Turken Gida – Chapter Ten
by JanaftyAzumi ya raba tsakiya, mun gama goma na marmari mun shiga goma na wuya kamar yadda hausawa ke faɗi.
Yau in muka kai azumi mun kai sha biyar kenan, a duka shekarun da muka kwashe da aure ni da Yallaɓai na saba duk watan ramadana Yallaɓai ba ya kaiwa dare a waje a gida ya ke yin buɗe baki tare damu haka ya sabar mana kuma nima haka na saba.
Amma wannan azumin sai al’amarin ya ɗan sauya. Saboda ya samu kwangila gina ma’aikatan nan na kaduna gabaɗaya ma’aikatan shi suna can kaduna shima yana zuwa har ya kwana ma kafin ya dawo sai ya zama na in baya gari sai dai mu yi buɗe baki tare da yara. Ranar da muka kai azumi na sha uku ya dawo daga Kaduna na yi masa har kunin tsamiya da ya ke matuƙar so, amman bai shigo gidan ba sai wajen tara na dare. Na kira shi a waya na ji ko bai dawo daga kadunan ba ne? Sai ya ce mini ya dawo ya na Gwammaja da ya faɗa mini haka har a cikin raina ban yi zargin wani abu ba, sai da ya dawo na kawo masa abin buɗe baki bai ci abinci ba,kunin ma kaɗan ya sha ya ce mini cikin shi ya cika a lokacin sai da na yi mamaki sanin Yallaɓai ba ya iya cin komai a waje sai ya dawo gida barin ma da azumi saboda ya san ina gida na shirya masa abin buɗe baki kamar yadda na saba.
“Ka ci wani abu ne a can Gwammaja?
Tambayar da na yi masa a lokacin kenan. Shi kuma kai tsaye ya ce mini Nene ce ta matsa masa sai da ya tsaya ya yi buɗe baki. Na ɗan yi mamaki saboda hakan bai taɓa faruwa ba ai Nene ta san ya na da mata me ya sa za ta ce sai ya yi buɗe baki a wajenta? Amma sai wata zuciya ta kitsa min kyakyawan Niyya cewa ita ɗin uwa ce a gare shi ta na da wannan damar kuma abu na rana ɗaya. Sai ko a fuska ban nuna masa damuwata ba na basar da komai ya wuce sannan ya faran tamin rai da ya ce da Asuba na ɗumama masa kuninshi ya na so ya yi sahur da shi.
Haka ko aka yi da asuba bai ci komai ba kunin na ɗumama masa ya sha da buredi ni kuma da yara muka sha tea sai na soya mana ƙwai muka haɗa da shi. Ranar kuma da wuri ya dawo gida muka yi buɗe baki tare ana kiran sallar isha’i ya yi alwala ya tafi masallaci bai dawo ba sai da ya tsaya ya yi sallar tarawihi kamar yadda ya saba ni kuma ni da yara daman muke yin namu a gida.
Sannan da rana kuma da ba na komai sai na yi ta karatun Qur’ani tunda duk watan Ramadan in ya zagayo sai na yi sauka kamar yadda na saba.
*
Saude tana zuwa da safe ta yi min yan aikace aikace sannan ta ɗan rage mini aikin yamma tunda kafin la’asar ta ke komawa gida sauran aikin kuma ni na ke yi Jidda na kama min ɗan abin da ba a rasa ba.
Yau alale na yi mana mai kifi da ƙwai sai na yi mana zoɓo, Yallaɓai ya aiko da kayan ciki sai na yi ferfesu shi kuma sai na dafa masa ruwan tea da ya ji kayan ganyen shayi na citta saboda ya na so duk dare Yallaɓai zai sha kafin ya kwanta. Muna da kayan marmari sai na ce Jidda ta raba biyu sauran kuma su yi fruit salat ni da Yallaɓai kuma sai na yayyaka mana tunda shi ya fi son cin su a haka. Bayan mun gama haɗa komai na bar ma Jidda gyara Kitchen ɗin amma bayan na haɗa duka kayan buɗe baki a falon su Jidda in da muke zama gabaɗayan mu a saman cafet mu yi buɗe bakin tare.
Wanka na je na yi, saboda na gaji kuma yau ɗin nan ina ɗan jin azumin nan kaɗan ina fitowa wanka ana kiran salla daman ina da Dabino a ɗaki na yi buɗe baki Jidda ma na san ta yi na ta Baby dai daman azuminta rabi da rabi ne in ta ɗauka da ta yi rabi sai ta fara kukan yunwa Babanta kuma ya ce ta ci abincinta da cewa ta yi rabi gobe ma in ta yi rabi ɗaya kenan. > Janaftybaby: Sai da na saka wata doguwar rigata na Atamfa sannan na ta da salla daman na ɗauro alwala ina cikin sallar na ji ana kiran wayata sai da na idar na jawo na duba sai na ga Amina ce sai da na shafa salatin da fara sannan na kira ta daga baya.
Mun gaisa ne ta yi mini barka da shan ruwa. Mu ɗan tambayi lafiyan juna kafin mu yi sallama Amina akwai ƙokari tunda aka shiga watan Ramadan duk bayan kwana biyu sai ta kirani ta yi mini barka da shan ruwa ita da Rahila suna da wannan ƙoƙarin a gidanmu. Ni ma dai farkon watan na kira duka yan gidanmu na yi musu barka da shigowa watan Ramadana wata mai albarka har Ma’u sai da na kira ban wareta ba wannan karon sannan Alhajinmu ma mun yi waya dashi sau uku kenan shi da Gwaggo saboda tun ranar da muka kai azumi na uku da na je gidan kai musu saƙon Yallaɓai ban ƙara komawa ba washegari kuma na je Gwammaja na gaishe da Nene tun daga kuma ranar ne ban ƙara fita ba.
Wayar ta ɗan dauke min hankali na buɗe data ina ganin masu turamin saƙon Happy iftar group ɗin Gidanmu na shiga na ga Ya Abubakar ya turo addu’a daman shi ke da wannan ƙoƙarin Ya Hamza ya yi tagging ya ce Allah ya ba da lada. Sai ni ma na yi Tagging na ce Amin tare de cewa fatan mun sha ruwa lafiya? duk ba sa kusa da wayarsu tun da an sha ruwa ana can ana hada hadar buɗe baki sai nima na fita daga nan na ɗan duba saƙonnin private sai na ga Munnira ta yi min mgana da cewa Matar Yallaɓai sai na tura mata da amsa da cewa matar ƙanin Yallaɓai sannan na saka mata emojin dariya na fita. Datar na kashe na ijiye wayar saman gado sannan na cire hijabin jikina na ninke ina mamakin me ya tsaida Yallaɓai har yanzu bai dawo ba? Tunda Office ya je bai ma fita da wuri ba sai bayan da a ka yi sallar azahar.
Falo na fita dai dai Jidda ma ta fito da Hijabinta alamun ta idar da sallah ne.
“Barka da shan ruwa Umma.”
Ina kallonta na ce” Yauwa barkan mu dai Jiddan Umma. Ina Baby?
Sai ta ce min ta na ciki ta na sallah, ganin ta juya za ta koma ɗaki ya sa na ce” Taho ki yi buɗe baki mana Jidda.’
Cikin mamaki a fuskarta ta ce” Umma Abba bai dawo ba?
Kai na kaɗa kafin na ce” Yana hanya in sha Allahu. Taho ko kunin ki zuba ki sha cikin ki ya warware.”
Sai ta amsa da toh hijabin jikinta ta cire ta zauna nima sai na zauna ta zuba mini kunun na ce kaɗan itama sai ta zuba nata sai ga Baby ta fito jikina ta faɗa tana faɗin” Umma azumi na goma.’
Ina dariya na ce” Lalle Baby mai himma ce kai kai har azumin ki ya kai goma?
Ta na washe baki ta ce” Umma ke guda nawa kika yi? Ina kallonta na ce” Ai muna tare da ke nima azumina goma.”
“Yaa Jidda fa?
Ta faɗa tana kallonta ina dariya na ce” itama dai dai da naki.” Sai ta miƙe ta na tsallen murna Jidda ta kalleta amma dai ba ta yi mgana ba saboda ba ta da hayaniya sosai.
Har muka gama shan kunu ba Yallaɓai ba dalilin shi Baby sai cewa ta ke yi Umma ina Abba? Sai na tashi na shiga ciki na ɗauko wayata na kira shi bai ma ɗauka ba a lokacin sai da na ƙara kira sannan ya ɗaga wayar na ji hayaniya a in da yake amma ba sosai ba.
“Yallaɓai na barka da shan ruwa.”
“Barka da shan ruwa Sadiya ta.”
Shima ya maida min martani. Mirmishi na yi mai sauti kafin na ce” Kana ina ne? Na ga an sha ruwa ba ka dawo gida ba.”
Sai kawai ya ce” Ina nan zuwa na ɗan shiga Gwammaja ne duba Nene Daughter ta kirani ta ce da zazzaɓi ta yi ni”
Cikin jimami na ce” Ayya. Allah ya ba ta lafiya ka gaishe ta.”
Ya amsa mini da Amin sai kawai ya ce mu yi buɗe bakin mu kar mu jira shi in ya dawo sai shi ya yi na shi ban kawo komai ba na yi fatan Allah ya ƙara sauki mu ka yi sallama.
Tare da yara muka yi buɗe baki ba mu ci abinci ba kawai kayan marmari muka sha sai ferfesu. Sai da muka yi sallar isha’i da tarawehi sannan muka ci abinci ni alale ɗaya na ci ma na ji cikina ya cika Jidda ta gaji da wuri ta kwanta Baby ne ma ta ɗan daɗe ba ta yi barci ba tana kallon cartoon sai da na kora ta na ce ta je ta kwanta saboda makaranta. Duk da ma yanzu 12pm suke tashi saboda azumi. > Janaftybaby: Tun ina saran dawowar Yallaɓai da wuri har na fidda rai sai na fara tunanin ko Jikin Nenen ne ya yi tsanani har sake kiran shi na yi ban same shi ba duk na damu. Ina ta tunanin Allah ya sa ba jikin Nenen ya yi tsanani ba ne kamar zan kira Gimbiya sai na fasa tunda ni dai ba waya muke yi ba sai wani abu na jaje ko barka ni ba ma zan iya tuna last muka yi waya da ita ba gaskiya amma ina da lambarta kuma nima na san ta na da nawa tunda muna ganin status ɗin juna.
Har na fara gyangyaɗi na ji ƙaran buɗe get sannan da shigowar motar Yallaɓai sannan na mike ina duba agogon wayata goma da rabi har ta gota sha ɗaya saura na dare. Ajiyar zuciya na sauke na fita zuwa falon farko dai dai ya buɗe kofar falon ya shigo muka ci karo da juna ni da shi.
“Ya jikin Nenen?
Da haka na tare shi domin a zato na jikin nata ne ya yi tsanani ya sa bai shigo gida da wuri ba. Lumshe idanuwansa ya yi daga gani a gajiye ya ke saboda ya na ƙarosowa gabana ya rumgumeni yana mai sauke ajiyar zuciya nima sai na rumgumeshi ta baya ina faɗin” Nenen na lafiya ko?
Cikin muryan gajiya ya ce” Lafiya lau. Na gaji Sadiya ta ko’ina na jikina ciwo ya ke yi min.”
Ko bai faɗa ba na ga hakan a muryan shi da yanayin shi sai kawai na ce mu je na haɗa masa ruwan wanka ya yi wanka sai ya ji daɗin jikin shi. Muna riƙe da hannun juna har bedroom ɗim mu ina tambayan shi ya jikin Nene ya ce min da sauƙi likita ya zo gida ya dubata. Maleria ce ta kamata cikin tausayinta na ce” Allah sarki. Allah ya ba ta lafiya. Amma dai ta ijiye azumin ko?
Sai da ya gyaɗa min kafin ya ce” Yau ɗin ma ta ɗauka da jikin ya zafi sai ta ajiye”
Ina taya shi tuɓe kayan jikinsa ya ke tambayata su Jidda na ce sun kwanta. Kai ya kaɗa kafin ya ce” Na yo ma Baby tsaraba ya na mota na manta dashi.”
Ban maida masa martanin mganar shi na tura shi zuwa kofa ina faɗin” Ka yo wanka.”
Domin ni kaina na gaji barci na ke ji idanuwana har rufewa suke yi amma ban kwanta ba sai da na kwashe kayan da ya cire na zuba cikin kwandon kayan wanki na fito masa da wasu riga da wando masu taushi na barci. Lokacin da ya fito har na fara gangyaɗi sai da ya yarfamin ruwan hannunsa sannan na farka.
“Ki kwanta mana. Kina barci a zaune?
Ya faɗa ya na nufar gaban madubin ɗakin. Sai da na yi Hamma sannan na ce” Zan baka abinci ne shi ya sa ban kwanta ba.”
Bai juyo ba amma ya ɗau mai ya na ɗan shafawa ya ce” Yi kwanciyarki kawai na yi buɗe baki a gidan Nene amma zan duba na gani ko zan iya cin wani abu kafin na kwanta.”
Ban damu ba na ce to sai kawai na kwanta ina jin sa ya na faɗin” Haka za ki kwaanta? Tsabar barci umh kawai na ce masa. Daga nan ban san yadda aka ƙare ba sai dai can ina jin sa ya na cire mini rigan jikina ina ta masa magagi sai da asuba da muka tashi sahur ne na fahimci rigar barci ya sakamin kuma wani ikon Allah duk gajiya da zan ji da mugun barcina ta bakin Yallaɓai huɗu na yi na asuba na ke tashi wani lokacin ma kafin huɗun na tashi Yallaɓai ne sai na yi ta fama dashi kafin ya ta shi har mamaki na ke yi ina faɗin haka maza suke? Ni dai Yallaɓai sai na yi da gaske ya ke iya tashi Sahur in na tashe sa tun lokacin da na tashi sai ya koma barci da cewa in na gama haɗa abin buɗe bakin sai ya tashi, to fa in na gama sai na haɗa da jan hannun shi ya ke iya tashi in kuma zan kyaleshi sai an fara kiran salla zai tashi lokacin an gama ma Sahur ɗin.
Kamar haka ne yau ma uku da rabi na farka barcin da gajiya duk sun sake ni na ganni na nannaɗe jikin Yallaɓai duk na yaɓa masa kafa. Sai da na yi mirmishi bayan na sauko daga kan gado na gyara masa bargo sannan na fita zuwa tiolet na ɗauro alwala na zo na shimfiɗa darduma na yi salla raka’a biyu na ɗan zauna na yi addu’o’ina sannan na miƙe na cire hijabin na nannaɗe tare da darduma na mayar ajiyar su ban ta da Yallaɓai ba sai na buɗe kofar bedroom ɗin na fita na bi ta cikin kitchen sai na ga Yallaɓai ya kwaso kololin da na bari a falo zuwa kitchen sai na bubbuɗe na gani bai ci alelen ba amma dai ya sha zoɓo kuma ya sha kayan marmari, ban damu ba tunda Baby ba ta azumi sannan nima zan ci alalen tunda jiya ban ci ba. > Janaftybaby: Gas na kunna na ɗora ruwan tea kawai. Muna da sauran buredi tunda jiya ya shigo da shi. Bayan na juye a fulas sai na ɗumama alalen sannan na soya ƙwai saboda Jidda da Babanta sai da na gama komai na kai falo sannan na shiga ɗakin su Jidda na tashe ta, ina tashin ta Baby na ji ta yi zaraf ta miƙe tana faɗin” Umma nima zan yi azumin.”
Kai tssye na ce” To ku wanke baki ku fito mu yi sahur.”
Daga nan na fice tiolet na shiga na yi brush ina fitowa hannuna da danshin ruwa na lallaɓa domin na shafa ma Yallaɓai ruwa a fuska saboda ya tashi sai dai ina zuwa dai dai saitin kan shi wayarsa ta kawo haske alamun ana kira ban saka hannu ba sai na leƙa sai na ga Daughter na kira. Mamaki ya kamani me ya sa ta ke kiran shi yanzu? Sai wata zuciyar ta ce min ko dai jikin Nene ne?
Tunanin haka ya sa sai na yi niyyar amsa kiran sai na saka hannu na ɗauki wayar na buɗe bayan wayar ta yanke. Tunda na san password ɗin wayarsa ina shirin kiranta ne kawai sai ga saƙon ta ya shigo wayar har ga Allah ba halina ba ne duba wayar miji duk da wayar Yallaɓai ba ta da shamaki a wajena ban taɓa tunanin bin diddiginsa ba. Kuma har ga Allah lokacin da saƙon ya shigo hannuna ne ya faɗa kan saƙo sai ya buɗe kuma ban isa a lokacin na hana idanuwana karanta abin da ta rubuta ba.
“Daddy na a tashi a yi sahur. Ko duk santin girkin nawa ne yasa ka kasa tashi? Na ga tuƙwaici na gode. Amma ka yi min laifi domin na ce ba zan karɓa ba yanzu haka ma za su dawo wajenka domin zan siya ma ƴaƴana kayan kwalliyar salla da su. Thank you so much for been their for me Daddy.”
Na yi ƙoƙarin bayan na gama karanta wannan na fita amma sai zuciya ta rinjaye ni na srolling sama ina ganin saƙonnin da ta ke tura masa. Tun da aka fara azumi ta ke tura masa saƙo da asuba a tashi a yi sahur sannan sai ta tura masa sakon barka da shan ruwa wani lokacin ya ba ta amsa wani lokacin ya yi shuru. Na duba saƙonin har wanda ta na Abuja lokacin da mijinta ya rasu. Wani saƙo da ya ba ni mamaki ya sa na ji kirjina sai da ya buga dam! Shine ta tura masa” Na yi kewarka Daddy yaushe za ka zo?
Shi kuma sai ya ba ta amsa da Gobe in sha Allahu.
Kirjina ne na ji ya fara suya, har ina ganin duhu duhu da ya sa ban ƙara gaba ba na ijiye masa wayar a nan saman side drower ɗin da ya ke kwance. Kallonsa na ke yi ina mamakin Yallaɓai ashe shima ya iya munafuncin maza? Ashe jiya ba Nene ba ce ta tsaida shi ba ashe Gimbiya ce ta tsaida shi, bayan ta yi masa girki ya ci har ya na santi daga karshe har ya na ba ta tuƙwaici ni kuma ko oho. Wani ƙululin abu ya tokaremin a kirji da wani haushin Yallaɓai don Allah menene na ƙarya tsakani ga Allah? Sai kawai na juya da na so na fita ne ba zan tashe shi ba sai dai yau ya yi ɗaure amma sai na danne zuciyata da na yi wani tunani sai kawai na dawo na fara buga gefen gadon yau ko sunan shi ban kira ba. Sannan ban taɓa shi kamar yadda na saba ba. Bai da wani nauyin barci sai gashi ya buɗe idanuwansa da suka yi nauyi yana kallona sai kawai na juya ina faɗin.
“Ka tashi lokacin Sahur ya yi.”
Da ga haka na yi ficewata na bar shi a raina kuma na kudiri niyyar ko bai tashi ba na gama tashin shi. Daga yau sai ita wacce ke tashin sa sai ta cigaba da tashin shi. Ban da munafunci ta san ya na da mata amma wai ta ce duk asuba sai ta kira shi ya ta shi ya yi sahur? Ban taɓa lura ba saboda da na tashi na ke zuwa kitchen domin samar da abin buɗe baki ban taɓa cin karo da kiran nata ba sai yau.
Tun da na zauna a wajen nan ban yi dariya ba. Tun kafin ya fito na ce ma Jidda ta zuba ma kanta da Baby sai ta kalleni kafin ta ce” Umma Abba fa? Wani kallo na yi mata kafin na ce” Kar ki ci ki tsaya jiran wani Abba.”
Ita kanta na san ta yi mamaki domin sai da ta kalleni ni kuma na kauda kaina ina cin alalen da ma ɗumama sai ruwan tea wanda ban saka madara ba na ke sha dashi Baby dai sai cin ƙwanta ta ke yi ba ta damu ba Jidda kuma jikinta a sanyaye ta ke kurɓan tea ɗin ta ke sha tare da buredi ni kuma a raina ina ta roƙon Allah ya sa kar Yallaɓai ya tashi yau sai dai ya yi ɗaure sai dai addu’ata ba ta karɓu ba sai ga shi ya fito ya na sanye da jallabiya mai ruwan ƙasa Baby > Janaftybaby: na ganin shi tana ƙoƙarin miƙewa ban san lokacin da na daka mata tsawa ba.
“Ke koma ki zauna ko na saɓa miki.”
Haka na faɗa cikin zare mata ido. Daga Yallaɓai har Jidda da kallo suka bini, ita kuma sai ta kalleni ta ruɗe har ba ta san kafarta ya ture tea ɗin gabanta ba. Sai ga shi ya malale min a saman cafet kallon tea ɗin na yi yana gangarowa wani abu na tokaremin zuciya.
Ganin irin kallon da na ke yi ma Baby ne ya sa Jidda ta yi sauri miƙewa ta na faɗin” Ki yi hakuri Umma bari na gyara wajen.”
Yallaɓai na tsaye hannunsa harɗe a kirjinsa yana bin mu da kallo barin ma ni. Kawai sai na yi kyafci ina kallon Baby da ta yi kamar za ta yi kuka na kaɗa kai kafin na ce” Lalle ko za ki ci ubanki Maimuna”
Ta na jin abin da na ce ta barke min da kuka, tsawa na ƙara daka mata kafin na ce” Za ki yi min shuru ko sai na zo na tattaki a nan wajen?
Na faɗa ina mata wani kallo, Sai kawai Yallaɓai ya kira ta sai ta kalleni ta kasa tashi shi kuma sai ya ce ta zo mana ya na kiranta ganin na kauda kai ne ya sa ta tashi ta nufe shi ta na kuka ta faɗa jikinsa ya rumgumeta yana faɗin” Shii Umma ce! Kyaleta kun kwance da ita ko?
Kukan Baby ma ƙara harzuƙani ya ke yi amman ban yi mgana ba sannan ban ɗago kaina ba. Ina jin su yana ta lallashinta har sai da ta daina kuka sannan ya ce ta koma ɗaki ta kwanta ita kuma Jidda ta dawo da tsumma ta goge wajen tas ta gyara da na ce ta zauna ta ƙarishe shan tea ɗin ta sai ta ce mini ta ƙoshi. Uban gayyar kuma na tsaye ban kuma ce ya zauna ba sai da ya gaji sannan ya zauna a ƙasa kusa dani yana faɗin.
“Zuba min tea.”
Da na so na ce ya kira Gimbiya sai kuma na fasa na haɗa masa tea ɗin na tura masa gabanshi da ƙwan da buredin ganin yadda na ƙi kallon shi ya sa cikin mamaki ya kira sunana.
“Sadiya.”
Ban ɗago ba amma na amsa sai kawai na ji yana faɗin” Me ke faruwa ne?
Sai a lokacin na yi masa kallon ƙasa ƙasa kafin na ce” Me ka gani?
“Abubuwa da ya wa. Na ga kamar ranki yana ɓace ne me ya faru? Ke da yara ne?
Ya faɗa yana kallona nima sai a lokacin na kalle shi sai kawai na kauda kai kafin na yi mirmishi gefen baki na miƙe ina faɗin” Bakomai.”
Abin ya bashi mamaki ganin na bar shi a falon na yi shigewata ciki kuma na san ya bi ni da kallo ban kuma ko waigo ba. Ban ƙara ganin Yallaɓai ba sai da ya zo daukan hula da carbi ina kan darduma ya ce mini ya tafi masallaci sai na gyaɗa masa kai kawai ba tare da na yi masa mgana ba.
Da safe ma haka na tashi gim da raina ko fara’a ban yi masa ba daga shi har ƴayan shi Jidda dai ta ga har da safen ban huce ba sai ta sameni a falo ina zaune domin ɗakin na bar ma Yallaɓai gabaɗaya.
“Umma ki yi hakuri don Allah.”
Har da Baby ma kamar ta yi kuka ta ce” Ki yi hakuri Umma.”
Sai suka ba ni tausayi laifin Ubansu ne ya shafe su sai na ɗan saki fuska na ce musu zo su wajena na haɗa su na rumgume na saki fuskata shi ya sa suka tafi makaranta suma sun warware. Amma shi kan Yallaɓai ya kasa gane kaina da ya matsamin sai na ce masa ban ji daɗi ne.
“To ko mu je asibiti ne? Me ke damun ki?
Kai tsaye na ce” Ba sai mun je ba. Ciwon kai ne kaɗan zai bari zuwa anjuma.”
Kasa fita ya yi saboda yadda ya ga ina basar dashi ya san halina dole akwai wani abu da ya yi mini ne.
“Sadiya don Allah ki faɗa min me ya faru?
Na ce masa bakomai ba sau adadi amma bai yarda ba. Ganin ya damu sai na ɗan saki raina saboda na ga ya na damuna da tambaya tun da ba gaya masa abin da ke danuna zan yi ba gwara na saki raina ko zai kyaleni da tambayoyin sa.
Na ɗan sakin masa har muka zauna muna ta hira sai muka ganganro kan mganar kayan salla ya ce yana jiran cikon payment na aikin da suka yi a Rano ne a wannan sati sai a yi mganar kayan salla da ɗinki da sauran su ya so ba zai fita ba ne sai kuma Musbahu ya kira shi ya ce wasu mutane sun zo suna jiran shi. Da zai fita sai na ce bari na shirya ya sauke ni Gwammaja na duba Nene, da gayya na faɗi haka saboda na ji me zai ce sai kuma bai ba ni kunya ba.
“Nene ta samu sauƙi fa. Ke da ba ki da lafiya, ki bari ko zuwa jibi tunda ba ki ji daɗin kema.” > Janaftybaby: Kai tsaye na ce” Na ji sauƙi mu je ka sauke ni zan iya zuwa.”
Na ɗauka zai ƙara mgana sai kuma ya yi shuru sai da muka jira Saude ta zo na bar mata gidan daman mun yi wanka mun shirya ni shadda na saka da farim mayafi shi kuma sai ya saka kananun kaya.
Da ya kai ni Gwammaja bai shiga ba saukeni kawai ya yi ya wuce office ni kuma na shiga ciki sai da na lelleƙa daƙunan su Hajiya iya muka gaisa sannan na ƙarisa ɗakin Nene na ganta garas da ita ita kaɗai ce a shashen ita ta ke faɗa mini Gimbiya ta leƙa wajen aiki.
Da na yi mata ya jiki ta na mirmishi ta ce” Tafida sai da ya ta so ki? Ɗan zazzabi ne Gimbiya ta ɗaga masa hankali tun jiya ina shan mganguna na warware.”
Sai na yi mata fatan samun sauƙi bayan tambayan yara na ce suna makaranta mun ɗan taba hira da ita anan na yi azahar ina shirin tafiya sai ga Gimbiya ta dawo mun gaisa sama sama kamar yadda muka saba. Ta dai tambayi su jidda na ce suna makaranta.
Ƙarfe biyu na koma gida na. Daga kuma ranar ko a fuska ban ƙara nuna ma Yallaɓai wani abu ba. Ban damu da ma ƙara saka masa ido ba saboda mu zauna lafiya amma ni na san ba ta fasa kiran shi da tura masa saƙo ba, amma dai bai ƙara buɗe baki a waje ba sai a gida mun shiga goman karshe an fara ibadar na tahujjud Yallaɓai masallaci ya ke zuwa ni kuma in ta da yara mu yi namu a gidaa.
Ranar da za mu ɗau azumi na ashirin da 24 Yallaɓai ya dawo daga masallaci ya ɗan kwanta huɗu da rabi na tashe shi sai ya shiga tiolet yana wanke baki a lokacin na ga Gimbiya ta na kiran shi bayan ta katse sai ta tura mssa saƙo zuciya ta rinjaye ne na ɗau wayar na duba saƙon na ta.
“Daddy jiya ba ka zo ba? Kuma fa na yi maka kunin tsamiya mai daɗi”
Motsin fitowarsa na ji da na so na yi saurn ijiye masa wayar ne sai kuma na fasa sai da ya fito. Ya yi mamakin ganina tsaye da wayarsa sai da ya matso gabana sannan na miƙa masa wayarsa ya karɓa kafin ya samu sararin mgana na ce.
“An tura maka saƙo.”
Ina gama faɗin haka na fice na san kuma bayan ya duba saƙon ya ji nauyi domin ba na ce kunya ba tunda maza ba su san kunya ba. Har ya fito muka yi sahur jikinsa a sanyaye ni kuma sai na yi masa bariki ban nuna masa ko a fuska na ji haushi ba sai ya ɗan saki jikinshi amma a raina na kudiri niyyar koya masa hankali daga shi har Gimbiyar ta shi.
Washegari ya tura mini kuɗin kayan salla nawa da na yara sai na su Nene da na Gwaggo. Daman yana yi musu kaya duk shekara. Dija collaction na tura ma kuɗin daman mun yi mgana na zaɓi komai har Marwa na yi ma kaya da Saude saboda mun yi waya a gida za ta yi salla in ta dawo sai kuma ta gama pratical ɗin ta za ta koma makaranta. Kuma daman ta turo mini kayan na zaɓa tuni suna wajen ɗinki kuɗin ne sai da ya tura mini bayan mun gama lissafi na tura mata.
Ni da yara kala huɗu ya yi mana. Leshi biyu atamfa biyu. Nene Atamfofi biyu su Hajiya Iya kowacce ɗaya sai Jawahir kala biyu Adanan kuɗi ya tura masa sai Gwaggo guda ɗaya Alhajinmu kuma shadda mai kyau. Sai ni mayafai guda biyu da Hijabi ni da yara sai takalman mu har Nene an siya mata takalmi da Hijabi gabaɗaya tun lokacin da a ka kawo kayan na nuna masa ya ce komai ya yi. Telanmu kuma daman na yi masa mgana kuma ga kuɗi har da na Nene na kai mana ɗinki tare da na Jawahir da Marwa Saude kuma na ta na bata mamanta na ɗinki ita za ta ɗinka mata. Gwaggo kuma da Alhajinmu na kai musu na su suna ta godiya duk da suma su Yaya Hamza duk sun yi musu. Nene ma na kai mata takalmi da hijabinta na ce kaya na wajen ɗinki ta na ta saka albarka.
Ranar da muka ɗau azumi na ashirin da shidda Mimisco ta aiko da kaya yan kanti kala biyu biyu na jidda da baby. Anty Bahijja ma ta aiko musu da material a ɗinke sai Anty Maimuna itama kala biyu amma Bby uku ta yi mata har da wani riga da wando masu kyau da takalma. Gimbiya kuma Yallaɓai ta ba ma kayan ya kawo ma su, kayan kwalliya ne sai hijabai da mayafai sai takalma masu igiya sai abun hannu da ɗan kunne sai kwalban da ake kitso da shi kayan kuma ta ce suna wajen ɗinki duk Yallaɓai ne ya ke koramin jawabi nan yaran suna ta murna shima bakin shi ya ƙi rufuwa. Daga gani ya ji daɗi kuma har hakan ya nuna a saman fuskar shi. > Janaftybaby: Ni dai ban nuna masa komai ba na yi godiya har ya na saka min kati a waya ta ni kuma na san na kiran da na ce zan yi ma Gimbiya na yi mata godiya ne. Kai namiji munafuki ne wallahi.
Ranar da muka ɗau azumin ashirin da bakwai ɗaure Yallaɓai ya yi saboda na zo tashin shi na ga Gimbiya na kiran shi sai kawai raina ya ɓaci ban tashe shi ba. Ni kaɗai na yi sahur saboda Jidda na ce ta huta jiya ta sha wahala. Yallaɓai bai tashi ba sai da aka fara kiran salla lokacin ina zaune na idar da raka’atul fajir, ya tashi ya na kalle kalle kiran sallar da ya jiyo ne ya sa ya kalleni cikin muryan barci ya na faɗin
“Sadiya mun makara ne? Na ji kamar ana kiran salla?
Sai da na kalle shi kafin na ce” Kai dai ka makara. Ni na yi sahur ɗina.”
Cikin mamaki da tuni barcin ya sake shi ya ce” Ban ga ne ba? Ni fa?
Kai tsaye na amsa masa da cewa” Ba ka yi ba.”
“Me ya sa ba ki tashe ni ba?
Sai da na yi shuru kafin na ce” Ban tashe ka ba. Saboda na ga wacce ka rabama girki da ita na kiranki sai na koma a tunanina ta tashe ka yau ɗin”
Galala ya yi ya na kallona sunana ya kira na yi masa banza sai kawai na miƙe na kabbarta salla ganin haka yasa shima ya mike amma sai ya ya ɗau wayarsa ya duba sannan ya mike ya fita zuwa tiolet ya ɗauro alwala ya fita zuwa masallaci sanda ya dawo ina ji da na yi baricn ƙarya weekend ne yara ba makaranta sun ma yi hutu jiya jumma’a.
Na san mganar da na faɗa masa na cin ransa bai iya hakuri ba ina barci ya tashe ni da mganar wai bai gane me na ke nufi da ya raba mana girki ba? Da wa ya raba mana girki?
Kai tsaye na ce” Da wacce ta ke yi maka girki kana zuwa ka ci ka biya tuƙwaici mana.”
Wani kallo ya yi mini ni kuma ina shirin na juya na koma barci ya riƙo ni ya na kiran sunana.
“Sadiya.”
Ido na sakar masa kafin na ce” Na’am Yusuf.”
Kawai sai ya girgiza kai bayan ya saki hannuna kafin ya ce” Sadiya karki fara abin da ba halin ki ba ne. Bincike mini waya kike yi yanzu saboda ba ki yarda da ni ba?
Kai tsaye na ce” Allah shi kyauta. Kawai dai akasi aka samu na gani.”
Komawa na yi na kwanta ina faɗin” Karka damu ba wani abu fa.”
Miƙewa ya yi ya na kallona ni kuma sai na ja bargo har saman kaina. Hannu ya saka ya janye bargo ya na faɗin” Ki tashi mu yi mgana”
Sai na ƙi tashi na riƙe bargon ina faɗin” Wata mgana? Ai mun gama mganar nan ko?
Zura min ido ya yi kafin ya ce” E duk da haka na ce ki tashi mu yi mgana.”
Na ko ƙi tashi na juya zan gyara kwanciya a saman kaina Yallaɓai ya yi min tsawa.
“Sadiya na ce ki tashi mu yi mgana ko? Kar ki bari raina ya ɓaci wallahi.”
Yadda ya yi mganar ne ya sa na gane ranshi ya ɓaci sai na miƙe na zauna a saman gado shima sai ya zauna ya na mai sauke ajiyar zuciya.
“Sadiya wallahi ba komai tsakanina da Daughter fa. Kawai dai kin san am her favorite ne tun a baya. Kuma ni tana kira ne ba domin ta san ba ni da mata ko wani abu ba just normal na yan’uwan juna kin gane?
Sai kawai na gyaɗa masa kai, domin ni na san kawai yana faɗa ne.
“Kar ki ɗauke shi a wani abu don Allah. Ni ina mijinki haƙƙi ne a kanki ki tashe ni kamar yadda kika saba.”
“To ba za a ƙara ba.”
Na faɗa saboda na gaji da jin mgananunsa.
“Kuma game da abinci in na je duba Nene sai ta yi mini ta yi in na ce ba zan ci ba sai Nene ta ce ko kaɗan ne na taɓa. Kin san dai ba zan yi ma Nene gaddama ba. Mganar tuƙwaici kuma wannan kyautatawa ce kema kuma ai ina yi miki ko?
Ina ta kallon shi dai amman na kasa mgana.
“Ba ki son kiran ne?
Sai na ce mata ta daina Sadiya ta ba ta so.”
Wani kallo na yi masa kamar in yi dariya saboda na ga zai raina min wayau amma ban yi ba.
“Zan faɗa mata ta daina kirana da asuba gashi yau ta ja mini yin ɗaure.”
Ya faɗa ya na yar dariya har yana shafa min kumatu. Yaƙe kawai na yi masa ban yi mgana ba. Hamma ƙarya na fara yi masa sai ya ce na koma na kwanta shi zai fita can falo akwai aikin da zai yi har ya ɗau laptop ɗin sa ya fice ina bin shi da kallon mamaki. > Janaftybaby: Ajiyar zuciya na sauke ko ba komai a zuciyar Yallaɓai game da Gimbiya ita har gobe shi ne zaɓin ta tsoro na ɗaya wannan karon mafarkinta zai iya zama gaskiya in dai ba wani ikon Allah ba tunda ba ta da shamaƙi da hakan ta kowanni fanni.
Tun kuma daga mganar da muka yi ba mu ƙara tada mganar ba. Ita ma ta daina kiran asuba ina tunanin da gasken ya yi mata mgana sai na ji daɗi ko ba komai ya nuna mata ni matarsa ina da daraja. daga nan nima sai na watsar da abin da ke cikin zuciyata na kishi na rumgumi mijina.
Sai cefanen salla tare muka je kasuwan muka siyo komai sauran kayan miya kuma Musbahu ya ce ya ba ma kuɗi zai kawo minibana gobe salla nama kuma daman a can gida sa suke yankawa a raba gabaɗaya amma dai ya siya mana na kasuwa kilo huɗu sai kaji muka haɗa da shi ni kuma a gida na siya fulawa zan yi cincin da cake da donut ga masu tayani Saude da Marwa da ta zo mini salla duk tare muke ayyukan gefe ɗaya kuma ina ta mana shirin Annirvesary ko Yallaɓai bai san shirina ba da ya tambayeni nace masa kawai ya tura mini kuɗi suprise ne shima ya ce a ranar akwai suprise ɗin da zai ba ni ina ta murna har ina zolayanshi na ce Yallaɓai ko ka biya mini Umra ne? Yana mirmishi ya ce in sha Allahu za mu je Umra Sadiya ta.
Da ni da yara duk mun yi ƙunshi salla wata Hajjaju ce maƙoyar su Rahila na kira har gida ta yi mana kunshi na biya ta. kitso kuma mai yi mana kitso ta zo gida ta yi ma su Jidda har da Marwa da Saude bayan ni na wanke musu kan na su a gida.
Ni dai ana gobe sallah na je shagon Amesty ta yi mini Saloon. Ban cika son yin kitso ba saboda Yallaɓai ya fi son in bar gashina a haka ta bakin shi ya ce ya fi mai daɗin taɓawa.