Turken Gida – Chapter Thirty-two
by Janafty*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*
*BAYAN WATANNI UKU*
Watanni uku sun zo sun shuɗe kamar ƙiftawan ido. A kwana a tashi babu wuya a wajen Allah da haka muke ta cinye kwanakin mu ba tare da mun farga ba. A cikin watanni ukun da suka gabata, ba ƙoƙarin da ban yi domin na manta da abin da ya faru tsakanina da Gimbiya da su Anty Bahijja ba amma na kasa. Duk lokacin da na tuna sai na ji gabaɗaya rayuwata ta yi ƙunci. Sai na ji. . .