Turken Gida – Chapter Eight
by JanaftyMutuwa ɗaya ce haƙiƙa na tausaya mata ganin ko shekara biyu ba ta rufe da auran ba. Yallaɓai a ranar suka tafi Abuja tare da Uncle Abba da Nene, da Anty Maimuna Anty Bahijja za ta taho daga baya. Sai Hajiya iya Maman farko kaɗai aka bari a gida.
Can suka kwana Tariq da Farida daga kaduna suka tafi. Ni kuma ranar litini na je ganin likita sai ranar na je lab na karɓo sakamakon test ɗina na kai mata shima ta ce lafiya lau ba wata matsala. Sai muka je matakin gaba na A transvaginal ultrasound.
Ta ba ni nan da kwana shidda na dawo.
A ranar su Yallaɓai suka dawo daga Abuja kwanan su ɗaya amman an bar Anty Maimuna acan tare da Nene da Hajiya Kaltume sai an yi uku za ta dawo.
Ranar talata muka je Abuja gaisuwa. Ni da Hauwa da Munnira sai Jamila da Hindatu, Hafsat daman ta na can Abujan ne, sai Mimisco da direbanta ne ma ya tuƙa mu.
Mun iske gidan Gimbiya cike da yan uwa da abokan arziƙi. Kaf yayyenta mata da matan mazan suna nan, Hajiya kaltume da Nene ne tare da ita a matsayinsu na manya. Har Sameena a can na ganta ta ce tun ranar da da aka yi rasuwar ta zo sai an yi bakwai za ta koma.
Tariq ma na nan shi da Farida da yara. Amman dai shi ya ce min da zaran an yi sadakar uku zai koma gida.
Ba Gimbiya ke bin Tariq ba akwai wata mace sannan ita a shekaru ba za ta gaza 33 ba ko na girmeta bai wuce da shekara ɗaya ba.
Lokacin da nake yi mata gaisuwa ta yi matuƙar ba ni tausauyi ta yi kuka idanuwanta sun shige ciki, ba ta mgana sai dai ɗaga kai ba ta ci ba ta sha sai an yi da gaske ta ke tsakura da kuma ta ci sai ta amayar dashi. Ta rame sai farin fata da dogon hanci gabaɗaya sai ta bani tausayi har araina ina yi mata addu’an Allah ya ba ta dangana.
A bakin Sameena na ke jin Alhajin na gidanta ne lokacin da ciwon shi ya tashi. Ashe yana da ciwon hanta a Egypt ya ke ganin likita a daran su ka kai shi babba asibiti a nan Abuja da niyyar kafin a fita dashi waje, da asuban ranar Allah ya yi masa rasuwa.
Allahu akbar. Allah ka sa mu yi kyakyawan karshe.
Mun je gidajen duka matan shi mun yi musu gaisuwa tun da dukkansu suna anguwa ɗaya ne asokoro. Kuma gidajen su ba nisa bai wuce ka ga gida uku a tsakani ba. Yana da manyan ƴaƴa ba shi da ƙananu da Gimbiya ta haihu ne zai iya samun yara. Ba kuma yaro ba ne don ko da ta aure shi ya yi shekara 60 Allah na tuba a lokacin har ina ma Hauwa gulma me za ta yi da tsoho mai mata da ƴaƴa haka? Ashe zaman ma ba mai tsaho ba ne.
Duk da na zo garin da Yaya Auwal ya ke ban je ba. Saboda gaisuwa muka zo kar a ce daga zuwa ina yawo. Sai dai na kira Lailan na faɗa mata mun shigo garin, sai ta ce in da sarari za ta shigo ta yi musu gaisuwa.
Yallaɓai na bari, a gida shi da yara amma mun yi mgana ya ce gobe ranar uku za su dawo sai na ce kawai in sun dawo daga makaranta ya faɗa ma Salisu ya kai su gidan Rahila tunda ya ce za su kwana washegari sai a haɗu gabaɗaya a koma kano.
Shi ya sa na kira Rahila na ce, za a kawo mata su Jidda su kwana a wajenta kafin mu dawo tun da Salisu ya san gidanta. Saude kuma Yallaɓai baya nan ban taɓa kwatantan barin ta ita kaɗai da yara a gida ba. > Janaftybaby: Ma’u ta karrama mu ba zan raina mata ba. Shema’u sune yan gaba gaba Ma’u mijinta ne babba a maza duk da ya na da yaya mace, amman itama Anty Ma’u sama Anty Ma’u ƙasa sai abin da ta ce. Ina ta mamakin ina abokiyar zamanta Hajiya Zainab? Sai can na ganta ta ci kwalliyarta da kin ganta kin ga wacce ta gaji arziƙi ba haye ba. Ita ba ruwanta gaskiya ba ta son hayaniya ma Ma’u kuma da ya ke yar bariki ne duk ta siye dangin Alhajin da siyasar ta.
Yaya Murja sai da ta yada mini mganar wai sai yanzu na zo biki da rana. Ni ko na ce Yallabai na gida tare muka zo dashi shima ya zo ɗaurin aure.
Shema’u kuma ba ta mini magana ba ta yi wani ɗan iskan ɗinki duk ya kama jikinta fuska da jiki sun sha mai ta yi wani fayau saboda in rama wulakancin da ta mini sai da na bari ta shigo ɗakin da aka saukemu sannan na kalleta ina faɗin
“Shema’u ranar da muka sauke ki a gidan Nene Tariq ke faɗin wai kin karɓi lambar wayar Uncle Abba.”
Ba ita kaɗai ba gabaɗaya waɗanda ke wajen sai da suka kalleni daman na yi alƙwarin yadda ta yi min cin mutumci a gidan Rahila sai na rama.
Ina mirmishi na ce” Wai kin roɗa ne? To gwara ma ki bi wani sarki shi Uncle Abba mata har ƴayan sarakuna daga Rano an yi masa talla bai ɗaga kai ba ballanta ke, na san dai zuwa yanzu kin ma san ya fi karfinki tunda lambar wayar ma ba tashi ya baki ta Tariq ne.”
Ƙur ta yi min da ido, ni kuma sai na gauraye fuskata da mirmishi Rahila na ta mini sigina na yi kamar ban gani ba har Yaya Murja mai baki ta kasa mgana.
Shema’u kuma dakyar ta iya yaƙe kafin ta ce” Oh. Wannan daman na karɓi lambarsa ne saboda na ga ya yi min kama da wani sai daga baya na gane bashi ba ne, ni fa Sadiya ɗan’uwan mijinki ya yi mini tsufa kaf ma a dangin sa ba wanda zai iya dai dai da Shema’u.’
Ta faɗa cikin danne yanayinta ina dage mata gira na ce”Da gaske?
Cikin renin wayau Anty Aina ce ta yi mgana.
“Sadiya ki bar mganar don Allah.”
Sai na yi dariya kafin na ce” An barta.”
Shema’u na yaƙe ta fice amman ni kaina na san ta ji abin da ake ji in ka tozarta wani a cikin jama’a sai da ta fita Yaya Balki ta ce ya aka yi ne na gyara zama ina faɗa musu yadda aka ƙare.
Yaya Balki na dariya ta ce” Wannan akwai ɗan jaka da rabi. Zai haɗa fada.”
Ina dariya na ce” Kaɗan daga aikin Uncle Abba kenan.”
Rahila ta ce ta gane shi ta taɓa ganin shi a gidana Yaya Murja ba ta ce komai ba sai daga baya ta ce” Ko ma dai menene ba kyau cin fuska a cikin jama’a.”
Kai tsaye na ce” Ba cin fuska ba ne. Ai naga nan duk ɗayan ne ko?
Ta kalleni na kalleta sai kuma ba ta ƙara mgana ba. Ma’u ba ta ɗakin amman na san za ta ji labari Zaituna kam duk muna tare da ita amman ta ci abinci har da guzurin alale, ni da mangariba muka tafi ni da Rahila da Zaituna Yaya Murja ta ce sai ta kai Amarya amma Yaya Aina da Yaya Balki ban ji suna zencen ba amman dai can muka bar su.
Na dawo gida da Waina da sinasir Ma’u ta matsa dukkanmu sai da muka taho dashi
Shi na ci na sha ruwa tunda mai siga ne sai dare Yallaɓai ya je ya ɗauko su Jidda suka dawo gida.
Su sun ci abinci Yallaɓai ne na dafa ma Indomie da ruwan tea ya ci kafin ya kwanta.
Washegari Lahadi da asuban fari sai ga wayar Tariq Allah ya yi ma mijin Gimbiya rasuwa.
*Janafty* > Janaftybaby: Duk anan gidan Gimbiyar muka kwana. Abinci sai dai a kawo shi a dafen shi komai ga shi. Saboda ya na da kuɗi dan kwangila ne ya tara abin duniya kuma a baya ya yi siyasa.
Washegari ranar da aka yi sadakar uku da wuri su Yallaɓai suka iso shi da Uncle Abba da su Kawu Sa’adu sai Anty Bahijja. har cikin gida kuma sun shigo an yi ma juna gaisuwa.
Ni ina can ɗakin da muka kwana ba mu haɗu ba sai can yamma ma. Mun dai yi mgana ta waya da daddare kuma sun ƙara shigowa, a bakin Munnira na ji ta na faɗin wai Tafida ne ma ya matsa ma Gimbiya da lallashi har ta amince ta sha tee ɗin da yawa kuma sannan sai yau aka ji ta taɓa buɗe baki ta yi mgana amman ga Tafida kaɗai. Ban yi mamaki ba sanin shaƙuwarsu kuma a lokacin ai abar tausayi ce.
Washegari muka dawo kano amma mun bar Nene a can ita da Hajiya Kaltume da sauran ƴan uwanta. Mota ɗaya muka shiga da Anty Bahijja na ji suna mgana da Mimisco da cewa wai Gimbiya ba ta mgana da kowa sai Tafida sannan shi kaɗai ke ba ta abu ta karɓa ta sha. Su Nene haka suke yi kamar za su ari baki amman ba ta cin komai ba ta mgana sai kuka.
Anty Bahijja ta ƙare maganar ta da cewa” Ga shi kuma kin ga ba gari ɗaya ba. Balle a ce ko da yaushe ya riƙa zuwa ya na matsa mata ta ci abinci”
Ina kujeran zama ta tsakiya saboda motar irin babba ce ta yara ta mijin Mimisco ne.
Ni da Hauwa muna zaune waje ɗaya har muna haɗa ido muka kalli juna amman ba mu yi mgana ba.
“Ba matsala ba ne. Jiya mun yi mgana Hajiya ana tunanin da an yi arba’in Gimbiya za ta koma Rano.”
In ji Mimisco sai Anty Bahijja ta ce” Ai ya ma fi sauƙi. Allah dai ya ba ta dangana baiwar Allah.”
Mimisco ta amsa da Amin.sai ita Anty Bahijja ta ƙara da cewa” To Nene fa? Ko itama tare da Hajiya Kaltumen za su zauna har arba’in ɗin?
Sai ta yi shuru kafin ta ce” In za ta iya sai ta zauna. Tunda na taho mata da magungunanta da ta manta. Gida daman ba wani abu take yi ba.”
Muna jin su suna ta tattaunawarsu har muka iso kano. Da ya ke mun iso da wuri Yallaɓai suna baya mun riga su yo gaba gaskiya. A bakin hanya na ce su sauke ni na samu adaidaita zuwa gida.
Sai da na isa gidana na yi salla na dafa indomie na ci sannan na dawo hayyacina. Sannan na kira Yallaɓai sai ya ce min suma sun kusa ƙarisowa, sai na ce ya kira Salisu ya faɗa masa in ya dauko su Jidda daga makaranta gida zai kawo su na dawo sai ya ce to.
Ni kuma sai na kira Rahila na ce mata na dawo sai ta ƙara min gaisuwa ni kuma na yi mata godiya har ta na cewa” Uban godiya ke fa ba ki da hali wani lokaci.”
Daga nan ta kashe wayarta ta bar ni ina dariya.
Bayan Rahila da Laila ba wanda na faɗa ma an yi ma su Yallaɓai rasuwa sai gashi kwana ɗaya tsakani da dawowarmu daga Abuja a group gidanmu na ga Yaya Balki na yi min gaisuwa da na tamnbayi in da suka ji sai ta ce Yaya Murja ta faɗa mata da ta je gidanta itama ta ce Ma’u ce ta faɗa mata.
Abin sai ya bani mamaki na ga ni dai ba tamin gaisuwa ba. Amman ta je tana faɗa, ban yi mamaki ba tunda tana tare da Anty Bahijja ta kuma yarda da ita shi ya sa wasu labaran na dangin mijina kafin ni na kai ga furta ma wani Ma’u ta yaɗa shi a gari. Tsaki na yi a fili kafin na ce” Wannan ai gwara ta kashe auran nata ta auri Nasir ko Musabahu da wannan bin diddigin na ta.”
A daren kuma sai ga ta ita da Alhajinta wai sun zo ma Yallaɓai gaisuwa. Kuma abin da ya ɓata mini rai shi Alhajin ya kira Yallaɓai ya faɗa masa za su zo amman Ma’u ba ta kirani ba, shima Yallaban ya kira wayata bai samu ba ƙwatsam na gansu lokacin shi bai ma riga ya dawo gidan ba.
Da ɗan fara’ata na karɓe su. Bayan mun gaisa sun yi mini gaisuwa sai na ce ai Yallaɓan bai dawo ba sai ya ce ai sun yi mgana dashi ya na kan hanya. Kafin ya ƙariso na kawo muusu ruwa da lemu na yi shinkafa da miya na kawo musu suka ce sun ƙoshi sai da suka ci abinci sannan suka fito daga gida.
Ba ko daɗewa sai ga shi ya iso. Saboda mu ba su waje sai na ja Ma’u zuwa falon na biyu na kora su Jidda ɗakin su bayan sun gaida Ma’u ta amsa cikin fara’anta har tana faɗin” Jidda idon ki kenan? Ina nan dai ina jiran ki a wannan hutun.” > Janaftybaby: Sai Jidda ta fara kallo na, sai na yi saurin cewa” A’a ni ba ruwana ki tambayi babanki in ya barki in an yi hutu sai ki je.”
Da sauri Ma’u ta ce” Ai ni dai na san Yallaɓai ba zai hana ba.”
Sai kawai na ɗan yi yake. Muna zaune ba mgana sai baɓatun talabijin.
“Ashe kin je Abujan kema?
“Uhm”
Na faɗa ina kauda kaina ba na son kallon Ma’u saboda kallonta ba alheri a cikin yanayin kallon ta.
“Allah ya jikan sa.”
Na amsa da Amin shuru na wani lokaci sannan ta ce” Allah sarki ta ba ni tausayi rashin miji ba daɗi.”
“Ai fa kam.”
Na faɗa ban bama mganar muhimmamci ba.
“Allah ya kawo mata kyakyawan zaɓi.”
Na amsa da Amin na ɗauka daga nan maaganar za ta tsaya sai kawai na ji tana faɗin.
“Anty Bahijja na gaya mini halin da ta ke ciki kamar in yi mata kuka ta ce mini ba ta cin abinci sai kuka ba ta kuma mgana da kowa sai Yallaɓan ki”
Kure ta da ido na yi domin na san daman sai ta zo wannan gabar.”
“Ta ce min shi kaɗai ke iya cewa ta ci abinci ta ci kuma shi kaɗai take yi ma mgana. Abun mamaki ko da ya ke na ji labarin an ce daman sun shaku da juna.”
Ta fada tana mini mirmishi.
“Haka na ji.”
Nima sai na ba ta amsa amman ban nuna wani abu daga saman fuskata ba.”
“Allah sarki. To bakomai tunda na ji Anty Bahijja na faɗin ana arba’in za a dawo da ita Rano Sai na ce ai ko ga shi kusa ina Rano ina Kano? Yallaɓai sai ya riƙa zuwa yana kula da ita baiwar Allah abin tausayi.’
Ta gama faɗa har tana bayyana jimamin a saman fuskarta.
Ni na san da biyu ta yi wannan maganar sai kawai na yi mata mirmishi kafin na ce” Gaskiya ne. “
Sai na datse bakina ban kara yin mgana ba amman ina kallonta ta gefen ido tana mirmishi kafa ɗaya ta ɗora kan ɗaya kamar falon gidan Alhajin na ta ne.
Yadda ta ga na haɗe rai ina duba wayata ya sa ba ta ƙara mgana ba. Ba daɗewa ma sai ga shi Yallaɓai ya leƙo ya ce Ma’u ta fito za su wuce tsabar haushi iyakata a bakin kofa ban fita haraba ba Yallaɓai ne ya fita ba su shigo da mota ba sun yi parking daga waje ne.
Kamar maganar Ma’u ba za ta dame ni ba, sai gashi kuma tana sukan raina ace wai komai ya faru a dangin mijina sai Ma’u ta sani in na ji haushinta ta wani fannin kuma ban ganin laifinta ba kowa ya ba ta dama ba sai yayar Mijina. Ta kuma wani bangaren itama Anty Bahijja sai na ke yi mata uzuri saboda in dai Ma’un da na sani ne makircinta zai iya siya mata kowa da kuma wannan makircin ta siye Anty Bahijja. Renin na ta har ya yi yawan da za ta zo har gidana tana gaya min mgana na ci ji yatsa da na ƙyaleta amman dai na san za ta ƙara wata rana dole za mu haɗu.
Washegari na koma asibitin domin ganin likita. Wannan karon ma Dr Aisha ta ce vaginal ɗina komai lafiya lau sai matakin gaba na A hysterosalpingogram a type of X RAY, that allows your provider to see your uterus and follopian tubes. Dr Aisha ta faɗa mini scan ɗin is very painfull tunda na cikin mahaifa ne. Ta gaya mini zan iya bucking anan asibitin ko mu fita waje, da na kira Yallaɓai sai ya ce kawai na yi bucking anan asibitin, ban dawo gida ba sai da na yi bucking sun ba ni sati ɗaya na dawo su yi min scan ɗin. Ban damu da wahala ko wani abu ba babban burina na kai ga matakin nasarata shine a gabana.
**
BAYAN SATI UKU.
Bayan sati da huɗu rasuwar mijin Gimbiya a lissafi kuma bai fi saura kwana biyu ya yi arba’in da rasuwa ba.
Kuma har alokacin Nene da Hajiya Kaltume ke zaune da ita sai dai yan’uwa da ba su samu zuwa ba sukan je domin yi mata gaisuwa.
Har na ji Yallaɓai suna mgana da Mimisco akan a cikin satin su Nene za su dawo da Gimbiya gida.
A cikin sati ukun da suka gabata lamarin Gimbiya ya fara ba ni mamaki har na fara tunanin ko ba ta da tawakalli ne kuma har sai da na furta ma Yallaɓai har ya ji haushina. Haba abun nata ya yi yawa ba kanta farau rashin miji ba Allah na tuba sauran matan shi da suka yi shekaru aru aru da shi ma sun ɗau dangana haka ma ƴa’ƴan shi da suka rasa uba suma sun dangana amman ita ba alamun dangana a lamarinta. > Janaftybaby: Na tuna ni kaina fa uwata ba ta a duniya nan na ɗau tawakalli Yallaɓai ba shi da uba shima ya ɗau dangana. Har wani lokacin in na jin masa shaƙiyanci ko ina son ya yi min wani abu ya ce ba zai yi ba sai na marairai ce ina faɗin.” Yallaɓai ka tausaya mini ka ga ni fa marainiya ce.’
In na ce haka a lokacin sai ya yi dariyan nishaɗi kafin ya ce” Au ke sai yanzu kika san ke marainiya ce? Mu ai mun daɗe cikin maraici kuma ba mu mutu ba.”
Ko kuma ya ce” Ke ba marainiya ba ce Alhaji ai bai mutu ba ko kin kashe shi ne? In ya faɗi haka daga ni har shi sai mun ƙyalƙyace da dariya. Saboda mun yi shaida babu abun bautawa da gaskiya sai Allah. Kuma Annabi muhammdu manzonsa ne, sannan rayuwa da mutuwa duk ta na hannun shi ne.
Sai dai ta bangaren Gimbiya ba ta san wannan ba, tun da a ka yi rasuwar nan saboda ba ta jin mganar kowa sai na Yallabai a rana ban san adadin sai nawa ya ke kiran waya a ba ta ba, yana lallashinta ta samu ta ci wani abu. Ko in ta fara kuka sai su kira shi su ba ta ya yi ta mata nasiha, duk wannan ƙokarin da ya ke yi mata ba ta dangana ba. Bayan wanda yan’uwa ke yi mata shima duk bai sa ta dangana ba. Tun ina tausayinta har ta koma ba ni haushi. Na yi ta tunanin ita ko wani irin so ta ke yi masa haka. ko dai garken yaya ta tara da shi sai haka amman aure duka duka wata ashirin ba ciki ba goyo haba lamarin nata ya yi yawa har na fara gajiya da jin labarin halin da ta ke ciki a bakin Yallaɓai in yana faɗa min Daughter ta zama abin tausayi, tun in yana faɗa ina nuna jimami har na daina saboda lamarinta ya wuce na musulma mai tawakalli ya koma hauka da jayayya da ubangiji.
Nan ko sati ba a yi ba sai da Yallaɓai ya koma Abuja ya kwana ɗaya sannan ya dawo. Wai ta shige ɗaki tun safe ta rufe kanta tana kuka kuma tun daren jiya ba ta ci komai ba su Nene sun yi sun yi da ita ta buɗe ta ƙi har azahar shi ne Nene ta kira Yallaɓai a waya ta ce ya bar duk abin da ya ke yi ya zo Abuja. Shi ne fa ya na ma office ya dawo gida ya na faɗa min tare da cewa na haɗa masa kayan tafiya na kwana ɗaya tun da ba zai yuyu ya je a yau ya kuma dawo ba.
A lokacin ne na furta masa abin da ke zuciya ta.
“Haba kamar dai ba ta da tawakkalli. Wai kanta farau mutuwar miji?
Na faɗa ina mai sakin tsaki tun da shima yana kan aikinsa ne amman an wani ta da shi zuwa Abuja. Ni ina ganin gulma ne ace duk cikin yan’uwanta da suke uwa daya uba ɗaya mata da maza ba ta ga wanda za ta riƙa jin mganarsa ba sai Yallaɓai da zaman da ya yi a gidansu na ɗan lokaci ne, za a ce ya fi mata yan’uwanta da suka fito ciki ɗaya ne?
Tsawa Yallaɓai ya daka mini kafin cikin ɓacin rai ya kalleni ya na faɗin” Sadiya wannan wani irin mgana ne?
Kallonsa na tsaya yi saboda sai na ga kamar ban faɗi wani abu mara kyau ba.
“Me na ce? Gasikiya na faɗa hakuri ake yi. In ta na wannan abun kamar tana faɗa da Allah ne.”
Kawai sai Yallaɓai ya fara faɗa ta in da ya ke shiga ba ta nan ya ke fita ba. Wai na san zafin mutuwan miji kuwa.?
Ni ko kai tsaye na ce” Ban san na miji ba. Amman ai na san zafin mutuwar uwa ko?
Na faɗa ina kallon shi saboda na ga zai wani hau kaina daga faɗin gaskiya saboda ma na ƙara kunsa ma sa kai tsaye na sake faɗin” Kuma na tabbata ba yau aka saba mata rashi ba. Ai ta rasa uba da yan’uwata me ya sa ba ta yi haka ba sai yanzu? Gaskiya ku yi mata faɗan ta zama mai tawakkalli kuka ko rufe kai a ɗaki ba shi zai kawo mafita ba.”
Ni kaina tsaye na ke mgana kuma shi kan shi Yallaɓan ya san ni.
Amman a mamakina kai tsaye ya kalleni kafin ya girgiza kai ya na faɗin” Na yi miki uziru saboda ba ki san zafin mutuwar miji ba. Amman ba shi zai hana na ce ba ki da tausayi ba Sadiya.”
Baki buɗe na kalli Yallaɓai ya na sauya kaya cikin nuna kaina na ce” Ni ce ba ni da tausayi Yallaɓai?
Kai tsaye ya ce” Ƙwarai da gaske. Domin duk mai tausayi tausaya ma halin da Daughter ta ke ciki zai yi ba maganganun banza marasa tushe ballantana makama ba. Shirme kawai.”
“Daga faɗin gaskiya?
“Ki riƙe gaskiyan ta ki ba a so.”
Haka ya maida mini amsa a fusace. > Janaftybaby: Ajiyar zuciya kawai na sauke domiin na ji raina na tafarfasa zan iya maida masa martani amman sai na ƙyale shi, ɗakin na bar mishi kayan na shi ma ban gama haɗawa ba na ce ya haɗa da kan shi tun da da ga faɗin gaskiya sai na yi laifi ya je can ya tare saboda kula da ita. Da zai tafi ko sallaman da muka saba ba mu yi ba, shima fuska a haɗe nima na haɗe nawa ko haraba ban raka shi ba, daga falo na yi masa fatan Allah ya kiyaye hanya.
Amman Yallaɓai ya ba ni mamaki, yadda ya wani ɗau zafi daga fafin gaskiya. Wani abu ke tsaya min a maƙogwaro in na ji yana ambaton ta da Daughter ƙatuwar mace shima ya na namiji magidanci da wani sanabe da iyayi.
Har ya je ya yi kwanan ɗayansa ya dawo ba mu yi waya ba. Ya san halina yadda bai kirani ba nima ban neme shi ba su Jidda suna ta tambayan Abba na ce ya ta fi Abuja.
Da ya dawo ban yi masa tarban da na saba ba. Ni ban haɗe rai ba sannan ban sakar masa ba, sai dai lokacin da ya dawo sai bai dawo da fushin ba. Shi ya fara saki sai nima na saki amman na so ya cigaba ya sanni ni sai na iya gaba dashi ba wani abu mai wahala ba ne a wajena. Amman kalmar ba ni da tausayi da ya kirani da shi ya taɓa ni kuma sai da na yi masa mgana sai ya ce na yi hakuri amman nima ai bai dace na ce haka ba, kenan har a lokacin bai ga gaskiyan abin da na faɗa ba to ai shike nan ni kuma na saka a raina ba zan kara mgana ba.
Abin da ma ya faru a can ɗin ban tambaye shi ba shi da bakin shi ya ke faɗa mini Ulcer ta kama Gimbiya sannan kuma jininta ya hau sai da likita ya zo gida ya duba ta. Bakina ƙanin kafata na ce Allah ya ba ta lafiya domin na fahimci Yallaɓai kiris ya ke jira da ni ya yaɓa mini mgana.
Bayan arba’in da kwana uku Gimbiya ta dawo Rano. Mimisco ta je tare da ita ma aka maida ta rano. Sai yayyenta maza da suka je saboda sun gana da yan uwan marigayin da yaran shi. Farko sun nuna ba su so tafiyar ta ba sun nuna gwara ta zauna a gidanta ta gama takaba sai su kuma ƴan uwanta su kawo dalilin halin da ta ke ciki in ta koma gida ta na ganin mutane za ta samu ta dawo dai dai ba kamar zamanta anan ba, da haka suka amince ta koma gida amman sai da aka kai ta duka gidajen matan ta yi sallama da su. Suna kuka tana kuka an kwashe mata duka kayanta a ka rufe gidan aka mika makullin ga iyalanshi tunda sun ce suna kan tatrara abin da ya bari ne bayan an gama za a bincika in da baahi a biya in babu kuma in lokaci ya yi za su nemesu domin rabon gado.
Gimbiya ta yi sallama da garin Abuja, aikin nata ba mganar shi daman tun da aka yi rasuwar ba ta je ba. Ana tunanin in komai ya lafa a yi mata transfer ko zuwa cikin garin kano ne. Kwana biyu tsakani da dawowarta na je yi ma Nene bangajiya tun da sai da ta ƙara kwana a Reno sanman ta dawo gida ita ce ma ta ke bani labarin abin da ya faru kafin ta tahowar su.
“Allah sarki. Allah ya yi mishi Rahama ita kuma Allah ya ba ta dangana.”
Nene ta amsa da Amin kafin t ce” Ai an fara karɓa mata rubutu wajen wani malami a can rano. Da safen nan mun yi mgana da Hajiya ta ce ta fara sha da safe. To Saudatu ta rame ta lalace ta fita hayyacinta. Rayuwarta akwai tausayi sosai.”
Nene ta ke faɗa cikin rawan murya. Ni kuma sai na ce” Har yanzu ba ta fara dangana ba Nene? Sai ta ce a hankali dai amma in na ga Saudatu sai na tausaya mata.
A gidan na yini ina nan Hauwa da Munirra suka zo da su Suwaiba domin yi ma Nene gaisuwa da barka da zuwa kaf ahalin gidan nan Yaya Usman ne kawai bai zo ba da Anty Zabba amman dai sun yi gaisuwa ta waya, har Muhammad Kabir da Nafisa sun zo gaisuwa daga katsina.
Sati ɗaya da dawowarta Yallaɓai ya ce na shirya muje Rano domin na ƙara yi musu gaisuwa ban yi musu ba na shirya ashe tare da Mutakƙa ne da Hauwa sai na ji daɗi a motar Yallaɓai muka je ranar weekend yara kuma wajen Nene muka bar su gabaɗaya.
Mun je mun iske mutane cike a gidan a kallah dai ba za ta yi kaɗaici ba. Sannan ga babbar Aminiyarta babbar ɗiyar Anty Zuwaira Naja’atu duk da ita Gimbiya ta girmi Naja’atu amman kuma Allah ya haɗa wannan kawancen lokacin da aka yi rasuwar ita da mijinta ba sa ƙasar suna Italy. > Janaftybaby: Kuma lokacin da aka yi rasuwar ta so dawowa sai matslan visa ya hana ta sai dai su yi mgana a waya to faa sai cikin satin nan ta dawo. Amman a kano take aure da yaron wani mashuririn ɗan kasuwa a garin kano mai suna Buhari manga. Ba su cika ma zama a Nigeria ba yawancin kuma duka yayan da Naja’atu ta haifa guda uku a kasar waje ta ke zuwa ta yi renon cikin ta ta haihu.
Ita muka iske tare da Gimbiya wacce ta faɗe ta rame sai dogon fuska da hanci bakinta duk ya bushe idanuwanta duk sun zurma. Tana sanye da hijabi da caabaha. Mun gaisa da Naja’atu duk ba wani damuwa da mutane ta yi ba, irina ce shi ya sa na ke yi mata uzuri ban cika damuwa da halinta ba ammam duk in da muka haɗu za ta gaisheni da tambayan su Jidda.
A ɗakin Hajiyar Tafida muka zauna ita kuma Gimbiya da ƙawayenta suna ɗakin Hajiya Kaltume kamar acan aka sauke ta tana takabar nata. Muna Rano har bayan la’asar na yo alwala daga bayin waje Hauwa ta rigani yin na ta shiga ɗakin Hajiya ni kuma lokacin da na yo tawa sai na ga maza sun shigo yan gaisuwa sun shiga ɗakin sai na wuce ɗakin da Gimbiya ke ciki Naja’atu ma ta bani darduma na shimfiɗa na ta da salla.
Na kai raka’a ta biyu na miƙe a raka’a ta uku Yallaɓai ya shigo na ji muryan Mutaƙka da na Uncle Abba sai na wasu mazan amman tun da ina salla ba zan iya sanin su ba. Ina ji Mutaƙka na yi ma Gimbiya sallama daman kuma Yallaɓai ya ce bayan la’asar za mu tafi.
Daga nan sai kowa ya fita har Naja’atu aka bar Yallaɓai da Gimbiya. Ban sani ba ko shi ya gane ni ce ke sallah ko kuma bai gane ni ba amman ita ta san nice na ke yin salla a wajen
Suna ta gefen damana ne, ina kai sujjadar ƙarshe na ga Yallaɓai ya duƙa a gaban Gimbiya yana mai kiran ta da sunan da ya saba kiran ta dashi.
“Daughter.”
Sai ta ɗago ta kalle shi a marairaice kafin ta amsa murya shaƙe.
“Daddy.”
Dai dai lokacin da na ce” Assalamu alakum waramatullah
Hagu da dama da kuma ƙarfi, ina juyawa bangaren dama muka haɗa ido da Yallaɓai har da ita Gimbiyan
Ina salla ne amman kirjina na wani irin suya ne. Kallon yadda ya gurfana na yi a gaban Gimbiya har gwiwar kafarsa na gugan kafafunta da ke tankwashe sai kawai na kauda kaina na miƙe ina na ɗe darduman da na yi sallah da shi.
Ko kunya ya ji da ya ganni sai ya yi saurin matsawa baya ya na mai miƙewa tsaye.
“Da man ke ce ke salla?
Ya faɗa ya na kallona sai kawai na kalle shi kafin na ce” E”
Sannan na ijiye darduman a saman hannun kujera kafin na kama hanyar barin ɗakin ina faɗin” Ku cigaba da mganar ku.”
Ban san ko sun bi ni da kallo ba saboda ni ban juyawa ba har na fice daga ɗakin.
Ba dota ba doya ba daddy ba Dada. Tun daga lokacin na rage fara’a har Hauwa sai da ta tambayeni ko lafiya na ce lafiya lau kila Yallaɓai ya tsargu ne ya sa bai daɗe a ɗakin ba ya fito ya leƙo nan ya na cewa mu fito za mu biya gidan su Nene kafin mu wuce.
Sallama muka yi musu, sannan mun kara shiga wajen Gimbiya muka ƙara yi mata Allah ya jikan rai ya ba da danganta ta amsa a hankali. Daganan sai gidan su Nene muka je muka gaida Innayi ko minti talatin ba mu yi ba muka kamo hanyar gida. A cikin zuciya na ga to damuwar ta mace ce, namiji fa sunan shi Namiji ba abin da ba zai yi ba sai kawai na watsar da abin na ɗan saki fuska Yallabai daman suna hira da Mutaƙƙa ya nna ta faman sako ni a ciki da a shake na ke amsa masa sai daga baya na saki jiki muna ta hira. Sai da muka biya Gwammaja muka ɗau yara sannan muka kai su Hauwa gida muka wuce namu gidan
Yallaɓai dai kamar ya kama kan shi ni dai ƙala ban ce masa ba sai shi ne da za mu kwanta ya ɗauko mganar.
“Dazu Allah ban san ke ce ke sallah ba.”
Na yi kamar ban ji sa ba sai ya ƙara cewa” Kin san da ya ke sai a hankali. Na shiga yi mata sallama na ke ƙoƙarin lallashinta ta riƙa cin abinci.”
“Haka fa. Ai ka kyauta.”
Daga nan na juya masa baya na ja bargo. Ban sani ba ko yabi ni da kallo amman ina da tabbacin ya yi haka. Bai takuramin ba amman ya raɓo ta bayana mun kwanta.
* > Janaftybaby: Haka rayuwar ta cigaba da tafiya. Wattani wajen biyu sun zo sun shuɗe kamar tafiyar iska. Har su Jidda sun yi jarabawa 3rd tearm sun yi hutu. Jidda Gidan Mimisco ta tafi hutu ita kuma Baby gidan Yaya Maimuna gida tsit daga ni sai Yallaɓai sai Saude da ke zuwa yi min aikace aikace.
Bangaren asibitina kuwa tuni na yi nisa a gwaje gwajen da ake yi minib wanda na yi na ƙarshe shi ne Pap smears ne kuma har na karɓi result ɗin wannan satin da ya wuce na kai ma Dr Aisha cikin ikon Allah ta ce mini shima ba wata matsala.
In da na ke ɗan samu salama kenan kuma ta na bani hop ɗin duk da saura gwaje gwajen ba mu gama ba, ba ni da watsala lokaci ne bai yi ba in ya yi zan ƙara haihuwa.
Zuwa lokacin shiryen shiryen bikin Yaya Usman ake yi domin cikin watan da za mu shiga kafin azumi za a yi bikin na shi. Anan Gwammaja za a yi bikin tunda ɗaurin auran ma a kaduna ne. Yadda Yallaɓai ya faɗa mini gabaɗaya da Anty Zabba da yaran za su zo kamo sai an gama biki za su koma fatakot har da amaryan.
Har anko ƙannensa su Nasara sun fidda Atamfa ce mu ma duk mazajen mu sun yi mana mu da yara. Aure dai ya tabbata ba fashi amarya na dawowa daga london aka tsaida date ɗin biki.
A kuma tsuƙin ne na kirga za mu yi 15 years Anniversery da aure ni da Yallaɓai zuwa bayan sallan azumi da kwana shidda kenan. Ni kaɗai a raina na shirya za mu yi walima tun da tun na 10years ba mu kara ba lokacin Baby ta cika shekara ɗaya sai muka haɗe da birthady ɗin ta.
Ba mu kara yi ba sai wanman karon na ke fatan mu sake yi. Daman a gida ne daga ni sai shi sai yara muka yanka cake ɗin mu sha hotunan mu da ciye ciye washegari kuma Yallaɓai ya fita damu mu wajen wassani da sauran su. Tun tuni na so na yi masa mganar amman bai samun lokaci Alhamdulillah yana ta samu kwangila bayan gama gina gidan buredi a Rano dalilin haka ya samu kwangilan gina bayuka na wasu makaratun sakandiri a garin na Rano sai ya kasance zamansa a nan office ba sosai ba sai dai Musabahu ya zauna wani lokacin gidan bulo kuma daman sun ɗauki yara ma su kula da shi, shi dai Musabahu manaja ne kawai.
Abin da na fara lura da shi shi ne Gimbiya ta fara ƙoƙarin takura ma rayuwar aurena ta na daga can gidansu tana takaba.
Ni na san cewa Yallaɓai na zuwa ganinta tun da yana yawan zuwa Rano. Ban kuma taɓa nuna damuwata ba ko na nuna fuska ban ji daɗi. Sai dai na ga ba ta da hankali in ya dawo gida sai ta kira shi a waya ta ji wai yadda ya koma gida. Da safe kuma ta iya kiran sassafe tsirfa kala kala daga ta ce Anty Bahijja za ta ba da saƙo a kawo mata sai ta ce Nene sai ta ce Anty Maimuna wani lokacin ita ce ma za ta ce ya siya mata abu kaza ya taho mata dashi tsirfa kala kala ranar da bai je Rano ba ta riƙa kira kenan ta na korafin me ya sa bai zo ba? Abin da ke ba ni mamaki shi kuma sai ya na biye mata sau ɗaya na yi masa mgana da cewa wani lokacin ta na kiran shi a waya ba ta da abin faɗa sai kawai ya ce min abar tausayi ce kuma ga shi ta samu hawan jini dalilin rasuwar nan shi ya sa ba a son ana ɓata mata rai.
Na ga ƙoƙarin Yallaɓai da ya iya faɗa min haka amman kuma ta wanni fannin ban yi mamaki ba mun taɓa samun matsala da shi a baya tun ban haifi Baby ba akan Gimbiya muka yi faɗa da Yallaɓai na ce in son Gimbiya ya ke yi me ya sa ya aure ni bai aure ta ba saboda na ga bin binin ya yi yawa amman sai buɗe baki ya yi ya ce mini” In da bai haɗu da ni har Allah ya haɗa zukatanmu ba to ya ba ni tabbacin bashi da mata sai Saudatu.”
Har Gimbiya ta yi aure ban daina fargaban wata rana zan ta shi na ga Yallaɓai ya auro min ita ba na huta da ta yi aure amman yanzu kam bayan ta zama bazawara ta sake dawo mini cikin rayuwata ta na yi min barazana.
Akwai wata rana baƙin ciki kamar na kama Yallaɓai da duka da asuban fari fa, ya je sallar asuba bai dawo ba ta yi ta kiran wayarsa ina ganin an saka Daughter na san ita se sai ban ɗauka ba. > Janaftybaby: Sau uku ta na kiran sa har wata zuciya ta ce na ɗauka sai wata ta kwabe ni sai da ya dawo na ce an kira shi a gabana ya ɗaga waya ya kirata bayan sun gaisa shi ya ma ɗauko ko wani abu ne ya faru ya na tambayanta ko akwai matsala ne ina jin muryanta ta cikin wayar tun da wayar da ɗan kara ta na faɗin.
“Daddy yau za ka shigo?
Sai ya ce ya na sa ran yau sai kawai ta ce” Ka taho mini da tsaraba.”
Shi kuma ya ce me take so ta ce duk abin da ya ke so.
Tsabar takaici na kasa mgana.
Sai na shanye takaicina na kalle shi ina faɗin” Wai ta gama takaba ne?
Kai tsaye ya ce min” Cikin wata nan za ta fita in sha Allahu.”
Sai kawai na girgiza kaina, ina so na yi mgana amman kuma sai na fasa saboda maganar ba ta da amfani sai kawai na yi masa shuru kuma ya je Ranon a ranar kuma ina da tabbacin ya yi mata tsaraba tunda bayan ya dawo gida muna tare ta kira tana yi masa godiya. Ƙarin abin haushin ma wani lokacin in dai ya kai dare a can abincina sai dai ya zama kwantai sai ya ce Hajiya ta matsa masa ya tsaya ya ci abinci. Kuma Yallaɓai na ganin ina nuna damuwar hakan a saman fuskata bai taɓa damuwa da ya ba ni haƙuri ba shi a wajen shi ba a yi komai ba sai kawai na koma gefe na na zura masa ido ina ganin gudun ruwan shi amman dai ni na san ko na ƙi ko na so ai ƙarshen alewa daman ƙasa ne.
KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.*
07045308523.
*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE*