Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    Aminu kano Teaching Hospital.
    Gynecologist Unit.

    Ina zaune a kan kujeran da ke fuskarta wajen zaman likita. Idanuwana kir a kan Dr Aisha Bukar ina ƙare mata kallo. Ta fi Dr Fatima shekaru ita babbar mace ce gaskiya a kallah in ba ta haura 40 ba za ta tsaya a hakan ta na da kaurin jiki, ga tsawo ga kiba sannan ba ta da wani haske sosai.

    Tana zaune tana duba fayel ɗin gabanta gefe ɗaya kuma hankalinta na kan system ɗin dake gabanta da alama dai akwai abin da ta ke dubawa a ciki. Fuskarta da gilashi siriri sannan sanye take da rigan likitoci kanta kuma ta sanya ƙaramin breziya Hijab fari.

    “Sadiya Sulaiman Yashe”

    “Maa.”

    Ba ta kalle ni ba hankalinta na kan system ɗin gabanta ta ce” Ke ce wacce Dr Fatima ta yi transfer ɗin ki daga ABU KO?

    Sai na gyaɗa mata kai lokaci ɗaya da cewa” Yes” Saboda da turanci ta yi maganar.

    Tsayin mintina goma sannan ta ce” Ga Report ɗin ki da ta tura mini ina kan dubawa.”

    Da hausa ta yi mganar wannan karon kafin ta dawo da hankalinta kaina.

    “Sunana Dr Aisha Bukar. Zan cigaba da jagorantar matsalarki har zuwa lokacin da za ki samu waraka in sha Allahu.”

    Ba ta jira jin ta bakina ba kawai ta cigaba ta faɗin.

    ” A yadda na ga ɗan brief na matslar ki, kafin mu je kan matakan da muke ɗauka ga masu irin laluran ki, kin san abin da ke damun ki? Ko dalilin da ya sa ba ki sake haihuwa ba?

    Na ɗaga mata kai zan yi mgana kawai cikin zaƙin muryanta ta ce.

    “SECONDARY INFERTILITY”

    Kai tsaye kuma ta cigaba da bayanin ta.

    “Kuma shi Secondary infertility ( rashin samun ciki bayan mace ta haihu ko hayayyafa) yana faruwa ne lokacin da mace ta haihu sai kuma haihuwa ta zo ta ɗauke kwata kwata ayi ta nemanta ruwa a jallo amma bata samuwa wani lokacin har sai an dangana da asibiti. Mace a haihuwar farko ta san lafiyarta lau saboda ta samu ciki ba tare da neman taimakon likita ko shan magani ba, amma kuma daga nan sai haihuwar tayi ɓatan dabo.”

    Nan ma sai ta ɗan dakata kafin ta cigaba da faɗin.

    “Yawancin abubuwan da ke haifar da secondary infertility sun haɗa da low egg quality(wato kwan haihuwar mace ya kasance baida karfin haihuwar) matsalar mahaifa, matsalar rashin karfin maniyyi, yanayin abinci da wasu abubuwan wanda suka danganci rayuwar mace kama daga yanayin cututtuka da uwa uba Family Planning”

    Ta ɗan ɗago ta kalleni ganin ina kallonta sannan hankalina na kanta ya sa ta ɗan gyara zama gilashin ta sannan ta sake cigaba da faɗin.

    “Babban abunda ke kawo secondary infertility musamman a kasar hausa shine family planning wato tsarin iyali. Yawancin mata idan sunyi tsarin iyali yana haifar masu da matsaloli wanda cikin matsalolin nan babbansu shine sanadin family planning.
    Family planning na haifar da jinkirin rashin samu ciki da wuri saboda karfinshi da kuma aikin da yake a productive system na mace
    Kama daga hormones har zuwa Reproductive organs

    “Kuma kowani abu ya na da Siide effect, kuma shi planning yana ninka adadin shekarunsa sau ɗaya ma’ana zai iya haurawa da kashi ɗaya, wani lokacin har biyu, kamar ke ɗin nan kin yi na shekaru biyar amman ya haura ki har shekara tara ba ki haihu ba, sannan kafin ki samu ciki side effect ya taɓa ki kin ta samun matsaloli ko?
    Ba ta damu da na amsa ba ta cigaba da faɗin. > Janaftybaby: “Secondary infertility kuma mace ta taɓa haihuwa sai ta zo ta hanyar planning ko kuma haihuwar ta tsaya mata chak, shine za ta je asibiti ayi aune aune sai a bata maganin da zai dakile karfin planning din nan da kuma wanda zai taimaka mata wajen buɗe mahaifar ta da hormones ɗin don a samu cikin, kamar irin problem ɗin ki kin gane?

    Sai na gyaɗa mata kaina alamun gamsuwa. Tana mgana da hausa ta na haɗawa da turanci a maganarta kawai na fahimci ita ɗin kanuri ce saboda ba ta da hausa sosai.

    Fayel ɗina ta jawo ta fara rubutu kafin ta ce” Kafin mu kai ga ɗora ki kan mgani Akwai bukatar sai kin yi wasu gwaje gwaje kamar yadda tsarin mu ya ke.”

    Mintina sama da biyu sannan ta sake ɗagowa tana kallona kafin ta ce”

    “Muna da gwaje gwaje a kallah guda tara waɗanda sai kin yi su gabaɗaya ne za mu iya gano ta in da matsalar ki take, da kuma hanyar da zamu ɗora ki kan mgani.”

    Gwaje Gwajen da ake sun haɗa da

    1.A semen analysis (mace da namiji zasu tara, sai a tara sterile container a debi sperm din daidai lokaci da namiji ke kawowa, da gaggawa ake yin awon sbd kada sperm cells din su mutu kafin ayi awon wanda hakan zai iya lalata sakamakon da ake bukata a wannan awon ne ake gane cewa sperm din namiji na active zai iya haihuwa ko aa.
    2.Blood tests to look at hormone levels (zai nuna level din hormones, suna over secreting ne ko under secreting)
    3.A transvaginal ultrasound
    4.A hysterosalpingogram, a type of X-ray that allows your provider to see your uterus and fallopian tubes( wannan da x-ray machine ake yin shi,zai nuna cikin mahaifa da kyallemun mahaifa duka honestly speaking its painful)

    5.Blood tests. Samples of your blood can be tested for a hormone called progesterone to check whether you’re ovulating. …

    6.Chlamydia test. Chlamydia is an STI that can affect fertility

    7.Pap smears
    8.FSH follicle Stimulatiing Hormone
    9.LH Luteinizing Hormones
    All these are the most common primary and secondary fertility tests for women.”

    Ta na gama yi min bayanan ta miƙo mini takardan mai tambarin sunan asibitin a jiki, hannuna biyu na saka na karɓa ita kuma sai ta maida hankalinta a wajen system ɗin gabanta.

    “Ki je lab ki kai musu, za su yi miki cikakken bayanin a can”

    A sanyaye na ce” Yanzu Dr?

    “Yes. Ki je yanzu a can za su ƙara miki ƙarin bayani da yadda za a yi.”

    Sai na miƙe ina mata godiya.

    “Sai an baki result sai ki dawo mun da shi , on Monday ranar da zai ma ranar clinic ɗin ki.”

    Na yi mata godiya sai kawai ta gyaɗa kanta. Ina fita na nufi Yallaɓai ya na ganina ya taso, sai na bashi takardan ina faɗa masa yadda muka yi da ita sai ya ce mu je lab ɗin.

    Tare muka je lap ɗin amman shi bai shiga ba ni ce na shiga na ba su takardan, laboratory ɗin da ya karɓa ya duba takardan sai ya ce.

    “Muna bukatar ki zo da mijin ki “

    Haka ya ce mini wani ɗan baki ne, kai tsaye na ce” Tare mu ke yana waje.”
    Sai ya ce na je na shigo da shi, bayan mun dawo tare sun bamu wajen zama, sai wani lap tecnicial ɗin ya fara mana bayanin gwajin da za mu fara yi a matakin farko wato Semi analysis na sperm ɗina da na Yallaɓai.”

    “Ya za mu iya kawo muku samples ɗin?

    Yallaɓai ya tambaya sai ya kora mana jawabi a tsanake, yanzu dai ya ce za mu fara yin bucking ko gobe ko jibi za mu iya kawowa amman mu kawo shi cikin gaggawa.
    Kafin mu tafi sai da ya bamu sterile container ya ce mu yi amfani da shi, kafin mu baro asibitin har kuɗin test ɗin sai da muka biya suka samu takardan da cewar sai jibi in sha Allahu za mu kawo ya yi ta jadaddamana da kar mu ɓata lokaci ana son a yi awon da gaggawa ne.

    Mun fito daga asibitin muna hanya sai kawai na yi tunanin bari na tsaya a kasuwa na ƴan siyayya ta daga nan na tsaya in yi saloon kafin na koma gida.

    Nan take Yallaɓai ya tura mini 50k kuma ya ijiye ni a kasuwar Wambai.

    “Yanzu sai ina?

    Na faɗa ina ƙoƙarin buɗe motar na sauka bayan mun iso shagon da na ke zuwa gyaran kai kusa da kasuwar Wambai.

    “Office zan fara zuwa akwai mutanen da zan gani.”

    Sai da na fita sannan na leƙa ta window motar ina faɗin” Ka tura list ɗin ga babban shago saboda su kawo mana da wuri” > Janaftybaby: Sai ya gyaɗa min kai kafin ya ce” Kin tabbata ba abin da za a buƙata daga baya?
    Jin abin da ya ce ne ya sa sai na buɗe motar na sake shiga na karɓi wayarsa na dubo list ɗin da na tura masa.

    Kallonsa na yi kafin na ce” Ina jin su kenan. Amman za ka iya ce ko zai duba wancan list ɗin?

    “In ya na da shi ba”

    Ina ƴar dariya na ce” Ya na da shi mana. Ai suna ijiye rocord saboda babban shago ne.”

    Sai ya jinjina min kai kafin ya ce” ƙarfe nawa za ki koma gida?
    Ina gyara zaman mayafin jikina zuwa saman kaina na ce” Da na gama siyayya zan koma gida in sha Allahu”

    Hannuna ya riƙe ya sumbata kafin ya ce” Take care. Ki koma gida da wuri.”
    Ni kuma sai na sunkunya na sumbaci ƙuncinsa ina faɗin” Allah ya ba da sa’a.”

    Daga nan muka yi sallama ya sauke ni ya wuce, shagon wata Amesty ne anan na ke zuwa gyaran kai tun da daɗewa. Ina shiga ta na ganina ta tarɓeni saboda mun saba da juna har lambar wayar juna gare mu.

    “Hajiya zuwa ba waya?

    Ina zama kan ɗaya daga cikin kujerun dake cikin shagon na ce” Ba da niyyar zuwa na fito ba. Daga asibiti na muke sai kawai na ce Yallaɓai ya sauke ni anan, daman ina ta wa ƙen zuwa.”

    Yaran shagon na ta gaisheni, ina amsawa ita kuma sai ta je ta ɗauko min ruwa. Ba musulma ba ce amman in ka ganta sai ka rantse musulma ce hausa a bakinta kamar jakar Kano dressing ɗinta irin na hausawa ne.

    “Na gode.”

    Na faɗa lokacin da ta ba ni ruwa na karɓa na sha kaɗan saboda ina jin kishi. Amesty na zaune gefe na tana faɗin” Ina su Jidda kwana biyu? Ina Baby mai kuka.”

    Ina dariya na ce” Duk suna makaranta.”
    Saboda ba ko yaushe na ke yi musu gyaran kan ba, amma na fi kawo su lokacin salla ko biki saboda ba ni da lokaci tsayawa na yi musu.

    “Me za mu yi? Wankin kai ko Saloon?

    Sai na zare mayafina na tuɓe ɗankwalina na zame ina nuna mata kaina.

    “Saloon ko? Kamar wata biyu kenan ban yi ba.”
    Ta na dubawa sannan ta kalleni ta na faɗin” Gaskiya. Bari mu yi Saloon ɗin”

    Daman in dai na zo da kanta ta ke yi mini saɓanin sauran da yaran ta ke yi musu, ni kuma muna yi duk abin da na gani ina mata tambaya saboda ɓarayina ne, na iya wankin kai Saloon ɗin ma na iya, Amesty na dariya ta ce” Hajiya wannan shagon na Saloon sai yaushe za a buɗe shi?

    Nima ina mata dariyan na ce” Yallaɓai ya ce Soon in sha Allahu.”.
    Sai ta ce Allah ya nuna mana.

    Na yi awa ɗaya da wani abu a shagon Amesty, kafin a gama min Saloon kaina ya yi kyau. Ba ni da kuɗi a hannuna sai na ce zan tura mata ta banki in na koma gida da haka muka yi sallama ta rako ni har waje.

    Daga nan na samu Adaidaita zuwa cikin kasuwar Wambai akwai shagon da na ke siyan su bra da pant da kananun gajerun wanduna na yara nan na fara tsayawa na siya ma su Jidda pant da vest sai sikat na yara da ƙananun wanduna sai na siya ma Jidda da Baby dogayen wanduna baƙaƙe saboda makaranta. Har da safuna na siya musu farare da baƙake, nima na siya ma kaina pant da bra sannan na siya ma Marwa, daga nan na wuce shagon Musa mai kayan costimetic na siya irin su shampoo sai sabulin da su Jidda ke wanka, sannan na siya Veet da kayan wankin tiolet sai Moneyfresh saboda Mopping, na yi siyayya sosai na amfanin gidana har man kitso na siya mana. Saboda siyayya shago biyu ne kawai shi ya sa ban wani daɗe ba na dauki drop ɗin Adaidaita zuwa gida a ƙofar gida na ga Saude ta na jirana.

    “Shi ne ba za ki kirani ba?! In ban dawo da wuri ba fa.”

    Kanta na ƙasa ta ce” Na kira ki ba ki ɗauka ba. Yanzu na zo fa daman.”

    Sai da ta ce ta kirani sannan na tuna wayata na can cikin jaka, key na saka na buɗe gidan Saude ta taya ni ɗaukan kayan zuwa cikin gida duk na ji na gaji, ga cikina kamar an yi yasa kamar ban karya ba kafin na fita sai da na haɗa tea na sake sha sannan na dawo dai dai.

    Sai da na natsu sannan na kira Farida na yi mata ban gajiya da yadda suka koma gida. Sannan sai na kira Amina ba ta ɗauka ba sai na kira Khaleesat itama na yi mata ya hanya. Lailan ma Yaya Auwal mun yi mgana da ita. > Janaftybaby: Da rana tuwo na yi tun da shinkar tuwon kaɗai ya rage mana. Saude sai wajen uku na rana na bata kuɗin mota ta tafi gida, ni kaɗai a gidan jin an kira sallar la’asar sai na yi sallah sannan na kira Yallaɓai nan ya ke faɗa mini ya na Rano ya je duba aiki. Ni kuma daman na manta ne ban faɗa masa mganar a saka drinks ɗin yara na makaranta ba da kayan kamshin girki tun da shagon babba ne a can kasuwar Singer ba abin ba sa saidawa.

    “Ai na tura masa na ce kuma ya saka duk abin da ya kamata.”

    Sai na ce ya dai sake kiran shi ya faɗa masa sai a manta wani abun sai ya ce to.

    Sai shidda saura su Jidda su ka dawo, na so na yi wanki gajiya ya sa sai na ce bari na bari zuwa gobe sai na yi wankin.

    Sai wajen tara na dare Yallaɓai ya dawo gidan yana tambaya ta ba a kawo kayan abinci ba? Na ce ba su kawo ba nan ta ke ya sake kiran shi manager ɗin sai ya ce a ba’ a gama haɗa kayan ba ne sai zuwa da safe in sha Allahu.

    Da wuri muka kwanta su Jidda daman ko da Yallaɓai ya dawo sun kwanta. Ina kwance a saman ƙirjinsa sai na kira sunan shi.

    “Yallaɓai.”

    “Uhm”

    “Ba ka ga Saloon ɗina ba ne”

    “Na gani mana”

    Ya faɗa ya na ƴar dariya duk da ba na ganin fuskar shi amman ina jin sautin dariyan shi.

    Baki na tura kafin na ce” Shi ne ko ka ce ya yi kyau?

    Hannunsa ya kai ya zare mini hulan kaina ya na mai tura hannun shi a cikin gashin sannan ya kai hancinsa ya shinshina ya kuma sumbata da baki kafin ya ce” Kina da gajen hakuri. So na ke yi daman na baki kyakyawan tuƙwaici.”

    Na ga ko kyakyawan tuƙwaici a daran nan sai da Yallaɓai ya saka ni jiƙa kai gabaɗaya kamshin Saloon ya bi ruwa ina tura baki na ce” Yallaɓai wannan tuƙwaicin naka ban yi maraba da shi ba.”

    Yana min dariya ya ce” Saboda mene?
    Hararan shi kawai, na haye gado na shige cikin bargo ina tura baki, sai da ya tsane kanshi da danshin ruwa sannan ya hayo gadon ya na min dariya ni ko ko busar da kan ban samu na yi ba na dai tsane shi da towel.

    Har da asuba sai da ya ƙara jiƙa mini kai, lamarin yallaɓai ya ishe ni har sai da na tsare shi ina masa tambayoyi.

    “Yallaɓai ka faɗa mini gaskiya me kake sha ne a bayan ido na?

    Na faɗa ina mai tsare sa da ido. Muna dining ne bayan mun gama karyawa su jidda sun tafi makaranta.

    Wani kallo ya yi mini na bangane ba kafin ya ce” Kamar na me fa?
    Ina haɗe rai na ce” Ko ka siya manpower ne ka fara sha a ɓoye ban sani ba?

    Sai ya buɗe baki yana kallona kafin ya rufe ya na dariya. Ni ko ban yi dariya na tsare shi da ido ina faɗin” To Yallaɓai gwara na sani. Kana samu ɓarnan ruwa da yawa yanzu.”

    Haɓa ya riƙe kafin ya ce” Fisabillahi Sadiya kamar ni na yi lalacewan da sai na sha wani abu za mu yi barnan ruwa?

    Kai na kaɗa kafin na ce” shi ne na ke tambaya.”
    Miƙewa ya yi a kaina sai da ya yi mika sannan ya sunkuya dai dai kunnina na dama kafin ya ce.”

    “Ke ba ki san muna girma ba ne muna ƙara sanin daɗin abin da darajarsa ba”

    Kallonsa na yi sai ya dage mini gira kafin na samu zarafin mgana ya sumbaci wuyana da sauri na ture shi na miƙe ina hararanshi.

    “Miye haka?

    Saboda na ga ya na ƙokarin riƙo ni kuma yana min wani kallon ƙasa ƙasa.

    “Allah zan busar miki da gashin da kaina.”
    Ya faɗa ya na ƙokarin jawo ni ai da sauri na warce na fara zagayen dining ɗin ina faɗin” Bar shi kawai na yafe. Ina da hannu”
    Shima sai ya fara bi na ya na faɗin” Kai Sadiya ta. Guduna kike yi yau kuma?

    Ya faɗa har yana marairaicewa. Na san halin shi cikin sauri na ce” E wallahi yau na guje ka.”
    Dariya ya yi min ni ko na haɗe rai, haka muka dinga zagayen falon nan daga karshe na fice da gudu zuwa bedroom ɗin ina shiga kafin na rufe ƙofa ya cimmin karfi ba daya ba turani ya yi kan gado ya biyo bayana ya na faɗin” Duk wayon Amarya dai.”
    Ina ture shi ko gizau sai ya fara min cakulkuli ina ta dariya kamar zan mutu ina faɗin” Yallaɓai cikina don Allah ka bari.”

    Sai da ya ga numfashina na sama sannan ya kyaleni ya na faɗin” Gobe dai dole ki bari na yi shagalina tunda kin ga asibiti na bukatar samples.” > Janaftybaby: Ko mgana ban yi mishi ba ina maida numfashi shima sai ya yi rigingine ya na nishi, ina ganin haka na lallaba na haye kanshi na fara masa cakulkuli da ƙarfi tun yana daurewa har ya fara dariya yana hantsila kafa, karshenta dai muka yi biji biji da gadon fililluka duk a kasa in ya yi min cakulkuli nima na yi masa daga haraba ma za a iya jiyo dariyan mu.
    Har sai da muka gaji sannan muka koma muka kwanta muna hutawa.

    Karfe sha ɗaya Yallabai ya yi wanka ya fita ya ce zai je Gwammaja ne daga can zai ta fi office ya fita ba daɗewa Saude ta zo ita na bari da gyaran gida na kwaso under ɗin yallabai da nawa sai kayan barcin mu na fita can in da muke wanki na kafa kujera kayan ba su da yawa kuma ba su yi wani datti ba cikin lokaci na gama na shanya na saka abin matse shanya na kama dasu.

    Bayana sai da ya riƙe ina gamawa na yi wanka da ruwa mai zafi, sannan na gyara bedroom ɗin da muka yi kaca kaca dashi ni da Yallaɓai. Ina da sauran fulawa sai na tura Saude kasuwar ƴan kaba ta siyo min kayan miya har da kabeji, ƙuli kuma daman ina da sauran shi sai dai bai da yawa ne. Da ya ke ina son gurasa to ina yi da kaina lokaci bayan lokaci.

    Gurasa na yi mana. Ita kuma Saude ta niƙa min sauran kayan miyan a blander na saka su a cikin fridge bayan ta ci na saka mata guda uku a leda na ce ta tafi da shi gida. Da safen daman Yallaɓai ya yi mganar albashinta daman mu da kan mu mun kan je gidansu hannu da hannu mu ba ma mahaifiyarta haka tsarin ya ke, sai na ce mata ƙila mu shigo zuwa dare.

    Su Jidda suna dawowa su ka ga gurasa na yi suna ta tsallen murna. Kayan abinci ko sai bayan mangariba suka kawo mana. Yallaɓai baya nan dole su suka kwaso su zuwa cikin gida. Ma sha Allah na furta a raina komai an kawo har da su maclean da kayan maggi, ni da Jidda muka gyara komai a muhallinsa na Nene kuma na cire mata nata kayan Tea ne sai sabulan wanka da na wanki sai katan ɗin taliya da maracroni sai coouscous, tun da ta na so, shi ma saboda ya saba siya mata duk wata ne a matsayinsa na Namiji amman abincin gidan gabaɗaya yana Wuyan Yaya Usman ne gaskiya duk da sauran duk suna yi, matan ma kowacce tana iya bakin ƙokarinta. Kayan tea ɗin ma gida uku ne Nene da Hajiya Iya sai Maman farko.

    Da Yallaɓai ya dawo sai na nuna masa ya kalleni kafin ya ce” Ba matsala dai ko?
    Sai na rumgumeshi ina faɗin” Ba matsala mun gode Yallaɓai Allah ya ƙara buɗi da wadata.”
    Sai shima ya riƙe ni yana amswa da Amin Amin. Ni nasan na yi dacen miji, in dai Yallaɓai ya na dashi ba zan taɓa neman wani abu na rasa ba.

    A daran muka fita mu ka je Gwammaja mu ka kaima Nene nata ya ƙara mata da 20k tana ta saka albarka farko ma ta ce ba za ta amsa ba ni na ce ta karɓa.
    Sai ta saka hannu ta karɓa tana faɗin” Komai fa suna yi min Sadiya to kuɗin kuma na mene ne?
    Ina mirmishi na ce” ki rike a hannun ki Nene kina yin baki da ga Rano ko na sallamansu kya samu.”

    “Haka ne. Na gode Allah ya yi albarka”

    Muka amsa da Amin Amin muna gidan sai ga Mimisco(Anty Zuwaira) ita da mijinta itama kayan abincin ta zo da shi da kayan tea, sai mganar zuwa ganin likita ga Nene, tunda nauyin asibitin na ta Mimisco ce ta ce a bar mata za ta iya.

    Mun gaisa da ita kamar yadda muka saba ni dai ban taɓa samun matsala da ita ba. Tana da ilmi ta kuma san yadda za ta zauna da jama’a. Saboda zuwanta ya sa muka ɓata lokaci tunda Yallaɓai suna ta hira da mijinta. Sai wajen tara da rabi muka baro gidan bayan Yallaɓai duk ya shiga ɗakunan su Hajiya Iya ya ba su 10k kowacce suka karɓa suna godiya a hanya ne ma da za mu je Ɗorayi Yallabai ke faɗa, min Yaya Usman ya shigo garin jiya amman bai kwana ba ya koma a ranar.

    “To. Ya zo biko ne?

    Hankalinsa na wajen tuƙi ya ce” Ban sani ba. Na san dai ba zai rasa zuwa gidan su ba.”
    Sai na jinjina kai kafin na ce” Hmm. Allah ya kyauta.”.
    Saboda ina so na yi magana ina tsoron kar Yallaɓai ya taso min shi mai ɗan uwa. > Janaftybaby: Mun fara zuwa gidanmu muka sake duba Alhaji 20k Yallaɓai ya ba ma Alhajinmu. Gwaggo kuma 10k suna ta saka albarka. A bakin Gwaggo na ji labarin yau da safe Baaba ta koma na ce Allah ya tsare. Daganan mun shiga gidan su Saude 50k Yallabai ya ba ma Balaraba daman a wata 30k kuɗin aikinta amman Yallaɓai na yi musu ihsani kuma kafim mu baro gidan sai da ya yi mganar ya na so ya saka Saude a makaranta bai da ce a barta haka ba karatun boko ba, ta gama firamari ba ta cigaba ba. Mahaifiyarta har da hawaye tana ta godiya zaman amana ne da maƙotaka ya haɗamu har na ga Saude na ce ta riƙa zuwa tana kama min aiki saboda na taimaka musu.

    Daga gidan su Saude gida muka dawo tun da daman mun yi sallama da su Gwaggo muna hanya Yallaɓai ya ce na tura mai acct number Datti zai saka masa wani abu ina ta masa godiya.

    “Tsakanin mu ba Godiya Sadiya ta.”

    Haka ya faɗa ya na kallona ni kuma sai na yi masa mirnishi kafin na ce” Duk da haka dai zan gode maka. Yallaɓaina Allah ya sa a fi haka.”
    Sai ya amsa min da Amin muna yi ma juna mirmishi.

    *

    Washegari da sasaafe, bayan Yallaɓai ya ja mun yi ta barnar ruwa ni dai ai nace dole zan kira mai kitso kafin Yallaɓai ya sa gashina ya sauke ƙasa saboda jiƙashi da na ke da ruwa.
    Sai bayan su Jidda sun tafi makaranta a gurguje muka yi abin da aka umarcemu mu kawo daga Lab. Saboda yadda ya jadaddamana cikin sauri muka yi wanka Yallaɓai ya kai ni asibitin na kai musu da sauri suka karɓa bayan na haɗa musu da takardan da suka ba ni shekaranjiya. Suna karɓa suka ce mu jira a waje za su ba mu result ɗin.
    Tare da Yallaɓai muka yi zaman jira ana ta kiran shi ma a office bai tafi ba sai da aka gama test ɗin suka kuma bamu result ɗin da cewa zan kaima likita ranar clinic ɗina.
    Daga nan Yallaɓai ya dawo da ni gida ya ijiye shi kuma ya wuce office domin ya faɗa mini akwai kwangilan da ya samu na zanen wani kamfani da za a buɗe a kaduna ne. Na bishi da Allah ya ba da sa’a shi ya wuce ni kuma na buɗe gida na shiga.

    Ban san me result ɗin ya nuna ba tunda rubutun likitoci sai su sai na adata kafin ranar Monday. Ranar yini na yi gugan kayan under ɗin mu da na wanke mana na goge su tas na feshe da turare, na jera mana a cikin wardrope, ganin na samu natsuwa ya sa na ɗau wayata na kira Aisha lame na yi mata mganar ina son Body lotion, sau Face soap sai Fade cream sai showergel na wanka

    Sai ta ce mini za a kawo mini sai na ce kamar yadda muka saba zan tura mata kuɗin ta, Aisha Lame ba abin da ba ta saidawa na gyaran jikin mata. Kuma kayan ta suna da kyau da inganci su na ke amfani dashi shi ya sa kullum Yallaɓai sai ya ce ya na son taɓa fuskata saboda taushi da santsi sannan ba guraje, jikina kuma ya yi fresh ya yi taushi domin Showe gel ɗin ta ba baya ba yana bala’in gyara fata.

    Tana aikawa da kayanta ko’ina a faɗin Nigeria

    Daga ita sai na kira Surayya Dee mai kayan gyara na BOJUWA ta dalilin Aisha lame na san Surayya. Kuma na yi amfani da kayanta na yaɓa da ingancinsu.

    Ni duk bayan wata uku na ke shan mganin sanyi sannan na ɗora da na gyara Ni macece da ta yarda da gyara shi ne har gobe ya sa na ke da matsayi a zuciyar Yallaɓai. Duk da har kayan marmari ba na wasa da su da duk abin da zai kawo mini Ni’ima amman kuma ban zauna ba ina gyaran jikina tare da can ainihin majalisar ɗinkin duniyan gabaɗaya.
    Maganin infection na ce ina so Surayya ta aiko minibda shi in na gama zan siya kazan uwargida tana ta dariya ta ce” Hajiyar Injiniya ba a dai gajiya da gyara.”

    Nima ina dariyan na ce” Ba a gajiya Hajiya Surayya. Gyara shi ne mace da gyaran ya sa har gobe muke ƙyalli a idanuwan mazajen mu.”

    Tana ta dariya mun rabu akan yau ɗin nan mai kawo mata kaya zai kawo mini tun da ya san gidana, tun da ba yau muke tare ba, sama da shekara ɗaya tun da na gwada kayanta na san ingancin su.
    Domin ke ma ki dace da ingantattun kayan gyara contact Surayya Halin yau on
    +234 803 277. Kano Nigeria tana aikawa da kayanta ko’ina. > Janaftybaby: Zuwa yamma sai ga saƙon Surayya Halin yau, a daran kuma na tura mata har kudin kazar da zan siya. Mayuka na bangaren Aisha lame kuma sai washegari da safe ta aiko mini dashi.

    Ranar jumma’a gidan Rahila muka yini ni da su Jidda, Rahilar ba ta da lafiya zazzaɓi daga ita har Bbyn na ta sai dare Yallabai ya je ya dauko mu, mun sha hira mun yi tsiya mun yi daɗi ta ji sauƙi tun da har kitso sai da ta yi mini daman ta iya ta rufa mini asiri kafin Yallaɓai ya saka ruwa ya sauke mini gashi.
    mun rabu da Rahila ta roƙe ni ƙanwar mijin Ma’u za ta yi aure za ta biyo mini mu je tare kai tsaye na ce” In ta gayyace ni ba? In ba ta gayyace ni ba wallahi ba zan je gayyar soɗi ba.”

    Rahila na dariya ta ce” Ki ji tsoron Allah Sadiya. Ke yanzu sai kin jira Ma’u ta gayyace ki.”
    Ina hararanta na ce”Kwarai kuwa. Kawai tusa kai ba kwarjini in ta gaya min zan iya zuwa amman ba ta gaya mini ba sai dai na ce a sha biki lafiya.”

    Washegarin asabar kamar ta san mun yi maaganar da Rahila sai ga shi ta tura mini katin biki sannan daga baya ta kirani.

    “Ina fatan za ki zo dai zo ko Sadiya?

    Sai na ce mata in sha Allahu tun da sati na sama ne.

    **
    Ranar Monday, na koma asibiti na ga Dr Aisha bayan na ba ta sakamakon ta duba cikin ikon Allah ta ce da ga ni har Yallaɓai sperm din mu suna active matsalan ba daga nan ba ne yanzu tun da an yi wannan an tabbatar da ba matsala za su yi focusing a kaina ne.

    Sai ta rubuta mini blood tests to look hormone levels. Na je na kai lap aka ɗibi jinina suka ce na dawo nan da kwana biyu domin karɓan result. Tun ina hanya na kira Yallabai na faɗa masa likita tace matakin farko ba matsala yanzu dai sauran gwaje gwajen akai na ne.

    “Alhamdulillah. Suma sauran in sha Allahu ba matsala.”

    “In sha Allahu.”
    Na amsa masa cike da yaƙinin hakan

    A satin Hauwa ta zo gida na ta yini ita da yara a bakin ta na ke jin Anty Zabba ta koma amman sai bayan Yaya Usman ya koma ni ko sai na ce” Ya fi mata. Amma ba ta gina gidanta ta bar ma wata shi saboda kishi ba.”

    Sai dare Muttaƙa ya zo ya dauke su.
    Washegari gidan Halima na je na kai mata Atamfar da na da siya mata a Dija collection+234
    Domin kayanta ta na ba da su ne akan farashi sari mai sauƙi.
    Sai na siya rigar yaro ssi pampers da na je sai na ɗora mata 5k na ce nawa ne kuɗin kayan kuma daga Yallaɓai ne tana ta godiya a gabana ma ta kira shi tana yi masa godiya ya ce ba komai.

    Ina shirin tafiya sai ga Anty Bahijja wai sun zo nan kusa ne ganin gidan da ƙanwar mijin Ma’u za ta zauna shi ne ta biyo wajen Halima. Da gangan na yi ma Anty Bahijja taɗin bikin ina dariya na ce.

    “Anty Bahijja ashe biki gare ku ba gayyata.”

    Sai ta kalleni kafin ta ce” Ba ni ya kamata na gayyace ki ba Ma’u ce.”
    Ina mirmishi na ce” Ai fa ta gayyace mu muna nan zuwa.”

    Na ga ta kalleni da mamaki amman sai ta shanye ta ce sai mun zo ni dai anan na barta na koma gida da wuri saboda yara.

    Ranar asabar da wuri na shirya daman na faɗa ma Yallabai tun kwanaki ya ce ya ba ni izini. Shi na bar ma yara a gida na ce in zai fita ya kai su Gwammaja wajen Nene, ni kuma Rahila ta kirani ta ce wai mu a haɗu a Ɗorayi ni kuma na ce ba zan koma baya ba tun da na san gida yayar mijin Ma’un ta taɓa rasuwa muka je gaisuwa na san iyayin Yaya Murja ce za ta ce a haɗu a gida a tafi gabaɗaya tun safe Rahila ke kirana nace ina dalili su yi gaba sai azahar zan taho.

    Ban ma samu zuwa ba sai bayan azahar ganin na yi rana kawai Yallaɓai ya ce na jira mu fita tare shima Alhaji Mustapha ya gayyace shi ɗaurin aure sai da muka kai su Jidda Gwammaja sannan muka wuce Maitama in da gidan iyayen mijin Ma’u suke, ko da na je su Rahila sun jima da tsufa da zuwa Ma’u har da rumgumeni can na ga su Anty Bahijja Hajiya sama Hajiya ƙasa tun da mijinta shine babba a ɗakin ita mahaifiyar Alhaji Mustapha kuma suna ji da shi, shi ya sa ita ke faɗa aji, ina ta mamakin yadda take ba da umarni a dangin mijinta an ce so so ne amman son kai yafi ita ta samu dama tana yadda ta ga dama amman idanuwanta na kan wasu kar su ji daɗi a gidan mijinsu sannan kar su zama masu faɗi a cika a dangi amman ita gashi tana yarda ta ga dama.

    *TURKEN GIDA.*

    KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.*
    07045308523.

    *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE*

    Note
    error: Content is protected !!