Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    Lokaci bayan lokaci ina kiran Ma’u na ji yadda a ke ciki. Zamantakewarta da Alhajin nata dai sai a hankali, tun da ya yi niyyar auren nan sai ya yi ita kuma Ma’u rashin haƙurin ta ya sa duk ta zube a wajen shi. Shi fa daman Namiji haka yake. In suka tashi ƙara aure to ba sa ji ba sa gani ne in ba ka yi haƙuri ba to za ka yi nadama ko kuma ka ga a na yi. Kuma a yadda na lura ita Uwargidan Ma’u ta na yin komai da gayya ne saboda tura ma Ma’u haushi. Ko ramuwa ta ke yi wa ya sanin mata. Domin Ma’u ta yi lokacin ta yanzu ne alƙadarinta ya ƙarye take girban a bin da ta shuƙa.

    Ni dai haƙuri nake ba ta domin babu kamar haƙuri. Ba a yanzu za ta ga riban hakurin ba sai nan gaba. In dai za mu yi waya da Ma’u sai na ji ta cikin kuka Allah sarki wallahi tausayinta nake ji. Saboda ni na san zafin ƙishi, ga kuma ita abu ya haɗe mata biyu ga kishi ga ba zaman lafiya da miji. dole ta yi kuka, abin da ya ba ni mamaki cikin lokaci ƙankani wannan rashin jituwar dake tsakanina da Ma’u ya gushe. Har mantawa na ke yi da ba ma jituwa, ko ban kira ta abu kaɗan za ta kirani ta na faɗa mini ni kuma na yi ta ba ta hakuri domin shi ne kaɗai abin da zan iya faɗa mata. Sannan shawaran haƙuri na da zafi sai dai tana da riba a nan gaba.

    Tana kawo mini ƙorafin cewa ranar da ya ke gidanta kusan raba dare ya ke yi waya ko chart in ta yi magana sai ya ce ba ta isa ta hana shi yin waya ba. Na yi ta ce mata ta yi haƙuri ta ƙyale shi ta riƙa shigewa cikin ɗakin ta, ba ta ji ba ballanta hankalinta ya tashi tun da ta faɗa mini ba a ɗakinta ya ke wayar ba ko falo ko cikin Bedroom ɗin shi. Sannan ta ce ba ya mgana da ita ko gaishe shi ta yi da ƙyar ya ke amsawa. Ya kuma je can Kura ya karɓo yaran ya kai su gidan Uwargidan, da ita kawai ya ke shawara yanzu ita ce ke kitsa masa komai a kanta duk na ce ta kauda kanta daman yana yi ne saboda ta yi mgana to ta yi kamar ba ta ji ba kuma ba ta gani ba. Ni ko Yallaɓai ban taɓa masa mganar ba sai ranar ya na gida na ya ji muna waya duk da tashi na yi daga falon saboda sirrina bai kamata na yi wayar yana wajen ba.

    Sai da na dawo falon ne jin bai tambaye ni ba, na san halin shi Yallaɓai bai cika bin diddigi ba. Ni ce ma na faɗa masa Alhaji Mustapha zai ƙara aure. Kawai sai ya fashe da dariya ya na faɗin.”Ma sha Allah. Ta uku fa zai yi ko?
    Ya faɗa ya na kallona sai kawai na gyaɗa masa kai ban samu zarafin mgana ba.

    “Kai ya yi ƙoƙari da kyau. Gwara in kana da shi ka cike sunnar gabaɗaya.”

    Kawai sai na yi jagale ina kallon Yallaɓai har wani dariyan nishaɗi yake yi.

    “Yaushe ne bikin?

    “Ban sani ba.”

    Na faɗa ina tsumewa, sai ya sake kallona yana mini dariya. Haɗe rai na yi ina kauda kai kafin na ce” Yallaɓai ko kai ma kana shirin yo ta ukun ne?
    Sai ya kalleni kafin ya ce” To in Allah ya kaddara min zan ce ba na so ne?
    Har sai da na buɗe baki saboda mamakin sa. Ni fa daman tuni na sha jinin jikina Yallaɓai zai iya ƙara aure in ma bai cike ƙofa ba.

    “Kishi kike yi? Ba ki so na ƙara aure?

    Tsaki na so na ja amma sai na yi shi a ƙasan raina.

    “Ai ni ka gama mini kishiya Yallaɓai. Duk wacce za ta zo daga baya ba za ta ɗaga mini hankali ba.”

    “Ki ce wallahi.”

    Ya faɗa ya na mini dariya sai na ga ya mai da ni kamar wata shashasha. Hararan sa na yi, ban sake mgana ba.

    “Ki rantse in yanzu na ce zan ƙara aure ba za ki ji komai a ranki ba?

    “Ba zan ji ba. Ba kuma sai na rantse ba.”

    Kawai sai Yallaɓai ya ta so ya zo gabana ya durƙusa.

    “Ki ce wallahi ba za ki yi kishi ba.”

    Sai kawai na kalle shi, lura na yi maganar ma nishaɗi take saka shi.

    “Ba sai na rantse ba.”

    “To ƙarya ne. Ke ɗin ce ba za ki ki kishi ba?

    Ya faɗa har ya na jan mini kumatu, na ture hannunshi kafin na ce” Me ya sa zan yi kishi! Na faɗa maka ni ka ga mini kishiya. Yanzu ai tsakanin ka da Gimbiyar ka ne.”

    “Saboda kina sona Sadiya. Shi ya sa za ki ji kishi na.”

    Kamar zan yi mgana sai na fasa ganin ko na tanka ba zai bar maganar ba zai ta tsokana ne yana mini dariya sai kawai na kauda kaina ban yi magana ba. Cikina ya shafa kafin ya ce.

    “Bomboy fito ka ga mamanka sarkin kishi.” > Janaftybaby: Da dai ya ga ban kula shi ba sai ya koma wajen zaman shi daman aiki ya ke yi a cikin system ɗin shi ya baro ya zo jin ta baki ganin kuma na ɗaure fuska ya sa dole ya ƙyaleni a cewar s na zama jagwam magana ma masifa ce da faɗa a wajena. Saboda ma yadda ya yi ban samu faɗa masa matsalan Ma’u ba na kama kaina sanin ina ma faɗa masa sai ya ce laifinta ne tun da Namiji ne, ba zai ga laifin ɗan’uwansa ba.

    Mun yi waya da Ma’u kwana biyu ranar wata laraba Yallaɓai ma ba gidana yake ba, misalin tara na dare sai ga Ma’u a gidana afujajan cikin kuka sai da na ji gabaɗaya hankalina ya ɗaga, Yallaɓai ya fita kenan ya zo yi mana sallama ina tunanin ko gida bai kai ba lokacin da ta zo. Ɗaki na ja ta cikin tashin hankalin ina tambayan ta ko lafiya na girgiza da take faɗa mini Alhaji Mustapha ne ya ce ta bar masa gidansa ya sake ta saki ɗaya. Sannan lamarin bai tsaya a nan ba sai da ya haɗa mata da mari gabaɗaya farar fuskarta gefen hagu ya ta sa da shatin hannunsa.

    “Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un har da mari?

    Na faɗa ina cikin matsanancin tashin hankali.
    Ma’u ko kuka kawai take yi ta ma kasa mgana gabaɗaya sai na ji ƙafafuwana sun yi sanyi. Cikin jikina sai da na ji ya cire waje ɗaya ya motsa saboda tashin hankali.

    “Me kika yi masa da zafi haka Ma’u?

    Na faɗa ina mai dafa kafaɗanta cikin yanayina na damuwa. Da ƙyar na samu ta tsaigata da kukan nata ta yi mini bayani da cewa yau a gidanta ya ke yi jiya ma haka to a cewarta jiya sai wajen sha ɗaya ya shigo gidan kuma ya yi shigewarsa ɗakin sa ko da ta shiga yana ta waya haushi ya sa ta fita ta bar masa ɗakin shi ne yau da ya dawo ya shiga ɗakinta a kan gadon ta yana waya da budurwansa ita kuma ranta ya ɓaci ta fizge wayar ta haɗa da bango ta fashe shi ne ya kifa mata mari, ita kuma ranta ya ɓaci ta yi ta faɗin mganganu shima yana faɗa daga ƙarshe ya ce ta bar masa gida ya saketa saki ɗaya.

    “Innalillahi Ma’u me ya aike ki? Me ya sa kika biye masa?

    “Haba Sadiya a kan gadona na sunna zai kwanta yama yi mini waya da budurwa na yi magana yana ce mini ai ba budurwa ba ce matarsa ce tun da saura wata ɗaya auren su. Ni kuma raina ya ɓaci na fasa wayar shi ne ya mare ni. Sadiya bai ishe shi ba har sai da ya ce ya sake ni, ni fa wai Alhaji ya saka ni fa Ma’u”

    Ta faɗa cikin gunjin kuka gabaɗaya sai na ji kaina ya sara. Ba ni a ka saka ba amma na ji sakin nan a raina. A raina ina tunanin yadda Alhaji Mustapa ke son Ma’u ya na ririta yau ita ce ya sake ta saboda wata mace. Macen ma da bai aure ta ba. Lalle duniya juyi juyi na gaba ya koma baya. Lallashinta nake yi amma ni kaina na rasa kalaman bakina, lamarin ya dake ni, na ji abun a cikin raina na rasa yadda zan yi da Ma’u kuka kawai take lamarin akwai cin rai da baƙin ciki namiji ya sake ka saboda wata mace macen ma ba ta ma shigo gidan ba, to in ta shigo kenan sai abin da ya yi gaba.

    Ni kaina kamar in yi kuka idanuwana har sun kaɗa hawaye sun tarun mini a ƙwarmin idanuwana, abin da Alhaji Mustapha ya yi zalinci ne kuma rashin adalci ne a kan gadon aurenta? Tsakani ga Allah ya kyauta kenan, sai na fahimci so kawai yake yi daman ya ga yadda Ma’un za ta yi ne. Duk yadda na ke cewa ta yi hakuri sai na ji hakan da ta yi ta ni a wajena dai-dai ta yi ta kuma san mutumcinta amma marin ne da ta bari a ka yi shi ne kuskurenta sannan me ya sa ta fasa ma sa waya? Da da ta yi masa magana bai ji ba sai ta bar masa ɗakin duk tsiya dai ba kwana zai yi ai ya na wayar ba. Kai gabaɗaya na girgiza da lamarin nan jikina ya yi sanyi matuƙa har na gaza wajen lallashin Ma’u.

    Na bar Ma’u a ciki na fito falo Baby ta yi barci Jidda ce kaɗai ba ta yi barci ba. Amma na kora ta ɗaki daman tana falon su tana karatu ne. Jidda fa ba ta yarda ta yi zaman gida a banza ba ko da yaushe cikin duba littafanta na makaranta take yi. Na zauna na rasa mafita wa zan kira a daran nan? Har na yi tunanin kiran Ya Aina sai na fasa in na yi tunanin Ɗorayi sai na ji gwiwata ta yi sanyi. > Janaftybaby: Duk wanda zan kira yanzu wataƙila ma sun kai ga kwanciya kar na ɗaga musu hankali, Yallaɓai na ji shawaran na kira shi ya kwanta mini a zuciyata har na ciro wayar a chaji zan kira shi sai na fasa tuna yana gidan Gimbiya bai da ce na kira shi ba, ko ba domin komai ba akwai sirrin da ba na so ta ji, shawaran na tsayar ni da zuciyata a kan da safe sai na kira shi, da haka na koma ciki na samu Ma’u har lokacin na dirjan kuka nan fa na zauna ina ta ba ta haƙuri na san lamarin akwai ciwo amma ta yi hakuri zuwa da safe sai mu ga yadda za mu yi ta koma gidan mijinta.

    “Ba zan koma ba Sadiya. Allah na gama zama da shi tun da har ni zai wulaƙanta a kan wata macen da bai aura ba.”

    “A’a Ma’u ba za a yi haka ba. Za ki koma gidan ki. In ba ki koma ba ta vi riba kenan kin bari wata macen da ba ta ma shigo ba ta kore ki daga gidan mijin ki da ƴaƴanki.”
    Na gama faɗa ina bubbuga bayanta alamun lallashi.

    “Duk ma abin da ya faru ai shi ya so haka Sadiya. Tun da ya ɗauko maganar auren nan ba irin cin kashin da Alhaji bai yi mini ina ta kauda kai ba saboda kin ce na yi haƙuri amma yau ya kureni har da mari fa? Sannan ya ce mini ya sake ni na bar masa gida. Ni Ma’u ni ce wai namiji ya sake ni kuma ya yi mini koran wulaƙanci?

    Sai ta sake fashewa da kuka tabbas an yi mata tozarci duk da dai shima ina tunanin cikin ɓacin rai ya yi saki amma dai abin da ya yi bai kyautu ba, a yadda na ke jin zuciyata in ni ce ka yi ma wannan tozarci wallahi ba ma zan tsaya a kusa ba tafiya zan yi in da sai ka fara kuka kafin na dawo. Ni a tunanina ko na ce a hange na saki shi ne ƙarshen tozarcin da namiji zai yi ma mace saboda zai ƙara aure.

    Amma ba zan ce Ma’u kar ta koma gidan ta ba, sulhu a ke nema, gidan ta daban nawa gidan dabam haka zalika, zuciyarmu ba iri ɗaya ba ne amma ni kam ba zan zauna ka mare ni ka mari banza ba, duk da haka tun da ta zo wajena da kukanta sai na tabbatar da an ƙwatar mata yancin ta. Tuni Alhajin ya zube min a idona ina ganinsa da ɗan kima a baya amma a daran na ji gabaɗaya na daina mutumtata shi.

    Mun kai har wajen misalin biyun dare ina ba ma Ma’u baki a ɗakina mu ka kwana ni da ita saboda na ga ba ta ma cikin natsuwarta. Tana fashin salla ai da na saka ta mun yi tsayuwar dare a kan Alhaji Mustapha amma ni sai da na yi raka’a biyu sannan na kwanta. Duk da nauyin cikina amma ina ƙoƙarin yin salololin dare tun da na riga na saba. Ina da tabbacin Ma’u ba ta samu barci a daren ba duk lokacin da zan farka idanuwanta biyu. Baiwar Allah ta ba ni tausayi ni ma ai na shiga haka a baya kuma na san yadda mutun ke ji a zuciyarsa. Na so na zauna nima ban yi barci ba na ta ya ta jimami da ban baki amma ina barci ɓarawo sai da ya sace ni sai asuba na farka har ma mun kusa makara. Ina idar da salla na fita zuwa ɗakin su Jidda ganin Ma’u ta samu barci can na je muka yi azkar da karatun Qur’ani sai bakwai saura na baro ɗakin na bar su su ɗan ƙara runtsawa tun da ba zuwa makaranta yanzu mun kan kai sha ɗaya ma ba mu tashi ba in ba Yallabai na gidan ba ne in zai fita da wuri.

    Falo na dawo na cire waya ta a chaji ta daɗe da cika tun jiya amma na manta ban cire ba. Yallabai na kira sai da ta shiga ma na ga kamar ya yi safe da yawa ina ma wannan tunanin na ji ya ɗaga wayar a muryansa na fahimci kamar ya na barci ne na tashe shi.

    “Sadiya me ya faru?

    Ya faɗa da sauri Allah sarki bawan Allah shi ma hankalin shi ya tashi ganin kirana a wannan lokacin. Ina da ciki fargabansa kar ya zo wani abu ne ya faru mara daɗi.

    “Ka kwantar da hankalin ka bakomai.”

    Na faɗa cikin kwantar da murya ina jin ajiyar zuciyarsa.

    “To ina kwana? Wallahi na tsorata da na ga kiran ki, “

    Saboda ya san ni ba mai damun sa da waya ba ne in har ya na can gidan, in kuma ya ga na kira to ba lafiya.

    “Kai kaɗai ne a in da kake?

    Na tambaye shi sai ya ce shi kaɗai Gimbiya ta can ɗakin yara.

    “Me ya faru ne?

    Ya sake tambaya kamar bai yarda da cewa wani abu bai faru ba.”

    “Jiya ne bayan fitan ka sai ga Ma’u ta zo mini cikin kuka Alhaji Mustapha ya sake ta.”

    “Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un wani irin saki kuma?

    “To ai har da marin ta ma ya yi Yallaɓai”

    “Mari? > Janaftybaby: Ya maimaita cikin sigan tambaya.

    “Ƙwarai kuma ya ce ta bar masa gidan sa a daran”

    “Subhanallah me ya faru a tsakanin su haka?

    “Ka taho gida in ba damuwa yanzu sai mu yi mganar.”

    Nan da nan ya ce min gashi nan zuwa. Bayan mun kashe wayar na zauna kawai ina tunani rayuwa kenan
    Yau wai ni ce Ma’u ta zo mini da matsalanta, yau ina su Ya Murja ina su Anty Bahijjan ina su Shema’u? Yau duk ba za su yi mata amfani ba dole dolenta dai jininta ne zai yi mata wani anfanin da a da take ganin ni ban isa ba, kuma yadda ta zo ta faɗa mini wallahi sai Alhaji Mustapha ya roƙi gafaran Ma’u a kan wannan cin zarafin da ya yi mata. Zuciya ta sai ta fara zafi ina cin wani raɗadi daga ƙasan zuciyata kamar ni a ka yi mawa, na yadda akwai jinin Ma’u a jinina shi ya sa yake motsawa a kan ta in wani abu ya same ta.

    Ina nan zaune a falon su Jidda sama da mintina arba’in har Yallaɓai ya shigo gidan. Shima dai ya nuna damuwarsa a saman fuskarsa na zauna na zayyana masa duk abin da ya faru na ƙarishe da faɗin” Tun jiya da ta zo ta ke kuka. Ta ce ba za ta koma ba tun da ya tozarta ta, ba ta yi barci sai da safen nan ba ka ganta ba gwanin ban tausayi.”

    “Gaskiya bai kyauta ba. Haba da hankalin shi me ya sa zai yi haka?

    Yallaɓai ya faɗa kai tsaye, shi ma ai ya san gaskiya kowa kuma ya ji wannan mganar sai ya ce bai kyauta ba.

    “Kuma a kan gaskiyanta ta yi mgana. A kan gadon ta fa ya je yana yin waya shi ne ta yi mgana ya yi mata wannan wulaƙanci.”

    Na faɗa cikin bayyana jin haushina.

    “Shi ya sa na ce miki bai kyauta ba. Ya kuma nuna ko auren ya yi ba zai yi adalci ba. In ba wawanci ba me ya sa za ka zo cikin gida kan gadon ku na sunna kana waya da wata macen da ba ka riga ka aura ba, kenan itama ka nuna mata matar ka ba ta da daraja a wajen ka in ta shigo gidan za ta iya taka ta yadda ta ga dama tun da kai ka ba ta damar haka.’

    “Gaskiyan mgana kenan”

    Na faɗa ina kallon Yallaɓai ina mirmishi. Shi ya sa na ke son Yallaɓai ta wanni fanni akwai shi da faɗin gaskiya komai ɗacin ta.

    “Ita kuma rashin kyautawarta ɗaya ne me ya sa ta fasa masa waya? Da ta yi masa magana bai ji ba da ta ƙyale shi ta bar masa ɗaki in ta yi haƙuri zai wuce har kuma wata rana ya dawo ya na jin kunya. “

    Duk abin da Yallaɓai ya faɗa gaskiya ne, nan na zauna ina faɗa masa wasu abubuwan da suka faru a baya ya jinjina kai yana faɗin” Duk laifin shi ne a matsayin shi na magidanci bai zama adali ba, ai ba a ce in za ka ƙara aure ka tozarta matarka ta gida ba. Ita kuma in ta nuna damuwarta ba ta yi laifi ba mijinta ne zai ƙara aure kuma tana dai-dai da ta nuna kishinta afili sai dai kuskurenta ɗaya me ya sa ba ta yi kishin cikin ilimi ba? Ta yi kishin da ta ta yar ma da mijinta hankalinshi kuma ganin tana kishin ne ya sa ya ke yi duk abin da ya yi, in da a ce ta yi masa kamar ba ta san yana yi ba da tuni ba ta kai su ga haka ba. Ta yi koyi da ke mana? Na san kina kishi na amma kishin mummuƙe kika yi mini sai da na dawo ina jin kuyar ki cikin ruwan sanyi kika saka na gane ba ni da wayau”

    Ya ƙarishe faɗa yana kallona yadda na ga bai yi dariya ba ne na ga ne ba wasa yake yi ba. Sai da na harare shi sannan ya yi mini mirmishi yana faɗin ai gaskiya ne kishin mata masu Aji kenan a gasa namiji ta ruwan sanyi da zai zo ya na ba da haƙuri da kan shi, shuru na yi ban yi magana ba domin ni kaina ai ya gasa min aya a hannu kawai dai ana kauda kai ne a zamantakewa.
    Mun tattauna dashi sosai daga karshe ya ce mu karya sai mu tafi tare da shi har da Ma’un nan kuma take ya kira Alhajin Mutspha ya ce za mu taho gidan Ma’u nan ba daɗewa ba ko kunya ya na faɗa ma Yallabai sun samu matsala jiya ba ta kwana a gidan ba Yallaɓai ya ce ya sani gidan sa ta kwana tare ma za mu taho ya ce yana gidan Hajiya Zainab amma zai taho nan gidan Ma’u yanzu.

    “Ka ji min munafuki wato saboda ita Hajiyar ta san Ma’u ba ta nan shi ya sa ya je can ya kwana.”

    Na fada cikin jin haushi tun da duk na ji wayar na su a speaker ya saka wayar lokacin da ya kira shi.

    “To mi ye laifin shi? Matan ahi biyu bai kamata ya yi kwanan gauro ba.” > Janaftybaby: Wata uwar harara na jefi Yallaɓai dashi sai ya fara mini dariya ya na faɗin” Daga magana? Yi hakuri ba ni na kai zomin ba rataya kawai a ka ba ni.”
    Saboda haushi ban tanka shi ba yanzu yanzu ya na maganar kamar zai yi gaskiya a lamarin shin amma kuma yanzu ya na so ya yi son kai a lamarin shi.

    Tare da shi muka dafa ruwan zafi shi ya ma soya ƙwai, ba buredi sai ya fita ya siyo, kafin ya dawo Ma’u ta tashi na saka ma ruwan a hiter ya yi zafi na ce ta yi wanka mu karya Yallaɓai ya zo za mu tafi can gidan na ta gabaɗaya.
    Sai da ta yi wanka nima na yi, kaya na bata ta saka nima na zurma doguwar rigata mai kama da buhu ta bakin Yallaɓai bujun bujun ga cikina gaba ina tafiya a tale, Yallaɓai na falo can na je na same shi muka karya ita Ma’u ciki na kai mata na ta saboda ta samu sakewa. Sai da za mu tafi na ta da su Jidda suna ta barci na ce mata za mu fita ta yi musu wani abu su karya dashi ita da Baby in kuma za su sha Tea ne dai ga su ga gidan nan mu mun fita zuwa gidan Umman su Ma’u.

    Yallaɓai ya ɗauke mu a motar shi, sai da muka ɗau hanya ne suka ƙara gaisawa da Ma’u ya na ba ta haƙuri sai ta fashe da kuka ta na faɗin” Baban su Jidda sakina fa ya yi a kan wata macen?

    “Ki yi haƙuri ya yi kuskure kuma zan faɗa masa.”

    “Kuma wallahi sai ya biya ta marin ta da ya yi.”

    Na faɗa a fusace, sai Yallabai ya kalleni kafin ya ce”To ya biya ta, ko rama marin na ta za ta yi?

    “In ta kama ba”

    Sai Yallaɓai ya girgiza kai hankalin shi na wajen tuƙi ya ce” Ma’u kar ki biye ma wannan ƴar’uwan ta ki, a kusa ta ke kin dai gane”
    “Ba wani a kusa na ke sai gaskiya ai ba zai mari banza ba.”
    “To na ji bai mari banza ba, daman ai ya san bai kyauta ba kuma ina da tabbacin yanzu haka ya yi nadama.”

    “Daga baya kenan an yi sadaka da bazawara.”

    Har Ma’u sai da ta yi dariya shi ko Yallaɓai kallona kawai ya ke yi yaa girgiza kai ganin yadda na haƙiƙance.

    “To ni dai ki yi haƙuri kar mu je sulhu ki ɓata ma lamarin.”

    Na harari Yallaɓai ina faɗin” In dai har ina wajen sai na yi magana in kuma ba ka son hakan ta faru sai dai ka sauke ni na koma gida tun da ba ka son na faɗi gaskiya.”
    Na faɗa ina murguɗa masa baki ai sai ya yi shuru bai ƙara mgana ba, ko da muka isa gidan Alhajin na Ma’u bai iso ba sai da muka shiga muka jira shi.

    Lokacin da ya zo har ya yi wanka ya ba za shadda na maiƙo har da babban riga a raina na ce kuɗi masu gidan rana duk su suke saka shi wani jin kai da ganin zai iya yin komai. Da ƙyar na gaishe shi saboda ina jin haushin shi a nan falon Ma’u muka zauna shi Yallaɓai ya fara ba ma dama ya maimaita magana sai kame kame yake yi, wai ta raina shi tun da ya ce zai ƙara aure taƙi kwantar da hankalinta ta sauya ta na abubuwa waɗanda ba halinta ba har ya na cewa wai haƙuri ya ke yi da ita sai jiya ta ƙure shi, shi kuma ran shi ya ɓaci har ya mare ta kuma ya furta sakin amma a jiyan bayan ta fita har bayan ta ya bi bai ganta ba kuma a jiyan ya janye sakin ya mai da ɗakin ta

    Kallonsa nake yi a ƙasa ƙasa ina taɓe baki, ita ma Ma’u ta faɗi na ta a zencen gaskiya duka laifin shi ne. Duk shi ya rikita Ma’u ta koma haka a zaman nan ya ya bi Hajiya Zainab ban san sau adadin nawa ba ne, yana alfahari da cewa ita ba ruwanta ba ta ɗaga masa hankali lokacin da zai auri Ma’u ba yanzu ma ba ta ɗaga masa ba, sai yanzu ne ita za ta ɗaga masa hankali. Ya yi ta maganganu Yallaɓai ya ba ni haushi bai wani nuna masa kuskurensa ba yana wani lallaɓa sa, ni yadda ya nuna mini a gida ban ɗauka zai yi masa wannan lakwa lakwan ba. Daga ƙarshe an samu masalaha ya ba ta haƙuri itama ta bashi, kuma ya yi alƙwarin ba zai sake yin waya a gidanta ba in ma zai yi to ya kauce ma jin ta da ganinta. Ni ko ganin ba a yi maganar mari ba na gyara zama da cikina tulale a gaba na ce.

    “To marin da ka yi mata fa? Tsakani ga Allah ba ka kyauta me ya sa za ka mare ta a kan wata?

    Na faɗa ina kauda kaina cikin jin hauahi. Yallaɓai na yi mini abin da ba na so mutumin nan ya wani tattare wai an gama mgana ina dawo da su baya.
    “To ka gama mgana ba ka yi maganar mari ba?
    Na faɗa ina kure sa da ido, kawai ya wani bi ya tattare ni ai gwara a nuna masa bai mari banza ba. > Janaftybaby: “Ahto ka sani cewa Ma’u tana da gata duk abin da zai shiga tsakanin ku kar ka sake kai hannunka jikinta. In kuma ka sake to za mu kai mganar gaba, tun da Alhajin mu mata ya ba ka ba jaka ba”

    Yadda na fiffitike ne ya sa har shi Alhaji Mustapha sai da ya yi dariya.

    “Alhaji ka rabu da ita. Kasan masu ciki suna da saurin harzuƙa.”

    Na ma kasa mgana saboda Yallaɓai ya kai ni bango.

    “Haba ba komai gaskiya ta faɗa na yi nadama kuma ni da ita zan rarrasheta. A yi mini afuwa Ya Sadiya.”

    Ya ce mini yana kallona Yallaɓai ma yana dariya dukkansu a ɗage nake kallon su a cikin zuciyata na ce ai duk kanwar ja ce.

    “Yau na sake yadda da maganan nan ta hausawa da suke cewa jini jini ne. Ga shi yau Sadiya na mini faɗa saboda na taɓa mata Ma’u.”

    Sai da ya yi maganar sai na ji kunya na tashi ina mirmishi na ja Ma’u muka shiga ciki muka bar su nan a falo.
    A ciki ba shawaran da ban ba ma Ma’u ba, ganin tana cikin damuwa ya sa na ce ta je ko Kura wajen Baaba ta bar Kano za ta samu natsuwa na kwana biyu sai ta dawo.

    “Ina zan je Sadiya? Baaba fa cikin kishiyoyi take ba na so na je na bar mata abin faɗe”

    “Ai ba dawo mata kika yi ba. Zuwa za ki yi da niyar za ki yi sati ɗaya daga nan in kika huta zuciyarki ta yi sanyi sai ki dawo ba tare da ita ko ita Baaban ta san wani abu ya faru ba.”

    Sai ta kalleni kafin ta jinjina kai ni kuma sai na ƙara da cewa” Saboda zuciyarki ta yi sanyi. Kuma Baaba uwa ce in kina ganinta hankalin ki zai kwanta ga su Zainab za ki samu yar natsuwa. In ma za ki dawo sai ku dawo tare saboda ta ɗebe miki kewa. Yara kuma kar ki yi mgana lokacin da ya ga dama ya dawo da su duk ɗaya ne da can da nan ɗin. Kar ki sake ki sake yi masa mgana kin ji ko?

    Sai ta gyaɗa min kai alamun ta ji, hannuna ta riƙe tana faɗin” Na gode Sadiya. Allah ya bar ki da Yallaɓai har abada ya ba ku zaman lafiya.”
    Na amsa da amin amin nima ina mata ƙwatanƙwacin addu’ar da ta yi mini.
    Ba mu baro gidan ba sai da muka sulhuta komai sai gashi tare suka rakomu har haraban gida muna fita bayan mun ɗau hanya Yallaɓai ya kalleni yana faɗin.

    “Kin ga ni ko? Shi ya sa na ce miki kar ki zaƙe mata da miji sai Allah.”

    “Uhm”

    Kawai na ce ina kallon Yallaɓai da na so kar na yi magana amma na ga dai ba zan iya haƙuri ba.

    “Yallaɓai ni dai ka daina mini irin haka. Kawai ina so na ƙwatar ma y’ar uwata yancin ta kana dakatar da ni”

    Ya kalleni ya sake kallona kafin ya ce” Me na yi kuma? Daga mgana. To ai na bar miki kin karɓan mata Umma Sadiya”
    Ya faɗa yana mini dariya na yi kamar na kai masa duka saboda haushi amma ban yi ba saboda dai ya wuce duka in dai a wajena ne. Yallaɓai ai sha kumdum ne maƙura ne.
    Muna hanya wayar sa na tsakiyar mu Gimbiya na ta kiran shi ya ɗauka ban ji dai me ta ce ba amma na ji shi ya na ce mata gashi nan zuwa. Ina zaune a gefe ko kala ban ce ba, ita wai nan ya fita da safe ranar girkinta shi ne take ta jaraban kiran shi.

    Kafin mu isa gida na sake masa maganar koyon mota kawai sai Yallaɓai ya ce” Ke da wannan abin a gaban ki ne za ki je koyon mota? Kya bari dai ki haihu.”

    “Za ka koya mini in na haihun! In ba za ka koya mini ba na nemo ko Adnan ko Musbahu”

    Sai ya fara dariya kafin ya ce” Ba za a yi haka ba Uwargida sarautar mata. Ke ce Alhaji Alhaji ya zama ke. Dole na ijiye duka harkokina na cika umarnnin ki.”
    Ko gatse dai ya yi na biye mishi na ce ƙwarai kuwa.
    Yana kawo ni gida ko shiga bai yi ba Amarya na ta kira kai Gimbiya ba ta da haƙuri a rayuwarta ni dai na sauka na shige gida shi kuma ya wuce ban san yadda suka ƙare ba domin ni ban sake ganin shi ba sai washegari da yamma da zai dawo gidana.

    Labarin abin da ya faru da Ma’u da mijinta daga ni sai Yallaɓai ko su Ya Aina ban taɓa faɗa mata ba duk ko yadda muke da ita. Na aminta da wani abu ɗaya ka riƙe sirrin wanda ya aminta dakai. Ba daɗi ta ji wannan mganar a bakin su sai ta ji ta raina ni, yadda nima ban faɗa ba itama kuma ba ta fidda mganar ba. Haba ai ba abin faɗe ba ne tun da ba abin daɗi ba ne muka rufe maganar a tsakanin mu tun da dai an samu sulhu. Kuma ko sati ba a yi ba mun haɗu a gida mun je duba Gwaggo da take zazzaɓi har ƙarin ruwa a ka yi mata a gida. > Janaftybaby: Ta ga har mun zo mun taru gabaɗaya mun kuma rabu ba ta ji na yi maganar ba tana komawa gida sai da ta kira ni tana mini godiya har tana cewa na nuna mata na fita. Da ita ne ko domin a yi mini dariya za ta faɗa amma ni na nuna mata na yi ma zumumci kara kamar Yadda Alhajinmu ya roƙe ni.

    “Ai ba mganar daɗi ba ne Ma’u. Sirrin ki kuma ai sirrina ne in na je na faɗa to ni za a yi ma dariya.”

    Ko Ya Aina sai da ta yi mini mgana. Ta ga ni da Ma’u gwanin sha’awa har Rahila ma sai da ta yi magana na yi dariya kawai na ce duniyar ma nawa take? Ya Aina ta ce haka ne kuma na burgeta. Rahila kuma har tana mini shaƙiyancin da cewa ko na kusa mutuwa ne na zama saliha, na ce mata ai ba yanzu zan mutu sai ta rigani mutuwa muna ta dariya ni da ita. Ba su san irin masifan da Yallaɓai da su Jidda ke karɓa ba, sun ga masifa da cikin nan kala kala.

    A ƙarshen watan aktober a ka ba da sanarwa lafawar cutar corona. Farkon watan November kuma a ka buɗe gari har da makarantu gabaɗaya. Su Jidda a na ta murna an koma makaranta ta ɗauka da sun koma za su fara jarabawa ne amma sai a ka ce sai sabuwar shekara saboda calander ya birkice Jamb sai sun sake rigister. Wato abubuwa da dama a hutun nan na corona ya dagula shi, komai ya koma baya sai dai kuma a hankali komai zai dai- dai ta ni dai ban yi maganar komawa makaranta ba, in ma na yi Yallaɓai dariya kawai zai yi mini na ji ma kamar ba ni da rabon karatun ne daman haka Yallaɓai yake so. Ko da na koma bayan na haihu renon fa ai aiki ne mai zaman kan shi kafin sai kawai na cire karatun a raina na ce wata ƙila ba alheri ba ne. Na mai da hankalina kan sana’ata na hijabai da inears. Kuma Alhamdulillah ina samun alheri matuƙa.

    Ga shi cikina ya yi ƙasa na shiga watan haihuwana. EDD dina 17 November ne. Har ina ce ma Yallaɓai in na haihu zan haɗa mana da Wedding Annivesary na cikar auren mu shekara 20 wanda tun June muka cika shekarun lokacin ina ta kaina laulayi ya saka ni gaba ya sa ko maganar ma ban yi ba Yallaɓai daman ni nake tuna masa tun a baya ballantana yanzu da harkokinsa suka yi yawa.

    *

    10 November 2020
    Tuesday. Talata.

    Lafiya lau na tashi ko ciwon bayan da kwana biyu na kan tashi dashi yau ban ji sa ba. Yara duk sun tafi makaranta daga ni sai Yallaɓai a gida kwanan su uku a Abuja sai jiya ya dawo da daddare ya sauka a gidana daman daga can gidan Gimbiya tafiyar ta kama shi.

    Lafiya lau muka karya, ya ce ba da wuri zai fita ba sai bayan azahar muna cikin bedroom Yallaɓai na kwance ni kuma ina zaune a gefen gado ina ware kayana da na yara sai na Yallabai da safen mai wanki ya kawo su. hira muke yi sama sama sai na ji shuru ashe barci ne ya ɗauke shi.
    Sai na cigaba da aikina. Na kwashe kayana na jere cikin kwaba haka ma na Yallabai na su Jidda ne na ce bari na kai musu ɗakin su, sai dai ina in mikewa ne ya gagara. Ƙafafuwana sun riƙe, bayana ya ƙage, daman kafafun sun kumbura cikin ya sunkunya ya yi kasa ba ni ma da riga a jikina da ga ni sai zani zafi kawai na ji ina yawan ji tun da cikina ya shiga watan haihuwan shi.

    Na yi ƙoƙarin dafa jikin gado na miƙe ai ban san lokacin na saki ƙara ba, wanda ya ta da Yallaɓai a firgce. Tuni har na duƙe a kasa ina riƙe bayana da na ji kamar ya tsage.

    “Me ya faru?

    Yallaɓai ya faɗa yana dirowa gabana.

    “Baya na. Wayyo Yallaɓai bayana ya tsage.”

    Na faɗa cikin tsananin azaba har ina cije bakina. Yallaɓai na duba bayan nawa ne ni kuma ina ta wash wash kawai na ji ruwa na bin kafafuna ina dubawa sai na ga har faya ta fashe ai sai na zaro ido cikin ƙaraji nake faɗin.

    “Haihuwa ce Yallaɓai. Haihuwa ce faya ta fashe.”

    Na faɗa ina makarƙyata jin yadda marata ke wani irin juyawa. Kusan fa na manta yadda haihuwa take shekaru goma ba wasa ba. Ji nake yi kamar ban taɓa haihuwa ba azaban da nake ji kamar ban taɓa jin irin shi ba.

    “Innaliillahi haihuwa? To mu tafi asibiti ko?

    Ya faɗa cikin ɗimuwa shi ma ya ruɗe kamar ni. Kawai sai na yi zaune kawai tuni zanin da ke jikina ya yi ta kanshi nima ina ta kaina na fahimci gajeruwar naguda zan yi. Haihuwa ce gadan gadan ta taho mini ban shirya ba.

    “Ba lokaci Yallaɓai. Ba lokaci ka zo ka zoo..” > Janaftybaby: Na faɗa da ƙaraji jin abu na turowa ta gaba na. Kan ɗa ne ya turo, Yallaɓai ya ruɗe bai taɓa ganin haihuwa ba sai ranar shima da ya matso kusa na riƙe shi gam ina nishi amma bakina bai mutu ba.

    “Zai fito. Zai fiiiiii.. too..”

    Na faɗa ina karta kumbuna na a jikin fatar hannun Yallaɓai saboda nishin da nake yi, ga kan ɗa na ƙoƙarin fitowa da Yallaɓai ya leƙa ya gani sai ya ruɗe faɗi yake yi” Ga shi nan fa zai fito na shiga uku.”.
    Ya faɗa cikin fitan hayyaci..
    Ni dai bam san yadda a ka yi ba domin kamar na shiɗe ne da na yi wani irin ƙarfafan nishi ina ƙara damke hannun Yallaɓai ihun har sai da muryata ta dishe. Sama sama na ji abu sulumf sulumf har sau biyu ya faɗo lokaci ɗaya da kukan jaririya

    “Inyainya. Inya.”

    Sai na koma na kwanta a ƙasan tayels ɗin dake bedroom ɗin domin cafet ɗin yana da ga wajen ƙuguna ne, wajen kaina kuma tayels ne haka na ji jikina ya saki yaraf na kwanta kawai ina maida numfashi ina jin Yallaɓai cikin fitan hayyaci yana faɗin.

    “Sadiya kin haihu. Wallahi kin haihu.”

    Muryansa cikin farinciki da wani irin ɗimuwa mara misali.
    Ni kuma ina ta sauke ajiyar zuciya a jere ga zufa da ya wanke minu jiki kamar an kwarara mini ruwa. Haihuwa na yi cikin abin da bai gaza da mintina goma ba. Allahu akbar Allah shi ne Ubangiji mai yin yadda ya so a lokacin da ya so.

    “Alhamdulillah.”
    Alhamdulillah’

    Na ke faɗa a zucci da sarari saboda Ubangiji ya yi mini sutura na haihu a cikin ɗakina tare da mijina cikin lafiya da ƙarfina. Allah ne abin godiya.

    *Janafty*

    Note
    error: Content is protected !!