Search
You have no alerts.
    The Den of Novels

    dan baka hanzarta zubar min da cikin
    nan ba ,zan gudu, dan kuwa zaku nemi
    gabad’aya ku rasa, bai tsaya ba, yace”ki fi
    ruwa gudu, idan kin tashi gudun ki tafi
    lahira karewarta kenan, ciki ne dai ni
    muhammed auwal bazan zubar ba,ba
    kuma zan saka hanunana ba,na dai d’auki
    zunubin aikata zina ,amman batu na
    zubda ciki
    bai k’arasa maganarsa ba ya k’arasa
    ficewa daga d’akin, aiko ta sake rushewa
    da kuka..
    Kai tsaye bakin get ya nufa inda yana
    zuwa ya tsaya ,a kan baba mai gadi ,yana
    bashi umarni “baba ka tsaya kan aikinka
    sosai ,acikin gidan akwai muwaddat kamar
    yadda kasani ,duk lokacin dana nemeta na
    rasa abakacin Aikinka, kuma wallahi tallahi
    kaji na rantse kotu ce zata rabumu .. .
    yana gama fad’ar haka ya juya ya nufi inda
    motar ummi take parke
    Bakin baba mai gadi na rawa yace ” Ina ai
    bama za’a yi i haka ba ,ai tunda ka fad’i
    haka, an gama.
    aranshi kuwa cewa yayi tsinanun ya’ya
    kawai Allah yasa karku kashe iyayenku da
    fitinarku, yana nan tsaye har sanda
    bunayya ya tadda mota,shi kuma ya bud’e
    mashi get ya fita, sannan ya samu guri ya
    zauna akan farar kunerarsa ya kunna radio
    ya soma sauraron labarai ..
    Ahankali yake tuki yana zance zuci ,har
    sanda ya kawo hospital inda mutanen da
    suka san shi d’an madam ne suka shiga yi
    masa, ya mai jiki,shi kuma yana basu
    amsa da alhamdullahi, adaidai bakin
    Coridon da zai Kai ka dakin da ummi take,
    suka had’u da abi wanda ya dawowarsa
    kenan daga massalaci .gaishe shi yayi
    had’e da tambayarsa jikin ummi ?
    Alhamdullahi ka godewa Allah jikin
    umminka yayi sauki sosai ,zuwa anjima
    nan zamu dawo gida yaya muwaddat din
    take, hope babu wani Abu da ya sameta
    jiya?
    “Lafiyar nan dai da sauki abi ,tare suka
    k’arasa cikin d’akin abi nayi masa nasiha
    koda suka isa d’akin ,sun iske ummi ta
    idar da sallah tana k’ok’arin mikewa da
    kyar ,sai dai har lokacin kallo d’aya zaka
    mata kasan tana cikin tashin hankali da
    damuwa mara misaltuwa ,kallo d’aya tayi
    masa ta d’auke kanta daga garesa ta
    koma kan gado ta zauna ya k’araso gareta
    yana kok’arin yi mata sannu cikin
    sanyayyiyar muryarsa ,amman Sam taki
    amsa masa illa ma sake
    tamkar wace aka aikowa da sakon
    mutuwa ,abi ne ma ya d’an bashi kulawa,
    amman shi ba wannan kulawar yake so ba
    shi yafi son ummi ta amsa masa, bazai
    iya jurar fushin umminsa ba … haka ya
    cigaba da tsayauwa agurin yana bata
    hakuri har karfe takwas ta bugu ganin ta
    mike tayi kwanciyarta akan gadon marasa
    lafiya ya juya ya tafi .
    had’e rai datayi
    Har yaje asibitin ya dawo damuwa ce cike
    da zuciyarsa ,duk wanda ya gansa yasan
    yana cikin matsanancin ‘bacin rai bai sake
    neman inda muwaddat take ba yayi
    zamansa a bangarensa ,baba mai gadi
    kuwa ya kasa ya tsare abakin get.
    Bayan sallar azahar yaji hon din shigowar
    mota, haka nan jikinsa ya bashi abi ne
    suka dawo ,dan haka ya tashi ahankali ya
    isa jikin window tare da yaye labule yana
    lekewa, tabbas shi din ne ya hango har da
    umminsa gabansa ne yayi wani irin mugun
    fad’uwa da karfin gaske.
    ya dawo ya canza kaya zuwa jallabiyar
    brown colour sa’banin d’azu da yake sanye
    da vest da boxer, ya fito yana taku cike da
    sanyin jiki ,koda ya fito har sun shiga cikin
    gidan shima yasanya Kai ,inda ya iske
    binta mai aiki sai faman jerawa ummi
    sannu take tana amsawa da kyar shima
    sannun yashiga yi mata ..
    Ganin binta tsaye ne yasa ummi taki korar
    bunayya,da binta zata tafi ummi tace “ina
    muwaddat?
    “Ina ganin tana d’akinta”
    “Je ki kice mata tazo yanzu”binta tace
    “tam had’e juyawa ta bar parlour’n.
    binta na barin bangaren ummi tashiga
    Zuwa bunayya ruwan bala’i ta inda take
    shiga bata Nan take fita ba abun har yaso
    bawa abi mamaki dan shi tunda yake bai
    taba sanin mukaramarsa na da irin
    wannan halin ba sai wannan lokaci
    “ishaq ka fad’awa d’anka…ka fad’a masa
    banason ganinsa arayuwata da duk inda
    nake ,har ya gama iya rayuwarsu kar ya
    kusanto inda nake bani bashi ..
    “Wallahi matukar baka bukatar nayi wani
    mummunar furuci akansa ya fad’a masa
    kiyayi zuwa inda nake ,ta k’arasa maganar
    tana hakki sama sama…
    Alama abi yayiwa bunayya ,daya bin
    umarninta yasan duk wannan abun datake
    na wani lokaci,da kuma bacin rai ,bacin
    rai kuwa babu abinda baya sawa
    Bunayya wanda idanunsa suka rikid’e
    sukayi ja tsabar tashin hankali da yake ciki,
    ya juya da kyar yake daga kafafunsa ya
    fice daga parlour’n.
    Yana fita ummi ta fashewa da wani sabon
    kuka.
    Jiki a matukar sanyaye muwaddat ta shigo
    parlour’n tamkar gazar da kwai ya fashewa aciki ,kanta sunkuye a kasa ,dan
    bazata iya duban idanun ummi, ba haka
    ma abi ,ummi ta d’ago ta dubeta cike da
    tsantsar ‘bacin rai da nadamar rikonta
    datayi arayuwa ,datasani kam tayi shi
    babu adadi ,data san haka zata zamo
    mata arayuwa wallahi da batayi ganganci
    d’aukota ba, ta barta tare da iyayenta
    ganinta yanzu yasa kukanta ya tsananta
    saboda wannan tashin hankali yasa tayi
    wata irin katuwar rama wanda yasa kallo
    d’aya zaka mata kasan tana d’auke da ciki
    ,muryar ummi a sarke tace “yanzu
    saboda Allah da annabi kun kyauta min
    kenan, barin ke muwaddat da kika biye
    masa, ke fa macece.. ?
    “da girmanki da hankalinki da tunaninki
    kika biye kaninki suka aikata zina..
    Abi yayi saurin runtse idanunsa kana ya
    bud’e su yana nunawa muwaddat gurin
    zama saboda ganin yadda jikinta ya soma
    “mai yasa kika biyewa kaninki kuka aikata
    mana haka muwaddat?
    “mai yasa muwaddat?
    “ko kin manta matsayinki ahalin yanzu kin
    tsaida mijin aure ,har ma da sa ranarsa
    akanki?
    “wai a ina ma kuka yi wannan cikin na
    tsawon wata biyar bamu sani ba?
    ummi ta mike tayo kanta gadan gadan abi
    ya tsaidaita ta hanyar rikota ..
    “ka barni nayiwa wannan shegiyar
    yarinya dukan mutuwa ,da girmanki
    muwaddat da hankalinki da tunaninki idan
    bunayya yaro ne ke yarinya ce ?
    “‘shekara ashirin da biyar zuwa da shida
    amman kika biye masa kika ruguza
    tarbiyar dana baki na tsawon shekaru,
    “yanxu me kike son duniya tace akaina?
    ta k’arasa mgnr tana kuka tana nunata da
    yatsan hannuta “hakika kun cuceni kun
    cuceni.. kunci amanata ,kun yaudareni
    yanzu ni na cancaci wannan tozarci
    muwaddat, na amince dake, na baki
    dukkanin yardata, ban taba tunanin zakiyi
    min haka ba “why muwaddat?
    why why why!!!
    kika biye wa son zuciyar auwal?
    “wayyo Allah ni mukarama, yau ni tawa ta
    sameni mai zancewa d’anuwana ya
    fahimceni..?
    abi ya kamota ya zaunar daita agefenshi
    “kiyi hkr mukarama ,kinsa Baki da lafiya
    zuciyarki na bukatar natsuwa ki d’auka
    haka tamu kaddaro tazo, babu yadda
    zamuyi bamu isa mu gujewa kaddararmu
    ba lahaula wala kuuwata illa billah, babu
    tsimi babu dabara duk abinda Allah ya
    tsarawa bawa to babu tantama sai abun ya
    sane shi ki yawaita furta kalmar inna lillahi
    wa inna ilaihi rajiun acikin zuciyarki…
    muwaddat ta taso daga inda take zaune
    jikinta na rawa, ahankali take d’aga
    kafafunta har ta K’araso ta durkushe
    agabansu’ abi dan girman Allah ka bar
    ummi ta zarta da duk wani hukunci data
    gadama akaina,na cancaci fiyye da duka
    agurin ummi akan abinda nayi, tayi min
    duk abinda zatayi koda kuwa ta kama ta
    kasheni ne, ka barta matsawar zata huce
    takaicin abinda nayi mata.
    ta juya ta fuskanci ummi idanunta taf da
    ruwan hawaye suna zuba akan kuncinta
    umminah kiyi hkr dan girman allah ki yafe
    mana,duk da ba ke ce kika kawoni duniya
    ba amman idan kika tsine min sai
    tsunuwarki tayi tasiri akaina, dan Allah
    ummi ki taimaka ki taimaki rayuwata ki
    rabani da wannan ciki koda kuwa mutuwa
    zanyi na gwan
    wannan cikin shegen dake jikina…
    haka akan dai na haifi
    daga ummi har abi saurin runtse
    idanuwansu sukayi da saboda d’acin
    kalmar data fad’a, “first jikan da zasu samu
    a duniya shine yazo mata ta wannan
    hanyar da bata dace ba, ita kuwa wani irin
    kuskure ta tafka arayuwrta?
    “ummi wallahi nayi danasani arayuwata.
    abi dan Allah kabawa ummina hakuri kace
    ta yafe min wallahi sharrin sheidan dana
    zuciya, wallahi bazan sake ba na tuba abi
    ta k’arasa maganr cikin kuka tana had’e
    hannunwanta duka ..
    shiru ne ya biyo baya sai sheshekan kukan
    ummi da nata dake tashi ahankali “baza’a
    zubar da cikin jikinki ba muwaddat ,za dai
    musan abinyi tashi ki shiga d’akinki abi ya
    fadi hkn yana kallonta…
    ta yunkura da kyar ta tashi tashiga jan
    kafafunta da suka mata nauyi ta nufi
    d’akinta tana kuka, tana shiga ta ta fad’a
    kan gadon tana sake fashewa da wani
    kukan “na cutar da kaina,na cuci
    rayuwarta yau nice d’auke da cikin shege”
    wayyo Allah ni muwaddat ina zan kai
    wannan kayan abun kunyar.. .
    ..?
    zumbur ummi ta mike tashiga zagaye
    parlour’n tana zance zuci” dan dole tasan
    abunyi kafin kunnuwan mutane gari dana
    danuwanta suji wannan abun kunyar da
    aka aikata acikin gidanta ,dan dole ta
    nemawa kanta mafuta, “to mai zanyi ?
    ‘mai zanyi akan wannan cikin..? Ta
    tambayi kanta.
    “dole na samo mafurtar abinyi, shiru tayi
    sannan ta nufi d’akin cikin sauri abi yabi
    bayanta shima atare suka Shiga d’akin
    “mukarama yanzu Yaya zamuyi?
    ta tako ta fad’a kirjinsa tana wani irin kuka
    mai ban tausayi •ban sani ba ishaq.
    bansan abinda zamuyi ba. amman nafi
    tunanin mu zubar da cikin nan kawai shine
    kwanciyar hankalinmu.
    “wannan ba shine mafuta ba mukarama ,
    illa zunubi da zamu d’aukarwa kanmu,
    muyi hakuri mu rungumi kaddararmu data
    samemu wannan abun daya faru duk
    laifinmu ne,kuskurenmu ne mukarama,
    tunda yaron nan tun farko ya nuna mana
    aure yake so, ya bini ya biki yayi iyakacib
    kokarinsa amman muka kekashe kasa
    muka ki yarda •mu kace karatu ‘yanzu
    ga illar abinda son zuciyarmu ya jawo
    Mana, da’ace mun barsa tun farko yayi
    aurensa da duk haka bata faru damu bae
    kalu bali ga iyaye masu hali irin namu
    ,mukarama ni dake muka tsunduma
    yaranmu cikin wannan mummunar
    rayuwar _
    •wa man kaddarallahu haqqa kadarihi*
    ki yarda da wannan kaddarar data
    samemu mikaram daman duk muslimi
    dole ne yayi imani da kaddara mai kyau ko
    akasinta, ni dai na yarda da kaddara data
    fada mana kuma na amsheta da hannu
    biyu biyu wannan shine sakamakon iyaye
    irinmu masu biye son zuciyarsu
    zare jikinta tayi a jikinsa ta koma ta
    kwanta akan katifa, numfashi take
    saukewa ahankali ahankali kana ta runtse
    idanunta gam ta dinga jin wannan bakon
    aliamarin dake faruwa daita tamkar a
    almara ko wani shirin film, itace zatayi jika
    ta wannan hanyar?
    “anya zata iya wannan hakuri ta bar cikin
    nah kuwa?
    “kai dole tasan abunyi, Cire cikin zatayi
    alabashi daga baya ,sai a yi musu aure ,
    Udata bar wannan abun kunyar azo ana
    zaginta a gari wallahi gara ta Cire mata
    . koda a boye ne batare da sanin daci da radadi tana jin bazata iya jure
    wannan abun kunyar data aikata da
    kaninta ba, tana jin tamkar tattara inata
    inata tabi uwa duniya. ko ta kashe kanta
    “karki kashe kanki ki mutu kafira ga zunubi
    zinar da kika aikata ga na kisan kai, gara ki
    Shiga uwa duniya
    take ta amince da wannan shawarar da
    zuciyarta ta bata”cikin sauri ta karasa inda
    jerin akwananta suke ta dauko karamar
    ciki ta isa gaban wardrobe dinta tashiga
    dibar kayanta da abubuwan amfaninta
    tana zubawa aciki..
    can bangaren ummi dake kwance akan
    gadonta tana faman joyi daga karshe ta
    yunkura ta mike jikinta tmkr ba nata ba, ta
    zauna tana sake goge hawayen daya
    gagara tsayawa a idanunta Ita isa bakin
    bayi da niyyar Shiga ta dauro alwala .cak ta
    tsaya kirjinta na wani irin harbawa can
    kuma tasoma jiyo motsin haka nan
    zuciyarta lace ta leke taga me ke faruwa .
    cikin sanda ta fito ahankali tana taka step.
    gabanta yayi wani irin mahaukaci bugawa
    da karfln gaske sakamakon abinda
    idanunta yacin karo dashi , muwaddat ce
    ke kiciniyar bude kofar babban parlour’n
    da niyyar fita.
    Wata uwar razananniyar Kara ta Saki
    hade da jero sallati ,wanda janyo hankalin
    abi ya fito daga d’akinsa a firgice Yana
    dubansu muwddat kuwa wani irin tsalle
    tayi hade da jifa da akwatin hannuta
    ,jikinta ya kama rawa take kuma dan
    cikinta yasoma motsi sosai abinda bata
    ta’ba ji ba kenan a tun samuwarsa..
    •me nake shirin gani yau ni mukarama?
    “me kike Shirin aikatawa muwaddat
    “ina zaki da akwati?
    muwaddat ta rushe da kuka jikinta na rawa
    . •tambayarki nake nace ina zaki ?
    “Kar dai guduwa zakiyi muwaddat ki barni
    cikin wannan tashin hankalin? tasoma taka
    step biyu biyu ko ganin gabanta batayi har
    ta k’araso gabanta tace •guduwa zakiyi ki
    barni ko me?
    jin tayi shiru taki amsa mata tambayoyunta
    yasa tashiga yaryarfa mata mari •guduwa
    fa kike shirun yi muwaddat?
    “yanzu daman zaki iya barin?
    “zaki iya guduwa ki barni cikin damuwa ?
    ” idan kin gudu ina zaki eye?
    Ki fada mun ina zaki tana tambayar ta tana yarfa
    Mata wasu marurukan daga karshe ta rufe ta da duka
    “Gara na kashe ki da hannu na binne gangar jikin ki
    akan ki gudu ki Shiga k’
    wannan shine kare na farkO da ta
    SMaya hannunta aiikin a tun
    ,duka tayi mata har
    sai da abi ya tsaidaita tukLJnM1
    kasa tana kuka •guduwa take Son yi ta
    barni ishaq Cikin tashin hankali “
    miki daga
    • kike k Ok’arin kinsa
    jurar rashinki ba, tasorna
    gindi Z•JWa inda di take
    durkushe gwiwaWinta tana ta
    ajikinta •karki barni dan Allah
    karki barn. ‘dan kika barni Zu•ciyata
    buga Zan mutu 10kacina baiyi
    zatayi tsanani da muni ta
    kama fuskarta da hannuwanta duka tana
    kallon Cikin •mai baki
    min kina bunayya ba?
    •wallahil dana San kina Son Shi
    haka da tuni na barku kun aure
    akanki San zaki
    hake, bansa adalilin Son iya
    mallaka masa jikinki
    makauniyar SOyayya kadai Ce
    Zata Sa ki jikinki bashi
    baki nuna kOda kina Shi
    rnuwaddat ta runt* idanunta Wasu
    zafafan zafl Shiga
    tana girgizawa ummi
    •yi min Shiru farkO
    sake tafka babban kuskuren
    aray•uwata da har na matu bazar’ daina
    danasani be, kika gudu kika
    har Zan dangwama Cikin
    karki sake tunanin barin
    muwaddat tana
    kwakwameta aiikinta• na da
    kaddara imani
    h awaye Cicciko a idanuta abi
    Sun bashi Zaka masu ka
    tabbatar da suna Cikin taghin hankali barin
    muwaddat daya Gama karanta
    dake dentin duk halin da zuciya
    ke ciki fuska Ce ke kaf’n baki
    ya yanayinta gabacfaya jikin
    ummi ya game yin tSanyi ta tuba mata
    tams-a Ce dina
    •kingani ko daga ni sai ke
    abi (nuke cikin hankali tSaWOn
    daren nan gagara ratsuna
    bumnaya ke can Yana sharar baccinsa shi
    nmi ba kunya b.a, mai kika biye
    •kiyi hkr wallahi nayi dan
    Allah ki yafe min Zan jin radadin
    abinda nake ji Zuciyata, ta Shiga
    Shata bayanta tana kuka ko ba
    muwaddat na da tsananifi biyayya
    tana dadin yadda take Santa
    Ahankali mikar daita tsare ta rabata
    aiikinta cfakina karki kZra
    barinmu duk runtse rnuna tare kinji
    gudawa abar a sanadin yin Ciki
    bash. da arnfani Yana da
    dayawa ga idan kin
    gudu kika san hannun Zaki facia?
    har guka Shiga dZkin dukkaninsu
    kuka
    ummi ta kwantar daita akan gadon ta
    kwanta kinji nima na hakura kema ki
    dawwalawa Allah lamarinki , taje ta kulle
    kofar har da zare key dan jin tsoron karta
    gudu tazo tashiga bayi..
    muwaddat ta runtse idanunta “batasan
    wani irin so ummi take mata ba ?
    shi kuwa abi zubewa yayi acikin d’aya daga
    cikin kujerun dake parlour’n ya goge
    hawayen dake k’ok’arin fitowa daga cikin
    kwarnin idanunsa “gabad’aya a halin yanzu
    baya ganin laifin yaran yafi d’aura laifin
    komai akansu
    bangaren bunayya shima ranar haka ya
    kwana Yana tunanin , wani sain Yaja tsaki
    wani lokacin yayi murmushin jin dadi..
    wayarsa dake gefensa ne tayi ringing
    alamun ana kiransa duba Wayar yayi ganin
    wacce ke kiran ne yasa shi jan dogon tsaki
    kafin daga baya ya d’auka, yayi shiru Yana
    jiran yaji abinda zata fad’a, yasamu damar
    cin ubanta da tushe a bangaren faiza kuwa
    dadi ne yakamata saboda ta yita kiran
    layinsa na London bai Shiga daga baya
    tayi tunanin ta kira na Nigeria taso
    tasoma jin sanyayyiyar muryarsa mai sata
    jin kasala a sansar jikinta, amnan yaki yin
    mgn sai hucin numfashinsa, a sanyaye
    tace “‘hello Yaya auwal..”
    “lafiya kika kirani ya fad’i hkn a takaice?
    duk da yadda ya amsa mata hakan bai sa
    taji zata fasa maganar datayi niwa ba .
    tace ‘Yaya auwal daman nace…
    “kika ce uban me da uwar me ?
    “faiza! faiza!! faiza!!! sau nawa na kiraki?
    muryarta a sanyaye tace “sau uku •na
    rantse da girman allah na haramta gareki
    koda kuwa banyi nasarar samun
    muwaddat ba, bariji gabad’aya a tsarina
    bana son mace irinki mara aji da kamun
    kai ,duk da kasancewarki yarinya amman
    wallahi gara na auri irin muwaddat sau
    hudu saboda bana sonki, kuma bazan
    taba sonki ba har abada ,saboda xuciyarta
    yayarki take so koda kuwa tafi yadda take
    shekaru Yana gama fad’ar haka ya katse
    kiran ya koma ya kwanta Yana fidda
    numfashi sama sama..
    Mmn sudais ce

    MUWADDAT

    ~NA
    *AYSHA A BAGUDO*

    ~DEDICATED TO~
    _AUNTY SALAMATU AYYUBA_
    _(UMMIN KADUNA )_

    bismillahirrahmanirrahim

    Note
    error: Content is protected !!