Turken Gida – Chapter Twenty-three
by Janafty*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*
Yanzu Gimbiya tana cikin wata biyu ne da tarewa. Zaman su ya fara miƙawa tun ina ganin lamarin kamar wasa har dai daga karshe na saka a raina gaskiya ne sannan zan saba ɗabi'ar haka ta zame min jiki ko domin samun zaman lafiya ta.
In na buɗe wardrope ɗina na ga cikin kayan Yallaɓai kashi uku babu kashi ɗaya a hankali a hankali ya na ta rage su, suna can gidan Gimbiya, bayan kaya ma hatta ma'ajiyar takalman. . .