Turken Gida – Chapter Forty-eight
by Janafty*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*
A daran da Yallaɓai ya dawo yake faɗa mini sunan yaro Muhammad. Na ce Allah ya raya mana Muhammad cikin addinin islama ya ce Amin Amin. Tare muka kwana cikin farinciki, da wuri ya fita saboda ya ce akwai mutanen da ke jiran shi a can office amma ya sha wankan shi ya ci gayu cikin shadda dark blue amma ba mai babban riga ba. Sai ya fito a angon ƙarninsa ina zolayansa kafin ya fita.
Bayan na dawo raka shi na yi ma Yumna wanka na goya ta na fara ayyuka Baby daman ita ta fara fita kafin Yallaɓai. Jiya da daddare na ji ta fara faɗin yau sunan Anty Gimbiya ba za ta je makaranta ba tun kafin Yallaɓai ya ji labari ya ɗaure mata kugu na ja mata kunne shi ya sa yau da safe ba ta yi rigiman ba za ta je ba. Shara na yi sannan na yi mopping gidan duk ya yi ƙura kwana biyu ban yi ba, da man Jidda ne ta sangartani yanzu kuma tana makaranta Baby kuma ga makaranta ranar weekend kuma tana Tahfez in ma ta dawo wanke-wanke kawai ya isa ta fara tura baki tana faɗin ita duk ta gaji shi ya sa ban ma dogara da ita domin na fahinci ko a zamanin baya Baby ta fi ni lalaci.
Har ga Allah ban yi niyyar zuwa sunan da wuri ba. Wajen sha ɗaya na safe sai ga wayar Hauwa tana faɗa mini na shirya na ce mata ni fa ba yanzu zan je ba sai anjuma.
“Don Allah ki shirya mu taho gidan ki mu wuce tare.”
“Ke da wa?
Na faɗa ina tura baki kamar tana ganina.
“Ni da Munnira mana. Mutanen Rano ma suna kan hanya yanzu muka gama waya da Ashen mu.”
Cikin mamaki na ce” Ikon Allah suma duk za su taho ne?
“E tare da yan gidan su Gimbiyar ne. Hajiyarsu ta aika ma Mama shi ne ta ce ashe ta shirya ta bi su.”
Ni dai sun takura mini ba ni da yadda zan yi sai na ce bari na shirya. Mun gama wayar da ita kenan Marwa ta kirani ashe har da ita a masu tahowa suna kuma a can gidan sunan za su sauka jin haka ya sa sai na ce bari na shirya kawai mu wuce tare da su Munnira. Ni daman yan gidanmu ban faɗan ma kowa ba Ma’u ce kawai ta sani kuma na san ba a bakina ta ji ba, ta yi mini maaganar ashe Gimbiya ta haihu na ce e ta yi fatan alheri ba ta zo ba kuma. Domin gabaɗaya alaqar su da Anty Bahijja ya ja baya. Ni yadda ma Ma’un take faɗa mini Amaryan Alhaji Mustpaha yanzu ita dangin shi suka rike ita da Hajiya Zainab ina jin har Anty Bahijjan ta yi ma Ma’u batulci. Na san ta sarai za ta aikata tun da ita daman ba ta da alkibla.
Kafin na shiga wanka na kira Hauwa a waya na ce na chanza shawara su biyo mun sai na ɗauke su a motata mu tafi tare sai ta ce mini to. Sai da na yi wanka na shirya cikin wani leshina sabo ne yana daga cikin kayan da na samu da sunan Yumna ɗinkin bubu doguwar riga. Leshin mai kalan maroon ne sai na yi amfani da mayafi kalan shi takalmi ma da jaka ina da maroon da su na yi amfani. Yumna kuma na yi mata gayu cikin kaya yan kanti jajaye harta takalmin kafanta da safa ja ne, haka hulan da ke kanta na gyara mata gashin kanta. Ta biyo a sumar kai amma Yallaɓai ba ya bari a yi mata kitso sau ɗaya Maman Nana da ta zo yi mana kitso ni da Baby na ɗan ce ta yi mata kalaba aka sanya mata band kitson ya yi kyau amma ta yi ta kuka saboda ba ta saba ba.
A daran Yallaɓai da ya dawo ya gani ya ce sai na kwace mata wai an ci zalin yarinya don an ga ba ta mgana tun ballanta da take ta kuka shi a tafau zafin kan ne ya saka ta kuka tun kuma daga ranar ya ce ba za a ƙara mata kitso ba sai ta girma an yaye ko sai kanta ya yi ƙwari. > Janaftybaby: Sanin halin Yallaɓai da naci wani lokacin in har aka sake kuma ya gani ni ce zan sha mgana sai kawai na ƙyaleta ban ƙara yi mata ba, amma kowa ya ganta sai ya ce ga ta da gashi amma ba a yi mata kitso sai na ce babanta ne ba ya so. Daga karshe ma sai na sissiya mata huluna kananun size kamar nata, na ke saka mata in zamu fita yau ma kalan ja mai maroon, na saka mata na rufe mata kan ta da shi, sannan na je ɗakin su Baby na ɗauko mata kaya a cikin dirowanta. Shadda na ɗauko mata doguwar riga da ƙaramin mayafi. Hauwa na tsaya ina ta jira sai wajen azahar ta shigo gidana shi ya sa sai da muka tsaya a gida muka yi salla sannan muka fito na rufe gida na tuƙa mu a mota ta, sai da muka tsaya a kan hanya na sha mai da safe Yallaɓai ya saka mini 5k ya ce na saka mai a mota, wani lokacin ma Adnan zai turo ya ɗau motar ya je ya saka mini wata rana ma da kan shi zai tura ya je ya ciko mini da tankina ya kawo mini. In ba lokaci kuma sai kawai ya ba ni kuɗin amma ba ko yaushe ba wani lokacin ina sakawa da kudina. Ai ya gama yi mini mai wuyar tun da ya siya mini motar. Na man da zan yi zirga-zirga na a cikin gari ba zai gagare ni ba.
A gidan man kafin layi ya zo kanmu na kira wayar Salisu na sanar da shi in ya ɗauko Baby daga makaranta gidan Maman su Khalipa zai kawo ta. Sai ya ce mini to, a bakin shi na ke jin ashe su Khalipa ba su je makaranta yau ba. Hauwa na ke faɗa mawa ta yi dariya kafin ta ce” To da man ai ba za su je ba. Suna fa ake yi sunan ma na gidan su.”
Ban ce komai ba, illa Yumna da nake kallo wacce ke hannun suna ta wasa da yaron Hauwa. Ita har ta yaye shi ma yana neman shekara uku ne ma. Munnira na tuna shi ya sa na kalli Hauwa kafin na ce” Wai kina ganin zuwan Hadiza ba zai hana Munnira zuwa gidan sunan nan ba kuwa?
Na faɗa ina kallon Hauwa. Domin na kira wayar Munnira da niyyar na ce mata mu haɗu a gidana sai mu wuce gabaɗaya. Sai ce mini ta yi mu tafi kawai ƙanwarta Hadiza ta zo daman mun yi ta ɗin da ita tace mini ta zo garin da yake a garin Minna take aure. A yau ɗin ne ta kai ma Munniran ziyara.
“To wa ya sani. Ina jin kamar fa Hadizan nan gidan Munniran za ta kwana “
Hauwa ta amsa mini daidai lokacin layi na zuwa kan mu sai ban ba ta amsa ba sai da na yi mgana da mai zuba man na faɗa masa na adadin da zai zuba mini ina da kuɗi a jaka ta, sai na bashi sai da muka bar gidan man muka ɗau hanyar sharaɗa sannan na kalli Hauwa kafin na ce” Wataƙila nan za ta kwana. Kila su zo tare in ta yi niyya ba.”
“Ai fa. Ta bakin ki in ta yi ra’ayi za ta jawo ta su taho tare”
Muna tafe muna hira ni da Hauwa har gidan Gimbiya. A waje na yi parking ɗin motata tun da ga na wasu nan duk a wajen, har da na Anty Bahijja na gani da man na san ai tana gidan tun safe. Gimbiya ce fa ballantana tana dukan ƙirjin cewa an sake yi musu farar haihuwa. Mun shiga gidan ina ɗauke da Yumna da jakata da key ɗin motata. sai Hauwa itama riƙe da goyonta ita ta ɗauko ledan kayan Baby da saƙon Gimbiya tun da ita ba ta ɗauko jaka ba.
Gida fa cike da baki, ashe har anko sun yi ba mu sani ba, ba wanda ya nuna mana. Ni da Hauwa muka kalli juna amma ba mu yi magana ba. Marwa ne da Ashe suka tare mu shi ya sa ma muka saki fuska sun sauka tun ɗazu. Ashe har tana yi mini tsiya.
“Anty Sadiya sunan na ku har da anko kuka fitar amma ba labari “
“Nima yadda kika gan shi haka na gan shi.”
Na faɗa ina dariya da yake tana da barkwanci ne ita Aisha. Ashe su Hauwa ke kiranta, lokacin sunan Yumna ba ta da lafiya ne shi ya sa ba ta zo ba, karɓan Yumna ta yi, ta fara ƙoƙarin yi mata kuka da sauri ta ce” Ke ƙaniyarki nima uwarki ce.”
Ni da Hauwa muna ta dariya. Mun gaisa da Marwa na dauƙi Afra ina faɗin ta yi mini girma a ido sosai ba kamar ganin ƙarshe da na yi mata ba.
“Umma ta kusa wattani shidda fa?
Sai na buɗe baki ina faɗin” Lokaci ba wuya. Allah ya sa mu da ce.”
Ta amsa da Amin tana dariya, Baby ta tambaya na ce tana makaranta amma in sun dawo nan za a kawo ta na ma taho mata kayan da za ta sauya.
“Su Jidda ana can makaranta ko?
“Wallahi tana can. Yau ma dai ba mu yi waya ba.”
“Allah ya ba da sa’a.” > Janaftybaby: Duk suna falon ne, tare da sauran dangin Gimbiya na Rano. Ban ware su ba na bisu muka gaisa cikin sakewa. Su Anty Bahijja da Naja ana ta kai da kawo su leshi ne a jikinsu iri ɗaya ina tunanin anko suka yi.
“Barka da aiki Anty Bahijja an yi suna lafiya?
Na faɗa lokacin da ta zo wucewa. Waigowa ta yi sai ta nuna kamar yanzu ta gani alhalin ni na san tun shigowata ta gan ni har ido ma mun haɗa da ita.
“Sadiya ce! Sai yanzu za ki zo mana Suna?
Ina mirmishi na tashi na isa wajenta ina faɗin” To ka ga ku Anty Bahijja ai ba sai mun yi samakko ba, kuma dai kin ga na tsaya na shirya angon ƙarni a gida ne kafin na fito “
“Gaskiya ne. Ina Yumna?
“Tana hannun Marwa”
Na bata amsa sai ta ce na shiga ciki mana, ta waiga ba ta ga Munnira ba sai Hauwa tun da har sun gaisa.
“Ina ɗayar yar tawagan na ki?
Sai da na yi dariya kafin na ce” Ta yi baƙuwa ƙanwar ta, ta zo kila anjuma ta leƙo “
Sai ta wani jinjina kai kafin ta ce” Kina dariya karya na yi ba yan tawagan ki ba ne? Duk wanda ya ce miki kule sai sun ce masa caass.”
Ni dai ina ta dariya ban yi magana ba, na tuna can kwanaki Mubeena ta taɓa faɗa mini Anty Maimuna ta ce wai tsoro na su Hauwa ke ji, sai abin da na ce shi suke yi shi ya sa duk in da nake suna bina a baya. Ni kuma na san haushi suke ji saboda suna tare da ni. Sai na jujjuya ina neman Mubeenan ban gan ta ba, wata kila ba ta zo ba ne, Anty Bahijja ta ce na shiga ciki Gimbiyar na ciki tare da ƙawayenta.
Na kama hanyar Bedroom ɗin da Gimbiya ke ciki muka haɗu da Naja, ta gaisheni na amsa ina tambayan ta ya hidima ta ce sun gode Allah. Daga nan na shiga ɗakin Gimbiya dake cike da kawayenta da ƙannenta har da yayyenta. Da fara’ata na shiga aka gaggaisa nan na ga autar su Gimbiya Maryama da ke aure a can Lagos ba ts cika zuwa ba na dai ji labarinta amma ban taba ganin ta ba sai yau, ni na fara yi mata mgana amma sai na ga tana amsa ni a fuzge ban bi ta kanta ba na isa gefen gado kusa da Gimbiya na zauna muna gaisawa ta ci shadda pink ta ji aiki an yi mata makeup ta yi ras da ita.
Suma ƙawayenta sun sha kwalliya sun sha anko.
Gaisawa muka yi ta ba ni Muhammad na ɗauka shima an yi masa gayun su na yara da kaya masu kyau da tsada.
“Allah Ya raya mana Muhammad”
Na faɗa sai ta amsa da Amin Amin.
“Ina Baby? Ko ta je makaranta ne?
“E ta tafi. Amma na kira Salisu zai kawo ta nan, tun da na zo mata da kayam da za ta saka.”
“Ayya. Su Jidda ana can makaranta. Ta kirani da safe muka gaisa ta ce Anty wani suna za mu riƙa kiran Muhamnad na ce ta saka masa suna cikin sanyin ta ta ce Anty Ammar ya yi?
Ina dariya na ce” Ta ko iya zaɓan suna. Allah ya raya Muhammad(Anwar)”
Aka amsa da Amin gabaɗaya da waɗanda ke gefen mu suna jin mu. Ina nan zaune sai ga Hauwa ta shigo sai na matsa mata gefena tazauna ta mika mata Muhammad, sannan na karɓi ledan sakonta na mika mata ta karɓa tana faɗin.
“Ba kya gajiya Madam! To na gode Ammar na godiya Allah ya saka da alheri “
“Haba ba yawa fa. Amin”
Yumna ta tambaya na ce tana wajen Marwa, yarinya Marwa ɗin ma ta yi barci nan saman gadom Gimbiya na kwantar da ita. Har ita Gimbiyar sai da ta tambayi Munnira wai ya ta gan mu mu biyu daga ni sai Hauwa na yi dariya na ce ta yi baƙuwa ne amma za ta taho daga baya. Mun saba in dai wani abu ne a dangin mazajen mu to mu uku suke ganin mu. Kowa ya san ni da su Hauwa mun zama aminai ne ba facaloli ba.
Abinci ta ce a kawo mana sai na ce a kai mana falo can za mu koma, ba mu ma kai ga barin dakin ba sai ga Suwaiba ta iso tare da ita muka fita falo ana ta hira. An kawo mana abinci tuwon shinkafa mai naman rago. Sai dambun zogale sai alale, sai muka haɗu da ni da Suwaiba da Hauwa muna cin abincin ina tambayan Jamila ta ce itama yau ƙanwar mijinta ake suna ta haihu sai anjauma za ta leƙo. Muna cin abinci muna hira su Marwa suka dawo in da muke suka zauna a cikin hiran ne Hauwa ke maganar me ya sa ba ta ga Suwaiba da ankon sunan ba?
“Wa? Mu a suwa. Naja ta tura mini na ce ba ni da halin yi.”
“Au da man ankon ma sai wanda ya isa ake nuna ma wa? > Janaftybaby: Hauwa ta faɗa tana riƙe baki. Suwaiba na dariya ta ce” Ku ba a nuna muku ba? Wataƙila saboda Sadiya ne domin na ga ana kishi da ita ko sunan ma in kun lura yanayin na Yumna aka kwaikwaya. Duk haihuwar su Khalipa ba ta yi anko ba sai wannan?
“Uhm’
Kawai na iya cewa kafin na yi magana Ashe ta karɓe da cewa” Wai ba a nuna muku ankon ba da gaske?
“Wallahi ba mu sani ba.”
Na rantse mata sai ta yi kasake kafin ta ce” To har Rano wannan akon bari mu ku ji.”
“Zai kai can mana. Kun manta gidan su na can ne.”
In ji Suwaiba, Marwa ta ce itama Anty Bahijja ta tura ma Kawu Abba ya ce ba zai siya ba sunan ne sai an yi anko. Shi ne ta ce ai nima da na haihu na yi anko kuma ya siya mata a lokacin shi ko ya ce ba shi ya siya ba da kuɗinta ta siya a wancan lokacin. Yanzu ma shine ya nuna mata in tana da kuɗi ta siya Marwa ta ce ita kam ba ta da kuɗi ba ta siya ba.
“Ikon Allah.!
Suwaiba ta sake faɗa tana mai mamaki, Hauwa ta ce da man ko na Yumna ba su yi ba gwara ma da ba su nuna mana ba muma ba za mu yi ba.
“Da sun sanar damu za mu yi ko don mu tura musu Aniyar su.”
Na faɗa ina mirmishi.
“Wallahi kuwa.”
In ji Marwa.
Muna ta hiran mu, Naja ta zo ta ga ba a kawo mana ruwa ba da kunin Aya ba.
“Wa ya kawo muku abincin?
Ta tambaya tana kallon mu.
“Maryama ce ta kawo musu abinci ba ruwa ba lemu.”
Ashe ta faɗa cikin gatse sai Naja ta yi dariya ta ce Ashe ta biyo ta karɓo mana. Ita ta bita sai ga shi ta dawo da ruwan gora da fanta sai kunin Aya da zobo cikin wani roba. Tana ta masifa wai an ce Maryama ta ba da zobo da kunin aya tana wani daga kai.
“Har tana ce mini ba kin sha ba ke Ashe? Na ce na sha in zan ƙara za ki hana ni ne?
Na kwashe da dariya ganin yadda Ashe ta yi da baki tana kwantata mana yadda suka kwashe da Autar su Gimbiya.
“Sai ta ce me?
In ji Suwaiba itama tana dariya.
“Me kuwa? Ta yi shuru ai ta san ni yadda ba ta taɓuwa nima haka. Naja ta ce na ku ne sai ta wuce ta buɗe dakin ta ba ni.”
Hauwa na dariya ta ce”Da man Maryama ba ta da dama. Ga rashin kunya da ta yi auran nan ne ma ta yi sauƙi.”
“Rashin kunya ai duk tare muka yi muna yan mata. Ni yanzu ai sai dai ta nuna mini zaman agolege ni kuma na gwada mata na Sulaja.”
Ni dai dariya har ina kwarewa, Yunma na zaman jikina ina ba ta alale har tana sulmiyowa.
“Ke da man ba cikin garin Lagos ɗin take aure ba?
“In ji wa! Ko dai ake raina ma wayau. Tana cikin garin Agege can mijinta yake kasuwanci. Shine da ta zo garin ta yi ta buɗa hanci wai ita a dole tana auran miji mai kuɗi suna zaune a garin lagos. Allah na tuba wallahi ko ni da mijina ke aikin gwammati a kallon farko mai hankali in ya yi mana ya san na fita jin daɗi “
Ni da Suwaiba muna tsintsira dariya ina faɗin Munnura ta yi missing na so tana wajen nan da an ji muryanta a sama. Abin da ya ɗan tsagaita hiran ma Faridan Tariq ne ta kira ni a waya ta ce ita ba ta samu zuwa ba suna sai sallar azumi take tunanin za su shigo garin. Sai na ke faɗa mata ina gidan sunan gamu nan ana ta hira ana dariya ta ce na gaida kowa da kowa. Muna zaune a falon sai ga Mubeena ashe tana makaranta suna da test duk ta sha wuya Naja na yi ma magana na ce a kawo ma Mubeena abinci daga makaranta take. An kawo mata itama irin na mu, muna nan muna ta hira sallar la’asar ne ya tada mu bayan mun yi salla mun idar muka fito an kira mai hoto kamar dai lokacin sunan Yumna.
Mun fiffito, sai ga Munnira yar halas ita da Hadiza ƙanwarta tana ko ganin mai hoto sai da ta riƙe baki kafin ta ce” To pha sabon salo tusa a lasifika.”
“To za ki fara ko?
Hauwa ta tare ta, tana dariya.
“To ai na ga ana ta so a kwaikwayo mu ne.”
“Ai komai ma irin naku ne. Ba ki ga har da su anko ba.?
Suwaiba ta fada mata tana dariya Munnira ta waiga ta sake waigawa kafin ta saki shewa da ƙarfi tana faɗin” Ahayye nanaye. Yau ina ganin abin da yafi karfina ni haihuwar mutun biyu”
“Kishin ne har da na suna? > Janaftybaby: Hadiza ta faɗa tana dariya Ashe ta ce” To miye ma ba a yi ma kishi yanzu? Kishi ya zama ɗan gata yanzu.”
Ni dai ganin hankula sun fara dawowa kanmu na ce Munnira ta yi wa Allah ta yi shuru
“Zan yi shuru amma in na ga abun da zan magantu wallahi sai na mangantu.”
“Nima ina bayan ki.”
In ji Ashe har suna tafawa sai na lura hatta Hadiza irin su Munnira ne, har tana cewa tun da dai a dake ba za mu dakun ma kowa ba ai da sauƙi.
“Ni dai ku rufa mana asiri mu bar gidan sunan nan lafiya kafin a yi mana rubuti.”
“Ai wallahi ba wacce ta isa tab.!”
Munnira ta faɗa har tana ɗaga murya na balla mata harara. Munnira ba ta shiga ciki ba sai da aka gama hotuna yadda ba a gayyace mu, mu ma ba mu tura kan mu ba, ni ko a sunan Yumna na kirata mun yi amma ni ko kallona ba wanda ya yi. Su Naja ne da su Anty Bahijja sai ƙawayenta da dangin ta ba ma kamar Maryama ɗin nan na yadda ta cika kauɗin tsiya.
Bayan an gama hotunan muka dawo cikin gida muka zazzauna a falo muna hira. Munnira ina kwabarta sai da ta yi ma Naja magana wai an fidda anko an nuna ma waɗanda aka so.
“Haba. Ban tura muku ba? To wallahi na manta ne”
Ta faɗa daga ji ma karya ne, Suwaiba ko ta ce” Sadiya ai ba a waya ya kamata a nuna mata har gida ya kamata a kai mata ta gani.”
“Anty Suwaiba abubuwan sun yi mini yawa. Jibi za mu bar kasar ni da Honey. Ankon ma Gimbiya ba ta so a fitar ba ni ce na matsa. Mantuwa ne duk wanda ban turamawa ba ya yi hakuri.”
“Ai ba komai. Kun hutattashe mu da kuɗin mu “
In ji Munnira.
“Afuwan Anty Sadiya.”
Naja ta faɗa, tana kallona ni ko sai na yi mirmishi na ce ba komai. Nan dai ta wuce tana juya mazaunai.
“Ƙarya take yi wallahi kunya ce, da man domin ta ji kunyar na yi magana “
“Allah ya shirye ki Munnira “
Hauwa ta faɗa tana dariya ni kuma sai na ce” Kuma da ba haka take ba. Da ni ce mai bakin amma yanzu Munnira ta taka ni.”
Na faɗa ina dariya kai tsaye ta ce” Wallahi da bakina kawai dai na ɗan yi lamɓo ne. Sai da na gama ganin takun kowa sannan na bayyana kalata.”
Muka kwashe da dariya gabaɗaya muna nan zaune aka mai do nepa falon ya yi haske Suwaiba ke tsokanan Anty Bahijja da ba chasu ne ta ce ita ina ruwanta da chasu yanzu ma gida za ta tafi, ba ta kuma daɗe da maganar ba muka ga tafiyarta ta fita ba daɗewa Maryama ta zo ta kunna waya da wakar Amarya ki haɗa kayan ki na Nura. Inuwa tana wani takawa yan gidansu na yi mata ihu
Ba zato kawai Munnira ta ce” wannan ai tsohuwar waka ce. Kuma ƙauyanci ne mu taka rawa da ita.”
Kallon Munnira kawai na ke yi kallon ina ruwan ki.
“Gaskiya ba. Kuma sautin waya ai ba sauti ba ne. A nemo speaker.”
Hadiza kanwarta ta amsa mata, daman duk zamu ce ta iske mu je mu.
Suka yi kamar ba su ji ba, Maryam ɗin ta cigaba da rawan ta suna yi mata tafi. Ita ke fadin a je ta fito mata da Gimbiya ta zo ta yi rawa. Sai kawai ta saka wakar uwar gida ran gida har Gimbiyan ta fito lokacin ta sauya kaya ma Maryam ɗin ta kamo hannunta tana bin wakar.
“Uwar gida ran gida Tafida yana yi miki rawa.”
In da aka ce shaba sai ta kira sunan Yallabai
Ni da su Munnira muka kalli juna kafin mu yi dariya cikin mu ba wacce ta yi tunanin Munnira za ta mike sai ganin ta kawai mu ka yi a cikin su tana juyi tana faɗin” A fagen na mu ne mu Uwagidaye ne bai kamata amayar ta shigo ba.”
Sadiya, Hauwa wannan fagen namu ne.”
Ni dai ban tashi ba Ashe da Hadiza suka mike suka mara mata baya Suwaiba na zuga su da tabbas filin naku ne. Sai kawai a ka bar musu filin Maryama ta saki baki ita da su Gimbiya. Ita Gimbiyar ba ta yi magana ba sai ita Maryam ɗin ta ce”Miye haka? Ai ko fili na Anty Gimbiya ne. Domin ita ce Uwargida ita ce Amarya.”
“Ina kika baro Uwargida Sadiya? Kirarinta ta Yallaɓai. Ta zama Tafida Tafida ya zama ita.”
Munnira tafaɗa cikin sigan wasa.
Sai kawai Maryama ta yi ja tsaki kafin ta ce” In ana babbakan giwa wake ta kiyashi? Uwargidan banza da wofi. Ai ko Amarya ita ke da Gida. Ita ta yi farar haihuwa zaranta maza har guda uku ta haifa. Kin ga ita ce gidan ma gabaɗaya.”
“Ai kuma ba a nan take ba ai an take bodari ta kai.” > Janaftybaby: Ashe ta mayar mata da martani Hadiza ta karɓa da cewa” Ko goma Amarya za ta zo ta haifa sai sun jira domin za su kira wasu yaya da Anty suma za a kira su yanzu kafin baya.”
Tun muna ganin abin cikin wasa har aka koma jefa ma juna mganganu cikin zafi. Sai na mike ina yi ma Munnira magana akan ta yi shuru.
“In yi shuru! Daga magana na ga yarinyar nan za ta yi mini rashin kunya. Ba ta sanni ba ne ko?
“Da aurena da yayana ki kirani yarinya dan sake tunani dai baiwar Allah.”
Maryama ta faɗa har tana tafawa hannuwa Gimbiyar na yi mata magana ta fara masifa tana faɗin” Ina ruwan su damu daga saka waka sai su shigo suna neman gaya mana mgana! Wa ke tsoron su?
“Na ce dai ki yi shuru ko?
Ta tsawarta mata.
“To abun na su ne kamar da gayya Anty Gimbiya.”
In ji Halima ni wallahi ban ma ganta ba sai yanzu ina tunanin ko yanzu ta zo, ko kuma ta zo da safe ta je gida ta dawo.
“E mana da gayya ne. Tawagan uwargida ne ta bakin su, to wallahi mata ba ta isa ta watsa mana taro ba sai dai mu watse ta”
“Ke ai kin yi kaɗan ki watse mu Maryama sai dai ke mu watse ki wallahi. “
Ashe ta shige tsakanin Munnira da Maryama tana faɗin haka.
“Anty Munnira bar mini wannan faɗan koma gefe ki yi kallo”
Ta matsar da Munnira gefe tana nuna Maryama da yatsa kafin ta ce” Maryama karyan iskanci kike yi. Ni ce nan daidai da kugun ki wallahi “
Kawai sai ta saka hannu ta kabar da hannun Ashe tana faɗin” Ke Ashe kin sanni na san ki. Faɗan nan ba naki ba ne amma tun da kin shiga saboda yayarki Hauwa na ƙawar matar can mu zuba da ni da ke shege ka fasa.”
Ta faɗa tana shan gaban Ashe har tana ture ta baya. Abu kamar wasa wasa ashe na gaske ne ni ina gefe rike da Yumna ina ta ma Munnira mganar su bari domin har da ita maryama na magana tana ma yar mata ita da Ashe har da Halima. Hauwa ma da wasu yan Rano suka je suna jan Ashe amma ta ce tun da rigima Maryama take so to ta tare shi ta same shi a wajen ta.
Gimbiya ma da ƴan’uwanta suna ta yi ma Maryam ɗin magana amma ba su ji ba.
Irin su Halima yan kan zagi suna faɗin daman da gayya ne.
Ga shi ba wasu manya Anty Bahijja ta tafi Anty Maimuna daman ba ta zo ba. Naja ce ta shiga tsakiyar su ta raba domin kaɗan ya rage afara kai ma juna duka.
“Miye haka? Daga suna na farinciki sai kuma ku ma yar mana da taro na tsiya.?
Ta faɗa cikin bacin rai kafin ta kalli Munnira tana faɗin” Anty Munni wannan ba girman ki ba ne don Allah ki ja tawagarki ku koma gefe domin a samu zaman lafiya.”
Munnira kuma ta ce sun yi kaɗan daga abin arziki sai a nemi a ce sune suka zo da fitina.
Karaf wata ƙawar Gimbiya ta ce” Kune mana. Ina ruwan ki da waƙar da aka saka na uwargida ko na Amarya. Maganar gaskiya ku ne ba kwa son zaman lafiya. Ko kuma daman domin ku lalata mana suna kuka zo.”
Munnira ta yi shewa ta dire da cewa an lalata su yi wani abun mana. Suwaiba na yi ma magana ita na samu ta jawo hannun Munnira amma sai Maryama ta ja tsiyar da cewa” Abin da ya kawo su kenan mana. Ga munafukar can ita ce ta turo su ita kuma ta koma gefe ta bakam kamar ba ta san me ke faruwa ba. Anty Gimbiya ki faɗa ma Kishiyarki ta ja tawagarta ta bar gidan nan kafin raina ya ɓaci a yi ɓaattaciya”
Maganar ta ba ni mamaki, sai kallo ya koma kaina duk sai na ji na muzanta. Naja ta zo gabana tana faɗin” Don Allah Anty Sadiya ki yi musu mgana su daina.”
“Na yi musu magana mana Naja ko ba ki gani ba ne? Ni zan ce su zo suna ne su yi rigima da wata? Ku yi mini adalci mana”
“Ba wani adalci, ke ce munafukar da man tun da kika zo kika ga abubuwa sun tafi daidai kishin ki ya motsa ba haka aka so wai ƙanin miji yafi miji kyau.”
Maryama ta faɗa tana wani girgiza jiki, sannan ta nuna Munnira da su Hauwa tana faɗin” Saboda baƙinciki sai ki ka yi amfani da waɗanan yan koren naki domin su wargazamana taro. To daga ke har su ba ku isa ba. Sai dai mu mu wargazaku mu kore ku tun da ba zaman lafiya ya kawo ku ba.”
Baki na saki ina kallonta kafin in nuna kaina ina faɗin” Da ni kike? > Janaftybaby: “Akwai wata munnafukar ce bayan ke. Kin ga Anty Gimbiya na ta farar haihuwa. Bakin cikin ki ya kasa boyuwa sai da kika bayyana. To sai dai ki mutu aamma gida ya zama namu haka ma Yaya Tafidan shima namu ne sai mun ga dama mu ba da aron shi.”
Maryama ta ba ni amsa ba tsoro ko tunanin wani. Kafafuwata suka fara rawa saboda ɓacin rai har ni na yi lalacewan da ƙanwar Gimbiya za ta ci zarafina. Yarinyar da ko Amina ta girme meta. Marwa ke rike ni tana cewa na yi haƙuri kar na tanka Suwaiba kuma tana yi ma Gimbiya mgana ta ja ma ƙanwarta kunne manganganunta suna tsauri da yawa.
“Me zan ce Anty Suwaiba? Ni ba zan hana ta ba domin duk abin da ta faɗa gsskiya. Taro na suka zo su watsa kuma sun ji daɗi.’
Kawai sai ta fashe da kuka munafunci, Munnira kuma ta fashe kawai sai ta dira kan ƙanwar Gimbiya ta shaƙo tana faɗin karya take yi, ai sune ma za su ce kishi ne ke damun yayarta domin duk wani abun da ta yi a wannan taron Sadiya ta kwaikwaya mu ba mu ce tana baƙin ciki ba sai mu ne za ki ce muna bakin ciki? To mun watse taron in ta isa sai ta yi wani abu ko ta ɗau mataki.
Ni ban san me ta buɗe baki ta faɗa ba, sai ji kawai na yi kaya kaya an fara kai duka Munnira ta fara kai ma Maryama Mari, ita kuma ta rama kawai sai suka fara dambe na ruɗe ina kiran sunan Munnira.
“Haba Munnira ba girman ki ba ne faɗa da wannan yarinyar.”
Hauwa ta fada har da ni a masu rabo Yumna wajen Marwa na bar ta,ƴan’uwansu na Rano suna ta faɗa suka ce ga mota can ta dawo ɗaukan su za su wuce ba za su iya da masifa ba, da man yau za su koma, ita kuma Hadiza ganin ana faɗa da yayarta sai ta shiga suka yi ma Maryanma taron dangi suka kaita kasa. Gimbiya da Naja ganin haka suka shiga tsakani, wajen ƙokarin raba su Munnira idanuwanta ya rufe ta ture Gimbiya sai da ta faɗi gefe kusa da kujera hannunta ya bugu sai da ta yi ƙara. Kukanta ne ma ya raba faɗan sai kowa ya koma kanta Naja ta ɗaga ta irin kukan da Gimbiya ke yi ko dukanta aka yi sai kuka.
“Innalillahi shike nan sun karya ta burin su ya cika.”
In ji wata cikin kawayen Gimbiyar.
“A kira Yaya Tafida mana shi sai ya zo ya ganin ma idanuwansa matarsa da Tawaganta za su nakasa masa mata.”
In ji Halima, ni gabaɗaya kaina ya kulle ma, amma sai da na yi na Munnira masifa.
“Da wannan yarinyar ne zaki zo kina faɗa Munnira! Gaskiya wannan rashin sanin kimar kai ne “
Har ga Allah in na san abin da zai faru kenan da ban zo ba. Na ce su tattara mu tafi na je da niyyar na ba ma Gimbiya haƙuri ta juyar mini da kai tana faɗin” burin ki ya cika kin samu abin da kike so. Amma ki sani wallahi ba zan bar maganar nan haka ba.”
Sai na ga ma tsayawa magana kamar ɓata bakina zan yi kawai sai na wuce. Har Ashe da Halima sai da na yi ma faɗa. Muka rankayo gabaɗaya zuwa waje muna fitowa Salisu na sauke Baby sai na ce kawai su juya. Motar na ce Munnira da Hadiza su shiga ya kai su gida ni kuma na ɗauko Hauwa da Ashe, tun da tace can za ta kwana sai Marwa da nima a gidana ta ce za ta kwana.
Suwaiba na cikin gidan mun bar,ta tana ban haƙuri.
“Munnira ta goga mini baƙin fanti a dangin Yallabai. Yanzu ko rantsuwa na yi ba za a yarda ba ni na saka Munnira dambe da ƙanwar Gimbiya ba “
Na faɗa cikin damuwa. Ni na san abin da na ke hange da man yaya lafiyan kura ballantana ta yi zawo. An ce ina baƙin ciki saboda ban haifi namiji ba kalaman sun yi mini dafi a zuciyata.
“Gaskiya ba ta kyauta ba. Haba ke kuma Ashe wallahi sai na faɗa ma Mama. Yanzu Sadiya kuka bar ma abin mgana.”
Hauwa ta faɗa tana dungurar kan Ƙanwarta Ashe.
Tura baki ta yi kafin ta ce” Ni fa ban yi nadama ba. Ni Anty Munnira ma shigan sauri ta yi mini. Ni ce na so na yi ma Maryama bugun tsiya wallahi”
“Kuma bakin ki bai mutu ba ko?
Hauwa ta sake faɗa sai ta yi shuru ni kuma na ma kasa mgana hankalina ya tashi. Ba wai domin za a kira Yallaɓai ba sai domin ni ban je sunan nan da wata zuciya ba. Amma gashi abubuwa marasa daɗi sun faru Allah kaɗai ya san a yanayin da labarin nan zai fita. > Janaftybaby: Fuskata ba walwala na sauke su Hauwa a gida tana faɗa mini wai na kwantar da hankalina ko Yallaɓai ya zo zai fahimceni in na yi masa bayani kallonta kawai na yi. In har an so ya fahimcenin ba.
Mun koma gida muka iske Baby a ƙofar gida tana jiran mu ita da Salisun. Shi ya bude mini get na shiga da motata ciki.
“Umma me ya sa muka dawo! Ni ba zan je sunan Anty Gimbiyar ba ne?
Baby ta fara tare ni da mgana bayan na fito daga mota.
“Ni matsa ki ban waje kafin na gwabje ki.”
Na faɗa a fusace saboda ta ba ni haushi. Marwa ce ta ja ta gefe tana yi mata mgana ni kuma na wuce cikin gida. A falon Yallaɓai na samu matsugunni ina mai da numfashi, gabaɗaya sai na tsargu kaina, wallahi ban ji daɗi ba ba kuma a son raina abin da ya faru ya faru ba. Ina zaune su Marwa suka shigo ko kallon su ban yi ba na tashi jaka da mayafi a hannu na shige ciki ina ji Yunma na kuka tana Uma na yi banza da ita.
Kwanciya na yi a kan gado kawai na rasa mafita. Tunanin maganar da zan harhaɗa na kare kaima a wajen Yallaɓai na ke yi amma da kamar wuya. Tun da a san tare nake da Munnira Allah ne kaɗai zai iya fitar da ni, na kasa haƙuri sai na ɗauki waya na kira wayar Yallaɓai bai ɗauka ba har sau uku a raina na ce shike nan wayar na hannuna sai ga kiran Suwaiba da sauri na ɗaga kiran
“Suwaiba sun kira Yallaɓan ne?
“E ya ce gashi nan a hanya zai zo. Ni dai na gaji da ba ma Gimbiya hakuri na baro gidan gani ni da Mubeena za mu samu adaidaita.”
Ta amsa mini, sai na furzar da iskar bakina kafin na ce” Wallahi Suwaiba na kasa sukuni Allah ne kaɗai zai fidda ni a wannan sabgar.”
“Gaskiya. Domin Gimbiya sai kuka take yi shima jaririn na kuka. Ina jin hannun nan da ta bugu ta yi gocewa ko targaɗe. Allah kaɗai ya san mganganun da za su faɗa masa in ya zo. Halima can na barta tana ta faɗin duk abin da ya faru da gayya ne ke ce kika shirya komai.”
“Uhm”
Kawai na iya faɗa na kashe wayar. Daman ai ba ta kaunata tun marin da na yi mata na kore ta a gidana ni na san tana neman ranar ɗaukan fansa a wajena sai yau ta samu dama ai sai ta yi amfani da damarta da kyau da kyau.
Ina nan zaune Yallaɓai bai kirani ba har aka fara kiran sallar mangariba. Daga Marwa har Baby ba su neme ni ba nima ban nemi kowa ba. Tiolet na faɗa na yo alwala na so na ta yar da salla. Ina cikin yin salla na ji shigowar motar Yallaɓai da ƙaran buɗe get sai da gabana ya faɗi. Ya shigo falon farko ina tahiyar ƙarshe ina jin sa yana kirana suna da karfi daga ji ran shi a ɓace ya ke.
“Sadiya”
“Sadiya”
Ban zan iya sanin ko na ƙarishe salatin Annabi ba, na sallame salla, da hijabin jikina na fito daga bedroom na buɗe kofa na fito korido shima ya buɗe ta falo ya fito sai muka haɗe.
“Na’am. Ina salla ne lokacin da ka shigo.”
“Me Daughter ta yi miki da za ki kwashi mutane ku je ku dake ta ita da ƙanwarta?
Baki na buɗe ina kallon Yallabai yadda ya yi mini tambayar a kausaahe alamun tabbaci ma gare shi ba hasashe ba. Sai na ma kasa mgana har na buɗe bakina sai kuma na yi shuru kawai.
“Ba da ke nake magana ba kin yi mini shuru kamar wani ɗan iska?
Ya faɗa yana mai yi mini ihu a saman kaina. Kawai sai na ɗaga ido ina mai ƙara kallonsa kafin na ce” Ni ban kwashi mutane su je su dake ta ba. Wa ya ce maka an dake ta? Ni dai na san Munnira sun yi faɗa da kanwarta ta shigo rabo ba ta sani ba ta ture ta shike nan abin da na sani. Kuma ni har ga Allah ba da yawuna Munnira ta yi abin da ta yi ba. Ni da hankalina zan kwashi mutane aje a yi tashin hankali? Me matarka ta yi mini da zafi da zan yi mata haka?
“Wa ya sanin miki. Duk abin da ya faru kina sane saboda ai su Munniran da Hauwa tare da ke suke. In kika tsawarta musu ai za su bari amma da ya ke kema akwai mugun nufi a ranki. Shi ya sa kika yi shuru sai da abu ya faru za ki zo kina faɗamini wai mai matata ta yi miki da zafi? Kika san abin da ta yi miki domin ni ba makaho ba ne tun haihuwan nan na ga take-taken ki, ko barka sai da na yi ta miki magana kika je, asibiti ma ba ki je kin duba ta ba sai da ta koma gida da na yi magana sai ki ce ba ki da lafiya. To duk na gama gano ki. Kin kuma kyauta da abin da kika yi. > Janaftybaby: Saboda ke an targaɗa mini mata a banza a wofi na gode Sadiya kin ji ko? Na ce Na gode.”
Ya faɗa cikin hargagi har yana yarfa hannu. Marwa da Baby suka fito da sauri daga dakin su Jidda suka gan mu cirko cirko ni da Yallabai.
“Ni ce mai mugun nufi a raina?. Ni Yusuf?
Na faɗa ina nuna kaina cikin tarim mamakinsa.
“E ke ce fa, kuma kin aiwatar da nufin ki, kin kyauta. Amma ki sani ba ita kika yi ma wannan tozarcin ba illa ni. In ma kin ji hauahi tana ta haihuwan Maza ni ba ki yi mini adalci ba. Domin na shafa faɗa miki da mazan da matan duk ɗaya ne a wajena me ya sa ba za ki yi mini kara Sadiya ki boye kishin ki ba? Abin da kika yi dai dai ne? Abin da kika yi sunan shi ne zubar da ƙima. Watarana in Saudatu ta gan ki ba ta darajaki ba. Juzt bleme your self domin ke kika zubar da girmanki, ta bi kuma ta tattaka shi.”
Wai Yallaɓai har yana nuna mini hannu yana gaggaya mini magana ina kallon shi kwarmin idanuwana suna cika da kwallah.
“Na ɗauka in ina da wani mugun nufi tun a shekaran baya zaka sani ba yanzu ba.”
“Da ba ki da shi. Yanzu kika ɓullo da sabbin hallaya marasa kyau. Kin bari sheɗan na zugaki. Tare da su waɗanda kika rike a naki. Na daɗe da sanin saboda ke su Hauwa ba sa zumumci da Daughter amma ban taɓa magana ba. Kuma a adalci ai dake da ita duk ɗaya ne yadda za su yi miki haka za su yi mata. Duk na share wannan ban taba magana ba sai abu ya zo har da duka har gidan ta? To ba ki isa ba yadda kema ban kyaleki ba suma ba zan ƙyale su ba na kira Nasir da Mutaƙƙa kowannen su zai ja ma matarsa kunne. In dai ba za su dauke ki ɗaya da Matata ba to sai dai a raba wannan alaqar taku gabaɗaya tun da ba ta alheri ba ce sai ta sharri.”
Ai ban san na kwashe da dariya ba, sai da na ga na yi ta cikin takaici da bakin ciki hawayen da suka zubo mini na share ina kallon Yallaɓai ido cikin ido kafin na ce”Wannan kuma wallahi ta yi kaɗan. Lokacin da tazo tare ta ganmu kuma wallahi tare za ta bar mu. Zama daram in ji mai naguda.”
Na faɗa ina mai riƙe kuguna. Domin na lura an gama shiryaa mai mganganu ni zai zo ya tara mini gajiya to wallahi bai isa ba.
“Ni kike faɗa ma haka Sadiya?
“An faɗa maka sai me? Kai waye? Mijina!
Na yi wata bazawar dariya kafin na nuna shi ina faɗin” Mijina ne kai da muka yi zaman aure na shekari sama da ashirin ashe kai ba za ka iya sanin abin da zan iyawa aikatawa da wanda ba zan iya aikatawa ba? Wato duk abin da matarka da danginta suka faɗa akaina shi ne gaskiya a wajenka ko? To bari ka ji na faɗa maka ko na ce na ƙara tunasar dakai ko garke Gimbiya za ta haifa maka na Maza wallahi ko a gefen gyalena da yau ban haihu ba da bakin ciki ya kashe ni. Maganar zuwa barka ban yi niyya zuwa ba ne, duk ita a nata haihuwan ka fahimci ni ban je ba amma a lokacin da na haifi Yunma ba ka fahimci sai da ta ga dama ta zo ba? Ita ka same ta ka yi mata mgana kamar yadda ka yi mini? Wato sai ni ce marainiyar ka dole ka zo ka same ni ka sauke mini magana. To bari ka ji na rantse da wanda raina ke hanun shi ina dai dai dakai daga kai har munafukar matar taka.”
“Sadiya.”
“Yusuf”
Yadda ya kira sunana cikin tsawa nima haka na buɗe murya na kira sunan shi yana huci ina huci.
Sai kukan Yumna muka ji, can sai na Baby ko ni juyawa ban yi ba shine ya juya yana kallon su yara sun ga abin da ba su taba gani ba.
“Marwa ki ja yaran nan ku koma ciiki.”
Ya faɗa yana sassauta muryan shi,
“A shiga da su ciki kuma? Daga baya kenan wai an yi sadaka da bazaawara. Ai sun gama ganin ka, kana ci ma uwarsu zarafi a kan wata banza a banza.’
Na faɗa ina haki saboda ɓacin rai.
“Kar ƙi kara ce mata Banza.”
“Na ce banza a banza Yusuf don Allah ka dauki mataki in ka isa.”
Na faɗa ina isa gaban shi na tsaya ina riƙe kuguna.
“Da gaske banza ce tun da ba ta iya ramin kanta sai dai na wani. Kuma wallahi tallahi ba ta isa na amsa laifin da ban aikata ba. Rashin kunya ba irin wacce ƙanwarta ba ta yi mini ba shi ba a faɗa maka ba sai gulma da munafunci?
Na faɗa ina zare masa ido.
“Ki matsa daga gabana kafin raina ya ɓaci na yi miki abin da ba ki yi tunani ba Sadiya.” > Janaftybaby: Ya ɗan fara saukowa tun da ya daina ɗaga murya ko saboda yara ne oho. Marwa ta ja su sun koma ciki amma har lokacin ana jiyo kukan su.
“Me zaka yi! Na ce Yusuf me za ka yi?
Na faɗa ina ƙara ɗaga murya ni fa tun da ya jawo wannan faɗan to gwara a yi shi kawai kowa ya san matsayin shi.
“Ƙina so ki ga abin da zan yi ne ?
“E. Ina so na gani. “
Sai ya wani nuna kanshi kafin ya ce” Ni kike tsarewa cikin gadara kina faɗin na ɗau mataki akan sadiya?
“E sai me? Tsoron me zan ji? Ƙarshen mataki kenan ka ce ka sake ni ko Yusuf? To ai ba ƙarewar rayuwata ba ce ta zo in na rabu dakai ba sai me.’
Kawai sai ya tsaya yana kallona nima ko ina kallon shi ido cikin ido.
“Yau yanzu ka ce na fice maka a gida zan fita. Tun da daman ka ce ba gidan Ubana ba ne.”
“To ki tafin ma who stop you? Na hana ki tafiya? The door is open Sadiya. A sauka lafiya.”
Ya faɗa yana nuna mini ƙofar falo. Na razana da kalamansa amma ina zuciyata ta ƙekashi ban nuna masa na razana ba, kawai sai na yi mirmishi kafin na ce” Da a ce yau Sulaiman Yashe bai da gida da na sha wulaƙanci.”
Ba ni da kuɗi a jikina daga ni sai hijabin salla na amma ina ganin in na koma ciki zai ga kamar na gaza ne. Sai kawai na wuce har na isa kofa falon sai na juya ina kallonsa dafe da kai a kausshe na ce.
“Ni Sadiya ni yau Yusuf ka kora a gidan ka ko?
“Kin ce za ki tafi kina tunanin zan tsayar da ke ne? Ki sauka lafiya na ce Halimaaa.!
Ya ja sunan shima a kausaahe yana kallona ina kallon shi. Idanuwanshi sun kala nima nawa ya kala ya yi jajir sai kawai na buɗe kofar falon na fice ina jin Marwa ta biyo ni tana Umma Umma.
Sai a lokacin na tuna da ita a fusace na waiga ina faɗin” Ki dauki mayafinki mu bar masa gidan shi Marwa.”
“Umma..amm”
“Wallahi zan mare ki za ki taho mu tafi ne ko na yi tafiyata.”
“Zan zo.”
Ta fada tana zakuɗa goyon ta dake bayanta har ta fara hawaye.
Baby ta fito ita da Yumna ina jin Yallabai ya rike su yana mgana da su kasa kasa.
Marwa ta dauko mayafi ta fito na ji ta tsaya tana mgana da Yallaɓai a fusace na ce” Wai ke ubanki ne da za ki tsaya kina masa mgana?
Ki jira har sai ya kai ga haɗa ki da jami’an tsaro sannan sai ki bar masa gidan sa.”
Na ga ya buɗe kofar falon ya fito Yumna na hannun shi tana ganina ta fara Uma tana miƙan hannuna na juya zan fita Marwa dake bayana ta ce” Umma ko Yumna ba za ki tsaya ki karba ba!
“Ba da ita na zo ba. Saboda haka ba da ita zan koma ba.”
Baby ta rigo tana Umma Umma cikin kuka na tsayar da ita da hannu ina faɗin” Kar ma ki ƙariso ki koma nan ne gidan Ubanki nima gidan nawa Uban zan koma ya tattaraku ya kai ma Matar so ta haɗa da farar haihuwa duk ta riƙe “
“Sadiya.”
Ya kira ni a tsawa ce, ko kallon shi ban yi ba na fice daga falon ina jin kukan Baby da yadda Yumna ta yanka ihu. Ni kaina duk dauriyata sai da na ji hawaye sun kece mini. Wani abu ya tsaya mini kahon zuciya, wai ni ce yau Yallabai ya kora daga gidan shi. Lalle duniya juyi juyi na gaba ya koma baya.