barta. Tun la’asar Halima ta tafi gida shi ya sa na koma ɗakin Nene, duk da ba ta fito fili ta furta mini ta ji maganar hatsniyar da muka yi a gidan sunan Ammar ba a maganganunta na san jirwaye take yi mini mai kama da wanka. Hausawa suka ce ruwa cikin cokali, ya ishi mai hankali wanka.
Ta yi ta ba ni haƙuri ne, tare da nuna mini na cigaba da haƙuri ina kauda kai. Sannan ta gangaro kan maganar Halima ta na nuna mini na yi hakuri da ita akwai yarinta a tare da ita, da ta ji labari ta yi mata faɗa sosai tun rashin kunyar da ta yi mini na farko. Ni dai ban ce komai ba illa to, amma ina ganin beken Nene, Haliman ce yarinya? Mata da mijinta da yayanta ai ta san abin da take yi. Na dai nuna ma Nene komai ya wuce amma a ƙasan raina na kudiri niyyar ba zan bi ƙanwar miji ta samu damar cin kasuwa a kaina ba. Ni ko yayar miji na ga tana tozartani kama kaina nake yi ballanta ita ƙaramar alhaki.
Mune sai goman dare Yallaɓai ya biyo muka tafi gida. Mu dai mun tsaya mun ci tuwo shi kuma sai da na dafa masa Tea da Indomie ya ci kafin ya kwanta. Sabgogin gaba na kawai na cigaba da yi ga matsowar azumi, shi ya sa na saro inears da yaawa wannan sallar har da mayafai da takalma na yara da manya. Yallabai ya ba ni 100k rance a cewarsa zan biya shi in na haɗa ribata na ce na ji na karba da shi na samu na ganganɗa na ɗinko hijabai diffirent ɗinki kala kala sama da hamsi suna gida sai dai da an saka oder na saka a leda na naɗe Baby na taya ni muna sawa a jaka ko a leda. Tun da Jidda na makaranta sai Baby ke taimakona yanzu. Kuma Alhamdulillah, ana siya sosai ina samu ga Jidda ma tana saka mini a status tana yi mini talla har yan makarantan su sun ce suna so. Irin mata yan dapertment din su, akwai wata ma course ɗin ɗaya sannan ɗakin su ɗaya Ummu Salma Hamza ɗiyar Iyan zazzau ne na garin zaria itama akwai ƙoƙari kamar Jidda shi ya sa suka fara ƙawance shima ɗin sai da Jidda ta neme shawarata ni kuma na faɗa ma Yallaɓai na ce ya saka a yi masa bincike kan yarinyar kar ya zo ta shiga jikin ɗiyarmu ta cutar damu.
Shi ya bincika kuma ya ce yarinyar ta fito babban gida masu tarbiya. Jin haka ya sa muka ba ma Jidda izini ta saki jiki da ita, to ita ce ta siya hijabai sama da kala ashirin kaloli dabam-dabam. Ni kuma sai na ba ta kyautar ɗaya da dogon wando da sikat da pant saboda kyautatawa mai son ɗiyata. Cikin saƙon Khaleesat na saka musu sakon su can gidan suka je suka karɓa. A lokacin suka fara test ni dai addu’ata ko da yaushe Allah ya tsare mini yarana Jidda kuma ina yi mata fatan sa’a da nasara. Yallabai kuma yaƙini gare shi a kan Jidda da cewa in sha Allahu za ta saka shi alfahari wata rana.
Cikin haka muka shiga watan Ramadana, Jidda sai kusan salla ta dawo gida hutun na su ma na sati ɗaya ne ana fice salla ta koma saboda suna shirye-shiryen fara jarabawar farkon zangon karatu. Mu dai muna gida muna bin su da addu’a sai da suka gama jarabawa suka samu hutu ta dawo gida, duk ra rame sai ɗan wuya da tsawo. Yallabai ya yi ta faɗa wai kar ta saka ma ranta karatu ta mutu saboda naci. Ta riƙa hutawa tana cin abinci, dawowar Jidda na sake saka mata ido ko zan ga wani canji ban ga komai ba sai ma girma da hankali da natsuwa da Jidda ta kara. In ina kallonta sai na cika da alfahari na ce Ubangiji ka gama yi mini komai tun da ka ba ni Jidda. Baby ce dai wannan ko aure ta yi na tabbata sai na rika yi ina kwaɓa mata. Shegen rawan kai ne da surutu gare ta.
Kafin su koma Ummu salma Hamza ta kawo mata ziyara takanas ta zaria. Direba ya kawo ta a ranar kuma suka koma, ni kaina har da ni a masu yi ma Ƙawar Jidda Hidima. Itama na ganta mai kyau da ita age mate ɗin Jidda ce, ita ta fi Jidda haske da kiɓa amma tsawon su ɗaya. Itama a zuwan da ta yi na fahimci tana da natsuwa sosai. Har Yallabai sai da Jidda ta kira shi ya dawo gida ya ga Ummu Salma suka gaaisa ni kuma ta ba ni mahaifiyarta muka yi waya. > Janaftybaby: Ta ce mini tana shigowa Kano, za ta neme ni wata rana na ce in sha Allahu. Amma ta ce na karɓi lambarta a wajen Ummu sai na kirata na ce in sha Allahu. Ta kawo ma Jidda Atamfa da mayafi, sai Baby ta kawo mata doguwar riga har Yumna an kawo kayan wasa tun da ta san sunansu a baki. Nima da za ta tafi na ba ta hijabai biyu na ce ta kai ma mamanta. Sai turaren wuta da na jiki sauran nawa ne na kwashe na ba ta, Jidda daman ta yi cincin da donut ta kwashe mata aka yi raffing. Yallabai kuma 20k ya ba ta tace karɓa ya zare mata da cewa shi mahaifin Jidda ne. Kuma duk wanda yake aminta da Jidda ya tabbata shi din uba ne gare shi, shi ya sa ta karba ta duka har kasa tana godiya.
Muka rakata har waje, direban daman da ya kawo ta, tafiya ya yi sai da za su tafi ya dawo. Ni da kaina na yi ma Jidda alƙwarin itama za ta je har gida wajen Ummu salma. An ce tuwon girma miyan shi nama.
Kafin babbar salla suka koma makaranta. A lokacin na yaye Yumna, da na biye ma Yallaɓai to ba zan yaye ta ba. A cewarsa wai ba ta gama yin ƙwari ba yarinya bukekiya tana yawon ta ko’ina, tuni na cire ta a nono tana da wattani sha bakwai cikin na sha takwas. Da wajen Ma’u zan kai ta yayen, tun da ita ta yi mini magana. Har Marwa itama ta yi nacin na kai mata Yumna yaye. Ma’un da muke kusa na yi niyyar na kai mata ita ta yayeta kwatsam sai muka wayi gari da rasuwar mijin Baaba. Ma’u na can Kura mu ma mun je mun kwana ɗaya mun dawo har Amina dake Kaduna ta taho. To Allah ya sa dai ita ce uwar yayen Yumna ita tafi da ita Kaduna a can ta yi babbar salla. Tun tana rigiman Umma Abba Baby har ta gaji ta haƙura tun da akwai yara a gida. Yallabai ya gaji da korafi na ɗauki hakkin yarinya ya haƙura shima.
Sai da ta yi wajen wata biyu sannan Amina ta dawo da ita. Yumna ta ɗan rame sannan ta kara girma sun kawo ta da sha tara na arziki ita da mijinta Yallabai na ta fadan wai na tura musu ɗawaniya. Na ce na ji ba komai ai ƙanwata ce in ta yi mata ba ta faɗi ba.
Rayuwa dai alhamdulillah tana tafiya cikin farinciki. Yallabai yanzu fa na neman ya sha kwana. Kuɗi kawai yake facaka har mota ya sauya wata jeep ce itama mai tsada. Adnan ya faɗa mini da muke hira da shi za ta kai miliyan huɗu daga nan na yi shuru. Sannan ya bude shagunan sai da kayan gini, komai na na’uin gini akwai, kofifi, interlock, simnti, kayan aikin tiolet, kwano, ba abin da babu a wajen ƙasan wajen kuma ya saki shagunan masu aski da wasu yan kasuwan sun kama sannan ginin gidan shi ya yi nisa har an yi linfter an saka kankare tuni yanzu ma rufe yace mini ake yi, an ma kusa gamawa da ya nuna mini a hoto. Sai ina ta mamakin gaggawan da yake yi a kan ginin nan sai da na yi masa mgana.
“Ina so ne ko ba ku tare ƙarshen shekaran nan ba to a farkon shekaran 2023 mu tare a sabon gida in sha Allahu.”
“Allah ya amince mai girma Md.”
Na faɗa ina dariya har ina jinjina, saboda maganar gaskiya Allah ya buɗa ma Yallabai kwangolili ne wasu na jiran wasu malam. Kuma in dai aka bashi kwangila ya yi shike nan duk wanda ya gani sai ya yaba yace a haɗa shi da shi sillar gasikiya da amana da aiki ba ha’in ci. Mu kan mu mun shaida Mijin mu na da kuɗi yanzu, abinci sai dai mu yi kyautarsa. Duk wani abu na daɗi muna ci, suturu kuwa na kece raini muke sawa mu da yayanmu. Ba mu ba har iyayen shi ma yana yi musu nima ba abinda zan ce masa sai godiya. Ya ba ni kuɗi na kai gida ya kai kayan abinci komai fa sai godiya. Da shi da Kawu sun yi ma Tariq fintikau shi duk cikin su ba shi da ƙarfi tun da aikin Gwammati yake yi. Su kuma yan buga buga ne da man.
****
BAYAN WATTANI HUƊU.
A watan october 2022 Baaba ta gama idda sai ga shi karshen ta dai gidanmu ta dawo da zama ita da sauran ƙannen Ma’u su Zainab. A ɗakin Hajiya Dubu su Ya Hamza suka gyara mata daman tarkace ake sawa a ciki. Baaba duk ta yi laushi kamar ba ita ba, ni ce wai za mu zauna muna hira da ita har muna dariya abin da ban taɓa tunanin fatuwarsa ba. Datti ya samu aiki a NNPC reshen jihar kaduna har an saka masa rana zai yi aure zai auri wata abokiyar karatunsa tun suna KAsu ba ta yi aure ba har ta yi masters tana aiki itama. > Janaftybaby: Duk kuma a kusan lokaci ɗaya aka saka musu ranar aure tare da Adnan, wanda shima ya fara aiki a ma’aikatan Yallabai a matsayin Engeanaring na karatu.
Tuni ginin gidanmu ya yi nisa ko na ce cikin kashi uku an yi biyu saura ɗaya. Tun da ko wancan satin da hanya ta bi da mu ni da Ma’u da su Ya Aina na ɗauko su a motata mun je gaba da in da gidanmu na mu yake, gaisuwa yayar Zaitunan Ya Abubakar ne ta rasu muka je mata gaisuwa. Na bi da su ta gidan har sauka ma muka yi suka gani, Mun shiga ciki ma’aikata ne sama da ashirin suna aiki, wasu sun sanni suna ta faman gaisheni waɗanda ba su sanni ba suna faɗa musu matar injiniya ce.
Mun iske suna ta saka inteelock na tsakar gida. Wasu na ciki ɗakunan suna yin filista, wasu na ma an gama ana saka kofofi daman POP da wearing din wuta ana gama rafta Yallabai ya ce an yi su. Na ga har fulawoyi aka shushuka a gidan har sun girma daman Yallaɓai akwai son shuke-shuke a gida. Ya Aina da Ya Balki suna santin girman gidan da kyan shi, Ma’u ko har da guzarin kasar wajen da yake tana da ƙaramin ciki sha take yi wai ta yi mata daɗi.
Muna tafe a hanyar komawarmu Ɗorayi Ya Murja ta ce”Gidan nan da girma yake. Amma na ga shashi huɗu ko aure Baban Jiddan zai ƙara?
Ya Balki tace” Ni ma abin da zan ce kenan bayan shashin Sadiya da na abokiyar zamanta nata ga biyu nan kusa da juna.”
“Nima fa ina ta mamaki.”
In ji Ma’u dake gidan Gaba su suna can baya ne.
Ina dariya na ce” To Allah masani. Mu ma dai haka muka gani da na yi magana ya ce ɗaya na shi ne ɗaya na baki. Daga karshe yace ga shi da yara maza ya yi awadace ne.”
“Uhm ya dai ce muku ne amma da wahala bai ƙara ko dayan ba ne ballanta yanzu da giyar kudi ke ɗiban shi “
In ji Ya Aina ni ko na saka dariya ina ba su labarin diramasu da Gimbiya.
“In Yau Yallaɓai ya ce zai yi aure ai akwai yaƙin duniya na uku shi da matarsa.”
“Ta yi ta gama. In dai ya yi niyya sai ya yi.”
In ji Ma’u ita da ta ga zahiri, ga amarya har ta haihu, itama an zama daya da ita.
Ni dai ina ta dariya har muka kariso gida, Rahila ba ta je ba, ba ta da lafiya ta ce sai gobe za ta leko, muna gidan har bayan la’asar muna ta hira da Baaba da Gwaggo. Har a raina ban kawo ma Yallaɓai aure yanzu ba, ba kuma don ban ji a raina zai ƙara ba amma sai don ina ganin wataƙila akwai sauran lokaci. Sai dai me? Sai na fara ganin canje-canje daga wajen shi, yana yawan kafa-kafa da wayarsa a kwanakin nan. Abin da a baya bai dame shi ba in ba aiki zai yi a ciki ba ko an kira shi ta yini a in da take bai taɓa ba ya fi amfani da laptop ɗinsa a kan wayarsa
Amma a kwaanakin nan Yallaɓai na kan wayarsa har murmishi zan ga yana yi wani lokacin, na rasa me ya ke dubawa ko kuma me ya ke karantawa? Sannan wata rana in yana gidana zai dawo ya yi wanka ya ci uban gayu ya fita in na yi magana sai yace akwai mutanen da zai gani ne. Ni kuma samin shi da jama’a da hulɗodi sai ban damu da fitan na shi ba amma a kwanankin na fara zargin Yallaɓai yana yin wani sabon abun da bai saba yin shi ba, sannan ranar ma Yumna na wasa da wayarsa da ya ijiye a saman kujeran falon sa ya shiga tiolet, sai na karɓa abin mamaki na san code ɗin buɗe wayarsa date ɗin aurenmu ne, amma sai na gwada ya ƙi buɗewa kenan ya canza. Da ya fito ya ga wayar a hannuna ya ɗan yi wani iri, da sauri kuma ya karɓe wayarsa ni kuma sai na ce masa Yumna ce za ta yi masa wasa da shi na karɓa
Tambayarsa na yi ashe kuma ya sauya code ɗin buɗe wayarsa.
“E na sauya.”
Bai kuma faɗa mini abin da ya sauya da shi ba sai da na tambaye shi.
“Date ɗin ranar da na buɗe ma’aikatana ne.”
Haka kawai ya faɗa daga nan kuma ya koma ya zauna ya cigaba da duba wayar tashi. Har yana wani mirmishi na yi kasake kaawai ina bin sa da kallon mamaki amma na kasa magana.
Na ɗauka ni kadai ce na fahimci Yallaɓai na yin wasu baƙin abubuwa. Sai da Gimbiya ta yi mini magana a chart, da man tun bayan faɗan da na yi mata muke yar daɗi da ita in ma wani abu ne ya shige mata duhu akan mijinmu za ta kira ni mu tattauna.
“Maman Jidda.”
Na amsa mata lokacin Allah ya sa ina online itama haka.
“Kin fahimci Daddy na yin wani abu a boye wanda ba ya so mu sani!? > Janaftybaby: Sai na ce mata ban fahimta ba, saboda ko na ce na fahimta ba ni da hujja tun da ban ji ba, kuma ban gani ba.
“Me kika gani? Me ya sa kuma kika ce haka?
Sai na rubuta mata tambayoyin na tura mata sai na ga tana yi mini Vn
Yana shigowa da sauri na buɗe.
“Maman Jidda Daddy na yin wani abu gaskiya. Yanzu fa kafa kafa yake yi da wayar sa kuma a da ba haka yake yi ba. Maman Jidda Daddy fa yanzu sai ya kai 1 na dare yana online sai ka rasa da wa yake yin charting da na yi magana sai ya ce wai da abokan hulɗarsa ne. Sannan sai ya rika yin wanka ya ci gayu ya ɗau mota ya fita sai dare yake dawowa ni fa gaskiya na fara ji a jikina anya anya kina ganin ba wata ce can a waje ta fara ɗauke masa hankali muna nan zaune ba mu sani ba.”
“Hmmm.”
Kawai na tura mata na ma kasa magana. Ashe dai ba ni kaɗai na lura da wani abu na ɗaukan hankalin Yallabai a kwanakin nan ba.
“Ki yi magana. Ke ma kin fahimci haka,?
“Nima na fahimta amma na kasa gane me ya jawo haka.”
Na amsa mata
“Kin ji ko. Wallahi mu tashi tsaye da bincike kar muna zaune wata shegiya ta ɗauke masa hankali.’
Sai kawai na ce mata to zan bincika itama a ɓarayinta ta bi komai a sannu sai ta amsa ni da to, wai har da cewa ta sanni da sanyi wani lokacin wannan karon ba abin yin sanyi ba ne sai kawai na tura mata dariya.
A ranar da muka yi magana yana gidan Gimbiya ne sai washegari da zai dawo gidana ya saba dawowa da wuri, amma yau har goman dare bai shigo ba na gaji da jiran shi kuma na kira shi bai ɗauka ba. Kamar zan kira Gimbiya sai na fasa tun da ni ban saba kiran ta haka ba. Baby ce daman ke jiran shi kan maganar JSSCE ɗin ta na makaranta ta ƙi yin barci daga ƙarshe da ta gaji da jira dole ta kwanta.
Ba Yallabai ya shigo ba sai sha ɗaya saura. A yanayin da ya shigo mini ba na lafiya ba ne. Toilet ya faɗa yana faɗa mini cikinsa ya lalace. Wayarsa da babban rigan sa ni ya bari da su tunda ni ce na tarbe shi.
Na shiga bedroom ɗin mu da niyyar na ijiye masa wayar da key ɗin mota sai rigan shi. Ina shirin ijiye masa wayar a saman gado kira ya shigo. Gabana ya faɗi ras!
Ganin sunan mai kiran RABI’ATU BUK.”
Har ta katse na kasa daina kallon wayar. Kaf a tunanina ban tunano wata yar uwan Yallaɓai mai wannan sunan ba. Ban gama mamaki ba gur! Saƙonta ya shigo wayar daga sama na ja na fara ganin abin da ta rubuto.
“Yallaɓai na ka isa gida lafiya? Mun gode…!
Daga nan sai saƙon ya yanke, jiki na rawa na watsar da rigar hannuna ina ƙoƙarin gwada buɗe wayar amma na kasa.
Wata zuciyar ta ce Sadiya ki natsu ki yi aiki da hankali. Sai kawai na ijiye ma sa wayarsa nan saman gadon na zauna a gefe na ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya ina girgizawa.
Mintina biyar sai ga shi ya buɗe kofar bedroom ɗin ya fito yana nishi sama sama.
“Cikina kawai ina hanya ya karta. Ina zuwa sai gudawa kina da ko pulajin ne Sadiya?
Ya faɗa yana dafe cikinsa. Lokaci ɗaya yana ƙarisowa gabana yana kuma ƙoƙarin cire rigar jikinsa.
“An kira wayarka. “
Ya kalleni a ɗan tsume yana cire rigan daga shi sai farar vest.
“Ta kuma turo saƙo.”
Sai kawai ya tsaya yana ksllona. Nima ina kallon fuskar shi yanayin shi ya nuna tsoro amma sai ya yi dakiya irin ta maza.
“Rabi’atu ce ko?
Ya faɗa yana kallona.
“E ita ce”
Na faɗa ina kallon shi, shima yana mai kallona sai kawai na ga ya yi murmishi. Mirmishin da na ji ya soke ni a ƙasan zuciyata.