Turken Gida – Chapter Six
by JanaftyPresent.
Da safen tea muka sha gabaɗayan mu amman ban da Yallaɓai saboda kamar akwai gajiya a tare dashi. Tun bayan da ya dawo daga sallar asuba ya kwanta yana ta barci sai na ƙyale shi tun da na ga har wayarsa ma sai da ya kashe.
Da wuri Saude ta zo na saka Jidda ta fito da kayan na su. Daga kitchen ɗina akwai wata kofa dake fidda mutum ta can baya in da muke yin wanki ko shanya. Ko tara ruwan sama can na ce su je su yi wankin har da Baby da ta saka rigiman sai ta yi na ce a ƙyaleta ta yi.
“Umma ba fa wanki ta iya ba. Ɓata jikinta kawai za ta yi da ruwa.”
Ina ɗakin na su ne a lokacin ina gyarawa saboda Saude ba za ta samu lokaci ba gwara ni na gyara gidan.
Kallon jidda na yi da ta shigo kawo min karan Baby.
“Bar ta yi. In ta jiƙa jikinta ai shike nan ta huta.”
Haka na faɗa ina mirmishi saboda ni dai na san ina kamar ta ban so aiki ba amman tunda tana so ai ba zan hana ta ba. Wucewa Jidda ta yi amman ranta bai so ba sai na bi ta da kallo ina dariya.
Jidda akwai son aiki da karambani in da ta biyo ni da na shiga uku. Har yanzu da shekaru suka tura ba na son aiki barin ma girki, ko anan domin ya zame mini dole ne na ga ba mai yi mini. Saude daman in ta zo sai dai na saka ta yi ma yara. In da Allah ya so ni da Rahama Yallaɓaina bai da tsirfan cewa ga abin da zai ci duk abin da na kwaɓa na bashi yana maraba.
A baya kafin na samu Saude na wahala sai dai in Marwa ta zo mini hutu. Marwa babbar ɗiyar Yaya Aina ce. Lokacin da ta ke gida kafin ta samu makarantar koyin aikin jinya a garin tsafe na more ta saboda yarinyar tana matuƙar sona. Shi ya sa nima na ke son ta ina kuma kyautata mata. Ba ta zuwa gidan kowa hutu sai gidana in ta zo ba na komai sai dai na ci na kwanta Yallaɓai ya yi ta mini tsiyan daman haka na ke so na kwanta na yi ta laushi ni kuma na ce na ji ba komai.
Marwa ba ta da ƙiyuwa. In ta zo har wankin kayana da guguna tana yi min kayan su Jidda sai dai na fito na ga ta wanke ta shanya, budurwa ce mai kimanin shekaru 20 zuwa da ɗaya.
Duk da ni da uwarta ba sosai muke yi ba amman kuma Allah ya haɗa jinina da Marwa kuma ina daraja haka saboda yaran Yaya Murja ba sa zuwa gida na amman gidan Ma’u kam suna zuwa mata hutu. Har gwarama Firdausi ta wajen Yaya Balki ta kan zo wajena ban da su Anti. (Aina) sunan Yaya Aina a ka sanya mata sai ake kiran ta da Anti ita ce babba a ɗakin Yaya Murja ƙannenta huɗu duk maza ne. Ni bai dame ni ba domin kowa ya san halina ka yi da ni, ya ka ƙare ballantana ma ba ka yi da ni ma gabaɗaya.
Allah na tuba gari da yawa ai maye ba ya ci kansa ba shi ya sa ina yi ma Marwa abin alheri har ɗinkuna ina yi mata lokacin da ta samu makaranta tsafe siyayya na yi mata mai yawa kuma har da ni a masu rakata, sannan in dai ta zo gida hutu ko da ba za ta daɗe ba sai ta zo gidana ba ta daɗe ba ta yi mini sati ɗaya. Sau tari in zan siya abin mata na kwalliya uku na kan siya saboda Marwa. Ita tunda ta fara amfani da su bra da pad in dai na fita kasuwa siyayya ina siya mata na ijiye in ta zo hutu ko ba ta zo gidana ba ina aika mata dashi na ce Yaya Aina ta iijiye mata. Ban taɓa jin na damu da ta gode mini ba koma me na yi nima ai uwar Marwa na ke, kuma abin da ke tsakanina da mahaifiyarta ba zai taɓa shafanta ba. > Janaftybaby: Ko kafin in gama gyara gidan har sun gama wankin duk da bai da wani yawa daga uniforms ɗin su sai kayan barcin su. Ko daman ita Saude akwai ƙokari a shekaru iyakarta 17 ko ta gota da kaɗan ne. Na ɗan taya su shanya wajen sharce kayan. Bayan mun gama na ce Saude ta yi ma Baby tsifa ita ma Jidda ta kwance kan ta in wanke musu. Tun da ba su samu zuwa kitso ba sai in yi musu da kaina.
In kana da ƴa’ƴa mata koyon kitso ba zai zama wani abu mai wahala ba. Kuma daman ina da mai kitson tun ta can anguwan dakata da muka ta so bayan mun dawo nan tana zuwa gida ta yi mana ina biyanta ranar da kuma ba ta samu zuwa ba na kan kira Salisu ne ya zo ya ɗauki su Jidda ya kai su. wani lokacin in ta gama yi musu kitson yarta ke dawomin da su ranar da ba su samu zuwa ba na yi musu da kaina tun ban ƙware ba har ba ƙware kaɗan kaɗan.
Da na so sai la’asar zan je gida amman sai Amina ta sake kirana tana faɗa mini duk yau Yaya Hamza da Yaya Auwal za su koma sai na yi tunanin na tafi bayan azahar.
Yallaɓai bai tashi ba sai da na gaji har wajen sha ɗaya saura bayan na wanke tiolet na jiƙo hannuna na zo na tura masa a cikin ƙirjinsa da sauri ya buɗe ido sai a cikin idanuwana.
Ɗan ɓata rai ya yi irin na masu barci ni kuma sai na yi masa mirmishi.
“Yallaɓai a tashi haka nan. Kalli fa rana ta yi.”
Na faɗa ina buɗe masa labulen window ɗin bedroom din. Ai sai ya kauda kai har ya na juyawa zai cigaba da kwanciya.
“Yallabai. Haba mana”
Na faɗa cikin yar shagwaɓa amman sai ƙara shigewa da kansa ya yi cikin bargo lokaci ɗaya cikin shaƙewar murya cike da barci ya ce.
“Sai azahar za ki tashe ni. Kin ji”.
Ya faɗa ya wani ƙara sakin numfashi sai na saki baki kawai ina kallon shi na buɗe baki in yi mgana wayata dake kan dressing mirro ta ɗau kiɗa alamun kira sai na bar wajensa na isa wajen wayar.
“FaridaAisha.”
Faridan Tariq ce. Haka na faɗa a fili kafin na juya ina kallon Yallaɓai lokaci ɗaya ina faɗin” Ka gani ko? Ƙila ma Tariq ke neman ka ka kama ka kashe waya kamar wanda ya kwana aikin gajiya.”
Na san ya na jina amman bai yi motsi ba sai ni ce na taka zuwa gefen gado na zauna sannan na ɗaga kiran
“Maman biyu.”
Daga can bangaren ta ce”Matar injiniya.”
Da fara’a muka gaisa sai ta ke ga ya min sun shigo garin ita da Tariq suna Gwammaja suna son ƙarisowa gidanmu amma an kira wayar Yallaɓan nawa a kashe
Da sauri na ce”Yau hutu ya ke ji tun da ya dawo sallar asuba ya kashe wayarsa. Amman ai yanzu yana jin mu. Za ku samu ƙariwan kuwa?
“E. Amman a tsaye gaskiya saboda daga nan sai kaduna in sha Allahu “
Ina buɗe baki kamar ta na ganina na ce”Kai. Yau kuma! Ba ku bari zuwa gobe?
Tana yar dariya ta ce”Mai gayya ne ya ce yau za mu tafi”
Ina dariya na ce”kuma an gama mgana ba.”
Sallama muka yi ta ce suna tafe. Muna gama wayar na juya ina kallon Yallaɓai amman bai tashi ba sai na miƙe ina faɗin” Yallaɓai ga su Tariq nan da iyalansa don Allah ka tashi ka yi wanka ka ƙarya kafin su kariso”
Dakyar da soɗin goshi na samu Yallaɓai ya tashi. Hararan shi na yi lokacin da na ga ya miƙe ya na miƙa.
“Gajiyar duk ta mene ne?
Sai da ya sargafo hannayensa ta saman wuyana muna kallon juna kafin ya ce” To kuma me ye na tambaya? Duk tsawon gajiyar da kika tara min ne na wannan watan na ke safkewa”
Ya ƙarishe yana ɗage mini gira. Ture hannun shi na yi daga kafaɗata na wuce ina faɗin” Ni ban ce ka tara min gajiya ba sai kai?
“To ke wani ƙokari kike yi ban da abin ki. Ni ke fa aikin.”
Ya faɗa yana biyo bayana. Juyawa na yi muka haɗa ido kafin na yi masa wani kallo sai kawai ya fara dariya ni kuma sai na rausayar da kai lokaci ɗaya ina faɗin”
“Au! Haka ka ce ko?
Na nuna shi da yatsa kafin na cigaba da faɗin” Kai nan har wani ƙokari gare ka? Ba domin ni ba Yallaɓai uhmm.”
Na faɗa ina cije baki. Yana dariya ya ce” Sadiya ki ji tsoron Allah.”
Na juya zan fita ina faɗin” Za mu haɗu ne anjuma zamu ga mai ƙokari da mara ƙokari “
Ta baya ya rumgumeni yana faɗin” Just a good morning Hug.” > Janaftybaby: Dakyar na tura shi Tiolet ya yi wanka kafin ya fito na soya masa yar sauran doyan da ta rage sannan na dafa masa ruwan tea mai haɗin kayan shayi. Ƙananun kaya ya saka tunda yau ya na gida a saman dining na zauna har sai da ya gama karyawa.
“Yallaɓai daga yau in dafa sauran shinkafar nan komai namu ya ƙare na kayan abinci.”
Na faɗa ina kokarin tattara kayan da ya yi amfani da shi.
“Kafin Anjuma ɗin Allah zai kawo mafita. In sha Allahu.”
“Allah ya sa.”
Haka na amsa ina mai fita daga falon zuwa kitchen. Na leka su Saude na ga Baby tana hawaye ana mata tsifa daman ita akwai zafin kai ita dai Jidda har ta tsife nata.
Ina dariya na ce”Baby ki bari a yi tsifa an juma Babanki ya ce zai si yo miki ice cream kin ji?
Jin haka yasa ta washe baki. Sai na ce to a daina kuka in ta na son shan Ice cream. Fita na yi daga ɗakin na rufo musu kofa duk da na yi wanka ina bukatar na ƙara tun da tun safe ne.
Ina wanka su Farida suka iso domin na ji lokacin da Yallaɓai ya fita ya buɗe musu get Tariq ya shigo da motarsa shi ya sa a gurguje na gama wanka na fito na shirya na saka riga da sikat na wani material sai ga Yallaɓai ya shigo.
“Ke sun fa ce suna kan hanya ne.”
“Ga ni nan zuwa Sorry.”
Sai ya juya ya fita ya na faɗn” Ki taho musu da ruwa.”
Sai na amsa da to. Mayafi na saka na rufe jikina sannan na biya ta kitchen na ɗauko musu ruwan gora a fridge da kofuna guda biyu bayan na saka a faranti.
Ina shiga falon Farida ta zo ta tarbeni. Falon ya yi albarka Baby ta ga yan biyu sai wasa suke yi, ƙila babansu ya kira su su gaida baban na su, Jidda ba ta falon tabbacin ta koma ciki.
“Sannun ku da zuwa.”
Na faɗa ina sauke ruwan saman center table ɗin da ke gaban Yallaɓai da Tariq.
“Yauwa Sadiyar Yallaɓai. Ai ina nan ina masa tsiyan yau ko ba ya so mu ganki ne ya ɓoye ki?
Ina dariya na zauna a kujeran kusa da Farida.
“Haba dai ko ɗaya. Ina wanka ne lokacin da kuka shigo.”
Tariq ya jinjina kai kafin ya ce” yan hutu. Shi ma ai yanzu ya ke faɗa mini bai daɗe da tashi barci ba.”
“Shi ne ɗan hutu. Amman ni tun asuba ban koma ba.”
Farida na hararan mijinta ta ce” Shima ɗin ya na fin haka ma yana barci.”
Yallaɓai ya ce” to daman mana. Ni da suka raina ne suka saka mini ido shi da kawunsa Abba.”
Tariq na dariya ya ce” Tafida yarinyar nan fa ta kirani. Ni dai kawun ka ya kusa kashe min aure. Madam fa ta ƙi yarda da rantsuwata shi ya sa na matsa mu zo ga ka ga Sadiya ƙila tafi yarda da mganar ku.”
Ina dariya Yallaɓai na dariya Farida ce ta haɗe rai kafin ta ce” To na sani ko sabuwar budurwa ya yi. Kira kan kira”
Ina dariya ne amman ina auna wawancin Shema’u kina mace ki zama mai arha haka! Amman tuna wacece ita sai ban yi mamaki ba.
“Maman biyu kar ki yarda. Tabbas ni ma kwanaki nan ban gane masa ba duk yadda aka yi ya fara neman aure a boye.”
Yallaɓai ya faɗa ya na haɗe ai sai Tariq ya kasa magana amman ya buɗe baki.
“Uhm. To Allah ya ba shi sa’a.”
Farida ta faɗa kai tsaye ganin ta ɗan shaka sai na karɓi mganar ina faɗin” ƙyale Yallabai.’
Nan na faɗa mata abin da ya faru a jiya duk da ta na nuna ba ta damu ni na san ta damu.
“Ku kam ba abokan rufin asiri ba ne. Daga kai har tazurin kawun ka.”
Tariq ya faɗa yana ture hannun Yusuf dake saman kafaɗansa.
Farida na dariya tana bamu labarin sun je gaida innayi sun haɗu da Uncle Abba shima dai tuburewa ya yi da bai san zencen ba shima Yusuf ga abin da ya ce.
“Ai gaskiya ne. Mu ba mu san yadda aka haihu a ragaya ba.”
Yallaɓai ya faɗa yana dariya sai Tariq ya miƙe ya na fadin” Madam lokacin mu ya ƙare anan fa.”
Itama sai ta miƙe tana rataya jakarta.
Dukkanmu sai muka miƙe gabaɗaya ina faɗin daga zuwa sai tafiya.
“To ai zuwan daman na a gaisa ne. Muna nan muna jiran ku ke da Yallaban na ki dai.”
“In sha Allahu.”
Na faɗa, muka bi su har waje ina yi ma yan biyu wasa. Kamar na sani na sako yar dubu ɗaya daga ɗaki shi na bama yaran ganin Farida ta zo ma da su Jidda bickit mai yawa.
Sun shiga mota ina bangaren Farida ina yi mata sallama. Yallaɓai kuma suna bakin motar shi da Tariq suna mgana.
“Man sai yaushe kenan? > Janaftybaby: Tariq ya buɗe mota ya shiga lokaci ɗaya ya na faɗin” Ai ni ƙila sai ranar da tuzurin kawun ka ya samu matar aure in za mu je tambaya sai na shigo.”
Dariya suka yi har suna tafawa.
Ni ko sai na ce” Kawun ku ke ma haka? To ai ba ku za ku yi masa tambaya ba.”
Tariq na dariyan mugunta ya ce” har auran ma za mu karɓa masa. Gaya min su wa za su je? To iyayen duk sun tsufa sun kare mu ɗin dai mune rufin asirin sa. Tafida ka bar gemun ka ya taru nima haka saboda na ga kamar kawun na ka ya fara maganar aure. Ko wani lokaci zai iya neman mu.”
Dariyan su suka sha suna tafawa nima ni da Farida muna ta ɗan dariya.
“Sai mun yi waya. Allah ya kiyaye hanya.”
Yallaɓai ya faɗa bayan sun ƙara musabaha da Tariq.
Shi ya bude musu get suka fita muna ɗaga musu hannu Allah ya sa baby ta samu biskit da ta yi rigiman sai ta je.
Mun dawo cikin falo na kalli Yallabai ina faɗin” Duk abin da kuka faɗa akan Uncle Abba sai na faɗa masa.”
Yana ƴar dariya ya ce” To wai shi ne me? In ba ki da kati ki yi mini mgana sai na saka miki.”
Kafaɗansa na kai ma duka ina dariya shima yana tayani. Mun zauna kan kujera ɗaya muna hira nan ne na ke gaya masa zan je Ɗorayi da wuri saboda yau su Yaya Auwal za su koma wajen aikin su.
“Ok. Zan kai ki ne da kaina?
“No. Ka bari dai sai ka je ka ɗauko ni”
Sai ya gyaɗa mini kai sai na mike na wuce da farantin ruwan da na kawo ina faɗin.
” Bari na je na wanke ma su jidda kan su.”
Da kai ya amsa min, sai na bar masa falon gabaɗaya. Kitchen na biya na sauke kayan hannuna sannan na shiga dakin su Jidda na ga sun gama tsifan har Saude ta ƙara share ɗaki.
“Saude je ki wanke min sauran kofunan da suka ɓaci bari na wanke musu kai tare za mu tafi ɗorayi.”
“Umma ba kin ce za ki yi mana kitso ba?
Jidda ta tambaya ne, sai na kalle ta kafin na ce” Sai na dawo ko zuwa dare ne.”
Mayafin jikina na cire na shiga tiolet ɗin akwai mayukan wanke kansu a ciki tunda daman rabi na kan raba na su da nawa. Kuma daman na iya ni nake yi ma kaina wankin kai ni da yayana a gida tunda ina da handrayer.
Ruwa na tara mai ɗumi sannan na kira Baby na fara wanke mata sannan jidda a karshe, bayan na gama na fito na jona handrayer na busar musu da gashin gabaɗaya na shafa musu man kitso Jidda ita ta ƙara taje kanta ta daure da band ni kuma na yi ma Baby duk da ana yi ta na kuka har sai da Yallabai ya leƙo yana faɗin” To a kyaleta mana tun da an gama”
Ina kallon shi kafin na ce” Za a dai gama amma ba a gama ba.”
Sai da na matse na samu na daure mata gashin. Yallaɓai ya ɗauke ta yana lallashinta lokaci ɗaya yana share mata hawaye, domin har da majina saboda kukan.
“Ba ki son gashin ne?
Yallaɓai ya faɗa duk cikin sigan lallashi sai ta gyaɗa masa kai, da sauri ya kalle ni kafin ya ce” Sadiya to a yi ma Baby aski ba ta son gashi balle ta rika kuka ko?
Sai ya kalleta kawai sai ta fashe da kuka tana faɗin” Ba na son aski.”
Yallaɓai sai ya kalleni kafin ya ce” To a bar mata gashin ta shi ke nan? Ya sake kallonta sai ta gyaɗa masa kai, rumgumeta ya yi, ni kuma me zan yi in ba dariya ba. Jidda ma ta na ta dariya Yallabai ya sunkunci Baby ya fice ya na faɗin” Tunda kun yi faɗa da Umma sai a ji da Abba ko?
Bin bayan su na yi bayan na ce jidda ta ƙara share ɗakin saboda gashi. Ganin har an kusa azahar sai na bi Saude kitchen na ce bari kawai na dora farar shinkafa ina da sauran miya sai a ci da shi kafin mu tafi.
Ni da na so fita tun bayan azahar sai gani har karfe uku sai da muka ci abinci na sauya kaya sannan na bar ma Yallaɓai amanar gidana da yarana ina ta ƙara jadadda masa.
Sai kawau ya ce” Na ji mai gida. Kina ta mini kashedi megadi ne ni?
Ina dariya na ce” Kamar haka! Tun da ko a ina aka je gida na Sadi baby ne.”
Na ƙarishe faɗa ina masa fari sai kawai ya yi mirmishi kafin ya ce” Hausawa suna cutar mu. Kai da guminka sai ka ji ana gidan Sadiya.”
“Ko gidan Maman jidda ba.”
Na faɗa ina yi masa dariya.
“To ba a cewa na Baban jidda.”
Yadda ya yi mganar ne yasa har ina riƙe ciki wajen dariya. Mun rabu sai mangariba zai zo ya dauke ni bayan ya sake duba Alhaji. > Janaftybaby: A daidaita muka samu zuwa Ɗorayi a kofar gida muka yi sallama da Saude bayan na ce ta gaida mamanta.
****
Ɗorayi.
Ko da na je gida cike da ƴaƴa da jikoki. Domin kaf su Yaya Murja da yaransu suka zo tun da yau lahadi ba makaranta. Na iske har Ma’u tare da Zainab da su Alhaji ƙarami. Rahila ce kawai ba ta zo ba wai ba ta jin daɗi
Mutanen Abuja dai sun riga sun tafi saboda nisa. Sai Yaya Hamza ne shi ma lokacin da na zo suna sallama ne za su ɗau hanya. Amina kuma za ta bi su su rage mata hanya daga zariya sai ta hau motar kaduna. Da ta ce sai gobe megidanta zai zo su koma tare to shima sai daga baya ya kirata ya ce suna da taro a wajen aiki da wahala ya samu zuwa. Ya dai yi ma Alhajinmu sannu ta waya. Tunda mijin Amina lacara ne a jami’ar kaduna.
Kallon ta na yi lokacin da muka samu keɓewa a ɗakin Mama ina faɗin” Ke yanzu da sai ki tafi ba mu yi sallama ba?
Ta na yar dariya ta ce” Ai na san kina hanya.”
Gyara zama na yi kafin na ce” Tun da Datti ya koma ya zo gidanki weekend kuwa?
“A’a ya ce suna ta test ne. Zai zauna a cikin makaranta ya yi karatu. Ƙila sai sun gama zai taho.’
Sai na jinjina kaina. Saboda Datti a farkon shigarsa jami’ar a gidan Amina ya fara zama amman sai aka samu matsala tun da akwai wani ƙanin mijinta a gidan da suka yi ta samun matsala da Datti har lamarin na neman shafan auren Amina tunda kowa kanshi ya sani. Sai Yallaɓai ya ba da shawaran gwara ya samu hostel ya koma can da zama, Allah ya sa ma akwai wani abokin shi ɗan nan kanon ne shi ya bashi waje a ɗakinsa suka yi sukwatin. Sai dai ya na ɗan zuwa wani lokacin ya yi ma Aminar weekend.
“Mubarak ɗin ma ba ya nan yanzu. “
Ita ta katse min tunani Mubarak sunan kanin mijin na ta.
“Me ya faru? Har ya gama karatun?
“Ban sani ba. Amma ina kyautata zaton kamar ya samu matsala ne duk da yayan na shi baya son faɗa mini. na san ya na Aji uku ne sai ya tafi can zuntu sama da wata biyu bai dawo ba gashi ana ta karatu sai na yi zargin wataƙila ya samu matsala ne a can makarantar.”
Sai na gyaɗa kai kafin na ce” Za ta iya yuyuwa. Ke dai tunda ba a faɗa miki ba. To ba ruwan ki.”
Tana dariya ta ce” Haba. Kamar ba ki sanni ba’
Aiko na san Amina miskila ce kafi mahaukaci ban haushi, mun ɗan yi hira sama sama kafin Khaleesat ta leƙo ta na fadin ta fito su wuce ni na riƙe mata karamin akwatin ta muka fito suna falon Alhajinmu muma sai muka shiga can.
“Na gode ƙwarai. Allah ya kai ku lafiya.”
Alhajinmu ya faɗa ya na ɗan kishigiɗe a saman kujera. Ya na riƙe da Amna Tasleem na kusa dashi.
Khaleesat ta duka a kusa da Mijinta ta na faɗin” Allah ya ƙara lafiya Alhaji sai mun ƙara dawowa.”
“Allah ya sa. Na gode Allah ya yi muku albarka gabaɗaya.”
Muka taya su amsawa da Amin mune rakiyar har waje bakin mota gabaɗayanmu ba mu iyayen ba, sannan ba yaran ba.
Sai da suka ɗaga muna ɗaga musu hannu suna ɗaga mana. Har sai da motar su ta ɓace ma ganin mu sannan muka koma cikin gida.
Aneesa ɗiyar Anty Balki ce ta tambayi su Jidda na ce suna gida, a ɗakin Mama muka yada zango gabaɗayan mu tun da an ce a bar Alhaji ya huta ɗakin Gwaggo kuma ta ce Baaba na ciki tana barci kar a dame ta.
A kusa da Yaya Aina na zauna ina faɗin” Wai su Marwa ba su samu hutu ba ne?
Kai tsaye ta ce mini” Sun kusa fara jarabawa. In ta dawo za su fara pratical a asibiti to babanta ya ce ta dawo gida ta yi kawai.”
“E. Gaskiya ai yafi. Ni ko wai ba ta da waya ne kwanaki ina ta kiranta a kashe “
“Ta lalace tana saka layinta a wayar wata ƙawarta ce.”
Sai na kaɗa kai kafin na ce” Haba shi ya sa ba na samunta. Ta dawo sai a gyara in ba ta yi sai a siya wata amman ba ta zauna ba waya ba.”
Yaya Balki ta yi karaf ta ce” Tun da tana da uwa Sadiya ba”
Sai na fashe da dariya kafin na ce” Kwarai kuma matar Injiniya ba.”
Yaya Aina na dariya amman ba ta yi mgana ba. Yaya Murja na zaune waje ɗaya da Ma’u sai da suka jiyo suna kallon mu, sai na yi kamar ban gansu ba muka cigaba da hiranmu da su Yaya Aina. Muna nan zaune sai ga Zaituna ta shigo fakam fakam kamar an jeho ta. > Janaftybaby: Yaya Balki ce ta yi mata mgana da cewa” Daga ina? Ɗazu mijin ki ya fita ya na cewa ba ki zo ba?
Ruwa ta ce a bata sai da Aneesa ta kawo mata pure water biyu ta shanyen su tana maida numfashi.
“Wallahi na ɗan je barka ne. Wata yayarmu ce ta haihu.”
Daga ji ƙarya take yi saboda sai wani faman kifta ido ta ke yi kamar wacce ta yi ma sarki karya.
“Za ki ci abinci ne?
In ji Yaya Murja ai da sauri ta ce” Wallahi kamar kin san ina jin yunwa. Can anguwa uku ne ba mu samu abin hawa ba sai da muka ci uban tafiya duk abincin da na ci ya gama zazzagewa.”
Su Ma’u na dariyanta ni ko ban yi dariya ba saboda ban ga abin dariya ba. Kallonta na ke yi kamar wata mahaukaciya ta hana kanta zaman lafiya saboda shegen shige shigenta ta kuma hana ɗan uwan mu ya huta. Firdausi a ka kira ta zubo mata jallop ɗin shinkafa da wake ta zauna ta na ci hannu baka hannu ƙwarya da Yaya Aina ta ce ta ci a hankali sai ta fake da cikin goyo tunda a lokacin ta na da goyon mai sunan Yaya Hamza.
Ba ta lura da ni ba sai da ta ci ta koshi sannan ta ganni.
“Sadiya daman kin zo?
Yanayin maganarta sai ya yi kama da ta renin wayau. Amman ta juya ta na yi ma Ma’u magana. Sai na ji ya kamata na rama na nuna mata matsayinta, sai kawai na kalleta kafin na ce” To daman ina za ki ganni kin shigo kamar an koro ki”
Na faɗa ina kallonta. A raina ina faɗin Yaya Abubakar ya haɗu da jarabawa na auran wannan matar, iyayenta talakawa ne ba su da komai Yaya Abubakar ne ke tallafe da su, yayanta namiji sai shaye shaye ƙannenta sai bin yan iskan anguwa amman ba ta duba haka ba ita ce yau cin bashi ita ce kafa adashe ta cinye ta sha shiga rigima Yaya Abubakar na fidda ta ina tsoron wata rana kar ta ɗauko abin da zai gagare shi ta saka a ɗaure shi.
“E na shigo ban ko gani na shawo tafiya”
Kai tsaye ina kallonta na ce” Wata tafiya? Ko dai yunwa domin daga ganin ki yunwar ce ke ɗawainiya dake daman.”
Yaya Balki na yar dariya ta ce” Da alama kam.”
Ita kuma sai ta wayance da cewa” Ban tsaya a gida na yi abinci ba ne, kuma can ɗin na kaɗan na ci kuma ga tafiya cikina duk sai ya zazzage”
“Ke kam Zaituna me zai hana ki tsayawa a gida ki yi abinci? Shi ya sa Yaya Abubakar da ya shigo ɗazu ya ce a zuba masa abinci ashe da yunwa kike barin shi.”
Yaya Balki ta faɗa tana kallon ta kafin ta samu zarafin mgana Yaya Aina ta karɓe da cewa” To ta ina ma mace na da miji da ƴaya za ta fita ba ta yi girki ba? Ai ko fitar sassafe ce ka yi dai ko fara ba mai ne kafin ka fita.”
Ina gyara zama na ce” Ta saba ne. Ita fa Zaituna ba ta son komai ba sai shigen yawo da shige shige. Ko mu nan da kika ganmu sai mun yi abinci muke fitowa daga gidajenmu ballatana ke.”
Na faɗa ina kallonta sai tafara kame kamen wai ita ina ta ke zuwa karaf ko Yaya Murja ta ce” A a Zaituna. Kina da shigen yawo kullum ba ki iya zaman gidan ki. Na rasa gidan wa kike zuwa da ya fi gidan mijin ki?
Har ta na rantsuwan wai ita ba in da ta ke zuwa ko da yaushe tana gida ba domin rashin lafiya Alhaji ai ta fi sati ba ta fita ba, Ma’u na dariya ta ce” Ko ana gobe rashin lafiya Alhaji kin biyo gidana kika ce daga anguwa kike hanya ta biyo da ke? Ko ba a yi haka ba?
Ta faɗa tana kallonta ganin an ƙure ta sai ta wayance da cewa ta tuna sun je gaisuwa can ɓarayin su Ma’u shi ya sa ta biya ta gidanta.
Ganin ta na neman sauya hirar ya sa na kalleta ina mai kiran sunanta.
“Zaituna kenan. Ki daina ma karya kowa ya san halin ki nan kwanaki na ji an ce kin cinye kuɗin adashen mutane har da yan sanda suka dauko miki, to ni dai ba zan ce ki bari ba amman in kika ɗauko rigimarki ki riƙa tsayar da ita a kan ki ko akan dangin ki, ki bar ɗan uwana ya huta duk kin tsufar da shi kin saka shi a uku, kar ki kashe mini ɗan’uwa gwara ma ki daina abin da kike yi.”
Sai ta kasa mgana Yaya Balki ta ce gaskiya ne Yaya Abubakar duk ya fara tsufa saboda wahala da rashin kwanciyar hankali. > Janaftybaby: Yaya Murja sai ta taɓe baki kafin ta ce” Ai Allah ya bashi wasu kudaɗen sai na ce ya kara aure ita kuma ta je can ta ƙarata, ka rasa abin da take siya da kuɗin da ta ke rigima komai dai dai gwargwado ya na yi miki zaituna me kika nema kika rasa?
Ganin mun yi mata taron dangi ya sa ta fara kuka tana murza idanuwana.
Yaya Balki ke faɗin” Me ye na kuka? Domin fa muna sonki ne ya sa muke gaya miki gaskiya da wasu dangin ne wallahi sai dai ki ji wata maganar, to ki ɗauka mu muna sonki ne shi ya sa muke faɗa miki gaskiya domin ki gyara.”
Yaya Aina ta karɓe da faɗin” Kwarai da gaske in wasu dangin mijin ne ita kanta ta san ba za su ɗauka ba. Faɗan ke so kan ki muke yi miki ki gyara saboda ke ba yarinya ba ce kin san abu mai kyau da mara kyau, in kika bari ya yi zuciya ya ɗau wani mataki akan ki ba za mu saka baki ba to kafin akai ga haka ki sauya rayuwar nan da kike yi, ki zauna a gidanki ki fita daga shiga rigima tunda ba abin da mijin ki ya rage ki da shi’
Kowa na ta tofa albarkacin bakin shi, Yaya Murja dai ta ƙare mganar da cewa” Ke ko koyi ba za ki yi da su khaleesat da Laila ba? Dube su kowacce tsaf ita da ƴaƴanta, kuma suna rawan jiki akam mazajensu suna tattalin su amman ke ba wannan a gabanki sai shirme, to ki fara gyara kanki da gidanki in kuma ba haka wata rana za ki yi nadama.”
Ma’u ta saka baki tana faɗin” Ki rika kwalliya Zaituna. Haba kamar ba mace ba, ba ki gyara balle ki gyara ƴayan ki? Namiji fa na son gyara kuma in kika gyara wallahi sai ya ji daɗi”
Nima na yi mata nasihan ta daina zama kaca kaca ta zauna a gidan ta gyara kanta tana kuka tana mana godiya tare da alƙwarin ta daina muna mata fatan haka daga nan sai muka saki maganar muka shiga wata hira ana mganar Baba Sani zai tafi gobe su Yaya Hamza sun bar kuɗi a ba su Yaya Aina ta ce in muna da wani abu mu haɗa masa ko in akwai mai sabulai da omo mu kawo ni dai na ce ina da sabulai zan aiko da safe Ma’u ta ce za ta ga abin da za ta aiko, har da kaya ma Yaya Balki ta ce tunda wancan zuwan da suka yi Matar Baba Sani ta mata zencen kayan yara haka suna so.
Yau dai zaman gwanin daɗi ba faɗa ba bakar magana kowa ya binne abin da ke ran shi, Yaya Aina ce ta kalli Ma’u lokaci ɗaya tana faɗin” Ke ko Ma’u dangin babanki na neman ki yanzu?
Sai ta yi shuru kafin ta ce” E. Muna waya da wasu daga ciki can kwanaki ma wata wacce da mamanta da babana uwar su ɗaya uba ɗaya ta zo wajena har ta yi kwanaki. Ni dai na daɗe ban je ba amman Alhaji ya ce in ya samu lokaci za mu je mu gan su.”
Yaya Murja ta yi karaf ta ce” Ba dole su neme ta ba. Sun ji labarin ba ta wulakanta ba. Ta na da abin duniya.”
Yaya Balki ke faɗin” To daman ai sai an san kana da amfani ake nemnka. Lokacin da suka san su za su wahala da ita ai ba su damu ba. Sai yanzu da suka san za su more ta. Ba komai abin da ta ke dashi ta yi musu ba shike nan ba.”
Ni ko ina gefe na ce shiken nan kuwa. In kana da shi ka yi in baka dashi ne in baka yin ba matsala. Ita dai sai gyaɗa kai ta yi tana faɗin in sha Allahu.
Sallar la’asar ya tashe mu a wajen, bayan mun idar da sallah na shiga ɗakin Gwaggo na gaida Baaba ta amsa kamar yadda ta saba amsa mini. Daga nan ɗakin Mama na yi shigewata ina duba wayata su Firdausi ne a tsakar gida suna shara wasu na wanke wanke su Yaya Murja na baro su ɗakin Gwaggo. Tun da su sun rigani zuwa karfe biyar Yaya Aina ta yi sallama ta wuce gida bayanta Yaya Balki tare suka fita da Zaituna ni ma sai na yi shirin tafiya har Ma’u na fadin ta ɗauka sai dare zan tafi, da haka na so amman sai na tuna zan yi ma su Jidda kitso ba zan zauna jiran Yallabai ba.
“Tafiya zan yi. Na yi ma su jidda tsifa zan kama musu kai gobe makaranta.”
Yaya Murja na gefe ta ce” Da kin zo da su Firdausi ta yi musu.”
Sai na ce mata ban yi tunanin Firdausin za ta zo ba ne, ina shirin tafiya Munirra ta kirani a waya ta na tambayan muna asibitin ne ko gida? Sai na ce mata muna gida sai ta ce mini gata nan zuwa ita ta tsayar da ni na jirata har sai da ta zo na rakata falon Alhaji ta gaishe shi.
“Matar ƙanin Yallabai ne Alhaji”
“Allah ya yi mata albarka. Na gode.”. > Janaftybaby: Har da kankana ta kawo masa Gwaggo na ta godiya, mun dawo ɗakin Mama sai ga su inna Mariya sun zo duba Alhaji ta ce Amina ce ta faɗa mata jiya shi ne ta ce bari ta zo ta duba shi, dalilin haka yasa na daɗe a gidan tun da sai bayan sun tafi tare ta ke da matan su Kawu Tasi’u, sannan ita Munnira ta ce min ba daɗewa za ta yi ba na fito rakata har bakin gida bayan ta yi sallama da su Gwaggo ta ke ce min.
“Ke na taɓa ki da alheri matar Yallaɓai. Kin ji Yaya Usman zai kara aure? Ban samu zarafin mgana ba ta cigaba da faɗin” To yanzu ma mganar da ake yi Anty Zabba na gidan su. “
Cikin nuna mamakin na ce”Wai har yanzu ba ta koma ba?
Munnira ta ce” Ina fa ta koma, a bakin Nasir na ji wannan satin mai shiga Yaya Usman ɗin zai zo, na so kiran Anty Zabba sai na fasa kar ta ce ina da son jin gulma”
Ina mata dariya na ce” Wallahi haka za ta ce.”
Munnira ta kama haɓa kafin ta ce” Shi ya sa ban kira ba. “
Na ce gwara hakan itama Munira ta na faɗin ba ta ji daɗi ba, koma mene da ta yi hakura ta zauna tunda matar na shi ba akanta za ta zauna ba.
“Uhm ke dai Munira Allah dai ya kyauta ya dai dai ta su.”
Ta amsa min da Amin Amin daga nan muka yi sallama na koma cikin gida sai na ga Aneesa da wayata wai ana ta kirana ina dubawa sai na ga Yallaɓai ne da sauri na ɗaga kiran.
“Yallaɓai ka taho ne?
Cikin wani irin murya ya ce min” Sadiya ta congratulation.”
Ina yar dariya na ce” Yallaɓai ka biya mini makka ne?
Shima dariyan ya yi kafin ya ce” In sha Allahu ina saka ran haka, amman dai yanzu ina so na faɗa miki ne an biya ni half payment na aikin nan namu na Rano.”
Cikin murna na ce” Don Allah fa Yallaɓai”
“Allah Sadiya ta. Yanzu kuɗin suka shigo sun kuma kirani sun faɗa mini.”
Ɗakin Mama na faɗa ina faɗin” Alhamdulillah mun yi kuɗi”
Ya na yar dariya ya ce” In an yi mangariba zan fito sai na zo mu dawo tare”
Da haka muka yi sallama, muna gama wayar na yi hamdala ina jin daɗi Allah ma ji roƙon bayin shi.
Na ƙosa mangariba ta yi ma saboda murna, ina idar da sallar mangariba na shirya lokacin har Yaya Murja ta tara yayanta sun tafi gida ni da Ma’u kawai ne a gidan ita kuma tana tare da Baaba. Yallaɓai sai bayan isha’i ya zo, ya ƙara duba Alhaji sannan na yi musu sallama muka tafi gida.
Muna hanya ya kalle ni kafin ya ce” Yanzu da me zamu fara Hajiya ta?
Ina dariya na ce” Mu je gida mana Alhajina.”
Sai muka kalli juna kafin mu kwashe da dariya, ni ko har ina dukan kafaɗansa kafin na ce” Ranka ya daɗe mai girma Tafida.”
Shi dai ya na ta dariya ni kuma ina masa kirari
“Angon Sadiya Ɗan gatan Nene, uban Jidda da Maimuna. Allah ya ƙara ja zamanin Tafida mai girma Injiniyan gine gine, mai muƙamin zane zane takawar ka lafiya”
Ya na dariya ya ce” Me kike so Sadiya? Ina masa dariya na ce” Me kuwa na ke so? Yallaɓaina kaɗai na ke so.”
Gira ya ɗaga min kafin ya ce” Kin yi kyakyawan zaɓi kuwa.”
Muna tafe muna hira, har muka isa gida. Baby har ta yi barci, dole na tashe ta tana kuka tana komai na yi mata kitso, Yallaɓai na ta faɗan wai ban iya kitso ba ne na saka yarinya tana kuka.
Baki sake na kalle shi kafin na ce” Au ban iya ba ko?
Ya na kallona ya ce” To ni dai ban san lokacin da kika koyi kitso ki ka iya ba”
Sai kawai na yi banza da shi Jidda dai lafiyan lau muka yi kitson mu, sai bayan na gama mu su ne na ce su yi shirin kwanciya Baby daman Babanta ya lallasheta har ta yi barci. Wanka na sake yi na yi shirin kwanciya Tea na haɗa mana muka sha sannan muka zauna kassafa kuɗi, abu na farko kayan abinci na yi masa mgana sai kuma na ce ya ijiye kuɗin makaranta yara tun da sun kusa fara jarabaawa.
“A’a ki bari sai zuwa lokacin ai da sauran lokaci.”
Kamar zan yi mgana sai kuma na fasa saboda na san wataƙila zuwa lokacin ya zo babu, mun yi mgana ya cire wasu kuɗi saboda Gidan bulo da office sai na yi masa mganar Halima ta haihu ba a yi mata komai ba sai ya ce zai turamin 20k ya ce a siyi abin da ya kamata ina so na ce ya rage min ko kaɗan a cikin kuɗina amman ban yi ba kamar ya san me na ke tunani sai ya ce
“Zan ba ki 50k ki rike a hannunki. Kuɗin ki kuma in gwammati ta biya mu sai na baki duka in sha Allahu.” > Janaftybaby: Ina yar shagwaɓa na ce” Yallaɓai buɗe saloon ɗin fa?
Da sauri ya ce” Wannan ni na ce zan buɗe miki, kuɗin ki kuma haƙƙn ki ne zan biya ki in sha Allahu.”
Sai ya ga na yi shuru sai ya shafa kumatuna kafin ya ce” Kar ki damu. In sha Allahu duk za a yi.”
Sai na gyaɗa masa kaina. Mun cigaba da lissafi ya ce 30k na kayan maggi da kayan tea, sai na ce ai ya haɗa gabaɗaya cikin na kayan abinci tunda tare muke siya a kasuwa a wani babban shago yana da lambar wayarsa list ɗin kawai zan rubuta ya tura masa da ƙudin har gida za a kawo mana kayan abinci.
Har da sabule da omo, ni kuma sai ya ce zai ƙara mini 30k saboda siyayyarmu ni da yara su Unders da sauran kayan kwalliyan mata.
Kuɗin asibiti kuma ya ce zai ware mini 50k saboda bamu san nawa za a nema ba sai dai goben in mun je mun gani. Sauran kuma ya ce zai yi amfani zai sallami sauran ma’aikata da shi ko da rabi rabi ne, ni na san har da kyatttuka sai ya yi in dai Yallaɓai ya samu kudi kamar suna masa kwaiƙwayi ni na yi masa mganar Nene, daman in za mu yi siyayya kayan abinci har da ita da kayan tea sai sabulan wanka sai ya ce na rubuta list ɗin gabaɗaya sai ya tura babban shago za a kawo kayan zuwa gobe in sha Allahu.
Sai na ce to a daran na rubuta abin da na manta na ce zuwa da safe zan tuna. Saboda zuwana asibiti tun asuba na tashi na yi ma yara shirin makaranta Yallaɓai jiya ya siyo indomie da kwai , sai buredi sai na soya musu buredin da tea ɗin suka tafi da shi makaranta, ni kuma muka shirya daman tun safe na tura ma Dr Fatima saƙo sai ta dawo min da amsar za ta ƙara kiran Dr Aisha ɗin amman na je asibitin na siya kati za a kai ni gynea unit ɗin in ce dai Dr. Aisha na zo gani a shigar mata da Fayel ɗina za ta duba ni in sha Allahu.
Tare muka fita da su Jidda muka kai su makaranta daga nan muka wuce Aminu kano. Da taimakon Yallaɓai nan da nan muka siya kati har aka yi mana hanya zuwa Gyea Unit da taimako irin masu zirga zirga rarraba katina Yallaɓai ya yi ma ihsani, ya faɗa mai mun zo ganin wata Dr Aisha bukar ne. Wajen ta zai kai mini Fayel ɗina sai ya ce ba matsala ba ta ƙariso ba amman tana hanya.
Sai wajen tara da wani abu likitocin suka fara zuwa. Muna zaune da Yallaɓai bangaren yan jira aka shigar da Fayel ɗin mu, Saboda ihsanin da Yallaɓai ya yi mishi sai ya shiga ciki ya yi ma Dr Aishan bayani sai ta ce eh ta na sane fayel ɗina daman a sama ya saka min ni ce ta farkon da aka fara kira na shiga ganin Dr Aisha Bukar kamar yadda ke rubuce jikin Office ɗinta.
KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.*
07045308523.
*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE*