Turken Gida – Chapter Five
by JanaftyTun ranar farko da na fara ganin Yusuf na ji a raina tabbas na haɗu da namijin da ya gama cika zaɓina. Sannan na san tabbas zai iya yin katanga da cikar burina na sai na gama Jami’a na samu aiki zan yi aure. Saboda in na bari ya suɓuce mini samun kamarsa zai yi mini wahala
Tun da gashi tuntuni ina tsumayen shi. Shi wanda ya dace ɗin amman ban samu nasaran haɗuwa dashi ba sai a wata ranar laraba. Daga cikin BUK na ke mun gama lacture tun safe har yamma na sha wahala ina tafe kamar zan faɗi, ba zan mata da kayan da ke jikina a ranar ba. Wata atamfa ce mai ruwan ganye hijabin jikina fari ne sai takalmin dake kafata mai saukaƙƙen tudu.
Daga bakin get ɗin jami’ar da na fito ni kaɗai ce. Ko anan ɗin ma ban yi wata ƙawa da na saki jiki da ita ba a dai gaisa kawai. Ina tsaye ina neman abin hawa ba ni da masaniyar tun a lokacin Yusuf ya ganni kuma Allah ya haɗa zuciyarsa da tawa a waje ɗaya.
Hauwa’u Jamilu ta fito tare da ƙawarta da tare na gansu Samira. Na gansu amman sai na ɗauke kaina kamar ban gan su ba, lokacin duniya na kwance sannan abubuwa duk ba su zama gari kamar yanzu ba. Ko wayar hannu nan sai wane da wane ke riƙe shi ko a ajinmu akwai ma su ita handset amman sai ɗaya ɗaya nima dai ina cikin mara shi.
“S. Yashe sai gobe.”
Haka Hauwa’u ta faɗa sai na kalle su kafin na ɗan gyaɗa kaina. Ganin ina ta tsaye ban samu abun hawa ba sai na fara tafiya zuwa bangaren yamma su kuma su Hauwa sun yi gabas. Ina tafe ina sauri saboda yamma ta fara sauka biyar za ta iya gotawa a lokacin.
Ban san ya na bina ba. Saboda ban ji takun tafiya ba sai da na ji sallamarsa cikin muryansa mai zaƙi da haiba ta maza masu kyau da Aji.
” ƴan mata doguwa Salamu Alaikum.”
Haka ya faɗa da farko ban yi niyyar na juya ba amman yanayin muryansa da salon da ya yi magana su suka rinjayi tunanina da zuciya na ɗan waiwaya na kalle shi yana daga bayana kaɗan ina juyowa sai kawai ya yi mini mirmishi irin mirmishinsa da na ke matuƙar so a tare dashi.
Na yi saurin ɗauke kaina na cigaba da tafiya amman na sauya takuna. Gaba na ta faɗuwa ban san so ba amman ina tunanin nima na fara son Yusuf a wannan ɗan kallon da na yi masa.
Lokacin da na yi gaba ina ta fargaban Allah ya sa ya cigaba da bina ya yi mini magiya sai na yi masa kwatancen gidanmu. Har ɗan rage sauri na yi ina jinsa ya na cigaba da bina lokaci ɗaya yana sake faɗin.
“Haba ƴan mata. Ina ta mgana shuru”
Ɗan sake kallon shi na yi. Kai ya haɗu! Haka na faɗa a cikin raina ban wani saki fuskar da zai fahimci yanayina ba amman tabbas Yusuf ya shiga cikin zuciyata a karon farko da muka haɗu. Cigaba da bina ya yi yana min mgana amman ban tanka shi ba sai dai kuma tuni na gama haddace kamaninshi da kayan dake jikinsa. Tun a wannan ganin farko ni na san Yusuf ɗan gayu ne kuma yana da ilimi kuma shi ɗin daga ganin ɗan manyan mutane.
Yana sanye da ƙananun kaya. Jeans baki ne sai T. Shirt fara ta na da zanen baki a jiki amman ban iya ganin me aka rubuta ba. Takalmin ƙafarsa mai rufi ne sannan akwai wasu takardu a hannunsa. Ta gefen ido na gama ƙare masa kallo a cikin zuciyata kamar in yi ta tsalle saboda murna. Tsayawa na yi ina taran abun hawa shi kuma sai ya ƙara marairaicewa yana faɗin.
“Tafiya za ki yi ko muryan ki ba ki bari na ji ba? > Janaftybaby: Sai na kalle shi kafin na ɗan ɗauke kaina ina faɗin” Ya dace ka tari budurwa a hanya kana yi mata mgana?
Da sauri ya ce”Afuwan. to ki faɗa min sunan ki sai ki bani lambar wayarki sai na samu lokaci na zo gida mu yi mgana.”
Kallonsa na yi sai ya yi wani sanyi kafin ya ce”Please.”
Sai kawai na rausayar da kai kafin na ce”Sunana Halima. Amman ana kirana da Sadiya.”
“Wow.! Nice name Sadiya ta.” A karon farko da ya fa kirana da Sadiyarsa.
Sai na yi mirmishi ina so na tambaye shi sunan shi amman na kasa.
“Ba ni da waya. Gidanmu kuma na Ɗorayi in ka ce gidan Alhaji Sulaiman Yashe za a nuna maka.”
Ƙuramin ido ya yi kafin ya ce” Sadiya kin tabbata zan same ki in naje?
Sai na samu kaina da ɗaga masa kai kafin na ce” In sha Allahu.” Mirmishi ya yi mini nima sai na maida masa martanin mirmishi.
Shi ya taran min motar haya na hau sannan ya ɗaga mini hannu kafin ya ce”Bye. See you “
Ina so na ɗaga masa hannu amman sai na fasa sai dai na gyaɗa masa kai ina ɗan mirmishi.
Na koma gida a ranar cikin farinciki har sai da Rahila ta fahimci yanayina.
“Sadiya karatun yau hala ya fi miki daɗi ne?
Sai na kalleta lokacin ina tsaye ne a tsakar ɗakin mu ina mirmishi ni kaɗai ban sani ba har Rahila ta shigo ta kama ni ina ta mirmishi ni kaɗai.
“Me kika gani?
Na faɗa ina kallonta sai ta ƙara matsowa kusa da ni cikin raɗa ta ce”Ko dai?
Da sauri na matsa baya ina faɗin” Ko dai me! Ni matsa ki ban waje.”
Na faɗa ina tureta ina mata dariya. Daga tsakar muka ji Gwaggo na gaisawa da Ya Muntari. Sai na ga Rahila na mirmishi a raina na ce daman haka ake ji in ka haɗu da wanda kake so. Sai na daina ganin laifin Rahila akan Yaya Muntari saboda na fahimci haɗuwar jini ce.
“Uhm kin ji muryan Yaya Muntari kin kasa sukuni.”
Sai ta harareni tana faɗin” Ya Muktar dai ko Sadiya?
Ta faɗa ƙasa ƙasa. Ni ko ina ta dariya da gayya na fita tsakar gida dai dai zai koma can waje in da ɗakunsa suke da sauri na ce” Ya Muntari ina yini.”
Sai ya juyo yana amsawa kafin ya ce” Sadiya yan makaranta an dawo.”
Sai na amsa masa ina kallon Rahila ta cikin ɗakin mu tana faman harara ta. Ni kuma ina dariya. Yanzu saboda makaranta an ɗauke mini aikin gida sai in ranar weekend ne. Rahila ce da Amina ke yi tun da Ma’u na Minna sai an yi hutu ta ke zuwa ganin gida.
Haɗuwata da saurayin da ban san sunan shi ba sama da sati ɗaya bai zo ba kuma ban ƙara ganin shi ba. Har in na fito daga cikin Jami’a. Na yi ta tsayawa ko da yaushe ina hasashen zan ƙara ganinsa amman shuru sai na fara damuwa. Ko ya zo ne bai gane gidan ba? Ko kuma dai! Na kasa iya fassara yanayin da na ke ji amman na rage walwala da fara’a kamar dai ina so na bayyana damuwar haka. In na kwanta sai na riƙa mafarkin shi tabbacin dai ya samu matsugunni a cikin zuciyata.
Har na fara fidda rai domin an fi kwana goma da haɗuwarmu . Kamar wasa ranar da ya fara zuwa kofar gidanmu muka san juna sosai ranar laraba ne da yamma da wuri na dawo daga makaranta bayan na yi sallar la’asar na ci abinci sai na ɗan kwanta amma ba barci na ke yi ba. Na ji dai yaro ya yi sallama amman ban maida hankalina a wajen ba.
“Wai Sadiya ta zo in ji wani a waje”
Haka na ji an faɗa. Kamar an jeho ne sai gani a tsakar gida ina faɗin” Waye?
Haka na faɗa ina kallon yaron Rahila na kan kujeran tsakar gida tana gyaran wake Gwaggo da Mama suna can ƙofar shashen Alhajinmu suna hira Amina na bakin ma zubar ruwa ta na wanke wanke. Gabaɗaya suka juyo suna kallona cikin mamaki.
“Ni ma ban san shi ba.”
Sai da na juya ina kallon su Gwaggo sannan na dawo hayyacina. Sai kuma na yi sanyi na kasa motsi.
“Je ka ce tana zuwa.”
Mama ta faɗa tana kallon yaron. Ya juya ya fita amman ni na kasa motsi daga in da na ke tsaye..
Rahila na dariya ta kalleni ta na faɗin” ki koma ciki ki ɗan gyara mana! Ko haka za ki fita?
Sai na dawo hayyacina na koma ɗaki da sauri na sauya hijabina na duba madubi na gyara fuskata duk ina tunanin shi ne ko ba shi ba ne? Sai dai zuciyata na ta rawa. Na saka takalmina na fito tsakar gida bakina na rawa na ce” Zan je waje.”
Gwaggo ce ta tanka ni Mama ba ta ma a wajen ta shiga ɗaki.
“To Sadiya. Amma kar ki daɗe saboda Alhaji.” > Janaftybaby: Sai na amsa mata na juya na fita Rahila na yi mini dariya ganin yadda na yi wani sanyi ina tafe kamar ba na son tafiyar.
Lokacin da na fita na ci karo da shi a tsaye a ƙofar gidanmu yau ya yi shigar manyan kaya ne. Yana tsaye ya na fuskantar ƙofar gidanmu hannayensa harɗe ƙirjinsa. Na ji lokacin da zuciyata ta ta yi tsalle ta dawo waje ɗaya lokacin da na ganshi. Sannan farinciki ya bayyana a saman fuskata lokacin da muka haɗa ido ya sakar min mirmishi nima na maida masa martanin mirmishinsa lokacin da na ke tafiya zuwa in da ya ke tsaye ya na kallona.
Bayan mun gaisa ina noƙewa kai tsaye ya fara faɗin” Sunana Yusuf Muhammad Inuwa. Ni anan garin aka haife ni amman mahaifina da mahaifiyata mutanen Rano ne. Na yi karatuna har matakin Masters ranar da kika ganni ma a Buk na je ganin supervisor ɗina ne akan project ɗina. Sadiya da gaske na ganki kuma sonki sannan ina son in mun gama fahimtar juna iyaye su shiga ciki domin maganar aure.”
Bayan takaitaccen bayanin da ya yi min ban ja aji ba na bashi dama mun ɗan jima muna hira har Yaya Abubakar ya dawo ya ganmu suka gaisa da juna. Daga wannan lokacin ba a ɗauki wata biyu ba hatta Alhajinmu ya san da Yusuf sannan in ya zo zence a wajena a cikin gida muke yi. Zuwa lokacin kuma ni da shi mun gama shaida muna son juna sannan mun aminta mu zauna kan inuwa ɗaya ta aure. Na gama mutuwa a kansa kamar yadda shima ya gama mutuwa a kaina, kowa dake gidanmu na gidajen auran su da mazan gabaɗaya su san labarin YALLAƁAI da tun a lokacin na laƙaba masa wannan sunann tuni na watsar da tunanin sai na gama Jami’a zan yi aure ba zan iya jira ba gwara na yi auren sai na cigaba da karatuna a ɗakin miji.
Ban taba sanin daga ɓarayin Yusuf zamu fuskanci barazana daga dangin sa ba. Duk da ya sha bani labarin gidansu da yan uwan shi na san suna da yawa tunda mata huɗu babanshi ya yi kafin rasuwarsa. Lokacin da muka haɗu da Yusuf a shekaru iyakarsa 27 to 28 ni kuma ina cikin shekarata ta ashirin na kuma san ya karanta Architecture ne masanin zane zane bai samu aiki ba amma yana buga buga. Mutum ne mai sabgogi da yawa da kuma ƙoƙarin neman na kansa.
Yusuf ya turo magabatansa daga Rano. Ya ce mini ƙanin mahaifiyarsa ne da ƙanin mahaifinsa sun zo sun gana da su Baba Aminu an ba su damar dawowata ta gaba za a tsaida mgana. A wannan gabar ne Alhajinmu ya gudanar da bincike a hakan Yusuf har na samu cikakken bayanin waye shi da asalin shi.
*
Marigayi Alhaji Muhammad Inuwa kafin rasuwarsa ya yi aiki a Ministry of Agriculture and natural resources. Ya rasu a shekaran 1999. Ya bar mata huɗu da tarin ya’ya guda 21. A kimanin ƴaƴan da haifa ashirin da takwas ne bakwai sun rasu.
Sannan bayan rasuwarsa da wattani matarsa ta huɗu ta bi bayan shi Hajiya karima.
Ɗan boko ne da ya yi shura tun a zamanin baya da boko bai yawaita ba. Sannan sun shiga gwamnati an dama da su sosai ta sanadin wani amininsa Alhaji Yusuf wanda ke riƙe da sarautar Tafidan Rano. Shima ya rasu tsakanin shi da abokin nashi shekara ɗaya ne shima ya rasu ya bar mata biyu da yaya maza da mata.
Alhaji Muhammad Inuwa da Alhaji Yusuf Tafidan Rano sun fito daga jiha ɗaya ne. Wato Rano sai kuma suka haɗu a makarantar kwana ta Barewa collage dake zariya. Ajin su ɗaya sannan ɗakin kwanan sy ma ɗaya ne. Daga lokacin suka fara aminta bayan sun gama sun nemi jami’a ɗaya ta Usman ɗan fodiyo University. Kowanne ya karanta bangaren da ya zaɓa shi Alhaji Inuwa sai ya yi karatunsa kan harkan Noma da tattalin ƙasa shi kuma Alhaji Yusuf Tafida sai ya kan harkan sanin Siyasa. Bayan sun gama karatun su sun samu manya ayyuka. Shi Yusuf a matsayinsa na jinin sarauta na Tafidan Rano yana da hanyoyin isa ga Gwammatin kano a lokacin. Dukkansu kowanen su ya je ya ƙaro karatu kuma dalilin Alhaji Yusuf Tafida rano Alhaji Inuwa ya tsinci kansa a Ministry of Agriculture na gwammatin Jihar kano a wancan zamanin. > Janaftybaby: Alhaji Muhammad Inuwa ya fara aure da Hauwa’u(Nene) wacce haifaffiyar Rano ce kuma duk an san juna. Kuma a sha’anin bikin ne Alhaji Yusuf Tafida ya haɗu da ƙawar Nene Aminiyarta Fatima Binta(Hajiyar Tafida)
Sai Aminan junan suka aure ƙawayen junan. Dalilin haka sai zumumcin su ya ƙullu a tsakaninsu mai ƙarfi. Kuma ya samu kafuwa har zamanin ƴaƴan su.
Shi dai Alhaji Yusuf Tafida kafin rasuwar ya ƙara mace ɗaya Hajiya kaltume. Ita ce ke da jibi da masautar kano kuma har ya rasu ƙaton gidan shi na nan a Rano. Amman dai yana da gida a cikin garin kano shi kuma Alhaji Inuwa a cikin garin kano ya gina ƙaton gida a gwammaja mai shashe da yawa daga nan Nene ta fahimci Mijin nata yana da ra’ayin zama da mace sama da ɗaya. Ya kuma tabbatar mata tun da sai da ya yi mata huɗu jeras sannan kuma dukkansu matan sun haifa masa zuru’a.
A bangaren ɗakin Nene Zuwaira ce Babba sai Maimuna. Sannan ta yi Bahijja. Sai da ta yi mata uku sannan ta samu namiji sai Alhaji Inuwa ya cika burinsa ya sanya masa sunan Amininsa Yusuf suna kiran shi( Tafida) a kuma a tsukin Hajiyar tafida itama ta sauka an samu namiji itama sai kawai shima Alhaji Yusuf ya saka masa sunan Amininsa Inuwa suna kiran shi(,Tariq) a kuma lokacin a gidan su Nene mahaifinta matan shi biyu mahaifiyar su Nene Innayi ta daina haihuwa amman abokiyar zamanta Hannatu( Inna) ta haifi ɗan ta Namiji sai ya ci sunan mahaifinsu Abdulmu’iz sai suna kiran shi da Abba shi ne kuma auta a gidan su Nene sai ya kasance waɗanan mazan guda uku sun tashi tare sun girma tare sun kuma ba da misalin kyakyawan zumunci juna a tsakanin su.
Bayan Yusuf sai Muttaƙa sai auta Halimatu.
Sai Maman Farko(Hajiya Saliha) ita yar kano ce ita ta ɗan fi Nene yawan ƴa’ƴa domin ƴaƴanta bakwai ne.
Usman shine Babba wanda Zuwaira da Maimuna ne ke gaban shi a tsarin manyan gidan sai shi. Bayan shi sai Nasaratu ita sa’ar Tafida ne sai Nasir sai Jafar sai Suwaiba da Jamila autar ta mai suna Hindatu. Daga ita sai Hajiya Zaliha(Hajiya iya) ita ƴaƴanta huɗu ne.
Hafsat ce babba sai Saffiya sai Muhammad kabir sai Musbahu.
Sai ta huɗun da ta rasu Hajiya karima ita ƴaƴanta uku ne. Ummu Salama sai Adnan Jawahir ce ƙaramar su. Kuma bayan rasuwarta riƙon su Jawahir ya koma ya koma ƙarkashin kulawar Nene.
Kaf ƴaƴan Marigayi Alhaji Inuwa kamar shi sun yi ilimi sun kuma tsaya da kafafun su. Ba matan ba sannan ba mazan ba wasu sai sun gama karatun suke auren wasu kuma suna cikin yi suke auren sai su ƙarisa a gidan mazajen su. Yusuf dai ya yi karatunsa na fimari kaf a garin Rano ne a gidan Alhaji Yusuf Tafida tare da Tariq da kuma Abba. Sannan bayan sun gama ya nema musu makarantar kwana a kaduna mai suna. Federal Sceince and tecnical collage (FSTC) Kafacan Kaduna. Su uku tare suka yi makaranta tun daga matakin fimari har matakin gama babban sakandiri daga nan sai Yusuf ya tafi Abu zaria. Tariq ya tafi jami’ar Ibadan shi kuma Abba ya tsaya anan BUK ya yi karatun shi.
Sun gama degree farko kuma kowanne ya zaɓi in da ya ke so ya cigaba da karatunsa. Shi Tariq Jami’ar lagos ya koma ya yi masters ɗinsa shi kuma Yusuf ya dawo kano ya yin da Abba bai cigaba ba ya koma Rano ya fara kasuwanci da noma tunda abin da ya karanta kenan. Yawancin zaman Yusuf ba a kano ba ne ya fi zaman Rano shi ya sa akwai sabo na musamman tsakaninsa da yaran gidan Marigayi Tafida, kuma a gidan ba a kiran sunan shi sai dai Baaba. Ita kuma Hajiyar Tafida ta ce Tafida mutun ɗaya ce ke kiran shi da Daddy Saudatu(Gimbiya) ƙanwar Tariq ce. Kuma ta ci sunan gimbiya ce matar sarkin Rano a wancan lokacin.
Mganar aurena da Yusuf ta yi barazana domin yan’uwansa sun ce ba zai yi ba ya yi gaggawa sannan bai gama karatu ba kuma ba shi da sana’a mai ƙarfi sai buge buge. Kuma shi Yusuf Mutun ne da ba ya son zama a ƙarkashin wani ya fi son ya zauna in his on. Ban taɓa ganin mutun mai tsari irin Yusuf ba ya karanta abin da ya shafi zane zane amman kuma ya na da sani kan abin da ya shafi gini da sauran su. > Janaftybaby: Tun kafin mu yi aure ya sha faɗa mini so ya ke yi ya buɗe kamfanin shi na kan shi ba ya ƙaunar aiki a ƙarkashin wani ya fi so ya cika burinsa na yadda zai gina kansa domin ƙara ma matasa karfin gwiwan kan dogaro da kansu. Bai taɓa faɗa mini yan’uwansa sun ƙi auran mu da farko ba sai daga baya saboda lokacin da suka ƙi sai ya kai su ƙara wajen kawun nan na su sna bangaren babansu da ke Rano su suka shige masa gaba akan mganar auran mu. Daga karshe da suka ga ya dage sai suka hakura suka bar shi ya yi. An saka rana ba lokaci mai tsawo ba sai aka sanya shi lokaci ɗaya da na su Rahila. Abu kamar wasa kamar mafarki sai ga shi abu ya tabbata kowa ya ji zan yi aure sai ya yi mamaki kamar irin su Ma’u da ba haka ta so ba sannan da ta ga Yusuf sai ta fahimci na tsere mata ko ba ta fada mini ba a fuskarta na ga hassada da kishina. Duk da rasuwar Mama ta saka an ƙara wata ɗaya kafin auran mu mutuwar da ta gigitamu har Alhajinmu da har gobe ya kasa manta rashin Mama. Da Gwaggo da ta daɗe cikin jimami shi ya sa a sha’anin bikin ba a yi wani taro sosai ba. Amma dai kayan ɗaki komai iri ɗaya ni da Rahila babu in da aka bambamta mu ni a anguwar Dakata muka fara zama ita kuma Rahila nan cikin anguwan Ɗorayi ne tana kusa da gida.
A tsarina ban taɓa tsara ma kaina fara rayuwa a gidan Haya ba. Amman sai gashi nan ne muka fara shimfiɗa rayuwarmu ni da Yusuf. Ya san ina karatu kuma ya yi alƙwarin barina har na gama karatuna. Mun sha amarcin mu sosai na ke jin daɗin zama da Yusuf in zan je makaranta wani lokacin har rakani yake yi in bai da wajen zuwa in shima yana da shiga makaranta sai mu jira juna mu koma tare. Yana samun kira haka in ana son zane sannan tun lokacin yana karambanin karɓan kwangila gini sai ya nemo ma’ikata da injiniya.
In na ce a zamana da Yusuf bai gatanta ni ba na yi ƙarya. Ya yi mini hidima da jikinsa da Aljuhunsa. Nene ta karɓe ni a matsayin surukarta. Amman ban da yayyen Yusuf da suke uwa ɗaya barin ma Anty Bahijjan sai bayan auran na ke sanin sun so hana auran mu a cewar su ya bari zuwa gaba sai ya auri Gimbiya. Sai daga baya na fahimci Gimbiya na son Yusuf soyayyar da ba ta iya ɓoye shi. Shi kuma ba ta gan shi a ƙanwa ma ya ɗauke ta. Suna son haɗa auren ne saboda amincin iyayensu amman kuma hakan bai yuyu ba. Farkon auran na yi musu biyayya kamar zan bauta musu saboda dai ina auran ɗan’uwansu. Kuskurena na farko shi ne na yi tunanin yin tsarin iyali saboda karatuna sai dai cikin Jidda shi ya zo ya shammace ni. Watanni tara da kwana huɗu da aurenmu na haifi Jidda da ta ci sunan Nene Hauwa’u.
lokacin ina aji biyu ne zan shiga uku na sha matukar wahala ga ciki ga karatu ga aure shi ya sa ina yaye ta na nemi shawaran Yusuf akan ina son in yi tsarin iyali shi kuma sai ya ba ni goyon baya muka je wani asibitin kuɗi na fara karɓan allura duk bayan 6 months har na shekara biyar. Daga wannan alluran sai ta zame mini matsala. Na gama karatun kuma ina son na ƙara haihuwa amman shuru ko domin goron su Anty Bahijja tunda suna ganin na daɗe ban ƙara haihuwa ba bayan Jidda sun ta zargin ko planning na ke yi amman ban faɗa musu ba tunda kamar na tona asirin kaina ne.
A kuma lokacin muka shiga rayuwa na halin babu. Yusuf ba aiki yake yi ba. Sannan aikin da ya kan samu ya ragu sai jifa jifa. Duk wani abin da na ke dashi sai da ya kare na zo da ɗan kunnen gold wanda na siya da sadakina amman sai dai na siyar da shi. Da cewar Yusuf in ya samu anam gaba zai siya mini. Saboda haka ya sa na nemi aiki a makaranta kuɗi anan kusa damu na fara koyarwa saboda mu rufa kan mu asiri. Ba zan raina ba in Yusuf ya samu na samu to amman yanayin aikinsa kafin ya samu fa? Kuma na yi na yi ya nemi aiki shi yaƙi a dole sai ya tsaya da kafafunsa. Ta ina za ka iya samar da kamfani baka da kuɗi?
Zan iya cewa renon jidda ma tare muka yi tun lokacin ina makaranta tare muke zuwa ya rike mini Jidda har mu fito daga karatu ko ya kai ta gida wajen Nene. Da na fara Koyarwa shi na ke barin ma a gida kafin na dawo ya gama duka aikin gida har girki ma ya yi. Kuma albashina ba na iya cin komai dashi ɓukatunmu na ke yi mana dashi. > Janaftybaby: Sai dai yan’uwan shi duk ba su ga haka ba a tunaninsu na tsaida haihuwa ne saboda Yusuf bai dashi ni ma na fara damuwa sai na fara yawon private hospital ana ce mini ba matsala zan ƙara haihuwa sai da Jidda ta kai shekara Takwas da wattani na ƙara haihuwan y’a mace sai ta ci sunan Anty Maimuna muna kiran ta Baby zuwa lokacin kuma Yusuf ya samu buɗi tunda har ya siya fili ya fara gini muma kuma Alhamdulillah muna cikin ni’imarsa.
Na sha wahala a haihuwan Baby C.S ma aka yi mini daga nan kuma sai na yi ta samu matsaloli na zubar jini da kasala sai juwwa. Daga baya sai na fara ramewa sannan haihuwa ta zo ta tsaya mini cak sai na fara jelen gen zuwa ganin likitoci a asibitocin kuɗi suna cin kuɗina suna gaya mini ba matsala in sha Allahu zan ƙara haihuwa. Tun ina ɓoye lamarin har ya fallasa ga dangin Yusuf tsarin iyali na yi ya ba ni matsala shi dai ya ce bashi ba ne ya faɗa sai na yi tunanin Ma’u tunda itama bayan ta gama karatu ta dawo gida ba daɗewa ta haɗu da Alhaji Mustapha cikin wattani kaɗan suka yi aure sai wayan gari na yi na ga Ma’u tsudum a cikin dangin mijina.
Saboda sanin Yusuf a harkan kwangilan gine gine sunan shi ya ɓace daga Yusuf zuwa Injiniyan da ya yi ma haye. Sannan da tsarina da shawarata mu ka samar da sunan kamfanin shi. HM TAFIDA AND SON LIMITED.” Hauwa’ u and Maimuna kenan da sunana ya so ya saka saboda gudun mgana na ce mu saka na ƴaƴanmu.
A can zariya road ya kama office ɗin kuma ya yi ma kamfanin sa rigister. Ya taimaka kwarai wajen samun kwangiloli masu tarin yawa. Kuma balle ya san jama’a connenction ɗin shi da mutane yasa har Gwamnati na bashi aikin kwangila. Akwai kwangilan da ya samu na gina wata makarantan koyon aikin Jinya ta ƙanin marigayi Alhaji Yusuf Tafida. Wanda shi ne yanzu a matsayin Tafidan rano yana aiki a ministry of education. Yusuf ya samu alheri sosai da shi ya ƙarisa mana gini sannan na bashi shawaran ya buɗe gidan buɗo saboda yanayin aikin shi. kuma ya yi na’am cikin lokaci kaɗan ya buɗe gidan Buɗo. Mun tare a sabon gida bayan ɗaukan shekaru sama da biyar ana ginin shi. Tsarin gidan da komai tsarina ne Yusuf kuma ya yi zanen sanan yan kwangilanshi suka gina gidan da jagorancin.
Tarewarmu a anguwan lodge road. Yusuf ya hana ni aiki ya ce na zauna a gida na huta. Duk da ina da ra’ayin fashion na shiga makarantar koyon kwalliya da gyaran kai. Har zanen shagon da Yusuf zai buɗe mini ya zana amman har yau bai tabbata ba. Amman hidimdimu ba za su bari hakan ya samu ba. Tun da muka koma wannan gidan ƴan’uwansa suke tunanin ina can na samu daula kuma ban haihuwa sai kwanciya ina cin daula sun manta irin gwagwarmayan da muka sha a baya komai Yusuf ya samu ko ya mallaka tare da ni aka mallake shi. Ko bayan tarewarmu a sabon gida sun so ya ƙara aure domin Gimbiya ba ta yi aure ba har Masters ta yi. Da ta ga dai Yallaɓai na Sadiya ne ita kaɗai sai ta hakura ta auri wani tsohon sanata matansa uku ita ce ta huɗu. Ta na can Abuja kuma har ta samu aiki da NGO.
A shekaru sama da goma sha huɗu da wattani da aurena da Yusuf na san me ake kira aure da gwagwamarya. Ba zan ce ba mu taba samun matsala ba mun sha samu tun da ni ina da saurin fushi ga baki shi kuma yana da sanyi wani lokacin amma in ya yi fushi ba shi da kyau. Mun sha samun matsala akan ƴan uwan shi mussaman Anty Bahijja da Anty Maimuna. Daga karshe shi sai ya bi bayan ƴan uwan shi ya bani rashin gaskiya. Nene dai ba na ce ta taɓa nuna mini kiyayya ba. Ban taɓa samun matsala da ita ba shi ya sa na ke yi mata biyayya iya iyawata. Sannan akan zamantakewa ma muna samun matsala amma sai mu shirya kan mu a tsakaninmu. Amman matsalan da muka sha samu da ya yi ƙamari shi ne akan Gimbiya. Ban samu salama ba sai da ta yi aure. Yusuf ya samu kusanci sosai da Gimbiya itama kuma ba ta sakin jiki da kowa sai shi in na nuna fushi ko kishi sai ya ce ina da matsala ina da zargi. Kuma sai ta zo gidan Nene shi kuma in ya je ya biye mata ya kai dare har kwalliyan da na yi sai ya lalace in na yi mgana sai ya ce bai san lokaci ya tafi ba suna can suna hira da Gimbiya. > Janaftybaby: Ban samu salama ba sai da ta yi aure sannan na ji hankalina ya kwanta amman fa da in na ji zai je Rano yini na ke yi zullumi.
Da shekaru suka gangara haka sai nima na fahimci an gogi jigida. Na daina matsa ma kaina kan wasu abubuwan tun da na fahimci ni ba zan ga karshen su ba nima ba za su ga karshe na ba. Sannan irin wannan matsalolin ana samun su a kowani dangi. Sai dai na wata ta fi wata. Nene ce dole ne ita ne kawai ban daina yi ma biyayya ba amman sauran duk abin da na ga zan yi shi na ke yi. Na daina tsoron a ce na yi ko ban yi ba saboda shekaru sun gungura nima wuyana ya isa kaurin da na isa ga kaina. Shi ya sa na ke tafiyar da rayuwata da ga ni sai mijina sai ƴaƴa na. Sauran abin da ya fi ƙarfina na bar ma Allah ni yanzu abu ɗaya ne a gaba na. Ina son na ƙara haihuwa ko domin Yallaɓai mai son yara sosai.
KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.*
07045308523.
*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE*