Muwaddat – Chapter Eleven
by Aysha A Bagudo…….washegari da ummi zata tafi hospital tace” muwaddah ta shirya suje ta duba lafiyarta ,duk wani abinda ya kamata ummi tayi mata tayi ,inda ta gano muwaddah bata d’auke da cutar komai ajikinta, illa malaria wanda mostly daman ita ke haddasawa mutun ciwon kai mai tsananin, allurai tayi mata har guda uku da magunguna, da kyar muwaddah ta sha tana zuba shagwa’ba ,byn ta sha maganin ta samu guri ta kwana akan gadon dake ajiye a office din ummi…
sai gurin azahar suka koma gida ,muwaddah nata jiran ummi tayi mata zance tafiyarta ilori aranar dan ita har tagama shirinta tun daren jiya, amma taji ummi ta share da zance, sai ma gayyatar M. A asibintinta data ji tana yi ,”bunayya ina son gobe idan Allah ya kaimu ka shirya ka fara zuwa asibiti domin taimakamin da wasu abubuwa kafin lokacin komawarka yayi.
tsadadden murmushin nan nasa yayi mai tafiyar da ruhi saboda dimples dinsa dake lotsawa a duk sanda yayi, hakan ke sake fito da ainihin kyawun halittar da Allah yayi masa ,ahankali ya motsa la’b’bansa tamkar mai koyan mgn yace “kai ummi yaushe zan kama zuwa wani asibiti , ai wannan asibintin naki sai ke, ni aikina ya wuce zuwa wannan asibintin naki ,ko kin manta abinda na karanta ne ummi ?
“idan kin manta ummi bari na tuna miki d’anki muhammed auwal ishaq orthopedic sugyren ya karanta a kasar london tsadadd’en
course din nan wanda samun likitoci irinmu ke da wuya a wannan lokacin ,ni yanzu idan ba gani nayi fuskar mutun tayi damage ba,jikin mutun yayi dagadaga ba , ko bangaren macen da brest dinta ya zama tsuma , ni kuma nayi k’ok’arin naga na maida shi na yarinya kmr muwaddah da sauraransu, bazan tsaya wani ‘bata lokacina akan wasu abubuwa ba, miwaddah najin haka taja tsaki aikinka kenan duk maganarka bata wuce nono tayi mgnr a kasan ranta tana kawar da idanunta daga garesa..
Ummi tace “Allah ya shiryeka bunayya, ban da abunka ai zaka iya zuwa, baza’a rasa wanda zaka taimakawa ba, tunda kullun da irin matsalolin da muke fuskanta asibiti.
“a’a ummi bafa zani wani asibinti domin yin allura da k’arin ruwa ko cs da dai abubuwa makamantansu ba, amman idan kun samu abinda ya danganci aikina kuna iya kirana….
ummi ta ba’ta fuskar tace “wannan girman kan naka da son girma nan ke had’ani da kai wallahi, bansan inda ka samo irin wannan halin ba , mahaifinka sam babu ruwansa , “haba ummi ki dai sake magana karki ce baki san inda na samu halaiyeta ba, ai ni komai nawa na abi ne babu wani banbaci atsakaninmu sai abinda baza’a rasa ba,kuma ina alfahari da hkn ya k’arasa maganar yana murmushi tare da kallon inda muwaddah ke zaune, wacce ko kallon inda yake bata yi ba..
haka suka yita hirarsu ta tsakanin uwa da d’a, yayinda muwaddah
tayi shiru tana sauraransu, dataji hirar ta isheta ta mike ta koma d’aki,
bayan tafiyarta ummi ta sake fuskantarsa sosai da zancen ,da kayar dai ta samu ta shawo kansa ya amince zashi a gobe..
washegari wuraren shabiyu saura ummi ta kira layinsa saboda taji shi shiru har lokacin bashi da ala’mun zuwa ,lokacin da kiranta yashigo wayarsa yana makale da muwaddat a d’akinta yana rud’ata da salon wasaninsa masu tsayawa arai da wuyar mantawa , mikewa zaune yayi daita ajikinsa ya zaunar daita akan cinyarsa ,tayi yunkurin tashi Amman ya rike hannuta gam cikin nashi yana murzawa ahankali ahankali, sannan ya lalu’bo wayar acikin aljihun wandosa yana dubawa, kafin daga bisani ya d’auka muryarsa a kasalance yace “ummi ……
“Wai bazaka zo bane bunayya?
” zanzo mana ummi “
ummi tace “to ai naga har to 12 yanzu banganka ba “karki damu ummi nah gani nan zuwa yanzu just give me some minit “to shikenan d’an albarka ina nan ina expecting din zuwanka,ya katse kiran ya kwanta flat akan katifar tare da fixgo muwaddah samansa ,sai gata ta haye ruwan cikin suna fuskantar juna ya had’e fuskarsu yana busa mata numfashinsa mai gauraye da hucin sha’awarta kana yace ” muje ki rakani asibitin gurin ummi, ta girgiza masa kai ala’mun bazata ba.
“ba zaki ba?
tace “ka tafi dan Allah ina son na huta ,hannuwansa duka yasa ya kamo fuskarta ya d’aura lip’s dinsa akan nata yana yana yawo dashi kafin daga baya yasoma k’ok’arin tsotsa lis’p dinta ,tayi saurin kawar da fuskarta gefe tana fidda numfashi sama sama tare da cewa”i don’t like it bunayya, banason abinda kake min, abubuwan da kake min kwanakin nan sun fara damuna plz control your self.. ..
tana gama fad’ar haka ta kai hannuta kirjinsa tana k’ok’arin mikewa tsaye,bai mata komai ba har tagama mikewa ta tsaya tare da jiya masa baya shi kuma ya tashi da kyar yana gyara zaman rigarsa ya fice daga d’akin.
Tana ganin fitarsa ta sanyawa kofar d’akinta key ta koma tayi kwananciyarta tana fidda numfashi sama sama dan ita kad’ai tasan yadda take ji ajikinta a duk sanda suka kasance tare .
ahankali M.A yake direving yana tunanin muwaddah, har ya k’araso tangamemen asibintin ummi wanda ya amsa sunansa saboda tsaruwar da yayi, amman still tunanin muwaddah yaki barin cikin kwal’kwaluwarsa, yarasa wani irin zazzafan kauna take mata ?
Ya rasa me yasa yake sonta irin hk da har yake jin idan ya rasa arayuwarsa zai iya mutuwa ?
M. I profetional hospital shine sunan hospital din ummi , kai tsaye gurin da’aka tanada domin ajiye motar M. D ya nufa yayi parking din motarsa a daidai lokacin da wasu daliban likitoci suka fito harabar asibinti sanye da fararen kaya , “basma Kalli motar can inji cewar kausar tana matsa yatsun hannun da karfi , basma a d’an kid’eme ta tsurawa tsaleliyar farar motar mai bakin glass idanun tana kallo har lokacin da M. A ya fito daga cikin motar sanye da farin riga da wando jeans baki ,sai bakin glass dake manne da idanunsa kallo daya yayi musu ya d’auke kansa akansu ya soma neman layin ummi kira daya ta d’auka “ya’akayi bunayya ka k’araso ne?
“eh ummi “okay ka bani minti biyu zansa a taho da kai, “haba ummi duk matsayina ,maimakon kizo da kanki shine zaki turo wasu , ni dai dan Allah kizo da kanki kinji ummi nah”to shikenan gani nan, ya katse kiran tare da maida wayar cikin aljihunsa ya rungume duka hannuwansa akirji yana jiran fitowar ummi ,yayinda har lokacin basma da kausar idanunsa ke kansa suna santin irin kyawun dayake dashi..
“ummi ta fito da kanta tarban tilon shagwa’ba’bben d’anta , hakan kuwa yayi masa dadi sosai ya sakar mata murmushi ya riko hannunta”ummina ina sonki dayawa …
“Nima haka yarona ina sonka fiyye da yadda kake sona , tare suka jera zuwa cikin asibinti suna mgn kasa kasa , duk inda suka gilma sai an gaishe da ummi cike da girmamawa ,ita kuma sai nunawa mutane M. A take , ga yaronta dake karatu a London, haka mutane sukayita gaishe shi yana amsa musu a dake cike da miskilanci, har suka k’arasa office din da’aka tanada dominsa .
ummi tana murmushi tace “bunayya ga office dinka dake, zaman jiranka ..
ahankali ya saki murmushi yana karewa office din kallon ,komai yayi babu abinda babu ,hadadd’en office ne wanda ke d’auke da makeken table zagaye da mazaunin likita, sai kujera guda biyu dake fuskanta ta likita Wanda idan akayi baki zasu zauna akai , daga can gefen kuma gadon duba marasa lafiya ne zagaye da farin labule ,da extra room, sai bayi da tangameman hotonsa wanda yayi a gurin graduation dinsa a London,daga bangaren gabas kuma daddumar sallah ne,sai karamin frame din hoton abi da ummi shi kuma yana tsakiyarsu a gefen calander, sai kamshi office din yake yi tamkar daman akwai Wanda ke aiki acikinsa , naunayen ajiyar zuciya ya sauke had’e da lumshe idanunsa ya juyo ya kalli ummi byn ya karewa office din kallo “ummi nah na gani na gode kuma na yaba sosai komai yayi kmr yadda nake bukata ,Amman nifa ba aiki zanyi ahalin yanzu ba.
“nasani bunayya,nasan ba aiki zakayi ba amman ina son kasan da zamansa, saboda ina son anan zakayi aikinka tare dani idan ka had’a master’s dinka, ya zagayo bayanta ya d’aura habarsa a kan kafad’arta yace “shikenan ummi nah tunda hk kike so bani da yadda zanyi …ummi tayi murmushi ta shafo fuskarsa tace “haka nake son ji ,Allah yayi maka albarka “ameen umminah,suka fito tare daga cikin office din ummi ta rufe ,ahankali suke takawa ummi na zagayawa dashi cikin asibintin har kusan la’asar sannan ya fito da zumar komawa gida anan ya sake cin karo da basma da kausar ya kallesu ,suma kallonsa suke ,ya kawar da fuskarsa yashiga motarsa ya figa aguje ya nufi bakin get.
basma ta juyo ta kalli kausar “gsky mai motar nan ya had’u dayawa haka ma motarsa ya hud’u “wallahi kamar kinsa abinda nake son fad’a kenan koda yake kyawunsa bana banza bane mahaifiyarsa akwai tsabar kyau ,kausar tayi shiru saboda kyawunsa da had’uwarsa yafi karfin tunaninta ,ina ma ta samu irinsa , saboda irin mijin datake muradin samu kennan arayuwata, sai dai sama tayiwa yaro nisa sai dai ya d’aga kai sama yayi kallo,ina ita ina auren d’an M. D, mukarama, tun tana sauraron surutun basma har tazo bata fahimtar komai ..
*********
Sai daya jera kwana biyu yana zariyar zuwa hospital din ummi bisa tursasawarta ,sai dai babu abinda yake sai zaman office dinta da latse latsen waya ,kwana na uku yace bai zuwa gidansu nabeel zashi , duk yadda ummi tayi dashi yace bai zuwa haka ta hakura ta barshi .
cikin kwana na biyar ummi ta kirasa cikin tashin hankali muryarta kmr zatayi kuka byn ya d’auka tace “bunayya kana ina kazo hospital yanxu Yanzu dan Allah?
Shima cikin matsanancin tashin hankali yace “lafiya ummi ,me ya faru ?
“kai dai kazo yanxu ta katse kira, batare da ‘bata lokaci ba ,ya fito cikin Sauri rigarsa a hannu yana k’ak’orin sakawa, a daidai bakin motarsa ya k’arasa saka rigar ya bud’e motar yashiga ya zauna yana kunna motar hade da danna hon da karfin gaske .
Yana isa a harabar asibinti yayi parking yana k’ok’arin fitowa daga cikin tsaleliyar motarsa sukayi kicibis da kausar sanye cikin uniform ,ahankali ya fito daga cikin motar yasoma tafiya cikin takunsa na d’aukar hankali, ta tsura bayansa ido tana kallonsa tana jin ina ma yazamo mallakinta ,jikinsa ne yabashi kallonsa take dan haka ya waiwayo shima yana dubanta sai dai nashi kallon da gani na tsantsar tsana ne tattare da takaicin kallon datake masa ,yaja tsaki ya girgiza kai kawai ya wuce saboda arayuwarsa ya tsani irin wannan kallon da mata ke masa ,kusan minti goma tayi a dan kare agurin tana kallon bayansa …
Tun daya shiga emergency hankalinsa ya tashi matuka sakamakon kukan da tarar da wasu matune nayi , Allah Allah yake ya isa office din ummi yaga halin datake ciki a daidai bakin kofar shiga office dinta suka had’u ta riko hannunta cikin azama ta nufi d’akin tiyata dashi bai ce komai illa binta dayake ahankali har suka shigo d’akin dake cike da manyan likitoci ..
Suna ganinsu suka ja baya suna duban yaron da ake tunanin shi zai duba mara lafiya .
abinda ya gigita ummi har yasa ta kirasa cikin tashin hankali ,shi sam bai d’aga masa hankali ba, saboda inda sabo ya rigada ya saba ganin irin irinsu agurin practical ,wata k’aramar yarinya ce kwance akan gadon marasa lafiya a d’akin tiyata wacce shekarun haihuwanta bazasu wuce shahud’u ba a duniya , tana fidda numfashi sama sama ranta hannun Allah, sai dai gabad’aya fuskarta tayi damage,sakamakon ‘yan ta’ada da suka kawowa mahaifinta ta hanyar kawo masa hari ,saboda ba’ason ya zarce kujerarsa ta d’an majalisar jahar dayake kai , sukayi rashin sa’a basu samesa a gidan ba ,wannan bakincikin yasa sukayi tillon diyarsa fad’e sannan suka watsa mata acid a fuska .
ahankali M. A yake kallon yarinyar yana girigiza kai , yana sake mamakin wannan tashin hankali da maseefar son siyasa irin ta mutanen nigeria,akan siyasa babu abinda bazasu iya yi ba, ya tausayawa yarinyar sosai ,batare da bata lokaci ba ya bukaci kayan aiki yana cigaba da dubanta tare da tunani ta inda zai fara ,cikin rawar jiki ummi take bada sauran likitocin umarni ,cikin kankanin lokaci M.A yashiga taimakawa yarinya cikin gaugawa, yayinda manya likutocin dake aiki a asibintin suka zagayeshi suna taimaka masa , ban da ummi wacce tuni ta fice daga d’akin din dan ta kasa tsayuwa saboda yadda fuskar yarinya yayi dan nama fuskarta har yasoma zagwanye.. ..
sosai M. A yashiga k’ok’ari akan yarinyar, domin taimakawa rayuwarta, sai dai duk wannan aikin da yake zuciyarsa na bugawa saboda wannan shine karo na farko da zai yi aikin daya danganci haka.
bashi ya fito daga d’akin tiyata ba sai gurin shida na yammacin rana, inda har lokacin iyayen yarinya sun kasa tsaye sun kasa zaune sai zariya suke suna rusa kuka,ta gabansu yazo ya wuce, kai tsaye gida ya wuce saboda ya gaji dayawa,yana zuwa gida bathroom yashiga ya sakarwa kansa shower ya gama ya d’auro alwala ya fito ya tada sallah ,byn yayi sallah yaso ya kwanta saboda wani irin bacci yake ji amman sanin da yayi bacci a daidai wannan lokacin bashi da kyau ,yasa ya koma parlour’nsa ya kwanta flat akan kujerar kushin me zaman mutun uku ya d’auki remut ya kunna TV ya janyo wayarsa ya kira cikin gida a kawo masa coffee ..
***********
ranar bacci M. A yayi sosai can gurin asuba wayarsa ce ta tashesa daga bacci kiran gaugauwa daga asibintin ummi yana d’auka “yace muhsin ya’akayi? Muhsin daya daga cikin likitocin dake aiki ne asibitin, yace
“daman yarinyar da akayi wa sugyren din ce fa har yanxu bata motsa ba, M.A yasa hannu ya d’auki agogonsa yana duba lokaci ,yace” okay nan da awa daya idan bata motsa ba ka bari nasani “okay…
Muhsin bai kira ba sai byn awa ya sake tabbatar masa fa yarinyar har lokacin bata farka ba ,bashiri ya mike ya shirya ya bar gidan xuwa asibiti ,akan hanyarsa ta zuwa asibiti ya kira ummi yake fad’a abinda ya faru tace”nima yanzu nake shirin kiranka sai gashi ka kira Allah dai ya bada sa’a yasa ayi nasara aiki “ameen ummi ..
……muwaddah kuwa tunda taji wayarsa da ummi hankalinta yayi matukar tashe saboda ummi ta bata labarin abinda ya faru jiya ,jikinta yayi mugu mugun sanyi dan batason ya samu matsala da aikinsa, gabad’aya a sanyaye ta dinga abubuwanta, ganin haka yasa ummi tashiga rarrashinta tana bata baki akan tayi hakuri” cikin kwanakin nan zata shirya mata tafiyarta zuwa ilori , dan a tunaninta kodan saboda haka ne yasa tayi sanyi taki sakin jikinta .
shi kuwa auwal tunda ya isa asibitin bai samu zama ba,sai kai kawo yake ,har sai da yarinya ta farfad’o tukunan hankalinsa ya kwanta ,batare da ‘bata lokaci ba ya kira ummi a waya ya sanar mata, murna tayi sosai had’e da jiro masa addua , tun safe hankalinta bai kwanta ba sai yanzu daya kirata .
byn sun gama waya ta dubi muwaddat dake zaune tana kallon zeeyword.
” muwaddat ta kira sunanta cikin farinciki” “na’am ummi ta amsa tana dubanta “kinji bunayya ya samu nasara akan aikin nan “
murmushi tayi cikin sakin fuska saboda har ga Allah taji dadi sosai ,ahankali ta motsa labbanta tace”Allah yasa yafi haka “amen inji cewar ummi muwaddat tacigaba “ai jikina ya bani tabbas zai yi nasara saboda bunayya nada matukar kwazo .
“Haka ne Amman da fari naji tsoro sosai saboda karonsa na farko kenan “haka ne Allah dai ya taimaka.
Ummi tace “ameen tare da cewa yauwa bari na aikeki gidan alhj nuhu ki kaiwa hjy kubura wad’an nan atamfofin da kamfala,ai duk kalolin da kika d’auka sun miki ko?
“sun yi min ummi, sai dai ni kamfalar nafi so wallahi, ina jin kmr na had’esu duka na dinka dogayen riguna dasu, dan babu wace kalarta batayi min kyau ba “
“Allah shalelen umminta da abi ..?
Muwaddat tayi murmushin tace “da gaske nake “to ai shikenan bari abarsu kawai ki sha kwaliyarki dan nafi son kullun nayita ganin ki tsaf tsaf ,sai ki maida mata da atamfofin .
muwaddat ta mike ta amshi farar ledar dake rike a hannun ummi “tana lekawa ,”ummi naga ke baki d’auki kamfalar ba?
ummi tace nifa bawani damuna tayi ba, nafi ga atamfar dai.
muwaddat ta cire kamfalolin ta ajiye akan kujera, ta kama hanyar fita “karki dade kije yanzu ki dawo kafin abi ya dawo, kai kawai ta daga mata ta k’arasa ficewa.
kai tsaye inda ummi ta aike ta nufa,tana shiga gidan, da mijin hjy kubura tasoma cin karo a harabar gidan yana zaune rike da jarida daily trust, gabansa k’aramin tebur ne mai d’auke da tattaciyar ruwan inibi da ruwa ,sai ritsetsen tubinsa mai kama dana yan giya.
sallamarta yasa ya bar abinda yake ya d’ago ahankali yana kallota ,har ta iso daf dashi bai d’auke idanunshi daga gareta ba, ta bude baki da kyar ta gaishe shi “ina yini ?
da sauri yace lafiya lau muwaddat yammata ya gida da hutun makarata ?
“lafiya lau ta bashi amsa atakaice tana tafiya batare da ta sake kallon inda yake ba. shi kuma yabi bayanta da kallo cikin rausayar da kai, shi dai muwaddat tana matukar burgeshi duk sanda ya ganta sai yaji wani abu ya tsarga masa ,yana son tukararta amman babu fuskar da zai bayyana mata abinda ke cikin ransa, ahankali ta k’arasa cikin gidan inda ta iske hjy kubura zaune tana kallon tashar arewa 24 ta gaisheta tare da mikawa mata afamfofi tace “gashi inji ummi tace na kawo , hjy kubura ta amsa tana murmushin jin dadi ganin duk an kwashe rabin kayan ,muwaddat ta juya abunta tasoma kokarin barin parlour’n ,hjy kubura ta ajiye laidar a gefe tace “ki gayawa ummintaki zuwa anjima idan na natsa zan kirata..muwaddat tace
“to ,tacigaba da tafiyarta.
inda tabar alhj nuhu zaune a nan ta dawo ta iske shi yana kallon kofar shiga cikin gidan ,bata ko kalli inda yake ba saboda tsarguwa datayi dashi, dan sam batason yawon kallo arayuwarta koda ta juya baya tana takawa ahankali jikinta na bata idanunsa akanta suke,shi kuwa ahji nuhu ido ya tsurawa bayanta tare da sauke ajiyar zuciya yana lasar lips dinsa da tuni suka fara bushewa ,da sauri ya mike daga zaune dayake ya biyota, wanda lokacin tuni har muwaddat ta kai kofar get din gidansu , ya tsaida ita cikin tsarkewar muryar yana kiran sunanta “muwaddat muwaddat!! ….
taja ta tsaya tana juyowa ahankali tare da tsare gira da had’e fuska sosai “tace menene?
sai da gaban alhaji nuhu ya buga saboda firgicin daya ziyarcesa ,duk da yadda zuciyarsa ke bugawa hkn bai hanashi k’arasowa inda take tsaye ba, ya d’an lumshe idanunsa yana fad’ad’a fuskarsa “uhm ammm muwaddat daman ina son na d’an miki wani bayani ne gsky akan wani lamari mai girma dake zuciyata , wato muwaddat na dan jima ina son bayyana miki sirrin dake raina akanki “
tayi shiru tana sauraronsa har sanda ya numfasa sannan yacigaba “muwaddat azahirin gsky idan kin kalli cikin kwayar idanuna zaki iya fahimtar inda zancena ya dosa tayi saurin katsesa ” ni ban fahimci komai akan zancenka ba “ya gyara tsayuwa yana rungume hannuwansa akirji ga kuma ritsetsen cikinsa “eh to daman dai na dad’e ina sonki kuma aurenki nake son yi idan kin amince”
idanunta ta rausaya cikin nasa dariya na neman kufce mata a yadda take kallonsa da ritsetsen tunbinsa, da jajayen kwalala idanuwansa kmr na agolan nafawa, hancinsa a zube kmr faranti yasa dryar ta k’arasa kwacewa dry tana rufe bakin da hannuwanta .
take alhji nuhu yashiga kallon jikinsa yana dubanta, gabadaya ya rasa driyar me take masa ,ita kuwa sai dariya take gabadaya bata ta’ba ganin abinda ya sata dariya ba irin maganar alhj nuhu ,ta kalli wannan ritsetsen cikin nasa tana sake kwashewa da dariya gabad’aya mutun babu fasali Amman yace wai ita yake so..
alhji nuhu na dubanta yace “nasan kina dariya ne saboda kina ganin kmr nayi miki tsufa ko ?
Ya fadi hk saboda shi in da tuninasa yaje kenan , ya numfasa kana yacigaba da mgn “ita soyayya da kike ganinta muwaddat babu ruwanta da wannan, ni dai ina sonki tsakani ga Allah idan har kin yarda kin amince zan gabatar da kai….
A matukar tsawace tace “dakata dan Allah baba zance komai me ni ban ma San abinda zan kiraka dashi ba ?
“duk wanda kika fad’a bazai dameni ba matukar zaki soni ki aureni .
ta sake kwashewa da wata dry adaidai wannan lokacin motar M.A ta karyo kwanar unguwar ,
ahankali yake driving ciki hadaddiyar motarsa baka wuluk kirar tucsion 4wd, tunda ya karyo idanunsa ya sauka akansu tana dry shima alhj nuhu na murmusawa , annurin fuskarsa ta d’auke, zuciyarsa tashiga dokawa, muwaddah ta kasa tsaida dryar har zuwa sanda M.A ya k’araso kofar gidan wanda zuciyarsa bata daina bugawa ba ,ita kuma ganinsa bai sa ta daina driyar da take ba .
parking yayi ya fito batare daya tsaya rufe motar ba ya zuba duka hannuwansa acikin aljihun wandonsa yasoma takowa ahankali zuwa inda suke, sai lokacin gabanta yashiga dukan uku uku saboda irin kallon kaskancin daya aiko musu dashi dip dariya dake bayyane akan fuskarta ta ‘bace ,yana gama k’arasowa alhj nuhu ya juya da niyyar barin gurin tunda yana da labarin yadda M.A yake korar mata samari, har yayi taku biyu M.A yace “no baba ka dawo muyi magana ta kunne da kunne da kai alhji nuhu ya d’an dawo ya tsaya yaji me zaice .
M.A ya dubesa a wulakance yace “wannan shine karo na farko dana ganka tsaye da wannan ?
“me kawoka gurinta?
muwaddat tayi saurin dubansa “itace ma wanna kmr wanda bai san sunanta ba..
shi kuwa alhji nuhu tsuru yayi da ido yana kallon kwayar idanu M.A dake cike da tsantsar kishi kafin daga bisani yace “wai da sonta nake amman dai karka damu zan yiwa shi mahaifin naku magana “you are very stupid kai da mganar da zaka yi masa “ni kace wa stupid?
“ance maka stupid more than donkeys, banda buduwar zuciya irin taka shekararka nawa shekararta nawa a duniya da zakace kana sonta kuma har da aure?
” to wannan yazama karo na farko da karshe da zan sake ganin kafarka a kofar gidan nan da sunan kazo zan.. “bunayya ….. muwaddat ta kira sunansa cikin rawar murya ya kake k’ok’arin yin abinda bai dace ba nifa ba son nake ba “shiiiiiii bana son jin komai ya katseta “ina sane sarai ba sai kin fad’a min ba kya son wannan mutumin mai tubi kmr tulun giyya ba…..
alhj nuhu ya fusata sosai cike da kunfar baki yace “kai a she baka da kunya, ina ganinka kmr yaro kirki a she d’an iska ne ban sani ba?
“kwarai kuwa na wuce haka akan wannan ya nuna masa inda muwaddat take tsaye da yatsan hannusa “ai kuwa zaka gane baka da wayo ,ba dai ni kayiwa wannan iskanci ba ?
“Ai sanin babu abinda zaka yi yasa nayi maka , abinda nake so da kai ,ka rike girmanka ka daina d’aura idanunka akan abinda bazaka iya dashi ba, koda kuwa ya zama mallakinka …
fuuuuu alhj nuhu ya juya ya nufi cikin gidansa yana suritai “aikin banza kawai kananan yara daku sai iskancin banza da wofi ko an ce maka tashen balaga hauka ne, idan kaima sonta kake ai sai ka fito a gabza da kai , ba ka tsaya rainawa mutane wayo ba ,yana mgn yana k’ara sauri dan kar M.A ya jiyosa ya tara musa jama’a a da ya lura yaron bashi da kunya”
M.A ya kalli muwaddat yace ” ke kuma ya nuna ta da yatsansa “sai wani bud’e masa baki kiyi kina washe masa hakora “a’a to makeke son nayi ni wallahi dariya yabani “babu wani idan kina sonshi ne tun wuri ki cire hkn aranki ,dan ki sani an haifeki ne saboda ni, nima kuma haka, dan haka wallahi zamuyi mugun samun matsala dake idan kina tsayuwa da irin wannan tsofofin da duk basir yagama rakikesu, babu fa abinda zakiji airinsu alhj nuhu da alhj jibirl ,ki tsaya irinmu mune zamu baki abinda zai sa kiji kwanciyar hankali, amman idan kinji kina son shi shikenan tunbisa ma kawai ya isheki juyawa tayi a matukar fusace tashiga gida tana jan tsaki .
Zaune ta iske ummi da binta mai aiki a palour cikin hiran jin dad’i
da nishad’i ta zauna tana huci “ummi tace lafiya ke kuma kika shigo kina nimfarfashi?
kasa magana tayi, binta data ga hk tayi murmushi “yar gidan umminta wa ta’bo mana ke?
Ko rufe baki batayi ba M.A ya shigo cikin miskilanci yace “ni ne kuma nasan babu abinda za’a iya min ya k’arasa mgnr tare da zama gefen
ummin yana
tab’e fuska yana ta huci.
binta ta kwashe da dry “lallai kam babu abinda za’a yi, domin kuwa babu mai shiga tsakaninku, Allah dai ya huci zuciyoyinku.. M.A
ya kalli muwaddat dake gefe ummi rik’e da kuncinta tana dubansa daga kallon datake masa ya fahimci yadda ranta ya ‘baci ,shima tsumammun idanunsa ya tsura mata cikin had’e fuska yace, ummi
“Wlh ni baby kunya take bani ,da irin mutanen da suke zuwa gurinta da sunan so ummi tayi murmushi me kuma ya faruwa su wad’ane mutane zaka fara ko?
“babu wani zan fara ummi wai yanzu ina dawowa na ganta tsaye da wancan shashan tsohon yana tsarata abun gwanar kunya ita kuma sai washe masa baki take ..
Ya maida idanunsa akanta yace ” yanzu dan Allah bby kirarsa bata razanaki ba “wallahi ni da mace nake irin su alhj nuhu, alhji jibirl basu taba samu kofar da zan tsaya dasu ba.. ummi tayi dry “kai dai babu ruwanka da samarinta..
Ita kuwa muwaddat harara ta watsa masa cikin ‘bacin tace “ina ruwanka to?
” ai gara auren irinsu da auren yara kanana …..”wallahi karya ne bama zaa taba hadawa ba ki dai canza tunani wallahi wadan tsafafin babu abinda zasu miki ..
ta juya ta kalli ummi..
” ummi kiyiwa yaron nan magana ya fita daga harakata da lamarin gabadaya, nifa shiyasa wani lokacin har banason ya dawo kasar nan, gara muyita gaisa a waya dashi .
“karya ne yarinya..wannan mgnrki karya ce wallahi ,ni nasan kusan kin fi kowa jin dadi dawowata ,saboda abinda ido da ido zai gane bazai kai kunne da kunne ba ko ba hka ?
Muwaddat tace “ba’asani ba ,ni dai ka daina shiga rayuwata da samarina ta k’arasa mgnr cikin tsigar wasa, duk Wanda yazo gurina sai ka korensa ko ni Sa’ar wasanka ce”?
bata kai ga rufe baki ya taso cikin fushi ya tsaya gabanta yana nunata jikinsa har rawa yake yace “an koresu din sai kiyi abinda zakiyi ,wallahi sau d’ari zan ganki da irinsu alhj nuhu sai na koresu yana gama fad’ar hk ya juya fuuuuuuu ya bar parlour’n..
ummi tabi bayansa da kallo tare da cewa “binta taya ganin karfin hali ,Anya kuwa bunayya na cin hankalinsa?
” ji yadda yake wani hakikancewa kmr wani ubanta ko mijinta .?
ummin na gama fad’ar hk ta mike zata bi bayansa muwaddat tayi saurin riko hannuta “haba ummi wasani fa, nifa da wasa nakeyi wallahi har ga Allah banji haushinsa ba….
ajiyar zuciya ummi ta sauke sannan ta koma zauninta tace “duk da hk dai rainin hankalinsa na neman wuce iyaka “hakuri zakiyi hjy tunda ita muwaddat din tace wasa ne, kin kuma san da wannan yar tsamar atsakaninsu daka ce ma shine yayanta da auren zumunci za’a yi inji cewar binta tana murmushin.
ummi tayi sauri “tace a’a ban ciki da wani auren zumunci yaje can ya nemo Matarsa itama haka, ina dalili, daga yanxu kar ki sake yarda ya dinga kore miki samari…
suna cikin magana abi ya daga labule yashigo da sallama, muwaddat ta mike ta amshi jakar hannunsa da ledar hannunsa, ta mikawa binta dake tsaye ledar tayi masa sannu da zuwa ta nufi d’akinsa itama binta tayi masa sannu da zuwa tayi ta kama gabanta..
Abi ya k’araso ya zauna kusa da ummi “hubbey fad’an me naji kina yi haka kuma ke dawa?
“sannu da zuwa, ni da wa inda ba da wannan d’an naka ba?
abi yayi murmushin me kuma auwaluluna yayi?
nan tashiga zayyano masa abinda yayi …
“to ayi masa afuwa a yafe masa shima watakila yana da dalilinsa na yin hakan, yanxu dai ina bukatar ki saki fuskarki domin itace karfin gwiwata ummi tayi murmushi “kai ko, duk lokacin da ake serious issue sai kasan yadda ka shashantar dashi..
muwaddat ta dawo parlour’n rike da tire mai d’auke da ruwa da lemu mai sanyi ta tsiya acikin glass cup ta mikawa abi “yauwa muwaddat sannu da kokari ya gida?
“lafiya lau abi ya aiki ?
“alhamdullahi ta juya ta nufi kitchen.. ya d’an kurbi ruwan lemu yana duban ummi “har yanxu banga fuskarki ta dawo min tmkr yadda nake so ba ,idan tacigaba da zama haka zanje na tsilla wankana na tafi zance .
“daman yau nayi babban kamu har cikin ma’aikata ,yar yariya fara sol dagowa wacce zata gyara min tsufana “suka sa dariya atare ummi tace “ya rabbi..ni dai tashi muje daga ciki.. ta mike tayi hanyar d’akinsa ya biyo bayanta muje din tare da cewa “kinsa surajo mai aiki a kafanina .. ?
“wani surajo vice chiaman na kamfaninka?
“shi kuwa da sauri tace “me yayi Allah dai yasa ba sallamarsa zakayi ba?
“ina ai surajo yafi karfin da kamfani zata koresa saboda himma da hazakarsa tare da rikon amanarsa, bari dai nayi wanka na fito, “okay tashiga taimaka masa ya cire kayansa yashiga bayi ta rufo masa kofar ,ta karasa gaban wordrobe dinsa ta bud’e ta fito masa da jallabiya black colour…
💗💗💗💗💗
MUWADDAT
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
_AUNTY SALAMATU AYYUBA_
_(UMMIN KADUNA )_
~BEST AUNTY FOREVER AND EVER~
alhamdullahi am back again.
warning!!!
don’t read this novel if you know you are not married… ❌❌❌coz this book contains only for mature people , if you read it, is for your own risk …..
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim