Turken Gida – Chapter Fourteen
by JanaftyHaka suka yi ta kirana amma na kasa iya jarumtar ɗaukar wayarsu. Sai na ke jin kamar da na amsa wayarsu suka fara jefemin tambaya da cewa shin da gaske ne Yallaɓai ne ya ƙara aure ? Na tabbata rauni ne zai zo ya yi min rumfa ɗan jarumta da na samu ya ƙwace min na saka kuka shi ya sa na kasa iya ɗaga wayar ko ɗaya daga cikin su.
Yaya Balki sau biyu ta kirani Rahila ce wajen sau huɗu da ta ga ban ɗauka ba sai ta haƙura amma ban da Amina da saboda na. . .