Turken Gida – Chapter Thirty
by Janafty*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*
Na shiga gidan Ya Aina ko gani ba na yi saboda tashin hankali da damuwa. Tafe na ke ina jefa ƙafuwana ba tare da na san in da za su faɗa ba. Ya Aina na hanga a ɗan karamin madafinta dake tsakar gida sai ƙannen Marwa na gefen ɗakinta a kan tarbarma suna cin abinci. Ko sallama ma ban yi ba ni dai kawai na shigo kuma na dumfari ɗakin Ya Aina so na ke yi na samu waje ni kaɗai na. . .