Search
You have no alerts.
    The Den of Novels

    ..sauran kwana biyu muwaddah ta tafi ilori,nabeel ya kawowa M. A ziyara sun dad’e a d’akinsa suna hirar karatu daga bisani suka zarce da hirar muwaddah, inda nabeel yace M. A yakira masa ita su gaisa ,batare da ‘bata lokaci ba ya d’auki wayarsa ya kira layinta tare da fad’a mata dalilin kiran, amman abun mamaki kai tsaye tace masa ba zata zo ba.. ..

    jikinsa yayi mugu mugun sanyi gbdy ya rasa ma mai zai cewa nabeel ?ai idan ya fad’a masa abinda tace dariya zai yi masa, murmshi nabeel yayi ya dafa kafad’arsa ” friend halan cewa tayi bazata zo ba naga duk kayi wani iri?

    M. A yayi shiru ya kasa cewa komai dan bai San abinda zai fad’a masa ba ,dan wani bakinciki ne ya tokare masa wuya, “tunda ba zakayi mgn ba tashi ka rakani na gaishe da su ummi daga nan magaisa daita, ahankali suka mike stare suka fito daga bangarensa suka nufi bangaren ummi .
    yayinda M. A alokacin babu abinda idanun M. A suke kwad’ayin ganin kmr muwaddat so yake yaga bakin cewa baza”azo ba …

    Lokacin da suka shiga part din ummi ,suka iske gabadaya ahlin gidan zaune a parlour muwadda ummi da abi suna hira, tana ganin shigowarsu ta mike tsam ta haye saman ummi tana rausaya kmr wata fure, atare suka bita da kallo kafin daga baya
    M. A yayi gyaran murya tare da nunawa nabeel gurin zama da hannunsa sanan ya zauna.
    nabeel ya zauna had’e da gaishe da ummi da abi dake zaune suna murmushi ganinsa , suka amsa cikin sakin fuska da kulawa suna tmbyrsa ‘yan gidansu ,nabeel yace “duk suna lafiya sunce agaisheku ,hira suka shiga yi sama sama har inda nabeel yace daman nazo mu gaisa daku ne da kuma muwadda , gashi kuma naga ta gudu ummi tayi murmushi tace “uhmmm baby kenan ai sha’aninta sai ita, ai hka halinta yake bata son mutane da Zara mutane sun wuce uku to yanzu zatabar gurin ,idan kaga dariyata ko motsinta to ita da wannan kanin nata ne ,.

    suka kwashe da dariya ban da M. A da yayi kicin kicin da ransa tmkr wanda aka aikowa da sakon muwata yana takaicin kiransa da yaro da ummi take , can kmr minti goma nabeel ya mike yana musu sallama ummi tace”kar dai tafiya zakayi tun baka ci komai ba ?

    yace” ummi wallahi a koshe nake ban dade da cin abinci ba na fito , nagode sosai da kulawa Allah ya k’ara girma yayi gaba M.A na biye dashi a baya suna zantawa har bakin motarsa M. A yayi masa rakiya yashiga motarsa ya tafi shi kuma ya dawo part din ummi da niyyar cin kaniyar muwadda har zai haye bene sai yaji abi ya kirasa yana d’an juyo ahankali yasoma lokaci daya kuma yasoma jiyo kamshin turarenta mai tsuma zuciya da kashi jiki ya waiga hanyar step itace ke saukawa tana rausaya sai dai fuskarta a had’e tazo ta wuceshi ta zauna kusa da ummi ,abi ya numfasa yace “ni kuwa bunayya sai nake ganin abokinka nabeel yana dama dama da diyata ko dai shima yana son ayi yar gida ne?

    M. A ya fad’ad’a murmushinsa yace “kai abi shi ya soma wannan dayen aikin ,bare ma bai ce ba ,sai dai idan ana so ayi masa tayinta ne, sai mamanta ta shirya masa toshi akai masa dan naga kmr tana yi dashi ,gbdy suka kwashe da dariya ban da muwadda dake aika masa da wani shegen kallo ,takowa yayi ahankali har inda take zaune yace “ke yarinya kallon wulakacin me kike min?
    “tunda baki son tsofaffin samarinki ,baki son yaro irinmu, ai kya so nabeel tunda shi ya girmemin nesa ba kusa ba ….

    ki hanzarta fad’awa mamanki ta tanadi gida da mota har ma da kujerar hajji matukar nabeel za’abawa ke saboda shi daman ya’yan manya irinki yake son aure ..
    ummi tace “tafi can makwad’aitan banza ,baku kawo ba kuna neman abaku saboda mutuwar zuciya”no ummi ba haka bane yanzu zamani ya canza ririta maza akeyi fiyye da tunaninki “to banda diyata wallahi ta k’arasa mgnr tare da cewa ga abincinka can kan dining table amman bansani ba ko a d’akinka zakaci..

    “anan zanci kai tsaye ya nufi table din cin abinci ya d’an ja kujera gabansa ya xauna sai daya bubbud’e yaga abincin da’aka shirya masa sannan yace ” muwaddat taso ki xuba min abinci .

    “baza’azo a zuba ba, kar Allah yasa kaci “da kuwa kin jawowa kanki matsala dani yarinya ,kin dai san hali…ummi tayi saurin cewa tasan hali me zaka mata ?

    “No ummi babu ruwanki wannan tsakaninmu ne muddin batazo ba tasan abinda zamanta ko babyn mamanta?
    sosai ta fahimci inda manufar zansa ya nufa ,kar yazo ya hanata bacci daren ,dan hk ta mike domin k’ok’arin isa inda yake ta tsaya tana tmbyrsa abinda za’a zuba masa ,ummi tace “wallahi muwaddat duk kece kike biye masa shi yasa ya rainaki banci haka yaushe …..
    abi yace “uhmmm babu ruwanki tsakaninsu ne.

    M.A ya nuna mata kalar abincin dayake so ta zuba masa yana duban fuskarta yana shafa saman kafarta da tafin kafarsa nan take jikinta ya kama rawa cikin sauri sauri ta zuba masa ta juya ,bai ce mata komai ganin har lokacin idanun ummi na kansu , yaja plet din abinci gabansa ya fara ci yaso kwarai yana cin abinci yana kallon kyakkyawa fuskarta amman yana d’agowa gefen dayafi tunanin zata zauna yaga wayam ta bar parl tun, daga lokacin bai sake d”aura kwayar idanunsa akanta ba har dare , cikin dare yayi k’ok’arin zuwa d’akinta koda yaje yaji kofar a kulle ….
    Yana barin bakin kofar d’akinta bangarensa ya nufa duk yana jinsa wani iri iri yaso had’u daita ko dan ragewa kansa sha’awarta dake makale azuciyarsa, haka ya kwanta ya kunna wayarsa yana kallon nonuwanta yayinda hannuwansa duka ke kan joystick dinsa yana lumshe ido da kyar yassmu bacci yayi nasarar daukarsa cike da tunaninta.

    ********
    washegari da misalin karfe takwas na dare byn ya gama duk wani shirinsa part ummi ya nufa domin ya sanar mata da damuwarsa akan muwaddat ,bakinsa d’auke da sallama yashiga k’aramin parlour’n ,ana ya iske abi zaune yana shan coffee yana sauraren labarai ,ummi na zaune a gabansa ,hannunta akan kafafunsa tana yi masa masaging ,atare suka amsa masa sallama cike da matsanancin farinciki, kullun idan suka kalli tillon d’an nasu sai su rasa abinda ke musu dadi ,tabbas ya’ya rahma ne ga rayuwar iyaye ,Allah dai yabamu masu albarka.
    Shigowarsa bai sa ummi ta cire hannunta akan kafafun abi ba sai ma cigaba datayi da abinda take masa,shi kuma yana lumshe idanu..

    Ahankali M.A ya k’araso ya zauna kusa da abi tmkr zai shige jikinsa cikin fara’a abi ya kai hannunsa ya shafa kansa yace “babana ya’akayi ne ?
    M.A ya sune kai tare da Sosa keyarsa alamar jin kunyar ummi ,parlour’n ya d’an yi shiru ,can abi ya waigo ya dubesa sannan yace “bunayya kayi shiru ina fatan dai lafiya ko akwai abinda kake so ne ?
    Ya jefa masa tmbyr duk da yasan tatsuniyar gizo bata wuce ta koki ,M.A ya shafa fuskarsa sannan ya d’ago cikin yanayi na rud’ani yace dama..daman ina so ..sai kuma yayi shiru saboda idanun ummi dake kansa..

    Murmushi abi yayi yace “relax my son kwantar da hankalinka ni mahaifinka ne ita kuma wannan mahaifiyarka ce ka saki jiki kayi mana magana muna sauraronka, wani irin numfashi yashiga fitarwa mai zafi saboda tunanin yadda ummi zata amshi mgnr agabansa ..

    Abi ya sauke naunayen ajiyar zuciya sannan yace “hakika bunayya zaka aikatawa abi da umminka babban kuskure matukar ka boye musu damuwarka ,zanji babu dadi araina Amman babu komai kana iya tafiya idan baka shirya gaya mana mataslarka ba muryarsa a kasalance yace “abi daman magana nake son yi da ummi ..abi yayi shiru can ya numfasa yace “to shikenan bari na tashi na baku guri ya yunkura ya Mike tsaye yana murmushi ya bar musu d’akin .
    byn fitarsa ummi tace “ina jinka meye matsalarka?
    Natsuwa ya Nemo ya sanyawa zuciyarsa dama gangar jikinsa sannan ya fara mgn cikin murya tausayawa “ummi daman akan muwaddat ne ,wallahi ni dai har ga Allah ina sonta kuma da aure na fad’awa abi shine naga kema yakamata na fad’a miki ……
    ummi tayi shiru kawai tana kallonsa cike da matsanancin mamaki can ta numfasa had’e da kiran sunansa Wanda wannan ne karon na farko tunda aka haifeshi bata ta’ba kiransa da Auwal ba, “auwal ni aganina Kamar kayi kankanta a batu na soyayya bare akai ga batu na aure ,yanxu fa kake 22 a duniya ,ba soyayya ce ta dace da kai ba ,karatu ne yafi dace da rayuwarka , muwaddat kuma da kake kwakwar so bazan baka ita ba saboda kayi mata kankanta a aure, bama haka ba, bana dai son nayi muku auren kuruciya ne daga kai har ita yara ne gara tasu wanda ya girmeta mai hankali ..

    Ya dubi ummi kmr zaiyi mata kuka yace ” ummi ki daina tunani haka ,nima mai hankali ne, duk abinda kike tunani na kuruciya bazanyi arayuwar aurenmu daita ba,”kai dai ka hakura kawai banason naci..
    kansa ya sunkuyar kasa “bazan iya hakura daita ba ummi saboda ni kaina a halin yanzu nasan ba soyayya bace ta dace da rayuwata ba ,Amman bansan yadda akayi zuciyata ta farka wannan alamarin mai wuya misaltuwa ba ,zuciyata batayi shawara dani ba ummi da sam bazan kamu da soyayyar abinda nasan zai wahalar dani ba ,sai dai babu yadda zanyi na d’auki abun a matsayin wata jarabawa ce daga Allah, Dan girman Allah ummi ki amince ki yarda ki bani auren muwaddat ,ni ita kadai ce araina ita nake so ,duk rayuwar da babu ita to babu Auwal …..

    “Ni dai ba zan yi wannan had’in ba, ka hakura ka cigaba da karantunka .. yana jin ta fad’i hk yasan ba yarda zatayi ba ,shi ya rasa dalilin dayasa batason aurensa da muwaddat ,Sam bai d’auki hujarta tacewar suna da kuruciya ba zuciyarsa tafi zargin wani abu daban .mikewa yayi ya bar parlour’n jikinsa a sanyaye, tabi bayansa da kallo har sai data daina ganinsa “shiru tayi byn fitarsa, saboda ta lura mgnrta ta haifar masa da damuwa “me yakamata tayi ?
    “idan ita ta amince da aurensu ita muwaddat din fa?
    ” kwata kwata bata ga wata alamar tana son shi ba, illa shakuwar dake tsakaninsu mikewa tayi cikin sanyi jiki ta shiga bayi tana zance zuci . …

    *********

    washegari tunda sanyi safiya direban alhji ishaq ya d’auki muwaddat a mota suka d’auki hanyar ilorin, tunda suka hau babban titi ibadan, ba abinda direba yake sai sharara gudu.

    muwaddat ta kwanta abayan mota tana tunanin rayuwar dazatayi a garin ilori kafin ta dawo, hkn nan yau ta tsinci zuciyarta tana murna ganin mahaifiyarta da kannenta sa’banin lokunta baya da bata son zuwa saboda takurawarsu gareta akan abinda tafi tsana arayuwarta .

    yayinda kuma wani bangare na zuciyarta yake cike da matsanancin kewar muhammed auwal dinta..
    “amman duk da hakan tana dokin nesanta kanta daga gareshi ,sannan da d’okin ganin ‘yan’uwanta taji dadin yadda ummi tace sai tayi watanin a can kafin ta dawo sam ranta bai ‘baci da hukunci ummi ba , gara tayi nisa akan tacigaba da rayuwa tare da auwal yana tsuma zuciyar da tsumammiyar soyayyarsa da bata hango nasarar komai acikinta..

    runse idanuwanta tayi “Allah sarki ko ya zai ji idan ya dawo ya iske bana nan?
    ahankali zuciyarta tashiga hasko mata irin bori da haukan da zai yi, tayi murmushi kawai “my trouble auwal ….ta furta hkn tana bud’e idanunta.
    Allah Allah ta dinga yi ta ganta a ilori wurin mahaifiyarta da ‘yanuwanta ko zata ragewa zuciyarta damuwar datake ciki..

    sun isa garin ilorin da misalin sha biyu da ‘yan mintuna ,mai gadin gidan ne ya fara yi musu maraba yana ganin motar gidan alhaji ishaq, ya hamgame tafkeken get din gidan, direban ya danna hon tare da dannan hancin motar cikin harabar gidan.
    direban nagama tsaida motar ,nan da nan sai ga yaran gidan suna ta fitowa da gudu zasu zo tarar auntynsu, eiman ce takaraso da gudunta tazo ta rungume muwaddat tare da fadin “tun daxu muke ta zuba ido ,muyi waya lagos abi yace tuni kun taho kuna hanya “

    muwaddat tayi murmushi tace “muna hanya wallahi sai yanzu Allah ya yi isowar mu, ince dai dady yana gida?
    “baya nan sun tafi kalgo da yaya al’aemeen da yaya akram da aunty faiza .

    “waye kuma yaya ala’meen muwaddah ta tmby cike da yatsina fuska?
    “yaya ala’meen na kalgo mana dan kawu muntari kinsa yanzu a agidan nan yake tunda yagama karatunsa a rasha ya dawo nan ds zama ,sai alokacin muwaddat ta tuna a she fa suna da wani d’anuwa a kasar turai,
    “yaya al’meen babban dan yayan hjy hajara mahaifiyar muwaddah ne sannan kuma shine na uku a kamfanin dady ,shi yake rike da ragamar kasuwancisa na gida dana waje saboda yaya akram tunda dawo kasar bashi da wata isashiyar lafiya, mutunci da amana tare da mutuntaka yasa ala’meen yazama na hannun damar dady.. ..

    Ahankali muwaddat ta kai hannu ta d’auki karaminn kaninta saber suka shiga cikin gida, yara na ririke daita suna murnar ganinta.
    a main parlour din gidan ta tadda mahaifiyarta ta isa gabanta tana fara’a cike da murna ganin mahaifiyarta hjy hajara ta d’an saki murmushi na murnar ganin babbar yarta sannan tace “mutanen iko har kun iso?

    muwaddat tace “wallahi momy isowarmu kenan har nagaji da zaman mota “sai data rusuna ta gaida mahaifiyarta tukunna ta zauna kannenta gabadaya suka zagayeta, duk dadi ya kamata gata ga mahaifiyarta ga kannenta wannan yana daya daga cikin abinda yasa wani lokacin take son kasncewa dasu, takowani bangare idan kana cikinsu zaka samu natsuwa ayi hira ba kmr can ba, gida shiru daga su sai su babu wani dibe kewa idan ba abi yana gida ba..

    a daidai lokacin direban daya kawo muwaddat ya dinga shigowa da lodin kayan tsarabar da suka zo dashi ,bayan an kawowa direban abinci yaci ya d’an huta yace”zai tafi domin alhj ishaq yace kar ya kwana hjy hajara tayi masa alkhairi mai yawa ya kama hanyar komawa gida yini sukayi suna hira da ‘yan kannenta ..

    *********

    a birnin iko kuwa agajiye auwal yashigo gidan kafad’arsa rataye da yar saman rigarsa hannunsa rike da wayoyinsa yana furzar da iske gajiyar daya kwaso ,kai tsaye part dinsa ya nufa ya fad’a cikin d’aya daga cikin kujerun parlour’n yana sauke numfashi “washhhhhhhh allah ya fad’i yana dafe goshinsa da hannunsa d’aya had’e da relaxing “kai zuwa aiki not easy “
    bayan kamar minti talatin ya mike tsaye ya shiga uwar d’akinsa ya , ya shiga bayi ya watsa ruwa ya fito yana goge kanshi da karamin towel , ya tsaya gaban mirrow yana kallon face dinsa, murmushi ya saki tare da girgiza kai sannan ya kai hannunsa ya d’auki d’aya daga cikin wayoyinsa yashiga neman number muwaddat domin ta kawo masa coffe, abun mamakin number’ta swichoff ake sanar masa,ya ajiye wayar yana jan dogon tsaki ya k’arasa gaban wardrobe dinsa ya bud’e ya ciro kayan shan iska wando three quarter da rigar hamless ya dawo gaban mirrow ya d’auki man gyaran gashi ya shafa akansa ,ya murza hannuwansa yana kwantar da gashin kansa “ya rabbi ko me yasa ta kashe wayarta?
    ya fad’a sannan ya feshe ilahirin jikinsa da turare me sanyin kamshi ,ya kira number Ummi “tana d’auka muryarsa a raunane ala’mun gajiya yace “ummi na dawo kicewa baby ta kawo min abinci “

    “okay kawai ta fad’a atakaice ,shi kuma ya kashe wayar ya dawo parlour’n ya janyo system dinsa ya jona a chage ya kunna yasoma opereting dinta , ko cikakken minti biyar bai yi ba, yajiyo k’ara kwnoking kofar d’akinsa ahankali ya yunkura yana gyara wandonsa daya d’an zamo daga tsukaken kugunsa yana fad’in “baby nah har kin k’araso i really miss you my baby .

    “sai dai yana bud’e kofar yayi turus saboda zatonsa bai tabbataba ba, musabaha sukayi da sadik direban ummi, sannan ya d’an matsa masa yashigo parlour’n hannunsa rike da sakakken basket din kaba , wani kulolon bakin ciki ne ya ziyarci zuciyarsa “a kufule ya d’auki waya da niyyar sake kira number muwaddat,still shiru dan haka sadiq na fita shima ya nufi bangaren ummi yana shiga yasoma zare idanu ,yana duban ta inda zai ganta sam bai kawo bata gidan ba, tunaninsa ko boye masa kanta tayi saboda yawon damunta dayake yi, ganin bai ganta ba ya dubi ummi dake zaune tana duba jarida “ummi…..”na’am bunayya ya’akayi ?
    ” ina muwaddat?
    wata fad’uwar gaba ce ta ziyarci zuciyar ummi ta d’an d’aure, dan daman shi ya d’aure fuska “tace oho ka duba d’akinta mana juyawa yayi da sauri ya isa bakin kofar d’akinta ya buga kofar amman shiru babu ko motsi kasada kawai yayi ya tura kofar parlour’n yashiga, koina agyare sai kamshn turarenta ne ke tashi ta kona, ahankali yake bin d’akin da kallo yana jin fad’uwar gaba da bai san dalilinsa ba.

    koina tsab amman babu ita babu dalilinta ya k’arasa jikin kofar bayi, ko zai ji motsinta ,nan ma shiru ya sake yin kasadar shiga wayam bai ganta ba ya dawo main parlour din yana kwallawa binta kira, yatsina fuska ummi tayi tana mamakinsa .
    gabad’aya behivious dinsa ya canza baza kace wannan shiru shiru miskili yaron bane mara son magana .. .

    kallonsa take tana k’ara mamakin yaushe ta haifesa ya girma har yasan wata aba soyayya dayake neman haukacewa , binta ta k’araso da sauri ta tsaya daga nesa kad’an dashi saboda yadda taji kiran “ranka ya dade gani “ina muwaddat ? ya tambayeta yana tsare gira tamkar wani hamshakin
    magidanci.

    binta ta kalli ummi sannan ta juyo ta kalleshi “ina muwaddat ya sake maimaitawa yana rawar murya ?
    “ranka ya dad’e ban sani ba ,amman ka duba d’akinta wata killa tana ciki tana hutawa “bata ciki na duba koina ban ganta ba “to gsky bansa inda tayi ba.. “

    bai tsaya sake cewa komai ba kawai ya fita a matukar fusace gabad’aya ya kasa samun natsuwa ya koma part dinsa zuciyarsa na harbawa da karfin gaske , ahankali yashiga zagaye parlour’n ya kai gwaro ya kai mari, kafin daga baya ya sake fitowa kai tsaye wajen gidan ya koma yasamu guri ya zauna a d’an karamin dakalin gidan yana jiran yaga ta inda zata bullo har shida tayi bai ga dawowarta ba, wanda zuwa wannan lokacin har abi ya dawo daga office , hakan yasa ya mike ya koma ciki zuciyarsa na tabbatar masa da tana cikin gidan bataje koina ba, dan bata ta’ba wuce wannan lokacin a waje ba.

    take wani bangare na zuciyarsa ya bashi tabbacin tana d’akin ummi naunauyen ajiyar zuciya ya sauke yace “ya rabbi kasa lafiyarta lau.. shiru yayi tare da rufe fuskarsa da hannuwansa after like few second ya sauke hannun yana furzar da iska tare da sakin ajiyar zuciya .

    *********
    washegari da daddare bayan dady ya dawo daga kalgo gabad’aya yaran gidan suna parlour’n suna cin snaks,ban da faiza dan hutu taje, yaya ala’meen ya shigo cikin parlour’n ya gaishe da dady sabir ya taho da gudu ya dannesa , shi kuma yana dariya ya d’aga shi sama iman tace “la yaya bamu gaya maka ba jiya byn tafiyarku kalgo aunty muwaddat taxo daga lagos muwaddat dake can gefe zaune ta d’ago kanta da kyar ta gaidashi ya amsa mata cikin rashin sakin fuska yace “sannu fa ya mutanen iko?

    “lafiya ta bashi amsa tana d’auke kanta daga kallonsa “dady yace “ok a she fa aminu bai san muwaddat ba?
    ala’meen ya d’an kad’a kai “ina jin ko nasanta tana yarinya ne eiman tace “gasky yaya ba k’aramin dadewa kayi ba a turai dan na lura kowa aka nuna maka sai kace wai bakasan shi ba ..
    momy “tace rabu dashi mantuwa ne dai dashi ta yaya zai ce bai san muwaddat ba, tun kafin ya bar kasar nan ake zuwa daita kalgo yayi murmushi “kwarai anyi haka goggo nima ba ina nufin ban santa bane kawai dai kamanninta ne na manta da yake ba hoton tane dani ba ..

    ita dai muwaddat tun daga gaisuwa bata sake cewa komai saboda yadda taga bakinsa na yauki dan ita batason wulakanci da yawon mgn , Dan ta raina irin marabar dayayi mata, ganin irin yadda mutanen gidan suke ta murna da rawar jiki daita hatta yaya akram da bai jin dadin jikinsa dackansa yazo suka gaisa ,shi sai gani tayi yana rawar jiki da kannenta.
    ala’meen ya samu guri ya zauna yace “eiman ina mamana tashige ne taxo tabani abinci naci eiman tace “kai dai yaya komai sai dai kace faiza ko ihsan ne zasu yi maka bazaka bari wani ya had’a maka ba, dole dai sai su.. cikin harara yace “ina ganin eiman sai na fara doke miki baki akan surutu nan naki.

    Ihsan tace to ai kaine yaya kafiye sakar mata fuska dayawa .
    dady yace”wannan ai abu ne mai kyau ban da abunki ihsan idan bai jaku ajiki ba kud’in ma bazaku sake dashi ba kmr yadda kuke a yanzu , ala’meen yayi murmushi “barta dady ina ganin itama ajiye sunan uwar zanyi a gefe na jibgi banza, suka kwashe da dariya ala’meen sai daya gama barkwancinsa sannan yace momy ihsan a shirya min abinci yunwa nake ji dan banso wannan jagwal din ta xubo min eiman tayi tsagal tace “kai yaya nice jagwaal din kmr wata gwanjo?

    “itace mana ko kin ta’ba ganin na yarda kin zuba min abinci? dariya suka sake kwashewa da shi adaidai lokacin da ihsan ta ajiye masa kular abinsa..

    duk hirarsu tana shiga cikin kwalkwaluwar muwaddat ahankali take satar kallonsa kyakkyawa ne shima, asalin fulanin kalgo amman bai kai muhammed auwal dinta a komai ba,auwal dinta kyakkwan ne ajin farko miskilani mai kyau da haiba dogo mai matsakaitan jiki mara son hayaniya da barkwanci shi sam wannan haukan bakwarcin bata gabansa dan wani lokacin idan abi nayi sharesu yake yayita cika yana batsewa sai dai ita tabiye musu ..

    ahankali jikinta ya dinga bata ita ala’meen yake satar kallo dan hk ta mike tsam ta yiwa dady sallama ta nufi d’akinta tana shiga ta sauke numfashi mai had’e da soyayyar auwal sai yanzu take sake jin wani irin kewarsa amman yazama dole ta nisanta kanta dashi domin a yadda take ji zata iya mallaka masa komai nata wanda hkn shine babban abun kunyar dazata aikata arayuwarta.

    “ya rabbi have marcy on me “ka za’ba min abinda yafi dacewa da rayuwata, Allah ka sani, ina son bawanka muhammed auwal amman ummi na neman hanani mallakarsa,
    ” ya Allah ka fahimtar daita.. tabbas ita kanta tasan abun kunya ne gareta ace ta auri kaninta auwal amman yaya zatayi da kaddarar soyayyarsa?
    ahankali ta zauna bakin abun gado tayi shiru tana tunaninsa kafin daga baya ta janyo wayarta dake kashe tana jujjuyawa kmr ta kunna sai kuma taga gara kawai ya nema ko a waya ya rasa,
    Saboda jin muryarsa kawai yana saukar mata da kasala mara misaltuwa, zamewa tayi ta kwanta tana runtse idanunta gabad’aya bacci take son yi amman ta kasa runtsawa sai juyi take tare da janyo pillow ta rungume ajikinta , jiya zuwa yau kawai tashiga wani yanayi akan rashinsa ta dinga jin ina ma bata baro garin lagos ba, da yanzu suna can tare makale da juna , a yanxu da suka yi nisa da juna ta fahimci rabuwa dashi ba k’aramin tashin hankali bane gareta saboda ya rigada yayi gangar jikinta da zuciyarta mugun sabo da salonsa, cigaba juyi tayi akan katifarta tana tunaninsa.

    *******
    Bangaren auwal kuwa tun jiya ya kasa zama ya yashiga bangaren ummi yafi so babu adadi, haka ya dinga zariya tamkar wani mahaukaci ,yana jin kmr ya saka ihu gabadaya tunaninsa tana cikin wani hali na rashin lafiya ne yasa bai ganta ba, a ranar sam bai samu ishashen bacci ba saboda kewarta.

    da misalin karfe 9:00 na washegarin ranar ya fito ya nufi bangaren ummi ,duk ya bi ya damu kwarai da gaske har wata katuwar rama yayi daman ya lafiyar kura ?
    ji ya dinga yi kmr ana fixgar ransa , tun shekarajiya rabon daya saka muwaddat dinsa acikin kwayar idanunshi ,ya iske su ummi a parlour hankalinsu kwance sai sheka dariya suke suna hirar barkeanci ita da abi .
    jikinsa a sanyaye ya k’araso zuwa inda suke ya rusuna ya gaishesu cike da girmamawa, suka amsa masa cikin sakin fuska, tukunnan yasamu guri ya zauna yana baza idanuwa ko zai ga sanyi idaniyansa .

    abi yayi d’an murmushi sannan ya tsura masa ido yana dubansa batare daya yace masa komai ba ,
    shiru ne ya ziyarci parlour’n, byn kmr minti biyu ummi ta mike da kanta ta had’o masa abun kari ,chips da soyayyen kwai da ruwan tea mai kauri , ta janyo karamin table gabansa ta ajiye da kulawa sannan ta nufi d’akinta domin k’arasa shirinta na zuwa gurin aikin.

    da kyar ya iya bud’e bakinsa yace “ummi . .
    ta juyo ahankali tana had’e fuska tare da cewa
    “kaci abinci first before anything, sannan kar naji kayi magana ka ci abinci kawai ,kai kawai ya iya d’aga mata batare da ya kalli inda abinci yake ba, saboda sam baya jin cikinsa zai iya amsar komai matukar bai san halin da muwaddat take ba.
    zuciyarsa muwaddat kawai take son gani, ita kawai yake kwadayin gani yasan da zarar ya ganta zai koshi.
    gabad’aya ya tattara hankalinsa zuwa kofar d’akinta yaga ko zai ga wulgawarta.
    , abi ya d’ago “ya dubesa ahankali yace”ya’akayi ne bunayya ko akwai damuwa ne ?
    ya juyo da kyar yace”abi….sai kuma yayi shiru “to me ma zai ce masa ..?
    ganin yaki yin magana yasa abi ya mike yana kiran direbansa a waya, saboda yasan duk abinda zai fito daga bakinsa bazai wuce akan muwaddat ba …..

    abi na barin parlour’n shima ya mike jikinsa na rawa ,abubuwa sun yi masa yawa ,zuwa yanzu zuciyarsa tagama samun natsuwar muwaddat tana cikin koshin lafiya kodan ganin ummi da abi cikin kwanciyar hankali da annashuwa, domin kuwa da wani abu na damunta fuskarsu kad’ai ya isa ya sheida masa ,ya koma d’akinsa ya kwanta lamo yana tunanin inda ta shige acikin gidan.

    wasa wasa sai da muwaddat ta share wata guda cur a ilori ,sannan auwal yasan inda take,abakin akram kuma daman kwalkwaluwarsa ce ta bashi shawarar ya kira can yaji tunda ya tabbatarwa kansa muwaddat bata gidan domin duk inda zata boye aciki gidan dole zai kwakulota, yana gama wayar ya nufi gurin ummi tamkar wani zarare , ya isketa zaune shigowarta kenan daga asibiti tana hutawa .

    ya k’arasa ya durkusa a gabanta kmr zai yi kuka “ummi nah me yasa kika aikata min haka?
    ” ummi zaki kasheni da kanki wallahi, at least yau tsawon wata guda kenan kina kallona ina haukan neman muwaddat ashe kinsa inda take ummi……?

    “to me zan ce maka bunayya?
    “me kake son nayi idan ba haka ba ?
    gani nayi kana neman hargitsa min kwakwaluwa da shirina akanta “me kake tunani mutane zasu ce idan na baka aure muwaddat?

    ” muwaddat, auntynka ce fa ..
    “yanzu misali idan an aura maka ita me zaka iya mata dan Allah dan annabi in banda tsaurin ido da rigima irin naka..?

    wani far yayi da idanu zuciyar na dokawa numfashinsa da yayi kokarin d’aukewa yayi saurin dawowa dashi gangar jikinsa sannan yace “haba ummi nah ,bai kamata kece min haka ba ,ki duba lamarin da kyau, tunda nace ina sonta, ai nasan yadda zanyi daita..

    “kai rufe min baki ban son shirme banza, ka daina ganin ka had’a degree dinka, ka samun aiki a hannuka yasa zakayi tunani ka isa aure .
    “no no aure not yet for you now sai dai gaba ,idan kuma auren kake so kaje gaba ka nemo mata…
    ya marairace muryarsa sosai tmkr mai shirin zubda hawaye sannan yace “wai ummi me yasa kike ganin kmr nayiwa muwaddat ‘kankanta, Allah ummi ki daina min kallon yaro, saboda ni ba yaro bane,duk lokacin da naji kince min yaro bakinciki nake ji kmr na kashe kaina ..

    wata bazawarar dariya ummi tayi “to kai din meye bunayya ?
    “yaushe na haifeka ka girma?
    ” think har pent muwaddat ta saka maka acikin gidan nan, ta baka abinci abaki..

    “ko ma dai menene ummi ai ba itace ta kawoni duniya ba.. ..
    ummi tayi saurin zaro ido waje driya na neman kufce mata amman tayi sauri meidawa ta had’e rai sosai dan kar ya kawo mata wargi “ummi wallahi zan iya da ita ina tabbatar miki nan da wani lokaci zan …
    taja tsaki tace “karka nemi raina min hankali bunayya ..
    ,ko tursasani dan bazan iya had’a wannan auren ba, idan kai kanka kana da hankali bazaka sawa ranka yin aure a halin yanzu ba, guda nawa kake bunayya?

    duk yadda M.A yaso ya fahimtar da ummi cewar shi fa aure yake so, taki sai kawai ya tashi cikin hanzari ya koma d’akinsa ya hau shirya kayansa gudu gudu yana duba agogon hannushi cikin gaugawa yagama shirinsa tsab ya fito ya bud’e bayan motarsa ya saka jakar kayansa ya zagaya yashiga mazaunin direba ya fige motar aguje ya bar gidan..

    wani irin gudu yake sharara akan titi duk wanda yaga irin gudun dayake sai yabi motar da kallo tare da tausayawa matukin mota ,aguje ya dinga wuce motaci akan titi yana cizan lip’s dinsa na kasa burinsa bai wuce ya gansa agabanta ba.

    koda ya isa gidan a bangaren yaya akram yayi masauki, yana zauna akan daya daga cikin kujerun dake parlour’n tare da runtse tsumammun idanunsa , d’aya byn daya yaran gida suka dinga shigowa suna gaisheshi , ya bude idanunsa da kyar yana amsa musu cikin rashin sakin fuska , cikin minti biyar kacal aka cika masa gabansa da kayan motsa baki , amman babu abinda ya fara ci ,illa ruwan lemu daya tsiyaya a glass cup yashiga kurba ahankali ahankali , shima ya sha ne kawai saboda gajiyar hanya daya dibo.

    ahankali tashigo parlour’n bakinta d’auke da sallama, taja ta tsaya daga gefe can ta jingina bayanta da bango ta rungume hannuwanta bisa kirjinta tare da tsura masa fararen idanunta tana kallonsa cike da matsanancin soyayyarsa take gabanta yashiga fad’uwa sbd fargaba dan ganin ko kallon inda take tsaye bai ba ,illa kur’ban ruwan lemun daya cigaba dayi, ahankali ta bud’e bakinta “bunayya sannu da zuwa ya… ..
    da sauri ya dakata daita ta hanyar daga mata “bana bukatar jin maganarki ko wani abu ..
    cikin firgici da tashin hankali tashiga d’aga kafafunta zuwa inda yake “me yasa bunayya?
    ” dan Allah kayi hakuri wallahi ba laifina bane i don’t mean to hurt you a matukar tsawace yace “nace karki min magana kada ki kulani ,kada ki karaso gareni kawai kija bakinki kiyi min shiru. ..

    jikinta na rawa ta k’araso ta durkushe agabansa,har bata san sanda ta d’aura hannuwanta duka bisa cinyoyinsa tana kallon cikin kwayar idanunsa da suka rikid’e suka canza kala ,ya kawar da fuskarta gefe guda yana kallon wani bangare alamun baya son kallon fuskarta.

    “dan allah muhammed auwal kayi hakuri ta kai hanuta ta juyo da fuskarsa gareta suna fuskantar juna a take zuciyoyinsu suka bugawa ,take suka soma jin wani sauyi na daban agabadaya ilahirin jikinsu wanda ke gauraye da tsantsar soyayya.

    idanunta suka cicciko da ruwan hawaye muryarta a sarke tace “dan..dan Allah auwal kayi hakuri karkayi fushi dani ,ya buge mata hannuta batare dayace mata komai ba, ta sake kai hanuta jikinsa “dan Allah ka saurareni mana “
    “ki kyaleni ni mana nima daina sonki tun da burinki kenan na daina sonki , dan allah ki rabu dani ,ki manta dani, ki manta da maganar na ta’ba sonki arayuwa ki.. ki mantani ya k’arasa fad’ar haka yana fidda huci mai zafi.

    ..dan allah kayi hakuri mana akwai maganar da idan na fad’a maka zaka saurareni bazan iya jure ciwon rabuwa da kai ba, ta karasa mgnr tana kwakwameshi ajikita tana kuka… ya fixge rigarsa data rike yana furzar da iske had’e da kawar da fuskarsa.

    Tarasa yadda zatayi dashi zance zuci tasoma jikinta na rawa ……”ina kaunarka Auwal Dan Allah karka juya min baya akowani hali zan kasance tare da kai, ta maimaita hkn acikin zuciyarta yafi sau Goma ,tana mai kai hannu ta shafa kasumbar dake kwance a fuskarsa, kafin daga bisani ta riko fuskarsa sosai ta sanya kwayar idanunta dake tsiyaya ruwan hawaye acikin nasa …..aran tace ban san hka soyayyarka tayi tasiri acikin zuciyata ba, sai lokacin danayi nisa da kai ..
    “a da ‘kan’kantarka nake yiwa amman a yanxu nasan kai ne duniyata ruhina yana tare da kai , “nayi alkwarin bazan ta’ba rabuwa da kai ba, bazan sake yin nisa da ruhinka ba ta karasa mgnr duk acikin zuciyarta tana rungumeshi gam ajikinta tana zubar da hawayen rashin bayyana masa abinda ke zuciyarta…..

    kuka take sosai tana rungume dashi ajikinta tmkr za’a kwace mata shi “kayi hakuri Dan girman Allah ka daina fushi dani bazan iya jurar fushika ba.. hawayen dake boye acikin idanunsa yayi saurin maidawa domin idan yayi kuskuren bari suka sauka akan kuncinsa tabbas ya tabbata yaron datake kiransa dashi shi kuma abinda yafi tsana kenan arayuwarsa….

    mmn sudais ce
    MUWADDAT PAGE 15

    Note
    error: Content is protected !!