Turken Gida – Chapter Twenty-two
by JanaftyIna zaune ne amma na kasa tashi domin sai na ke jin gabaɗaya ilahirin jikina na rawa. To in ma na tashi wa zan je tarowa? Kishiya ko miji? Kawai sai na yi zama na amma fa zuciyata bugawa ta ke yi da sauri da sauri cikin lokaci ƙalilan hankalina ya tashi ina neman fita hayyacina saboda wani iri abu na ke ji yana ta so min daga ƙasan zuciyata.
Kishi masifa ne, zai iya haifar ma da mata lalura mai karfin da nan ta ke za a iya kai su emergency a yi tunanin ciwon ya daɗe. . .