Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    Washe gari tun safe muka tashi da aikin nama muka soye shi a ka raba a ka ɗibar ma dangin mijin Saude kafin mu haɗa kayan tafiya. Tashar mota ya samo mana tun daga ƙofar gidan Saude a garin Jigawa har zuwa ƙofar gidan su a anguwan Ɗorayi da ke Kano, zuwa la’asar duk muna Kano ni daman muna isowa na shige gidan Gwaggo na yi salla na iske har lokacin Alhajinmu bai dawo ba.

    “Gaskiya Alhajinmu ya ga wuri. Yashe ta yi masa daɗi wannan karon.”

    Na faɗa ina dariya Gwaggo ta ce ai ko wannan karon dai ya daɗe, ni kaina ban samu kiran shi ba sai a lokacin har ya ba ni Baba Aminu muka gaisa da shi yana ta saka mana albarka.

    Ina shirin tafiya sai ga saƙon naman suna da yawa daga gidan su Saude har da omo da sabulu na Gwaggo. Da zan tafi tare da Gwaggo muka shiga gidan ta yi ma Saude barka a nan na bar ta na wuce gida na shiga gida ba daɗewa domin ruwan zafi kawai na ɗora ban ma san me zan dafa ba su Jidda suka dawo daga makaranta kawai sai na sulala mana indomie na haɗa da ƙwai na dafa mana muka ci, tun da yamma ta yi sannan yau Yallaɓai na gidan Gimbiya ba ni da wata matsala.

    Saboda yana neman shiri bayan mangariba sai ga kiran shi, tambayarsa ita ce na dawo? Na ce masa na dawo tun ɗazu sai ya ce mini zai shigo gidan in ya dawo. Ban ma san ashe tafiya ya yi ba sai da ya zo gidan wajajen taran dare, ina ɗakina saboda yana son shirin da gaske har ciki ya biyo ni, muka gaisa shi ne fa ya ke faɗa mini Dutse ya je akwai wani gidan radio da za a gina kuma shi a ka ba ma kwangilar wajen shi ya sa ba ya samun zama ni dai nawa fatan alheri kawai.

    Tare da shi muka fito falo ina ba ma su Jidda naman sunan da a ka bani na gidan su Saude. Tsoka bibbiyu na ba su ni kuma sai na saka sauran tsoka ɗayan a bakina akwai kuma saura biyu a hannuna da ƙashi.

    ” Umma Sadiya. Ni ina nawa naman sunan?

    Ba zato kawai na ji maganarsa ban tsaya nuna masa mamakina ba na miƙa masa sauran na hannuna. Sai dai na shanye mamakin nawa da na ga ya saka hannu ya karɓa har kuma ya ɗauki tsokan da ta rage ya saka a baki ya na taunawa.

    “Lah Abba kai ma kana cin naman suna?

    Baby ta faɗa tana yi masa dariya duƙawa ya yi daga in da muke tsaye a bayan kujerun falon ya lakace mata hanci yana faɗin” E mana. Ai har na ki naman sunan na ci.”
    “Na Ya Jidda fa?
    Ta faɗa ta na dariya.
    “Har na ta ma na ci.”
    “To na Umma fa?
    Sai na kalle shi, nima ni ya kallah kafin ya yi dariya ni kuma sai na kauda kaina na zagaya na zauna saman kujeran da Jidda ke zaune ta na ta duba wani littafin Chemistry ba ta shiga maganar Baby da Abban na ta ba.

    Na ga dai ya yi mata raɗa a kunne tana kallona tana dariya amma ban san me ya faɗa mata ba. Bai zauna ba ya yi mana sallama ya tafi. Saboda gulma har yana zuwa yana sumbatar goshina. Yaushe rabon duniya da ayyarahe? Amma dai ban kushe sa ba, na yi masa yaƙe Baby ce ta raka shi har haraban gida amma daga ni har Jidda muna daga in da muke ko motsawa ba mu yi ba.

    Washegari da safe bai zo ba amma ya kira ni a waya yana tambayan yadda na tashi ni da yara. Na ce masa muna lafiya sai ya ce zai ta fi Dutse sai zuwa anjuma in ya dawo na ce a dawo lafiya. Ranar a gida na yini ina warware gajiya mun yi waya da Anty Laila maƙotan ta na son hijabai sun gani a wajenta da yake ta siya kuma shima Ya Auwal ya siya mata wasu. Nan da nan na ji ciniki na ce ta tura mini colours da simple ɗin irin wanda suke so sai na tura a ɗin ka musu daga can za a tura musu Abujan ba sai an ma an kawo mini shi nan ba. > Janaftybaby: Datti ma mun yi waya amma ni na kira shi ina masa tsiyan tun da ya fara zaman kansa ya daina neman mutane.

    “Kai Ya Sadiya ko kwanaki ba na kira ki ban same ki ba “

    “Uhm kai Datti fita idanuwana na rufe. “

    Sai ya fara dariya yana faɗin” To na ji na amsa laifina a yi min afuwa”
    Sannan na yarda muka gaisa yana tambayan ya yara na ce suna lafiya.
    “Ko jiya sai da Jidda ta yi zencen ka da cewa Uncle Datti shuru kwana biyu”
    “Allah sarki Jiddodi ta na lafiya ko? Ya mganar jarabawarta?
    “Yallaɓai ya ce a wannan shekaran za ta yi har Jamb ma.”
    “Za ta iya ai ta na da ƙwanya mu ta yi gado”

    Dariya na yi shima yana ta ya ni, mun sha hira da shi ya ce ma ƙarshen wata zai shigo garin ba sa samun hutu ne mai tsawo ni ko na ce daman aikin kamfani ai sai mai haƙuri. Ina jin zumunci har Ya Aina na kira da Ya Balki muka gaisa Ya Murja ce da na kira ba ta gida yara suka ɗau wayar Rahila kuma Ya Muntari ya ɗauka ya ce min wayar na hannunsa tun jiya wutar layin su ta lalace wayar ta kwana ba chaji sai ya fita da ita yau ɗin domin ya sa mata chaji bai ma daɗe da kunna wayar ba sai ga kirana. Na dai ce ya gaisheta in ya koma gida ya ce in sha Allahu zai faɗa mata. Amina ce kaɗai da ban kira ba saboda ita ko kafin tafiya ta Jigawa ai mun yi waya. Ma’u kuma daman na yanke alaqa da ita, ba ta kirana ba na kiranta sai dai in mun haɗu a gidajen ƴan’uwa amma dai ban goge lambarta ba kamar yadda nima na ke da yaƙinin ba ta share tawa ba.

    Daga nan na yi ta shige shige na a I. G. Ni kaɗai ban taɓa jin ina jin haushin halina ba sai kwanakin nan ba ni da wata ƙawa Aminiya shaƙiƙiyan da yau in na shiga matsala zan je mata da mgana ta saurareni kuma ta ba ni shawara kamar yadda na ga wasu suna dashi, ni ko ni ɗaya tal ban taɓa ƙawa ba bare ba sai su Munnira su kuma aure ne ya haɗa ni da su duk da mun shaƙu amma akwai wani matsalan nawa da ba na iya faɗa musu saboda shi aure ai sirri ne, kuma cikin kowani aure da zamantakewa akwai matsaloli kowa kuma da irin na shi matsalan. Ba komai ba ne za ka zo kana faɗa akwai wani abun da ya ke buƙatar sakaya. Yau da a ce bani da shigen halin rashin sakin jiki da mutane da yanzu ina da ƙawaye na tuna tun muna makaranta ƙawayen da suka yi ta shige mini ina ba sar da su. Har na zo matakin jami’a yan set ɗin mu sun yi ta shige mini amma na ƙi ba ma kowa fuska har Maijidda ma ta layin mu ta so ni har muka haɗu a jami’a da ta ga dai ba na yi da ita sai ta kama kanta.

    Ta yi aure a cikin garin Kano nan amma ban taɓa zuwa gidan ta ba na dai je bikin da Rahila ta matsa mii kuma har gida Maijiddan ta kawo min IV da mintin gayyata. Kaf waɗanda muka yi karatun jami’a da su ba na zumunci da kowa. Wasu ina ɗan kiran su a waya jaje ko murna shima na zo na daina daga baya nima tun suna bina har kowa ya rabu da ni ina dai cikin group ɗin kuma ina ganin ana ta abubuwa in sha’ani ya tashi na ɗayan mu a haɗa kudi kuma a je, ni dai na kan ba da wani lokaci amma zuwa ban taɓa yi ba. Sai dai in ga ana turo hotuna suna zumunci su amma ni na ware kaina kamar saniyar ware. Ban taɓa jin abin ya dame ni ba sai yanzu amma a ƙasan zuciya na ƙudiri a raina nima yanzu zan nemi jama’a domin na fahimci jama’a rahama ne.

    Ranar ma sai dare Yallaɓai ya zo gidan kuma again a ɗakin barcin mu ya sameni ina ta rubutu.

    “Madam wai labarai kika fara rubutawa ne?

    “Me ka gani?

    Na ɗago ina kallon shi bayan na dakata da rubutun da nake yi. Gyara zama na yi a gefen gadon lokaci ɗaya ina gyara zaman doguwar rigar material ɗin dake jikina.

    “To gani na yi kwanan nan kina ta faman rubuce rubuce.”

    Kallonsa na yi ina tuna yaushe ne ya ganni ina rubutu? Ni dai ina tunanin wannan ne na biyu amma zai ce wai kwanan nan ya na ganina ina rubuce rubuce.

    “Kawai abin kasuwanci ne. Ina rubuta waɗanda suka karɓi hijabai ne.”

    “Da kyau Hajiyar Business”

    “Ya Hanya?

    Sai na kau da maganar ganin duk ya gaji daga yanayin ma yadda ya ke mgana.

    “Lafiya lau. Amma na gaji sosai”

    “To ka zauna mana.”

    Na faɗa ina nuna masa gefen gado saboda na ga yana tsaye kuma ga shi ya ce ya gaji.”

    “Bari kawai na ƙarisa gida na yi wanka na huta gabaɗaya.”

    “Kuma fa haka ne.” > Janaftybaby: Na faɗa ina kau da tunanin ya ƙi amsar ta yi na ne. Ni fa taimakon sa na yi ganin ya ce ya gaji kuma yana tsaye kamar wani dakaren soja.

    “Maganar mu fa Sadiya?

    “Wacce magana?

    Na tambaya ina kallon shi.
    Sai ya gyara tsayuwa yana mai harɗe hannayensa a ƙirji kafin ya ce.

    “Mganar da na ce in kika dawo za mu yi. Domin mu warware rashin jituwan dake tsakanin mu.”

    Sai na yi mirmishin takaici kafin na ce” Muna gabar ne har yanzu? Ai ina jin kamar mun warware komai.”

    “A’a.

    “To me ya yi saura?

    “Komai ma.”

    Ya katseni ya na mai tsareni da idanuwansa.

    “Kin daina gaba da ni amma kuma kin ƙi komawa kamar yadda kike a baya Sadiya.”

    “Mun daina gaba da juna za ka ce ko?

    Ya na kallona na cigaba da faɗin” Tun da kaima ba ka yi mini magana Yallaɓai.”

    Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce” Duk na ji na amsa laifina shi ya sa na ce mu zauna mu yi magana domin mu fahimci juna.”

    “Na ji za mu yi in sha Alkahu.”

    Na faɗa ina ƙokarin komawa in cigaba da rubutuna.

    “To yaushe?

    Sai da na ɗago na kalle shi ido na cikin ido sannan na ce.

    “Sai ranar da na karɓi girki.”

    Murmishi ya yi kafin ya ƙariso gaba na ban yi aune ba kawai ya ɗan rankwafa ya sumbaci laɓɓana kafin ya miƙe ya fice yana faɗin.

    “Sai da safe Sadiya ta.”

    “Sai da safe.”

    Na amsa masa a saman laɓɓana bayan fitan shi har ina shafa wajen. Yaushe rabon da a yi haka! Tun kafin faɗan mu da shi a kan Khalipa. Yaron na raina ina son tambayan shi amma na fasa tun da ya nuna min iyakata ya je amma ƙaunar da nake yi ma jininsa ba zan fasa saboda shi ba, ko faɗan mu ne ya sa kwana biyu tun da na dawo bai tarkatomun Khalipan ba, amma na ƙudiri niyyar in na ga ba a kawo shi ba zan kira Gumbiyar na ce ta kawo shi ya yi mini kwana biyu na saba da shi duk da ɓarnar shi, shi kuma na san ya yi sabo da gidana sosai kawai dai kwana ɗaki ɗayan da Yallaɓai ya tsiro da shi na ga ana cutata shi ya sa na yi magana amma ba da niyyar Khalipa ya daina zuwa ba tun a baya ban hana shi zuwa ba sai yanzu?.

    **

    Tun da yau Yallaɓai zai dawo gida na na kira Maman Nana na ce in ta samu lokaci ta zo ta yi mini kitso. Da safen ko ta zo ta yi min 2step ƙananu. Kuma kitson ya yi kyau tun da na duba a cameran waya ta na gani. Sai azahar ta tafi bayan na yi mana girki duk dai macaroni na dafa mana muka ci da ranar. Bayan tafiyan ta na gyara gidan na yi shara na saka turare ɗan kwanciya na yi na ɗan huta zuwa la’asar na tashi bayan na yi sallar la’asar
    Sannan na ɗora ma su Jidda girki da man macaronin guda ɗaya na dafa.

    Cous-cous na dafa mai kayan lambu daman kuma Yallaɓai na so shi ya sa na yi. Sai zoɓon da na haɗa daman tun safe na riga na dafa genyen zoɓon haɗawan kawai na yi. Sai sauran kayan marmarin da suka rage mana na yanka na yi mana fruit salad ni da Yallaɓai.
    Shidda saura su Jidda suka dawo makaranta ajaran majaran saboda yunwa ko uniform ba su cire ba suka fara cin abinci. Baby na faɗa min Umma cikina kamar an kwashe min kayan cikina ina gefe ina ta yi mata dariya ganin tana cin abinci hannu baka hannu ƙwarya.

    “Baby ki ci a sannu kar ki shaƙe.’

    “Umma ba ki san yunwan da na ke ji ba ne”

    Ina ta mata dariya ni na je na kawo musu da zoɓon ya yi sanyi na saka a firiza.

    “Ya Jidda ke ma duk yunwar ba baka sai kunne?

    Sunne kai ta yi ta na faɗin.

    “Umma ni kin ji na yi magana ne?

    “Ba ki ce komai ba. Ke dai ci abinci kawai.”

    Na faɗa ina yar dariya. Yarinya na jin yunwa tana noƙewa.

    Bayan sun gama cin abincin sun ƙoshi, suka sauya kaya zuwa na gida lokacin an kira salla sai muka yi alwala muka yi salla yau ba mu yi karatu ba saboda wankin uniform muka fita ta baya muka wanke su tare da yan riganunan barcin Baby da ƙananun wandunan ta daman Jidda ke wanke musu tare da na ta. Muna gamawa ana kiran sallar isha’i muka sake ɗauro alwala muka yi sallar isha’i. Muna idarwa ni kuma na faɗa wanka bayan na fito na yi gayu na cikin riga da zani na wata atamfata hollond ta na cikin kayan da na siya lokacin auran Yallaɓai da Gimbiya. > Janaftybaby: Na kashe ɗauri na ture ka ga tsiya na ba za gashina ya sauko har kafaɗuna. Har da su jan baki na saka na kuma zirara gazal a girana, na fita falo wajen yara da dai na ga shuru Yallaɓai bai shigo ba sai na diɓi abincina na ci na kora da zoɓo da fruit salat. Bai kuma shigo ba sai goma har ta ma gota. Tuni har na kaɗa su Jidda ɗakin su na ce su yi shirin kwanciya so ni kaɗai ya iske zaune a falon ina kallo duk da hankalina ba akan kallon yake ba.

    Miƙewa na yi ina kallon shi, nufar sa na yi ganinsa da ledoji a hannunsa.

    “Sannu da zuwa.”

    Na faɗa ina karɓan ledojin hannunasa.

    “Yauwa Madam ya gidan?

    Ya faɗa lokaci ɗaya yana sakar min ledojin a hannuna.
    Na amsa da lafiya lau lokacin da na nufi kitchen na duba ledojin tsire ne sai fura mai sanyi an dama ta a leda. Na san ni ya siyo mawa da yake ya san ina son fura duk da cikina ya cika amma ta ba ni sha’awa zan sha zuwa anjuma in cikina ya sassaɓe.
    Naman dai a firiza na saka shi da safe sai mu ci na san na mu ne Yallaɓai ba ya son tsire ya fi son gashi na naman rago. Sai ya ce wai tsire duk ƙuli ne ba nama ba.

    Ko da na fito ba shi a falon ya na ciki sai na koma kitchen ɗin na hada masa abinci na kai dining sai da na gama shirya masa duk abin da zai buƙata sannan na koma bedroom ɗin na iske Yallaɓai ya fito daga wanka ya na saka sauƙaƙƙun kayan zama cikin gida riga da wata ƙaramar riga mara hannu. Sai ma yau na ƙare ma Yallaɓai kallo da gaske kam Yallaɓai ya fara ijiye tumbi da na ƙura ma gashin kansa ido har na hango ƙyali ƙyalin furfura a saman kan shi har ma da sajen shi. A raina na ce su Yallaɓai tafiya ta fara miƙawa.

    “Tunanin me Sadiya ta take yi ne ahalin ga ni a kusa?

    Ya faɗa ya na mai sagalo hannun shi a kafaɗana sai na tattaro murmushi na kalle shi na yi masa.

    “Abinci.?

    Na faɗa ina kallon shi sai ya shafa cikin sa yana faɗin daman yunwar yake ji. Ya ƙi sakina ya na dafe da ni muka fita can falo sai da zai zauna saman kujeran dinning ne ya sake ni.
    Nima gefen sa na zauna na zuba masa cous-cous ɗin da zoɓo sai fruit salaf ɗin sai ya ce na zuba masa leda ɗaya na fura yana so zai sha sai na koma kitchen na juyo masa a wani ƙaramin mug. Ina gefen shi har ya gama cin abinci kuma daga yanayin sa na fahimci ya ji daɗin haka. Barin ma yadda na ga ya ci abincin sosai da alamu dai yau Yallaɓai ya yi ta su Baby ta babuwa ta addabi cikin sa.

    “Girki ya yi daɗi. Haka ma mai girkin ta yi kyau.”

    Ya faɗa ya na kallona sai na yi murmushi k amma ban ce komai ba.

    Bayan na tattara abubuwan da ya ɓata na mai da kitchen ina dawowa ya ce wai kallo za mu yi, kujera mai zaman mutum biyu na samu na zauna amma Yallaɓai sai da ya biyo ni ya nane minI, ina basarwa ina komai karshenta dai sai gani a saman jikinsa kamar yadda muke yi a baya in muna kallo. Ɗankwalin kaina ya zame min yama ta wasa da gashin kaina shi ke kallon ni kuma na kwantar da kaina kawai a saman ƙirjinsa ina tunanin rayuwa juyi juyi. Yanzu fa yadda nake yi da Yallabai haka itama Gimbiya take yi da shi gabaɗaya sai na ji ƙuncin zuciyata ya dawo. Har wani gishiri gishiri na ji miyan bakina na yi saboda takaici ina jin sa yana ta ɓabatun magana amma ban biye masa ba.

    “Ƙitson nan ya yi kyau. Yaushe a ka yi shi?

    “Yau.”

    Na bashi amsa kai tsaye.

    “Lalle ko za ki karɓi tuƙwaici domin kitson ya yi kyau sosai.”

    Ya gama faɗa sannan ya sumbaci kaina.
    Ni ko mgana ban yi ba ganin haka ya sa ya leƙo fuskata yana faɗin” Kin yi shuru?
    “Me zan ce?
    “Komai ma ki ce Sadiya ta.”
    Sai kawai na yi masa shuru saboda ni ai ya gama shanye ruwan kaina ba wani sauran abin da zai yi mini da zai kankare mganganunsa a wajena suna nan damfare a ƙasan zuciyata sun yi min tsataa.

    Ganin kamar ba ya jin barci ya sa na fara yi masa hamman ƙarya na ce ina jin barci dole ya kashe kallon muka koma bedroon ɗin mu amma ni na fara yin gaba shi kuma ya tsaya duba yara sannan ya kashe wutar duka ɗakunan kafin ya shigo har na yi shirin kwanciya amma ban kwanta ba. Na saka wata doguwar rigar barcina mai taushi. > Janaftybaby: Ina shafa humra a wuyana da hannayena ya shigo. Shima dai tiolet ya shiga ya kama ruwa ya wanke baki sannan ya dawo ya tuɓe riga ya kuma tuɓe wando da ga shi sai gajerun wando ya hau gadon a gefena maimakon ya yi nashi ɓarayin sai ya mirgino har kan filona ya tsoma na shi kan

    Muka yi shuru ni da shi, muna kallon rufin dakin da hasken wutar tun da bai riga ya kashe ba.
    Juyowa ya yi ya na kallona ni kuma da sauri na ce” Ka rage mana hasken wutar mana.”
    “Ba yanzu ba.”
    Sai na ƙura masa ido kafin na samu sararin magana ya cigaba da faɗin.
    “Sai mun yi maganar mu.”
    Na kalle shi amma ban yi magana ba sai na ga ya miƙe zaune nima ya umarce ni da na tashi ba ni da mafita dole na mike zaune a saman gadon muna kallon juna.

    “Sadiya”

    “Na’am.”

    Na amsa mishi kamar yadda ya kira sunana.

    Sai kawai na ga ya kama duka hannuwana ya jimƙe cikin tafukan hannayen shi.

    “Ki faɗa mini duka abin da na yi miki da ya ɓata miki rai ni kuma na yi miki alƙwarin zan ba ki haƙuri.”

    Ya faɗa yana murza hannayena sannan kuma yana mai tsareni da ido.

    “Ni fa ba komai. Komai ya wuce.”

    “Bai wuce ba.”

    “Allah na ce maka ba komai ba sai ka ba ni haƙuri ba.'”

    “Me ya sa kike haka ne?

    Ya faɗa ya na tsareni da idanuwansa a kaushashe ya cigaba da faɗin.

    “Fahimtar juna nake so mu yi Sadiya. Ni dake ba shekaranjiya muka faro rayuwar nan ba, ba kuma jiya ba ne, ba kuma yau ba ne. Sabo da haka maganar komai ya wuce ni dake mun san ba haka ba ne ko?

    Ya gama faɗa ya na mai tsare ni da idanuwansa kuma ya kama hannayena ya riƙe ba halin na ƙwaci kaina.

    “Haka ne”

    “To ki yi magana domin mu fahimci juna.”

    “Na ce ba komai fa”

    Na faɗa ina kauda kaina sai ga shi ya saka hannu ya dawo da fuskata zuwa in da yake.

    “Ni na san akwai komai fa”

    “To mene ne? Komai ya wuce tun da na haƙura ga shi ni da kai muna zaune a waje ɗaya.”

    Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce” Komai bai wuce ba. Saboda na yi miki mganganu ranar marasa daɗi kuma na san har ga Allah ke ma ranki ba zai yi miki daɗi ba.’

    Ashe ya san abin da ya yi? Shima ya san bai kyauta ba! A lokacin ya sani ko sai yanzu daga baya.”

    “Raina ne ya ɓaci a ranar har na kasa fahimtar ki sai daga baya da na zauna na yi tunani sai na fahimci ni ne ban kyauta ba sannan na yi miki rashin adalci.”

    Ƙura masa ido na yi, hawaye suna taruwa a ƙwarmin idanuwana. Maganganunsa na baya suna mini amsa kuwwa kamar a lokacin yake faɗa mini.

    “Na yi kuskure. Kuma na gane kuskure na don Allah ki yi haƙuri ki manta komai.”

    “In manta komai fa ka ce?

    Na katse shi cikin rawan murya.

    “E ki manta na ce. Ki ɗauka na faɗa ne a fatar baki amma ba har cikin zuciya ta ba.”

    “Har gorin haihuwan da ka yi mini Yusuf? Har cewan da ka yi ina baƙin ciki da Gimbiya da ƴaƴanta? Har goran ta mini da ka yi na cewa ba kai ka ce na je na yi planning ba ni na saka kai na? Har shi na manta har shi kake so na manta kamar komai bai faru ba?

    Sai ya kasa mgana na ƙura masa ido, amma ya dukar da kaina ya na faɗin

    “Ki yi haƙuri ɓacin rai ne.”

    “Sai ɓacin rai ya sa ka yi mini gorin gida Yallaɓai?

    Na faɗa ina mai kecewa da kuka. Kukan da ke taso mini daga ƙasan zuciyata. Kukan sanadin rasa gudan jinina kukan ɓacin rai da baƙin ciki da mganganun Yallaɓai suka dasa min a cikin zuciyata.

    “Ka rufe idanuwan ka. Ka manta da ko planning ɗin da na yi da amincewar ka na yi. Kuma in da na tara sanin haka zai faru da ni zan yi har jawo mini matsala ne? Kuma ka sani ko ban yi ba in Allah ya ce Jidda da Baby kaɗai ne rabona na ƴaƴana a nan duniya ba ni da yadda zan yi kokawa da kaddara ta. Kuma ka ce ina baƙin ciki da Gimbiya da ƴaƴan ka, wannan kam sai na ce ba ka yi mini adalci ba ban taɓa zama da matarka da wata zuciyar ba sai zuciyar musulunci su Khalipa kuwa ɗaya suke da su Jidda a wajena. Amma rana ɗaya kuskure kaɗan da kai ne ka yi amma ka rufe idanuwanka ka ce ba na son jininka. Sannan daga ƙarshe ka yi mini gori. Gorin nan gidan uban su khalipa ne ni kuma ba gidan ubana ba ne.'”

    Na dakata ina shessheƙan kuka ina ji ya na damƙe hannayena da ke cikin na shi alamun rarrashi amma bai hana ni kuka ba.

    Na nuna saitin zuciyata ina cigaba da faɗin. > Janaftybaby: “A nan mganganun ka suka yi min illa. Ban taɓa tunanin irin ta ka martabawan ba kenan Yusuf. Na ɗauka ni ina da ƙima da karamcin da za ka guji faɗa mini kalaman da za su sosa mini rai in har kana yi min karan shekarun da muka shafe ni da kai muna zaman aure. Ni da kai mun wuce karnin soyyayya mun koma abu ɗaya. Abu ɗaya Yallaɓai.”

    Na ƙarishe ina mai cigaba da kukana sai na ji kamar lokacin ne ma lamarin yake faruwa.

    “Ki yi haƙuri. Sharrin sheɗan ne.”

    Ina jin sa amma ban yi magana ba ina cigaba da kukana, sai ga shi ya matso kusa da ni ya rumgumeni ya na faman lallashina.

    “Am sorry.”

    “Ki yi haƙuri don Allah ki yafe mini Sadiya ta.”

    Sai kawai na ƙara karfin kukana ina ƙokarin ƙwace kaina daga riƙon sa amma shi bai sake ni ba.

    “Wallahi ni kaina na azabtu da kalaman da na faɗa miki. Sharrin zuciya ne.”

    Hannayena na saka duka biyu ina dukan shi a ƙirji lokaci ɗaya ina kuka har da sheshesheƙa.

    “Sharrin zuciya ne ya sa ka yi min goron haihuwa? Ƴaƴana biyu fa, ko a haka Allah ya bar ni na gode masa kuma ko garke Gimbiya za ta haifa maka wallahi ni mai farinciki da haka, ban taɓa jin zan yi baƙin ciki saboda ka samu ƙaruwa da wata matar ba ni ba. Illa ni mai farinciki be ina cewa jinin ka jinina ne, duk ɗaya na ɗauke su da su Jidda. Amma kai zuciyarka ta saka maka bambamci Yusuf.”

    Na faɗa ina ta dukansa ta ko’ina kuma bai hana ni ba sai da na gaji don kaina sannan na lafe a jikinsa na yi laushi.

    “Ki yi haƙuri ina mai neman afuwarki.”

    Ya yi ta nanata na yi haƙuri har sai da muryansa ta dishashe nima nawa ya daɗe da disashewa saboda kuka.

    Ɗago kaina ya yi ya na share mini hawaye.

    “Ba zan ƙara ba. Kin ji ko?

    Ya faɗa ya na matse mini fuska sannan ya sumbaci goshina.
    Sai kuma ya gangaro wajen laɓbana ya na sumbatata. Ban buɗe masa bakin ba sai na datse shi kuma sai ya kalleni ya na faɗin” Ba ki maraba da ni ne? Ko ba ki haƙura ba ne?

    Ina kallon shi saboda akwai hasken a ɗakin shima ni yake kallo na tsawon wani lokaci.

    “Na tsufa Yallaɓai me za ka ji in ka maraban ce ni?

    Ya buɗe baki da sauri zai yi magana na yi saurin rufe masa baki da hannuna guda ɗaya.

    “Yaushe rabon da ka neme ni mu yi ɓarnan ruwa? Na tsufa ko? Ko na ƙafe ne yanzu babu danshin ruwa?

    Na faɗa ina zubar ƙwalla da sauri ya fizge bakin shi, yana kallona na buɗe baki na yi magana ya damƙe bakina ya shiga sumbata na da karfi da karfi lokaci ɗaya yana sabule min rigar barcin da ke jikina.
    Sumbatata yake yi da zafi zafi tun ina tamke bakina har dai na saki na ba da kai bori ya hau. Bai saki bakina ba sai da ya kai ni kwance bayan ya raba ni da rigar jikina.
    Ina haki ya na haki, ya dakata ya na kallona. Ya yi wurgi da gajeren wandon da ya cire daga jikinsa. Ni da shi naked muna kallon duka jikin mu abin da ba mu taɓa yi ba in za mu ribaci juna sai a cikin duhu ba mu taɓa kaɗaicewa da juna cikin haske irin na yau ba.

    “Ni za ki faɗa ma kin tsufa Sadiya? Ni na ɓare ki a leda kina ƴ’ar yarinyar ki. Ni ma ke kika ɓare ni a leda ina saurayina. Sadiya ko wajen babu danshin ruwa ni Yusuf zan da dasasa shi har sai na ɓulɓulo da wannan danshin”

    Ina shirin mgana ya saka nauyin ƙirjinsa ya danne ni. Lokaci ɗaya ya na haɗe nipples ɗin sa da nonuwana. Har tsakiyar kaina na ji abin ban dawo hayyacina ba na ji ya ƙara kama bakina, komai da zafi zafi yake yi mini alamun yau in na shiga hannu sai na gane ba ni da wayau. Ai ko na gane domin da gaske ya ke ko ba danshi sai da ya ɓulɓulo da wannan danshi na yi ta zubar ruwa. Ranar ba in da Yallabai ba lashe a jikina ba hauka ne kawai ban yi ba amma har ihu sai da ya sakani, kusan fa famshe duk kwanakin sa ya yi, da ya sauka muna gama sauke numfashi sai ya sake damƙo ni da na fara masa magiya sai ya ce ai na ce wajen babu danshi to danshi ya ke so ya ɓulɓulo mini da shi.

    Da hasken wutar lantarki muka yi komai yana kallona ina kallon shi ni da na ji nauyi sai na runtse idanuwana muka daina haɗa ido da shi bai ƙyale ni ba sai da ya ce na yarda ban tsufa ba? Na yarda ko mun tsufa za mu iya samo wannan danshin ruwan na ce masa na amince sannan ya sarara mini sai da na yi gashi. > Janaftybaby: Dukkan mu sai da muka tsarkake jikinmu muka saka wasu kayan barcin muka koma muka kwanta maƙale da juna. Zuciya ta yi sanyi duk haushin da nake ji a kan Yallabai ya tafi ban ma san in da fushin na wa ya je ba, amma na danganta haka da yadda ya fahimci ya yi laifi kuma ya ba ni dama na yi magana ya ba ni haƙuri.
    Barci muka yi cikin salama makale da juna wanda mun daɗe rabon mu da wannan yanayin.

    Ko bayan sallar asuba sai da Yallaɓai ya sake biyo danshin nan ta bakin shi, bayan mun gama ne muna sauke numfashi ba mu ma tsarkake jikin mu ba a lokacin kaina na saman hannunsa na hagu da ya rumgumo ni da shi.

    “Yallaɓai.”

    “Uhm”

    “Ranar da na je kaduna.”

    “Uhm”

    Ya sake faɗa kamar mai jin barci.

    “Na samu miscarriage”

    “Uhm”

    Sai kuma na ga da sauri ya mike zaune har ya na wancalar da kaina sai kuma ya saka hannu ya ta da ni zaune ina mai danne kafaɗuna da duka hannayen shi guda biyu.

    “Me kika ce”?

    Ina murmushi na ce” Na ce na samu ɓari a kaduna. Cikin wata ɗaya ne ni kaina ban san dashi ba sai da ya fita.”

    Ƙura minI ido ya yi kafin ya ce” Da gaske kike yi Sadiya?
    Ya faɗa da wani irin murna a muryansa.
    Sai na gyaɗa masa kai alamun haka ne sai kawai ya rumgumeni ƙamƙam yana faɗin.
    “Alhamdulillah.”
    “Ka ji abin da na ce da kyau Yallabai?
    Na faɗa ina tantama in ya fahimci na ce ɓari na yi.

    Sai da ya saki rumgumar da ya yi mini ya na kallona sannan ya riƙe hannayena yana dariya ya ce” Na ji da kyau. Kin yi barin ciki ko Sadiya?
    Sai na gyaɗa masa kai sai kawai ya ce” Ina farincikine ne a ƙalla dai ina da yaƙinin za ki sake haihuwa zan sake ganin ki ɗauke da cikina Sadiya”
    Murnan da ya yi ta ba ni mamaki ban taɓa tunanin zai yi murnan in na ƙara samun ciki ba.

    “Na yi kewar laulayin ki. Fushin ki in kina da ciki na yi kewar ganin kumbararun kafafuwanki. Na yi kewar ganin cikin ki ya turo Sadiya. Ina kewar ganin kina shayar da Baby everything da kika sani ina kewar shi a tare da ke”

    Hawaye suka cika min ƙwarmin idanuwana.

    “A ƙalla yanzu zan ta saka hop. Sannan zan ƙara dakewa ko?

    Ya ƙarishe faɗa yana mai shafa jikina.
    Shi murna kawai yake yi.

    “Kai ba ka jimamin rashin cikin da muka yi?

    Sai sannan ya ɗan sauya fuska kafin ya ce” Na yi jimami sosai amma me ya fitar da shi? Wannan tafiyar da kika yi ranki a ɓace ko?
    Ban ba shi amsa ya saka hannuna ya ɗan mari kan shi yana faɗin” Ni ne ko ? Ni ne ko? Sai kuma ya koma ya kwanta a kan cinyata ta wajen cibiyata ya na faɗin” Ni ne na ɓata ma Umma rai, laifina ne da ya sa muka rasa gudan jinnin mu. Sadiya ki yafe mini”

    Ya faɗa lokaci ɗaya ya na rungumo cikina zuwa kuguna.
    Sai na shafa kan shi cikin tattausan lafazi na ce” Ba laifinka ba ne daman can Allah ya yi ba mai zama ba ne.”

    “Kuma Allah zai ba mu wani ka ji ko?

    Sai ya ɗago ya na kallona kafin na gyaɗa masa ina faɗin” In sha Allahu. Kar ka damu.’
    Sai ya sake komawa ya kwantar da kansa a cinyata yana faɗin” In sha Allahu ma ya bi cikin danshin ya shige.

    “Me?

    Na tambaya ina kallon shi.

    Cikina ya shafa kafin ma ya yi magana na samu amsana sai na samu kaina da amsa wa da Allah ya sa. Duƙawa na yi da kaina na sumbaci goshin sa.

    “Ina ƙaunarki Sadiya ta.”

    “Nima haka.”

    “Kema me?

    “Ina sonka Yallaɓai na.”

    Na faɗa ina yi masa murmishi, shima kallona ya ke yi cike da so da ƙauna.
    Muna wannan kwanciyar ta soyayya na zayyane masa abin da ya faru a Kaduna da kwanakin da na yi a gadon asibiti.

    “Ban ji daɗi da ba ni na wahala da ke ba.”

    “Haka Allah ya so.”

    “Allah ya saka ma Amina da mijinta da alheri.”

    “Amin Amin.”

    *

    Shike nan faɗa ya ƙare tsakanina da Yallaɓai ni da na ce ko na yafe masa ba zan manta ba sai gashi tuni na manta na kama mijina gam mun fi ma baya ɗinkewa da nuna ma juna soyayya. Jidda kam ta na lura da mun shirya ranar har tsiya ta yi mini da ta ga na kira mai ƙunshi har gida ta na yi mini buɗe bakin yarinyar sai ce mini ta yi.

    “Su Umma manya an gama fushi da Abba kuma yanzu an dawo ana yi masa kwalliya.” > Janaftybaby: Da na balla mata harara sannan na rakata da daƙuwa sai ta shige ɗaki tana mini dariya. Da Yallaɓai ya dawo sai da na faɗa masa shima dariyan ya yi ta yi kafin ya ce” Ahto da gaskiyan uwata an gama min yanga da jan Aji an ga dai ba wani sai ni an dawo mini.”
    Da ya faɗi haka sai da na maka masa filon da ke hannuna ina kunƙuni ina cewa zan dai yi maneji da shi, shi ko ya ce ko yanzu ya tashi ƙara aure zai samu budurwa ni kuma in na samu tsoho ma na gode Allah domin duk ya gama suɗe danshin haka na yi ta maka masa filo amma bai yi shuru ba sai da ya ƙarisa ai ko ya daku da filon kujera.

    Amina ma sai da ta yi mini shaƙiyanci daga ta kira muna waya ina faɗin Yallaɓai ma ya ce a yi musu godiya ita da Dr.
    Sai cewa ta yi” Ya Sadiya wai kin yafe ma Yallaɓan ne da har kika bashi labarin kin samu ɓari?

    “To ya na iya Amina. Ya yi ta bani haƙuri sannan ya ce sharrin sheɗan ne shi ya sa na haƙura.”

    Sai kawai Amina ta fara mini dariya.

    “Nan fa kika ce har abada ba za ki manta da abin da ya yi miki ba.”

    Cikin masifa na ce” Ai ban ce na manta ba na dai ce na yafe masa. Kuma kowa ai yana kuskure ko?
    Ganin ta mai da ni mahaukaciya ya sa na kashe wayata ina masifa. Ni kaina ina mamakin yadda duk yadda na kai ga ƙullatan Yallaɓai da ya zo ya lallasheni ya ba ni haƙuri shike nan sai na ji na haƙura sannan na manta da komai mun cigaba da rayuwarmu kamar komai bai faru ba.

    Ganin mun shirya ya sa na ce ya dawo mini da ɗana Khalipa. Ya na jin haka washe gari sai ga Gimbiyar ya kwaso mini ita da yaran gabaɗaya. Nan suka yi mini yini, har dare muna tare ranar kuma Yallabai ya na gidana ne daddare muna falon Yallaɓai yaran kuma suna falon su sai ga Baby ta zo kawo min ƙaran Khalipa wai yana mini tsalle saman kujera.

    “Ƙyale shi Baby shima gidan su ne ki bar shi ya shaƙata”

    Yallabai ya gano mgana na tusa masa ita kums sai ta miƙe tana faɗin don ya na gidan su ai ba za a bar shi ya yi ɓarna ba. Da motar ta ta zo bayan isha’i ta tuka kanta da yara suka koma gida Khalipa da na ce a bar mini shi ta ce jibi za su tafi Rano ganin kamar ba ta son barin na shi ya sa sai na ƙyaleta Yallaɓai kuma na ji amma bai yi mgana ba.

    Sai da muka yi shirin kwanciya sannan Yallabai ya yi maganar akan maganar da na yi ɗazu a kan Khalipa.

    “Laa Allah ni ba da wata munafa na yi mganar ba.”

    “Uhm to shike nan tun da kin ce haka.”

    Da haka a ka bar maganar amma na ji sanyi a raina tun da ya fahimci in da magana ya dosa. Ni dai ban san ya abin ya ke ba amma ranar da Khalipa ya zo gidana zai kwana da ya yi barcin uban ya kai shi ɗakin su Jidda ya kuma ce ko zai yi kukan jini su bar shi in ya gaji zai kwanta. Sai ga shi ranar barcin mu ka sha, sai da safe Jidda ke faɗin ya tashi yana rigima ya na kiran sunan Abba da ya ga an yi banza da shi ne ya koma ya kwanta. Tun daga lokacin na samu lafiyan Khalipa a raina na ce daman iskanci ne da na yi shuru da yanzu an daɗe ana cuta ta.

    Ganin mun samu jituwa da Yallaɓai a wani dare da yana gida na bayan mun gama samun natsuwa sai na ce masa ina so zan koma makaranta.

    “Makaranta? Wata makarantar? Islamiya?

    Yallaɓai ya tambaya cikin mamaki.

    “A’a boko dai. Masters nake so na koma na yi.”

    Kawai ba sai Yallaɓai ya fara mini dariya ba sai ka ce ya ga mahaukaciya sabon kamu nan da nan na harzuƙa.

    “Mene abin dariya a mgana ta?

    Sai ya dakata yana faɗin” Ki yi haƙuri amma mganar ce ta ba ni dariya ke yanzu gotai gotai da ke da budurwan ƴ’a ki ce za ki koma makaranta?

    “To ana girma da karatu ne?

    “A’a kawai dai.”

    Sai kawai ya cigaba da dariyan shi. Na cika na yi fam ina shirin fashewa.

    “Kin ga yi haƙuri.”

    “Izinin ka na ke nema shekaran da za mu shiga nake so na koma.”

    “To ai ni ba zan hana ki ba amma da zan ba ki wata shawara.”

    Sai na kalle shi ta wutsiyar ido duk da akwai duhu a ɗakin amma muna kallon juna ta hasken dake shigowa ta jikin labulan window ɗin bedroom ɗin.

    “Kina so?

    “Ina jin ka”

    Na faɗa a daƙune. > Janaftybaby: “Ki haƙura da karatun nan Sadiya. Digree gare ki fa yanzu mata ne nawa ne ke neman kwalin karatun ki ba su samu ba? Komawa makaranta abu ne mai kyau amma wahala kawai za ki ƙara ma kan ki a yanzu. Saboda ƙwaƙwalwar ba za ki haɗa ta da lokacin baya da na yanzu ba?

    “Wannan ne shawaran?

    Na faɗa ina kallon shi domin so na yi ma na juya masa baya.

    “Shawaran ita ce ki bari kawai na ƙara miki jari ki cigaba da kasuwancin sai da hijaban ki kawai “

    Ya gama faɗa har yana wata dariya. Raina ya ɓaci na ƙufula.

    “Ka ba ni izinin na cigaba da karatun?

    “Why not in kina sha’awa? Sai na ce Allah ya ba da sa’a.”

    “Amin”

    Na fada azafafe sannan na juya masa baya sai ya biyo ni ya na faɗin” To jarin fa?
    “Ba na buƙata”
    “To shike ko kuɗina sun huta”
    Ya faɗa yana mini dariya kara shige min ya yi yana tsokanata da Sadiya ta masu mastars ke dole sai kin kamo kwalin karatuna ina jin sa na yi masa banza domin haushi ya ba ni ya ina mganar cigaba na kuma yana mini dariya.

    Tun daga lokacin ya samu sara da na yi magan sai ya ce su Sadiyallle masu degree da Masters ni ko na ce da ikon Allah, na gane in ina fushi ma ya fi jin daɗin tsokana ta sai na daina nuna na ji haushin shi,
    Maganar jari kuma tun da na ce ba na so bai ƙara mini mgana ba, ni kuma da gasken ba na so shi ya sa ma har su Ya Hamza na faɗa ma zan koma makaranta da na ce Yallabai ya amince fatan alheri kawai suka yi mini. Na gama shirina tsab saboda muna tunkaran sabuwar shekara da cewa ko Yallaɓai bai taimaka mini da sisin shi ba zan kwashe jarin hijabai na koma makaranta da shi.

    ****

    *2020*

    Da gaske na ke yi na nemi gurbin Masters a BUK Kano, kuma har na samu, har na yi cuku cuku, kuma ilai dai bangarena na farko na sake ɗauka na kula da tattalin arziki wato Economics
    Sannan Jidda na son ta biya Jamb tun da sai bayan sun rubuta Jam ɗin za su fara jarabawar su ta WAEC. Ko lokacin da Jidda za ta cike Jamb tare da Musbahu suka je ni ban san ina ta cike ba sai da ta dawo take faɗa minI a first chioce ABU Zariya ta cike.

    “Ni dai ba ruwana kin san dai Abban ku ya ce a garin nan za ki yi karatu ba ya son nesa.”

    “To ni Umma ina son ABU ne kuma ai ba ga Kawu Hamza a zaria ba”

    Kallonta na yi kafin na ce” Ya san da shi ɗin ya ce ba za ki je ba”

    Za ta fara mini magiya na katse ta faɗin”
    Ba ruwana na ma faɗa miki.”
    Ai ko da ya dawo ta faɗa masa ta sha faɗa ya kuma ce mata ta ma cire rai ba anan za ta yi ba BUK za ta yi domin ba ya so ta yi nesa.
    Jidda na ji ta na gani dole ta cire rai tun da Ya ce ba za ta je ba to mgana ta ƙare.

    A she ya je sun yi mgana da Gimbiya itama ta roƙe shi, amma ya ce ya gama mganar sa. Ni daman ban saka baki ba sabo da tun da ya kafe da wahala ya sauya ra’ayi infact nima shirin nawa karatun nake yi Yallaɓai tun ya na ɗauka wasa ne har dai ya ga na miƙe ga kaina. Wasu abubuwan duk ta online Datti ya yi mini su sauran kuma na shiga cikin makaranta na ƙarisa. Da dai Yallaɓai ya ga tabbas na samu addmission har ya na zuga ni wai na yi part-time.

    Ni ko na ce full-time zan yi. Ɗa gare ni ko jika da zan yi part-time sai ya yi shuru. Ina shirin yin rigistration ne Yallaɓai ma ya ba ni kuɗi ya ce na hidimar makaranta ban tambaye shi ba kuma da bai ba ni ba, ba zan tambaya ba.
    Kwatsam kawai aka fara cutar corona a Negeria, daman tun december 2019 cutar ta fara ɓulla a na mganar ta a kafafen sada zumunta.
    Kafin a motsa ta fara yaɗuwa a Nigeria kafin ka ce me an shiga lockdown wannan hutun na corona shi ya ruguza burina na komawa makaranta Yallaɓai sai ya koma yana mini dariya har wani suna ya saka mini wai mai kwalin masters zaman gida dole.

    Sai ga shi da ga ni har yara mun koma mun dafe a gida. Jidda ke ba ni tausayi su da ke da shirin zana jarabawar fita an yi musu tsiya.

    *Janafty* > Janaftybaby:

    Note
    error: Content is protected !!