[12/10/2024, 12:57 PM] Hauwa Galadima: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI*
Zaku ce ya akayi haka 🥲 na fiku takaici da baƙin ciki rasa rubutun nan a karo na biyu 😭😭 in shiga in duba folder tace dubani in da kika ajiye. Komai ya goge wlh. Bazance dan me ba domin bansan hikimar ubangiji cikin al’amarin ba. A kullum ina addu’ar Allah ya bani ikon rubuta alkhairi. Idan da rabo zan sake rubuta WASU MATAN amma abun da ciwo kayi rubutu ya goge.
Ban cika baki ba amma se kunce gara da akayi haka. It was meant to come in the next 1 year or more ashe yanzu Allah ya nufa. Asha karatu lafiya.
*PAGE 1*
“Malam idan kaje ƊAN ALJANNAH zan sauka” na faɗa ina nunowa me Adaidaitan da muke ciki saitin in da ze ajiye ni, bayan daya gama daidaita parking na sauka ba tareda na kalli Hansa’u data kalli ɗaya ɓangaren ba nace
“Da ace kuturwa Allah yayi ni se inji haushi dan kince ba zaki tayani aiki ba, dake ko babu ke bazan rasa wanda zasu rufamun asiri ba” na faɗa ina miƙawa me Adaidaita ɗari biyar. Bata tankamun ba na juya ba tareda na amsa tambayar da me mashin ɗin yake mun ba akan iya kuɗi na ze ɗauka ko na mu biyun na shige kantin. Na rigada na rubuta list ɗin abubuwan da zan siya dan haka kai tsaye na shiga ɗauka cikin abinda be wuce minti sha biyar ba na gama dan ma na tarar da layi gurin biyan kuɗi. Wani Adaidaitan na tare ya ƙarasa dani kofar Nasarawa gidan Anty Labiba. Munir na ƙofar gida da abokinsa ina hango su naji raina ya sake ɓaci dan nasan ƙarshe yanzu Anty Labiba se ta tado da zancen da bana so amma ganin ya riga da ya ganni in na ce mu juya ma ze ga ai saboda shi ne yasa nacewa me Adaidaitan ya faka na sauka ina cin magani na biyashi kuɗin sa.
“Barka da zuwa Hajiya Halima” Abokin nasa wanda seda na sauka na gane Yahuza ne ya faɗa yana mun murmushi, na ɗauke kai sama ciki ciki nace “yawwa”. Kafin na miƙawa me Adaidaita kuɗin sa Munir daya iso kusada dani ya rigani, ɗari biyar ya bashi sannan ya duƙa ya shiga ɗaukar ledojin siyayyar dana zube a ƙasa. Murmushin sa me kyau yayi kafin yace
“Ashe kece zaki zo shiyasa na kasa tafiya”. Na wuce cikin gidan ba tare da na tankashi ba ina ji ya biyo bayana. Anty Labiba na zaune kan tudun gurin wanke wanke tana cire hancin kayan miya ta ɗago tana amsa sallamar mu.
“Aa, Munir. Ashe baku tafi ba?” Ta faɗa tana tsame hannunta daga abinda takeyi, a ƙasa ya aje kayan yana cewa
“Eh wlh, haka nan fa muka tsaya ashe rabon na ganta ne yasa” ya faɗa yana nuna ni. Na tura baki gaba ina wucewa falon Antyn ina jiyo ta tana cewa
“Billahillazi dai Munir se in ce baka da zuciya, yanzu saboda Allah ba zaka bar yarinyar nan ga mata nan fululu a gari masu sonka kamar suyi me ba? Wlh idan nice kai inuwar Halima bazan sake kallo ba balle har maganar arziƙi ta haɗa mu”.
Ya shafa kansa yace
“Ba zaki gane ba Anty” se tayi saurin tare shi tace “dama ta ina zan gane? To dai tun wuri gara kawa kanka faɗa ka nemi wata dan nan kusa banga Halima nada rabon gane wautar data tafka ko in ce take shirin tafkawa ba. Ita tayi asara wlh samun saurayi nagartacce kamarka me abinyi a zamanin nan” .
“Bari na wuce, adai cigaba da taya mu da addu’a a kuma sake tayani rarrashinta Anty” ya faɗa jin zata ɓaro wani zancen sannan ya juya ya fita nan kuwa Anty Labiba ta dasa mitar da bata gajiya dayi tunda na watsa mata ƙasa a ido nace bana son ƙanin mijinta kuma ɗan ɗakinta. Seda na jiyo ƙarar tashin mota alamar sun tafi kafin na aje mayafina na, kujera na aje kusada inda ya zube mun kayan na shiga gaida Anty Labiba ta wani amsa mun a ɗage ni se ta bani dariya ma irin wannan ɗaukar dumar magaji da nishi. Shikenan kuma se akace dan ya mata dole nima ya mun in so shi? Kowa fa da ra’ayinsa a rayuwar nan, ni da wanda nake so shima rashin zuciya yasa har ya bari maganar ta fito bayan tun ni dashi daya furta mun na sanar masa ina da wanda nake so ba kuma na ra’ayinsa.
Kayan na shiga fito dasu daga leda Anty Labiba ta kalleni tace
“Ban gaya miki karki sake zuwa gidan nan kice zaki wa wancan santolon cima zaunen abinci ba?” Nan da nan na haɗa rai nayi kicin kicin bata damu ba taci gaba da cewa
“Tsabar rashin sanin ciwon kai, mazan arziƙi na wahaltawa yammatansu amma shi mace ce take wahalta masa yana kwance ba cas ba as gaki yar wahala ki ringa dafa abinci ki kai masa ba godi bare na gode balle a baki tukuici to ba’a gidan ba dan gas ɗina bana gomnati bane kije can gidanku kiyi”. Kan ince wani abu Uncle Sale ya fito daga falo yana cewa
“Meye haka Labiba?” Kitchen ɗin ta dake tsakar gida ta shige ba tareda ta amsa masa ba na gaishe shi ya amsa yana tambayata su Anty kafin ya bita kitchen ɗin ni kuma na wuce falo ɗauko wayata dan na manta ban tambayi Bilal abincin me miya yake so ko kuma jallof ba.
Sau biya na kirshi be amsa ba hakan yasa na barshi na tafi akan nayi masa jollop ɗin kawai tunda na siyo kaza harda cabbage da zanyi coslow. Seda na jira Anty Labiba ta gama miyarta ta fita daga kitchen ɗin kafin na shiga nawa aikin, nasan magana Uncle Sale ya mata shiyasa ta barni dukda haka shiga goma fita goma seta mun habaicin ni yar wahala ce ina wa wani can ƙaton banza girki, tsakani da Allah ta ina mijin da zan aura ya zama ƙaton banza? Laifi ne idan na dafa abinci na basa?
Ana kiran la’asar na kammala komai, cikin sababbin kulolinta na shirya abincin dama na gyara ƙaramin falonta na saka turaren wuta na kulle, ban bari ta lura ba na shige da kulolin da plates na sake kullo ɗakin kafin na koma ɗakin su Amir na shiga wanka. Ina tsaka da shiryawa ta shigo tana cewa
“Naga kin aje mana tsurar shinkafa da salad ina kazar?”
“Guda ɗaya ce fa Anty” na faɗa zuge zip ɗin skit ɗina, ta ballamun harara tace
“Ko ɗan tsako ne wlh se na ci, ban muƙullin falo na” sena yi waje da sauri ina cewa “Amma tsakani da Allah dai an san abun nan na mutum ɗaya ne kuma za’a sa masa rani, bafa shi da lafiya banda ma bani da kuɗi me kaza ɗaya zata masa ma” na wuce falon tareda maido ƙofa dan karta biyo no taga kulolinta ta dasa mun sabuwar tijara. Fukafukai na ɗakko mata da ƙundu na zubo mata albasa da koren tattasan da nayi garnishing pepper chicken ɗin dasu ina ajiyewa kuwa ta fara auna mun zagi wai mayya na maida ita ko me? A karo na biyu Uncle Sale daya dawo daga sallah ya sake ceto na, sanin yau weekend yana gidan ma yasa har nayi karambanin zuwa badan haka ba gara in zauna a gidanmu