Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*
    Ban ji daɗin ɓullowar cutar corona ba, sannan ban ji daɗin lockdown ɗin da a ka san ya mana ba gabaɗaya ƙasa ta tsaya waje ɗaya cak. Ba makarantu ba zuwa aiki komai ya tsaya, in fita ta kama ka dole sai ka saka takumkumi kamar wani ɓarawo kana tsaka tsan tsan. Shikenan Burina na son komawa makaranta ya tsaya cak shima amma duk da haka ban karaya ba faɗa ma kaina nake yi na san na ɗan lokaci ne kasa za ta daidai ta na cika burina na komawa makaranta.

    Kowa na cikin takura da wannan lockdown ɗin amma sai na ga kamar Yallaɓai shi murna ma yake yi, ko don ba aikin gwammati yake yi ba ne wataƙila domin ya ga na shi ayukan ba su tsaya ba ne shi ya sa. Sai daga baya na fahimci har da zama na a gida ban samu tafiya makaranta ba kamar yadda na ci buri saboda ba shi da aiki sai tsokana ta har wani suna ya saka mini yanzu Hajiya Saadiya mai kwalin mastes. In kuma ya tashi tsokana ta da cewa masu masters dai an koma zaman gida tun ina nuna jin haushina shi kuma ya yi ta dariya har wani jin daɗin tsokana ta yake yi ranar dai na gaji na ƙufulu na ƙudirta a raina in ya sake tsokana ta sai na mayar masa da martani kamar ya ko san ina jiran shi sai ga shi ranar ya kwana a gidan Gimbiya sai ya biyo nan gidan da safe mu gaisa sai ya iske ni na ci gayu na cikin riga da wando ina zaune a saman kujeran falon ina danna waya ta lokaci ɗaya kuma ina ɗan kallon talabijin ɗin da Baby ta kunna cartoon a ke yi a MBC3

    Da Surraya Dee mai kyan ɗa’a muke chart na tura mata ciko kuɗin ta domin satin da ya wuce na siya mganin sanyi da haɗin kaza. Tana ta mini tsiya saboda sai da ta ƙara kirana ta ce ta ji shuru ba ta ji ni ba, ni kuma na ce mata lokacin muna ɗan hatsaniya ne da megidan da ya ke ta san yanayin tun da itama matar aure ce. Ta ce Mazan ne sai a hankali su yi tutsu in sun so a yi daɗi ana yi in suka so tsiya ma sun san ta kan shi. Shi ne fa muke ta hira da ita a kan matsalolin rayuwa na yau da gobe.

    Jidda na ɗaki tun da suka daina zuwa makaranta in dai ba aiki za ta yi ba tana cikin ɗaki tana karantu Baby ce yar falo mu yi ta hidiman mu, itama ɗin yau ta na can falon Abban na su ta na zane zane a takardu ta bar ni, ni kaɗai ina ta danna waya ta. To tun da an kulle mu a gida sai kafafen sada zumunta suka zama ababen debe mana kewa. Na ji shigowarsa suna mgana da Baby a falo ban tashi daga zaunen da nake ba sai ga shi ya shigo cikin shigar ƙananun kaya ni Yallaɓai har mamaki ya ke ba ni shi bai son ya girma ba ne? Ko don jikinsa ba ya nuna shekarun sa? Ya kama kafar wajen shekaru arba’in da bakwai amma kuma yana jin kansa kamar ɗan shekaru talatin.

    “Wannan kallon fa Madam?

    Ya faɗa lokaci ɗaya yana jan hancina. Ashe ya ƙariso har gaba na ban sani ba.

    “Ko na yi miki kyau ne?

    Ya sake faɗa yana mini murmushi har yana kashe mini ido ɗaya.

    Sai na yi dariya kafin na ce” Wani kyau? Ina kallon ka ne, a raina ina cewa Yallaɓai na ya fara tsufa”

    Yana zama gefena yana faɗin” Ko? Ke dai ce da mganarki amma ni har yanzu ji na, na ke yi kamar ɗan saurayi mai shekaru talatin.”
    Sai na buge kafaɗansa ina dariya kafin na ce” Jidda fa ƴ’ar ka ce? Ko ka manta ne?
    Sai ya jawo kafaɗata saman tashi ya saka hannunsa guda ɗaya ya zagayo ƙuguna da shi.

    “To sai me! Ke in ba fa na faɗa ba ɗan Saurayi a ke kallona. Kuma tsab in na tsai da budurwa yar sha za ta tsaya mini”

    Hararan sa na yi kafin na ce” Wai ko dai ƙara aure da za ka yi da yarinya ƙarama ne Yallaɓai?

    “Me kika gani?

    Ya faɗa yana dariya ƙasa ƙasa. > Janaftybaby: “To na ga da an fara mgana sai ka ce ko yanzu za ka iya auro yarinya yar sha sa’ar Jidda.”

    “To in ma da gaske ne Haramun ne?

    Ai sai na buɗe baki ina kallon Yallaɓai. Ganin na kasa mgana ne ya sa ya rufe mini baki yana mini dariya sai na ture shi gefe ina hararan shi. Shi kuma ya na ƙara naniƙe ni ina ture shi yana minidariya.

    “My Sady kishi”

    “Ina ruwana ai ba a kaina za ta zauna ba kuma ai ni ka gama mini kishiya. Gimbiya ce a kan layi “

    Dariyan nishaɗi ya yi kafin ya ce” Ka ji ta kamar gaske”
    Na yi masa banza saboda na ga alamun ya na so maganar ya yi dariya ya na jin nishaɗi. Da gaske nake yi ai ni ya gama mini kishiya ko wata zai aura sai dai Gimbiya ta ji ƙwatan ƙwancin yadda na ji a lokacin da ya auro ta. Kallon sa nake yi yana tambaya ta Jidda na ce ta na ɗaki sai ya tashi ya shiga dakin na bi shi da kallo. Yallaɓai bai taɓa ce mini yana sha’awan tara mata ba amma ni a ƙasan raina na ke jin giyar kuɗi za ta iya ɗibar sa ya ji mun yi masa kaɗan kuma wannan wargajenjen filin da na ji labarin ya siya ba, ba iya ni da Gimbiya ba ne. Wataƙila shashen mata huɗu ne zai gina a hasashena tun da bai taɓa furta mini haka ba. Ya ce sai an gama ginin kamfanin shi an buɗe shi sannan zai fara ginin gida can kwanaki ma da muka bi ta hanyar na ga Kamfani ya yi nisa kaɗan ya rage a ƙarisa.

    In ana misalin maza jajirtattu masu jajircewa da juriya to sunan Yallaɓai zan fara kamawa a shekarun da na san shi sama da shekaru goma sha takwas ya jajirce domin mafarkinsa ya tabbata na gina kamfanin shi, domin ya taimaki matasan da aikin yi to ko a haka ya tsaya wallahi ya cigaba domin matasan da suke aiki a ƙarkashin shi shi kan shi bai san iyakar su ba. Da masu ilimin da ma waɗanda ba su da ilimin duk na shi ne, masu ilimin suna aiki a bangaren ma’aikatan shi mara sa ilimin kuma suna aiki a bangaren kwangilan gine ginen shi. Kuma ya na da tausayi da kyautatawa ga kuma mu yadda ya ke kyautatama mu da iyayen shi, shi ya sa Allah ba zai bar shi ya taɓe ba.

    “Ke wai me ke damun ki kike yawan shiga tunani ne?

    Na ji yana faɗa lokaci ɗaya ya na mai zama a gefe na. Har ya na wani jawo ni jikinsa yana shafa bayana zuwa kuguna sannan ya cigaba da faɗin.
    “Uhm mene ne. Faɗa mini damuwarki yanzu na yi miki mganin ta.”
    Kamar abun arziƙi na ɗago ina kallon shi kafin na marairai ce ina faɗin” Yallaɓai wai yaushe za a buɗe gari ne? Tsakani ga Allah ba a kyauta mana ba da yanzu fa mun yi nisa da lectures”

    Me Yallaɓai zai yi in ba dariya ba, har ya na ƙyaƙyatawa. Ni kuma sai na haɗe rai na koma gefe na yi bakam. Ina jiran ya taɓo ni sauke masa jin haushin shi da nake ji.

    “Ai in za ki shirya zaman gida ki shirya. Domin cutar ma ƙara yaɗuwa ta ke yi ba ma maganar a buɗe gari.”

    Kallona ya ke yi fa yana tsintsira min dariya.

    “Hajiyar Masters. Ki yi wannan master ɗin ki a gidan auren ki, taho mu je ciki ni ma ai malamin ne sai na baki karatu”

    Ya ma miƙo hannu ya kamani na bige hannun shi ina hararan shi amma bai saka ya daina dariya ba.

    “Yallaɓai.”

    Na kira sunan shi a tsume.

    “Na’am My Sady masu kwalin masters”

    “Ni dai ko murna kake yi da faruwan wannan abin ne?
    Ko daman can da ka ce ka bar ni na koma makaranta ba har zuciyar ka ba ne?

    Na ƙarishe ina mai kura masa ido. Ya na danne dariyarsa ya ce” Wallahi har raina na amince miki. Ya za a yi na yi murna da haka?
    Ya ƙarishe faɗa yana daga hannu sama amma bai daina mini dariya ba.

    “Na ga kamar murna kake yi. Wato gara da a ka yi haka ko?

    “Murna kuma! Da girmana Sadiya?

    Ya faɗa yana sosa sajensa amma bai daina dariya ba kawai sai na miƙe fuu da wayata ina faɗin”Ohon in ma ka na murnan gwara da a ka yi ne gwara ka daina saboda ba ni kaɗai ba ce a gidan har da ƴaƴan ka”

    “Kuma haka ne fa.”

    Ya faɗa yana kuma cigaba da dariya.

    “Kuma in sha Allahu, za a buɗe gari kuma zan shiga makaranta Ehe.”

    Na faɗa ina mai barin masa falon sai ya biyo ni yana faɗa mini.
    “In sha Allahu wa ya isa ya hana ki zama mai kwalin masters”
    Gabaɗaya Yallabai ya mai da ni abar nishaɗinsa na so ina shige ɗaki na rufe ne sai ya shammace ni ya biyo ni yana faɗin shi fa ba dariya yake yi mini > Janaftybaby: “Wallahi in na tuna yadda kika ci burin karatun nan sai na ji duk ba daɗi. Sorry My Sady in sha Allahu zaman gidan ba zai yi tsawo ba.”

    Wani kallo na yi masa saboda yana faɗa ne amma yana danne dariyan shi kawai sai na fusata na jawo filo na wurga masa ina faɗin.
    ” Ka fita Yallaɓai”
    “Na je ina?
    Har tsayawa yake yi yana tambaya ta, sai na ƙara rarumo ɗayan ina ƙokarin jifan sa da shi sai ya mamayeni ya rumgumeni yana mini dariya ni kuma ina fizge fizge sai ya fara min cakulcakuli a dole sai na yi dariya. Yallaɓai akwai mugunta wallahi sai da na yi hawaye, har fa sai da na ce masa zan yi fitsari a wando in bai daina ba sannan ya ƙyaleni. Bai bar gidan ba sai da na dai na fushi na dawo ina dariya ni ce har haraba na raka shi muna soyewar mu.

    *

    Tun ina saka ran za a buɗe gari na yi registration ɗin makaranta har na cire rai ganin har mun shiga wata biyu muna kwararan na uku, sai na ce gwara na zauna na yi ma kaina tunanin mafita. Tun da karatu dai ba zai yuyu ba gwara na mai da hankalina kan sana’ar hijabai na da yadda zan ƙara ingata shi, sai na fara tunanin sunan da sanya ma kasuwancina. Da ƙwaƙwalwar ta ƙi sai na nemo Jidda na ce ta sama min suna. Haka muka zauna muna ta zaɓe har sunana ta haɗa ni da Yallaɓai SADYUF na ce ba na so da a baya ne zan iya haɗawa dashi amma tun da ya yo mini kishiya na fahimci Yallaɓai ba nawa ba ne ni kaɗai. Ta haɗa da haruffan sunanta da na Baby na ce ba na so sunan ya yi kama da na ma’aikatan Yallaɓai ne. HM TAFIDA AND SON’S LIMITED. Sai na ce a samu dai wani ganin zai yi wahala na ce kawai ta haɗa min da sunana, mun yi kwanaki ba a samu wanda ya yi min ba sai da na ce mata ina so na saro inears wear sai ta ce to bari a haɗa gabaɗaya. Da ƙyar dai Jidda ta samo min SADY S YASHE HIJABS AND MORE. Sai na ji sunan ya kwanta min arai nan take na ce bari mu tafi da wannan sunan kawai.

    Musbahu na nema tun da shi ne ɗan gida ne kuma idon gari ne kusan ya san ko’ina. In da Allah ya taimake ni kuɗin da Yallaɓai ya tura mini na hidimam makaranta da na ce zan mai da masa sai ya ce na riƙe na ƙara jari ya bar mini, da su na yi amfani domin ƙara bunƙasa kasuwancina. Musbahu ya shige mini gaba a ka buga mini ledojin da tambarin logona na SADY S YASHE HIJABS AND MORE. An yi manya da ƙanana sannan an yi na kwali su na manya costumer ne
    Sannan an yi min sticker na mannawa a jikin kaya bayan na siya ledoji farare da zan riƙa saka hijaban da kayan in an siya. Tun dai an samu zaman gida bari mu kama sana’a zama bai ganmu ba. Musbahu ya saka cikin masu zanen su na kamfani ya zana min logo mai kyau na saka shi a duka handle ɗina na kafafen sada zumunta.

    Kuma kowa ya gani sai ya ce sunan ya yi kyau. Ya Hamza sai da ya ce bai ga sunan Yallaɓai ba ina dariya ban ce komai ba har Ma’u da muka daɗe ba mu yi mgana ba da na ɗora a status a ƙasa na yi caption da cewa.

    “SADY HIJABS AND MORE. Muna siyar da nau’in hijaban da kuke so sannan za mu fara kawo muku inners wears, kamar su pants, bra, sikat, mini trouser and more. Please potonorize your Sister. Sadiya Sulaiman Yashe C.E.O”

    A nan Yallaɓai ya gani ya yi tagging ya turo mini dariya. Na shaka na auna masa naushin hannu na sticket kawai sai ya yo mini Vn ranar ma ba a gidana ya kwana ba yana gidan Gimbiya amma a daran zai dawo gidana.

    “Daman shawaran nan na kawo miki tun farko kiƙa ƙi karɓa. Duk wanda ya tuba don wuya ba lada.”

    Haka ya ce min fa sannan ya ƙarishe da dariya. Ina masa Typing sai ga shi ya sake turomin mgana.

    “Congratulation My Sady. Duk abin da kika saka ma suna ko hannu sunan shi Nasara. I wish you the best”

    Kalamansa suka wanke mini zuciya na fasa tura masa abin da na yi niyya.

    “Thank you Mijin Sadiya.”

    Kamar ya ijiye wayar amma dai ya tafi bai kashe data ba. Mutane sai fatan alheri suke yi mini har Anty Maimuna sai da ta ce yana da kyau kam na ƙara da wani abun Anty Zuwaira kuma ta yi tagging da zamu siya in sha Allahu. Daman ita ai ba ta da matsala Anty Bahijja ne ta gani ba ta yi mgana ba. Amma har Gimbiya ta yi mini murna sannan ta ce za ta yi mini talla a status ɗin mutanenta su gani ko za su siya na ce Na gode. > Janaftybaby: Daga nan na kashe data na sauka sai zuwa can an juma Sameena ta kira ta ce ta na son hijabai da na pant da bra shi ne take faɗa min a status ɗin Yallaɓai ta gani ya ɗora sai da muka gama waya sannan na buɗe data na gani.

    Ya saka ne amma bai yi wani rubutu ba. Na ga kara domin sun ta sakawa a status suna yi mini tallah. Marwa ma ta saka Hauwa ma da ta yi waya Munnira ma haka yan gidanmu Ya Balki sai Amina har da Datti Ya Auwal dai da Ya Hamza ba a saka su a lissafi su waɗanan ba su damu da saka statua ba irin Yallaɓai ne. Ya Abubakar kuma shi wannan ɗan buga buga ne bai ma cika hawa online ɗin ba. Gidan su Yallabai su Musbahu ne da su Adnan sai Jawahir da su Suwaiba sune daman nawa. Duk kuma wanda ya ga logon zai ce zane ne, ma su abu da abin su kura da kallabin kitse.

    Kamar wasa na yi ta samun odar masu siyan hijabai da inners barin ma da azumi ya ke tunkaro mu. Da ya ke a mota kawai ake saka mun ina tura masa bayanan da kololin na Hijabai inners kuma sara na yi da yawa na yara da manya na tura kuɗi a ka kawo minI har na cin kasuwar salla. hijaban dai sai na ƙaro tun da guda 50 na ce a akawo mini. Da suka iso duk wanda ya siya ni da Jidda muka yi zaman saka su. A leda muna manna sticker sai lamarin ya burgeni ni kaina komai da tsari kan ya fi burgewa Jidda ta yi Vadeo muna saka sticker ta kuma ɗora mini a status ta ce kaya sun iso. Nan da nan cikin sati ɗaya kaya suka ƙare sai na sake tura kudi ɓarin ma Inners ɗin sun tafi yadda ma ban yi zato ba daman su Hijabai ana siyan su sosai. Wannan karon sai na ce a sako mini da mayafai da kayan barci suma dai ba laifin ana ta siye da na gida da na waje.

    Sana’ata na riƙe gadan gadan. In dai ka ganni da waya to ina can ina marketing. Yallabai har suna ya sauya min wai hajiyar Hijabai ni dai na ce ka ji da iyayin ka tun da karatun dai bai zo hannuna ba gwara na kama abin da ya zo hannuna. Ana cikin haka a ka kawo mana kayan saka ranar Suhailat ɗin Anty Bahijja bayan sallar azumi za a yi bikin kuma Kaduna za a kai Amarya. Ni da kaina na kira ta a waya na yi mata Allah ya sanya alheri. Ni ba na gaba da ita muna gaisawa in mun haɗu amma daga wannan gaisuwan kowa sabgan gaban shi yake yi tun da aka yi mana tsakani ni da ita.

    Cikin ikon Ubangiji muka riski watan ramadana cikin lockdow abubuwa duk sai a hankali saboda yanayin zirgan zirgan gari duk da ba kamar lokacin gari na sake ba wannan karon ma Yallaɓai ya siya buhun gero da siga sai wake buhu ɗaya na alale da ƙosai na kai ma Maman Saude yin kunin ita kuma Maman Nana mai yi min kitso a ka ba ta yin ƙosai da alalen. Sannan ya rarraba ma matansa da ke aiki a ƙarkashin sa kayan abinci wasu kuma ya ba su kuɗi, daga can Rano Kawu Abba ya aiko mana da su ƙwai da dankalin turawa. Nima Yallabai ya ba ni kayan abinci har da kuɗi na kai gida duk da na san itama Gimbiya ya ba ta ta kai can Rano amma ni bai gaya mini ba, ban nemi da sai na ji ba kuma
    Azumi ashirin da tara muka yi kuma ban sha ko ɗaya ba ko da ban ga period ɗina ban damu ba, ko watan da ya wuce ma bai zo ba saboda an sha yin azumi ni ban sha ba sai ban saka tunanin komai a raina ba. Yallaɓai ya yi mana kayan alfarma ni da yara har salla ta wuce muna saka sabbin kaya sannan ya yi ma iyayena har Inna Mariya ya yi ma turmin atamfa wannan shekaran. Ni kuma na caɓa da cinikin hijabai da inears wannan sallar kaf su Ya Hamza wajena suka yi ma iyalansu siyayya kuma na ji daɗi a dangin Yallaɓai kuma su Musbahu ne da su Anty Zuwaira har Anty Maimuna ta siya ma yara. Gimbiya ma ta siya kuma ta kawo mini costumer kuma na ji daɗi na gode mata. Yallaɓai ma kuɗi ya ba ni na yara sai kawai na cire musu a ciki da ni kaina na saka kuɗin a ciki. Kuma ba abin zan ce ma Allah sai godiya ina samu ina yi ma kaina hidima sannan abu na ƴan uwa ya ta so ina ɗauka na yi ba sai na je ina yi ma Yallaɓai yar murya ba.
    An ɗaga bikin ɗiyar Anty Bahijja sai gab da babbar sallah a bakin Munnira nake jin wai uban mijin ne ya biya ma Sulaihait ɗin kujeran makka tare da mijin ana ɗaura auren za su tafi tare na ce Allah ya sa su je lafiya su dawo lafiya.

    **** > Janaftybaby: Kamar kar a yi salla sai na fara rashin lafiya. Kuma rashin lafiya irin a tsatsaye haka. Kasala ya riƙa damuna na dai na cin abinci komai ba ya mini daɗi ban da kunin tsamiya mai zafi ba abin da ke shiga cikina. Sannan ba na iya shan kowani ruwa. Ba ni da aiki sai kwanciya tun ina ganin abin wasa har dai na fara tunanin watakila ina da ciki. Tun da in dai na ci abinci sai na yi amai ga Yallaɓai ba ya nan ya je Dutse wajen kwanan su huɗu a can, karyata kaina nake yi da ba ciki gare ni ba saboda ko wancan da na yi ɓarin shi ban ga alamomin shi ba sai kawai na fi amimta da maleria ke damuna na saka a ka siya mini mganin maleria na fara sha. Ai duk ranar da na sha sai na yi amai sannan sai na fara miyau
    ba na iya haɗiye miyau. Sannan na yi ta kwana da zazzaɓi gari na wayewa sai na ji sauki. Jidda ta ce za ta rakani asibiti na ce ba zan je ba har waya ta sata ta yi ma Yallaɓai waya ta faɗa mai halin da na ke ciki sai ya ce ta ba ni wayar haka ya riƙa mini faɗa ya kuma ce umarni ne maza maza na tashi na shirya Jidda ta rakani asibiti na ga likita.

    Ba yadda na iya haka na shirya. Sai a lokacin na fahimci na rame sannan na ƙara haske, wani asibitin kuɗi muka je muna zuwa suka yi mini tambayoyi na faɗa musu wajen wata uku kenan ban ga al’adata ba sun ɗibi jinina da kuma fitsari muka zauna jiran sakamako Yallaɓai kuma sai kira ya ke yi Jidda ce ke ɗaga kiran ni ina ta kaina sai kwanciya nake yi a kujerun asibiti. Lokacin da sakamako ya fito likita ya ba ni farar takarda sannan ya faɗa mini ina da shigar ciki ɗan kimanin wattani biyu da kwanaki. Duk da alomomin masu ciki sun bayyana a tare da ni ban saka ma kaina yaƙini ba. Hawaye suka zubo minibsai na sharce su a cikin raina na yi ma Allah godiya sannan na yi masa kirari. Jidda na wajen domin ita ta riƙe ni muka shiga da muka fito ina riƙe da takardan muka samu adaidaita da zai mai da mu gida. Amma sai da Jidda ta biya Pharmacy ta siya mini magungunar da ya rubutamin na ƙarin jini da na cin abinci.
    Da farko da Yallaɓai ya ce zai kira Salisu ya kai mu tun da motar na hannun shi in fita haka ta kama ina kiran shi ni na ce ya ƙyale shi mu fita mu hau adaidaita sahu. Har a cikin adaidaita kwanciya na yi da leda a hannuna ina tara miyau duk cikina da na yi da ga na Jidda har na Baby ban yi miyau ba, kai ban ma yi wannan laulayin mai wahalar wa ba. Tun kafin mu kai gida Jidda ta kira Yallaɓai tana murna tana faɗa mai likita ya ce Umma na da ciki.

    “Jidda da gaske kike yi?

    Ina ji saboda wayar an ƙure mata kara. A yanayin muryan Yallaɓai za ka san akwai zaƙuwa da zamuɗi.

    “Na rantse da Allah Abba Umma za ta sake haihuwa.”

    Ta faɗa cikin har sai da mai adaidaitan ya juyo yana kallonta ina ganin shi sai da ya yi murmishi ya juya kai ya na faɗin” Hajiya yanzu daman wannan budurwan ƴar ki ce? Wallahi na dauka ƙanwarki ce ni dai dariya kawai na yi ba tare da na yi magana ba.

    “Ma sha Allah. Allah ya inganta.'”

    Na ce Amin ita Jidda ba ta ma jin sa ta na can ta na waya, ban yi mamakin kalamansa ba saboda ba shi kaɗai ya taɓa faɗan haka ba sau tari mutanen da ba su sani ba in suka ganni da Jidda sai su yi tunanin ƙanwata ce. Saboda na haifi Jidda da ƙananun shekaru shi ya sa muka ta so kamar ƴa da ƙanwa sannan na mori ƙaramin jiki.

    Ji kawai na yi Jidda ta manna min waya a kunne ta ce ga Abba na mgana. Sai da na cire facemark na tofar da miyau a ledan da ke hannuna sannan na karɓi wayar

    ” Yallaɓai.”

    “Congratulations My Sady. “

    “Congratulations Yallaɓai na.”

    Na faɗa a hankali ina murmushi.

    “Alhamdulillah Allah abin godiya. Kin gani ko? Daman ni a jiki na na ke jin ba ki gama haifa min ƴaƴa ba Sadiya. Yanzu kin aminta da magana ta?

    “Na aminta Yallaɓai.”

    Na faɗa a hankali saboda jikina gabaɗaya ba ƙarfi, faɗi yake yi yana cikin farinciki mai tsanani sai na katse shi da cewa.

    “Yallaɓai ban da lafiya. Jikina ba ƙarfi ba na iya cin abinci ba na shan ruwa.” > Janaftybaby: Na ce kamar zan yi masa kuka shi kuma sai ya ruɗe.
    “Sannu. Me likitan ya ce! Me ya sa ba su riƙe ki a can ba?
    Sai na kasa mgana domin maganar ma wahala take yi mini sai kawai na ce ya bari mu koma gida sai mu yi magana. Dalilin da ya sa ya katse wayar kenan muna ko komawa gida ya sake kira ya na tambayana yadda nake ji.

    “Yallaɓai miyau ya yi ta taruwa a bakina. Ni komai ma baya mini daɗi ban iya zama fa sai kwanciya ban taɓa laulayi mai zafi irin wannan ba.”

    Yallaɓai duk ya damu sai lallashina ya ke yi, daga ƙarshe ya ce zuwa gobe zai dawo na kula da kaina. Sai da ya kashe wayar na ji taruwan kwalla ina tausayin kaina ina tausayin shi ban ɗauka bayan tsawon shekaru goma zan sake samun ciki ba. Amma na yi yaƙini da ubangiji mai bayarwa a lokacin da ya so da kuma wanda ya so. Na saka a raina in ina da rabo Allah zai sake ba ni sai ga shi kuma ashe ina cikin waɗanda Ubangiji ke yi ma Ni’ima in sun yi haƙuri ya ƙara musu a lokacin da ba su yi tssammani ba. Ban taɓa tunanin Yallaɓai zai yi mini rawan jiki in na samu ciki ba sai ga shi yana yi min bawan Allah ya na son haihuwa. Na ɗauka tun da Gimbiya ta haifa masa biyu duka maza yanzu ba ya zumuɗinta amma sai ya kore mini shakku. Lokacin da na faɗa masaa na yi ɓari da ya nuna da yakinin wata rana zan sake samun ciki na haihu bai ɗadani da ƙasa ba kamar yadda bayan samun cikin ya nuna farincikin sa.
    Kwana ya yi ya na kirana yana jin jiki. Jidda kam ya yi mata kashedin ta kula da ni ban san adadi ba. Baby da Jidda ta faɗa mata Umma za ta haifa musu wata Baby yini ta yi tsalle da ihu ni dai ina kwance zama ma ba na so ina yi.

    Washegari da rana Yallaɓai ya dawo duk da ba gidana zai sauka ba, yana gidan Gimbiya ne tun da ni ranar da zai bar gidana ya yi tafiyar. Amma duk da haka gidana ya fara sauka ya duba ni ya iske ni kwance da gwangwani miyau da a ka cika min da ƙasa. Ya rumgumeni nima na lafe a jikimsa shi ina sauke numfashi. Yallaɓai ya yi ta shafa marata kamar ya buɗe ya ga abin da ke ciki. Shi kan shi ya ce na rame bakina ya bushe ya yi ɓawo to ko ruwa fa ba na sha sannan ban iya cin komai sai kunin tsamiya.

    Duk bakina da surutu na bakina ya mutu. Allah ya sa Jidda na gida ita ke kula da gidan da yin abinci. Yallaɓai ya faɗa ma Gimbiya ina da ciki ya kuma kawo ta ta duba ni ita da su Khalipa, ina kwance ne ina fama da kaina a saman kujeran falon su Jidda. Ina kallon Gimbiyar tun da muka gaisa ta koma gefe ta tsume. Duk da ban da lafiya amma na fahimci kamar ranar ranta na bace ne, sai na danganta haka da ƙila ita da Mijinta ne. Ko jiran shi da ya ce ta yi ma ba ta yi ba, la’asar na yi ta ce min za ta ta fi wai za ta biya ta shago. Su Khalipa ma da Jidda ta ce ta bar su sai ta ce wai daga Shago Gwammaja za ta biya shi ya sa ba za ta bar su ba. Ni dai ina kwance amma sai da na tofa na ce ta bar su mana in Yallaɓai ya dawo sai ya mai da su amma sai ta ce kar wai su dame ni ba ni da lafiya. Ina jin haka ban takura ma kaina ba na ce su gaida Nene in sun je.

    Tun kuma daga ranar sama da sati ba ta dawo ba na tuna lokacin cikin Khalipa da kwanciyar da ta yi ta yi a asiniti ina jigila da ita. A raina na ce da ban haihu ba da na ji haushin duniya. Munnira ce ta kira ni a waya tana faɗa mini haihuwar Salma Yayar Jawahir C.S a ka yi mata, a ranar da ta kira ni ta ce jiya da daddare ne ta haihun shi ne ta kira ni ta ji yaushe za mu je! Tun da anan Kano ne a Dala. Shi ne na ce mata ba ni da lafiya ma ina gida. A ranar ta zo duba ni kafin in faɗa mata ina da ciki ita ta fara cewa matar injinya ciki ne da ke na ce mata e sai ta buga shewa ta riƙe hanci ta rangaɗa guda ta kuma kira Hauwa tana faɗa mata sai Hauwa ta fara faɗa min an ware ta ba a faɗa mata ba. Ni ko na ce ba wanda na sanar ma wa, nan Munnira ta yini har da lissafin sai ta ɗauko DJ ranar sunan na yi dariya kawai a raina na ce Allah ya sa na rabu dai lafiya. > Janaftybaby: Washegari sai ga Hauwa ta zo duba ni. To su ne da aka haɗu ca gidan Salma ranar suna duk wanda ya ga bai ganni ba sai su ce ina gida ina fama da laulayi. Anan ne wasu suka ji, su Anty Bahijja kuma ina da tabbacin Gimbiya ta faɗa mata gwara ma Anty Maimuna in ta ce ba ta sani ba amma zai yi wahala Anty Bahijja ta ji abu ita ba ta ji ba musamman za ta kira ta a waya ta faɗa mata. Anty Zuwaira har gida ta zo ta duba ni ta ba ni dubu ashirin ta ce na siya gero tun da na ce kunu kawai nake sha ina son ta saboda wallahi tana da matukar kirki shi ya sa nake girmamata. Ita ta ce mini Nene ce ta faɗa mata ba ni da lafiya ta zo ta duba ni, Nenen kuma na san Yallaɓai ne ya sanar da ita. Mubeena na zuwa duba ni akai akai har Marwa ma ta zo ita kuma Kawu ne ya faɗa mata ita kuma ta yaɗa ma Ya Aina ta nan maganar cikina ya faso a dangin mu kowa ya ji sai ya ce ikon Allah lalle bayan wuya sai dai daɗi sannan ba a cire ma Ubangiji yaƙini in ka yi hakuri za ka ci riba. Sun zo dukkansu sun duba ni har da Ma’u Gwaggo ma ta zo har gida kuma na ji daɗi su Ya Hamza a waya suka gaishe ni da matan su. Zainatun Ya Abubakar ta zo yi min yini, ta yi mini wanki da girki ranar.

    Ranar da Nene ta zo ita da Hajiya iya da Maman farko a raina na ce duk abin dake cikina ɗan gata ne. Tun da har su Nene suka zo duniya. Nene ko faɗi ta ke yi Allah ya raba lafiya. Amma ko su kan su sun yi ta ƙorafin rama ta da rashin cin abinci na ce komai na ci sai na yi amai kuni kawai ke zama a cikina shima mai zafi. Ruwa ko rabon da in sha har na manta. Yallaɓai tsausayina ya ke yi sai ya ce ya za a yi ɗan adam ya rayu ba ruwa na ce to ga shi dai ka gani. Gimbiya sau ɗaya ta dawo shima ba ta daɗe ba ta tafi sai na ga kamar ba ta murna da samun cikina. Amma sai na yi saurin cire tunanin haka a raina sai na yi mata uzuri na kuma saka mata kyakyawan yaƙini. Inna Mariya ni da kaina na kira ta na faɗa mata ta yi ta murna ta kuma zo har gida ta duba ni.

    Ko da nake kwance in ana son Hijabai ko kaya Jidda ke mgana da mai ɗinka min daga Zaria a kawo kuma ta zauna duk ta saka musu sticker ta kuma saka su a ledojinsu shi ya sa ba ni da damuwa. Na shafe wata ɗaya da wani abu ina wannan zazzafan laulayi sannan na ɗan fara samuwa. Na fara cin abinci tuwo haka sai ɗanwake sai awara sai dambu, amma ban da su shinkafa da taliya. Duk sona da fura da kayan marmari na daina son su yanzu, ruwa kuma na fara sha amma sai mai sanyi ko na ce mai ƙanƙara ya na narkewa ina sha. Yallabai ya yi ta faɗa wai sanyi zai kamani amma shi kan shi da ya ga shi ne ruwan da na ke sha sai ya ƙyale ni. Na ɗan fara samuwa tun da na daina kwanciya kasalar sai dare ya yi yanzu ta ke nika min jiki, sannan tun da na fara laulayin nan ban yadda mun yi ɓarnan ruwa da Yallaɓai ba to ina ta kaina. Shima kuma bai matsa mini ba, kuma bai sani ba kwata kwata abin ne na ji ba na ma son shi. Na ɗan fara dan kiɓan kumatu amma fa kaya na duk sun yi mini yawa. Na faɗa a raina na faɗa asarari da cewa wannan cikin ɗan gata ne shi ya sa ya ke wahalar da ni. Amma dai na ji sauƙi sosai ba kamar kwanakin baya ba.

    Cikina na wata uku cikin na huɗu aka fara hidiman bikin Sulaihat ɗin Anty Bahijja. Matar nan ba ta zo ta duba ni ba duk da ta san ba ni da lafiya. Amma dai Anty Maimuna ranar ta biyo Nasara sun taho tare. Da Anty Bahijja da Halima ba su zo ba daman ita Halima tuni ta koma bangaren Gimbiya. Yarinyar nan mun sha haɗuwa a Gwammaja ko sha’anin su ta yi kamar ba ta ganni ba. Wai ni ce Halima ta ke gani ta wulaƙanta, lalle na yarda rayuwa ta na cike da mutane masu abin mamaki. Yadda ba a saka ni a shirye shirye ba, ban tusa kaina ba an dai fidda ankon mother eve da na yinin biki. Yallaɓai ya siya mini tun da matarsa ce ta ɗauko Gimbiya. Jidda kuma Anty Zuwaira ta yi mata tare da sauran sa’aninta su Farhan Anty Maimuna Baby ma su suka yi mata, ni ina fama da kaina ba ma ta kan bikin na ke yi ba, bikin zai kama babbar salla saura kwana tara ne. > Janaftybaby: Na dai san Kaduna za a kai ta. Bikin kuma zai yi jama’a tun da har Anty Zabba da muka yi waya ta ce za su zo gabaɗaya har da yara tun da ba makaranta. Sannan kaf su mazan gidan da ke zaune ne sa za su taho da matan su. Matar Jafar ce kawai ba za ta zo ba ita za ta tarbi bakin nan in ji Anty Bahijja, nima duk a bakin Munnira na ke jin wasu labaran a bakin ta na ji su Gimbiya su ne ƙirjin biki sannan har list an yi na mutanen da za a tafi da su a kaduna. A dalilin ina fama da kaina ban ji a raina zan je kai Amarya kaduna ba, ko da ma ina lafiya ba zan tusa kaina ba.

    Ban je gidan bikin ba ma sai ranar laraba da a ka yi mothers eve ɗin. Yallaɓai ma cewa ya yi in ba zan iya ba na yi zama na su Jidda su tafi sai na ce zan iya. Tare da su Hauwa muka tafi can muka iske matar Muhammad Kabir Nafisa har Faridan Tariq ta zo Marwa ma ta zo muna tare da ita tun da gidana ta sauka. Anty Bahijja ta sha gayu ka ce ita ma Amarya ce da ƙawayenta suma yan gayu su Gimbiya ana ta shiga da fita har makeup ta yi su Khalipa ma an sha gayu. Anwar ne ma na gan shi a hannun Baby ta na fama dashi,
    Ni dai na je na gaishe da uwar biki na yi mata fatan alheri shi ne ta ke ce mini an ce ba ni da lafiya na warke kenan na ce mata Alhamdulillah.

    Kowa ya ganni sai ya ce na rame amma fa na yi shar da ni. Suwaiba kam har sai da ta ishe ni wai ban ga kyan da na yi ba ne ko Tafida ya ganni kafin na fito na ce ban sani ba. Mun haɗu da Gimbiya amma ba ta minI mgana ba da cewa ita ta na fama da jama’a ba ta ganni ba ni ko na ce ba zan bi ta domin mu gaisa ba. Ita da Najan Anty Zuwaira ne akan komai kuma suma sun ui gayyar ƙawayen su irin su yan gayu kirari kawai suke yi mata tun da kusa damu suka zauna a haraban gidan in da aka saka kanofi da kujeru. Su Ma’u ana gefe ba karsashi to ta ga iyayenta a kinibibi dole ta koma baya.

    Gimbiya suke ta raba takeaway da snack a ciki da naman kaza sai ruwa da lemu. Da ta zo wajen ƙawayen na su sai shewa ya hau ta shi ana yi mata kirari.
    “Ka ga Saudatu sa’ar mata. Gimbiya kike sunan ki ne. Kuma kin cika Gimbiya a zuciyar Injiniya Yusuf Tafida. Takawarki lafiya giwar Tafida. Takawarki lafiya Amaryan Tafida. Takawarki lafiya uwar maza a gida ko da kika je an haihu amma ke da kika tashi sai kika yi irin haihuwan da ba a taɓa yi ba. Ka ga uwar maza a gidan Alhaji Yusuf Tafida. Ko gobe aka sake masa haihuwa ba za a kwantata irin ta ki ba”

    Sai suka buga shewa ta miƙa hannu suka tafa ta jiya musu kugu kafin ta ce” Wallahi ko gobe aka sake masa haihuwa ba za ta kama kafar irin tawa haihuwar ba faɗi ki ƙara.”
    Ta faɗa ta na wani fari da ƙara juyawa.
    “Takawar ki lafiya ki juyi dai Gimbiya a girman ki ne. Kin ci lokacin kuma za ki ci na wasu in sha Allahu kuma daga kanki ba ƙari kin cika duka gurbaben mata huɗun nan”
    Sai kawai ta ɓalle jaka ta fara zazzaga ma mai yi mata wannan kirarin kudi suna ta ihu da shewa sai hankula duk ya koma kan su.

    Duk da Maganar suke yi amma ko waye ya ji ya san magana ce mai harshe damo ko na ce habaici.
    Hauwa ta kalleni ganin na yi shuru kawai ina zaune.
    “Kamar fa da ke suke. Wai ko da ta zo an haihu amma ba a yi kamar irin ta ta ba”
    “Kuma wai ko da an sake haihuwan ba za a sake irin ta ta ba”
    Munnira ta amshe itama.

    “Da Sadiya fa suke yi. Shi ya sa na tsani Gimbiyar nan munafuka ce baƙn ciki take yi kin samu ciki ta so ne ita ta yi ta haihuwa ke kuma ki zama yar kallo.”

    Hauwa ta saki tsski kafin ta ce” Wallahi haka ne ma. Sai kin ji mganganun da take zuwa gida ta na yi. Ta yi ma Tafidan da Dangin sa haihuwan da ba a taɓa yi masa ba. Tun da ta haifi maza har ji fa na yi wai ta ce yadda ya ke son su Khalipa ko su Jidda albarka.”

    “Ka ji sakarya. Ya fara samun su Jidda? Ai wallahi ƙarya ta ke yi.’

    Baƙin ciki suka hana ni mgana amma na daure jin Munnira ta ce wallahi za ta tashi ta je ta yi musu mgana sai na riƙe ta ina faɗin” Rabu da su so suke a tanka a yi wani abu kuma ace ba mu da gaskiya ku ƙyaleta. In za ta je ta faɗa ma duniya cewa Yallabai ma ya fi son ta a kaina ni bai dame ni ba. Fatana na sauka lafiya.”

    “Allah ya sa ki haifi namiji na ga ta tsiya.” > Janaftybaby: Sai na yi mirmishi ina tuna wayar da na yi da Dr. Aisha AKTH. da na faɗa mata ina da ciki ta yi murna karshe ta ce Allah ya kawo boy ni kuma na ce mata ko boy ko girl duk wanda ya Allah ya bani ina iso.
    Yanzu ɗin ma cewa na yi.

    “Ko namiji ko mace duk wanda Allah ya ba ni iso.”

    Suna kallona sai na kaɗa kai kafin na ce” Ni ba ruwana da jinsi Ni ko duka mata zan tara ina so. Ita haihuwan maza ke gabanta.”

    Daga nan na kashe maganar. Amma har Suwaiba sai da ta zo wajen mu ta na zagin Gimbiya a cewarta ni ban yi kishi da ita ba ita da ta aure mini miji sai ita. Ant Zabba ba ta wajen da ya ke so sun iso har da Amaryan Usman ɗin itama da tsohon ciki za ta yi haihuwa na uku kenan itama kamar Gimbiyar gwarne take yi. Da ta zo wajen mu ta ji ana mai da zence ta yi ta mini masifa ta na faɗin ina da sanyi na daina sanyi da kishiya za ta rika cin kasuwarta a kaina na yi dariya kawai ban ce komai ba.

    Sun yi fa abubuwa Gimbiya da gayya ta ke komai amma ni ban biye mata, sai mangariba a ka tashi sai a lokacin Ant Zuwaira ta zo tana zuwa kuma ta nemo ni ni da Munnira da Anty Zabba ta ce mu shirya da mu za a je Kaduna kai Amarya.

    “Anty Zuwaira ina fama da kaina'”

    “Ai kin ji sauƙi ko ba za ki iya zuwa ba ne?

    Sai na kasa musa mata sai ta buga kafaɗata da cewa” Ku ne matan kawunne manya saboda haka da ku za a je.”
    Sai na ce to Allah ya kai mu Hauwa a ka ce ba za ta je su sai daga baya ba a son a je da yawa ne. Anty Zuwaira ta ce ba da ita ba Anty Maimuna ce da Nasara sai Suwaiba da Halima a yayyen uwa iyaye kenan sai Maman farko da Hajiyar Tafida da ƙanwar baban Sulaihat ɗin a kakkanin Amarya. Sai ƴaƴan yayyen baban ta guda biyu ƙawayenta. Sai a nan aka zaɓo ɗiyar Anty Maimuna sai yar makarantar su guda ɗaya ƙawarta. A Rano kuma an saka yayar Gimbiya amma ita ban ji an saka ta ba sannan har da Faridan Tariq Marwa ma an saka ta ita kaɗai a ce a matan kawun ne. Ana so a yi lamarin da tsari ne kamar da angon ya bukata ba su son cikowa abun ka ga masu kuɗi. An ce matukin jirgin kasa ne Captain akwai kuɗi a hannun shi sannan zuru’an su suna da kuɗi nima duk a bakin Munnira nake ji tsuliyan gari.

    Da na koma gida ni kaɗai yara duk suna can na baro su za su kwana. Sai ga Yallaɓai ba a gidana yake ba sai ya ce Gimbiya da yara can za su kwana sai washegari jumma’a ranar walima muna karyawa ya ce.

    “Za ki iya zuwa kaduna kuwa?
    Ya Zuwaira ta matsa mini sai ke dai kin je.”

    “Nima haka ta faɗa mini jiya. Ni da Munnira da Anty Zabba.”

    Yana kurɓa tea ɗin dake hannun shi a mug ya ce” Na ce ga Daughter tun da ita ce ta ce minibza ta je kai Amarya amma sai ta ce a a dole sai ke tun da ke ce Babba.”

    Ban yi magana ba amma ni kaina na san Gimbiya za ta ce sai ta je kaduna kai amarya yadda ta ke rawan jiki da bikin nan.

    “Shike nan tun da za ki iya zuwa sai ki shirya. Amma please ki kular mini da kanki da Baby na.”

    Ya faɗa ya na mini murmishi.
    Nima sai na yi masa murmushi kafin na ce” Da na ce ko ita Gimbiyar ta je?
    “A’a gaskiya Ya Zuwaira ta faɗa ke ce Babba kuma ke ɗin ce wakiliyata so ke ɗin ya kamata ki je tun da kin ji sauƙi.”
    Sai na gyaɗa kaina ban saka aka ba wallahi.
    Ranar mun je walima ban san me ya faru ba mun haɗu da Gimbiya a ƙofar shiga falon Anty Bahijja ina washe mata baki ta yi kamar ba ta ganni ba ta ɗauke kanta. Har ta na ture kafaɗanta sai da muka shiga ciki ne Suwaiba ke faɗa mini kan tafiya kaduna ne an ce su bari sau ranar lahadi sai su je tare da wasu kayan ita da Naja shi ne ta ce ita tuni su yi mgana da Tafida kuma ya ce za ta je Kaduna. Ita kuma Anty Zuwaira ta ce ni ce zamu tafi da Amarya gobe shi ne ta fita tana ƙunƙuni

    “Topha.”

    Na faɗa a fili a raina na ce ni ban ga abin ɓacin rai ba.
    Munnira ta ce ta raina wayon ta akan kai amarya sai kace zuwa madina?
    Ni dai Allah ya kyauta kawai na ce kuma a ranar sai da Anty Zuwaira ta tabbatar mini da na shirya da ni za a je. > Janaftybaby: Ranar ma ba ta yi mini mgana ba sai fushi take yi tana cika ta na batsewa. Ma’u ta ba ni tausayi da bikin nan kamar ba a santa ba, ita kanta Anty Bahijja ta na fama da mutane ba ta bi ta kanta ba, sai dai tana raɓe wajen dangin mijinta da a ce muna zaman amana ne ni da ita za mu haɗe to da yake ba ta da hali sai ta zama kamar mujiya ga shi Shema ta yi aure da a da ne tare za su zo.

    An sha wa’azi malamai uku aka gayyato mata suka yi ma amarya wa’azin zaman aure da zamantakewa sai mangariba a ka tashi. Yallaɓai ya zo ya ɗauke ni wajen taran dare kuma ko gidan bai shiga ba. Bayan mun koma na ga ya na ta waya abin da ya sa na fahimci da Gimbiya yake mgana saboda maganar da ya yi mata.

    “Me ya sa kike da taurin kai ne Saudatu? Na ce miki ba za ki je ba Sadiya ce babba ita za ta je kuma hakan ne ya kamata.”

    “Ok to ki yi yadda kike so”

    Ya faɗa a fusace ya kashe wayar. Ban taɓa jin ya kira sunanta ba sai ranar, ta kwaɓe musu saboda zuwana Kaduna ni ko da karambani bayan mun kwanta na ga har lokacin bai huce ba sai na ce masa na hakura ya bar ta ta je kawai.

    “Wallahi ba za ta je ba. Ke ma in ba za ki je ba fine amma na riga na rantse ba za ta je ba kuma kin san ba macen da isa ta saka ni na yi kaffaran kan aikin banza da wofi.”

    Ai ina jin haka sai na koma na lafe a kan filo na ji shuru. Shi da kan shi da ya hucen ya matso ni jikinsa lokacin na ma ɗan fara barci ina ƙoƙarin motsawa na ji yana mini raɗa
    a kunni.

    “Sai da safe”

    Ban amsa mishi ba saboda barcin ya fara fizgata. Na dai ƙara shiga jikinsa sosai na lafe shi kuma ina jin sa yana rufe mana jiki da bargo.

    *Janafty*

    Note
    error: Content is protected !!