💔 JIDDA 💔*
*By*
Maman Maama
Bismillahir Rahmanir Rahim
Assalamu alaikum masoyana da masoyan littattafai na. Kamar yadda nayi alkawari tun kafin in fara Tagwaye cewa zanyi su su biyu da Jidda to alhamdulillah an kammala Tagwaye ga kuma Jidda nan yazo muku, ina kuma fatan zaku karbe shi kamar yadda kuka karbi Tagwaye koma fiye da haka.
Dan dai idan nace Jidda is a must read for every woman zai zamanto kamar naso kaina da yawa ne, amma gaskiya in baki karanta Jidda ba zan iya cewa an barki a baya. It is going to be a hit, that I promise you.
Tafiyar Jidda da banbanci da sauran littattafai na, banbancin kuwa shine about 70% na labarin Jidda is based on true life events, musamman daga farkon sa zuwa tsakiyar sa, karshen sa ne kawai zai zama fiction yadda zai fi kayatar da ku. I gave this book my all, na rubuta shine from the very depth of my heart. Sometimes ina murmushi, while other times ina share hawaye, so get ready to do both.
Littafin Jidda na siyarwa ne kamar yadda na riga na fada tun kafin fara Tagwaye. Da farko nayi niyyar sai na gama gabaki daya zan fara posting, but I found out cewa ba zan iya ba, without your motivation I lost my courage, wannan ya tabbatar min idan babu readers babu Maman Maama dan haka zamu fara a haka.
Sai dai ba za’a ke samun posting kullum ba saboda alhamdulillah kullum responsibilities suna kara yi min yawa ne, I guess wannan shine girman ko? Lol. Za’a ke fashin kwana dai dai, misali in akayi Saturday ba za’a yi Sunday ba sai Monday. Yes, nasan wadansu ba zasu iya jira ba and I advise them to wait sai anyi nisa ko kuma ma su bari a gama sai su karbi document. Please in kinsan ba zaki iya jira ba kar ki biya, don’t pay and be pressuring me please. Fashin kwana dai dai so that you will have well arranged and well edited episodes insha Allah. I assure you that ba zakuyi dana sanin siyan Jidda ba, it is going to be one of your best dan for me Jidda already ya kere wa saura a zuciya ta.
Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din
Please banda kira, WhatsApp only
Again dai ina tunawa nasu siyan online novels cewa copyright (hakkin mallaka) na marubuciya ce, ita kadai take da right din copying da kuma sharing littafin ta, duk wanda yayi hakan bayan ita to ya shiga hakkin ta kuma duk munsan cewa Allah baya yafe hakkin wani har sai shi ya yafe da kansa.
Allah yasa mu gane ameen.
Akwai 18 free pages insha Allah
Asha karatu lfy
Episode One……..The Beginning and the End of Me
Free page
A duk lokacin dana duba rayuwata, kamar in inaso in bada labarina, na rasa dalilin da yasa bana iya farawa ta farko na, bana iya farawa ta lokacin da aka haife ni ko kuma ince lokacin da na bude idona na ganni a duniya. A kowanne lokaci in na duba bayana ina farawa ne da ranar dana fara ganinsa, a gurina wannan ranar, wannan hour din, wannan minute din da kuma wannan second din da idanuwan sa suka shiga cikin nawa a lokacin ne rayuwata ta fara. A lokacin ne kuma rayuwata ta kare.
Ranar visiting day ce a makarantar yammata ta garin Taura dake jahar Jigawa. Kasancewar yan ss3 ne kadai a makarantar suna zaman extension wanda ake yi lokacin zana jarabawar karshe ta secondary ya saka makarantar take shiru ba kamar sauran ranakun visiting ba.
Ni da babbar kawata a lokacin, Mufida, munyi duk abinda yake al’ada ta dalibai dan wannan ranar, munyi wanki da guga da kitso, sannan muka tashi da wuri mukayi wanka muka yi kwalliya dai dai irin wacce ake barin dalibai suyi sannan muka fita class area tare da sauran É—alibai dan jiran tsammani, duk da dai muna saka ran tabbas za’a zo mana visiting daga gidajen mu dan ba’a taba fashin zuwa mana ba sai dai in da kwakwkwaran dalili.
Can nesa muka samu benchi muka zauna, dan ba’a bari dalibi yaje gurin sai an kira shi sai su headgirl da kuma prefect on duty. Kasancewa ta health prefect kuma kasancewar ba duty na bane ranar yasa nayi zamana muna hira excitedly da Mufida. “Yaya Mukhtar yace min zaizo, yace tare da matarsa Aunty Halima ma zasu zo” Mufida tace “hmm. Ni bansan ma dawa dawa za’a zo min ba. Nasan dai Mama confirmed zata zo”
Kiran sunana da mukaji anayi ya saka mukayi saurin juyawa cike da mamaki. Na kalli agogon fatar da yake hannuna, few minutes after ten, nooo there must be a mistake dan nasan yan gidan mu ko wanka basu gama yi ba balle girki balle har su dauko hanya daga kano balle su zo. “Hauwa’u Habib” aka sake kirana. Na mike ina kallon Baba mai kiran alkhairi da yake tsaye da takarda a hannunsa “Baba? Hauwa’u Habib da gaske?”
Ya nuna min takardar, “karanta da kanki in kina ganin ban iya karatu ba” na girgiza kai na “akwai Hauwa Muhammad Habib, ko dai ita ce akayi mistake, ni ba yanzu zasu zo ba sai yamma suke zuwa” yayi gaba yana cewa “sai kije can ki gani ai, in bake din bace ba sai ki dawo ki kira waccan din” na gyada kai tare da binsa da sauri ina yiwa Mufida signal cewa ina zuwa, yana ta zabga sauri, ni kuma in akwai abinda ban iya ba to sauri ne, generally ma ni komai nawa a sanyaye nake yinsa tun daga magana har tafiya har komai. Da wahala kaji ni na daga murya.
A gaban staffroom, inda few iyayen yara suka fara zuwa kuma mostly maza ne suka fara zuwa na hango motar Abban mu, nan take jikina yayi sanyi, shikenan ta faru ta kare anyiwa mai dami daya sata, shikenan Abba shi kadai yazo. A lokacin na ganshi ya fito daga staffroom yana duba agogon sa sannan ya dago kai briefly ya kalle ni yace “kiyi sauri mana! Kina tafiya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki, sauri nake yi daurin aure ne dani a gumel shi yasa banzo da iyayenki ba”
Na durkusa a gabansa “Abba sannu da zuwa, ina kwana?” Bai amsa ba ya cigaba da magana “kiyi sauri ki dauki sakon ki in wuce, already ma na makara har goma ta wuce. Umman ki ce ta tsayar dani wai sai ta soya miki miya” ya karasa yana zagaya wa baya tare da bude booth, na bishi can na sake gaishe shi “Abba ina kwana?” Ya fito da kwalin indomie da bagko ya ajiye sannan yace “lafiya lau, ya karatun? Komai dai lafiya ko? Babu wata matsala ko?”
Na gyada kai na automatically hawaye yana zubowa. Ya tsaya yana kallona, “kuka kuma? Wato kin fi son uwarki akai na ko? Shine kike kuka dan ni nazo uwarki bata zo ba ko?” Nayi saurin girgiza kai ina share hawayena. Wasu kuma sababbi suna replacing dinsu. Yace “kinga, sauri nake yi yanzu shi yasa ban taho dasu ba, kuma suna can suna rigimar tasu da suka saba. Ki bari in na koma gida, in mun sami albashi, sai in hado su da wani a cikin yayyenki ya kawo su ki gansu”
Na sake share hawayen ina gyada kai, sannan nace “Abba ina Farhan?” Ya danyi murmushi yace “tana can tana kuka wai sai ta biyo ni, rigimammiyar yarinya kawai, duk halinku ai iri daya ne” sai kuma ya fara shafa aljihun sa “kinga na manta ma ta bani takarda in baki. Yar banza, ko me ta rubuta a ciki?”
Ya dauko wata farar takarda daga aljihunsa ya miko min na karba ina dan murmushi kadan sai kuma hawaye suka biyo murmushin, ina ta burin ganin ummana da yanuwana, shi Abba ma yana daga can karshe a list din wadanda nake son gani.
Ya sake mayar da hannun sa aljihu ya dauko 1000 ya miko min. “Kun kusa kammala wa ai, in kika lallaba kayan nan da kuma kudin nan zasu ishe ki. Sai ki dage da karatu dan naga kamar kinfi yanuwanki son karatun, gashi nan kaf yan uwanki mata babu wacce take morar karatun ta duk sun biye wa mazajensu sunyi zamansu suna zuba yaya. In kika dage kika ci ssce sai ki wuce kiyi nursing, ko Allah zai saka in mori kudina a kanki”
Na gyada kai “insha Allah Abba” wayarsa ta fara kara, ya bude mota “kinga har an fara kirana a waya. Na tafi, in sunzo to….in kuma basu zo ba sai kun gama jarabawa” na ja baya ina daga masa hannu, bai ma lura ba yana magana a wayarsa har sai da ya juya mota sannan ya daga min hannu briefly ya wuce.
Na sunkuya na dauki kwalin da hannu daya, na kuma dauki bagkon da daya hannun na fara tafiya a hankali zuwa hanyar hostel. Tun daga nesa Mufida ta hango ni, ta mike da sauri ta zo ta karbi kwalin hannuna “wai da gaske yan gidanku ne? Har sun tafi?” Maimakon in bata amsa sai sababbin hawaye suka biyo kuncina, ta ja bakinta tayi shiru muka cigaba da tafiya tare dan tasan in ta cigaba da jan maganar zan cigaba da kuka ne kuma daga nan in ba sa’a naci ba zan iya samun attack na asthma.
Sai da muka je har daki muka zauna a kwanar mu sannan nace mata “Abba ne yazo shi kadai” na bata labari in brief na abinda ya faru. Ta bani hakuri tana kokarin yi min hira dan in manta sannan ta fara fito da kayan da aka kawo min tana sakawa a lokar kayan abincin mu. Ta dauko food flask guda biyu, daga maikon jikin dayan munsan miya ce a ciki, ta bude dayan sai ga taliya.
Na danyi murmushi, Allah sarki Umma, na tabbatar shinkafa tayi niyyar dafa min dan tasan nafi son ta amma azalzalar Abba ya saka ta dafa taliya, nasan bai ma gaya mata cewa ba zai zo dasu ba sai da safe zata ga ya fito yace ta kawo sako zai taho. Na dauko takardar da Farhan ta rubuto min na bude na fara karantawa
Dear Sister
Abba yace ba zai zo damu ba, zanyi miki dan malele ma bai barni nayi ba yace ba zai jira ba. Kiyi hakuri insha Allah zan roki yaya Mukhtar ya kawo mu ni da Aunty Halima da Mammy da Amira. Akwai labari sosai, in gaya miki nayi sabon kamu a cikin invigilators din mu. Sai nazo zan baki labarin sa.
Kar kiyi kuka.
Farhan
Murmushi nake yi ina karatawa amma ina zuwa gurin kar kiyi kuka sai na fara kukan, na rufe fuskata da takardar ina kuka ina missing yaruwata. Na rasa dalilin da yasa ita take day school ni kuma nake boarding duk da cewa set din mu daya da komai.
Mufida ta zuba abinci muka ci sannan ta zuba wa duk yan dakin aka kai musu, muka yi alwala mukayi sallah sannan muka sake gyara fuskar mu muka koma class area dan yanzu ne aka fara zuwa sosai. Bamu dade da komawa ba kuwa ai gashi anzo kiran Mufida “Zainab Muhammad Gidado” ta mike da sauri tana murna, “dama wallahi motar can data shigo sai da jikina ya bani sune, irin motar Yaya Doctor” na dan yi murmushin takaici, wato yau sai dai inga kowa da yanuwansa banda ni. Ta ja hannuna “taho muje mana” na makale “kin san Malam Yakubu yana can, kar ya dizga ni a gaban mutane yace naje kwadayin jar miya” tayi dariya “dalla can, ke tsoro ne da ke, akwai mutane da yawa a gurin ba zai gane cewa ba’a kira ki ba”
Na dan sake yin jim, ni mutum ce mai bin doka da ka’ida tun ina yarinya, ina da rules akan kaina kuma ina da su akan wasu, sannan ina iyakacin kokari na na ganin ban yi stepping boundary ba ko wanne iri ne, uwa uba, ina matukar gudun wulakanci. Na kuma girgiza kaina. Ta jani da karfi “me zakiyi to in kin zauna din, sai dai kiyi ta kallon mutane suna shiga da fita? Ko kuma so kike ki koma daki kiyi ta kuka?”
Tana maganar tana ja na ina tirjewa kamar uwa da rigimammiyar yarta, na san she meant no harm, tana so ta rage min jimamin rashin zuwan yan gidan mu. A haka muka je gurin da ta hango motar gidan su, muna zuwa gurin ta sake ni ta tafi gurin mahaifiyarta da gudu ta rungume ta “mamana oyoyo” sai kuma ta gaishe da amaryar babansu “sannu da zuwa Aunty” sannan ta juya kan sisters dinta biyu da aka zo dasu, Muhibbat da Muhsina, suka rungume juna, sai naji ina kewar nawa yanuwan, da yanzu muna nan muna hira abin mu, da yanzu Farhan ta bani labaran da ta ce zata bani na sabon saurayin da tayi.
Na danyi kokarin gaishe da maman su Mufida amma duk hankalin su yana kan yarsu, sai naja baya na tsaya ina kallon su feeling awkward, feeling like a trespasser. Har na fara tunanin juyawa in koma sai Mufida ta gabatar dani “Mama ga Jidda fa, Jiddan da nake gaya muku” Mama ta juyo tayi assessing dina tun daga sama zuwa kasa, sannan kuma sai naga tayi murmushi da alama zuciyarta ta yarda da abinda idonta ya gani “a’a Jidda yan makaranta, ya karatu?” Na durkusa nayi gaisuwa ta biyu duk suka amsa min da sakakkiyar fuska, sannan muka shinfida tabarmar da suka zo da ita muka zauna suna ta hira ina dan saka baki kadan a inda naga sun sako dani. A dan lokacin na lura da wani abu, Maman su Mufida tana matukar son Æ´aÆ´an ta kuma bata boyewa, kuma na lura auntyn su tana da kirki.
Ni dai ina zaune daga dan gefe kadan ina ta wasa da zaren tabarma da hannuna, ba wai rashin sabo da su ne ya saka na kasa sakewa ba. A’a, wani irin abu nake ji tun da nazo gurin, wani irin feeling na kamar ana kallona, wani irin kallo mai kaifin da nake jin kamar yana ratsa kayan jikina ya huda skin dina da tsoka ta da kashi na ya zarce har cikin zuciyata. Wannan yasa nayi ta gyara zama ina kuma gyara hijab dina amma na kasa jin dai dai, kuma na rasa a ina idanuwan da suke kallona suke.
Na kasa sakewa, nayi ta waige waige amma na kasa gane waye yake kallona. Maman su Mufida ce ta gane discomfort dina “Jidda kin ki sakin jikinki kina ta kalle kalle. Ko neman yan gidan ku kike yi?” Sai Mufida ta basu labarin zuwan Abba na, suka yi ta min dariya ni kuma naji kamar zanyi kuka. Aunty tace “kiyi hakuri kinji? Haka suke mazan nan, nima sanda ina makaranta bana son namiji yazo min visiting, boring” na gyada kai, at least ita ta fahimce ni.
Na mike “zan koma ciki Mufida, sai kin taho” ta mike itama “bara in raka ki hanya to” Aunty tace “to kunga, ku tafi da kaya suna mota, shikenan kun huta” ambaton mota ya saka muka juya muka kalli motar a tare. And then I saw him and I saw the eyes.
Yana zaune a cikin mota a seat din driver yayi adjusting mirror dai dai inda nake, daga ganin karkacewar mirror din kasan karkata shi akayi da niyya. Ina juyawa kuwa idona ya fada cikin nasa, bana ganinsa sosai, bana ganin jikinsa tunda ya juya bayansa, ba kuma na ganin fuskarsa gabaki daya tunda girman mirror din yayi wa fuskar kadan, sai dai idonsa kawai na gani wadanda suka sauka a cikin nawa. And I lost myself a cikin su.
That second, that very second da idanuna suka shiga cikin nasa, wannan shine karshen rayuwata, karshen rayuwata a matsayin Jidda amma kuma farkon rayuwata a matsayin tasa. Last bugun da zuciyata tayi kafin in waiga shine last bugawar da tayi for me, the next bugun da tayi is for him, kuma daga lokacin ta cigaba da bugawa for him. Daga wannan last bugun ta tashi daga tawa ta koma tasa, ta daina bin duk wani umarni na sai dai umarnin sa, ta damka mishi mulkinta tun ma kafin ya nemi takara ballantana har ayi zabe. What a selfish heart!
Nayi kokarin cire idanuna daga cikin nasa amma na kasa, naji kamar Mufida tayi magana amma kwakwalwa ta bata iya assessing abinda tace ba balle ta bada ma’ana, sai dai naga motsinta ta tafi inda motar take da sauri. Bakinta yana motsi kamar tana yi masa magana. And he took his eyes away from me for a second, second din da naji kamar hour guda ne, ya danyi mata magana sannan ya kuma dawo min da idanuwansa kaina, tamkar dan da ya dawo gidansu.
“Jidda” naji muryar Mufida ta ratsa tunani na naji kuma hannunta yana girgiza kafada ta, tunanin me kike yi ne haka. Na dan kifta idanuna ina so su taimake ni suyi cooperating su rabu da kallon idonsa su dawo gare ni. Na kalle ta atlast, tace “ki zo ki gaishe da yaya Faruq”
“Faruq” baki na ya motsa ya ambata a hankali, kamar yana aikawa zuciyata sakon sunan sabon mamallakin ta, commander in charge dinta, wanda yayi min juyin mulki a garin da ni kadai nake ciki nake rayuwata sai shi yau daya shigo ya cika ko’ina ya barni a rakube a gefe, with just his eyes.
Ta kama hannuna muka karasa gurin motar tare “yaya Doctor ga kawata Jidda”
“Jidda” naji ya fada a hankali. Na lunshe idona na bude feeling very proud of my name. Ashe haka sunana yake da dadi? Ko dai maganar sa ce mai dadi? Ko muryarsa ce tayi min dadi. Ko ma dai menene yana da alaka dashi, dan ban taba jin irin wannan akan sunana ba sai da ya fito daga bakinsa.
Ya bude kofar motar, sannan ya zuro kafarsa daya waje ya kuma juyo fuskarsa sosai yana facing dina, and he smiled. His lips curving and his eyes softening. Na sake kokarin dauke idona daga fuskarsa amma na kasa, musamman yanzu da na samu access da dukkan fuskarsa not just the eyes.
Farar fatar sa tayi kama da wadda ake cewa “wanke hannu ka taba” irin wadda zaka yi tunanin in ka dangwala hannunka zaka tabo jini. Ko kuma ido na ne ya nuna min hakan? Ko kuma bakar sumar kansa da baki kuma cikakken sajen fuskarsa ne ya kara haskaka fatar ta sa? Cikakken fuskarsa tayi matukar dacewa da kyakykyawan dogon hancinsa. Sai dai duk wadannan a baya suke, babban abinda yafi birgeni a fuskarsa shine idonsa, wanda zan iya spending hours looking at.
Ya fito gabaki daya sannan ya mike tsaye, tsahon sa ya saka sai na daga kai na kafin in cigaba da kallon fuskar tashi, but that will look awkward right? Dole na hakura da kallon na sunkuyar da kaina ina kallon kafafuwana da suke cikin safa a kuma cikin sandals, ba wai dan kafafuwan suna birgeni ba sai dan bani da wani zabi.
“Jidda” ya sake fada, zuciyata ta motsa a cikin kirjina. Mufida ta taba ni “ki gaida yaya Doctor yana yi miki magana” “ina ruwanki” ya fada. “In bata gaishe ni ba ina ruwan ki. Chakwaikwaiwa!” Tayi dariya “kai Yaya, kawai dai ranta a bace yake tun safe, abbanta ne yazo ba ummanta ba shine take ta fushi” ya gyara tsayuwar sa yace “haka ne? I see. Wato ba kwa son maza suyi visiting dinku kunfi son mata ko? Shi yasa ni ma tunda nazo baki ko kalle ni ba sai kika barni da leke ta window ko? Yayi kyau”
Ta kama hannunsa, nabi hannun da kallo ina lura da zobban azurfa guda biyu dasuke jere a middle finger dinsa da manuni, “ha! Yaya, wallahi ban san kana cikin mota ba” ya karbe hannunsa “inafa zaki sani? Kina can kina daddanne min uwa. Kina can kina introducing friend dinki to all but me”
Ta dawo kusa dani ta dafa ni “Jidda kenan. My very best friend” ta nuna shi “Jidda ga yaya Faruq, my favorite brother. One in million” ya sake yin murmushi mai sauti. “Dadin baki ko? To ko kwandala ba zan baki ba” na dan russuna, still kaina yana kasa “ina wuni?” Yayi shiru amma ina jin idonsa a kaina, “bana amsa gaisuwa sai an kalle ni” Mufida tayi dariya “ba ka san Jidda ba, zaka bushe a gurin kafin ta daga kai ta kalle ka” yace “baki san ni bane ba, bayan kallo i bet she is going to smile back at me kafin ta bar gurin nan” ta daga kafada “okay, amma ni nasan kawata ba zata bani kunya ba”
Read Also: Tsutsar Nama Complete
Sai ta zagaya bayan motar ta dauka jakar ghana must go da kuma bagko guda dai dai, da kyar ta fito dasu daga booth din sannan tace “Jidda zo mu dauka mu tafi” yayi saurin cewa “what? Wannan uban kayan zata dauka?” Tace “zamu dauka, da ni da ita” ta fada tana nuna kanta sannan ta nuna ni, na tafi inda take still kaina a kasa na fara kokarin kama jakar sai yazo ya janye hannun jakar daga hannuna. “ba zata dauka ba” ya fada yana kallon Mufida” ta tabe taki ta fara yi masa shagwaba. “Ni baka damu dani ba Yaya Doctor, ni zan dauka ni kadai kenan”
Ya danyi dariya yace “haba sweety kema kinsan kece favorite sister dina duk duniya amma ki duba yanayin jikinki da nata ba daya bane, in ta dauki wannan kayan kafin taje hostel din ku ai ta karya kafa ko hannu” sai naji haushin yadda yayi min kallon karama, duk da nasan Mufida ta fini ki ba amma ni ma ai ba karamar da har za’a yi kwatance dani ba ce ba nace “zan iya fa, dazu ma mun dauki wasu kayan, kullum ai muna daukan kaya” Mufida tace “da daukan ruwa, bucket din penti muke dauka kullum” nace “dazu ma shi muka dauka. Am stronger than I look”
Yayi murmushi “show me” na bude ido “what?” Yace “Æ™arfin” na cigaba da kallon sa cikin rashin fahimta sai ya daga hannunsa ya nuna min kwanjin sa, ai kuwa na gani duk da ta cikin riga ne, nayi saurin dauke kaina ina jin tsigar jikina tana tashi, yayi dariya. “Ga nawa, show me yours” Mufida tace “wow, Yaya Doctor tsara kaga nawa nima” ta tattare hijab din ta tayi yadda yayi da hannun sa tare da daddagewa lallai wai sai kwanji ya fito, yayi dariya yana dan dukan hannunta kadan “ji wani kwanji kamar na kadangare” ta turo baki yace “ai kina dashi ma, kawarki ita irin na sauro ne da ita” na bata rai “sauro? Sauro ai bashi dashi” yace “that’s exactly what am saying, baki dashi” nace da sauri “ina da shi mana” ya gyara hannunsa tare da jingina da jikin mota yace “then show me”
Muryar Mama muka ji “wai baku tafi kai kayan ba har yanzu?” Mufida ta daga murya, “Mama Yaya Doctor ne ya hana mu dauka” ya bude ido “Mama sharri take yi min” ta murguda masa baki shi kuma yayi mata alamar zai zaneta da hannunsa. Muka kuma yin kokarin dauka sai ya janye jakar yana kallona yace “am serious fa, in dai ina gurin nan ba zaki dauki kayan nan ba. Baku da laborers haka da zasu shigar muku dasu?” Mufida tace “akwai su amma sai an basu kudi” ya zaro kudi a aljihunsa idonsa a kaina ba tare daya kirga ba ya mika mata, tayi saurin karba tana dan tsallen murna sannan ta fara waige waigen neman mai daukan kaya.
Ya rankwafo da kansa yana kallon cikin fuska ta, muka hada ido nayi saurin kallon gefe, sai ya zagaya da fuskar sa ta gefen da nake kallo, muka sake hada ido sai na rufe idona, ya danyi murmushi mai sauti yace, muryarsa can kasa yadda na tabbatar ko da hankalin mufida yana kan mu ba zata ji abinda yace ba “smile, please”. na sake rintse idona ina jin muryar sa a jikina tana zuwa har inda banyi tunanin murya tana iya zuwa ba, ina jin yakin da ake yi a tsakanin Æ™waÆ™walwa ta da kuma zuciyata, zuciyata which already belongs to him tana son yin obeying din umarninsa, yayinda Æ™waÆ™walwa ta take kokarin cigaba da maintening dignity dina. “Smile, ko da dan kadan ne, ko da iyakacin lips dinki ne, ko da bai gama zagaya kyakykyawar fuskar ki ba”
Na sake juya fuskata gefe, zuciyata tana so ta cigaba da zama a wajen tana sauraron muryar sa yayin da Æ™waÆ™walwa ta take gayamin “run!” Yace “bude idonki ki kalle ni, ko ba zakiyi murmushi ba ki kalle ni kawai kafin ki tafi, dan Allah” na juya masa bayana sannan na bude ido na naga Mufida tana bawa masu shigar da kaya sako, sannan na kuma jin alamar ana kallona daga side din da yan gidan su suke, na kalli gurin and I saw Mama, idonta a kaina da kuma wani irin yanayi a fuskarta. Daga bayana naji yace “in baki kalle ni kinyi min murmushi ba, zan iya kwana a asibiti a yau”
Ba tare da na sake magana ko na waiwaya na kalle shi ba na bi bayan mai daukar kaya, duk da cewa zuciyata tana kokawa, tana so ta sake kallon cikin idanunsa, Mufida ta biyo bayana da bakaken ledoji biyu a hannunta, ta miko min daya “ai dai wannan ba zaki karye ba in kika dauka ko?” Duk mukayi dariya a tare, duk da ni tawa dariyar bata kai ciki ba, all I wanted a lokacin is to look into his eyes again. Ina jinta tana min hira, bansan ma me take cewa ba har muka danyi nisa kadan sannan kuma ina jin idanuwan sa still a kaina, I can even swear cewa magana yake yi da zuciyarsa, addu’a yake yi in sake waigawa. And I did.
Na dan dakata da takuna, ina jin kamar ba zan iya kara taku daya ba har sai na kalle shi, sannan na juya na kalli inda.