Karfe A wuta Complete Book
Continuation.
Cikin hanzari ya kalli Nabila, yana mamakin a ina ta san wannan sunan, dan sam bai san Walid ya gaya mata labarin sa ba.
Ya ƙureta da ido, ta kawar da kanta gefe, ta ce “Eh, idan ka kashe ni, ka ci amanarta, ta barka ka kusa dawowa hanya, amma ka koma ruwa fiye da baya. Zan so na ji ƙarshen labarinta, amma kafin nan bari na tafi yanzu, ga kayan dubiya nan na kawo maka, Allah ya ƙara sauƙi” sai da ta gama maganar sannan ta ɗago ta kalleshi, still ita yake kallo.
Ta sake cewa “Ina fatan zaka yafe mini laifin da nayi, rashin sani ne” ta tashi a hankali ta ɗauki jakarta ta fita, tana yi wa Allah godiya da wannan karon, ba ta sha shaƙa ba, hakan ya sa ta ƙara kin ƙwarin gwiwar cigaba da gwagwarmayar da ƙuduri aniya.
Bayan fitar Nabila, Viper ya ɗaga kai yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya, Walid ya ce “Ko ba ka yi magana ba, na san menene a ranka, ba kowa bane ba, ni ne nan na gaya mata labarinka”.
Ya tsayar da idonsa a kan Walid ya ce “Saboda me?”
“Saboda dalili mai ƙarfi, cigaba da cusa kanta a lamuranka cikin duhun kai, tamkar ƙara yawan matsalolinka ne, zuciyar mace ta na da rauni, fiye da dukkaninmu, ina ganin hakan zai iya yi mana am….. Bai ƙarasa ba, viper ya katse shi ya ce “Ta yaya? Na ce ta yaya? Meye amfanin gaya matan, na gaya maka bana buƙatar cigaba da ganin yarinyar nan, sai an haɗa baki da ita an ƙara rusa ni kenan? Da raunin na su ake amfani a sarafasu a cuci mutum, halittu ne su marasa imani….
“Raunin ‘ya mace, da tausayinta irin na halitta, kar ka manta shi ya jefa ka a cikin halin da ka ke ciki, idan mace ɗaya zuwa goma sun cutar da kai, ɗaya zuwa biyu sun yi maka abun da ba zaka taɓa iya biyansu ba, wanda tausayi da soyayyar da mace ta nuna maka, giɓin da ta bar maka ne, ya ƙara assasa tunzura zuciyarka ka ke fama da jinyar da muka rasa bakin zaren yi maka maganinta. Idan zaka yi adalci, ka yi musu hukunci da halin ƙanwata, Jauhar ko ba dukkansu ba. Yarinyar nan gaskiya ta gaya maka, idan ka yi kisan kai ka ci amanarta, wannan miyagun ƙwayoyin da ka ke ƙara ɗurawa kanka, su ma ba ka yi mata adalci ba”.
Al’amin da ya ji maganganun Walid sun ishe shi, sai ya miƙe tsam ya sake ficewa.
Walid ya yi wa Ɗan mama inkiya ya bi bayan sa ya ga ina zai yi.
*
Ramma ce take dukan gefen fion da Abdul yake “Abdulyasar Abdul yasar” ya buɗe idonsa da kyar ya kalleta.
“Ka tashi ka yi sallar asuba, gari yayi haske, sallar ma baka yi” ya ja tsaki ya sake juyawa.
Ta sake cewa “Ka tashi gari fa yayi haske”
“Kin san jiya da daddare fa ban yi bacci ba, ki ƙyaleni”
Ramma ta ce “Haka ne kam, dama ba ka da lafiya, wataƙila a cikin baccin za a zare maka rai, ban sani ba ko kana da abun da zaka gaya wa Allah a kan rashin salla” kan ta rufe baki ya tashi zaune yana ƙifta ido.
Ta girgiza kai ta ce “Kai yanzu baka shirya wa mutuwa ba, ka ke rashin mutunci? Allah sarki ɗan Adam abun tausayi” ji yayi jikinsa yayi mugun sanyi, kamar mutuwar ce ke tunkaro shi, ya je ya yi alwala, ya fito ya tarar tana gyara gadon da ya tashi.
Wayarsa ce ta fara ringing, ya tashi da sauri, ya ɗauka, ya saka a kunnensa “Hello mummy”
“Kana ina ne?”
Ya ce “Ina gidana”
“To zuwa anjima ka zo gida, zaka yi magana da babanka, shugaban jam’iyya ya ce ka je ka ga ‘yar sa, ku daidaita kanku, ayi magana dan ba za su yadda a baka takara ba, baka da aure”.
“Haba mummy, aure kuma? Ni wai dole ne auren nan, a haƙura mana”
“Ban gane a haƙura ba, waye zai yadda ka yi deputy governor ba ka da aure, lallai ka zo anjima ku yi magana dama yana cewa ni nake hure maka kunne”
Abdul ya ce “Ba ni da lafiya fa”
“Ka sha magani ka zo, ulcer ce?”
Ya ce “Eh, kuma wallahi ina jin jiki, dan Allah ki bashi haƙuri zan zo ne”
Cikin damuwa ta ce “Ko na turo a ɗaukko mini kai, ba na son ciwon cikin nan naka fa”
Ya kashingiɗa ya ce “A’a, zan warware, idan na ji sauƙi zan zo, sai anjima zan ɗan kwanta” ya ajiye wayar. Tun da ya fara wayar, ramma ta ƙura masa ido har ya gama.
Ta ce “Ka ga banbancin rayuwar mace da ta namiji ko? Kaga duk abun nan da ka ke yi, kai an samo maka mata ni mecece makomata?”
Read Also Amaryar Zayyad na Rahama Kabir
Ya kalleta ya ce “Kishi ki ke yi ne?”
“Allah ya rufa mini asiri, na rasa a kan wa zan yi kishi sai kai, ka wulaƙanta mini rayuwa ka cuce ni, kai ka yi aure ka tara iyali, ni kuma babu wanda zai kalleni, ka yi mini fyaɗe ka mayar da ni ƙaramar karuwa, har ciki na ɗauka duk ta ƙazamar hanya ka wulaƙanta rayuwata”
Abdul ya zauna sosai ya ce “Ke ki ka fara wulaƙanta rayuwarki, da ku ka yi yinƙurin cewa zaku nemi hakkinku a kotu, alhalin ba zaku iya ja da ni ba”
“Sannu tsohon azzalumi, dama mai kuɗi shikaɗai Allah ya ce ya ji daɗi a duniya? Yanzu duk wannan abun taƙamarka kana da kuɗi ni ‘yar talakawa ce? In sha Allah sai Allah ya ƙasƙantaka da kai da masu goya maka baya, suka tsaya maka kake rashin mutunci. Na san akwai ire-irena da yawa yaran talakawa da kuka zalunta, Allah ya na kallonku. In sha Allah sai Allah ya nuna maka iyakarka tun a duniya Abdul yasar”
Duk da ya ji zafin maganganunta amma sai cewa yayi “Ko wanda ya raɗa mini sunan nan, bai kai ki iya faɗar sunan ba Rahama, Abdul yassar”
Kallonsa tayi tana kuka, haushin kanta yakamata da lokacin da yake waya, ba ta yi ihu a wayar ta ce a taimaka mata ba sace ta yayi. Yanzu ko wayarsa ta ɗauka ba zata iya operating ɗin ta ba, kuma ba ta da lambar wanda ta haddace balle ta kira.
*
Abba yana zaune yana kallon labarai a Aljazeera, Nabila ta shiga da sallama, yana kashingiɗe, ya tashi zaune yana murmushi ya ce “Barrister, kin yi mini wuyar gani da yawa fa, kullum na dawo kina aiki, baki dawo ba aiki ya hana mini arfana sukuni”
Tayi murmushi ta ce “Abba ni kaina ina kewarka, bana samun zama, yanzu na shiryu ai, ina aiki sosai da sosai, na san addu’a ka ke yi mini”
Ya ce “Kullum Addu’ata a kanku take, mussaman ke arfana, Allah ya yi miki jagora a dukkan lamuranki”.
“Eh mu ma Allah ba zai tagayyara namu ba” Umma tayi maganar tana harar Nabila.
Nabila ko a jikinta ta ce “Abba dan Allah abu na zo roƙonka”
Ya ce “Ina jinki ƴar albarka”
“Abba dan Allah mota nake so, wallahi wahala nake sha samun napep, ayi ta haɗani da maza, ga zirga-zirga na yi ta kashe kuɗin mota, kuma haryanzu ni ba na yi wa client ɗina charges mai yawa”
Yayi dariya ya ce “Nawa ki ka tara?”
Tayi shiru sannan ta ce “Ina da 400k”
Ya kwashe da dariya ya ce “400k, sai dai a gyara miki tsohuwar honda ta”
Cikin shagwaɓa ta ce “Haba Abba, big girl kamar ni, da tsohuwar mota, ka taimaka Please”
“Babu komai, za a sai mota in sha Allah, amma da sharaɗi ba na son yawon babu gaira babu dalili, kuma ke zaki din ga zuba manki, ba zan sai mota na din ga cacar mai ba”
Cikin takaici Umma ta ce “Major mu fa? Muna zaune zaka saya wa Arfa mota, wannan wane irin rashin adalci ne?”
Ya kalleta ya ce “Da walida zan saya wa mota, ba zaki faɗi haka ba, ku fa da me? Ga mota nan ana kai ku unguwa a ciki, meye na kishi da ‘yar cikinku? Ku daina haɗa kanku da ita, kun san abun da nake nufi”.
Arfa ta tashi ta ce “Abba sai da safe” ta juya zata fita, ta yi wa Umma gwalo, a ranta ta ce “Saura ma babar su DSP idan ta ji, sai dai ku mutu”.
Ta koma bedroom ɗin ta tana murna, ta ɗauki wayarta, Viper ya faɗo mata a rai.
Lambarsa da ta saka a wayarta, ta lalubo, ta zubawa ido, murmushi ta yi, ta kira lambar ta saka a kunnenta.
Yana zaune a kan katifa, yana ta shan sigari, zubawa lambar ido yayi, ya gaji ya ajiye wayar, ya cigaba da abun da yake gabansa. Ba ta gaji ba ta din ga kiransa babu ƙaƙƙautawa, har sai da ya hasala, ya ɗaga wayar, amma bai yi magana ba.
“Har na kusa fushi sannan ka ɗaga, na san da ‘yar madara ce, ko ba ta san mai lambar ba, zata ɗaga kuma za ta saurareni, haka zalika zata yafe mini laifin da na yi mata. Akwai abubuwan koyi sosai da sosai a rayuwar ta, da ya ci ace ko ba duka ba, ka yi koyi da wasu, ba ta wulaƙanta ɗan Adam da tana yi, da ba ta riƙe ka da amana da tausayawa ba. Ina sake roƙonka yafiya, da kuma fatan samun haɗin kanka, ka ƙarasa mini labarinka da kanka, ina sha’awar kasancewa wani ɓangare na labarin nan, mai ban tausayi da ratsa zuciya Viper, sai da safe” tun da ta fara maganar, ya sunkuyar da kai, ya saki sigarin da take hannunsa, ya sunkuyar da kai hannunsa yana rawa. Ta gama maganar ta katse wayar, amma ya kasa ajiye wayar.
Sai da liti ya dafa shi ya ce “Maza yane?” Ya ɗago idanunsa ya kalli liti.
“Kamar Muryar wannan shegiyar yarinyar na jiyo a wayar, duk Walid ne da wannan sheɗancin”
Ya cigaba da ƙurawa Liti ido, babu abun da yake fata, banda ya zubar da hawaye ko na mintuna biyar ne, amma ko na sakan ɗaya ya kasa tsawon shekarun nan.
Murya a sanyaye ya ce “Liti”
“Na’am mai zamani”.
“Ina kewar jauhar sosai”
Walid da da yayi musu shiru, dan ya lura daga Viper har liti haushin sa suke ji, amma maganar da Viper yayi yanzu ta sanya jikinsa ya yi sanyi, tausayin Viper ya ƙara kama shi.
“Da yanzu yarona ya isa shiga makaranta, wataƙila ma ta kuma haifa mini wasu”
Walid ya taso, ya dawo gaban Al’amin, ya riƙe hannunsa ya ce “Ka ƙara haƙuri mai zamani”.
“Zuwa yaushe? Ko na ɗauki fansa kamar yadda nake buri da fata, kashe kaina zan yi saboda ba ni da wata makoma, idan kuwa hakan ba zai samu ba, zan koma in da na fito na ƙarasa rayuwata”.
“Dan Allah maza ka daina irin wannan maganganun, kana karya mana zuciya wallahi ” liti yayi maganar cikin damuwa.
Viper ya girgiza kai ya ce “Ba zaka gane ba”
Kawai ya gyara ya kwanta, gaba ɗaya suka kewaye shi suna kallonsa.
Nabila kuwa kallon wayar ta cigaba da yi, ta ce “Allah ya bani nasara a kanka, ya bani ikon taimaka maka”.
Kira ne ya shigo wayarta, ta ɗaga ta saka a kunnenta, ta yi sallama.
“Wa’alaikum Salam da ‘yar ƙwalisa”.
“Wa ke magana?”
Yayi murmushi ya ce “Bawan Allah ne”
“To, ai kowa ma bawan Allah ne, wanne daga ciki?”
Yayi gyaran murya ya ce “Wani case ne da ni, nake so a taimaka mini”
Nabila ta yi hamma ta ce “Office zaka zo, ba ta waya ba” ta katse kiran, dan a zatonta irin samarin nan, ne masu kiran wayar mata anyhow, duk da Muryar wannan ba ta yaro ba ce.
Wani nannauyan bacci, yayi awon gaba da ita wanda babu abun da take yi ban da mafarkin Viper, dan sai da ta kusa makara yau.
Kwanaki uku da zuwanta wurin su Viper, ba ta sake zuwa ba, she’s very busy, tana ta off and down na tattara hujjoji, duk da ana ta taɗiyeta, duk in da za ta bi ta samo shaida, sai a rufe, sai da aka aike da dattijon nan gidan kaso.
Gashi sai tayi ta sintiri a hanata ganinsa.
Kamar uba da ɗa haka Walid yake ta lallaɓa Viper ya ci abinci, sai dai ya cakala ya bari, ba ya cin abinci.
Private numbrn nan da ake kiransa da ita ce, ta kira shi, wayar tana ta ringing liti ya ce “Maza ka ɗaga mana”
“Me zan ce?”
Walid ya ce “Ko ba ka da abun cewa, ka ɗaga kawai”
Ganin ba shi da niyyar ɗagawar, ya sanya Walid ya ɗaga ya sakata a hansfree.
“Aminu Viper, kwana biyu. Ashe ta dawo maka da wayar. Alamu sun nuna kwana biyu ka yi sanyi, Kodayake kai sai an sakankance ka ke ɓarna. Gargaɗi nake sake yi maka, ka nesanta yarinyar nan da ga gareka, za a iya cutar da kai ta hanyarta”.
“Ni nake da ikon yanke hukuncin abun da yake daidai da rayuwata, babu wanda ya isa ya juya mini rayuwa yadda nake so, ka cigaba da ɓuya ko ka bayyana kanka, zan yi abun da nake ganin shi ne dai-dai da rayuwata.
Mutumin yayi murmushi ya ce “Aminu Viper, shikenan idan ka ƙi ji, ba zaka ƙi gani ba ai”
“Babu abun da ban gani ba, dan haka na shirya ganin koma menene” ya katse wayar.
Liti ya ce “Duk walid ne ya janyo komai, ni na san a rina, wannan yarinyar idonta kawai zaka kalla ka gane munafuka ce”
Kallon da Viper yayi masa ne, ya sanya shi yin shiru, Walid yayi dariya ya ce “Ayi dai mu gani, za a gane waye mai gaskiya tsakanina da ku”.
Liti ya ce “Ba wata gaskiya da ka ke da ita, ka dakatar da mu daga making moves, wallahi mun kusa fita operation kwanan nan”
“Ku fita yaƙi ma ba operation ba”
Haka liti da Walid suka kusa yin faɗa.
Tun ana gobe Nabila zata je wurin Naja’atu Bunkure, suke waya da sumayya, take bata ƙwarin gwiwa, a kan za ta iya, kar ta ji tsoro.
Da safe sai da ta fara zuwa wurin aikinsu, ta samu barrister Habib, shi ma ya ƙara mata ƙwarin gwiwa, da yi mata fatan alkhairi.
Cikin ƙasaita take fiya a farfajiyar office ɗin, har ta ƙarasa, mutane ta tarar jingim. Wanda galibin su mata ne, suna jiran shiga wurin Barrister Naja’atu Bunkure.
Kai tsaye Nabila ta shiga wurin sakatariyarta, ta nuna mata ID card ɗin ta, nan da nan ta bawa Nabila wurin zama, na ciki na fitowa ta yi mata iso zuwa wurin Barrister Naja’atu.
Tun a hanya take maimaita “la hula wala ƙuwwata illa billa”. Har ta shiga wurin Bunkure.
Tayi sallama, ba tare da ta ɗago ta kalli Nabila ba ta amsa mata, ta ƙarasa ta zauna ba tare da an yi mata umarnin hakan ba.
Kayan jikin Nabila kawai ta kalla, ta fuskanci ba kalar gajiyayyun da suke zuwa wurinta bane ba.
Ta gyara zaman gilashin fuskarta ta na kallon Nabila.
“Sannu da aiki ma” Nabila tayi maganar tana murmushi.
“Yauwwa sannu”
Nabila ta ɗaga mata id card ɗin ta ta ce “I am barrister Nabila Yusuf maitama”
Bunkure ta jinjina kai ta ce “You look familiar to me”
Nabila ta jinjina kai ta ce “Na yi mamaki ma, da ki ka iya tuna kamar kin sanni, saboda na san jama’ar ne da yawa. Ni abun da ki ka yi mini ba zan taɓa mantawa ba har abada”
Bunkure ta ce “Ohh really”
“Yeah and i have a promise to fulfil, a dalilin abun da ki ka yi mini”
Ta kashingiɗa da jikin kujerarta ta ce “That’s very good, ina son mutane masu yarda da kansu, ba na buƙatar sanin me nayi miki, ko kuma wani alwashi ki ka yi ba, ga ki ga bunkure Allah ya ida nufi “
Nabila ta ce “Na ji daɗi da ki ka ce Allah, dan kuwa shi ne gaba da komai, na gode sosai barrister”
“Mentioned not”
Nabila ta gyara zamanta ta ce “Yauwwa, ba komai ne ya kawo ni ba, na zo ne a kan wani case, duk da ba mu haɗu a court ba, an kai wanda nake depending prison, amma ban ganki a court ba sai wakilanki”
Bunkure ta ƙarewa Nabila kallo, sannan ta ce “Wane case ki ke magana a kai?”
“Yarinya da aka yi wa fyaɗe, ki ka ce kin tsaya mata, ni ce lawyer wanda ake ƙara, na je wurin ‘yan sanda ana ta yi mini yawo da hankali, ina son doctors report, kuma ina son zan ga yarinyar zan yi magana da ita”.
Naja ta yi wa Nabila kallon baki da hankali sannan ta ce “Kin san a gaban wa ki ke?”
“I am barrister Nabila, ba ruwana da a gaban wa nake, ina neman hujja ne da zan kare client ɗina”
“Nawa suka baki, ki ka samu ƙwarin gwiwar yin wannan kasadar? Zan ninka miki, ki ajiye case ɗin, kafin ki kunyata a idon duniya “
“Watch your words, it can be use against you a kotu, kin san me nake nufi, you are also a lawyer”
“Who the hell are you?” Bunkure ta yi maganar tana tashi tsaye, Nabila ma ta tashi tana sake ɗaga mata id card ɗin ta “Sai da na fara gabatar miki da kaina, sannan na gaya miki meya kawo ni.
Ko dai ki bani abun da nake buƙata kawai, ko kuma na fasawa duniya wacece ke?”
“Ni ɗin? Yaushe ki ka yi grduating, da me ki ke taƙama ki ke jin karanki ya kai tsaikon da zaki tunkare ni kina gaya mini maganar da ki ka ga dama?”
Nabila ta girgiza kai ta ce “Cikin dukkanin girmamawa ta seniority a aiki, nake faɗar duk abin da nake magana a kai. You were my mentor before, abun da ki ka yi mini ya tabattar mini you are green snake under green grass. Keep your eyes open, Barrister bunkure, zan iya baki mamaki a lokacin da baki zata ba. Zan cigaba da bibiyar case ɗin ramma, da ƙoƙarin wanke wanda nake karewa har sai na yi exposing ainihin gaskiya ko da kuwa ita ce ajalina” tun da ta yi face to face da ita, ta ji duk wata fargaba da tsoron da take ji sun kau.
Ta ɗauki jakarta, ta fita daga office ɗin.
Tsaki Bunkure ta yi ta daki tebur, ta ɗauki wayarta, ta danna ta kara a kunnenta.
“Yauwwa barrister Kabir ya kake?”
“Lafiya ƙalau manyan ƙasa ya aikin?”
“Normal ne, wacece Nabila a ma’aikatanka?”
Ya ce “Lafiya kuwa? Ya aka yi ki ka santa?
“Wacece ita, a id card ɗin ta na ga a wurinka take aiki”
Ya ce “Barrister Nabila, a law firm ɗina take”.
“Ta zubawa kanta fetur a jiki, tana kuri, idan na ƙyatta ashana, ba ita ba har kai, zaka ƙone ƙurmus ka ja mata kunne, ɓera ba ya taka rawa a gaban mage, ko da kuwa tana kan gargara ne”
Kabir ya ce “Subhanallah, me ta yi?”
“Ka bincike ta, ba na bari ayi mini kuskure biyu, ko yinƙurin yi aka yi, ina daƙile duk wani abu da zai kawo mini cikas”.
Kabir ya ce “Na fahimta, ki yi haƙuri dan Allah zan yi magana da ita, zan kuma ja mata kunne” ta ajiye wayar tana tsaki.
Cike da annashuwa ta fito daga wurin, tare da jin kanta tamkar ta yi facing ɗin babban abun tsoronta.
Ta tsaya a gefen hanya, ta ciro wayarta, ta kira Viper, ya ɗaga sai dai bai yi magana ba.
“Hello, ya jiki? Na san ba zaka yi magana ba, dama so nake na ji ya jikinka, na so zuwa na ganka amma rana tayi sosai, zan je wani wuri ne, ka kula da kanka sosai” ta katse wayar, ji yayi tamkar ya aikata wani uban zunubi, ya din ga bin wayar da kallo, yana tunanin yarinyar nan tana da hankali kuwa?.
Gida ta tafi cikin matsanancin farinciki, duk da ba su kwasheta da daɗi ba ita da.
Gida ta tafi ta yi wanka, ta ɗauki wayarta ta kira sumayya, amma line busy.
Ta ajiye wayar ta kwanta tana bacci.
*
Shiru shiru Abdul bai je kiran iyayensa ba, yana nan yana fama da kansa, kuma ya hana duk abokansa zuwar masa gida.
Duk da Allah ya isa, da fatan mutuwa da ramma take yi masa, hakan ba ya hanata tausaya masa, idan ciwon ciki ya murɗe shi, har mamaki take yi da ya ce mata ulcer ce, dan ita ta ɗauka yunwa ce take kawo ulcer, yaran masu kuɗi ba sa yi.
Da daddare yana kwance a kan gado, tana zaune a ƙasa tana karanta wani novel na turanci, da ta ɗauka a falonsa, duk da ba wani ganewa take yi ba, amma yana ɗebe mata kewa.
Tana ji aka kira shi a waya, ya ce yana zuwa, ya tashi ya fita.
Bayan ya fita, ta ɗaukko pillow, ta ajiye a ƙasa ta cigaba da karatunta.
Hamma da take ta yi ba ƙaƙƙautawa ne ya sanya ta gane bacci take ji sosai, ta tashi za ta rufe ƙofar ɗakin, kasancewar ya bar key ɗin ta ciki, dan ciwon cikin nan da yake yi, ta samu sassauci daga akuyancinsa.
Sai dai ta buɗe ƙofar falon ba ya nan, ta fito ta wuce kitchen, ta daɗe a kitchen, ta zubawa fridge ido, komai akwai na morewa rayuw a gidan, amma gaba ɗaya ba ta jin daɗinsu, saboda ƙazantacciyar rayuwar da take ciki.
Ta sha ruwa mai sanyi, ta cika cikinta, ta fito falo, sai dai abun da ta tarar ya sanya gabanta mummunan faɗuwa.
Cikin hanzari ya ture Nina daga jikinsa, ya yi tsilli-tsilli da ido, yana kallon ramma.
“Abdul wacece wannan?”
“Amm maid ɗina ce, mai aikina ce”.
“Kamar yaya, ina solomon ɗin, shi zaman me yake yi? Me ka ke yi da mace a zaune a gidanka? Abdul kar ka raina mini hankali mana, karuwa ka ajiye Abdul?”
“Kar ki sake ce mini karuwa, ni ba karuwa ba ce, ke ce karuwa amma shi ki tambaye shi yadda aka yi na zo gidan nan?” Ta yi tsaki za ta tafi.
“Abdul ka yi mini magana wace banzar ce wannan?”
Abdul ya miƙe ya ce “ya isa haka, ki je gida za mu yi magana “
“Ban gane ba, ka gaya mini wacece wannan?”
Bayan ramma ya bi da sauri, Nina ta biyo shi, amma yana shiga ɗakin, ya mayar da ƙofa ya rufe da key ta ciki.
Ramma tuni ta kwanta wani abu mai zafi ya tsaya mata a rai.
“Rahma, ki tashi mu yi magana dan Allah, zan yi miki bayani” tayi masa shiru ta ƙi motsawa.
“Dan Allah ki tashi ki ji, zan yi miki bayani”
Ramma ta waiwayo sosai ta kalleshi ta ce “Ba ni zaka yi wa bayani ba, Allah zaka yi wa bayanin abun da kake aikatawa ba tare da tsoronsa ba. Ni baƙincikina, muzanta rayuwata da ka yi ne da wulaƙanta ni.
Ka yi zina da wasu, ko wankan janaba baka yi, ka zo ka kuma afka mini, wannan wace irin rayuwa ce, Abdul yasar ka gama da rayuwata, wallahi ko baka kashe ni, ina son kashe kaina na huta, dan dai kawai ina tunanin makomata ne, amma ka cuceni wallahi” tayi maganar hawaye na ta gangarowa ta gefen idonta.
Hannu ya sa yana share mata hawayen, amma ya kasa ce mata komai.
Ya numfasa ya ce “Kina ji na?”
“Dalla ƙyale ni, ba abun da zan ji, ni ƙyanƙyamika ma nake ji, mazinaci ƙazami mara tsoron Allah”
Duk da yadda maganganunta suka yi masa zafi, amma ya daure ya ce “Dan Allah Rahma ki daina kirana da mazinaci, kalmar nan na yi mini ciwo sosai. Wallahi tun a kanki ban sake zina ba, yanzu ba abun da ki ke tunani ba”
Aikuwa kamar ya tunzura ta, ta tashi zaune ta ce “Ni abun da ka ke yi mini menene? Na faɗa na kuma” ta sauka daga kan gadon tana huci, cikin ɓacin rai.
*
Naja’atu kuwa tana zaune a bakin gado, tana ta haɗa ƙwayoyi a cikin roba, ta na zuba ruwa a ciki, shiru ta yi tana tunanin maganganun da Nabila ta gaya mata, mamakin ƙarfin halin yarinyar take yi, yadda ake shakkarta da shakkar yin gaba da gaba da ita, ita wannan yarinyar zata yi wa cin mutunci haka. Me take nufi da za tayi exposing ɗin ta. Ta daki teburin gabanta ta ce “Wai ma wacece ita?” Ta yi wata ajiyar zuciya ta ɗaga kai, ta shanye ƙwayoyin cikin robar nan da ta narka.
Nabila ce zaune tare da Nasir, tana bashi labarin yadda suka yi da Naja’atu Bunkure, yake ƙara ja mata kunne, a kan ta bi sha’anin matar nan a hankali, kar ta yi mata illa.
Tayi murmushi ta ce “In sha Allah ni zan karya alkadarin matar nan”
Ya ce “To, Allah ya sa”
Ya amsa da “Amin, na ji an ce kin ce mota ki ke so?”
Ta jinjina masa kai ta ce “Abba ya saya mini mota,kai kuma ka din ga zuba mini mai” tayi maganar cikin shagwaɓa. Kasa amsa mata yayi, sai bin ta da kallo da yake yi, yana murmushi.
Ta ce “DSP ya ake ciki ne, da zancen binciken viper?”
Ya numfasa ya ce “Ina ta cigaba da bincike, gashi ana cigaba da matsa mini a kan kama shi, abubuwan ma na rasa yadda zan yi, duk shaidar da na kama sai ta zille, ace in sake shi, na rasa wannan wane irin abu ne. Amma dai an kwatanta mini wani yaro, dealer ne na wiwi, wai shi ɗan mama, idan na kama shi, ba zan bari a san na kama shi ba, sai na dangana da kama Viper in sha Allah” gabanta yayi mummunan faɗuwa ta ce “To wai suwaye suke sakawa a saki shaidun naka?”
Ya ce “Ban sani ba, daga sama kawai ake cewa na sake su”.
Ta jinjina kai ta ce “Kuma anya ba su san in da yake ba, raina maka hankali kawai suke yi ba?”
DSP ya ce “To ko ma dai menene, zan ɓoye bincikena, sai na dangana da kama shi, na danƙa musu shi, su san yadda za su yi da shi. Ina nan mun samu bayanan lokutan da yake zuwa an tabattar mana da idan muka kama shi, zamu iya kama Viper “
Kamar an mintsine ta ta miƙe, ta ce “Bari na koma ɗaki, zan yi wani uzuri” har da gudu ta haɗa, ta tafi ɗakinta, ta ɗauki wayarta ta din ga kiran Viper, amma yaƙi ɗagawa, tayi masa missed calls sun fi goma, amma ko ɗaya ya ƙi ɗagawa, ga yamma ta yi sosai, idan ta fita kan ta dawo magariba zata iya yi.
Jikinta ne ya hau tsuma, saboda irin kallon da yake yi mata, yayi gaba da nufin ta bi bayan shi, amma ta ƙi, ya tsaya ya waiwayo yana kallonta, ta kalli Walid, ya gyaɗa mata kai alamar ta bi shi.
Kamar mara gaskiya haka ta bi bayansa, sai da suka ɗan yi nesa da gidan kaɗan, sannan ya waiwayo ya kalleta ya ce “Me ki ke nema a wurina?”
Ta kalleshi ta sunkuyar da kai. “Ki yi mini magana, me ki ke nema a wurina? Meyasa ki ke sintirin zuwa in da nake? Idan so ki ke a kama ni, ki kawo su su kama ni mana, wace irin yarinya ce ke ne?”
Yadda yake maganar cikin hargowa, sai da ta ja da baya, saboda tsoro.
“Talk! Me ki ke so, waye ya turo ki?”
“Ni ba wanda ya turo ni” ta yi maganar cike da tsoro.
“Me ki ke nema?”
A sangarce ta ce “Ni ka daina yi mini magana a haka, tsorata ni ka ke yi, ni ban san me zan ce maka ba”ta yi maganar tana kawar da kanta gefe.
Ya tsareta da idanunsa, ita kuma taƙi ɗagowa, ta sunkuyar da kanta ƙasa tana haɗe fuska cikin tsoro.
Ya sunkuyo dai-dai tsawon ta ya ce “Ki bani amsa” tayi shiru ta ƙi magana.
Hakan ya ƙara hasala shi, ya buga ƙafarsa ya ce “Ki yi magana kan na saka ki yi ta ƙarfin tsiya”
Cikin rauni ta ce “Na gaya maka, ni babu wanda ya turo ni, ni na turo kaina, kuma ni tsoro ka ke bani ban san ta ina zan fara ba, tsorata ni ka ke yi”
Ba ta ƙarasa maganar cikin nutsuwa ba, ta ji hannunsa a wuyanta. “Naja’atu Bunkure, meye alaƙarki da ita? Ita ki ke yi wa aiki a kaina, da ita da Indabo ko?” Ba ta yi masa magana ba, sai idanuwanta da suka yo waje, ga hawaye na bin fuskarta, sai dai kallon da ta yi masa, ya sanya ƙirjinsa bugawa da ƙarfi, ya saketa ya ja da baya, yana dafe saitin zuciyarsa.
Dai-dai lokacin Walid ya ƙaraso ya ce “Viper meyasa ka ke haka ne? Ban sanka da cin zarafin mata ba, meyasa ka ke ƙoƙarin farawa yanzu?” Ya nuna Nabila da yatsansa, amma ya kasa magana sai haki yake yi, saboda zuciyarsa ta ƙi nutsuwa. Ta ƙura masa ido, tana kuka.
Kawai ya juya ya bar wurin, Walid ya ce “Sannu, kin ga abun da nake guje miki a kansa ko? Shiyasa na ce ki daina zuwa anyhow. Mun gode da gudunmawarki ga ɗan uwanmu, amma ki daina zuwan nan, ina tsoron yayi miki illa wataran”.
Ta girgiza kai ta share hawayenta ta ce “Ina da kafiya wasu lokutan, haryanzu ban ji cewar zan karaya ba, da ya bi ni a sannu, da zan yi masa bayanin abun da ya haɗa ni da Naja’atu Bunkure. Kawai ji nake ya zame mini wajibi na taimake shi, ina son sanin ƙarshen labarinsa, har cikin zuciyata nake son ba shi gudunmawa, na yi masa uzuri, wataran ba zai yi mini haka ba, bari na tafi. Ayyuka sun yi mini yawa ne sosai, amma ina nan zan je wurin likitan ƙwaƙwalwar, zan kuma dawowa”
Walid ya girgiza mata kai ya ce “Rayuwarki fa, ke kanki zaki jefa kanki cikin hatsari”
Nabila ta share hawayenta ta ce “Kar ka damu da ni, shi ɗin a ceto rayuwar sa da hankalinsa, a ƙwato masa hakkinsa, ba a san amfanin da zai yi wa al’umma nan gaba ba, ina son kamo bakin zaren lamarin ne, bari na tafi” ta juya ta tafi.
Walid ya girgiza kai, duk haryanzu bai tabattar da manufar Nabila a kan Al’amin ba, amma a jikinsa yake jin ba zata cutar da shi ba.
Ya koma gidan su, ya tarar da Al’amin ya cika yayi fam, ya kalle shi ya ce “Mai zamani ba ka kyautawa gaskiya, shi yaƙi ɗan zamba ne, ko da turotan aka yi, sai ka bari mu bi komai a hankali, haka Ƙanwata tayi ta fama da kai, da wannan zafin zuciyar ta ka, ƙarshe ta zame maka sanyin idaniyarka. Ka din ga bin komai a hankali, bamu san mai gobe za ta haifar ba, kar ka daki kwano. Ina son mu ƙara zurafafa bincike a kanta, wanda na yi bai gamsar da ni ba”
“Mai laya”
“Viper”
“Ka ƙyale ni da maganar yarinyar nan”
Walid ya ce “Ba zan ƙyaleka ba, sai ka fuskanci gaskiya Viper”.
Nabila tana tafe, tana mamakin dalilin da ya sanya Viper yake son kasheta wasu lokutan, amma meyasa ya rikice haka da ya ji ta ambaci Naja’atu Bunkure?.
Gaba ɗaya al’amuran case ɗin Viper sarƙaƙiyarsu ta yi yawa, a labarin da Walid ya bata, ba ta ji in da Najar tayi masa wani abu ba, kodayeke haryanzu labarin bai kammala ba.
Gida ta yi niyyar tafiya, dan kanta ciwo yake yi mata, amma kwana biyu ba ta haɗu da sumayya ba, kuma gashi ba ta bata labarin karonta da Naja’atu ba, dan haka ta kira nufi gidan radiyon su Sumayya.
*
Ramma na zaune na karyawa take kallon Abdul, yadda ya sha kunu, yana video call da wani likita, yana yi masa bayani, a kan wani result na patient da ya turo masa, yanayin yadda yake bayanin ya tabattar mata da ya san abun da yake yi. Sai da ya gama sannan ya rufe tab ɗin, ya kalleta ya ce “Kalli gabanki kar ki lashe ni”
Ta kwaɓe baki ta ce “Ban ga abun lasa a jikinka ba, jiki duk najasa”.
Cikin ko in kula ya ce “Haka dai ki ke zaune da ni” tayi guntun tsaki, ta cigaba da tauna a hankali.
Can ta sake kallonsa ta ce “Abdul yasar”
Ya ce “Your excellency”
Ta ɓata fuska ta ce “Ba na son wata your excellency”.
“Ke ba abun alfaharinki bane ba, ace ke yarinyar deputy governor ce ba”
“Malam ka daina zaƙewa ba zaka taɓa ci ba, ai shugaba nagari ake fata, kai idan ka zama shugaba ai ina ga sai ka halatta zina, tun da gaka bature, yahudawa ne abun koyinka”
Ya girgiza kai ya ce “A’a iskancin nawa bai kai nan ba”
Ramma ta ce “Ga wanda bai sanka ba ba, ni tambayarka zan yi, wai dan Allah da gaske kai likita ne? Mamaki nake yi” yayi mata banza yana shan tea.
“Taɓ, kura da fatar akuya, ba su san har giya ka ke sha ba, ashe wataran zaka yi kisan kai, ko ma in ce kana yi. Saboda irinka wasu mazan suke raka mata asibiti, dan tsaf zaka yi wa matan mutane ɓarna tun da ka saba” yadda ya dire kofin yana kallonta ne ya sanya ta sha jinin jikinta.
“Meyasa ba ki da ɗa’a?”
“Saboda ɗa’a muhalli ne da ita, nan kuma ba wurin da ya dace na nuna ta bane”
Ya jinjina kai ya ce “Haka ne, duk matar da na yi lalata da ita, ita ta kawo mini kanta, kar ki ƙara yi mini irin haka”
“Nima ni na kawo maka kaina kenan ko? Baka da kunya ko kaɗan, sai dai idan ka gama kumburin ka fashe, har abada mutumin banza ka ke a idona, ‘ya mace ba ta taɓa mantawa da wanda ya kawar mata da mutunci, ko da kuwa ta hanyar aure ne, balle ta mummunar hanya, irin wadda ka yi mini, wallahi ban da zuciyar musulunci da tuni na kashe kaina na huta, kaf danginmu babu mazinaci, amma ni kalle ni yanzu. Tsaki yayi, ya tashi ya zai fice.
“Wallahi duk in da zaka je, Allah ya isata, na nan na bibiyarka har kabarinka” Dummm ƙirjinsa ya buga, ya waiwayo yana kallon ramma da ke ta uban kuka.
Bai taɓa dana sanin aikata duk wani laifi da yake yi ba, sai a kan fyaɗen da ya yi wa ramma. Galibin saɓon da yake yi, tsakaninsa da Ubangiji ne, ba a taɓa tsayawa gaba da gaba, ana tsine masa da yi masa Allah ya isa ba, ya sha attempting ya mayar da ita, amma sai ya ji ba zai iya rabuwa da ita ba, kuma kamar yadda take yawan faɗa, ya riga ya gama lalata mata rayuwa, ba za ta yi daraja a idon jama’a ba.
Motarsa ya shiga, ya tarar da wayoyinsa a ciki suka kwana, a buge ya dawo jiya tab ɗin sa ce kawai a cikin gidan, missed calls ɗin mahaifinsa babu adadi, ga na Naja’atu Bunkure, banda na mahaifiyarsa. Tunani yake yi ko lafiya ake yi masa wannan uban kiran hakan, shi ya san bai yi wani laifin ba balle ace.
Haka ya ja mota, ya nufi gidan su, yana jin yadda Allah ya isan ramma, ke ƙara yi masa amsa kuwwa.
Falon indabo ya nufa, ya na zuwa ya hau shi da faɗa, “Wane irin rashin mutunci ne zai sanya ka ƙi ɗaga waya tun jiya? Har na fara tunanin wani abun ne ya same ka? Kana can mashaya kana iskancin naka daka saba ko? Wallahi ka nutsu ba za ka lalata mini siyasa da shirina a banza a wofi ba, saboda shashancinka da rashin sanin ciwon kai ba, dole ka san abun da ka ke ciki ka shiga hankalinka”
Zama yayi ya haɗe rai, yaƙi magana, har Indabo yayi masifarsa ya gama, sai da ya gama haki, sannan ya ce “Jiya Naja’atu ta zo mini hankali a tashe, yarinyar da ka yi wa fyaɗe, mutumin da aka ce shi yayi, wata lawyer za ta tsaya masa, ta je har office ɗin Naja’atu neman in da aka tsaya a case ɗin. Ina tsoron ranar da abokan adawa za su ɗagomu, ko su bankaɗo miyagun laifukan da ka ke aikatawa. Yanzu ina ka kai yarinyar yaya aka yi da ita?”
“Ban sani ba, wace yarinyar nake magana a kai? Yarinyar da ka yi wa lalatar nake yi maka magana”.
“Amm…m…wai ita rahama?”
“Kai ka sani, ina tambayar ka kana tambayata?”
Abdul ya ce “Ba Naja ce ta je ba, zata ba su kuɗi a rufe zancen ba?”
“Zan kife ka da mari wallahi, uban najar, ba ta je ba suka ƙi karɓar kuɗin, suka ce sai an karɓar musu hakkinsu ba? Ka ce mini zaka kashe yarinyar yaya ka yi da ita? Sannna yaya ka yi da uwar yarinyar, muddin case ɗin ya cigaba aka samu sani leakage mun kaɗe, zan iya asarar wannan wahalar ta wa, takarar ma ba zaka samu ba”.
Abdul ya dubi Indabo ya ce “Amma daddy ka riƙe muƙamai da dama a garin nan da ƙasar nan, kai yakamata ace ka zama governor nan ba ma deputy governor ba da ka ke ƙoƙarin ɗora ni a kai ba, ni da ka bar ni da sabgar siyasar nan takura mini za ayi na kasa sukuni yadda nake so”.
Indabo ya jinjina kai ya ce “Taɓɗijan, bilki anya ni na haifi yaron nan kuwa? Kina jin abun da yake faɗa?”
Ta sha kunu ta ce “Wace irin magana ce wannan ka ke yi?”
“Ki na jin abun da yake gaya mini, Abdul siyasa lissafi ce, idan ya ƙwace maka, babu wata fomular da zata yi maka solving duk wani hardship da zaka shiga. Na gama da jihar nan, sonake ka riƙa mini, sama nake tunani tawagarmu mu ƙarasa mamaye ƙasar nan, komai a lissafe nake yin sa”.
Abdul ya yi ajiyar zuciya ya ce “Yarinyar ta mutu ai, babarta ce take nan”
“Ka tabattar?”
Abdul ya jinjina kai. Indabo ya ce “Dole aje a nemo babarta, ita ma a kawar da ita, kar su ɓata mana aiki”
Cikin tashin hankali ya ce “Ita ma wai kashetan za ayi?”
Indabo ya ce “To me za ayi idan ba a kasheta ba? Sai asirinmu ya tonu kuma, sannan azo a fara neman mafita?.
And na ɗaga komawata Abuja, sai Allah ya kaimu weekends, kai kuma zaka tafi jibi in Allah ya kaimu, akwai meeting da shugabannin jam’iyya na ƙasa da na jiha, sannan akwai meeting na musamman da deligates, dan dai a samu ayi nasara. Sai ka je ka yi shiri ka bar ni da sauran”
Gaba ɗaya jikin Abdul ya yi sanyi, ya tsare mahaifinsa da ido.
“Menene kuma ka tsaya kana kallona? Kafin ƙarshen watan nan kuma za a kai kuɗin aurenka, gidan party chairman kai da ‘yar sa”.
Abdul ya murza goshinsa, saboda yadda kansa yake sara masa, gaba ɗaya ya rasa abun yi.
*
A nutse sumayya take kallon Nabila ta ce “Arfa, idanunki sun nuna akwai damuwa, meyake damunki ne kamar ma fa kuka ki ka yi” kamar Sumayya ta soso mata wurin da yake yi mata ƙaiƙayi, kawai ta saka mata kuka.
Sumayya ta ce “Matsalata da ke kenan, shagwaɓa arfa” ta share hawayenta tana zumɓura baki.
Sumayya ta yi murmushi ta ce “Ƙila fa ba wani abin kirki ne ya saki kukan ba, ina jinki ko duk Najar ce, yaya ku ka yi da ita?”
Nabila ta ce “Wannan ai azzalumar mace ce” nan ta gaya wa Sumayya yadda suka yi.
Sumayya ta jinjina kai ta ce “To hakan ne ya saki kuka?” Nabila ta girgiza kai ta ce “Ke na gaji ne, kaina ya ɗauki caji, kin ga rashin mutuncin da barrister Kabir ma yayi mini duk saboda ita, ni kamar na karaya ma, amma wallahi ba zan janye ba”
Sumayya ta yi dariya ta ce “Manya gatan wasa, karaya ba taki ba ce ba, akwai ƙalubale sosai a duk wata nasara da ake son cimma, dan haka ki yi haƙuri ki cigaba da addu’a, In sha Allah sai kin cika burinki a kan Naja’atu”.
“Wallahi sumy da kamar na karaya, amma ba zan karayan ba in sha Allah, sai na cika burina”
“Yauwwa mutuniyar Viper” da sauri Nabila ta kalleta ta ce “Me ki ka ce?”
“Mutuniyar Viper mana, ko shi yanzu kin ɗaga masa ƙafa, kin haƙura da nemansa kin koma kan fansarki ta naja’atu bunkure?”
Nabila ta ƙurawa fuskar Sumayya ido ta ce “Al’amin mai dogon zamani” tayi maganar tana murmushi.
Sumayya ta ce “Ban gane ba”
“Kawai shaƙar da yayi mini nake tunawa ne, na kusa sheƙawa”.
“Amma haryanzu ba ki sanarwa DSP ba, yakamata ki tamakawa aikinsa fa”
Nabila ta ce “Taɓ haka kurum ya gaya wa Abba, ya saka Abba ya harbe ni da bindiga har lahira, na je wurin ɗan daba, ba dani ba bari na tafi gida, marata ma ciwo take”
Nabila ta tashi, sumayya ma ta tashi za ta rakata, a reception suka haɗu da P.A, gaban sumayya ya faɗi, ya din ga bin su da kallo, ita da Nabila.
“Malam ka kalli gabanka mana, ji jaraba zai saka na faɗi” Nabila ta yi maganar cikin ɗaga murya tana kallon P.A
Sumayya ta ce “Na shiga uku, haba Arfa, babba ki ke yi wa haka?”
“To waye ya ce ya kalle ni?”
P.A ya ce “Yi haƙuri, wallahi kallon sani nake yi miki ne, kina yi mini kama da wata da na sani”
Nabila ta kwaɓe baki, yayin da jikin sumayya ya hau rawa.
Ya ce “Sumayya wurinki na zo fa” gaba ɗaya sumayya ta rikice, dan kar P.A yayi wani abun da zai sanya Nabila gane wani abun, dan sharp brain ce da ita sosai.
Nabila ta ce “Bar rakiyar kawai, ni na tafi sai mun yi waya, kuma ki daina ccacanza lambobi kina kirana, kamar wata mara gaskiya ko ‘yar 419, idan na kira layinki ba zaki ɗaga ba, sai ki yi ta canza lamba” gaban sumayya ya faɗi, mussaman kallon da P.A yayi mata.
Cikin yaƙe Sumayya ta ce “Layina ne yake bani matslaa, sai mun yi waya”.
P.A ya tasa ta a gaba, zuwa news room, in da take aiki, ya rufe ƙofa ya kalleta ya ce “Wato canza lamba ki ke yi ki yi waya da ita ko?”.
Sumayya ta ce “Ban san me zaku iya yi mata ba, dole sai na tantance abun zan din ga gaya muku a kanta”.
“Haka muka yi da ke? Kin zaɓi ki salwantar da rayuwarta kenan?”
“Ba zan salwantar da rayuwarta ba, kuma babu abun da zai same ta sai wanda Allah ya ƙaddara mata, ku bani a hankali ai ina sanar muku da duk wani abu da take aikatawa kamar yadda ku ka buƙata. Menene na biyo ni nan kuma, ka yi mini magana a gabanta sai ta gane”.
P.A ya ce “Ta gane me? Muddin ki ka bari ta gane, sai ta zama gawa, an sanar mini ta zo ne, kuma na san muddin ta zo, wani muhimmin abun ne ya kawo ta. Me yake faruwa? Dan kar ki yi zaton ke kaɗai ki ke yi mana aiki, duk motsinki kema ana saka mana ido a kai”.
Sumayya ta yi ajiyar zuciya ta ce “Zauna mu yi magana”.
Nabila kuwa bayan ta fito harabar radiyon, still motar nan ta sake gani, wadda aka taɓa bin ta da ita, ta ganta a law firm ɗin su, yanzu ma gata a gidan rediyon su Sumayya, kuma lambar motar ce ta sake tabattar mata da motar ce dai.
Wani guntun murmushi ta yi ta ce “Bari dai na ga ƙwal uwar daka”.
*
Ramma ba ta sake ganin Abdul ba sai can dare, ba ta yi zaton zai kulata ba ma, ta ɗauka fushin da yayi ne ya hana shi dawowa, dan har ta fara bacci, ta ji motsinsa a bedroom ɗin. Ta buɗe ido ta kalleshi, ta ga bai kulata ba. “Kayi dare da yawa yau” ya waiwaya ya kalleta ya ce “Idonki biyu?”
“A’a motsinka ne ya tashe ni”
“Barin gidan nan zamu yi, gobe in Allah ya kaimu” cikin rashin fahimta ta ce “Saboda me?”
“Wani dalili kawai, zan yi tafiya ne na sati ɗaya”
“Kuma ka tafi ka bar ni nikaɗai?”
Ya ce “Eh babu abun da zai same ki, can zamu koma gaba ɗaya, bana son a gano ki a nan”.
Ta taɓe baki ta ce “Kana nufin dai haka zan cigaba da zama kenan?”
“A’a ina tunani a kan zaman mu”
Tayi shiru, ta gyara kwanciyar ta, ta cigaba da baccinta.
Juya tayi, ta ganshi a zaune, yana hana haɗa ƙwayoyi, ya ɓalle wannan ya ɓalli waccan. Matsawa ta yi ta ƙwace ta ce “Ba zaka sha wannan ƙwayoyin ka mayar da ni jakarka ba, ba zai yiwu ba, wallahi ko na bar maka ɗakin” a sanyaye ya ce “Ba wanda ki ke tunani bane ba, damuwace ta ɗan yi mini yawa, bacci nake son na yi” ta saka hannu ta kwashe packets ɗin ta ce “Kai kamar ba likita ba, anya ma ba likitan bogi bane ba, haryanzu ina tantama babu likitan kirki da zai yi abun da ka ke yi”.
“Ke ba zaki gane ba ne, ki bani kawai idan ba haka ba, baccin ba zai yiwu ba”.
“Aikuwa sai dai kar ka yi” ta watsa su bayan gadon, ta gyara kwanciyar ta.
*
Nabila tana zaune, tana kaɗa ƙafa tana cin gugguru, ta na zancen zuci, ta kalli wayarta da take silent, sai haske take yi, ta saka hannu ta ɗauka, ta saka a kunnenta.
“Hello barka da dare”
A hankali ta ce “Yauwwa”
“Ya gida aiki?”
“Alhamdilillah”
“Na ce ina da ƙorafi, a taimaka mini an ce na je office, na je sau biyu ba kya nan”
Ta yamutsa fuska ta ce “Wake magana ne?”
Ya ce “Ni ne”
“To kai wa?”
“Bawan Allah, ni ne na kira ki rannan. Wataƙila ina da magana mai muhimmanci da ke”.
Nabila ta yi guntun tsaki ta ce “Da maganar mai muhimmanci har haka, da ba a waya zaka tsaya kana zagaye-zagaye ba”. Ta katsewayar, tana cigaba da ɓata fuska.
Lambar Viper ta kira, ta na jiran ya ɗaga, har ta sare da zai ɗaga, ta ji ya ɗaga wayar.
Tayi gyaran murya ta ce “Ka na ji na? Na san ma kana ji, ba magana zaka yi ba. An ce baka taɓa mata, amma ni kullum burinka ka kashe ni, ka yi ta shaƙe ni, ko cikakkiyar lafiya ba ni da ita, idan ka yi haƙuri ka ba a hankali zan yi maka bayanin komai, amma ka fiye zafin zuciya haryanzu maƙogwarona kamar an shaƙeni da ƙarfe nake ji” ta yi maganar har da kukan kissa.
Yayi shiru yana sauraren ta.
“Ba zan yi zuciya na daina zuwa ba, har sai ka gaya mini sauran labarin nan, na ji ina ‘yar madara take, ina son saninta, akwai abubuwan koyi da yawa a rayuwar ta. Zan sake dawowa in sha Allah, amma ka rage zafin rai dan Allah, mu yi magana ta fahimta”
Nasir ne ya shigo ɗakin unexpected, ta ɗaga kai ta kalleshi, ya ƙura mata ido.
Ba ta canza daga yadda take ba, ta ce “Sai anjima, zamu yi magana” ta katse kiran ta kalli Nasir ta ce “Yaya shigowa ba excuse?”
“Da wa ki ke waya?” Ta gyaɗa kai ta ce “Wani ne”
“Wani wa?”
“Is confidential”
Ya ƙura mata ido ya ce “Confidential as how?”
“Haba Yaya, client ɗina ne fa”
“Amma ki ke wannan kashe muryar?”
Ta ce “Ikon Allah, to ai he’s not just a client, ammm” ba ta ƙarasa ba ya juya ya fice, ta yi ajiyar ta ce “Ohh ni Nabila, yaya ai sai dai ka yi haƙuri”
Walid ne ya shigo ɗakin, dawowarsa kenan, ya tarar da Viper, a ɗakinsa, yana goge wuƙarsa sweazland. Ɗan mama kuma na zaune a gefensa.
Zaro ido ya yi ya ce “Me zan gani haka? Viper waye ya ɗaukko wannan wuƙar, ya kawo maka?” Al’amin yayi shiru yana jujjuyata a hannunsa.
Ya kalli ɗan mama da yake sunkuyar da kai, aikuwa a fusace ya saka ƙafa ya daki ɗan mama ya ce “Amma an yi shegen yaro, wallahi baka da mutunci ɗan mama, uban wa ye ya ce ka ɗaukko masa wuƙar nan?”
Ɗan mama ya ce “To wai ya zan yi dan Allah? Cewa yayi sai na ɗaukko masa, kuma Oga liti ne ya ɗaukko ya bani, wai operation za su fita gobe, Madaki yana cikin gari”
Walid ya din ga ɗurawa Ɗan mama ashariya, ya juya ya nufi Viper, Amma Viper ya miƙe tsaye, ya fito da harshen sa waje ya mayar.
Walid ya nuna kansa ya ce “Ni zaka sakawa ƙarfe?”
“Ƙwarai, muddin ka yi ƙoƙarin dakatar da ni, wallahi jininka za ta sha, ai na gaya maka ka nesanta yarinyar da ni, muddin ina ganinta ba ni da wata nutsuwa, dan haka ba ka da ikon, dakatar da ni”.
Walid cikin ɓacin rai ya ce “Hanyar da muke ƙoƙarin bi, ba mai ɓullewa ba ce, ka yi haƙuri”
“Shhhh” ya yi maganar tsare Walid da ido.
“Dalla matsa, ni zaka yi wa barazana, ka je ka yi duk abun da ka ga dama, na daina shiga harka, tafiya zan yi ku ƙarata da kai da su litin, mu gani idan hanyar za ta fishshe ku”
Suna cikin faɗa liti ya shigo, suka ya tarar da su, liti ya ce “Kai walid, ba zaka hanamu abun da muke so ba, ka hanamu motsawa, wancan banzan madakin, yana ta rashin mutunci a gari, wallahi sai mun ɗauki fansa” Walid ya fice ya bar musu gidan cikin matsanancin ɓacin rai.
*
Abdul ne da ramma suke tafe a mota, tana ta kallon hanya, ya yi locking ɗin motar, ga glass ɗin ta tint ne.
“Wai tafiyar nan ba zata ƙare ba, ni fa na gaji”.
“Eh, cinikinki zan je na yi na sayar” ta harare shi, ta cigaba da kallon titi.
Wata unguwa suka yi, babu gidaje da yawa a wurin, sai tsilla-tsilla, kuma manya manyan gidaje ne, na alfarma a rukunin.
A ƙofar wani ƙaton gida ya tsaya, aka buɗe masa gate, ya shiga, wasu irin manyan karnuka na ta kai komo a harabar gidan, ya zagaya yayi parking, ya cire lock ɗin motar, ta buɗe ta fita.
Shi ma ya fito, ya buɗe boot, ya ciro akwatuna, ya ce “Mu je”
“Yanzu da ka mayar da ni gida, gara ka sake kawo ni nan?”
Yayi gaba ya ce “Idan karnuka suka cinyeki, kya taho” ta bi bayansa tana rarraba ido, gida mai kyau na alfarma.
Saman bene suka hau, ya kaita wani katafaren bedroom, ya ce “A nan zaki zauna, zuwa lokacin da zan dawo, kafin nan na samo mafita, zaki iya shiga ko ina, an ajiye duk abun da ki ke buƙata, sai dai ko haraba ba zaki fita ba. Zan ajiye miki waya duk abun da ake ciki, ki kirani ko idan kina buƙatar wani abu, wayar lambata kawai zaki iya kira”.
“Wai dan Allah nikaɗai zaka bari a gidan nan, ni tsoro nake ji wallahi”
“Ki yi haƙuri mana, ba zan daɗe ba, na ɗan lokaci ne, zaki yi missing ɗi na ko?” Yayi maganar yana kissing ɗin goshinta. Kuka take yi sosai, ya rungumeta yana rarrashin ta.
*
Yau ma kaca-kaca Walid ya yi da su Viper, Liti yana supporting ɗin Viper a kan iya wuya, kawai su afka su ɗauki fansa.
Duk yadda walid ya so fahimtar da su, suka ƙi fahimta.
Nabila ta fara gane kan hanyar zuwa gidan su Viper, kanta baya kullewa kamar da.
Babu tsammani ta yi karo da Walid, ta ja ta tsaya, ta zata zai yi mata masifa, ta ce “Ina wuni?”
“Lafiya ƙalau”
“Amm yana ina?”
Ya nuna mata dutsen da yake can gaba, ya ce “Yana can, amma ki daina wahalar da kanki, taurin Al’amin yayi yawa, an ɗaukko masa wuƙarsa, zai je ya yi gaba da gaba da madaki yau, ki ƙyale shi kawai”
Ta girgiza kai ta ce “A’a, zan jarraba sa’ata” tayi gaba ta nufi in da dutsen yake, ba ta ƙarasa ba ta hango shi, a zaune a gefen bishiya, cikin inuwa yana ɗan kaɗa ƙafa, ya na shan sigari.
Ta ƙarasa ta zauna a kusa da shi ta ce “Barka da rana” bai amsa ba, ta saka hannunta, ta zare sauran karan tabar hannunsa ta ce “Ayi mini uzuri, ba na son hayaƙi, mara zuciya na sake dawowa. Dan Allah kar ka shaƙe ni, magana zamu yi ta fahimtar juna”
Ya ɗaga kai ya kalleta, ya yinƙura ya miƙe, ita ma ta tashi ta tsaya a gaban sa, ka saurare ni ko sau ɗaya ne, zafin zuciya da gaggawa shi ya sanya ka rasa da yawan mutane masu muhimmanci a rayuwarka”.
Sweazland ya saka mata a wuyanta, ya ce “Gargaɗi na ƙarshe, ki rabu da ni, ki fita daga rayuwata”.
Ta kalli yadda wuƙar ke ƙyalli a saitin wuyanta ta ce “Sai na ji ƙarshen labarinka, na ji wa ka kashe? Kuma ina jauhar da abun da yake cikinta?”
Ya kalleta ita ma cikin ƙwarin gwiwa ta cigaba da kallonsa, duk da ƙasan zuciyarta a tsorace take.
“Ki daina kallona a haka, meyasa ki ke son ki zama raunina ne?” yayi maganar muryarsa na rawa.