Turken Gida – Chapter Twenty
by JanaftyRanar alhamis su Jidda suka yi hutun makaranta. Jidda daman ita ce ta ke ɗaukan first postion a ajinsu Baby kuma Third, sun karɓo kyatuttuka tunda an yi speach and prize giving day ban je ba amma Yallaɓai ya je musu tare ma suka dawo.
Ko da suka dawo mai kitso ta zo, da mai ƙunshi har an yi min ƙunshi saura kitso.
Marwa daman ta na nan domin ni na ce ce ta tattaro, ta dawo wajena sai an gama biki, Amina ma ta iso tun azahar Hauwa da Munnira suna gidan suma tun safe sai zlZaitunan. . .