Turken Gida – Chapter Four
by JanaftySanda su Ma’u suka ɗau hanyar gidansu da ke Rijiyar zaki. Zaune ta ke a bangaren mai zaman banza, kamar ba ita ce ta gama kuka wurjajan ba. Wannan karon mirmishi ne da Annuri ke fitowa daga ƙarƙashin zuciyan Ma’u kuma har ya ke iya bayyana a saman fuskarta.
Mijinta Alhaji Mustapha na tuki, sai ya waiwayo da hankalinsa zuwa kanta a tunaninsa har a lokacin ba ta bar kuka ba, amman ga mamakinsa sai ya ganta zaune tana mirmishi. Cikin mamaki ya ce”Har kin huce kenan Hajiyata?
Kallonsa ta yi ta na ɗan mirmishi kafin ta ce”Me ye a ciki? Ba fa komai Alhajina. Farinciki na ke yi yau Sadiya ta kalleni a matsayin ƴar’uwa. Zuciyata na cike da farincikin da ban taɓa tsintar kaina a ciki ba.”
Ta ƙarishe faɗa fararan haƙoranta na bayyana a waje. Ma’u Fara ce farinta mai irin ja ja ɗin nan ne, taNa da fadin fuska sannan ba ta da tsawo kuma tana da ɗan jiki, sai kibar ta yi mata kyau sosai.
“Ni fa Sadiya ce ke ba ni mamaki har yanzu. Kina ƴar’uwanta haba. Sai ka ce bare ko bare ce ke ai wannan ƙiyayyar ta yi yawa Asma’u. Ni ko da muke haɗuwa ba ta son yi mini magana ban kawo haka ƙiyayyar nata a kan ki ya yi ƙamari ba, na fi danganta haka da halinta ne tunda ko Anty Bahijja za ki ji ta na complain da Matar Tafida ba ta son mutane, ga shi kuma ta auri ɗan dangi.”
Maganarsa ya katse mata tunanin da ta ke yi, kallon shi ta yi mirmishin da ya ke so game da ita. Asma’u ba ta fushi ko an ɓata mata rai yanzu yanzu za ta huce ka ga har tana mirmishi.
“Bakomai Alhajina ai komai ya wuce yanzu. Kuma da man ko lokacin muna gida ni da Rahila mun fi Sadiya son mutane, ita haka take ba ta cika son mutane ba gaskiya.”
“Amman ko halinta ba mai kyau ba ne. Ina mamakin yadda Injiniya ke iya zama da ita da wannan murɗewan na ta.”
Mirmishi Ma’u ta yi masa ba tare da ta ƙara magana ba. Ta gaji da bashi amsa tana Allah Allah ya yi shuru ya maida hankalinsa kan tuƙinsa amman sai da ya juyo da niyar ƙara yin wata mgana sai kuma wayarsa da ke gaban Aljihunsa ta fara ɗaukan sauti alamun ana kiran shi, shi ya katse masa mganarsa sai ya maida hankalinsa kan wayarsa.
“Alhaji Garzali ne..”
Haka ya faɗa sannan ya ɗaga wayar. Mirmishin gefen kawai ta yi, ya na waya hannunsa ɗaya na saman sitiyari hankalinsa rabi na kan waya rabi na kan tuƙi, shi ya sa ma ya rage gudun motar sai aka ci kuma sa’a dare ya yi sosai ba yalwar giftawan motoci sosai.
Ƙuri Ma’u ta yi masa da ido, tana ƙare masa kallo. Alhaji Mustapha ba zaɓin ta ba ne, ba kuma shi ne muradinta da mafarkinta ba. Ba domin Sadiya ba da ƙila yanzu ita ce a gidan Yaya Hamza kuma ita ce mahaifiyarsu su Afnan ba Khaleesat ba, ba domin Sadiya ta yi mata baƙin ciki ba da yanzu ba ta auri wannan magidajen kanon ba. Shi ya sa har gobe wannan dafin da Sadiya ta bar mata ya kasa ɓacewa daga cikin zuciyarta. So ta ke yi ko da ƙwatanƙwacin irin baƙin cikin da ta ji ne, itama Sadiya ta ɗanɗani irin shi ta ji in da daɗi.
“Ma’u..Ma’u..”
Muryan Alhajin nata ya katse mata tunani, sai ta dawo da ƙwayan idanuwanta a kansa, daman can sunan ta na kallon shi ne amman tunaninta da hankalinta ba su a kansa kwata kwata.
“Tunanin me kike yi haka? Ina ta magana kin yi shuru?
Basarwa ta yi kafin ta yi mirmishin da ta san ya na sace zuciyansa.
“Tunaninka na ke yi mana My Alhaji.”
Ta faɗa lokaci ɗaya ta na yi masa fari da wani kallo da shi kaɗai ta san yana kunna shi, aiko sai ga shi ya ke ce da wata dariyan nishaɗi kafin ya buga sitiyari lokaci ɗaya yana faɗin” Ma’u. Ma’u na, ba ki da dama.”
Mirmishi ta sake yi tana kara narke masa, dariyan ya sake yi kafin ya ce”Alhaji Ghali na gaishe da Amarya Ma’u.”
Cikin yar dariya ta ce”Ina amswa. Ya iyalan nasa? Ya amsa mata da suna lafiya kafin ya ɗora da faɗin” Kin san ko har gobe in na je gidan sai Hajiya Fati ta yi mini tsiyan ba ki zo mata Allah ya sanya alheri ba, lokacin bikin ƴa’ƴanta.” > Janaftybaby: Kai tsaye Ma’u ta ce”Ayya. Ba ka gaya mata bana nan ba ne lokacin? Kuma ai Hajiya ta je ta wakilceni”
Ya na dariya ya ce”Nima haka na ce, da Hajiya da Ma’u duk abu ɗaya ne a waje na.”
Taɓe baki ta yi, a farko sannan ta ɗan saki fuska kaɗan. Hira ya cigaba da yi mata, sai faman taɓe baki ta ke yi, in zai juyo sai ta sakar masa lallausan mirmishin da ta san ya na kunna sa har cikin zuciyarsa.
Kanta ta maida jikin window din motar tana kallon hanya har ga Allah ba ta son surutu, surutun ma a wajen Namiji, ba haka ta so mijin auranta ya kasance ba, ta na son namiji mai Aji da kamewa amman mai ake yi da gidahumin namiji, waiwayawa ta yi ta na ƙara kallon Mijin nata wani abu da ya daɗe da tokare mata zuciya duk sanda ta kalleshi a matsayin mijinta ya sake ta so mata. To ta san ba ta san shi me ya sa ta aure shi?
Ba saboda kowa ba ne sai Saboda da BAABA. da kuma KUƊI. Ba domin kuɗin Alhaji Mustpha ba, da ko hanya ba za ta iya haɗawa da shi ba, tunda ya yi yamma da irin zaɓin mijin da ta daɗe tana mafarkin samu. Alhaji Mustpaha irin ƙauyawan kanawan nan ne, shi bai yi boko ba sai arabi, amman fa ya san kan kasuwanci yana kasuwancin Fata sannan kuma ɗan chajin ne, yana da kuɗi sosai. Kuma mahaifinsa ma har ya mutu sana’ar fata ya ke yi, shi ya sa zuru’arsu ke da kuɗi, amman bayan nan mugun bagidajen ƙauye ne, mara lissafi. Sannan ita ba ta taɓa hango kanta a matsayin macen da za ta yi aure ta zo a mace ta biyu, ta tsani zama da kishiya a rayuwarta saboda mahaifiyarta tun auranta na fari ba ta ji daɗin kishiya ba, kafin ta zo ta auri mahaifinta mutuwa ta zo ta raba, sannan a auranta na uku ma gidan kishiyiyon ta je, da har gobe ba ta huta ba. Shi ya sa ta yi fatan samun gidanta ita kaɗai ta gina shi duk yadda ta ga dama ba wai ya kasance ita ce zata shiga gidan da wata ta gina ba.
Amman kaddara ta riga fata, ko da ya ke Sadiya ce ta sauya mata kaddaranta. Domin saura ƙiris ta cika mafarkinta ta yi sanadiyar lalata komai, shi ya sa itama ba ta da wani buri sai na ganin ta lalata ma Sadiya jin daɗin duniyarta ta gigita mata rayuwarta yadda ƙwatankwacin yadda ba ta samu abin da ta ke so ba, itama ba ta fatan Sadiya ta cigaba da samun abin da ta ke so, in ma ta samu to za ta yi sanadiyar lalata shi ya zama baƙinciki a gare ta. Tana da burika da dama akan Sadiya waɗanda ko kwatansu ba ta cika ba. Nasara a kan Sadiya yanzu ta fara yi in a baya ita ta ta yi kuskuren barin Sadiya yin nasara a kanta wannan ƙarnin baya ne da ya shuɗe. Wannan ƙarnin na yanzu ita ce za ta cigaba da samun nasara akan Sadiya daga nan har abadan.
Ba ta ma san sun iso gida ba, sai da ta ji yana hon sannan ta farga da har sun iso gida, gidan Asma’u ƙaton gida ne mai kama da Aljannar duniya, amman duk wannan daular ba ya gabanta matukar ba ta ɗanɗana ma Sadiya irin ɗacin da ta ke ji a cikin zuciyarta ba, ba za ta taɓa samun kwanciyar hankali ba.
Ita ta fara yin gaba zuwa cikin gida. Ta bar Alhajinta na magana da megadi, a falon gidan ta ci karo da ƙanwarta Zainab ƴar kimanin shekaru 16 zuwa 17, da ke hannunta tana zaune ta na kallo, abin sai ya ba ta mamaki ta na ganinta ta yi saurin miƙewa tana sosai ido, wani kallo Ma’u ta yi mata kafin ta ce”Uban me kike yi har yanzu ba ki yi barci ba?
Cikin In ina Zainab ta fara faɗin” Ina. Ina. Kallo ne.”
Kafin Ma’u ta samu zarafin magana Alhaji Mustapha ya shigo falon kawai sai ta fasa maganar da za ta yi sai ma ta kalleta tana faɗin” Kin tabbatar da kin saka su Baba ƙarami sun yi fitsari kafin su kwanta ko?
Da sauri ta ɗaga kanta, Alhaji Mustapha na tambayan me ya faru? Ba ta tsaya bashi amsa ba ta kama hanyar ɗakinta lokaci ɗaya ta na faɗin” Ki kashe kallon nan ki je ki kwanta.”
Daga haka ta shihe koridon da zai sada ta da ɗakin barcinta a ƙasan ranta ta na ji kamar ta ce Alhaji ya je gidan Hajiya yau ba ta cikin Mood ɗin da za ta iya dauriyan kwana dashi. > Janaftybaby: Shi ya sa ta na shiga ɗakin barcin na ta ta maida ƙofa ta rufe. Wayarta ta sauke nan saman gadon da mayafinta sannan ta buɗe kofar tiolet ta shiga wanka za ta yi, ta na cikin wankan ta ji Alhajin nata na ƙwanƙwasa mata kofar, tsaki ta ja a fili da ɓoye wani abu na suƙan zuciyarta dagacan ƙasa.
Ta na fitowa ɗaure da Towel, har lokacin bai tafi ba ko ya tafin ma ya sake dawowa.
“Ma’u. Ma’u ta,..’
Tsaki kawai ta ƙara ja a fili sannan ta isa ga kofar ta murza key, ta na buɗewa kawai ta juya ta dawo cikin ɗakin gaban madubin da ke shake da kayan kwalliya ta tsaya shi kuma cikin jallabiya ya shigo yana mai washe baki.
“Au wanka kike yi ne?
Juyowa ta yi sannan ta gyaɗa masa kai tana mirmishi, shi kuma sai ya rumgumota ta baya fuskarsa da nata na bayyana ta cikin madubin, Asma’u ta yi mirmishi, mirmishin da a saman leɓenta kawai ya tsaya, tana kallon Alhaji Mustapha kansa har ya fara furfusa ga uban sauƙo, a fuskarta mirmishi ne, amman a ƙasan zuciyarta ƙuna ne da wani irin turiri da ya ke ta so mata.
Ita ko za ta iya yafe ma Sadiya? Kai ina sai ta gigita rayuwar Sadiya. Sai ta yi sadiyar zama sanadin da farincikin Sadiya zai yanke na har abada. Yadda ita ba ta zauna ita kaɗai ba, itama Sadiya burinta ba zai cika ba, sai ta gayyato mata damuwowi masu tarin yawa a rayuwarta wannan alƙwarin ASMA’U SULAIMAN YASHE ce.
**
*BAYAN KWANA HUƊU*
LODGE ROAD.
JUMMA’A.
Karfe 7:40am na safe Salisu ya zo ya ɗauki su Jidda zuwa makaranta. Suna tafiya ban huta ba na shiga ɗakinsu ina haɗa musu kayansu, na zuwa gidan Anty Maimuna ko jiya sai da ta kirani a waya tana gwaɓa mini magana wai wannan satin ma hala gidanmu za su je? Ban biye mata ba na ce yau in sha Allahu za su zo.
A ƙaramar jakar baya na Jidda na haɗa musu kayansu da duk abin da za su buƙata, tiolet na shiga na ɗauko musu brush na fito kenan sai na ga Yusuf zaune a gefen gadon su Jidda.
Sanye yake da jallabiya. Tun bayan dawowarsa sallar asuba ya kwanta ban ma san ya tashi ba.
Tsayawa na yi sororo ina kallon shi kafin na yi mirmishi na ƙariso ina faɗin”Har ka tashi?
Miƙewa ya yi ya zo gabana ya buɗe min hannuwansa na faɗa ya rumgumeni yana faɗin” Ina kwana Sadiya ta.”
Na amsa ina sakin sa kafin na ce”Na ga barcin ka ya yi nisa shi ya sa na ce su Jidda kar su tashe ka, su tafi kawai.”
Ya na tsaye ya harɗe hannuwansa a saman kirjinsa ni kuma sai na duka ina saka musu brush ɗin su a cikin jakan da na haɗa musu kaya.
“Kayan me ye wannan?
Ina duƙe na ce” Kayan su Jidda ne.
“Na zuwa ina kuma?
Sai da na ɗago sannan na kallesa kafin na ce”Gidan Anty Maimuna. Wancan satin kasan ba su samu zuwa ba.”
Sai a lokacin ya ce”Oh. Na tuna ko jiya da na je gida Nene sai da ta yi min magana. Wai Anty Maimuna na ta faɗa.”
Ina kallon idanuwansa na ce”Wai faɗan me?
Taɓe baki ya yi kafin ya ce”Ban sani ba, amman ta tambayeni me ya hanasu zuwa wancan satin na ce ma Nene ban sani ba.”
Baki kawai na saki ina kallon shi, wai bai sani ba, Me ya sa Yusuf ya ke yi mini haka ne? Yadda ya ga ina kallonsa ne ya sa ya fara dariya, ya matso ya riƙeni na matsa baya ina haɗe rai kafin na ce”Ba ka sani ba ko? To ai ya yi kyau.”
Ina gama faɗin haka na juya na bar masa ɗakin. Wai ni haka maza suke ko nawa mijin ne haka? Sau tari wasu laifuffukan da danginshi ke kallona da shi har da laifin shi, sai a yi abu kuma ya san dalilin faruwan shi amman in suka tare shi da maganar sai ya ce bai sani ba, kuma na yi masa ƙorafi har na gaji ya kasa dainawa, in na yi magana sai ya ce ai bai sani ba ne, ko game da zuwa sha’anin dangin shi, gajiya suka yi suka ƙyaleni, da suka fahimci ba ma su kaɗai ba hatta nawa dangin ba kasafai na ke shiga ba, ganewan suka yi ko gajiya suka yi da abu ɗaya suka kyaleni ban sanin musu ba.
Kitchen na koma, daman yara saboda yau jumma’a ne drink suka tafi da shi da Bicuit, sai tea da suka sha da biredi kafin su tafi, doya na fara ferewa zan soya mu sha tea da shi, ina feran doyan ya shigo kitchen ɗin yana faɗin”Fushi kika yi?
Banza dashi na yi, saboda ya ba ni haushi, burin sa na yi ta laifi a idon danginsa shi kuma ya na jin daɗi. > Janaftybaby: Zuwa ya yi ya rumgumeni ta baya. Lokaci ɗaya yana ɗora kansa saman kafaɗana bayan ya rankwafa.
“Sorry, kin ji ko?
Taɓe baki na yi kafin na ce”Ba dai da man so kake yi ko da yaushe na zama mai laifi a wajen ƴan’uwanka ba? To ai shikenan.”
Matse cikina ya yi da hannayensa da ya saƙalo ta cikina. Sannan da ƴar murya ya ce” To ai na ce ne ban sani ba, kin sani da yawan mantuwa.”
Mirmishin gefen baki kawai na yi, ba tare da na yi magana ba ya yi ta taƙalan mgana da ni na yi masa gim daga e, sai a’a kawai na ke amsa masa, sanin halina ya san in raina ya baci haka na ke yi sai ya sake ni yana faɗin” Bari na je na yi wanka. Zan je Rano.”
Sai da na ji ya ambaci Rano sannan na ɗago ina kallonsa kafin na ce”Uncle Abba bai kira ka ba?
Kai ya girgiza kafin ya ce” Ya kirani amman bai yi mini maganar ba, amman in mun haɗu zan tuna masa.”
Kai na jinjina, ba tare da na yi magana ba shi kuma ya fice daga kitchen ɗin, bayan ya rufo mini ƙofar. Na bi shi da kallo kawai, a baya ne ba na ƙaunar na ji ya ce zai je Rano duk da tushen shi ne, saboda GIMBIYA, amman tunda yanzu ta yi aure ban damu da yawan zuwan shi ba, in na yi duba da irin ayyukansa na kwangilan gine gine in an samu yana zuwa ko Uncle Abba ya yi masa hanya, tun da shi har gobe ya na garin Rano kuma a nan ya gina ƙaton gida duk da bai yi aure ba.
Gun bayan lamarin da ya faru tsakani na da Ma’u da yadda Alhajinmu ya goya mata baya. Tun da na dawo gida ban wani saki ba, ko Jidda sai da ta ce Umma ko ba ki da lafiya ne? Gabaɗaya zuciyata ba ta mini daɗi, ballatana da gabaɗaya ƴan gidanmu suka goya ma Ma’u baya, Yaya Hamza ne kaɗai bai shiga maganar ba shi daman sai a yi abu goma bai saka baki ba, mutum ne mai fahimta shi ya sa ko a baya nake ƙaunar Yaya Hamza saboda hallayarsa ɗaya ne a cikin dubu. Shi da Yaya Auwalu za a daɗe ana abu ba su maida kai ba.
Yaya Abubakar har sake kirana ya yi, bayan na ɗauka zagina ne kawai bai yi ba akan Ma’u. Su Yaya Murja kar a ji labari. Yaya Aina har cewa ta yi za ta iya yanke ni akan Ma’u.
A group ɗin Gidanmu an fi kwana uku maganar kawai ake tattaunawa. Ban san ina suka samu cikakken bayanin abin da ya wakana tsakaninmu da Alhajimu ba, sai ga shi Yaya Murja na maida yarda aka yi, to har na yi mamaki Ma’u ce ta faɗa mata ta na jin daɗi haka. Yaya Aina har ta na cewa gwara da Alhajinmu ya yi min haka ƙila zan shiga tairayina.
A mganar nan mutane biyu ne suka ce nima ya kamata a duba maganata ƙawar Ma’u ta yi magana domin tozarci. Yaya Balki da Amina. Sauran kuma duk iyalan Ma’u ne, shi ya sa nima na sauya musu matsayi. Rahila dai ba ta saka baki ba wannan karon, domin ta san halina wallahi sai na yanketa. Sai na yi amfani da shawaran da na yanke a cikin zuciyata akan na shiga na yi magana na ƙara ba ma Ma’u hakuri a gaban kowa kamar yadda take yi min amman munafuki shi daman a koda yaushe yana shirye ne.
Sai kawai ta rigani shiga ta yi magana, hakuri ta ba ma kowa sannan ta ce a bar maganar daga karshe ta yi tagging ɗina kafin ta ce”Komai ya wuce, zumunci da ni da Sadiya har aljannah ko ƴar’uwata?
Ban yi wani mamaki ba, sanin ba tun yau ba Ma’u ta kware a iya acting ba sai nima na fito muka yi acting ɗin a tare, kai tsaye na ce”Kowa ya yi hakuri mun daidaita barakan dake tsakaninmu da ƴar’uwata Asma’u.”
Sai gashi sun fito suna murna, Yaya Murja ni kaɗai nasan haushinta da nake ji, har da cewa Allah Sarki Ma’u mai hakuri ce daman, ke kuma Sadiya a rage zafin zuciya. Ita da Yaya Abubakar Ma’u kamar ƙanwar uwarsu, ko da ya ke shi Yaya Abubakar akwai tsohuwar soyayya, ita kuma Yaya Murja har da son abin duniya, tunda Mijin Ma’u na da kuɗi ana zuwa ana maula dole ta riƙa zama mai goyon bayanta, ni fa a gidanmu na riga na san halin kowa sannan na yi ma kowa wajen zamansa wallahi.
Har na gama soya doya raina a ɓace ya ke, na kwashi komai zuwa Dinning, sannan na koma Bedroom sai na iske Yusuf suna waya da Uncle Abba sai na ce ya ba ni mu yi magana kan dai maganar fara zuwa na ganin likita asibitin Shika dake Zaria ne. Sai ya ce sun sake magana da Dr. Fadel ya ce in ta bashi lokaci zai kira mu ya sanar da mu. > Janaftybaby: “Ki kwantar da hankalinki Sadiyan Yallaɓai. Da zaran ta saka lokacin ganin ki zan sanar ma Tafida kin ji ko?
Sai na gyaɗa masa kai kamar ya na ganina sannan muka yi sallama na miƙa ma Yusuf wayarsa. Tiolet na shiga nima na fara wanka ko da na fito baya falon. Sai na samu daman shiryawa a tsanake.
Riga da wando na saka na material Daman ni in dai ba fita zan yi ba, ba na saka kaya masu nauyi.
Kalan kayan maroon ne, sai na yi amfani da bakar hula mai raga raga, kaina har lokacin ban yi kitso ba mai zuwa har gida ta yi mini kitso ta yi tafiya ne, ni kuma ko sake wanke shi a gida ban yi ba, tunda na iya ina da kayan wanke kan, har su Jidda ni nakan wanke musu kai na gyara musu.
Takalmin gidana mai taushi na saka bayan na fesa turare mai ƙamshi na fita zuwa falo Yusuf na jira na mu karya sannan ya fita. Ni na zuba masa doyan sannan na haɗa masa tea ɗin, sannan na haɗa ma kaina na zauna kujeran gefensa.
Ban ɗaure fuska ba amman ban kuma saki fuskar ba, ganin yanayina yasa sai ya rika takala na da magana sai dai in bishi da ido kawai.
“Ko za ki shirya yau ki je ki gaida Nene, in na dawo daga Rano sai na biya ta gida mu dawo tare.”
Kai na gyaɗa kafin na ce”To shikenan sai na shirya na je ɗin.”
Yana mirmishi ya shafa kumatuna kafin ya ce”To a saki fuskar, shan kunin ya isa haka.”
Kalamansa suka ba ni dariya, sai na murmusa, mun cigaba da karyawa mun gama kenan na kallesa ina faɗin”Wata kwangilar a ka samu a Rano kuma?
Ya na miƙewa ya ce”Ban sani ba. Abba ya ce na shigo mu je mu gani.”
Sai na gyaɗa kaina kafin na ce” Allah ya sa a dace? To su dai waɗancan masu payment ɗin shuru ko?
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce”Wallahi shuru. Amman ban cire rai ba tun da sun ce ko da yaushe zan iya jin su.” Fatan alheri na yi masa amman ban yi ɗoki ba domin ni nasan yanayin aikin shi, sai a yi shekara ana cewa za a biya shuru amman fa aka biya muna warkewa masha Allah tunda kuɗi ne ba kaɗan ba, kuma in aka samu aikin ana yin shi muna shiga hali tunda kuɗin shi zai ɗauka ya yi amfani dashi a karkashin kamfaninsa na HM. TAFIDA AND SON’S LIMITED. office ɗinsa na can hanyar zoo road kan titin Zaria Road.
Ni na raka shi har bakin mota kamar yadda muka saba, ya ba ni 2k ya ce na hau adaidaita zuwa gidansu da ke Gwammaja, muka rabu bayan ya rumgumeni ya sumbaceni, nima na maida masa martani, yana ɗaga min hannu nima ina ɗaga masa da fatan Allah ya kai shi lafiya ya dawo mini dashi lafiya.
Bayan tafiyarsa na koma cikin gida, falon farko na zauna saboda ka da Saude ta zo ta yi ta buga gida ina ciki ban sani ba, sai na kunna kallo tunda akwai wuta a tashar arewa 24 suna haskawa wani film hausa mai suna Ahalil kitab duk da na kalli Film din amman ina son waƙoƙin ciki sai na zauna ina kallo har na ji buga gida na je na buɗe ma Saude muka shigo tare, na zauna na cigaba da kallona ita kuma ta fara aikinta.
Kafin azahar ta gama min komai, ni har barci ma na yi a saman kujera anan falo da za ta tafi na ba ta 500 na ce ta hau abin hawa, tafiyarta ba dadewa su Jidda suka dawo daman na yi ma Salisu maganan zai kai su Alu Venue anguwan su Anty Maimuna sai ya ce mini bari ya je ya yi sallar jumma’a ya dawo kan nan sun shirya.
Sai murna suke yi tunda na ce can za su yi Weekend,tunda akwai jikokin yarta na fari Mardiya suna wajen Anty Maimunan ne sa’anin Baby ne, sannan autan ta ma sa’ar Jidda ne Afiyatu.
Ban yi musu girki ba, Coorfleck na ce su sha bayan sun sauya kaya sun yi sallah. Kayan su suka saka iri ɗaya shadda mai ruwan ƙasa da na ɗinka musu da sallah da ta wuce da mayafansu, iri ɗaya har takalminsu iri ɗaya ne, na faɗa ma Jidda su yi kitso a can saboda na san ba da wuri za su dawo ba. Ban san me ya sa Anty Maimuna ta ke kulafacin su Jidda ba, ko don Baby ita aka yi ma takwara? Ko kuma daman can ita mai son yara ce gaskiya. > Janaftybaby: Ɗaya da rabi na rana Salisu ya dawo ya ɗauke su suka tafi. Suna tafiya nima na shirya na saka wata atamfata hollad mai ruwan ganye, sai na yi amfani da green ɗin mayafi jaka da takalmina kuma na saka baƙi, key ɗin gidan da na ɗauka sai da na tabbatar da na kashe komai na wuta sannan na fita na rufe get ɗin da makulli, ban samu adai daita ba sai da na taka zuwa babban titi, anguwan shuru daman haka take to ta masu kuɗi ce, kowa na gidajenshi shi ya sa ƙawa ko ɗaya ban da shi a rukunin nan sun shigomin lokacin da muka tare amman ni da ya ke halina sai ni sau ɗaya na taba shiga gidan gefen mu gidan maman muhsana, da ta haihu na yi barka. Allah ya halliceni mace mara sson shige ma mutane, ko yan gidanmu in ba wani abu ya faru ba, ba kasafai nake zuwa ba, gwara na yi zama na a gida in yi barci ya fiye minim
Drop na ɗauka zuwa Gwammaja. Muna tafe na ji wayata na ringing a jaka na ɗaukota na duba sai na ga Zaituna ce Matar Yaya Abubakar. Na yi mamakin ganin kiranta domin ni dai ban wani yi da ita na fi yi da Anty Khaleesat ɗin Yaya Hamza. Ita Zaituna akwai kwaɗayi da surutu da an ce kace kace shi ya sa ban cika sakin mata ba, sannan daman ina jin haushin mijinta shi ya sa na ɗauka a dakune ban sakar mata fuska ba.
Bayan mun gaisa, sai na yi shuru ina jiran abin da za ta ce.
“Kina gida ne Sadiya?
Yamutsa na yi kafin na ce”A’ah me ya faru?
Kai tsaye ta ce”Ayya daman ina kusa da anguwarku ne, mun zo suna gidan wata ƴar’uwarmu ne, na ce bari in kira ki in kina gida, sai na biyo.”
Daga yanayin yadda take magana kamar a wahale, na fi tunanin ƙila sun je ne ma ba abinci za ta ce ina kusa bari ta kirani ta daɓo gayyar danginta su zo min gida, na ji daɗi da ba na gida saboda ita ma Zaituna ƴar ƙashin bayan Ma’u ce.
“Ai ko ba na gida, ina hanya za ni Gwammaja gidan su Yallaɓai.”
Sai ta ce to shike nan, daman ta ɗauka ina gida ne, daga nan muka yi sallama.
Na kashe wayata ina hararan wayar kamar ita ce a ciki, na tuna ko faɗan da muka yi da Ma’u a gidan Rahila, suna yan gaba gaban saka bakin cewa ni ce ba ni da gaskiya.
Wayata na mayar jaka, ni kaɗai ina ƙunƙuni ni fa su san halina duk wanda ya ci tuwo da ni wallahi miya ya sha, ga su ga Ma’un duk za su ci ubansu.
Mai adaidaita bai direni ko’ina ba sai ƙofar gidan Iyayen Mijina da ke Anguwan Gwamnaja. Na sauko daga adaidaitan ina miƙa mi shi kuɗin shi na ji an kira sunana.
“Anty Sadiya..”
Ina juyawa sai na ga Adnan ne, sai da na sallami mai adaidaitan ya tafi sannan na nufe shi, ya na tsaye a ƙofar gidan shi da abokonsa guda biyu sun sha manya kaya ƙila daga masallacin jumma’a suke.
“Adnan manyan kasa, yaushe a gari?
Na faɗa ina kallonsa yana dariya ya ce”Jiya na shigo garin. Ina su Jidda?
Ina amsa masa da cewa sun tafi gidan Anty Maimuna, abokansa suka gaisheni na amsa, jakar hannuna ya karɓa muka jera zuwa get ɗin gidan.
Gidan Marigayi Alhaji Muhammad Inuwa babban gida ne, mai bene sama da ƙasa. Ko haraban gidan wargajeje ne, duk da mai gidan ya fi shekara ashirin da rasuwa, gidan bai rankwafa ba, saboda ya hayyafa, kuma ƴa’ƴa sun tasa, in wannan bai kawo ba wannan zai kawo, shi ya sa ƙyallin gidan har gobe bai daina haskawa ba.
Muna tafe ne zuwa cikin gida Adnan na yi min hira makaranta. A ABU ZARIA ya ke karatunsa na Engniaring, a tsakar gidan muka ga Jawahir na shanyan ƙananun kayanta da ta wanke.
Tana ganina ta washe baki ta na faɗin” Anty Sadiya.”
Na amsa ina faɗin”Au kema kin zo hutun ne? Ko guduwa kika yi?
Dariya ta saka tana faɗin” Kai Anty Sadiya, da ne fa yanzu ai mun zama ƴan makaranta.”
Adnan ya ce”Tunda ba ki son bokon ki yi aure mana ko Anty Sadiya? Kai na gyaɗa ban yi magana ba Jawahir ta balla ma Adnan harara lokaci ɗaya ta na faɗin” To ai sai ka zo ka yi min auran ubana.”
Yana ƴar dariya kafin ya ce”Ko ba ki faɗa ni ubanki ne, domin zan iya ɗaura miki aure.”
Suka kacame da gaddamansu na saƙo da saƙo ni kuma ina ta dariya. Jakata na karɓa hannun Adnan ina faɗin”Bari na karisa, su Hajiya Iya ba sa nan ne na ji gidan shuru? > Janaftybaby: Jawahir ta ce” Maman Farko ba ta nan an yi musu rasuwa, Iya kuma ta kwanta ne Nene kuma ki haura sama ta na ciki.”
Wuce su na yi, na bar su suna musu, ya na cewa shi ubanta ne, ita kuma ta na cewa Allah ya kyauta ya zama babanta.
Shashen ƙasa Hajiya Iya ne da Mahaifiyar su Jawahir marigiyayiya Hajiya karima Allah ya jiƙanta, sama kuma Hajiya Nene da Maman Farko suke bangaren sama, amman a ƙasa akwai ɗakunan baki daga can haraba kuma akwai ɗakunan mazan gidan.
Sama na haura, ƙofar shashen Nene ne a farko tun kafin na shiga na jiyo hayaniya, ina sallama bayan na cire takalmi na sannan na shiga babban falon na Nene. Hauwa na gani zaune a falon sai fama take yi da yara, Hauwa matar ƙanin Yusuf ne mai bi masa, Muttaƙa. Sai ƴaƴan Halima da su ban ga uwarsu ba, ina ga su kaɗai aka kawo Nene ba ta falon ma gabaɗaya.
Hauwa na ganina ta tare ni da mirmishi, karamar ƴarta, Sahla ta nufoni ta na min oyoyo na taro ta ina ƴar dariya saboda yarinyar ta gane ni, duk in da ta gani ta riƙa gwarancin mgana kenan, suna zuwa gidana sosai nima ina zuwa saboda Hauwa tawa ce, duk cikin Facalolin gidan ba ni da kamar Hauwa.
A bangaren Matan gidan ba ni ba ce Babba ba, akwai Matar Yaya Usman Zabba’u, sai ni sannan Muniran Yaya Nasir sai Hauwa da tsakanin auren mu da na su shekara shidda ne. Amman ina son Hauwa saboda muna da kamaceceniyar hallaya, ba ruwanta tana da sanyin hali duk da yar uwa ce tun da ƴar rano ce a can Mutaƙƙa ya auro ta.
Gaisawa muka yi faram faram kamar yadda muka saba in mun haɗu.
“Ina Nene?
Sai ta ce mini ta shiga ciki ta kwanta.
Yaran Halima na kallah kafin na ce”Tare da Haliman suke? Na ga ban ganta ba?
Sai ta ce mini “A’a su kaɗai baban ya kawo ya ce Haliman ba ta jin daɗi”
Sai na ce Allah ya sauwake, sai da na ji Hauwa na faɗin ƙila ma Haihuwa ce.
Baki na saki domin ni har ga Allah ban san tana da ciki ba, har sai da na furta ma Hauwa. Ta na dariya ta ce” Kin daɗe baki ganta ba ne? Ni mun haɗu a walimar sabon gidan Anty Suwaiba, a can ne na ganta da cikin”.
Kai na jinjina kafin na ce” Ni kin san ban samu zuwa ba.”
Sai ta gyaɗa min kai, hira muka cigaba yi, amman hankalin Hauwa na ga yara, ita yayanta huɗu, sauran ta ce suna gida tare da babansu da Sahla kawai ta zo amman sai wahala take yi da yayan Halima da ba sa jin mgana.
Muna zaune muna hira Walid da wayonsa ya fi shekara biyar ya yi fitsari a cafet, mamaki ya isheni ganin Hauwa ta miƙe jikinta na rawa ta na masa faɗan me ya sa ya yi fitsari a zaune bai zai yi magana ba?
Sai kawai yaron nan ya fasa kuka ya nufi bedroom ɗin Nene, na saki baki galala ina kallon abin mamaki.
Ina kallo Hauwa ta je ta diɓo ruwa ta zo da towel tana tsane fitsarin ina zaune ko motsi ban yi ba, na yi wannan wahalar a baya amman ban yi wahalan ƴaƴan ƙannen miji da yayyensa ba, na yi dai na uwar mijina a baya amman a yanzu wallahi na daina, in ba a gode na baya ba a barshi.
Falon duk sun yi kaca kaca dashi sai da ta share, sannan ta dawo ta zauna Walid dai tun da ya shiga bai fito ba, Salha da Afra kuma Hauwa ta ce su sauka kasa su je wajen Anty Jawahir.
Sai da suka bar falon sannan na kalleta kafin na ce”Wai sannu da aiki.”
Mirmishi ta yi mini ba ta yi magana ba..ni kuma da ban iya shuru na ce”Ke wai har yanzu ba ki daina wannan wahalan ba? Uwarsu na can gida tana hutawa, ke kin baro na ki yayan wajen ubansu, kuma kin zo nan kina hidiman na wasu.”
Dariya ta yi kafin ta ce”Kai Anty Sadiya ba ki da dama.”
Daman haka ta kan kirani, kai na girgiza kafin na ce”Tab. Wallahi Hauwa ba ƙanwar miji ko y’ar mijin da zan yi ma bauta, na yi ma mahaifiyarsa ita ce dole na, ko ita na yi a baya yanzun ma sai abin da ba a rasa ba.”
> Janaftybaby: Ni ba kaina na damu dashi ba saboda ban samu miji ba daman kuma ni burina sai na gama jami’a zan yi aure.
Muna gabda gama zana jarabawarmu kawai Yaya Abubakar ya fara wani ciwo har da kwanciya a gadon asibiti ganin haka yasa na ce ba zan bari Ma’u ta kashe mini ɗan’uwa.
Ni na je na samu Hajiya Dubu na faɗa mata duk abin da na sani. Ita kuma ta samu Alhajinmu ta faɗa masa abinda ke faruwa ni na ba da shaidar Gwaggo ma ta sani da aka kirata sai ta amsa amman ta ce Abubakar ɗin ya ce a bar mganar kar kowa ya sani kuma itama tana ta tabbacin ciwon nan saboda Ma’u ne. Alhajinmu bai yanke hukunci ba sai aka sallamo Yaya Abubakar daga asibiti Alhajinmu ya taramu a gaban kowa da kowa har da masu auran da Yaya Hamza da Alhaji ya sa ya dawo garin.
A gaban kowa da kowa ya tsitsiye Yaya Abubakar sai da ya faɗi gaskiyan yana son Ma’u duk yadda ta yi ta masa inkiya da ido kar ya faɗa. Har Baaba an kirata tana wajen jin haka shima Yaya Hamza ya ce ya bar ma ɗan uwansa shi daman baya sonta.
Hankalin Ma’u da Baba ya tashi saboda Alhajinmu ya ce an maida auran Ma’u akan Yaya Abubakar kuma ya yi ta faɗan cewa ba domin na zo na faɗa ba da an yi auren kuma azo ana neman mafita. Ban manta kallon da Ma’u ta yi mini a wannan lokacin ita da Baaba. A kuma nan take ta fashe da kuka ta ce ba ta son Yaya Abubakar Yaya Hamza take so shi kuma ya ce a ƙanwa ya ɗauketa. Alhaji ya rasa mafita yace zai yi mgana da sauran yan uwanshi. Har sai da su Baba Aminu su ka zo garin. A ɗakin Hajiya suka zazzauna suka tattauna Hajiya Dubu saboda samar da masahala sai ta kalli Alhaji kafin ta ce
“Sule a shawarata kar ka matsa ma Ma’u ko Hamza. Tun da Hamza ya ce baya so. Abubakar ma yace ya hakura da ita to mu fasa wannan al’amarin kowanensu ya nemo mata itama ta nemo nata mijin mu aura musu sai na ke ganin kamar in muka yi haka za a samu mafita.”
Su Baba Aminu ma sun aminta da shawaran Hajiya kuma ita Alhaji ya ɗauka aka warware mganar auran Ma’u da Yaya Hamza har da Yaya Abubakar ɗin bayan an ce kowannen su ya zaɓo na shi matar daga waje. Wannan lamarin shi ya ƙara rura wutar kiyayya tsakani da Asma’u.
Kwana biyu da faruwan lamarin na samu salama saboda ko banza itama ba ta samu abin da take so ba. Sannan Yaya Abubakar ba zai ga laifin Yaya Hamza ba. Ina kwance a saman gadon Hajiya ba ta ɗakin tana makewayi Ma’u ta shigo har ɗakin ta tsaya a kaina.
“Lafiya Ma’u?
Idanuwanta jajir ta kalleni kafin ta fara mgana cikin zafi.”
“Wallahi na tsane ki Sadiya. Na tsane ki.”
Nima kai tsaye na ce” To ai nima ba sonki nake yi ba Ma’u.”
Sai kawai ta nuna ni da yatsa kafin ta ce” Tun da kika zama silan rasa burina Sadiya ina so ki rubuta ki ijiye na rantse da sarkin da ke busamin numfashi sai na kuntata ma rayuwarki sai na saka ki a uku fiye da yadda kika sakani ko kin samu farinciki sai na yi sanadiyar lalatashi zuwa baƙin ciki. Kamar yadda na saba cin nasara akanki haka zan cigaba da nasara akanki har ƙarshen rayuwarki.”.
Kai tsaye nima na kalleta kafin na ce”To in kin fasa. Ta Allah ba ta ki ba. Aniyar ki sai dai ta biki. Kuma ban yi nadaman abin da na yi ba. Da ki ɓata mana zuru’a gwara ke ki rasa na ki burin na zalunci.”
Sai kawai ta yi kwafa ta fice a ƙofar ɗaki suka haɗu da Hajiya tana kiran sunanta ta yi banza ta wuce da ta shigo sai ta tambaye ni ko mun yi faɗa da Ma’u ne? Ina komawa na kwanta na ce” Ni ina ruwana da ita.”
Hajiya na faɗin” Sai hakuri ki rika kyaleta yanzu kin san ga abin da ya faru.’
Ina jinta ban tanka ba.
Tun faruwan lamarin bayan wani lokaci Ma’u ta warware Yaya Abubakar ɗin ma da sauƙi. Ta nuna ma kowa ba komai amman ni nasan ba ta hakura ba. Tsakanina da ita sai ya ƙara lalacewa. Ko da yaushe in ta fakaici idon mutane sai ta gaya min mgana nima sai na rama haka dai muka yi rayu cikin bata sona nima bana sonta. Jarabawar mu ta fito cikin ikon Allah ni da Ma’u muka samu ban da Rahila ba ta damu ba tunda aure za ta yi ni kuma ina ta murna zan fara jami’ a. > Janaftybaby: Alhajinmu ya so ya hana Yaya Hamza ya matsa masa aka nema min gurbin karatu a jami’ar bayero a shashen tsumi da tattalin kasa economics. Ma’u kuma ta ce bording za ta yi sai aka nema mata Federal University Minna ko na ce ita ta nuna tana bukatar can ɗin.
Saboda lamarin da ya faru bikin Rahila da Yaya Muntari ba a ma ƙara mganar shi ba sai zuwa gaba in zukata sun huta.
Yaya Auwal kuma yana can keffi sai salla sallah ma ya ke zuwa ganin gida wani abun ma sai dai ya ji labari bai san faruwan shi ba.
Na fara zuwa jami’ a farkon shekaran 2002. Ma’u ma a shekaran ta tattara ta tafi Rahila kuma tana gida amman auran su da yaya Muntari ana tunanin karshen shekara tun da shima ya cigaba da karatunsa.
A kuma lokacin ne Allah ya yi ma Hajiya Dubu rasuwa. Rasuwan da ta gigitani matuka. Na yi kuka domin har daren da za ta rasu mun kusa raba dare muna hira sai dai mun wayi gari ba ta raye tabbas ni aka yi ma mutuwa. Rasuwar Hajiya dubu da wattani uku lokacin muna jarabawar semester farko a makaranta na haɗu da Yusuf Muhammad Inuwa(Tafida) kuma mun yi aure da shi a ƙarshen shekaran 2002 rana ɗaya aka yi bikin mu tare da Rahila da Yaya Muntari. Kuma ana saura kwana talatin da biyar auran mu Allah ya yi ma Mama rasuwa daga kwanciya barcu ciwon ciki dare zuwa asuba ta ce ga garin ku nan.
KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.*
07045308523.
*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE*