Typing📲
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
Bilyn Abdull ce 🤙🏻
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
My TikTok account 👇
Instagram👇🏻
BOOK 2
🅿️➖1️⃣
*_Assalamualaikum. Barkanku da wannan lokaci, fatan ansha ruwa lafiya? Anyi salla lafiya?. UBANGIJI ya karɓi ibadunmu, ya yafe mana kurakuranmu, yasa muna a cikin ƴantattun bayi. Ina mana Barka da dawowa filin daga, ya rabbi ka bani ikon rubuta abinda bazai cutar dani da ku ba. Ka tsarkake min alƙalamina domin rahamarka. Ka gafarta ma iyayenmu da malamamu damu baki ɗaya. Ka ɗauramu a bisa tafarki madaidaici da bazamuyi dana sani ba. ALLAH ka hanamu cutar da junanmu koda da kalma mara daɗi ce.🙏_*
Ayi mana afuwa da jinkirinmu yau da gobe sai ALLAH 🥰🥰❤️.
Ƴan ƙungiyar Bati ku matso nan munada meeting 😂. Kun san dai AZUMI aka gama ko, goman ƙarshen nan hummmm 😂 karki yarda ki zama a cikin wanda na ɗaga hannu nace ya ALLAH gasu nan….
Bazan dai ƙarasa ba amma gaskiya kada ki yarda sister dan in dai an amsa akwai cakwakiya gaskiya 😂😂😂😂🏃 500 kacal ne 😘
……..Sosai ciwon kai yay ma Maanal rijib a wannan yinin isowarsu Abuja, shima kuma AA ɗin zuwa yamma dole aka saka masa drip ma, dan sam baya jin wani ƙarfin jikinsa. Har cikin dare ba’a gama saka masa ruwan ba dan kusan leda uku ne. Dole Fawzan ya kwana tare da shi bisa umarnin Abah. Oum taso yin magana amma tai shiru, dan ita so tai ta kawo Maanal a daren sashen AA ɗin, amma ta fahimci take-taken Abah so yake ya kawo wani sharaɗin hora AA ɗin, dan dama shine ya bata umarnin wucewa da Maanal sashenta sanda suka iso.
Bayan sun baro sashen AA bin bayan Abah tai nasa sashen ta masa magana, amma sai ya nuna mata shi barci yake ji ta barsa dan ALLAH. Haushi ne sosai ya kamata, dan haka fuuu ta baro sashen. Da kallo ya bita ganin yanda ta wuce, sai kuma ya shiga girgiza kansa a fili ya furta, “Fateema son yaranki yayi miki yawa, in dai fushi ne ƙyama sakko dan sai na hora Ajwaad a gidan nan”. Daga haka ya shige toilet yana murmushi…
_★
Zuciyar Babban Yaya cike da wasi-wasi ya nufi sashen Oum ganin har goma saura na dare yau ma Maanal bata koma sashenta ba, ga AA ɗin kuma ma jikin nasa ya dawo dan yanzu haka wani ƙarin ruwa aka cire masa. Ganin bata a falo ya nufi bedroom ɗinta. Sai da yay sallama ta amsa tare da bashi izinin shiga sannan ya shigan. Yanayin yanda take a zaune da fiskarta dake cike da damuwa yasa gabansa faɗuwa, duk da yasan akwai damuwar yanayin da Auta ke ciki dai.
“Oum baƙya jin daɗi ne?”.
Ya faɗa cike da damuwa matuƙa yana kaiwa kusa da ita zaune. Idanu ta zuba masa kawai, dan duk yanda taso yin murmushi ko sassauta damuwar tata hakan ya gagara sam. Sai ma ƙwalla kaɗan da suka taru mata a idon. Ai sai babban Yaya ya sake rikicewa matuƙa.
Hannunsa ta riƙo tana girgiza masa kai, “Kaga kwantar da hankalinka bafa wani abu bane ba.”
“Haba Oum yazan yarda da hakan, kalla fa yanda damuwa ta bayyana a fuskarki sosai. Dan ALLAH in ma dan ciwon Auta ne ki daina tada hankalinki komai zai wuce kamar ba’ayi ba in sha ALLAHU. Dan yanzu hakama barci yake yi na cire masa drip ɗin dan ya ƙare. Jikinsa sam kuma babu zafi da ganin yanda yake barci ma kasan Alhamdullah babu wani damuwa ba kamar jiya da yinin yau ba. Yanzu haka ma nazo ne akan batun Maanal, nazata zata kwana a can ne yau ai tunda jikin da sauƙin itama?”.
Sosai ɓacin ran Oum ya ƙara bayyana akan fuskarta, ta ce, “Akan hakanne ai Abanku ya ɓata min rai Fadeel, yace wai bazata koma can ba yanzu sai bayan salla ya koyama Ajwaad hankali. Wane hankali kuma ake buƙatar koyama yaron nan bayan wanda ya koya. Kama ajiye batun wahalar ciwo da yasha a shekarun baya, a kwanakin nan kawai kaga hanlin daya shiga fa da wanda yake a ciki yanzu. Kowa fa a rayuwa da irin yanayinsa da kuma ƙaddararsa, amma Abanku ya kasa fahimtar hakan, ya kasa fahimtar Ajwaad nada zurfin ciki ne. Yanda Maanal keda muhimmanci a garesa bana tunanin dole sai ya buɗe baki yace wani abu za’a yarda dashi. Shin so yake na rasa yarona ne saboda wannan tsaurin nasa?”. Ta ƙare maganar muryarta na rawa kamar zata saki kuka.
Cikin sake rikicewa sosai Babban Yaya ya shiga girgiza mata kai nasa idanun na kaɗawa sosai shima. “Dan ALLAH Oum ki kwantar da hankalinki, ni bara naje na samesa yanzu. Ko kuma ki kira Baba ko Abba ki haɗashi da su…..”
“Saboda ban isa da gidana ba kenan ko mai uwa?”. Atare babban Yaya da Oum suka juya da sauri suna kallonsa, ƙarasa shigowa cikin ɗakin Abah yayi, cikin nuna ɓacin rai sosai ya cigaba da faɗin, “Saboda biyan buƙatar taka uwar ni a kira nawa iyayen a haɗani da su. Lallai Fadeel sannu, nace sannu kaji ko!”.
“Kayi haƙuri Abah ni ba haka nake nufi ba, amma Oum fa……”
“Malam tashi ka wuce sai da safe.”
Abah ya sake katseshi cikin sake nuna ɓacin rai. Kallon Oum Babban yaya yayi idanunsa na sake kaɗewa, kanta ta jinjina masa alamar yaje ɗin. Dan haka ya miƙe kawai ya nufi ƙofa. Da kallo Abah ya bisa, sai kuma ya girgiza kai a zuciyarsa yana ayyana (su dai akan uwarsu kowa ma ya mutu har liman babu ruwansu). A fili kam dubansa ya maida kan Oum data ɗauke kanta gefe tamkar ma bata san da shi ba a ɗakin. Sai kuma ta yunƙura zata miƙe. Yasan mi zatayi, dan haka cike da bada umarni ya ce, “Koma ki zauna”.
Komawar tayi ta zauna, kafin ta ɗago idanunta da suka sake kaɗewa a karo na farko ta kallesa, aiko ya sake yin kicin-kicin da fuska harda ɗan willa mata hararar data sakata janye idanun nata a kansa sannan ya furta, “Oh ke yanzu saboda na yanke hukuncin daya dace akan ɗanki shine kika ɗauki fushi da ni kin kira babban ɗanki kina sanar masa kuyi min taron dangi saboda ban isa nace ga yanda za’ai ba”.
Idanu Oum ta ɗan rumtse kaɗan, sai kuma ta buɗe a kansa. Baki ta buɗe kamar zatai magana sai kuma ta fasa saboda ƙwallar da suka cika mata idanu. Ɗauke nasa yay dan yasan yanzu sai ta karya masa zuciya, shi kuma a wannan karon ya ɗauka aniyar tauna tsakuwa dan aya taji tsoro, dolene ya hukunta Ajwaad kodan ya sake sanin muhimmancin Maanal. Bazai yiwu ya samu aurenta a ɓagas ba su kuma bashi ita a ɓagas. Ƙoƙarin barin ɗakin yayi, sai Oum kawai ta saki hawayen da take riƙewa cikin muryar kuka ta ce, “So kuke sai kun kashe min shi hankalinku zai kwanta ko Gadanga, yanzu horon da ƙaninka yay masa kawai bai wadatar a yafe masa ba”.
Murmushi Abah daya tsaya cak tun fara maganarta ya saki a hankali, sai kuma ya maida fuskarsa ya haɗe kafin ya juyo yana kallonta daga inda yake tsayen. “Rafeeq bai hora ɗanki ba, takarar nema sukai yay muku adalci ya sadaukar saboda ƙyaƙyƙyawar zuciyarsa, da kuma nasan zai yi hakan sai na hana masa”. Ya ƙare maganar yana mai juyawa ya fice abinsa. Wani irin ƙululun abu ne ya sake tokare wuyan Oum, har zuciyarta na tunzurata akan takai Maanal sashen Ajwaad koma miza’ayi ayin mana…….
_★
Alamun shigowarsa ya sata dakatawa daga kai-kawon da takeyi, zama tai kamar ba ita ba ta nutsu a bakin gadonsa tare da ɗaukar littafin addu’oin sa dake a bed side drawer ta fara karantawa. Da farko Abah daya shigo ransa a ɓace sam bai ganta ba. Sai da ta ɗago ta kallesa cikin tausasa harshe matuƙa ta furta, “Sannu da shigowa”. Sannan ya kalleta. Ciki-ciki ya amsa mata, dan haka ta taso da ƴar sassarfa tana faɗin, “Lafiya kuwa? Naga kamar ranka a ɓace?”. Tsaki yaja mai ƙarfi, sai kuma ya wullar da wayarsa a saman gadon nasa shima yana kaiwa zaune hannunsa akan goshinsa yana murzawa. “Fateema ce ke neman ɓatan rai Kamila”.
Ɓoyayyan murmushi Mamy ta saki, a zahiri kam cike da damuwa ta ce, “A haba kodai baka fahimta bane, amma nasan bazata ɓata maka rai da son ranta ba yallanɓai.”
“Mtsoww!! Bazaki gane ba Kamila, ita dai sam bata gajiya da rikici akan ƴaƴanta, dokar dana kafa jiya akan komawar Maanal sashen Ajwaad shine taketa faman fushi, yanzu naje mata sai da safe na samu ta tasa babban ɗanta gaba tana faɗa masa, shiko yana bada shawarar a haɗani da iyayena.”
Sosai Mamy takai zaune yanzu kam, hannunsa ta kamo cikin nata cike da kulawa. “Kayi haƙuri, zan sameta muyi nagana ta yanda zata fahimta. Dan tabbas Ajwaad ya cancanci a fara horashi kafin a bashi yarinyar nan kodan halaccin iyayenta da basu duba abinda ya faru a baya ba suka sake bashi batare da ko tada magana ba. Taurin kan yaron nan ne yayi yawa, ya kamata ya fahimci ba komai akema taurin kai ba a rayuwa….”
“Abinda nake son ta fahimta kenan ai nima Kamila. Amma tamaƙi ta nutsu ta saurareni, ni kuma so nake mu rabashi da halin kodan bambancin dake a tsakanin jiyansa da yau ɗinsa”.
“Karka damu zata fahimta in sha ALLAHU. Ka bata lokaci ta huce yanzu sai mu haɗu muyi magana. Idan ma ta kama Maanal ɗin ta dawo sashena da zama to, dan in ba hakaba bazai damu ba”
Ɗan jim Abah yayi, sai kuma ya jinjina kansa cike da gamsuwa ya ce, “Kumafa kinzo da shawara Kamila, dan in har Maanal na a sashen Fateema ba’a rabu da bukar bane an haifi habu za’ai. Dan ɗan nata dai can zai koma ya tare abinsa, kinga kuwa bazai damu ba.”
“Tabbas hakan ce zata kasance”. Cewar Mamy wani farin ciki na ratsa mata zuciya na nasara. Abah kuwa da bai san dawan garin ba ya sake furta, “To ai zanyi maganin abun, bari dai ya samu lafiya”.
“ALLAH ya bada iko, ina goyon bayanka kuma ɗari bisa ɗari a wannan gaɓar. Dan in aka biye ta Mamansu haka za’a mika masa ita kaga ya samu damar cigaba da mana abinda yaso tunda ta shagwaɓa shi daga ita har ƴan uwan nasa. Sun nuna masa komai ya nema sai ya samu komai girman sa”.
Sosai kalaman Mamy ke shigar Abah, yana kuma jin gamsuwa da su da tasirinsu ƙwarai da gaske a zuciyarsa fiye da yanda take ma fatan ya fahimta ɗin………✍️
(Mamy😏. Mamy☹️. Mamy😮💨. Matar nan ko🤔. Hummmm😥.)
Amin afuwa dan wlhy mura nake mai zafi, idan na samu sauƙi za’afi ganin page ɗin da tsaho…
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
Bilyn Abdull ce 🤙🏻
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
My TikTok account 👇
Instagram👇🏻
Arewabooks
Read My Book “AJIYA A DUHU” on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
WhatsApp channel
Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃
BOOK 2
🅿️➖2️⃣
……..A safiyar washe gari har kusan sha biyu Abah baiga idon Oum ba a gidan. Dan haka ya fahimci fushin nata fa na gaske ne. Shi dariya ma ta bashi, dan haka shima ya shareta. Har yamma dai bai ganta ɗin ba, ya dai daure har akai sallar magrib da isha’i sannan ya nufi sashenta. Ko’ina tsaff yake da ƙamshi, sai masu aikinta daya samu a falon ƙasa suna hira. Suka gaisheshi da girmamawa ya amsa musu da kulawa ya wuce.
Oum na zaune a doguwar kujera Maanal kwance ta ɗora kanta a cinyarta su duka idanunsu a tv. Sallamar Abahn ta saka Maanal ta shi zaune, kanta a ƙasa tai masa sannu da gaida shi. Shima fuska ɗauke da murmushi ya amsa mata tare da tambayarta ciwon kanta. A tausashe ta ce, “Ya daina Abah Alhamdullah”.
“Masha ALLAH ai haka ake so ɗiyar Abanta ƴar albarka.”
Murmushi Maanal tayi mai faɗi, sai kuma ta miƙe tsam, dining area ta nufa ta ɗakko ruwa a freight tazo ta ajiye gabansa, cike da dabara ta shige bedroom ɗin Oum. Shi ko Abah cike da mamaki sosai ya ke kallon Oum ganin tunda ya shigo falon bata ko ɗaga ido ta kallesa ba. Sai ma wani sake ciccin magani take. Ji yay kamar ya juya ya fita ya bar mata sashen. Har yay kamar zai juyan sai kuma ya dakata, ruwan da Maanal ta ajiye masa ya ɗauka ya sha kafin ya dubeta da ƙyau. A ɗan kausashe yace, “Har yanzu fushin ne kenan? Dan na hana ki bama ɗanki matarsa shine nima kika ɓiye min ganinki yini guda Fateema? Ni kenan ban isa sharɗanta doka a fahimceni ba ashe dai?. Miyasa kike da son kanki da yawa akan ƴaƴanki ne wai?”.
Karo na farko ta ɗago ta kallesa, idannunta cike da hawaye. Muryata na ɗan rawa ta ce, “Miye abun son kai anan Abahn su?. Yaron nan kodan halin daya shiga ai ya cancanci a yafe masa a kuma fahimcesa. Eh naji shi mai kuskure ne, amma koda bai fito yace yana son Maanal ba halin daya shiga kawai amsa ce. Amma sai ace baza’a bashi matarsa ba har sai bayan salla. Haba Gadanga ka fahimta mana, baifa da lafiya, yana buƙatar mai kulawa da shi…..” hawaye suka shiga ziraro mata batare data kai ƙarshen zancen ba. Shi Abah sai abun ma ya fara bashi dariya. Yanzu dan kawai yace Maanal bazata tare ba sai bayan salla shine abin kuskure har ta zauna tana kuka. Oh ya rabba, Fateemansa sarkin daru kenan. Kansa kawai ya girgiza, batare da yace komai ba ya juya zai bar mata ɗakin, dan dole ya turza sosai ta yanda ita da ɗan nata zasu san ba wasa yake akan al’amarin ba. Da sauri ta ce, “Gadanga!”. Tsayawa yay, tare da ɗan waiwayowa ya kalleta. Sai kawai ta sake sakar masa kuka. Da sauri ya fice abinsa, dan in tana irin wannan darun nata yafi buƙatar yin nesa da ita, idan ba haka ba sai ta karya masa zuciya ta sakashi yin abinda bai niyyar ba.
Kai tsaye daga sashen Oum ɗin sashen AA ya nufa, dan son sake duba jikinsa, saboda yau ma a kwance ya yini ko salla bai fita ba sakamakon rashin ƙwarin jiki da yake fama da shi har yanzu. A sashen ya samu babban Yaya da Fawzan a tare da shi, sai dai shi barci ma yake AA ɗin, su kuma suna ƴar hirarsu. Cike da girmamawa suka gaisheshi, ya amsa musu da kulawa yana taɓa goshin AA dake barci. Jikinsa babu zafi kamar jiya, dan da ganin ma yanda yake barcin zaka san Alhmdllh. A hankali ya sauke ajiyar zuciya, sai kuma ya ɗago idonsa akan su Babban Yaya ya ce, “Alhamdullah yanzu kam babu zazzaɓin ai. Ya kamata kuje ku kwanta ku huta kuma ni bara na zauna da shi yau”.
Idanu Fawzan ya ɗan waro waje da faɗin, “Haba Abah da kanka. Ai sai Oum ta zane mu.”
Dariya Abah yayi, hakama babban Yaya ya murmusa tare da faɗin, “A’a Abah mun yafe maka kaje abinka. Dan gaskiyar Fawzan Oum zata iya zane mu ne”.
Nan ma murmushi kawai Abah yayi, sai kuma ya zauna suka ɗan tattauna akan jikin AA ɗin da tun shekaran jiya da suka iso daga Kano sai a hankali, dan duk dauriyarsa sai da ya sake kaiwa kwance. Gashi ya kuma kafe bazai je asibiti ba, sai nan doctor yazo yake duba shi. Bayan Abah ya musu sallama ya fito babban Yaya ya biyosa da sauri. Dakatawa yayi yana kallonsa harya ƙaraso.
“Lafiya dai ko Fadeel?”.
Cike da ladabi babban Yaya ya ce, “Eh Abah, kawai dai akan batun tarewar Maanal ɗin ne dai, dan ALLAH kayi haƙuri a bashi matarsa, ALLAH bana jin daɗin yanda nake ganin Oum a cikin damuwa. Abubuwan sun mata yawa, ga ciwon Ajwaad ɗin ga kuma wannan batun. Abah harfa rama naga tamun yau ALLAH ”. Babban yaya ya ƙare maganar kamar zai yi kuka.
Murmushi Abah yayi, sai kuma ya ɗan furzar da iska tare da faɗin, “Wato Fadeel ya kamata muma kammu adalci muyima yarinyar da iyayenta suma. Dan tabbas da nasan Rafeeq zai zagaye yay wannan aikin sai na hanashi, saboda nifa har yanzu ina akan bakana sai Ajwaad ya sauke kansa ƙasa yazo da bakinsa ya nema na bashi Maanal bayan ya nema afuwarta, idan ma ta kama ya faɗa mana dalilinsa na wannan dagewar”.
Kai sosai Babban Yaya ya jinjina, ya ce, “Na fahimceka Abah, kuma nima ina bayanka. Sai dai hakan bazai hana na baka haƙuri ba na kuma nemawa Auta afuwa. Kasanshi da zurfin ciki, maybe akwai abinda bamu sani ba game da al’amarin, amma wlhy mu shaida ne Ajwaad na son Maanal matuƙa. Kuma sai nake ga mata da miji sai ALLAH, kamar barinsu su kasance a taren zai sa su sasanta kansu kodan soyayyar da suke ma juna su duka”
“Humm wace soyayya kuma Fadeel, yana sonta zai watsar da al’amarinta ya zauna jan jiki a sanda ya sake ganinta, to Miye na girman kan, aure abin wasa ne? Barshi dai a bata tare ɗin ba, zai fi jin zafin wannan bulalar fiye da wadda kake hangen. Ina son hakan ya zama izina a garesa ya canja wannan halin nashi kodan yanzu shi mai iyali ne nanda wani lokaci haihuwa za’a fara masa”.
“Tabbas aure ba abin wasa bane Abah, mu kuma masu biyayya ne ga kowanne irin hukunci daga gareku. Amma idan mukai dubi da halin kawai daya shiga akan tsoron rasata abun muyi nazari ne. Ta wani ɓangaren ina tsoron kar dangin mahaifinta ne fa sukai masa wani abun tun wancan lokaci tunda dama kakarsu ta nuna bata son aurenmu da su Shaheedeh. Abah kasan zata iya bin kowacce hanya domin cin nasara, sannan shi kansa asiri gaskiya ne fa”.
Sosai Abah ke kallon babban Yaya. Zuciyarsa nata faman kai-kawo akan kalamansa. Sai dai kuma baice komai ba akan hakan illa nufar hanyar fita da faɗin, “Zanyi nazari, amma ina akan bakana na bazata tare ba yanzu ku cigaba da jiyyarsa ALLAH ya tashi kafaɗunsa”. Daga haka ya fice abinsa. Da kallo kawai Babban Yaya ya bishi, shi kansa al’amarin Autan nasu na damunsa, da rikita shi, amma dai koma miye ai ta ƙare tunda an ɗaura, komai mizai biyo baya mai sauƙi ne insha ALLAHU……
Murmushi mai faɗi da yalwa Mamy ta saki, dan dukan tattaunawar Abah da su Babban Yaya a cikin kunnenta ta kasance. Tayi matuƙar yin farin cikin yanda shirinta yay tasiri akan Abah cikin sauƙi haka, dan sam batayi zaton zai amshi batun da muhimmanci ba duba da sanda take tsara masa yin hakan yi yay kamar maganar tata bata tasirantu a gareshi ba. Shiyyasa taga ƴar gwal ɗin tashi har yanzu babu fara’a ashe an sake wargaza mata shiri ne. Wani murmushin ta sake saki haƙoranta na bayyana sosai, sai kuma ta gimtse fuska da gyara yanayinta ta ƙarasa shigowa falon sosai tana sallama.
A tare Fawzan da Babban Yaya suka ɗago suna kallonta tare da amsa sallamar. Cikin yanayin da take nuna musu na kawaici ta amsa gaisuwar da suke mata, tare da tambayarsu yaya mai jikin. Suma cikin girmamawar da suke bata suka tabbatar mata da sauƙi, yanama yin barci ne. Kai kawai ta jinjina musu, batare data sake cewa komai ba ta nufi bedroom ɗin AA ɗin. Barcin kuwa yake har yanzu, fuskarsa tayi fayau. Guntun murmushi ta saki a hankali, dan tasan tabbas ƙaunar da takemasa dabance a cikinsu, tun daga ɗaukar cikinsa har haihuwarsa duk da wahalar data sha shi ɗin na musamman ne a gare ta. A karo na biyu ta sake sakin murmushin, sai kuma ta kai zaune kusa da shi gab tare da kai hannun ta shafa yalwatacciyar sumar kansa dake a hargitse. Addu’ar samun lafiya tai masa mai ɗorewa tsahon mintuna kafin ta tashi ta fita….
A hankali AA da tun tsaiwar Mamyn a kansa ya farka ya buɗe idanunsa ya bita da kallo, sai da ta maida ƙofar ta rufe ya sake maidasu ya lumshe luuuu. Ya jima kafin ya sake buɗesu, sai dai sun masa nauyi sosai alamar barci bai gama sakinsa ba. So yake ya tashi zaune, sai dai kansa juya masa yake yi, dan haka dole ya sake maida idanun ya rufe barcin ya ƙara yin awan gaba da shi cike da mafarkin Mamy da haka kawai ganinta a kansa tsaye ya tsaya masa a rai duk da yasan ba wani abu mara ƙyau tazo tayi a garesa ba, amma dai zuciyarsa ta riƙe abun matuƙa……….✍️
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
Bilyn Abdull ce 🤙🏻
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
My TikTok account 👇
Instagram👇🏻
BOOK 2
🅿️➖3️⃣
……..Mamy kam a inda tabar su Fawzan anan ta samesu, sai dai yanzu Nibras ta ƙaru.
Ɗan tsurama Nibras ɗin datai mata wani iri idanu tayi, sai kuma cikin tausasawa ta furta, “Nibras baki da lafiya ne?”.
Kallon Nibras ɗin Fawzan da Babban Yaya suma duk sukayi saboda jin furicin Mamyn. Cikin damuwa Fawzan ya ce, “Mamy gara kam ki tambayeta ke, dan tun jiya nima nake fama da ita amma sai tace ba komai gajiyar biki ce wai.”
Cikin jinjina kai Mamyn tace, “Itama gajiyar bikin akwaita ɗin ai, dama sai a hankali zata saki kowa duk da ga wani na tunkarowa kuma dai. Kinga kije ki samu ki gasa jikinki da ruwa mai zafi sosai sai kisha pracitemol ki kwanta abinki kiji. ALLAH ya ƙara sauƙi”.
Ji Nibras tai kamar ta zageta, amma sai ta daure ta jinjina mata kai kawai da faɗin, “To Mamy”. Daga haka ta juya ta fita zuciyarta na mata zafi da ƙuna matuƙa. Tazo ne dan taga fuskar AA ko zataji sassaucin abinda ke cizon zuciyarta, amma Mamyn ta wani korota. Ba komai zata dawo ne, dan in har yau Fawzan anan zai kwana ALLAH sai dai su kwana tare a sashen AA ɗin. Koba komai ta rage raɗaɗin kishin dake dafa mata zuciya. Sau ƙin ma har yanzu ko sau ɗaya bataga Maanal a sashen nashi ba..
Fitar Nibras ya saka Mamy ma yunƙurin tafiya, amma sai Babban Yaya ya dakatar da ita cikin ladabi. Tsayawa tai tana kallonsu su duka. Fawzan ya ce, “Mamy dan ALLAH magana zamuyi ne”.
Wani irin sanyi mai silalar da kuzari ne ya shiga bin jijiyiyin jininta yana gauraye jikin ta. Yayinda wani farin ciki ke cika zuciyarta tamkar kumfar omo a cikin ƙaton bahon wanki. Yau itace yaranta ke faɗa mata suna son yin magana da itane iya su kaɗai babu matar can a tsakkiyarsu. Ya rabba, ita kam mizatace da UBANGIJI yau. A zahiri kam sai ta dake babu wani alamun komai a fiskarta ta dawo ta zauna. Babban Yaya ne ya fuskanceta da ƙyau cikin nutsuwarsa.
“Mamy akan Ajwaad ne dama muke son dan ALLAH kisa baki a tsakanin rikicin Abah da Oum. Dan ALLAH ki taushi Abah akan ya bari Maanal ta tare a ɗakinta gobe idan ALLAH ya kaimu, dan gani yake kamar Oum ta kasa fahimtarsa ne saboda soyayyarmu ta rufe idonta, Auta na buƙatar matarsa a kusa da shi ya fahimci Oum dan ALLAH”.
Sosai kalmar soyayyar nan ta daki zuciyar Mamy, dan saida ta maimaitata a zuciya yafi sau uku. A fili kam sai ta sake raunana fuskar tata ta ce, “Oh dama wani abune ke faruwa? Ai ni na zata dan bashi da lafiya ne kawai bata tare ɗin ba. Yau gajiya tasa sau ɗaya kawai muka haɗu da Oum ɗin. Amma gaskiya ai Abahn naku ya faɗa, Mamanku ta cika rigima akan al’amarinku…..”
Cikin ƴar dariya Fawzan ya ce, “Kai Mamy kema haka zaki ce”.
“Ai gaskiya ne Fawzan, ita idan kaga tana fushi a gidan nan abu ya shafi ɗayanku ne. Karku damu zan sameshi muyi magana in sha ALLAHU. Itama zuwa da safe zan zauna da ita. Ni bara naje na ɗan kwanta nima kamar Nibras ɗin gaɓɓaina duk ciwo suke min”.
Godiya sukai mata da sai da safe. Fitarta babu jimawa Oum ta shigo itama. Su duka miƙewa sukai sukai kanta ganin har yanzu fiskarta a cinkushe, ga idannunta kamar wadda tayi kuka. Take suma duk fuskokinsu suka sauya. Murya a rauanne Babban Yaya ya ce, “Oumna Please ki cire damuwar nan, kin san fa Abah wani lokacin dan kawai ya kunnaki ne bawai abinda ke ransa kenan ba.”
“Amma Fadeel ya tausaya masa mana, kwance fa yake baida lafiya. Shin ALLAH ma ba muna masa laifi ba ya kuma gafarta mana saboda rahamarsa”.
“Hakane Oum shima zai huce”. Cewar Fawzan yana mata murmushi da kama hannunta ya sumbata. Haka sukaita lallashinta har sai da tayi murmushin itama. Kafin su nufi bedroom ɗin AA ɗin. Ganinsa zaune a bakin gado yasa ta ƙarasa shiga ciki da sauri, kusa da shi ta zauna tana mai riƙo hannunsa daya dafe kansa da shi, dan yaji duk zancen Mamy da su Babban Yaya. Mamakin Mamy da halinta ke sake raunana masa zuciya, amma yana mata fatan shiriya kafin lokaci ya ƙure mata. Yasan duk abin nan fa Abah keyi daga cikin shirinta ne, zai kuma bama kowa mamaki in sha ALLAHU cikin sauƙi.
“Auta yaya akayi? Kanne har yanzu dai?”.
Karan farko ya kalla Oum ya sakar mata murmushin ƙarfin hali, sai kuma ya kwantar da kansa a saman kafaɗarta. “Ya daina Oum”.
Ya faɗa acan ƙan maƙoshi.
“To Alhamdullah, ALLAH ya ƙara lafiya baby na kaji, yanzu mi kake son ci?”.
“Oum tea kawai”.
“To ba damuwa bara Fawzan ya haɗa maka”.
Kansa ya jinjina mata, sai kuma ya kalla Babban Yaya da Fawzan. Murmushi yay musu kaɗan, suma dake kallonsa suka maida masa murtani suna tambayarsa yaya jikin nasa. A samman laɓɓa yace da sauƙi. Daga haka Fawzan ya fita haɗa masa shayin. Kallon Oum ya ɗanyi, har ya janye idanun sai kuma ya tsira mata su, kafin tai ƙoƙarin dai-daita fiskarta har ya furta, “Oum kinyi kuka”.
“Kukan lafiya Auta ”. Ta faɗa tana ɗan harararsa cikin yanayin son basarwa. Ina bai gamsu ba, cikin rashin kuzari ya zamo ƙasan lallausan carpet ɗin gaban gadon ya zauna yana mai zuba mata idanunsa dake a shanye. Zatayi magana ya girgiza mata kai, “Oum Please ki daina damuwa, nasan a kaina ne ko? Dan ALLAH ki bari naji sauƙi fa, ki tambayi babban Yaya ma”. Ya ƙare maganar yana kallon babban yaya a raunane.
Cike da tabbatarwa babban Yaya ya jinjina kansa shima yana kaiwa zaune kusa da Oum ɗin, Fawzan ma yazo ya miƙama AA kofin tea ɗin daya haɗa masa suka zagayeta kowa na mata nashi daddaɗan kalamin, idan ka gansu abin sha’awa da birgewa sojojin yaƴanta zagaye da ita, basu barta ba har sai da fiskarta ta washe da fara’a kamar yanda suke so. Shima AA sai ƙoƙarin ƙarfafa kansa yake yanda hankalinta zai ƙara kwanciya. Ganin dare yayi Oum da babban Yaya suka baro sashen suna ƙara tattaunawa aka bar Fawzan da zai kwana da shi. Bayan wucewar tasu ne Fawzan ya zayyanema AA komai dake faruwa ana rikicin da Abah keyi akan tarewar Maanal kamar yanda ta buƙaci ji. Murmushi AA yayi mai faɗin da har ya saka Fawzan zuba masa idanu baki buɗe.
“Oh abin ma kai nishaɗi ya baka kenan?”.
Cewar Fawzan cike da mamaki. Murmushin AA ya sake saki a karo na biyu, sai kuma a hankali ya jingina da fuskar gadon yana kai hannu ya ɗan shafo gashi kumatunsa. “To yaya Fawzan in bai sakani nishaɗi ba kuka kake son nayi, banda ma abin Oum minene abin ɗaga hankali anan, ta bar masa ƴarsa mana”.
Dariya Yaya Fawzan yayi da faɗin, “Oh hakama zakace? ALLAH yasa ya jika, kaga idan sati ɗaya yay niyyar horaka sai ya maida shi wata uku kadai san halin Abah”.
Murmushi kawai AA yayi kaɗan batare daya sake cewa komai ba. Fawzan kuwa ya tasashi gaba da tsogumi…
__★
Washe gari da safe Alhamdullah Oum ta tashi da sauƙin damuwa ba kamar jiya ba. Dan tunda ta kira Mah-mah a ɗazun da asuba ta sanar mata sai Mah-mah ɗin ta tausheta da mata nasiha akan ta sakama Abah ɗin ido, ta bashi damarsa matsayin mahaifi dan ko yaya shima bazai yi abinda zai cutama Ajwaad ɗin ba ai, sannan kuma tunda a gida ɗaya suke ai babu wani abun ɗaga hankali in dai yaran yanzu ne masu ƙarancin kunya, shi da kansa ma zaice ya ɗauki matarsa basai ta ɓatama kanta rai ba. Ji tai zuciyarta ta rage jin haushin Abah ɗin, ta kuma ɗau alwashin daidaita komai a tsakanin AA ɗin da Maanal ta yanda Abahn da kansa zai tattarasu ya kora sashen nasu batare da alwashin nasa ya cika ba.
Yau ɗin yanda Manaal take ta faman sinne-sinnen kai ya saka Oum kamata ta duddungure da faɗin, “Wai Auta ni kike son maidawa surukarki a gidan nan, jiya na saka miki ido ne kawai naga iya gudunki, to kar naji karna gani. Maza tashi muje kitchen ki haɗama mijinki abinci yau kije ki duba jikinsa dai kada mu take doka”.
Murmushi Maanal tayi tana ɓoye fuskarta a jikin Oum ɗin, itako Oum na mata dariya. Atare da Oum suka shirya abinci mai sauƙi ma AA ɗin har kala uku, sai wanda suma zasu ci, dan yauma Abah a sashen Mamy zai karya. Suna kammalawa Oum tace taje tai wanka, yayi da masu aiki keta faman kimtsa sashen kamar yanda suka saba. Ba wata kwalliya Maanal tayi ba, ta dai gyara fuskarta ta ɗan saka kwalli da lipsgloss, sai tai simple ɗaurinta daya zauna mata ɗan kwantaccen gashinta ya ɗan fito ta gaban goshi kaɗan. Tana ƙoƙarin saka turare kiran Amaal ya shigo mata. Ɗagawa tai cike da shagwaɓa dan haushinsu take ji a Kano sunce zasu dawo amma sukai mata wayo. Dariya Amaal ɗin taita mata, sannan ta kwantar mata da hankali akan ai next week in sha ALLAHU suna nan tafe da sauran kayanta, dan Daddy yace sai zuwa ƙarshen sati za’a kai kayan gararsu ita da Huznah. Duk da dai Oum tace a ɗan saurara akwai sauran biki da zasu yi anan Abujan shiyyasa ma bata tare ba. Sosai ita Maanal ma abin ya bata mamaki, yanzu duk wancan kaikawon da akasha na Kano bai kuma isa ba. A fili kam sai suka cigaba da maganar su da Amaal. Tana ajiye wayar mai aikin Oum ta shigo tai kiranta, mayafi ta ɗauka ta sanya, dan haka kawai taji tana jin kunyar fita a haka matuƙa. Tayi ƙyau sosai, duk wanda ya ganta kuma yaga amarya, dan ƙamshinta daban ne, ga ƙunshinta raɗam yanata ɗaukar ido daga baƙin har jan, fatar jikinta kam da tasha gyara ba’a magana, sai wani irin glowing take a idanun mai kallo kamar ka lasheta. Ita kanta Oum kallonta kawai take tana murmushi, ta jima bataga ma’auratan da suka dace da juna ba irin Maanal da Autanta, sai dai ai musu fatan zama lafiya mai ɗorewa kuma. ALLAH ya kawo zuri’a masu albarka……….✍️
🏃Da suwa zamuje sashen AA ɗin ne?.
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
Bilyn Abdull ce 🤙🏻
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
BOOK 2
🅿️➖4️⃣
…….Basket ɗin da aka shirya masa kayan abincin Maanal ta ɗauka, kai kace wani anguwa zasu je ba cikin gidan ba. Sun fito gwanin sha’awa daka gansu kaga uwa da ɗiya ba uwar miji da matar ɗa ba. Oum tasan Mamy na sashen Abah dan haka bama tace Maanal taje ta gaida su ba, shiru ma gidan alamar kowa na sashensa, sai ma’aikata dake ta ƙoƙarin kimtsa ko’ina, sunta gaishesu har suka isa sashen AA. Haka kawai Maanal ke jin kamar tace bazataje ba, amma bazata iyama Oum musu ba duk tsanani. Kai tsaye Oum ta shige dan tasan bazasu sami kowa a falon ƙasan ba, Maanal dai biye da ita zuciyarta na mata wani nauyi. Dan kana shiga da sallamar sabon fenti dana sabbin kaya zaka fara cin karo. Tabbas dole ne mai kallo ya furta Masha ALLAH, dan kuwa dai Daddy yayi matuƙar ƙoƙari, daga Maanal ɗin har Huznah ya zuba musu dukiya. Duk da asace Maanal ke kallon komai sai da taji hawaye sun cika mata ido sosai, wata irin ƙaunar Daddy da Ammie na ratsata, falon ƙasa ma kenan, bata san yaya kitchen yake ba, kuma su Didi sun sanar mata daga saman har ƙasa Daddy ya cika mata su da kaya. Zuciyar Maanal bata ƙarasa fashewa ba sai da suka hawo upstairs ɗin, ya subahannallah komai yaji, a hakan ma nan ba’a kammala aikin ba dan ga manyan kwalaye nan a ajiye gefe an tule, zama sukai a cikin kujerun dan su an riga an shiryasu, dai-dai nan Fawzan ya shigo shima da alama yaje sashensa ne.
Cike da tsokana yace, “Inyee kaga Lilly amaryar Auta”.
Da sauri Maanal ta ɗan waro masa idanu, sai kuma ta ɓata fuska. Dariya Fawzan yake yi, Oum dake tayashi ta ce, “Ni ban taɓa ganin yaya irinka ba Fawzan, anya kuwa bazan turaka hutu Kano ba ka bar min yara su shaƙata”.
Dariya sosai Fawzan yake yi, ya kai zaune kusa da Oum ɗin yana gaisheta, itama Maanal ɗin sai ta gaisheshi. Oum ce kawai ta tambayi yaya jikin Autan nata, Maanal kam kunya ta hanata yin hakan. Fawzan ya ce, “Da sauƙi sosai Oum, dan tare mukaje massallaci ma da asuba yau. Ku shiga mana ai ya tashi”.
Murmushi Oum tai da faɗin, “Alhamdullahi”. Sai kuma ta juya ta kalla Maanal da kanta ke’a ƙasa. Cike da kulawa ta ce, “Auta tashi ki shiga masa da abincin gamu nan zuwa”. Kai kawai Maanal ta iya ɗaga mata, sai dai ji take kamar tace ma Oum ɗin a’a amma babu dama. Haka ta ɗauka basket ɗin kanta a ƙasa, Fawzan ne yay mata nuni da ɗakin yana tsokanarta, ita dai yau babu bakin maida murtani sai Oum ke kare mata. Sai da tai ɗan jimm a tsaye kafin tai knocking da yatsanta ɗaya kamar mai jin tsoro, tabbas badan bazata taɓa iya musu da Oum ba komi za’ai bazata je inda yake ba, duk da kuwa har cikin ranta tana jin damuwa da rashin lafiyar tasa. Jin shiru ta sake yin knocking ɗin, sai kawai jitai daga falo Fawzan nace mata ai ta shiga kawai ba lallai yajita ba. Nan ma jitai kamar ta saki hawaye, amma haka ta danne kamar mai tsoron shiga wuta ta tura ƙofar ɗakin a hankali. Sai da ta ɗan rumtse idannunta taja numfashi kafin ta saka ƙafarta a hankali lips ɗinta na motsawa alamar sallama. Bata kalla cikin ɗakin ba ta maida ƙofar ta rufe, yayinda wani sassanyan ƙamshi ya daki hancinta, ɗan sanyin acn da aka saka kaɗan yay wani shiga jikinta. Sosai ta saki ajiyar zuciya a cikin ƙirjinta. Sai kuma ta shiga bin ɗakin da kallo jin alamar kamar babu mutum, babu kowa kam, sai dai gadon babu gyara alamar yanzu aka tashi a kansa, ɗakin ya tsaru matuƙa, ga komai dai-dai misali babu wani tarkace, duk da safiya ce babu yawan haske a ɗakin, dan labulayen duk a sake suke, fitulun kuma a kashe sai mara haske sosai kalar blue. Hakan ya saka launin ɗakin sake zama mai ɗaukar hankali. Nanma ajiyar zuciya ta sauke, sai kuma ta cigaba da takawa a hankali kamar mai sanɗa da nufin ajiyewa ta fice abinta tunda ALLAH tasota baya ɗakin, sai dai kuma da’alama shirin nata zai bi ruwa, dan tana gab da isa tsakkiyar ƙaton bedroom ɗin ƙofar bathroom dake daga can cikin closet ɗinsa da zaka iya hangowa ta cikin ɗakin ta buɗe, harga ALLAH da farko tsorata tayi dan haka ta kalla wajen, sai dai kuma da gudu ta ɗauke idanun nata zuciyarta na wani kalar bugawa saboda saukarsu a kansa. Ba ƙaramin jin ta gama rikicewa tayi ba, dan daga shi sai ƙaramin towel daya ɗaura a ƙugunsa, buɗaɗɗen jikinsa jiƙe da raɓar ruwa alamar wanka yayi, dan hatta sumar kansa a jiƙe take itama dai da alama wanketan yayi. Shima dai cak ɗin ta tsaya, dan ganin nata ya saka shi jin shock na rashin zato dan tunda suka dawo bai gata ba, duk ciwon nan bata shigo dubashi ba. Kamar zai ɗauke kai dan jin haushi. Sai dai ganin yanda tai tsammm kanta a ƙasa ya sakashi sakin wani shegen murmushin gefen baki yana ɗan yin luuu da idanun nasa kamar zai lumshesu. Ƙaramin towel ya cira dake rataye a jikin wani ƙyaƙyƙyawan hanger dake gab da ƙofar bayin, dan an tsara su ne a wajen kala-kala ta cikin closet ɗin gwanin birgewa. Saman kansa ya kai towel ɗin kafin ya fara takowa harya fito daga closet ɗin gaba ɗaya.
Bedroom slippers ne a ƙafarsa masu taushi, duk da ba ƙara sautin takun nasa ke badawa ba sai take jin sa ita har tsakkiyar kanta, karo na farko a rayuwarta da taji wani mashahurin tsoron kasancewarsu su biyu kacal a waje, da ace zata iya da ɓacewa kawai zatai a ɗakin ta huta. Amma babu damar hakan gareta tunda ita ba aljana bace. Yana isowa gab da ita batama san wani ƙarfi yazo mata ba tai saurin juya masa baya tana sake ƙarfin rumtse idannunta hannayenta biyu data riƙe basket ɗin na ƙara damƙe shi da ƙyau. Cak ya tsaya shima dariya na neman cika masa zuciya, dan yanda ta juya ɗin da saurinta sai ka ɗauka wani kumurcin maciji ta gani ko zaki. Da ƙyar ya iya danne dariyar dake cinsa a rai ya matsa jikinta sosai, tsabar neman magana sai ya zagayo da hannayensa ta gefe da gefenta ya ɗaura akan nata hannayen dake riƙe da basket ɗin, badan ya riƙe hannun nata da ƙyau ba da sai basket ɗin yayi faɗuwar da abincin zai tarwatse a wajen. Yanda ta takure jikinta waje guda ya sake bashi damar manne jikinsa da bayanta sosai tare da duƙo kansa saman kafaɗarta yana busa mata numfashinsa a saman dokin wuya da cikin kunne, sannu a hankali ya sake matsar da fuskarsa jikin tata idanunsa a lumshe, kwantaccen gashin kumatunsa dake da damshin ruwa na gogar gefen fuskar tata. Da sauri ta zame hannunta dake riƙe da basket ya koma nasa hannun gaba ɗaya. Karo na farko ya saki ɗan murmushi mai sautin da har taji, har yanzu kuma idanun nasa a lumshen suke yana shaƙar ni’imtaccen ƙamshinta. Cikin matuƙar raɗar da koda wani ne a kusa da su da wahala yaji miya faɗa a hankali can ƙasan maƙoshi ya furta, “Good morning Bestie”.
Tsabar yanda maganar tashi taima Manaal shigar zuruff bama tasan ta zabura ba tana ƙoƙarin tureshi, dolensa ya bata damar fita a jikin nasa, dan duk ta daburce har tana neman kaɓe basket ɗin abincin hannun nasa. Hanyar fita ta nufa da sassarfa, muryarta na rawa, harshenta na sarƙewa ta furta, “Su Oum na falo”. Kafin yay wani yunƙuri harta fice. Kansa kawai ya girgiza yana mai sakin murmushin da har sai da haƙwaransa suka bayyana, a ransa kam ayyanawa yake (Zamu haɗe ne ai yarinya).
😂Tace maka ita ba yarinya bace yanzu kana sake maidata baya🏃
★ Sarai Oum ta lura da yanda Manaal ta dawo kamar wadda aka biyo, sai dai batai magana ba har sai da Manaal ɗin ta sanar musu cewar ya tashi. A dai-dai nan ma kiransa ya shigo wayar Oum ɗin. Basu ji abinda ya faɗa ba, Oum tadai miƙe tana murmushi tace su shiga.
Fawzan ne ya fara shiga, Oum biye da shi, itace ƙarshen shiga dan maƙalewa tayi a bayan Oum. Sosai Oum ta nuna farin cikin ganin yanda jikinsa yay sauƙi yau sosai fiye da kullum, shima ganin fara’a a fuskarta sai zuciyarsa ta masa sanyi. Fawzan kam ya tasashi gaba da tsokana shi da Maanal data zauna a cikin yanayin takura, dan tun haɗa idon farko da tayi da AA ta ɗauke kanta bata sake kallon sashen da yake ba. Yanzu ma da Fawzan ɗin ke tsokanarsu kanta a ƙasa sai Oum ke kare musu. A dai-dai nan Saheeba da Nibras sukai sallama. Kafin a basu iznin shigowa Naufal da Anum sun shigo. Kai tsaye yaran inda AA yake suka nufa cike da farin cikin ganinsa a zaune, shima fuskarsa da ɗan sakewa ya ɗaga Anum ya zaunar a jikinsa, Naufal kuma ya zauna a kusa da shi.
Da kai kawai ya amsa gaisuwar da Saheeba da Nibras sukai masa. Ba haka Nibras taso ba, amma har ranta taji daɗin ganin jikinsa da sauƙi sosai yau ɗin. Wani gefe na zuciyarta kuma najin zafin ganin Maanal a tare da shi, gashi data kallesa sai taga idanunsa akan Maanal ɗin suke, ita kuma ƴar ranin hankalin sai wani latse-latsen waya take yi ita adole ga mai aji. Oho ita Maanal bama tasan tanai ba, hasali ma jinta take duk a takure, da Oum zata barta ma da tuni ta wuce abinta ta koma sashenta ita kam…..
__★
A lokacin da anan ahalin gidan ke sashen AA a ɓangaren Mamy tana can tana waya da babbar yayarsu akan batun auren AA ɗin da Nuratu da sukaji su Abah sunyi shiru sunƙi cewa komai ga shi har yau laraba, a yanda tsarin nasu yake kuma daga gobe alhamis ya kamata ace biki ya fara musamman tasu ɓangarensu, amma sunji ɗif babu wani bayani. Shine tai kiran Mamy ɗin dan jin mike faruwa. Bayanin da Mamyn ke mata rai ɓace yasa tace yau zatazo Abujan dan tana Kano. Da wannan sukai sallama.
Zama Mamy tai tana mai dafe kanta. Eh lallai taci nasara akan Abah na hana Maanal tarewa a sashen AA, sai dai tana jin fargaba akan tunkararsa da batun bikin nan kuma. Musamman idan akai dubi da halin da AA ɗin ke’a ciki na ciwo. To amma kuma itama fatanta ai ayi bikin ne. Numfashi mai nauyi ta sauke sosai, tana mai tattara batun gefe ta jingine har isowar yayar tata dai, dan gara su tunkari Abahn tare zatafi samun ƙwarin gwiwa….
Kusan ƙarfe uku na rana kuwa yayar Mamy ta iso gidan. A lokacin kusan kowa yana a sashensa, dan hatta AA yana sashen Oum, daga sallar azhar daya samu iya fita yau shi da sauran yan uwansa suka wuce sashen Oum ɗin. Manaal dai na ɗakin tunda taji motsinsu taƙi fitowa, sai ma tayi kwanciyarta barcin dole, daga baya na gaskiyar ya ɗauketa.
Mamy da kanta ta fito ta tarbi ƴar uwarta, kai tsaye kuma sashenta suka wuce, suna dai-dai gifta window ɗin Oum dake kallon sashen Mamy ɗin sautin dariyar su Fawzan ta shiga kunnunwansu, kasa haƙuri sukai sai da suka leƙa. Aiko idanunsu suka gano musu zaratan mazajen ƴaƴan na Oum zagaye da ita tana bama AA abinci a baki, dai-dai kuma lokacin Babban Yaya shima ya buɗe nasa baki wai ta bashi, shine suka saka sanya dariya, shima Fawzan yace bazai yarda ba ya je aka bashi. Kai da kaga fuskar Oum kasan cike take da farin ciki, haka suma su babban Yayan, farin cikin Oum ɗinsu ya saka fuskokinsu bayyana murmushi na musamman, musamman ma shi da AA da ba cika son yin dariya sukai ba sai sun so. Fuuuuu Mamy ta wuce sashenta zuciyarta na tafasa. Koda suka shiga ɗaki saita sakar ma yayarta kuka. Ita kanta yayar tata wata irin masifa take ji na tafaso mata daga ƙirjinta, amma dole ta danne ta shiga lallashin Mamyn da nuna mata kuka fa ba shine mafita ba. Dole suzo susan abinyi dan al’amarin na Oum fa na neman zame musu ɗan zane. Dan tabbas ta rigada ta gama mallake zukatan yaran nan da salon makirci (kamar yanda suke fassara soyayyar Oum ɗin akan su AA. Sai dai kuma wannan nasu mummunan zaton ne kawai, dan ita dai baiwar ALLAH Oum har cikin zuciyarta ne, hasalima takan manta da cewar ba itace ta ɗauka cikin su AA tai naƙudarsu ba saboda yanda ta sakankance matuƙa)………✍️
_Dangin Mamy ina gaisuwa 🙄🥱🏃_
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏