Search
You have no alerts.
    The Den of Novels

    Tun bayan fitar bunayya daga d’akin abi,abi ya kasa samun natsuwar zuciya a game da al’amarin tillon d’ansa,

    ” a zahirin gaskiya yana jin tamkar ya biye masa ne, yayi masa abinda ya bukata, amman lokacin daya tuna shekarunsa a duniya a halin yanzu sai yaga gabadaya lamarinsa na tattare da kuruciya da sharrin soyayyar farko ne , Wanda mafi akasari akan samun haka acikin wannan duniya .

    soyayyar kuruciya mafi yawa matasa na tsintar kansu ciki wannan shaukin mai wuyar misaltuwa Wanda da wuya akai ga cimma burinta,

    Dan haka ya ajiye maganarsa amatsayin yarinta da kuruciya ne kawai ke dawainiyya da d’an nasa ,bancin hk ta yaya kamar bunayya zai ce ayi masa aure a wannan lokacin

    “auren ma da wace ta girmesa?

    tattara zance yayi ya ajiyesa amazaunin wasan yara da kuruciya , ya cigaba da abinda ke gabansa .

    Shi kuwa bunayya Ko daya dawo d’akinsa ya kasa samun sukuni, gabad’aya ya rasa abinda ke damunsa, zuciyarsa banda tafarfasa babu abinda take, ya kasa zaune, ya kasa tsaye, sai zariya yake acikin d’akin rike da kugunsa yayinda hannusa daya ke dafe da goshinsa ,gabad’aya hankalinsa baya gangar jikinsa, ‘kwa’kwaluwarsa ke hasko masa wai ga muwaddat dinsa can tare da ala’meen tana masa murmushin nan nata da yafi so da kauna akan komai acikin duniyar nan ,take wani zazzafan kishi ya turnuke zuciyarsa dama gangar jikinsa, ahankali ya runtse idanunsa yana girgiza kai, kirjinsa na wani irin dokawa da sauri ” Impossible ya furta a bayyane had’e da bud’e idanunsa ya cigaba da zagaye d’akin ..

    “Anya kuwa zan iya d’aukar lokaci batare da na kai kaina gareta ba ?

    Anya ba wani abu al’amen yake nufi dashi ba ?

    “to wai ma me taje yi d’akinsa a daidai wannan lokacin?

    “Ko ba’a gaya masa ba yasan ala’meen son muwaddat dinsa yake, tun da shi ba makaho bane ,dan idanuwansa sun fara hango masa mugun nufinsa akanta ..

    Abinda yakamata kawai kaje ka d’aukota ka dawo daita gida shine kawai besty solution da kwanciyar hankalinka gareka ,zuciyarsa ta umarcesa da fad’ar Hakan ,take kuwa ya amince da shawarar zuciyarsa ,ya kudirci aniyar ko bai je gobe ba kamar yadda ya furta mata ba, to kuwa cikin satin sai ya dangana da ilori ,duk ma abinda zai faru sai dai ya faru amman sai ya d’auko abarsa kafarta kafarsa ya k’arasa maganar yana

    fad’awa Kan makeken gadonsa da karfi ya kwanta ruf da ciki , yana furzar da iska mai zafi had’e da shafa sumar kansa ,sannan ya kai hannunsa ya janyo wayarsa shiru yayi sakamakon ganin har lokacin wayar tana kan layi ba’a tsinketa ba.

    ya sauke naunayen ajiyar zuciya yana duban screen din wayar sannan ya kai wayar kunnensa ,sautin muryar kukanta ya jiyo can kasa tamkar ta baby yana shiga cikin dodon kunnenshi, zuciyarsa ta cigaba da bugawar da take da karfin gaske, wani irin rad’ad’i ya dinga jin yana sauka akan tsokar dake makale da kirjinsa , runtse idanunsa yayi sosai had’e da Jan dogon tsaki sannan ya katse kiran gabadaya ya Mike ya shiga bathroom…

    Muwaddat kuwa har lokacin tana zaune tana kukan bakinciki abinda bunayya yayi mata , kukan ma ba wai akaron kanta taso yinsa ba, ji tayi kawai hawaye na fita daga cikin kwarnin idanunta, tayiwa kanta alkwarin duk runtse babu abinda zai sake shiga tsakaninta dashi, idan mutuwa zatayi da soyayyarsa , sai dai sonsa ya kasheta ,amman babu ita babu shi har abada ko komawa tayi lagos bazata shiga tsabgarsa ba .

    tana cikin wannan kukan mumy tashigo d’akin ganin har 11:00 na dare bata fito taci abinci ba .

    Tana ganin shigowar mumy tasoma k’ok’arin had’iye kukanta had’e da share hawayenta da sauri ,yayinda ita kuma mumy tana ganin haka ta maida kofar da sauri ta rufe ta k’arasa shigowa d’akin tana kiran sunanta “muwaddat meke faruwa ?

    ” lafiyarki ?

    “kukan me kike?

    “Waye ya mutu ko waye bashi da lafiya ?

    Tayi mata tambayar gabadaya ajere tana zama kusa daita.

    kai kawai muwaddat tashiga girgiza mata al’amun babu komai “ke ki bud’e baki ki min magana, ba wai ki dinga karkad’awa mutane kai ba “me ya faru ,me yasameki ?

    Muryata cike da kuka da in ina tace ” ba..Babu komai fa” “babu komai zaki zauna kina kuka kamar wace aka aikowa sakon mutuwa, ki gaya min abinda ke damunki ?

    Wasu sabbin hawayen suka sake gangaro wa bisa kuncinta , tasa bayan hannunta ta goge tana sake girgiza mata kai .

    Hankalin mumy ya sake tashe matuka, tace “wato kina boye min Abu ko ?

    Cikin rawar murya tace “Sam Sam ba haka bane mumy ,”kina boye min mana mumuy ta fad’i tana mai mikewa tsaye da sauri tayi hanyar fita domin kiran dady, muwaddat tayi saurin riko tafin hannuta “mumy karki yi fushi dani Dan Allah ,babu fa abinda ke damuna kawai dai ina cike da kewar ummina ne ……..

    ta tsinci kanta da fad’ar haka wasu siraren hawaye na gangaro mata .

    Naunayen ajiyar zuciya mumy ta sauke sannan ta koma ta zauna tana dubanta had’e da nazarinta “har ga Allah ta yarda da maganar diyarta, saboda tasan yadda shakuwar dake tsakaninsu da uwarta tafi karfin haka ,domin kuwa daya baya iya d’aukan dogon lokaci batare daya ba ,yanzu haka kullun garin Allah ya waye akalla basuyi waya ba sai sun yi sau Goma hatta bacci suke tashinta wani lokacin ko abinci zata ci sai takirata tana cin suna waya haka zalika abi ,Yayinda komai akayi ta bangaren kowanensu ,yanxu ne zasu bugawa juna suna cike da tsantsar farinciki suna labartawa juna “

    Ahankali mumy ta bud’e bakinta “to kuma shine zaki zauna kina kuka?

    ” idan kin gaji da zama damu kamata yayi kiyiwa umminki magana tasa azo a tafi dake .. .. ba wai ki zauna a d’aki kina kuka irin hk ba “

    Amman yanzu ki bari zuwa wani sati sai ki koma, saboda ina son kije kalgo ki ga inna kafin ki koma, ki d’an yi kwana biyu agurinta ,dan koda yaushe idan munje sai tayi maganarki ,Dan haka zan saka ala’meen ya kaici gobe tunda weekend ce sai kiyi musu kwana biyu “zuwa lahadi ko manday sai ku dawo, ki soma shiri komawa

    Muryarta a matukar raunane tace “to mumy “

    Mumy tace “Muje ki ci abinci Sam baki son cin abinci muwaddat, shiyasa gashi nan kullun jikin naki babu laka bare kuzari ,muwaddat ta Mike tsaye jikinta a matukar sanyaye tayi gaba tasoma tafiya tamkar kazar da kwai ya fashewa aciki , mumy ta bi d’akin da kallo sannan ta kai hannunta Kan wayarta dake yashe Akan gadon ta d’auka tana duddubawa, babu abinda ta gani duk number’s din yan gidansu ne Dana kawayenta , sai number guda daya data ga an rubuta (man ) muwaddat…mumy ta kira sunanta. …

    ta D’an tsaya tare da juyowa ta tsaya tana duban mumy “waye kuma man ?

    “Tayi shiru can tace ” d’an makarantarmu ne “meye tsakaninki dashi ?

    “Babu komai momy “to ki goge lambarsa bana bukatar ganinta cikin wayarki ,sannan ki dinga kiyayewa ,Allah kuma ya kiyaye mana ku a duk inda zaku sanya kafafunku .

    Muryarta ahankali tace ameen ta amshi wayar ta goge number man har ma data Auwal gabad’aya sannan ta sake juyawa ta cigaba da tafiya mumy ta biyo bayanta ,

    Mumy na fita ta kira ala’meen a waya ta sheida masa abinda take so ayi a gobe idan Allah yasa suna raye ta kirasa Dan ya kwana da shirinsa ,yace mata “babu damuwa Allah ya kaimu.

    Tun daren al’ameen ya shirya kayansa set biyu kacal ya d’auka sai kayan Pajams dinsa haka ma muwaddat mumy ce ta shirya mata kayanta cikin yar k’aramar akwati ..

    Washegari tunda sanyi safiya suka d’auki hanya zuwa kalgo, gudu kawai al’ameen yake sharara akan titi batare daya juyo ya kalli inda muwaddat take ba ,haka zalika itama bata kalli inda yake ba idanunta naga kallon titi ne, domin haushinsa take ji acikin zuciyarta, ganinta duk shine silar damuwarta silar da yasa ran bunayya ya ‘baci har suka samu sa’bani dashi , Dan da kace bai aiko kiranta ba alokacin da duk hakan bata kasance ba ..

    Tun yana dauriya har dai yasoma janta da hira tana amsa masa tana yatsina fuska amman ya dakewa zuciyarsa ya cigaba da janta Dan dai ta saki ranta sannan yana bukatar tafiyar tayi masa dadi gashi ga rabin rayuwarsa ,tafiya ce mai nisa tsakanin ilorin da kalgo sannan suka iso ..

    suna shigowa kauye ya rage gudu

    Adaidai wani madaidaicin gida yayi parking din motarsa ya fito yana Mika had’e da salati ,kusan minti goma ta fito tana kallon yanayin garin ,yana nan dai tamkar yadda ta sani acan baya sai ‘yan canje canje kad’an da taga garin ya samu na cigaba ,ciki kuwa har da gidan kakarta ,Kafin kace me tuni kofar gidan sun cika da kananun yaran unguwar da almajirai suna kallonsu had’e da zagaye motar .

    Daya daga cikin yaran ya k’araso gurin ala’meen yana washe baki “yaya ala’meen sannu da zuwa “yauwa musa sannu ya kake ya gida ?

    ala’meen ya fad’i hk yana zagayo ya bud’e boot ya d’auki akwatin kayanta,musa yayi sauri ya amsa had’e da shiga cikin gidan inna .

    Ya waigo ya dubeta tana kallon yaran dake zagaye suna wasa da tsalle tsalle “Muje ko ,nasan kin gaji dayawa “ba tace masa komai ba ta nufi hanyar cikin gidan tun

    daga farkon shigowarta gidan tasan ba iyayenta kad’ai rayuwa ta sauyawa ba har da kakarta , koina tsaf tsaf sannan a tsaftace malale da tayis har cikin tsakar gidan bakinta d’auke da sallama tasanyo kanta ta k’arasa shigowa, inna dake tsaye jiran shigowarta tun shigowar Musa ta fad’ad’a fuskarta da fara’a tana murnar ganin jikarta, “marhabun lale da mutanen iko da ilorin “muwaddat ta saki murmushi me tattare da gajiya sannan ta k’arasa ta rungume inna ajikinta “inna mun sameku lafiya ?

    “Lafiya kalau ya hanya ?

    Bata amsa ba ta saki inna tana dubanta “mu shiga daga ciki sannu kun kwaso gajiya “babban ango maraba sannu ,kun sha hanya “sai yanzu kika ganni tun dazu nake ta faman bud’e makoshi ina rattafa sallama amman kikayi min banza “yi hakuri mai gidan asaliyyan, ni na isa in shareka ai ko zan yi shariya sai dai in share wancan mai wuyan kamar lagwani , amman ba kai ba ,suka saka dariya ita dai muwaddat tayi gaba tashiga d’akin da inna ta nuna mata .

    Tana shiga ta zauna gefen gado tana tunanin abinda zata fara yi sallah ko wanka cikin haka inna tashigo d’akin tana sake yi mata sannu ,muwaddat ta yatsina fuska “Sannu me kuma zaki min ni da ke wuya kamar lagwani ?

    Inna tasa dariya jaira haushi kikaji kenan ?

    “Dadi abun yayi min shiyasa “ke jaira banciki da bakin ranki ,yanzu dai dame zaki fara wanka ko sallah ko abinci ?

    “Ina bayi tukunna dan gaskiya wanka zan fara ,

    Inna ta nuna mata bayi sannan ta sake yin waje .

    Muwaddat ta Mike tsaye ta bud’e akwatin kayanta ta ciro white towel ta d’auki makilin da brush ta nufi bayi wanka tayi ta fito ta sauya kaya zuwa doguwar riga sannan tashiga Jero sallolin dake kanta ..

    Bayan ta idar ta kai idanunta Kan hadadden kafet din dake gabanta kwanunka abinci ne sama da Goma ajiye ta d’ago tana duban inna tamkar zatayi kuka “wadan nan abincin fa inna?

    “,duk ke akawowa ki bubbude kiga Wanda yayi miki ,kai ta girgiza sannan tace “wane kika dafa aciki ?

    inna Ta janyo wata kula blue ta bud’e “ga Wanda na dafa miki “to shi kawai ma ya isa shima din kad’an zanci .

    Inna ta Mike zata fita amman jin abinda ta fad’a yasa ta d’an tsaya “ki dibi abinci kici sosai sannan ta sanya kai ta fita muwaddat ta d’auki plet ta dibi abinci kad’an tasoma tsakura bayan tagama ta nemi guri ta kwanta akan gadon inna ta ciro wayarta ta kunna takira mumy ta sheida mata sun iso ,sannan takira iyayen goyonta, suka hira har sanda ala’meen yashigo wayar take ,Dan haka bai ce mata komai ba ya koma gurin inna .

    **********

    Alameen Suna zaune tare da Inna suna Hira, cikin hirar ne take Masa zance aure” ala’meen yakamata zuwa yanzu ace ka’ajije iyali ga sa’anin haihuwarka Nan daga masu mata biyu sai uku sannan kowane da ya’yansa abun sha’awa, Mai zai Hana kai ma kasamu sukuni ka samu ka duba yarinyar data dace ko anan cikin dangi ne ka zaba ..?

    Ala’meen Yayi murmushi kawai Yana duban Inna har sanda ta numfasa sannan yace “maganarki gaskiya ne Inna yakamata, sai dai har yanzu ina kan dubawa dai, inshallah Nan ba da dadewa ba zan kawo Miki kyakkwar kishiya wacce tafiki kyau da komai ..

    Koma wace balarabiya ce fatana ka kawo ta gari yar gidan mutunci , ni kuwa sai naji ina maka sha’awar auren ayshatu ,wallahi baka ga yadda kuka dace da juna ba ,da zaka yarda da shawarata sai ka nemeta nasan babu abinda zai Hana ubanta yaki baka ,Kuma Nima zanyi farinciki sosai, Kai kowa ma zai ji Dadi hakan ta fad’a Tana duban ala’meen,ta ga yadda zai d’auki maganar .

    yadda take dubansa din yasa kirjinsa bugawa saboda maganar ta bugesa Sosai ,jin yayi shiru tace banji kace komai ba .?

    “To me kike son nace Inna ?ni kaina abinda ke cikin Raina kenan ,amman gabadaya yarinyar taki bani damar fahimtar daita, zan dai Bata lokaci Nan da kafin ta koma zanyi kokarin sanar mata,” to ka hanzarta Dan dai saboda Allah zuwa yanzu yadace ace ka’ajiye iyali ,idan Kuma kafinson na mutu Banga aurenka ba to shikena..

    ya kamo hannuwanta duka cikin nasa Yana Bata fuska “Kai Inna karki fad’i haka ,da yarda Allah bama aurena ba hatta ya’yanmu nida akram sai kin gansu,

    “kai rabani da zance wancan ja’irin tsohon tuzurun, koda yaushe shima hk nake fama dashi akan batun aure, har ma gara kai yanzu tunda nasan inda ka dosa, shi fa ko mgnr auren ma baya kauna yanzu, byn shekaru baya da kansa ya kawo min karar iyayensa akan yana son aure amman yanzu na rasa dalili , wasu abubuwa ma nagani nayi kmr wanda aljanna ta aura ..

    “duk yarinyar da aka nuna masa sai yace batayi masa ba.

    ala’meen ya numfasa kana yace “ni kaina abubuwan akram na damuna da ta’ba min zuciya, gabad’aya tun dawowarsa daga canada na rasa gane kansa da gindinsa , gashi yau ciwo gobe lafiya, kwanaki dana yi masa rakiya ganin likita ,karkiji irin fad’an da likitoci sukayi masa akan wasa da rayuwarsa da yake ,wai zuciyarsa na daf da bugawa, tambayar duniya nayi masa amman amsa daya akram yake bani babu komai ,shi baya tunanin komai alhalin ni nasan akwai abinda ke damunsa boyewa kawai yake , dan wallahi inna kwana akram yake yana kuka da buge buge a d’aki shine ma dalilin dayasa na bar masa d’akin na koma sama.

    “subuhanallah shikenan zargina ya tabbata, aljanna ce wallahi ta auresa, to ka sheidawa iyayensa ko ,dan asan matakin d’auka?

    “a’a inna ni dai nakan yi masa addua alokacin muna tare ,aiko bamuga ta zama dole a nemo masa taimako..

    Hira sukayi sosai har sai daya ga ala’mun inna ta fara jin bacci sannan ya bar gidan Yana mata sallama .

    **********

    duk inda yakamata ala’meen ya Kai muwaddat ta sada zumuci ya kaita sai yan tsirarrun gidajen ‘yan’uwa da gidan innarsa ne Bai Kai ba, suka barshi sai zuwa gobe lahadi Wanda daga Nan zasu wuce . .

    Tun da safe ya kaita gidan munira ta amshe su cike da fara’a tare da nuna mata gurin zama da murnata da komai ta karbeta hannu biyu biyu duk da basu wani san juna ba sosai saboda tun Tana yarinya rabonsu da juna ,muwaddat taji Dadi sosai saboda ita dai mutun ce Mai son a nuna ana sonta ,Kuma adamu daita tare da rawar jiki akan lamarinta, suka gaisa a mutunce cikin haka Mai gidanta ya fito ,yana ganin ala’meen yace “babban Yaya kun iso lafiya tun jiya nasamu labarin zuwanku ya mutane can ?ya Mika Masa hannu suka gaisa ala’meen yace “kowa lafiya duk sunce agaisheku ..

    cikin farar mijin munira yace “bakuwa sannu da zuwa ya hanya ?

    Muwaddat ma tayi Dan yi murmushi kad’an Tana gaidashi ,munira kuwa sai rawar jiki take Tana Nan Nan da muwaddat kafin kace me ta cika mata gabanta da abinci …

    Muwaddat Bata wani ci abinci kirki ba har gara ma lemu ta kan Dan tsiyaya Ta sha .

    Bayan awa daya ala’meen yace wa mijin munera “Dan Allah Bala idan bazaka damu ba ina son munira ta raka yarinyar nan gurin sauran dangi akwai inda bazan iya Kai ta ba ,gashi goggo tace” akaita Koina acikin dagin ta sada zumuci Bala yace” shikenan babu damuwa sai ta kaita ai “Yana gama fad’ar haka yayi gaba, shima ala’meen yace Bari ya Dan shiga gari kafin su dawo har ya Kai bakin kofa ya juyo Yana dubanta karki damu munira zata Kai ki duk inda yadace .

    Gyada Masa Kai kawai tayi batare datayi Masa magana ba, munira tace Bari na shiga na shirya nazo mu fita ga mamakin munira sai ji tayi tace” kariki damu kanki ki Bari kawai ba sai munje koina ba ,Nan ma kawai ya Isa wallahi garin akwai Rana sosai” keda da aka kawoki a cikin mota koina ac “

    Muwaddat tayi murmushi “bana son fita ne wallahi mu zauna muyi hirarmu har zuwa sanda zai dawo , munira tayi sororo Tana kallonta sannan tace “Anya ayi haka bayan kinji abinda goggo tace .?

    “Mubari kawai ai muje gurare dayawa jiya tashiga fad’a mata inda sukaje jiya dan haka muyi zamanmu muyi Hira … ana suka wuni zir suna Hira sai wuraren la’asar ala’meen ya dawo munira tayi Masa sannu da zuwa tare da tashi ta kawo Masa ruwa Mai sanyi ,ya amsa ya Sha idanunsa na kan muwaddat ,ala’meen ne ya fara magana “yau dai kun Sha yawo .

    Muwaddat tayi shiru domin ba tasan me zatace ba, sai munira ce tace “ai bamuje koina ba domin dai tace bazata iya bin Rana ba.

    ala’meen ya tsira mata ido yana kallonta batare daya ce komai ba ,anan ya fahimci momy ce kawai ta damu datazo gurun danginta amman ita Sam Bata wani damu ba .

    Tun shigowarsa muwaddat ta kasa sakewa bata wani Sanya baki cikin hirarsu ba saboda ala’meen dake binta da mayatacen kallo ,duk inda ta motsa idanunsa na kanta wanna dalilin yasa ta kasa sakin jikinta ..

    Can bayan kmr minti goma ya dubeta “tashi muje ko Kar muyi later saboda Ina son na bita ta gidan hajiya batayi magana ba ta Mike ta d’auki Jakarta ta rataya tayi gaba .

    munira ta mike tayi musu rakiya har harabar gidan inda ala’meen yayi parking din motarsa .

    Ala’meen yashiga mazaunin direba itama tashiga ya tayar suka tafi har suka shiga wata unguwa, taga yayi parking din motarsa a wani kofar gida ya d’an dubeta Dan Allah kiyi hakuri zamu shiga wurin hajiya mu gaisa .

    Batare data juyo ba tace “shiga ka fito ina jiranka ,bai ji dadin yadda tayi Masa ba, koda yake me yiwuwa dan batasan wace hajiyar yake nufi ba ,amman ko batasani ba sai ta tambayeshi ,shi Kuma sai ya fad’a mata gidan hajiyarsa yake nufi yasa Kai ya fita Tana kallonsa ..

    har zai shiga gidan sai Kuma ya dawo ya tsaya ta bangaren da take ‘”ki fito mu shiga Dan Allah gidan yayan mumy ne fa da suke ciki daya, wato mahaifina kinsa mumy bazata ji Dadi kixo garin nan har ki tafi baki zo kun gaisa ba ,jin haka yasa ta fito Tana yatsina fuska tamkar wace taga Kashi .

    Tasoma tafiya ahankali har suka shiga cikin gidan .

    Jin kad’an ta fito ta shiga motar tayi zamanta .. Koda ya fito yasameta cikin motar Tana waya bai yi mata magana ba ya bud’e motar yashiga ya tayar .

    Yana sauketa agidan inna ya k’ara gaba ,domin ya tsani yadda take yi Masa ,a yadda ya lura shi kawai takewa wannann miskilacin amman ai Yana ganin yadda takewa mutane ko d’azu daya koma gidan munira d’aukota Hira ya iskesu suna yi har da dariyata amman Tana ganinsa tayi shiru Bata sake cewa komai ba .

    Da sallama tashigo gidan Tana yatsina fuska Inna ta dubeta Tana yi mata sannu “kin gaji ko Daman ziyara haka yake dole ki gaji baki saba ba “wallahi Inna duk na gaji garin nan naku akwai Rana “Inna tayi murmushi in go nan tayi mata dakuwa ,”Allah yasa dai kema garin naku ne Kuma inshallau acikin garin Zaki karasa rayuwarki “Kai Inna ina zan iya rayuwa anan ,ku dai daya zamemu ku dole kuyita fama, mu ma dinga zuwan muku ziyara ta k’arasa maganar Tana shigewa d’aki dayake Bata fahimci inda zance Inna ya nufa ba ….

    Daddare ala’meen yashigo gidan yasa mu Inna Tana zaune akan tabarma yayinda muwaddat ke kwance akan gadon Tana rike da waya da dukkanin alamun chatting take, bayan sun gaisa da Inna ya waigo inda take kwance ya Kira sunanta..muwaddat

    Ta yatsina fuska sannan tace na’am ‘”ki shirya gobe da wuri saboda fitar asuba zamuyi “to kawai tace Masa atakaice Tana juya Masa baya ..

    Inna tayi kasa da muryarta can ta yadda muwaddat bazata jiyota ba “wai yana ga Kamar kana jin tsoron yarinyar, ka fad’a mata abinda ke ranka mana Kar fa wani yayi maka shigar sauri, duk da dai tunda tazo Banga Wanda ya kirata ba, ko ita takira ba ,bayan iyayenta “girgiza Kai yayi “ba yanzu ba tukunan Inna “

    “ya dai tabbata dai tsoron nata kake ji?

    “to kusan haka ne Inna duk lokacin Dana yunkuro zan fad’a mata sai fargaba ta hanani ..”ina ganinka jarumi a she kaima lusarina ne bansani ba…. “yanzu meye abun fargaba da jin rsoro anan?

    ” to Bari ni na sanar da iyayen nata “a’a Inna karki yi sauri yanke hukunci haka ,kinsa fa gaugawa daga sheidan ne, ki Bari mubi komai ahankali ke dai kiyi min addua kawai “to shikenan Allah yasa rabonka ce ,yace “ammen suka shiga wata hira har sanda goma ta buga yayi mata sallama da zai wuce ya k’arasa inda take kwance idanunta a lumshe suke ala’mun tayi bacci ya Dade tsaye akanta Yana dubanta Yana jin sanyi aransa sannan daga baya yasa Kai ya fice ….

    *********

    Washegari tun safe suka d’auki hanyar komawa ilori d’auke da tsaraba kauye iri iri danginsu daddawa kuka da gasashen kifi sai Kuma dankalin hausa Wanda yazamoto abinda aka fi nomawa kenan agarin kalgo ….

    Agajiye suka k’araso ilori saboda mugun gudun dayayi akan titi ….

    Suna shigowa harabar gidan idanunta ya sauka akan muhammed auwal zaune akan motarsa Yana fuskantar kofar tafkeken get din gidan yana ganinsu tare cikin motar yayi wata irin zabura ya duro ya tsaya yana kallon motar zuciyarsa na wani irin mahaukacin bugu.

    Ta tsura masa ido har sanda ya tsaya jikin motarsa ya harde hannayensa duka a saman kirjinsa tamkar wani babban mutun ,ahankali ta cigaba kallonsa kirjinta na wani irin mahaukacin bugu lokaci daya hankalinta yayi mugu mugun tashi ,kallo daya zaka mata kasan cewar ba cikin natsuwarta take ba ,tana cikin zallar tsoro da abinda idanunta suka ci karo dashi ne, sam batayi tunanin ganinsa a daidai wannan lokacin ba, ba ita ba hatta ala’meen ya d’an samu buguwar zuciya da irin kallon kaskanci dayake aiko musu dashi .

    Gaban bunayya ya dinga faduwa ya kura mata tsumammun idanunsa yana kallonta sam ya kasa d’auke idanunsa akanta yana duban abun tamkar a mafarki ,yayi bala’in mamakin ganinta tare da ala’meen, ya fara taku ahankali zai zo gurinta sai kuma wata zuciyar ta gargadeshi akan gara dai ya cigaba da tsayuwarsa a inda yake zai fi masa alkhairi ,idan ma ya k’arasa inda yake yace mata me ?

    Dan haka ya koma da baya ya jingina bayansa da jikin motarsa ya cigaba da kallonta ,Kallonsa take yi itama cike da matsanancin tsoro sannan a matukar kidime tun daga kasa har sama kirjinta na bugawa, zuciyarta kuwa kamar zata fito daga cikin kirjinta .

    Gabadaya halitar jikinta babu inda bai amsa ba .

    Da kyar tasamu ta yunkura ta zata fito daga cikin motar dan tuni ala’meen yayi parking taji sautin muryarsa a kasalance “koma ki zauna tukunna……

    Muwaddat page 21
    October 23, 2020 Muwaddat Complete

    Note
    error: Content is protected !!