Search
You have no alerts.

    MAKAUNIYAR KADDARA

    MAKAUNIYAR ƘADDARA😭

            *_Bilyn Abdul ce🤙🏻_*

    Da sunan ALLAH mai rahama mai jinƙai. Ya UBANGIJIN al’arshi ka bani ikon rubuta abin zai amfani al’ummar MANZON ALLAH. Ka tsare harshena da alƙalamina rubuta abinda zai cutar da ni da duk wanda zai karanta littafin nan. Ka bani ikon rubuta abinda zai amfaneni duniya da lahira ni da masu karatun.

    Ina mai farin cikin sake dawowa a wannan karon tare da ƴan uwana, yanda muka fara lafiya ALLAH ya sa mu gama lafiya, UBANGIJI ya bamu kariya yay riƙo da hannayenmu baki ɗaya.

    Ya rabbi ka gafartama Mahaifina da sauran al’umma da suka rigamu gidan gaskiya. Idan tamu tazo ALLAH yasa mucika da imani. ALLAH ka wajabta mana tsoranka da soyayyar MANZON ALLAH😭🙏🏻.

    Zafafa Next level

    Page 1

    …………..“Inada tabbacin wannan itace tashar da zaki iya samun motar duk wani gari da kike buƙatar zuwa”. Mai napep ya faɗa dai-dai yana samun wajen fakin, da ɗan karkato kansa yana duban yarinyar dake a baya zaune.
          Batace da shi komaiba. Sai ƙoƙarin kwance haɓar zaninta da takeyi jikinta na rawa. Ta miƙa masa ɗari biyar ɗin dake a ƙudundune saboda uban ƙullin da tasha a cikin zani. Baki ya buɗe kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ya ɗan fisgi ƙudundunanniyar ɗari biyar ɗin daga hannunta yana ƙunƙuni ƙasa-ƙasa.
          A yanzu ɗinma batace da shi komaiba, sai hawayen dake famar zarya daga idanunta zuwa kumatu.
    Tsohuwar ɗari biyu guda biyu da naira talatin a sama ya miƙa mata fuska a tsuke.
        “Nagode”.
    Ta faɗa a karo na farko tana amsar kuɗin. Batare da ta jira amsarsaba ta fito daga Napep ɗin tana kalle-kalle da ƙoƙarin sake maida kuɗin daya bata a haɓar zani ta ƙulle kamar ɗari biyar ɗin ɗazun.

         A kallo ɗaya zaka iya fahimtar ƙarancin shekarunta. Dan kuwa bazata wuce shekaru sha huɗu ba. A tsarin halitta batai kama da mai taɓin hankaliba, amma a yanayi zaka iya kiranta da mai ƙarancin hankalin. Duk da kuwa babu wani datti ko makamancin hakan a kaf illahirin jikinta.
          Ƙara kai hannu tayi ta share hawayenta a karo na babu adadi, cikin rauni da alamun tsoron dake tattare da ita ta furta, “ALLAH gani gareka. Da kai na dogara, a gareka kuma nake buƙatar taimak……”
         “Ƙanwata ina zakije?”.
    Karaɗin wani kwandasta ya katseta batare da takai ƙarshen addu’arta ba. Kallonsa tai da jajayen idanunta dake a kumbure saboda kuka tace, “Danya”.
           “Danya? Ƙanwata sai kinyi ƙarin bayani, dan nikam bamma taɓajin sunan wannan garin ba”.
        Shiru tai alamar nazari, ‘Gaskiyar kwandasta ɗin nan. Danya dai garinsu motama bata shiga sosai. To amma idan bata mantaba lokacin da zasu taho da Hajji Lanti bayan sun fito daga Danya a mashin, a Gozarki suka kwana, washe gari kuma daga Gozarki sukazo kusada, anan suka sami motar Katsina’.
           “Wai kodai bakisan ina kika dosa bane ƴammata?”.
         Kwandasta ɗin nan ya sake katseta. Da sauri tace, “Kusada zanje”.
         “……Kusa da kano, nesa da birnin katsina” kwandasta ya faɗa cike da barkwanci. ita dai batace da shi uffanba, sai ma faman waige-waige da takeyi, har yanzu akwai tsoron ko wani zai iya biyo bayanta tattare da ita.
         “Kinga ga motar da zaki hau can ta kaiki Gidan mutum ɗaya. Inada tabbacin daga can zaki samu motar kusada ƴar ƙyaƙyƙyawa”.
         “Nagode sosai” ta faɗa tana ɗan risinawa. Daga haka tai gaba da sassafa batare data sake bi takansa ba.
          Tana isowa motar daya nuna mata ko jiran ba’asi bata tsaya yiba saboda jin kwandasta ɗin motar nata faman faɗin, “Charanci, kankia, Gidan mutum ɗaya, Tsanyawa, Bichi, har kano.
        Can baya ta shige inda wata mata ke zaune ita da yaranta biyu da bazasu wuce sa’annintaba. Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya dasa hannu ta gyara ɗan labulen jikin gilashin yanda take fatan ko su Hajiya biyota sukayi bama zasu iya ganinta ba. Duk da hakan kuma roƙon ALLAH take a ranta ALLAH yasa motar ta cika da wuri su tafi.

         Addu’ar tata kuwa ta amsu. Dan ko cikin ƙanƙanin lokaci motar ta cika. Ita dai tana duƙunƙune cikin hijjab har kanta. Ko wanda ya shigo ya zauna a gefenta bata kallaba sanda ya shigo. Ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya jin motar ta ɗaga alamar zasu bar cikin tashar.
          Sunyi tafiya mai ɗan tsayi data tabbatar sunbar cikin birnin katsina ta tsinkayi maganar kwandasta na ambaton kowa ya bada kuɗin mota. Ciro kanta tai daga hijjab ɗin bayan ta kunto kuɗin data ɗaure a haɓar zaninta na canjin mai napep. Jin matarnan mai ƴaƴa na tambayar “Nawane gidan mutum ɗaya” ya sata tsaida hankalinta tana jiran amsar kwandasta ɗin itama.
        “Ɗari huɗu ne kuɗinki hajiya”. Ya bata amsa yana amsar kuɗin na kusa da shi.
        Matar tace, “Haba ɗana adai duba. Wlhy jiya a ɗari uku-uku mukazo. Yaran nanma ɗari bibbiyu na biya musu”.
         “Ai jiya kikace hajiya. Jiya kuma ba yau bace. Dan haka kuɗinki keda yaranki dubu da ɗari biyu ne”.
          Zatai magana wani dake can gaba yay saurin amshewa. “A’a fa gaskiya ɗari uku ne, ni kaina ɗazun nan da safe nazo a haka”.
         A take rigima ta kaure tsakanin kwandasta da matarnan da mutumin da yay maganar da safe yazo a ɗari uku. Da ƙyar dai aka tsaya akan ɗari uku da hamsin.
         Ita dai yarinyarnan dama bata tanka ba. Ta miƙa masa ɗari huɗun da mai napep ya bata canji.
          “Ƙanwata ina zakije?”.
    A taƙaice tace, “Gidan mutum ɗaya”.
         Canjin hamsin ya miƙo mata. Batare datace komaiba ta amsa ta maida a haɓar zaninta. Sai dai bata koma cikin hijjabinba tabi ayarin masu kallon hanya. Kasancewar motar mai lafiya ce bayan sallar la’asar kaɗan suka iso gidan mutum ɗaya. Danma sun ɗanyi tsaye-tsaye a hanya na sauke mutane.
              A gidan mutum ɗayarma dai a rikicen take. Dan ba taɓa yin tafiya irin haka ba sai wannan karon. Sanda zasu tafi kuwa hajji Lanti ce tai musu komai. Da ƙyar ta samu ta tambayi wani yaro mai saida biredi inda zata sami motar kusada. Shine ya nuna mata. Tai masa godiya.
           Ta iske ƙananun motoci kusan huɗu dake jere a kan hanyar da yaron yace mata itace hanyar kusada. Lokacin da suka tafi su tun daga cikin kusada suka shigo motar katsina.
         “Ƴammata kusada ne?”.
    Wani tsamurmurin saurayi ya faɗa yana nufota. Saurin ɗaga masa kanta tayi alamar eh. Cike da jin daɗi yace, “Yauwa taho muje, dama mutum ɗaya muke nema”.
        Har cikin ranta taji daɗin hakan. Ya nuna mata jar motar data gama fita hayyacinta. “Yauwa shiga nan. Bayin ALLAH a matsa mata mu kama hanya ko”.
          Cike da mita fasinjojin suka shiga muskutawa dan sama mata waje. badan wajen zai wadacetaba ta shiga ta zauna. Sai dai kasancewar ta mai ƙaramin jiki yasa bata takuraba matuƙa. Sai dai waɗanda ta tarar a ciki sunata faman mita sukam an takura musu. Direban ya cika haɗama da son kuɗi. Yanda direba bai tanka musuba itama bata tanka ba. Sai dai acan ƙasan ranta daɗi takeji zata koma gida taga Babanta da su Yaya Tinene, duk da su ba son ganinta sukeba.
          Tsabar rashin isashshiyar lafiyar motar basu iso ba sai gab da magriba, dan sun kwashe kusan awa ɗaya da rabi a hanya. Ga tsaye-tsaye da suka dingayi ana sauke wasu da ɗauka a ƙananun ƙauyika har kusan sau uku.
        Hankalinta bai tashiba sai da suka iso taga kowa na miƙawa direba ɗari da hamsin kuɗin mota. Cike da tashin hankali da fargaba ta miƙa masa naira tamanin ɗin da suka rage mata. Wani banzan kallo yay mata sheƙeƙe yana nuna kuɗin.
        “Naga kina miƙamin murtala huɗu (80n), bakiga abinda kowa ke badawa bane?”.
          Cikin rawar murya da cikowar ƙwalla a idanunta tace, “Wlhy su kaɗaine suka ragemani, dama ɗari biyar ce na taho da ita da ga katsina, to sai naba mai ƴar ƙurƙura……”
          “K! dakata. Wannan damuwarkice ba tawaba. Inda kinsan baki da kuɗin mota da baki bari nayi jigilar ɗakkoki ba ai. Dan haka ni kuɗina kawai na sani ba wai yanda kika taho daga katsina ba”.
           Sharr hawaye suka shiga sakko mata. Ta durƙusa a ƙasa zata fara roƙonsa, hayayyaƙo mata yayi da masifa. A take hankalin mutane ya fara dawowa kansu. Ita dai duƙe take tana kuka da roƙonsa.
             A mutanen da suka taru wajen duk basu bata goyon bayaba. Acewarsu miyyasa bata faɗa masaba kafin ta shigo. Idan data faɗa in yaso saiya taimaketa. Suma ɗin haƙuri take ta basu ita dai, dan harga ALLAH batasan adadin kuɗin motar ba. Hakama direba da zugar mutane ke sake harzuƙawa yana mata tujara.
            Tun tana roƙonsu a duƙe harta koma gurfane abin tausayi. A haka wani saurayi da tausayinta ya kamashi ya ciri naira ɗari ya bama mai motar. Daga haka suka sama mata lafiya. Har ƙasa ta duka taima saurayin godiya. Yace karta damu, tadai daina shiga mota babu kuɗi. Gara ma idan bata da shi ɗin ta dinga faɗa kafin ta shiga zaifi sauƙi. Godiya nanma tai masa ta miƙe riƙe da naira talatin ɗin daya sake rage mata tunada an biya mata ɗari.

           A kusada ɗinma ba sanin ina zata gano hanyar garinsu tai ba. Dan tunda tasan kanta bata taɓa zuwa cikin Kusada ba. Iyakarta ƙananun ƙauyukan dake gefen ƙauyensu kawai.
          Tana son tambaya tanajin tsoro, ga wani azababben ciwon ciki da takeji yana taso mata kaɗan-kaɗan. Duk yanda taso cigaba da tafiya sai ya gagara. Da ƙyar taja ƙafafunta zuwa wata runfa ta zauna. Da alama runfar mai yin faci ne. Kasancewar magriba tayi harya tashi.
         Zama tai ta duƙunƙune kanta cikin kafafu jikinta na rawa. Ga wata irin zufa na keto mata ta ko ina saboda azabar ciwon ciki. Tun tana zaune har sai da takai kwance a wajen tana juye-juye. Bata damu da cinnakun daketa galla mata cizo ba a jiki, dan ciwon da cikin nata ke mata ya danne komai.
          Tsahon lokacin data ɗauka a yanayin ciwone yasa har dare ya rufa bata saniba. Sai jin garin tai ya rage hayaniyar jama’a. Ba ciwon cikin bane kaɗai matsalarta harda Yunwa da ƙishi. Dan rabonta da abincin kirki tun jiya a gidan Hajiya. Abincin da aka bata a gidan da aka kaita ƙinci tayi sosai, dan tana tsoron taci su yanke mata kanta kamar yanda zuciyarta ke bata danshi suka kaita gidan.
        Tashi tayi zaune a hankali tana ɗan waige-waige. Titin babu haske. hakama jama’a duk sun nufi gidajensu sai ɗai-ɗaiku. Duk yawan motoci da mashinan ɗazun yanzu babusu. Sai wasu da basu wuce uku ba. Mashinanma bazasu gaza haka ba. Sai fitilar mai shayi da take hangowa can a wajen da motocin ke tsayawa (Tasha).
         Komawa tai ta kwanta. Dan haka kawai taji wani shegen tsoro ya turniƙeta. Ta rufe idanunta gam tana karanto abinda ta sani na addu’a. Cikin amincin ALLAH kuwa sai ga barci ya kwasheta. Da alama hakan nada nasaba da gajiyar dake tare da ita ta wahalar tafiya da gudun da taci kafin samun Napep..

    ★★★★★

           Tun kiran sallar farko na asubahi ta farka da wani irin ciwon ciki. Murkususu ta dingayi tana kuka. Ta jima tana shan azaba kafin ya lafa mata. Zuwa lokacin anata ƙoƙarin shiga sallar asuba. Tashi tai a jikkace, dan yunwa takeji sosai. Ta taka a hankali zuwa inda massallacin tashar nan yake. Butocin da akai alwala ta dinga taɓawa harta sami mai ruwa. Ɗakkowa tai ta dawo wajen rumfarnan. Ta zagaya bayanta tai fitsari da yin alwala. Sauran ruwan kuma ta shanye. Sai a yanzune ta tuna ko sallar La’asar ɗin jiya batayiba. Rabonta da salla tun ta azhar da bayan idarwarta ta gudo.
           A take ta fara maka sallolin nan batare da tabi tsarin daya dace na mai ramuwaba. Sai da ta gama jerosu har asubahi. Zuwa lokacin mutane nata fitowa, hakama masu mashina da motoci.
         Da farko zaman kallonsu tayi. Daga baya kuma saita mike bisa shawarar zuciyarta. Ƙarasawa tai wajen mai  shayin nan daketa ƙoƙarin ɗora tukunyar garwar shayinsa yana raira waƙar shata. bayan ta masa sallama ya amsa ta gaishesa da girmamawa dan babbane ba laifi.
          “Baba dan ALLAH tambaya nake?”.
    Ɗago kansa yay ya kalleta a karon farko. “ALLAH yasa na sani ɗiyata”. Ya faɗa da kafeta da kallon ƙurilla.
       Kanta a ƙasa tana ɗan juya yatsun hannunta cikin juna tace, “Baba dan ALLAH inane hanyar Danya?”.
          “Danya! Danya!?. To indai Danya dana sanice ta kusa da Gozarki hanyarta na nan gabas da mu”.
          Jin sunan Gozarki ya sata kallonsa cike da jin daɗi. Ta kaɗa kanta fuskarta na sauyawa alamar farin ciki tace, “Eh itace baba”.
             Yace, “To zaki zauna ki jira masu mashina dake shiga kenan. Idan kuma bazaki iya jiraba ki samu mai mashin anan ki biyasa talatin ya kaiki ainahin Gozarki ɗin anan zaki samu ƴan mashinan Danya”.
          Taji daɗin shawararsa. Hakan yasata masa godiya. Duk da talatin din ta rage mata a jiki, kuma yunwa takeji gara tabi shawararsa. Babu wani jimawa kuwa ta samu mai mashin. Kamar yanda mai shayi ya faɗa talatin mai-mashin din yace zata bashi. Sai da ta bashima sannan ta hau.
         Cikin mintuna ƙalilan suka iso Gozarki. Amma sai da ya kaita har hanyar ƙauyensu Danya. A take farin cikinta ya ƙara bayyana. Harta zauna da nufin jiran masu mashin dan babu wanda ya fito saboda akwai sauran safiya, sai kuma ta mike. Ba komai ta tunaba sai nasihar saurayin jiya daya cika mata naira ɗari. Bata da ko sile. Mizaisata zaman jiran mashin? Gara ta taka da ƙafa, duk da kuwa tasan akwai nisa. Amma ɗokin gata a kusa da gida sai ya gusar mata da komai har yunwar da takeji da rashin daɗin jiki.
           Tafiya ta fara a doguwar hanyar jan birjin da batasan iyakar lokacin ƙarewarsa ba. Ga ɗan sanyin safiya na busawa kaɗan-kaɗan.

          Tayi tafiya mai nisa ciwon cikin nan da batasan dalilinsaba a kwana biyun nan ya ƙara turniketa. Ƙarƙashin bishiyar dalbejiya ta samu ta zauna. Taci murƙususnta da kuka na wani lokaci kafin ta tashi ta cigaba da tafiya. Zuwa lokacin ƴan mashinan garinsu nata fitowa ɗai-ɗai da fasinjoji akai.
           Kafin ta gama ankara rana ta ƙwalle. Ga yunwa na cigaba da ragaɗar hanjin cikinta. Haka ta cigaba da jurewa tana jan ƙafafu tamkar mai tsohon ciki. A lokacin da dukkan wani ƙarfinta ke gab da ƙarewa ne ta hango rufin ginin makarantarsu dake da matuƙar tsaho fiye da duk gine-ginen gidajen garin. Ta saki murmushin yaƙe idanunta dake ganin duhu-duhu na lumshewa. Sai faman sauke ajiyar zuciya takeyi da sauri-sauri. A hankali hajijiya ta fara juya mata hanyar, saiko gata ƙasa yaraf babu numfashi……….✍

    💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
    TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
    Typing📲

     *_😭MAKAUNIYAR ƘADDARA!!😭_*
    
    
    
    
                *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

    ZAFAFA 5 NEXT LEVEL

    Page 2

    …………Saukar ruwa mai bala’in sanyi a jikinta ne ya sakata farkawa a firgice. Ta zabura zata ƙwalla ihu taji an riƙeta.
           Kafin ta gama tantance abinda ke faruwa muryar da bata gama sanin ta wacece ba ta tsinkaya yana faɗin, “Haba innar Karima, yanzu yarinyar da aka tsinto cikin wannan halin akema wannan izayar haka? A ganina kamata yayi musan halin da take ciki ai k…….”
            A fusace, cikin katseshi tace, “Sallau! Ince dai kai ka gama naka?. Kokuwa bayan taimakon kawota gida akwai wata a ƙasa ne a tsakaninku?”.
           Da sauri Sallau ya dubi tsirarun mutane da tarin yara da suka biyo bayanshi saboda ganin a yanda ya shigo da yarinyar cikin garin tamkar mara numfashi.
          Yace, “Haba! Haba! Innar Karima. Da ga taimakon yarinya kuma sai ki fassarani da neman laƙamani laihi. Naga dai na maki bayanin komai ban ɓoye maki a yanda na tsintota bisa hanyar shigowa gari a yashe ƙasa bata lunhwashi ba, kuma agaban kowa na hiɗi”.
           Baki ta ƙyaɓe tana wani juya idanunta abin tsoro, ta nuna masa hanyar ƙofa, “To ga hanya kama gabanka. Taimakonka kuma angode ince dai shikenan daɗa”.
         Cike da takaici Sallau ya buga ƙafarsa ya fito a gidan yana huci. A ransa kuwa sai tsinar Inna ya keyi akan mugun halinta da kowa ya sani a ƙauyen nasu.

          Duk mahawarar dake faruwa a tsakanin Inna da Sallau tana kwance a gefe cikin laimar ruwan da inna ta jiƙeta tana murƙususun azabar ciwon ciki. Yayinda yara da waɗanda suka shigo a manyan ke tsaye cirko-cirko na kallonsu. Matan makwafta nason taimakon yarinyar amma tsoron Inna ya hanasu iya yin komai, dan ba ƙaramar jarababbiya baceba kowa ya sani.
         A wannan halin wani dattijo ya shigo gidan ɗauke da icce saman kansa, sai gatari dake rataye bisa kafaɗarsa ta haggu. Tun a ƙofar gida yaci karo da tsirarun mutane, hakanne ya sakashi shigowa gidan da matuƙar sassafa. Ya jefar da iccen gefe guda saboda ruɗewar sake ganin wasu mutanen da sukafi waɗanda ke a waje yawa. Kafin yace wani abu nishin kukan yarinyar ya sashi saurin kai dubansa gareta.
          “Subahanallahi Zinneerah!!”
    ya faɗa a firgice yana nufar inda yarinyar take. Duk da yanda jikinta ya ɓaci a laimar ruwan daya gauraya da jar ƙasar garin bai fasa saka hannu ya kamota ya ɗago ba. Cike da firgicin da yafi na farko yake sake faɗin, “Zinneerah! K Zinneerah mike hwaruwa dake haka? Daga ina kika hito ne?”.
           Ina Zinneerah batasan yanayi ba, sai faman cigaba da murƙususunta takeyi a jikinsa. Duk ta naɗe masa ƙwaɓaɓɓiyar ƙasar jikinta akan matacciyar rigar yadinsa.
         Duk yanda yaso Zinneerah tayi magana bai samu hakanba. Su kuma waɗanda ke tsaitsaye a gidan tsoron Inna ya hanasu cewa komai. Yayinda ita kuma taketa sakin ɗanwakenta a tukunya tamkar batasan da shigowar mai-gidan ba ma.
         Tsahon lokaci suna a wajen har ciwon ciki ya lafama Zinneerah tai luf a jikin dattijon tana sauke tagwayen ajiyar zuciya. Da tsananin damuwa tattare da muryarsa yace, “Sannu Zinneerah, sannu kinji”.
           Kanta ta ɗago a karon farko ta dubesa, sai kuma ta yunƙura da ƙyar ta tashi zaune tana faɗin, “Baba!” kafin ya bata amsa ta maida dubanta ga sauran mutanen dake a gidan har zuwa kan Inna dake gyara wutar ɗan-wakenta. Ta duba jikinta matsanancin tsoro na bayyana mata a kan fuska.
         Kafin wani ya samu damar cewa komai Inna ta miƙe a hasale, dan takai matuƙar cika da haushi. Bakin wuta ta ɗauka tana miƙewa. Kafinma tace wani abu an fara rige-rigen fita a gidan da gudu dan kowa yasan hali.
        Da sauri Zinneerah ta kalli dattijon dake mata kallo irin na tsananin damuwa. “Baba yunwa nakeji”. Ta faɗa tana mai raba hankalinta biyu a kallonsa da kallon Inna dake masifa tana bin mutane da bakin wuta.
           Duk da tsoron Inna dake cike fal da ransa bai ƙi amsa ɗiyar tashi ba. Ya miƙe da rawar jiki yana faɗin, “To Zinneerah jirani”.
           Buta ya ɗauka ya nufi bayinsu, yana shiga ya ajiye butar yana waige-waige. ta inda katangarsu ta faɗi akai dannin itacen geza yay dabarar ficewa a gidan, yasan mutum ɗaya ce zata iya zuwa gidan ta taimaki Zinneerah daga halin Asabe. Duk da yunwar dake cin hanjin cikinsa shima bai fasa ɗaukar hanya ba zuwa ƙauyen Sanni inda babbar ɗiyarsa ke aure. Da yake babu nisa sosai, rafi ne ma kawai ya rabasu.
          A ƙasan ransa yana matuƙar jin ƙuna da zafin halin da ɗiyarsa Zinneerah ke a ciki, sai dai tsoron matarsa Asabe bazai barsa yay maganaba. Shi kansa yaga ƙarfin halinsa ainun a yau da har ya iya fuskantar Zinneerah kai tsaye, sai dai yasan shirun da Asabe tayi bana alkairi bane dan cike take da shi.
         Da wannan tunanin Baba ya iso ƙauyen Sanni.

           Ƙauyen Sanni ƙaramin garine da ko rabin rabin Ƙauyen Danya bai kaiba. Gaba ɗaya gidajen garin basufi goma sha biyarba. Sai dai a kowanne gida zaka samu family house ne mai tarin iyalai.  Kasancewar irin wannan lokacin na rani babu yawan maza duk sun tafi neman kuɗi birni sai mata kawai a gari da yara. Tun daga ƙofar gidansu Gajeje dake jerin gidaje uku da sukafi kowa yawan iyalai a ƙauyen ake jiyo arerewar mata da ihun yara da luguden daga.
        Baba yaɗan matsa ga yaran dake a gindin bishiyar ƙatuwar ceɗiya suna wasan langa. Ɗaya daga cikinsu ya taɓa yana faɗin, “Ɗana ko Gajeje na ciki?”.
           Wanda aka taɓa ɗin ya sauke ƙafarsa dake a ɗane yana kallon dattijon. “Eh baba tana nan, yanzuma suka gama sussukar maiwa anan”.
         “Yauwa dan ALLAH sanar mata ana sallama”.
            Kamar yaron bazaijeba sai kuma ya kwasa da gudu yana faɗin, “Kai Garzali ku jirani indawo”.

          Ba’a wani ja lokaciba wata mata ta fito, a yanayinta zaka ɗauka wani shekarune da ita masu yawa. Sai dai a kallon idanu zaka samu amsar ƙarancin shekarunta. Wahalar rayuwace kawai ta maidata tamkar mai shekaru arba’in a duniya. Ta gyara gyautan zanen data yafo a kanta tana washe baki da fadin, “A’a lale-lale. Baba kaine tahe a tsakkiyar ranarnan haka?”.
           Baba dake duban ɗiyar tashi daso da kauna ya murmusa yana jinjina mata kansa, “Nine kuwa tahe Gajeje”.
          “To sannu da zuwa Baba. Bara na kawo maka tabarma da ruwa ko…”
        Saurin dakatar da ita yayi ganin zata juya. “A’a Gajeje dakata, tahiyarnan tawa bata lahiya bace. Dan haka zama bai ganni anan ba”.
         Cike da tsoro tace, “Wani abune ya faru kuma? Ko Innace tsiyar tata ta motsa yau?”.
          “To ba’ace ba dai Gajeje. Ƴar uwarkice ta dawo cikin wani yanayin da sam ban gane masaba. Yanzu haka na barota a gida tana maɗoɗowar yunwa. Gashi kuma naga ran Asabe a ɓace yake, dan ko uffan taƙi hiɗi mani, kinsan kuma bata barin kowa ya hiɗi yanda akai ko?”.
           “Wai Baba kana nihin Zinni ce ta dawo gida?”.
        Da damuwa ƙarara a fuskarsa ya ɗaga mata kai.
           Zanen kanta ta gyara kawai rai ɓace tace, “Muje baba. Dan inna zumace sai da wuta. Karta sake bi ta hanyar da tabi a baya ta maidata wani gun kuma”.
          Sosai yaji daɗin hakan. Dan haka suka kamo hanyar komawa Danya suna tattaunawa akan matsalar Inna Asabe da halin da Zinneerah ke ciki a dalilinta.

    ★★★

             Baba da Gajeje sun iske ƙofar gidan a yamutse da hayaniyar Inna da wasu a mazan maƙwafta da suka kasa haƙuri suka tanka mata akan dukan Zinneerah da tahau yi tun bayan barin Baba gidan. Yayinda Zinneerah ke gefe tana murƙususun ciwon ciki.
         Ran Gajeje a ɓace da halin mahaifiyar tasu ta shiga cikin rikicin da ƙyar ta lafar da kowa. Kusan minti talatin aka samu wajen ya nutsa. Inna ta shiga gida mutanen dake a ƙofar gidan kuma kowa ya kama gabansa ana zagi da ALLAH wadai da halin Inna Asabe na rashin tausayi.
          Sai a lokacin Gajeje ta samu damar kama Zinneerah dake kwance gefe buɗu-buɗu da ƙasa tamkar an tonita a rami. Gidan ta shiga da ita, Inna zata fara sabuwar jaraba Gajeje ta haɗe fuska tana faɗin, “Innarmu! Innarmu!”.
         Shiru tayi saboda sanin halin babbar ƴar tata itama. Sannan duk yanda takai ga hawa akan masifarta da Gajeje tayi magana bata iya cigaba saboda wani dalilinta daba kowa ya gama saninsa ba.
           Itama Gajejen bata sake cewa komaiba sai kallon Tinene ƙanwarta tayi. “Ke Tinene ɗaukamin karauni a ɗakinku”.
         Baki Tinene ta cika da iska tana ƙunƙuni, sai dai kuma babu damar ƙinyi. Fuuu ta shige ɗakin kwanansu da ada can shine ɗakin mahaifiyar Zinneerah kafin tabar gidan. Wata tsohuwar tabarmar karauni ta ɗakko zuwa gindin bishiyar mangwaro dake a kusan tsakkiyar gidan. Zinneerah na zaune an jinginata da bishiyar, Baba na daga tsaye gefenta kaɗan yana kallonta dayin hawayen zuci. Sai Gajeje dake can kusa da Inna a gaban murhu taɗan kara ruwa jikin wutar ɗan waken Inna na saidawa dan yay ɗumi.
                Gidan yay tsit babu mai cewa uffan duk da kuwa kowa nada abin cewa a bakinsa. Musamman ma Baba, sai dai tsoron matarsa Inna bazai barsa iya furtawaba duk da tsantsar tausayin ƴarsa dake ransa.
          Gajeje ta juye ruwan ɗumin a wani roban wankansu ta sirka takai banɗaki tazo ta kama Zinneerah ta miƙar. Har banɗaki ta kaita da kanta. Bata wani tsaya jan zance ba ta ɗaurayema Zinneerah jiki da kanta duk da kuwa tanata mammaƙewa dan nauyin yayar tasu da suke kallo tamkar uwa a garesu. Tinene ta ƙwalama kira ta kawo mata zani da riga.
                Sosai Zinneerah taji daɗin jikinta da wannan wanka. sai faman sauke ajiyar zuciya takeyi da lumshe idanu. Baba dake tsaye har yanzu da kansa ya gyara mata tabarmar ta kwantar da ita.
          Inna na kallonsu a kaikaice, watsama Baba wata uwar harara tayi tana yin ƙwafa. Sai dai kuma batace komaiba ta cigaba da tsame ɗanwaken ta.
            Duk da Gajeje taga harar da Innar tasu taima mahaifinsu bata tankaba. Sai ma kwance gefen zaninta tayi tana ciro nera hamsin data sha ƙudindina. “K Tinene zokije nan wajen Dijen kamaye ki sayo mani kunu da suga”.
         “Yaya Gajeje tallafa zan ɗauka, kina ganin Inna harta gama kwashe ɗanwake, gahi Sa’a bata dawo ba, Karima kuma na rimaye”.
          Wani mugun kallo gajeje ta watsamata, a hasale tace, “Ni kike hiɗima haka Tinene?”.
          Kafin Tinene ta bata amsa Inna ta dubesu a hasale. “Wai Gajeje miyasa ke baƙya son zaman lahiyane? Ai gaskiya Tinenen ta hiɗi, inke idonki bai gane miki na kwashe ɗanwakenba”.
           “To amma Innarmu koda shirin ɗaukar ɗanwaken take nanda gidan Dije ne zai gagareta zuwa ta sayo mani kunu? Kenan iya shegen da sukema kowa nima ya hwara zuwa bisa kaina?”.
           Yanda Gajeje ke magana a hasalene ya saka Inna cewa, “K Tinene amshi ki sayo mata, ni bansan wani kace-nace”.
          Tinene na faman tunzura baki da ƙunƙuni tazo ta amshi hamsin ɗin ta fice bayan ta ɗauki wani tsohon kofi. Babu jimawa sai gata da kunun kuwa. Kusan tare suka shigo da Sa’a ɗauke da ƙaton botiki mai ɗauke da sauran gyaɗa da riɗi da taje talla.
          Da sauri ta ƙarasa shigowa tana fadin, “Kai, Kai, Zinni! Yaushe kika dawo?”.
           Murmushin ƙarfin hali Zinneerah taima Yayar tata da itama ke ƙaunarta a gidan, sai dai kuma ta kasa bata amsa sai Yaya Gajeje ce dake zuba suga a kunun da Tinene ta sayo ta bata amsar.
        Kafin Sa’a da hawaye suka cikama ido tace wani abu Gajeje ta maida hankalinta ga Tinene. “K samo mani lidde”.
          “Mu bamu da lidde nan gidan”. Cewar Tinene tana murguɗa baki.
        Jikake bamm! A goshin Tinene, Gajeje ta jefa mata murfin kwano dake kusa da su.
         A take ta zube ƙasa ta fara kururuwar ihu kamar wandda aka kashe. Inna ta saki kwanon yaji a ƙasa ta nufi ƴar tata da sauri. “Gajeje kashemin yarinya zakiyi akan wannan sheɗaniyar yarinyar data gudu yawon tambaɗarta?”.
          “Kaɗanma na mata Innarmu”.
    Gajeje ta bata amsa rai ɓace.
          Cikin raɗa-raɗa Sa’a data je ta ɗakko mata ludayin tace, “Yaya Gajeje ki ƙyalesu dan ALLAH, karki tahi gida a huce kan Zinni. Kindai san halin Innarmu ai”.
         Shiru Gajeje tayi bata tankaba. Baba ma dake tsaye har yanzu bai tanka musunba, hasalima hankalinsa na kan Zinneerah da ke shan kunun cike da zalamar yunwar da takeji.

          Zuwan Gajeje gidan ya matuƙar taimakawa wajen bama Zinneerah kulawa. Inda kuma ya katange duk wani bala’i da masifar dake cin Inna a rai. Dan bayanma ta kammala saida ɗanwakenta su Tinene sun ɗauka wani sun wuce talla zani ta ɗauka ta fice gidan wai taje barka wani ƙauye dake can gefensu shima.
         Hakan yama baba daɗi sosai. Dan koba komai sa samu damar jin yaya akai Zinneerah tabar gida a kwanaki ashirin da shida da suka shuɗe, da kuma yanda akai ta dawo musu yau a wannan halin?.
              Suna zaune shi da Gajeje suna tattaunawa akan hakan Zinneerah dake barci tun ɗazun ta farka a firgice da ciwon ciki. Duk kanta sukayo suna tambayar ko lafiya?. Bata iya amsasuba sai da ya lafa mata.
        Ta share hawayen dake sauka a kumatunta. “Yaya Gajeje cikina kemin ciwo”.
         Basu kawo komai a ransuba sai yunwa. Dan haka Gajeje tace, “Zinni yunwace nasani. Sannu kinji. Idan zaki iya tashi kiyo alwala kiyi sallar azahar da la’asar sai kizo ga abinci kici”.
               “Zan iya yaya Gajeje” 
    Ta faɗa tana maida kallonta ga baba dake kallonta cike da raunin zuciya dana idanu.
       “Baba ina wuni”.
    Murmushin ƙarfin hali yay mata da shafa kanta. “Lafiya lau Uwata yaya jikin?”.
          “Da sauƙi baba”.
    “To madalla. tashi kiyi sallar maraice na ƙara yi”.
          Bata musaba ta miƙe. Jin gidan shiru ya sata sanin Inna da su Tinene duk sun fice. Hakan ya mata daɗi. Alwala tayo tazo ta wucesu zuwa ɗakin kwanansu. Babu abinda ya canja a ɗakin nasu sai ma shirgin kayan dauɗar su Yaya Sa’a. Dama itace mai kimtsa ɗakin dayi musu wanki. Kayan taɗan ture gefe ta tayar da salla cike da ƙarfin hali dan batajin daɗin jikinta gaba ɗaya. Duk da sallar ba’a cikin tsari akayitaba tadai gabatar ta sake komawa wajen baba da yaya gajeje.
              Abinci yaya Gajeje ta fara bata taci. duk da yunwar da take ji har yanzu taci abincin a nutse dan sam dama ita bata da garaje ko gaggawa. Bayan ta kammala ta wanke hannu ne Yaya Gajeje ta ce, “Zinni kinga marece yayi inason na koma gida nabar su Rabi’u. Munason ki nutsu ki faɗa mana yaya akai kika bar gida ne batare da sanin kowaba? Ina kuma kikaje?”.
              Duk da ƙarancin shekarunta hakan bai hanata jin ɗaci ba a ranta. Ta share hawayen dake rige-rigen zubo mata tana gyara zama. “Baba wlhy ban gudu ba. Bayan tafiyarka kasuwa sai I…….
           Jin tayi shiru tana kallon hanyar shigowa yasa Baba da Gajeje saurin kallon wajen suma. Inna ce ke shigowa cikin gidan tamkar wadda aja jeho.
         Ganin yanda duk suka watso mata idanu ya sata fara magana a harzuƙe. “Halan cin nama na akeyi kuka watso mani idanu haka?. Wani annamimancin kike hiɗi masu a kaina ko?”.
         Ta ƙare maganar tana watsama Zinneerah mugun kallo.
            Gajeje ta dubi Baba da yay ƙasa da kansa. ta dubi Zinneerah da itama kan nata ke a ƙasa tana hawaye. Wani irin tausayinsu da jin zafin mahaifiyar tasune ya ɗarsu a ranta, musamman yanda take ƙasƙantar musu da mahaifi a gabansu duk da tsufansa. taɗan girgiza kanta tana dubanta. “Amma Inna miya kawo wannan zancen daga shigowarki? Yarinyar da ke cikin halin ciwo wane kuma munahincinki zatayi?. Ni a ganina kamata yayi kema ki shiga jerin masu murna da dawowar Zinni gida kodan tashin hankalin da muka shiga na rashin sanin inda take a kwanaki ashirin da shida ɗin nan”.
           “Tunda uwatace ta ɓata ko? Kune kuke ɗauka ɓata tayi dama ai, yarinyar da ta tafi yawan taɓaɗanta data saba har kuke damuwa da inda taje. Inda ba guduwa taiba wane shege ne ya dawo da ita yanzu da ƙahwarta?. adai jura zuwa rafi, wataran muna zaune za’a shigo mamu da ɗan dakan kuka na tabbacin yawon tazubar….”
        Tsam baba ya miƙe batare da cewa uffanba ya fice gidan. Itama Gajeje rai ɓace ta miƙe tana magana cike da rawar murya. “Innarmu wannan hurucin naki dai kau sam bai dace ba. Dan koba komai itama Zinni ɗiya take garegi, yanda kuwa take mace haka Sa’a da Tinene da Karima suke mata. Baƙya tsoron mugun alkaba’in da kike hiɗi gareta ya dawo bisa kanmu ne”.
          Wani mugun kallo Inna taima Gajeje. Kamar zatai magana sai kuma tai shiru. Itama Gajejen bata sake tankawaba sai miƙar da Zinneerah da ke kuka tayi suka shige ɗaki. Sai da taga ta kwanta sanann ta fara magana. “Zinni bara naje gida, insha ALLAHU gobe da hwarar sahiya zan dawo, dan akwai raɗin suna gidan malam mato dama da zamu shigo. To daga can nan zan wuto na yini. Ki ƙara haƙuri da halin Innarmu watarana sai labari kinji”.
           Kai Zinneerah ta ɗaga mata tana share hawaye. Muryarta na rawa tace, “Nagode Yaya Gajeje”.
        Murmushi kawai Gajeje tayi da shafa kanta ta fito a ɗakin. kai tsaye ɗakin Inna ta nufa dan tanaso suyi magana………….✍

    0 Comments

    Heads up! Your comment will be invisible to other guests and subscribers (except for replies), including you after a grace period.
    Note
    error: Content is protected !!