Search
You have no alerts.

    IDAN KAYA YA GAJI…GAMMO MA YA GAJI

    Misalin ƙarfe biyun daren ranar asabar, goma ga watan Agusta watan marka_markan ruwa
    kenan. Kamar yadda aka saba yau kwananmu uku cir ana ruwa, yayi ƙarfi kana ayi irin masu
    yif_yif ɗinnan afumangai . A nan jihar Jigawan Dutse A wannan daren ruwan ya shallake tunanin
    mai karatu wani irin ruwa mai ƙara haɗe da wata iriyar iska akeyi, ga ƙanƙara dake ta ragargazan
    kwanukan jama’a, sannan ba ma iyakar Jigawa bane kaɗai ruwan ba, garuruwa da dama na
    Arewa a cikin ruwan suke muna jin labarai a TV da rediyo, ruwan yayi ɓarna sosai, har ambaliya
    ruwan yayi a garin Jos cikin wata unguwa can tudun osi, asakamakon wani rafi dake wajajen
    ƴan tukwane daya cika, an yi asarar rayuka da dama, ruwa ya tafi da gidaje da mutane da dama,
    nasan ba zaku kasa tuna shekarar ba ko? A al’ada da ɗabi’ar mutane sukance in ana ruwa anfi
    samun bacci mai daɗi da nishaɗi, wanda yake cike da mafarkai masu daɗi ɗauke da yanayi mai
    burgewa. Wanda ni a wannan lokacin tsaye nake a ɗakina ina aikin kai kawo yadda kuka san
    soja a filin daga, gara ma su aikin kuɗinsu suke yi. Minti_minti ina ɗaga kaina in kalli agogon
    dake manne a bangon ɗakin nawa domin sanin haƙiƙanin lokaci. Sannan ina matsawa bakin
    taga in buɗe labule inga ko zan ga shigowar motar Babangida. Amma shiru, kafin ruwan ya
    tsananta wajajen sha biyun dare na yi karambanin kiran layinshi. Yanayin da ya sani dana sani
    kenan, ɗaga wayar akayi ba tare da ance komai ba, ina jiyo nishin Babangida tare da wata
    macen tabbacin suna gudanar da mu’amalar banza. Na kirane bai san ya ɗauki wayar ba, a_a
    yana sane ya ɗauka domin ya ninka mun azabar da yake bama ruhina, a_a ita karuwar da yake
    tare da’itane ta ɗauki wayar su suka barma kansu sani, ni dai babu guiwa na zare wayar a
    kunnena sabida abinda nake jiyo ma kunnuwana Babangida yana wani irin mugun sambatu na
    fitar hayyaci, da wani irin gurnanin da ni da nake a matsayin matarshi ma bansan ya iyasu ba
    kun dai gane. Na kirashi ne in sanar mishi irin zazzaɓin dake damuna matsananci, ba abun in
    fita ba kuma zargin daya saba ya hau kaina ko kuma ya haukace dan kishi, ashe rabon zanji
    wannan tashin hankalin ne.
    Hawayen dake zubowa daga guraben idanuna na share, na haɗiyi wani yawu mai ɗaci da kauri,
    na lumshe runannun idanuna ihun Babangida da sambatunshi suna tai mun amsa kuwa. Wai in
    tambayeku dama haka maza suke ne, ko kuwa nice dai banyi sa’a bane?.
    Ko da yake bani kaɗai bace banyi sa’a ba. Da yawa _yawan mazan wannan ƙarnin da muke cik
    zinace_zinace suka sanya a gabansu sai dai wanda Allah yasa yafi ƙarfin zuchiyarshi. Kai Ina
    cikin tsaka mai wuyar fita, ina cikin nadama, baƙin cikin kasancewata matar Babangida tur da
    namijin da baya iya killace kanshi ga iya kar halalinshi, tur da mazinatan maza masu irin halin
    bunsuranci irin na Babangida, Tur da Babangida.
    Bakin taga na dawo na yaye labulen da kyau, na nutsu bil haƙƙi zubar ruwannan a makeken
    tsakar gidan kawai nake kallo, da yadda ruwan yake gudu, da kuma yadda ya lalata shukokin
    fulawa da aka daddasa a gidan domin ƙawa. Gidane na alfarma amman a wajena bashi da wani
    amfani ko misƙala zarratin.
    Ƙarfe ukun dare dot sai naji wayata tayi ƙara a zabure na duba kasancewar wayar na riƙe a

    hannuna.
    Ganin sunan Maigogul akan tangaran ɗin wayar sai na tsinci kaina da faɗuwar gaba, nasan dole
    dai wani mummunan abunne ya faru, dan a gidanmu munanan abubbuwa suna yawan faruwa, in
    da sabo ma mun riga da mun saba. Iyai kuwa ina ɗagawa sai naji muryar Rakiya a madadin inji
    ta Maigogul.
    “Lolo kina jina” Lolo shine sunan da ake kirana dashi a gidanmu, da ƙawayena na duniya.
    Sabuwa kuma sunan da gama gari ke kirana dashi kenan, da kuma dangin Babangida ma haka,
    da ƙawayena na makaranta dan da Sabuwa nake amfani a makaranta, shine a jikin katin ɗan
    ƙasana ma.
    Ta faɗa da ƙarfi kasancewar ita dama Rakiya haka take magana gatsal_gatsal kamar rubar
    zawo.
    Ina jinki Rakiya lafiya da wannan muƙu_muƙun daren?”
    “Ina fa lafiya kin ganmu a gidan Labbai ɗan gidan da uban naku yake taƙama dashi ya rushe
    abunki da ginin biskit ginin laka. To gamu nan dai a gidan Labbai tare da su Sa’ada da Qamriyya
    ragowar basa gidan abun ma ya faru, Uzairu zuchiyata ne da Maigogul suka kawo mu wajen
    Labbai. Kinga babu abunda muka ɗauka ruwanma har gidansu Malam Tanko duk ya haɗa ya
    narka, gidaje da yawa duk sun rufta. To gidanma yayi ƙarko irin ruwan da ake zabgawa a
    wannan damuna ta bana da yawa yake. Har gidajen bulo da bulo ma sun rushe. Ɗaiɗaikun
    gidajene a unguwar basu rusheba, in basu rusheba zaki tadda kwanon gidan ya yaye. Ita kanta
    Labbai kwanon ɗakinta ya yaye kin ganmu a cikin ruwa a takure wallahi. Kujerunta duk sun
    tsotsi ruwa”
    Idanuna na runtse dama yaya lafiyar kura ballantana tayi hauka. Bayan na sauke ajjiyar zuchiya
    sai nace
    To Rakiya gobe da sassafe zan shigo gidan in sha Allah. Kun faɗa ma su Ramatu da Adama
    suma?”
    “Duk an sanarma kowa dama kece ƙarshe, su kuma waɗancan ai na faɗa miki sun tafi yawon
    barbaɗa acan dama zasu kwana basu san me ake ciki ba. Sai in sun dawo idanunsu ya gane
    musu”
    Ina jiyo Maigogul yana cewa.
    “Ki bar ce musu sun tafi yawo barbaɗa Rakiya ina faɗa miki, ki kiyayeni kar mu raba abun faɗe a
    gidan surukai da daddarennan”
    Ai kuwa Rakiya ta dira a wuyan Maigogul da hayaniya haya_haya, sai faɗi in faɗa suke yi. Nasan
    ba abun kunya bane a wajensu ace a gaban mijin Labbai ɗin suke wannan rikicin ba. Dan baƙin
    ciki da takaici sai kawai na datse wayata kawai, tare da dafe kaina daya ƙara tsananta ciwo.

    0 Comments

    Heads up! Your comment will be invisible to other guests and subscribers (except for replies), including you after a grace period.
    Note
    error: Content is protected !!