Turken Gida – Chapter Forty
by JanaftyDuk da na bar ma Yallaɓai ɗakin sai da ya ƙara biyo ni falon. Ina zaune ina cin dankalin hausa ɗanye kitchen na shiga na ga Jidda na ferewa wai shi ta ke sha'awa za ta soya ta ci nima nan take na ji ya shiga raina sai na ce kawai ta fere da ɗan yawa sai mu ci gabaɗaya. Shi ne kafin na taho na ɗauki wanda ta feren ƙarami na wanke na taho da shi falon Yallaɓai na zauna ina gutsira a hankali ina jin daɗin sa a bakina da cikina gabaɗaya. . .