Turken Gida – Chapter Seventeen
by JanaftyDa sallama na shiga falon hannuna ɗauke da farantin da na ɗora ruwa da lemu tare da ƙananun kofunan glass a saman shi.
Gabaɗayansu a tare suka amsa sallamata ashe Musbahu ne ya kawo ta ya na zaune gefen Yallaɓai a saman kujera mai zaman mutum ɗaya ɗaya. Ita kuma Nene ta zauna akan mai zaman mutum huɗu ne.
Sai da na ja center table ɗin da ke wajen na ɗora ruwan a kai sannan na durƙusa a gaban Nene ina gaisheta ta amsa cikin fara'a lokaci ɗaya ta na ba ni umarni na koma. . .