JIHAR KANO:
Kano na ɗaya daga cikin manyan birane a ƙasar Hausa. Kano itace cibiyar kasuwanci ta Najeriya gaba ɗaya. Jihar ta Kano tana da ƙananan hukumomi guda arba’in da hudu. Kana gari ne da yake da masarauta mai ɗunbun tarihi, mai kwarjini a cikin kasashen Hausa da kewayenta. Haka zalika Kano gari ne babba wanda mazauna cikinta ke magana da harshen Hausa. Itace gari mafi yawan jama’a a Najeriya baki ɗaya.
Kanon ta yi suna wajen kasuwancin da ta bunkasa a kai, har ya zamana ana cewa da ita Cibiyar Kasuwanci. Haka kuma tarihin Kano ya nuna daman can tana da suna wurin cinikayya tsakaninta da mutanen gabas ta tsakiya.
Yawan mutanen da suke garin na Kano sun haura kimanin mutane miliyan goma (10.000,000) a ƙidayar da aka yi a shekara ta alif dubu biyu da shida. Jihar Kano tana da matuƙar tasiri a yawan mutane Najeriya, saboda ita ce ta fi kowacce jiha yawan mutane daga ko’ina a faɗin duniya, tun daga na kudancin Najeriya, har zuwa ƙasashen dake maƙwabtaka da Najeriya,hakq kuma za ka tarar da mutanen sin ( wato china) da kuma na ƙasashen larabawa har da turawan yammacin duniya mutanen Kano sun shahara wajen addini sosai.
ƘOFAR MATA.
Cikin wani layin masu rangwamen arziki na shiga. Duk da kasancewa safiya ce sosai. Hakan bai hana ganin yara suna kai kawo a cikin unguwa ba. Wasu suna kan layin siyan ƙosai, wasu suna kan layin siyan fanke. Wasu yaran da gasarar kokko na gansu a hannunsu. Kasancewar baifi ƙarfe bakwai da rabin safiya ba. Anata hada_hadar shirin karya kumallo. A bakin wani madaidaicin gida na tsaya marar fenti, mai ɗauke da ƙatuwar bishiyar durumi a ƙofar gidan ƙosasshiyar gaske. A ƙarƙashin wannan bishiyar na hango motoci biyu a fake, ɗayar golf 3 ce, ɗayar kuma Vectra ce. Da dukkan halama motocin ta masu gidance. Wani matashine ya fito daga gidan hannunshi riƙe da bokitin ƙarfe cike dumbul da ruwa, ga soson buhu a ɗayan hannun nashi. A gaban motocinnan ya ajjiye bokitin, nan take ya soma watsa ma Vectra ɗinnan ruwa. Daga cikin gidan dai na jiyo hayaniya na tashi kuma muryar namiji nake jiyowa, har da kukan mace daga bisani na jiyo. Ba shiri na faɗa cikin gidan dan ganin meke faruwa haka.
Abun mamaki ashe gidan babbane sosai daga ciki, gashi da yalwar tsakar gida. Ɗakuna kuwa gasunan a jejjere kamar a zangon baƙi ( Hotel). Maza da matan gidan, harma da yaran gidan na tarar a tsakar gidan. Wani babban mutum na gani yana ta faɗa, muryarshi ce take fita har ƙofar gida. Babbane a shekaru, dan har da furfura a gemunshi da sumar kanshi. A gefenshi na hango wata doguwar fara kyakkyawar mace a tsaye jikinta sharkab da ruwa har ɗiga take yi tsabaragen jiƙewa, kuka take yi ƙaƙas tamkar wacce akayi ma mutuwa, gata ita dai ba yarinya bace. Wannan Dattijon cikin murya mai amon ɓacin rai yace.
“Haula ki dena kukan ya’isa ki bari su fito inji in shi Gwadabenne yasa matar tashi ta watsa miki ruwan kashi sai in ji. Ke da gidan mijinki babu wanda ya’isa ya takura miki wallahi, zan ture zumunta in kori Gwadabe da iyalinshi a gidana, wannan ƙazanta ta buskuta samodarar matarshi ni ya isheni. Ina mai takaici da baƙin cikin haɗa zuriya da matar Gwadabe da mu ka yi” Ya ƙarashe maganar yana huci kamar zaki.”
Gwadabe:.
Read Also: Jidda Na maman Mama
Da sauri ya fito daga ɗakin nashi rigarshi a hannu, shimi ce a jikinshi da koɗaɗɗen wandon jeans wanda akayi ma wanki sama da sau saba’in, duk yayi yaushi, ya sake kala daga turarren bulu, izuwa kalar sararin samaniya.
“Yaya Hambali kayi haƙuri dan Allah. Kema Yaya Haula ki yi haquri. Iyabo ba da saninta ta watsa miki ruwan kashi a jiki ba. Bata san kina banɗakin bane, amman kiyi haƙuri dan Allah, kuma zata kiyaye ” Gwadabe ya faɗa cikin sigar kare iyalinshi, duk da abinda ya faɗan gaskiya ne. Amman dake a hasale suke da Iyabo shi yasa maganar take ƙoƙarin zama babba. Dama ƙiris suke jira ta kuskure su dirar mata a wuya, sabida tsantsar ƙiyayyar da suke nuna ma Iyabo wacce har idanuwansu suka rufe wannan ƙiyayyar tashafi ɗan uwansu gudan jininsu Gwadabe. Harisu wanda ya kasance wa ga Gwadabe, ƙani ga Hambali, ɗa na uku a wajen mahaifiyarsu yace.