Search
You have no alerts.
    The Den of Novels

    ..tsaye yake acikin lanbun shakatawa na cikin gidan hannuwansa duka rungume a saman kirjinsa yana tafiya ahankali ahankali yana lumshe tsumammun idanunsa saboda sanyayyiyar iskar dake ratsa jikinsa ..
    kmr ance ya bud’e idanunsa kawai yaga faiza tsaye a gabansa tana fuskantarsa cikin mayunwacin halin da shi kansa bazai iya misaltawa ba,
    ya d’an tsura mata ido yana Kare mata kallo na wani lokaci , sam itama bata da munin da zai kita, sai dai shi sam baya jin sonta acikin zuciyarsa, dan matukar muwaddah na rayuwa a doron kasa ba zai iya rabar wata mace da sunan soyayya ba, bare aure,tsawon minti goma suna haka sannan ya juya ahankali ya soma d’aga zara zaran yatsun kafafunsa cikin isa da izza ,tabiyo bayansa da sauri tana kiran sunansa yaya bunayya! yaya bunayya !!”dan Allah ka tsaya ka saurareni bakasan yadda nake jin zuciyata ba akanka.
    ko tsayawa bai yi ba bare ya nuna alamun amsawa kuma tabbass tasan yana jinta tayi saurin tarar gabansa tana ware masa hannuwanta duka “wai yaya bunayya me yasa kake min haka ne?
    “me yasa kullun kake tsanata kiyayya gareni?
    “ina da komai da za’a so mace dan shi ,to me yasa ni bazaka soni ba? tsayawa yayi kawai yana kallonta tmkr bai santa ba bare wata danganta dake tsakaninsu illa dogon tsakin daya jaja da karfi yabi gefenta ya wuce tayi saurin riko laulausar tafin hannunsa cikin karfin hali wanda hkn datayi yasa har taji wani azababben ciwon kai …

    cikin wani irin tashin hankali ya daka mata tsawa “kina hauka ne da zaki rike min hannu?”ko kin fara shaye shaye ne bansani ba ?
    cike da kuzari da karfin zuciya tace ” an rike maka hannu me zakayi?
    ” muhammed auwal bari na gaya maka lokaci yayi da tsawarka ta daina firgitani ,lokaci yayi da kowa dake cikin danginmu zasu san abinda ke tsakanimu da kai ……
    tasss tasss taji ya saukar mata wasu gigitattun maruka har guda biyu akan fuskarta “ki kyaleni faiza …ki rabu dani faiza, tunda nace ki kyaleni ,ki kyaleni mana ko ana so dole ne?
    in soyayya ce nace bana yi ana so dole ne?
    bari kiji daga yau karki sake takura min akan wannan shirmen saboda bana sonki bana sonki ba kuma zan ta’ba sonki ba ..yana gama fad’ar hk ya juya fuuuuuuu a fusace ya kalleta anan .

    tabi bayanshi da kallo fuskarta cike da tsansar damuwa da nadamar rike masa hannu datayi watakilla da bai kai hannunsa jikinta da sunan mari ba, hawayen dake boye acikin kwarnin idanunta suka samu nasarar gangarowa bisa kuncinta, tasa hannu ta goge wasu na sake zubowa cike da matsanancin sanyi jiki ta bi hanyar baya dan kar wani ya ganta cikin damuwa ,most especial aunty’nta muwaddah wacce kwata kwata bata kaunar ta ganta cikin damuwa, koda faiza ta shiga d’akinta sai ta rushe da wani tsumammen kuka ,kwantanta damuwar data shiga baya fad’uwa duk yadda take tunanin M. A ya wuce nan,, ya wuce da tunaninta sam ba itace agabansa ba, “to ita yanzu ya zatayi da rayuwarta.. ?
    “hakika bata san yadda rayuwarta zata kasance nan gaba ba matukar M. A yaki amincewa da soyayyarta ,”shin me yasa bazai sota ba ya rabu da aunty’nta tunda itace daidai shi ba muwaddah ba?
    har yammanci rana tana kwance a d’akinta taki fito dan batason kowa yasan halin datake ciki ..

    zaman M. A a gidan yasa faiza ta nemi takurawa rayuwarsa ,dan kuwa baya samun damar ke’bewa da sanyi idanunsa yadda yake so, duk abinda yake idanunta na kansa ,dan hk a daren ranar daya cika sati biyu da zuwansa ,ya kudurci a niyyar komawa lagos a washegari , lokacin da yake sanarwa dady zance komawarsa tana gurin, aiko taji haushi ma ganarsa, taji tmkr ta d’aura hannuwanta duka bisa kanta ta rusa ihu ne dan bakinciki tunda tasan saboda ita yasa zai koma.. ranar dai bata samu ishashen baccin kirki ba sbd tsananin tunanin M. A.
    tun da garin Allah ya waye yasa awanke masa motarsa .
    yayinda shi kuma yana can makale da muwaddah yana romacing dinta da sunan sallama ,yaso kwarai su koma tare ,amman taki sai daya gama tsotse mata baki da laguda mata jiki zuwa kirjinta sannan ya barta ya d’auki hanyar birnin iko..

    da daddare suna zaune su duka a parlour’n dady ban da faiza dake kwance a d’aki cikin bargo tana fama da zazzabin tafiyar M. A ,ana cikin hira ala’meen ya shigo gayar da dady Wanda kaida ne kullun daren duniya zai shigo gurin dady su gaisa kmr yadda yaga yaya akram nayi, ihsan tace” yaya ala’meen d’azu na hau samanka ban sameka ba ,nayi zaton ko zance ka tafi gurin latifa ya cilla mata muguwar harara “to idan can naje sai me kin ganki ko mumy … ,wallahi da ba dan ke din mai sunan mahaifiya bace dana shuka miki rashin mutunci yau..
    Suka kwashe da dariya “ai kuwa da munganku arana inji cewar eiman …
    ihsan tace “bama za’a ganmu arana ba ,daman sako zan bayar ka kai mata,”sai ki bari idan zani ,eiman tace yaya ni kuma ina son zuwa gurinta ta min lalle da kitso , ala’meen yace “Allah idan kuka dameni da zancen wata latifa zan mazgeku yanxu, kun ji min yara da tonon silili kowa sai yasan da wata latifa..

    suka sake kwashewa da wata dariya har dady ,wanda cikin dariyar yace “,ku rabu dashi zan sa direba ya kaiku sai kuje har muwaddat itama ta gano gari ala’meen ya dubi inda take zaune tana waya ,magana take kasa kasa a waya Amman babu mai jin abinda take fad’i ,saboda a hankali take magana ya tsura mata idanunsa yana kallonta yana magana da kannenta, kallo daya tayi masa ta d’auke kanta tare da gaisheshi “,ina yini maimakon ya amsa gaisuwarta sai yace ya zaman bakunta ?”lfy tace akaitace bai sake cewa komai ba ya samu guri ya zauna yacigaba da kallonta .

    M. A datake waya dashi yace “Halan wannan tsohon mayen ne ?”nifa Allah zan masa rashin mutunci akanki dan me zai dinga shiga tsabgarki, kema har da wani gaishe shi ya k’arasa fad’ar mgnr yana Jan tsaki”cool dawn kanina babu komai fa atsakaninmu, ka cire zargi zuciyarka “karka manta shi da kai duk abu guda ne agurina kmr yadda zan mutuntaka haka yazama dole na mutuntashi sannan na girmama shi …
    “tsaki ya ja ” ki shirya next week zanzo in tafi dake sannan ya kashe kiran ..
    Tayi shiru ta d’ago idanunta ahankali suka had’a ido da ala’meen yayi sauri kawar da fuskarsa gefe yana cigaba da hirarsa “hanyar d’akin ta nufa kar dai zargin Auwal ya tabbata al’amen sonta yake ?

    “kai impossible hakan ma bazai ta’ba yiwuwa ba ,shi da yake da matar da zai aura ..shi kuwa al’ameen binta yayi da wani shu’umin kallo zuciyarsa na sake bun kasa da soyayyarta da tayi masa kamun kazar kuka .

    Washegari da safe bayan an gama kalaci duk yaran gidan suna parlour’n mumy ,dady ya shigo gabad’aya yaran suka kaceme da hayaniya, kowa da abinda yake fad’i muwaddat ce kawai tayi shiru ta kama kanta saboda tun jiya da M. A yayi fushi daita akan yaya ala’meen ta rasa samun kwanciyar hankali da natsuwar zuciya dady ya dubeta yace “muwaddat ki shirya direba ya kaiki yawo ki d’an ga gari eiman tayi saurin cewa “Amman dady har damu ko? Dady yace da dai kun bari an kaita ita kad’ai idan kuka fita tare zaku dameta da hayaniya” kai dady yau fa week ce babu makarata kabarmu mu fita tare itama zatafi jin dadi ko aunty ?
    Kafin muwaddat ta bata amsa dady yace “ko babu makaranta malamin lesson dinku zaizo an jima ..

    Ana cikin haka sai ga ala’meen yashigo a shirye cikin shirin fita ,t shirt ce ajikinsa da bakin wando jeans, dady yace” yauwa tunda yayanku yau yana gida bama sai na had’a muwaddat da direba ba ,ala’meen ga kanwarka nan ka d’an fita daita taga gari, Dan tun zuwanta ba inda taje .

    Ala’meen yayi shiru yana kallonta soyayarta na sake huda zuciyarsa, yana da inda zashi Amman hakan bazai hanashi bawa wannan fitar mahimmanci ba ,
    Cikin rawar jiki yace ,”to dady ta shirya mana ai sai mu fita ya kalli eiman ” fushin me kike yi ?

    ihsan tace “wai Dan dady yace ba damu za’a je ba saboda lesson din zaa yi mana , alameen ya harari eiman “ai ko babu lesson bazaki shigar min mota ba sai dai ku fita direba ..

    Dady yayi murmushi” wai me ke had’aka da eiman ne sam kafi biyewa faiza da ihsan akanta?
    “dady yarinyar ce bata da kunya “eiman tayi saurin cewa “wai dady Dan akan aunty Ltifa tayi min waya ta tambayeni yana gida shikenan tun lokacin ya tsaneni ,dady yace to kai meye abun jin haushi ba kai da kanka ka nuna kana sonta ba nima fa na lura a yan kwanakin baka zuwa gurinta kmr da ala’meen ya shafa sumar kansa yana murmushi “babu komai dady kawai ina hutawa zata janyo azo a dameni bayan nayi mata gargadi ko abokaina suka zo nemana karta kuskura tace ina gida sai dai idan ta tambayeni amman dayake mara jin magana ce da an xo nemana sai tace ina gida dady yace “ke eiman kinji abinda kikayi daga yanzu in ana nemansa kice yayi balaguro eiman tace “to dady ai shine yake cewa idan mutane sunzo nemansa su tambayeni kuma haka kawai sai na dinga yi karya,byn karya babu kyau ala’meen cikin wasa yace”zaki rufewa mutane baki ko sai na bubbugeki ,tayi shiru tana gunguni ya d’an waiga bai ga muwaddat yace “wai ina wace zan fita daita ne ?

    Faiza tace bari na dubota tana ciki tana shiryawa tana shiga d’akin ta iske muwaddat kwance a d’akinta mamaki yakamata tace “,kai aunty ke da ake jira za ki fita yawo tare da yaya ala’meen shine kawai zaki zo ki kwanta .

    Muwaddat ta d’an yatsina fuska “,nifa wallahi banason fita haka kawai ,ni bancewa dady ina son ganin gari ba A6mman dan rigima wai wani sai an kaini yawo “ko dai da yaya ala’meen ne baki son fita ?
    “amman ina laifin a fita dake kiga gari tunda har yanzu bakigama sanin garin ilori ba ..

    “Ke nifa ban iya fita da wannan magananne mutumin wallahi sai yasa Kan mutu ya d8auki caji Sam Sam maganarsa bata da limit “ke ina ruwanki da maganarsa ,tunda ke ba mai magana bace bare kice maganarsa ta dameki?
    “Kuma ba surutu garesa ba ,wallahi idan kikaji yadda a waje ake complain din rashin kula mutane da bai yi sai kinyi mamaki agida kam ya kan ‘bata lokacinsa akanmu, kuma yanzu kinga fita nashi uzurin zai yi dady ya sashi”
    “Kin fahimcesa ba daidai ba shiyasa naga kin sauya fuska lokacin da dady yace ya fita dake yawo ..

    “Kinga faiza banson dogon turanci kema yanzu na kula zama dashi yasa kin dawo aku kuturu , abinda za’a yi yanzu kawai kije kice kaina ke ciwo shiyasa nashigo na kwanta .

    “Gasky aunty bazan iya ba kawai ki taso idan kika ki kmr kin wulakanta dady ne muwaddat ta yarda da shawarar kanwarta ta tashi ,ta sauya kaya jikinta ta shirya tsaf ta fito cikin wani had’adden material mai maseefar tsada kayan sunyi mugun kama jikinta tayi kyau sosai kana kallonta kasan yar Hutu ce ba’a kashe kudi a banza ba hatta jaka da takalmi kace domin kayan aka kerasu ta d’an yafa Gyalenta ,kana ta fito parlour’n dady ya dubeta yana driya “kai yar gidan daddy wannan irin kwaliyar haka kar fa ki gigita mutane gari gashi babanki bai tashi miki aure ba .
    Ta dan yi murmushi saboda wasan da dady yake mata ala’meen kuwa idanunsa kyam akanta yana son yaga yadda zatayi magana zata ce mishi su fita ko kuwa Jan aji ba zai bari tayi mishi magana ba ,koda yake ta cancaci fiyye da hakan yacigaba da kallonta saboda kwaliyarta ta burgeshi, shiyasa sam ya kasa d’auke idanunsa akanta ,lokuta dayawa mace mai yanga tana burgeshi amman baya son Jan aji yayi yawa kuma bai fiyye shiri da shagababbiya ba ,yana daya daga cikin abinda yasa yake gwasale eiman shagwabatar tayi yawa kmr itace auta idan tana wasu abubuwan ko sabir k’aramin kaninsu baya abinda take yi .
    tun muwaddat na yarinya yasanta da shagwa’ba saboda gata da yayi mata yawa ,Yasan dole ne ta zama sangartacciya domin gata mugun abu ne kuma gata guba ne agurin wasu ya’ya Dan bakowanne Dan gata yake samun ingantacciyar tarbiya ba ,tun sanin dayayiwa muwaddat tana yarinya har yau da wannan fuskar yake kallonta ,shi yasa lokaci datazo yayi kmr bai Santa ba domin bayason yashiga harkokinta bare yasha haushi, amman d’an zaman datayi yanzu a gidan ya kula kmr tana da kamun kai ,domin yanayin halayenta suna burgeshi bata da son hayaniya kuma bata da yawon surutu sannan akwai natsuwa ,illarta girman kai da Jan aji, gashi shi yanzu zuciyarsa ta kamu da matsanancin soyayyarta….

    Muwaddat tayi zamanta da Jakarta a hannunta shi kuma yaki yace mata tashi su tafi, sai dady yace “ku tafi mana tunda kin shirya ,zaman me Kuke?

    Ala’meen ne ya fara mikewa batare idanunsa na akanta ba yace “ki sameni a mota bata amsa ba ta Mike tabi bayansa ,Kafin ta k’arasa gindin mota shi har yashiga ya zauna ,tasa hannu jikin motar tana kokarin budewa sai taji shi gam a kulle , bazata iya ce masa ya bud’e Mata ba ,kawai sai ta matsa ta bud’e gidan baya ta shiga ta zauna ala’meen ya d’an waigo kawai ya kalleta baice komai ba ,yayi zaton ko ta kasa bud’e gidan gaba zatace a bud’e mata ,Amman sai yaga ta kame a gidan baya ,a zuciyarsa yace lallai ma wannan yarinyar direba zata maidani ko me?

    Ya dai daure ya tada motar suka tafi suna hawa titi ya fara sharara gudu ban da kidan zamani ba abinda ke tashi acikin motar ,glass din motar ya saita gefenta domin yasamu damar kallonta adaidai wannan lokacin wayarta tayi k’ara ta d’auka tana magana da abi Sai wani magana take cikin shagwa’ba.

    Alameen ya natsu sosai ahankali take magana Amman ya fahimci da Wanda take waya ,har wani lallaminta t
    yake “haba yar gidan dady menene abun fushi kuma ?
    “Cikin zumbura baki tace “to abi bayan kaine yau baka tasheni a bacci ba shiyasa har na makara banyi sallah da wuri ba yace “kiyi hakuri abinda yasa tun asuba Dana shiga massalaci ban fito ba sai da gari ya waye sosai shiyasa ban bugo na tasheki daga bacci ba, na yi zaton idan umminki ta tashi zata tasheki Amman kibari in Allah ya yarda zan cigaba da tashinki da asuba ince dai idan na ta dake kiyi sallah kina min addua kullun ?

    A marairace tace ” haba abi ina maka mana taya daman za’ayi in yi sallah ban wa babana addua ba “yauwa yar diyata nasan zaki min ina fatan kina jin dadin zaman ilorin?
    “Abi babu laifi garin akwai dadi “da fatan hajara bata takura miki don nasanta da zafi akan yaro “dady wannan karon bata matsa min ba da yake tasan halinka Dana ummi “to fatan dai baki da damuwar komai “wallahi abi babu wata damuwa,sai dai gaskiya ni abi ina son na dawo “ki k’ara zama tukunna har yanzu da sauran lokaci kafin ki koma makarata ki dai dinga duba litattafanki saboda kinsa da kun koma zango karshe zaki shiga kuma zamanki anan zaki fi samun nasuwa saboda takurawar bunayya .

    “Shikenan abi tunda kace haka na amince zan zauna Amman nayi kewarku ban da bunayya ,abi yayi murmushi “mu ma muyi kewarki ,bunayya daman wani kewarsa kikayi bayan kuna tare duk kwanakin nan ince yau kwanansa uku da dawowa, nan da sati biyu masu zuwa zai koma London take gabanta ya fad’i yashiga dukan uku suna hira da abi cikin nishadi shi kuwa ala’meen tukinsa yake Amman hankalinsa na gurinta sai lokacin ya gano yawon amsa wayoyinta datake yi ashe ba wayoyin samari bane da iyayenta take ko da wancan miskililin yaron da baya ganin mutunci mutane shi Sam yaron baya burgeshi ..
    Satar kallonta yacigaba dayi wato Dan tsananin gata har tashinta suke daga bacci ,bayan daren da suke rabawa suna waya ita dasu .

    Bai rage gudu ba sai da suka shiga ciki wata unguwa sannan ya rage gudu ya karya kwana yashiga cikin layin a kofar wani madaidacin gida yayi parking ya bud’e murfin mota ya fito ya Dan jira ko zai ga ta fito daga cikin motar Amman sai ya lura bata da niyyar fitowa wata wayar ma take amsawa sai ya tuna ashe bai gaya mata cikin gidan zasu shiga ba ,sai daya bari tagama wayar sannan ya bud’e mata murfin motar “bisimillah ki fito muje ki gaida matar abokina ya tsira mata idanu ko zatace wani abu batayi magana ba ta zuro kafafunta ta fito daga cikin motar suka jira suka shiga cikin gidan .

    minal ce ta fara tararsu da faraa ta kaisu parlour’n ta tana fad’in “kai alameen sai yanzu tun dazu ake jiranka Amman ka shanya min miji ,yayita kokarin nemanka a waya bai sameka ba .

    “Al’amen yace ku ya femin madam wallahi wani Dan uzuri ne ya tsaidani, ya fad’a yayinda yake kokarin zama a daya daga cikin kujerun kushin din parlour’n ya d’an dubi muwaddat sannan ya cewa minal “madam gafa bakuwa na kawo miki .

    Itama ta dubi muwaddat cike da faraa yayinda ta nuna mata wurin zama da murnarta da komai ta karbeta sai kace tasanta muwaddat taji dadi sosai da irin tarbar da minal din tayi mata ,suka gaisa a mutunce ta fara tsokanar al’ameen in ce sabon kamu akayi shiyasa tutar latifa ta fara dusashewa ?

    Cikin murmushi yace “no wannan kanwatace a lagos take ta d’an zo mana Hutu ne ina angon naki ?
    “Yana ciki gajiya yayi da jiranka shiyasa ya shiga ya Dan kwanta bari na tasoshi .

    Tana shirin shiga sai gashi ya fito daga bedroom dinsu ganin ala’meen tare da muwaddat ya sashi washe Baki da yake ya taba ganinta sau biyu dayaje gidansu cikin fara’a yace “a she ba kai kad’ai bane ,cewa zakayi yau muna da babbar bakuwa ya fad’a yana kallon muwaddat.

    Ta dan kirkiro murmushi dole kana ta gaida shi minal kuwa sai rawar jiki take tana nan nan da muwaddat kafin kace me duk ta zagayesu da abubuwan motsa baki al’maen Yasan ba lallai bane muwaddat taci abubuwan da aka kawo mata Dan haka yayi hanzarin cika cup da ruwan lemu ya tura mata gabanta ,abun mamaki sai yaga ta d’auka tasha suna ta hira minal sai tsoma muwaddat take cikin maganar dole sai da muwaddat ta saki jiki tashiga cikin hirar ,ta dinga saka baki jifa jifa, ala’meen zuba mata ido yayi saboda lura dayayi yadda yarinya ta iya lafazin iya magana cikin natsuwa tare da kwantar da murya da gogewar harshe hakan ya tabbatar mishi da tasan abinda take ,ala’meen ya dubi minal sannan yace “madan Dan Allah zan barta anan saboda inda zamu da oganki idan mun dawo zan kaita taga gari kmr yadda dady ya bukata minal tace “babu damuwa ya Mike ya kada mukullin motar dake rike a hannunsa tare da watsa idanunsa akan muwaddat Amman ita Sam bata kallesa ba asalima hankinta na can gurin turawa M. A sako .
    Yace “ayshatul muwaddat ki zauna anan kafin muje mu dawo muryarsa ta ratsa cikin dodon kunnenta da sauri ta d’ago kanta suka had’a ido saboda yadda yakira complete name dinta ya razana zuciyarta domin tun tasowarta babu Wanda ke kiranta da wannan sunan bayan Auwal dinta sai yanzu dayayi mata ,da muwaddat akasanta kuma dashi kowa ke kiranta, ita kanta mantawa take da sunanta na gasky saboda ba’a kiranta dashi sakamakon sunan uwarsu ummi ne daita, suna girmama sunan babu abinda yabata mamaki kmr yadda ala’meen yayi amfani da sunan gurin kiranta ..

    Ahankali ta gyada masa kai kawai Amman batayi masa magana ba, har ya fice daga parlour’n suna hira da minal saki fuska da fara’ar da minal ta nuna mata ya burgeta da kuma kyakkyawan tarba da rawan jikin datayi daita yasa taji tana son minal .

    Minal dai yar wani fitaccen d’an siyasa ne anan garin ilorin ba’a Jima da yin bukinsu da Hisham ba Wanda ya kasance babban aboki agurin ala’meen tare suka kare karatu a Rasha har yanzu minal karatu take ,ayanzu haka tana karatunta a jamiar ilorin, hira ce ta balle tsakanin muwaddat da minal tamkar sun dade da sanin juna muwaddat ta saki jiki sosai har kowa ya labartawa kowa tarihin rayuwarsa.

    Anan muwaddat ta wuni cur a gidan minal sai kusan yamma sannan ala’meen suka dawo daga unguwar da suka tafi suna cikin mota akan hanyarsu ta dawowa ala’meen yace bari in kira yarinyar nan ince mata gamu nan zuwa zan d’an zaga daita yawo sai mu koma gida .

    Har ya fiddo wayarsa da niyyar zai kirata sai kuma ya tuna bashi da number ta ,yayi tsaki ya maida wayar aljihunnsa hisham ya dube sa yace “Anya manage babu wani abu tsakaninka da yarinyar nan?
    Ala’meen ya Dan hararesa yace “,me kagani ?
    “Ni Kan haka nan naji zuciyata na zargin akwai wani abu koma ince akwai soyayya mai karfi tsakaninku “kai rufa min asiri ai wannan ba irin tamu bace “saboda me kace haka ala’meen byn akwai zumunci mai karfi tsakaninmu ?
    “nasan babu yadda za’a yi ka furtawa iyayenta kana sonta suki baka ,sannan ka daina ganin tafi larfinka..

    Ajiyar zuciya ya sauke da karfin gaske “duk ba haka bane yarinyar ce yar shagwa’ba kai kanka kasan bana shiri da yan shagwa’ba ya fad’i hk yana waskewa ,zuciyarsa na dokawa ,domin a yanzu ma dayake maganarta wasu wurare a kirjinsa sake bud’ewa sukayi soyayyarta na kara nikaya aciki .

    Hisham yace “Amman ni kuwa yarinyar batayi min kalar shagwababbiya ba..
    “Eh to wani lokacin ni kaina ina mamakin yadda take magana a natse Amman shagababbiya ce gurin daka ganta ,iyayen goyonta sun sangartata ainun kar mutun yaje yasaka kansa cikin tasko.”ai kuma ba daga nan take ba bakowa gata yake lalatawa ba ,akwai wasu ya’yan gatan da zaka gansu da tarbiya da kamun kai idan dai kana sonta na bada goyon baya dari bisa dari Dan gaskiya yarinyar tayi da kace aurena bai Jima ba Dana k’ara ta biyu daita idan kai baka da ra’ayinta ..

    “Dan iska to yaya zakayi da minal ?
    “Yaya kuwa zanyi daita Karka fa manta nmj nake inda daidai da auren mata hudu “to kuma duk Dubin matan dake garin nan basu yi maka ba sai bakuwar gidanmu ,hisham cikin dariya yace” ita naga ta min kasan nafi son auren yayan Hutu shiyasa nake sha’awar in tara matan Hutu agidana nayi ta hutawa dasu “to kuwa kwalelenka anan ,wannan tafi karfinka “ta yaya kake tunanin tafi karfina? Ince abun ba kokuwa bane ya k’arasa mgnr yana kwashewa da dariya “
    alameen yace “ka hakura kawai Dan ba baka zamuyi ba “idan Baku bani ita ba zaku jikata ku sha ne ?
    “No no saurayi dai zamu bawa danye sharab Wanda ba’a cirewa yanar kaciya ba domin yarinyar bata dace da auren nmj mai mata ba “

    Hisham yayita dariya har da rike ciki “kai nafa San inda zamceka ya dosa Amman kake son yin wani kwana kwana kai kace min hasashena gaskiya ne …
    Wallahi duk wani kauksucenka Nasan kana son yarinyar nan so kuma mai girma ,tun zuwana gidan na nasan za’a rina, a duk ruwan idonka da wuya ace baka sota ba ,ba zanga laifinka ba domin kuwa yarinyar akwai ruwan kyau Amman karka manta kmr a kunnen latifa domin ni zan fara bata labari za’a yi yar gida cikin murmushi alameen yace “sai kabari dai sai na fad’a da bakina sai kaje ka sanar mata dayake mamatace “to meye maraban dambe da fad’a ?
    Alamen yace” zage zage sukayi dariya hisham yace “tunda uwar lafita ta rigada tace Tabaka ai tamkar tazama matarka ce fatiha ce kawai da za’a shafa ba .
    Alameen yace ” kai ni rabani da zanceta ba ita nakeyi ba yanzu ” sai ta muwaddat ba ,ai nasan za’a rina tunda kai ba mutumin kirki bane..”ni wallahi tausayi yarinyar take bani itama hjy mantawa tayi da halinka shiyasa ta nanika maka yarinyar ..
    Suna ta hira har suka iso gidan suna shiga parlour’n suka iskesu suna hira ,muwaddat kishigid’e Akan kujera kanta ko d’ankwali babu ana iya karewa dogon gashinta kallo Wanda ya sha gyara yagaji ,sai kyalli yake,da alamar hirar tayi mata dadi domin hankhankalinta baya kan komai sai tautaunawar da suke ita da minal Dan haka bata lura da shigowarsu ba sai da hisham yayi magana tana waigowa taga duk ita suke kallo ..

    Littafin muwaddat page 17

    bismillahi rahmani rahim

    Da sauri ta tashi zaune sosai tare da gyara zamanta ,basu daina kallonta ba hakan ya ankarar daita a she fa kanta babu d’ankwali sai lokacin tayi hanzarin d’auka ta d”aura gaskiya irin gyaran da muwaddat takewa gashinta ba namiji ba hatta mace ‘yaruwarta zai iya burgeta bare nmj .

    Hisham ya d’an juyo ya kalli abokinsa ya lura shima ita yake kallo minal ce ta katsesu ta hanyar yi musu sannu da zuwa sai da kowa ya zauna sannan muwaddat ma tayi musu sannu al’ameen ya amsa idanunsa akanta yace “yau dai kun sha hira ,tun sanda suka shigo muwaddat bata sake yin magana ba saboda tsarguwa datayi da irin kallon da al’ameen ke binta dashi haka minal ta fahimci muwaddat batason yin magana agaban al’ameen da tunda suka shigo ta kasa sakewa hisham ne ma yake d’an janta da magana amman Sam taki saka bakinta acikin surutun da suke .

    Al’ameen ya Mike da kanshi ya nufi fridge ya bud’e ya d’auko lemo mai sanyi ya zauna yana sha, sai da ya gama sannan ya sake dubanta “mu tafi ko kar muyi dare ,batayi magana ba sai kawai mikewa datayi ta lalubi Jakarta ta rataya minal ta dubi al’ameen “gaskiya banso dawowarku da wuri ba domin hirar da muke bamu gama ba “to ko zama zanyi ku karasa ?

    “Kai ma kasan bakuwa bazata iya sakewa a gabanku ba ,gashi daga shigowarku ta d’auke wuta ko magana bata iya yi ..

    Muwaddat dai gaba tayi abunta har gaban mota suka yi musu rakiya minal tayita rokon muwaddat akan ta dinga zuwar mata hira muwaddat tace “bazan iya miki alkwari ba amman idan nasamu lokacin da kuma mai kawoni zan dinga zuwa …

    Hisham ya d’an kalli inda Al’ameen yake yana.dariya domin jin abinda muwaddat tace shi kuwa al’ameen shiru yayi kmr bai ji ba d’an Jan ajinta yasoma bashi haushi ya bud’e mota yashiga ya juyo ya d’n zubawa muwaddat ido domin yaga inda zata shiga amman sai yaga hisham yana k’ok’arin bud’e mata gidan gaba shiru yayi bai yi magana ba sai data shiga ta zauna sukayi sallama dasu minal har ya tadda motar sun fara tafiya sannan yace “na d’auka direban zaki sake meidani irin na d’azu”haba dai ta yaya zan maida kai diteba”eh mana gashi nan da zamu zo kin wani kwanta abaya ina janki tayi shiru ,da yaga bazata yi mishi magana ba sai cewa yayi “halan nayi miki kama da direbanki ne da d’azu ki wani rashi rashi abaya ?

    “Ba kayi kama ba, tabashi amsa a agajerce dayake bata fiyye son doguwar magana kamarsa ba ,sukayi shiru gabad’aya can kuma ya sake janta da wata hirar da alamun muryata yake son ji, kallonta yayi tare da cewa “amman fa nayi mamakin yadda kuka dade kuna hira da minal musamman yadda kike ba ma’abociyar son magana ba ,”kasan ita magana zuwa take bawai ayita zuba kmr ruwa ba yace “ko ?

    “Tace kwarai kuwa tun daga nan basu sake magana ba har suka iso wani katafarin mail na sai da kayan makulashe yayi parking din motarsa acikin harabar wajen sai daya bud”e ya fito kana ya zagaya ya bud’e mata yace “bismillah fito mu shiga ko, ta d’an yatsina fuska kmr kar ta fito sai kuma taga hakan bai dace ba ko babu komai d’an’uwanta ne yakamata ta nuna kulawarta.

    ta fito tana yatsina fuska saboda kai tsaye gida taso taje ta kira bunayya dan tun safe take expecting kiransa amman ko miss call dinsa bata gani ba .

    Duk yadda taki son jerawa dashi sai daya saita kafad’unsu suka jera suka nufi kofar shiga mail din suna gota wasu matasa da suke tsaye kusa da kofar shiga mail din ,dayan ya zunguri sauran da suke tare yana yi musu nuni da muwaddat.

    “kai kai kai had’uwa ji wata hadaddiyar zalziyya suka kalleta gabad’aya, dayan yace “gaskiya da ba dan wancan gayen da suke tare ba, da sai na d’an latsa ko zan yi sa’ar ta sairareni ,daya daga cikinsu yace “kai tafi can kana ganin yarinya wata muguwar yar hutu amman har kake zaton zata iya sauraronka ..

    “Ai ba’a anan take ba ,su irin wad’an nan yammata da suke furgitamu in akayi sa’a sunfi saukin kai in Allah ya doraka akansu ,babu wuya sai kaga kun daidaita “kai dan Allah karya ne ba dai irin wannan kalar ba wannan ko acikin yayan talakawa ta fito bazata saurareka ba bare kana ganinta kaga masu gidan Rana kaga mace na takun kasaita, ko gwal din dake wuyanta ya isa ya sayi motarka .

    Suka kyalkyale da dariya yayinda duk maganar nan da sukeyi acikin kunnen al’ameen amman baya zaton muwaddat taji su ,saboda ita tarigashi shiga ciki, da sauri ya k’arasa ya sameta suka jera tare “ki shiga ciki sosai ki duba abinda kike bukata kai kawai ta gyada masa sannan ta fara zagayawa tana bada baya, wasu samari suka shiga dubanta suna magana kasa kasa “kai Anwar dubi yarinyar dake gabanka kaga wata halitta da kyan diri mai d’aukar hankali ,cikin hanzari wanda aka kira da Anwar ya d’aga kai yana duban muwaddat” kai gsky cikar nan ta hadu da yawa Allah yayi halitta a wannan guri ,ina ma ina ma ..saif yace ina ma me ?

    “Ina ma yarinta ce gsky Dana more rayuwar duniya “,to ai yanzu baka makara ba kana iya latsawa ,ko zan maka sallama daita ne

    ai baasan inda rana zata fadi ba?

    ” ,lallai kuwa ka kawo shawara dan gaskiya ina sonta ,ya kake ganin zamu bullowa abun .

    Jira zamuyi sai tagama tsiyayarta ta kai idan za’a yi mata bill sai kayi sauri ka biya mata,kaga daga nan nasan zata maka godiya kaga mu km mun samu hanyar gaisawa daita ko ba haka ba ?

    Al’ameen na jin tautaunawar da samarin keyi akan muwaddat kawai ya tsinci kansa da jin matsanancin kishi akan magana ,cikin hanzari ya matsa gaba kusa daita yace “am har yanzu baki ga abinda kike so ba ne?

    “Uhmm ina dai dubawa yace “Jimana ta d’ago da sauri ta dubeshi “idan bazaki damu ba ki koma cikin Mota ki zauna zan zabar miki duk abinda kike so ..

    Mamaki ya kama muwaddat domin ita bataga dalilin da zai ce ta koma mota ta zauna ba ,kamar ta tambayeshi sai kuma tayi shiru har ta juya zata tafi sai taji yace kmr dame dame kike so?

    Batare data juyo ba tace chocolate kawai nake bukata “da kuma me “shikenan nan suna maganar ne ahankali yadda duk munafurcin mutun bai isa yace yaji abinda suke cewa ba ,musamman yadda al’ameen ya lura da hankalin mutane wurin yana kanta ,duk sanda ya d’ago idanunsa sai yaga maza da suke ciki ita suke kallo hkn ya sake k’ara masa kishi a zuciyarsa ,tana fita daga ciki yaji ya D’an samu natsuwar zuciya .

    Ahankali take taka kasa kamar batason takawa Yayinda duk wani matashin dake tsaye agurin hankalinsa da natsuwarsa ke kanta, wasu suyi magana azahirance ,wasu kuma acikin zuciyoyinsu a irin wannan lokacin da tasan da tare take da Auwal da yanzu sunyi fad’a yafi sau babu adadi domin cewa zai yi ita ke kiransu da jikinta ta hanyar rausaya wacce ita Sam batasan tana yi ba ,haka ta taso ta samu kanta da tafiya a natse kamar bata son yi , shi yasa duk lokacin da fita takamasu tare baya yarda ya barta ta fito ,sai dai tajirasa a mota shi yaje ya dawo idan kuwa tayi masa magana sai yace”bazai iya kasada da rayuwarsa ba ,sannan bazai jurar wasu kwaratan banza na kallar masa mata ba ,tana isa harabar gurin wayarta tashiga k’ara ,a natse tasoma k’ok’arin bud’e Jakarta batare da ta kai dubata ba ta ciro wayar tana d’aura idanunta akan screen din wayar ganin sunan dake yawo ajikin screen din wayar ne yasa take gabanta ya fad’i ,gefe daya na cikin zuciyarta sanyi taji acikin ranta jikinta har rawa yake lokacin data d’auki kiran ta manna wayar a kunnenta “hello Auwal dina “babu wani Auwal dinki ,tun jiya rabon muyi magana dake ko araye nake ko mace baki da matsala kawai kin tattara kin shareni kina harkokin gabanki ko”?

    Yadda yayi maganar cikin shagwa’ba da tsigar isa yasata ta murmusa “kai my auwa ka fiye rigima , mai ma akayi daka d’auki zafi dayawa ?

    “Tun jiya nake tura maka sako babu respond sai yanzu dakayi ra’ayi kirana ..

    “Ai bazaki sani ba sai ki min laifi amman idan na nuna fushina ki fini fushi tun daren jiya rabon da muyi waya ban kiraki ba why not ke ki kirani ?

    “To kayi hakuri, kadan bani minti goma zan shiga wanka ne idan na fito zan kiraka ta fad’i haka tana istigifarin karyar datayi domin idan ta bari yasan bata gida kuma tana tare da al’ameen mai rabata dashi sai Allah “ban yarda ba, adaidai wannan lokacin nasan abinda kikeyi ba wanka ba ,idan kuma wanka ne ki turo min nonona nagansu nayi kewarsu …..

    ya k’arasa fad’ar haka yana buso mata iskar bakinsa ta cikin wayar,take numfashi nta ,ya ne mi d’aukewa ta dafe saitin zuciyarta “Auwal zaka kasheni fa “idan na kasheki nayi rayuwa dawa ?

    “Ga matan nan dayawa a duniya sai ka zaba ka durje.

    “no no Sam bazasu min ba ,karki manta inda nayi karatu cikin kyawawan matan turawa Wanda yawo tsirara agurinsu bawani Abu bane duk banji daya daga cikinsu Sumin da zan iya rayuwata dasu ba ,ni kece macen Da zuciyata ta yarda ta amincewa rayuwa daita .

    Ta k’arasa jikin mota taja ta tsaya tana cigaba da sauraransa gabadaya ta manta da inda take saboda yadda maganarsa ke shiga cikin jikinta da zuciyarta .

    Al’ameen kuwa tafiyarta ya bashi damar yi mata tsiyaya sosai sannan ya fito ya sameta jikin motar tana waya ,bai ji komai ba aransa saboda tunaninsa ita da iyayen goyonta ne ,batare da yayi magana ba ya bud’e mato yashiga ya zauna itama ta bud’e ahankali tashiga ta zauna tana jin zai tayar da motar tayi saurin katse kiran gabadaya ,koda ta gama katse wayar batayi magana ba suka wuce .

    M.A kuwa yayita k wayar taki d’auka akalla sai da yayi mata missed call biyar bata d’aga ba, sai zuciyarta dake dokawa saboda fargaba tasan tana d’auka wayarsa ta saka kanta cikin matsala,Dan zai fahimci inda take , daidai sun kai wani traffic al’ameen yace “ki d’auka mana ko kiran bashi da mahimmanci ne ?

    “Sannan ma waye mai kiran ?

    Yayi mata tambayar batare daya juyo ba yana taka motar saboda danja ta tsaya Kan layinsu tace “karka damu da kowaye kacigaba da tukinka kawai “

    Bai ji dadin abinda tayi masa ba, dan hk ya sake wani magana ba ya maida hankalinsa kan tukin dayake ita kuma tana kallon gefen titi shi kam jifa jifa ya kan juyo ya kalleta, yanayin yadda take yin magana yana bashi sha’awa ,ta d’an juyo ahankali ta kalleshi suka had’a yayi saurin kawar da idanunsa tamkar ba ita yake kallo ba ,tacigaba da kallonsa yanayin yadda yake tukinsa taji ya burgeta saboda wannan karon Jan motar yake sannu ahankali cikin natsuwa da kwarewa da nuna ganintar tuki kowa yaga yadda yake sarrafa sitiryarin yasan ya kware da tuki ,agaskiya tukin nasa ya burgeta tunda har taji tana sha’awar itama taja mota da kanta dan dai abi ne bayason can al’amen kamar yasan abinda yake zuciyarta ai ya d’an waigo ya dubeta “kin iya mota kuwa?

    Ta d’an kada kai “eh to Auwal ya fara koya min amman har yanzu hannuna bai fad’a ba “ya had’e rai dosai jin ta ambaci sunan Auwal ya cigaba “ai ina jin ko kin koyi tuki ina ganin dady’nki bazai barki kija mota ba da kanki ba, “nima ina tunanin haka shiyasa ban maida hankali wajen koyo ba .

    “Amman yana da kyau ki iya koda bazaki dinga ja ba, cikin murmushi tace ” zan yi kokari naga hannuna ya fad’a suka dan yi shiru ,sai dai muwaddat ta damu da yadda ya takura mata da kallo can ya sake takalota da magana “Amman tunda zaki dade agarin nan me zai hana ki dinga yawan kaiwa minal ziyara kmr yadda ta bukata?

    “ba damuwa duk sanda na sami lokaci zan rinka zuwa “idan kin samu lokaci ko idan mai kaiki yasamu lokaci?

    Jin ya jefa mata tambaya sai tace “daga ni har mai kai ni din .”amman ai ke kina da lokaci tunda ba karatu kikeyi ba kina cikin Hutu ba kuma aiki kike zuwa ba ..

    “Haka ne amman ina karatu saboda wannan zango gabadaya zan rubuta jarabata ta karshe ta bashi amsar tana had’e fuska saboda ta lura hira yake son suyi ,ita kuma bata fiyye son hira dashi ba ,haka suka cigaba da tafiya yana janta da magana tana d’an sharesa har suka iso gidan tana shirin fita daga motar yace “am…aysha.

    Ta waigo da sauri “kin mata kayanki ta kai ganinta ga kayan manya ledoji ne guda biyu shake da kayan ciye ciye ta d’an yi murmushi “nagode sosai amman chocolate kawai zan d’auka aciki daman kuma ita nace ina so ..

    Yace “shikenan naji amman ki d’aure ki shiga dasu ko su eiman da mamana suna so ,ta d’an yatsina fuska saboda bata son kinkimar kaya tace “bari idan nashiga sai na turo su d’auka ,ta fita ta fara tafiya zata shiga cikin gidan yana zaune a motar har tashige gidan ba abinda yake banda kallon tafiyarta taku take cikin natsuwa irin na matan da suka amsa sunansu mata ,shi kansa yasan tana da mugu kyau kmr yadda mutane suke fad’a kuma ya yarda da had’uwarta da ajinta ,yasan bazata ta’ba d’aukar kayan tashiga dashi ba ,da haka da kansa ya kinkimi kayan ya bita dashi cikin gidan ya tadda kannenta zagaye daita kowa na tambayarta guraren daya kaita ,ita kuma tana cewa su bari sai ta huta ..

    Al’ameen nashigowa parlour’n ya ajiye mata kayan gefenta ya tafi abunsa ta bi bayansa da kallo Wanda batasan dalilin hakan ba ,Allah sarki ta furta cikin zuciyarta tana jin rashin dadin abinda tayi masa ,tasan da Auwal ne sai dai abar kayan ,amman ko sama da kasa zasu had’e bazai d’auko mata ba ,ta ina ma girman kai da miskilancinsa zai sa ya biyota dashi “my Muhammed Auwal kenan yaro da izzan , shi Sam baya d’aukar raini ga kowa ga tsabar miskilanci Wanda yake daya daga cikin abinda yasa take naci akan kaunarsa .

    Tana son Auwal tamkar yadda take son rayuwarta ,tana son shi tana son su rayyu tare muddin rai Auwal daban yake acikin maza bazata gaji da furta hakan ba….

    Tunda take kallon maza bata taba ganin mai irin yanayinsa ba komai yafisu ,ba dan tana son shi ba ,sai dai tasan ummi bazata bari aurensa ba saboda kaninta ne …

    Tasan dakace auwal yayanta ne ,tasan sai inda karfin ummi ya kare amman sai ta mallakamusu juna

    Mummy ta fito daga d’akinta tana fara’a “aa yan yawo kun dawo ?

    Muwaddat tayi murmushin tace “Eh momy mun dawo “kece yau wata yarinya tasha yawo har ina da ina kukaje?
    Mmn sudais ce….

    Muwaddat page 18
    October 23, 2020 Muwaddat Complete
    bismillahirrahmanirrahim

    Note
    error: Content is protected !!