Amaryar Zayyad na Rahama Kabir
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Buy Affordable Data and Cable Subscription Here
Page 1
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
ZAINAB (Safna).
Table of Contents
Tunda aurenta ya gabato ta samu kanta cikin yanayi na fargaba da tunanin abinda zai je ya dawo, samakon faruwar wasu al’amura a shekarun baya da suka gabata. A lokacin da aka saka ranar aurenta da Sadiq biki ya rage saura kwana goma Allah yayi masa rasuwa, Safna ta samu kanta cikin mawuyacin halin da ba zata iya misaltashi ba, da kyar aka samu kanta dalilin tsananta addu’a da mayar da lamuranta ga Allah, a haka har ta samu ta dawo dai dai ta dangana tare da karɓan ƙaddarar ta. Bayan wani lokaci ta kuma haɗuwa da Lukman tun tana ƙin bashi dama har ta sake masa suka fara soyayya, cikin ƙanƙanin lokaci suka shaƙu daga bisani kuma ya turo manyansa aka fara maganar aure, an kawo sadaki da komai na aure saka rana ya rage wanda iyayensa ne suka ce a basu lokaci su gama shiri kan a saka, kwatsam Lukman da kanshi yazo yace ya fasa aurenta sannan ya yace ya yafe komai da suka kawo, Safna a lokacin kamar zata yi hauka domin ta kamu da tsananin son Lukman fiye da yadda taso Sadiq, babban tashin hankalinta yadda yaƙi faɗar meye dalilin janyewarsa. Safna gata da kyau, ilimi, nasaba, natsuwa da tarbiyya bata da makusa amma kuma ƙaddararta yana ga aure, da kyar ta iya haƙuri da rashin Lukman wanda har hakan yaso jefata cikin wani hali, ta kusa kamuwa da ciwon zuciya, ga hawan jini ya yayi mata dirar mikiya da ƙanƙanin shekarunta, ga rashin barci da ciwon ulcer da yayi mata mummunar kamu saboda rashin cin abinci, haka suka dinga zaryar asibiti da kyar aka samu aka shawo kanta ta dangana, tun daga wannan lokacin ta haƙura da zancen soyayya bata kula kowa duk nacin mutum sai dai yayi haƙuri ya rabu da ita, gata da farin jinin samari amma haka ta shafe shawon shekara biyu bata saurarensu.
Wani lokaci da yayarta Anty Maryam ta haihuwa a taron sunanta, sai rikici ya ɓarke a tsakanin dangin mijinta da danginta wanda hakan ya jawo tashin hankali har aljanu suka dinga zubar da mata a ƙasa, ciki har da Safna ta zube numfashinta ya ɗauke tamkar babu rai, hankula sun tashi sosai dan kyar aka shawo kan matsalar, amma ita Safna sai da ta kwana biyu a sanƙare bata san inda kanta yake ba anata aikin ruƙiyya da hayaƙi, a hakane har aka samu aljanin yayi magana wanda ya tabbatar da shine ya ke haifar da matsala a maganar aurenta, duk da Sadiq lamarin yazo da ƙarar kwana, sannan ba wai ya auri Safna bane kawai bai yarda wani namiji ya raɓeta ba, da kyar aka samu ya tafi ta dawo hayyacinta, tunda aka fahimci ga inda matsalar ta take kuma itama ta fahimci lallai tana da matsala duba da yawan mafarkin ruwa ko tana tashi sama da mafarkin macizai ko tana faɗa da wasu halittu, tunda ta yiwa malamin da yayi mata ruƙiyya bayani yace In Sha Allah zata samu lafiya, ya bayar da magani wanda za ta soma amfani dasu. Alhamdulillahi wannan shine hanyar warakar matsalar Safnah dan an kwashe shekara biyu ana aikin magani kuma an samu nasara dan har Allah ya sa ta fara kula samari a lokacin shekarunta ashirin da huɗu a duniya, ganin suna niman su hanata sukuni yasa ta tsaida Zayyad a matsayin wanda zata aura duk da bata ƙaunar mai mata, amma soyayyarsa tayi mata dirar mikiya wanda ba zata iya haƙura dashi ba duba da shima yadda yake mugun ƙaunarta.
Ba zata mance haɗuwarsu ta farko ba lokacin taje shagonsa dake kan babban hanya tsakanin Gomna Road da kuma Badikko, taje siyo fulawa da kayan haɗin donot, da ta gama siyayyarta an saka mata a leda ta tsaya bakin shagon zata tare napep ta wuce gidansu dake ɓangaren Abakwa GRA, sai ga wani yaro ɗan makaranta akan keke yazo zai wuce, tsautsayi yasa shi raɓar gefenta saboda gosilon daya haɗu a gurin, nan ya fasa mata ledar fulawa ya fashe ya soma zuba a ƙasa, da azama Safna ta kamo rigar yaron wanda ya sashi dole ya tsaya, ta shiga yi masa masifa akan lallai sai ya biyata, yaron ya soma bata haƙuri amma taƙi saurarensa dan abin yayi matuƙar ƙona mata rai, haka mutane suka fara taruwa a gurin masu bata haƙuri nayi masu bawa yaro laifi suna yi, Zayyad dake shago yaji haniyar tayi yawa sai ya fito yana tambayar yaran shagonsa meke faruwa? suka sanar dashi sai ya ƙaraso inda su Safna suke ya shiga bata haƙuri yace shi zai biyata, ya amsa ledar ya bawa ɗaya daga cikin yaransa akan su sake yi mata awo, nan taro ya watse sannan Zayyad ya gargaɗi yaron akan ya riƙa kula da hanya yayi masa godiya ya tafi. Zayyad ya koma shago ya zauna yana hango Safna har aka gama zuba mata ta amsa ta wuce, wannan dalilin yasa tasan shine asalin mai shagon da take yawan siya kaya a gurinsu, shima kuma dalilin daya saka shi riƙe fuskarta kenan, da ta zo siyan abu yana jin muryanta yake ganewa zai fito ya tsaya har a sallameta ta wuce, a hankali ya fara jin wani abu yana ɗarsuwa a zuciyarsa game da ita, tun yana ƙaryata kansa har ya yarda da ya kamu da sonta, ita kuma tana yawan zuwa shagonsa ne tayi siyayyar kayan fulawa saboda sana’arta kenan harkan snacks, donot da samosa tafi yi dan ta iya sosai tana yin na taron suna ko biki ko wani sha’ani, bata yarda da zaman banza ba dan har a gida tana yin na sayarwa, in tayi da yawa takan ɗiba ta tafi dashi makarantar bokon da take koyarwa ta bayar a shagon makarantar ana saida mata, in ya ƙare a bata kuɗin shima mai shagon ya cire ribarsa. Wannan shine sanadin haɗuwarta da Zayyad wanda baiyi ƙasa a guiwa ba har sai da ya kafa gomnatinsa a zuciyarta ya samu gurbi, tun tana ƙi har saida ta amince masa har suka shafe shekara guda da watanni kafin aka saka lokacin bikinsu, gashi yanzu saura wata ɗaya a ɗaura auren. Kiran daya shigo wayar Safna shine ya dawo da ita daga duniyar tunani data shiga, ta sauke numfashi ta ɗaga kiran da sauri dan har ya kusa tsinkewa ta kara a kunne.
Wa’alaikum Salam ina yini Maman Ilham.
Lafiya lau Alhamdulillahi, ya shirye shirye?
Hmmm lafiya lau.
Amaryarmu kenan ki daina wani hmmm ko kunyata kike ji? Abinda mun riga da mun zama ɗaya, dama na kira ki ne akan ki tura mini hoton ankonki ina so Abban Ilham ya siya mini ne nima na shiga tawagar ango kar a barni a baya.
Ok ba damuwa anjima zan tura miki ta WhatsApp In Sha Allah.
To nagode Allah ya nuna mana bikin lafiya sai anjima ɗin.
Yauwa a gaida yara nagode.
Daga haka suka kashe wayar, Safna tabi wayar da kallo tana mamakin Rashida yadda ko kaɗan bata taɓa nuna mata kishin zata auri mijinta ba, shigowar Anty Shafa falon yasa ta aje wayar tana cewa.
Anty wai kinji matar Zayyad ce tace in tura mata ankon bikina zata yi.
Ikon Allah! tunda nake ban taɓa ganin mace mai sauƙin kishi irin matar nan ba, ina ce itace kwanaki ta rako shi zance.?
Eh mana ai zuwanta ya kai sau biyu, sai ta biyo shi ita da yara su zauna anan cikin gida su barmu muyi zance a waje, har sai mun gama zai kirata ta fito su wuce.
Allah mai iko, gaskiya in har auren nan ya tabbata ina kyautata zaton zaku yi zaman lafiya.
Wlh Anty shiyasa bana fargaba da zai haɗamu gida ɗaya, kuma su anty Maryma sai ƙorafi suke yi akan kar na yadda amma ganin yadda take yi mini yasa nake ganin babu wata matsala dan ya haɗamu gida ɗaya.
Ki kwantar da hankalinki ki tsarkake zuciyarki In Sha Allah za kuyi zaman lafiya. Yauwa anjima mai gyaran jikin zata zo sai ki zauna cikin shiri.
To Safna tace mata, Anty Shafa ta zauna tana bawa yarinyarta nono, sai ga umma da Anty Maryam suma sun shigo, nan Anty Shafa ke basu labarin matar Zayyad tace a tura mata anko, anty Maryam taja guntun tsaki.
Wlh matar nan ki yi hattara da ita ban yarda da wannan shige miki da take yi ba, bayan muna da labarin sam bata jituwa da dangin mijinta.
Maryam karki karyawa Safna zuciya ta karaya, in kin san ba zaki ƙarfafa mata guiwa ba to ki daina kawo irin wannan maganar bana so, tunda ta nuna mata haka ya tabbatar da Zayyad yafi ƙarfin gidansa ne, sannan kuma akwai zaman lafiya a tsakaninsu tunda har zance ta taɓa rakoshi.
Umma nima shi na gani ba tada matsala wlh. Ni damuwata ɗaya ne kar wannan auren ma a kuma samun matsala irin na baya a fasa.
In Sha Allah ba abinda zai faru Zayyad sai ya zama mijinki Ƙanwata, ai Alhamdulillahi anyi maganin jinnun jikinki kuma an samu nasara da izinin Rabbil Ka’aba.
Cewar Anty Shafa da murmushi a fuskarta, anty maryam tace.
Kina amfani da magungunanki ko? ba kya wasa dasu.
Eh ina yi.
Yauwa. Amma ya maganar aikinki? zai barki ki cigaba da yi ko.
Hmmm Anty nifa wlh na gaji da zarya a hanya, shekara kusan huɗu fa ina koyarwa kawai zan kama business ne dan Zayyad yace zai bani jali nayi sana’ar cikin gida.
Safna daɗi soyayya! ke har kin yarda da zancen sa ko, karki yiwa kanki sagegeduwa fa Allah.
To Anty Maryam yace baya son matarsa tana aiki nima kuma na gaji da aikin, tunda shi yayi alƙawari nasan zai cika mini In Sha Allah.
Allah ya kyauta yasa ba daɗin baki ya cika ki dashi ba.
Ke dai Maryam kowa yana son wannan auren amma naga ke sam ba haka bena gunki.
Umma wlh ina son Safna ta yi auren kwanciyar hankali ne saboda duk cikinmu babu wacce take da kishiya, amma ace ita zata auri mai mata kema fa ba kishiyar nan gareki ba.
Ƙaddarar kowa daban, ita haka Allah ya ƙaddara mata, ai duk cikinku zan iya cewa babu wacce zata kai Safna adawa da ƙin namiji mai mata amma da yake yana cikin jarabawarta gashi zata auri mijin wata kuma Allah saiya ɗaura mata sonshi a haka, ni bana son yawan ƙorafin nan ku bita da fatan alkhairi.
Cewar Umma data miƙe dan shiga ɗakinta, nan suka cigaba da tattauna maganar bikin dan dama abinda ya kawo su kenan, suna so ayi bikin Safna fiye da yadda aka yi nasu a baya, shiyasa bini bini suna gida sun haɗu dan maganar bikin.
Malam Abdullahi shine mahaifinsu sai Umma Raliya mahaifiyarsu, gabaɗayansu mazauna cikin garin Kaduna ne sai dai asalinsu mutanen zaria ne daga ƙaramar hukumar Lere. Abba ma’aikacin gomnati ne yana koyarwa a makarantar sakondari, Yaransu biyar Anty Shafa’atu itace babba tana aure a tudun wada yaranta biyar sai anty Maryam tana aure a maƙarfi raod yaranta uku sannan yaya Mudassir sai Zainab data ci sunan mahaifiyar abbansu ana kiranta Safnah, sai auta yusuf. Alhamdulillahi wannan zuri’a sun ginu bisa tarbiyyar addinin islama da karatun zamani, duk da Anty Shafa da Maryam a iya secondary suke tsaya aka yi musu aure, amma fannin islamiya kuwa koda suka iya aure saida suka haɗa karatun sanawiyyarsu wanda dukkan su suna koyarwa a islamiyar dake kusa da gidajen aurensu. Yaya Mudan ya haɗe Digree ɗinsa fannin electric engineering, yana da shagon sayar da kayan wuta bai tsaya jiran aikin gomnati ba, Safna kuma tana da deploma a fannin islamic studies daga nan kuma bata ɗaura ba, sai ta samu aiki a wani private school ta soma koyarwa ana biyanta, fannin islamiya ma ta gama Mutawassiɗa tana shirin ɗaurawa ne Zayyad ya fito aurenta shine ta dakata dashi, Yusuf kuma yana matakin kammala secondary ya sauke Al-Qur’ani, wannan shine takaitaccen tarihin familyn su Safna.
Zayyad.
Yana zaune a office ɗinsa dake cikin babban shagonsa, wanda kayan masarufi yake sayarwa kuma babban dila ne dan har sari yana bayarwa, sannan akwai kimanin matasa biyar da suke aiki a ƙarƙashinsa. Wayarsa ce ta yi ƙara ya duba sai yaga yayansa Kamal ne da sauri ya ɗauka tare da yin sallama, bayan sun gaisa ya ce.
Yaya dama ina son zan kira ka riga ni. Batun kai lefe Hajya ta sanar dani wai kai dasu Baba Mamman zaku kai, wai yanzu haka ake yayi.
Eh ta sanar dani shiyasa ma na kiraka muji ya abin zai kaya, an sanar dasu Baba Mamman ɗin kuwa?
Ina ga ta faɗa musu, yanzu lokaci za a saka da za akai.
To Allah ya kaimu ina ganin ranar Juma’a zan shigo kaduna. Ya batun gidanka kuwa ka ƙarasa ginin?
An gama komai gyara kaɗan ya rage.
To madalla zan tura maka dubu ɗari biyar a cigaba da shirye shirye, amma da fatan Rashida bata ɗaga maka hankali ba.
Babu wata matsala dan sosai ta karɓi auren, baka ga yadda take hada hada ba da shirye shirye.
To Allah yasa ta ɗaure ya baku zaman lafiya, sai kayi ƙoƙari kayi adalci a tsakaninsu.
In Sha Allah, nagode yaya Allah ya saka da alkhairi.
Ya amsa da Amin kana suka yi sallama, Zayyad ya sauke ajiyar zuciya fatansa ayi bikin nan lafiya duk da yana da labarin faruwar matsalolin auren Safna na baya, hakan bai taɓa sashi fargaba ba dan yasan matar mutum kabarinsa, kuma yasan tana da matsalar jinnu basu ɓoye masa ba, fatansa dai Allah yasa zasu barsu su zauna lafiya, yadda yake matuƙar ƙaunarta baya jin akwai abinda zai hanashi kawo Safna gidansa, ji yake tamkar bai taɓa aure ba akan ta ne zai fara, ƙarin farin cikinsa yadda Rashida ta bashi haɗin kai da goyon bayan auren, shiyasa ya samu natsuwa yake gudanar da komai cikin kwanciyar hankali. Sai gabda magrib suka rufe shago ya shiga mota ya kamo hanyar gida.
Daya ƙaraso ya yi hon mai gadi ya buɗe masa ya shiga yayi parking yara suka rugo da gudu suka yi masa oyoyo tare da wasu yara su biyu maza baƙin fuska, ya kama hannun Aslam suka shiga falon, ga tv nan a kunne suna kallon wani tasha da aka sanya waƙoƙin Hausa sun cika volume ɗin ko sallamarsa basu ji ba, ganinsa ne yasa Anisa ƙanwar Rashida tayi saurin rage volume, Anty Wasila data rashe a ƙasa shirim ita ba kaɗan ba tayi saurin jawo ɗankwali ta ɗaura ta gaishe shi, ya amsa tare da yi mata sannu da zuwa dan ya shaidata yayar Rashida ce, ɗiyar wan mahaifinsu wacce mahaifiyar Rashida ta riƙe bayan rasuwar mamanta, Anisa ma ta gaishe shi ya amsa yana cewa.
Ganinki sai an cika form kin yi mata ƙaura a gidan nan kamar munyi miki laifi.
Makaranta ne ya ɓoye ni amma yanzu munyi hutu sai ka gaji da ganina. Tun ɗazu naso kiranka nace nazo gidanka ka tawo mini da abin daɗi dan nasan shagonka baya rasa kayan ciye ciye.
Da kin kira da na riƙo miki biscut, yasu mama da fatan kowa lafiya.?
Lafiya ƙalau.
Ta bashi amsa sai ya wuce zuwa ɗakinsa, ya soma rage rigar jikinsa sai ya isa gurin da yake aje flaks ɗinsa na ruwan zafi ya ɗaga yaji babu komai a ciki, yaja guntun tsaki ya koma ya zauna, shuru shuru yana jiran Rashida ta shigo bata shigo ba, dan lokcin daya shiga falon bata nan amma yasan zuwa lokacin tasan ya dawo.
Rahma Kabir ce, da fatan zaku sake bina a cikin wannan tafiya mai sabon salo. Ina uwargida da amarya da masu shirin shiga daga ciki wannan ma tafiyarku taku ce, akwai sirrin zamantakewa da yawa a ciki kar ku bari a baku labari.
Part 2
AMARYAR ZAYYAD
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 2
Har aka kira sallah Rashida bata shigo ba, ƙarshe Zayyad bayi ya shiga yayi alwala ya fito zuwa masallaci nan ya sameta zaune a cushing suna zuba uban hira, tana ganinsa ta ce masa sannu da zuwa yayi kamar bai ji ba ya fice zuwa masallaci, da guntun tsaki Rashida ta bishi tana duban Anty Wasila.
Bari ya dawo za kiji ya rufeni da ƙorafi, tunda ya ɗauko zancen auren nan komai nayi ban iya ba.
To kema banda abinki ai duk maza haka suke, da zarar zasu ƙara aure sai sun sauyawa mace sai dai haƙuri, bari muyi sallah sai mu ɗaura hirar kar ya dawo ya samemu.
Ta faɗa tana miƙewa, nan duk suka miƙe suka faɗa bedroom ɗinta dan yin alwala.
Zayyad koda ya dawo daga masallaci ya tadda falon ba kowa, hayaniyarsu Ilham yake ji daga ɗakinsu, hakan yasa shi wucewa kitchen ya saka ruwa a kettle ya jona a wuta sai ya koma ɗakinsa ya zauna yana danna waya, sai ga wayar Safna ta shigo ya ɗaga yana cewa.
Amaryar Zayyad da fatan yau baki fushi da ni ba.
Taya zanyi fushi da Sirrin Ruhi da fatan kana lafiya, yasu Ilham.
Lafiya lau Alhamdulillahi. In Sha Allah nan da anjima kaɗan zaki ganni ki tanadar miji abu mai daɗi dan nasan baki rasawa.
Dariya tayi tana cewa.
Kamar ka san akwai abinda na ajiye maka amma sai kazo zaka gani.
Haba matar ki ɗan bani satar amsa mana.
Naƙi wayon sai dai kazo.
Murmushi yayi mai sauti yana sauke wayar tare da duban ƙofarsa da aka murɗa ba a shigo ba, Rashida ce zata shigo amma data ji yana waya sai ta tsaya tare da jin wani ƙululun baƙin kishi ya tokare mata maƙoshi, amma sai ta shanye shi bayan ta haɗiye miyau mai ɗaci ta turo ƙofar ta shigo, kallon kallo suka yiwa juna fuskar ko wanne ba yabo ba fallasa, ta ƙaraso kusa da shi tana cewa.
Sannu da zuwa Abban Ilham ka shigo ɗazun ina bayi dana fito kuma na sha’afa muka shiga hira.
Ai dole ki manta dani tunda yanzu na zama mara amfani a gurinki kin daina sona.
Ya faɗa yana tsuke fuska, Rashida ta saki wani lallausar murmushi mai cike da ma’anoni da yawa.
Ni ɗin banza na da zan daina sonka, kaima kasanni da yawan mantuwa.
Eh hakane, amma Rashida meyasa kullun sai na tuna miki ki riƙa duba flaks ɗina in ba ruwa a ciki ki saka saboda inna dawo bana son jiran ruwan wanka.
Mantawa nayi kayi haƙuri.
To shi kuma singilet da ƙananun wanduna na da suka taru a bayi nace ki wanke su meya hana ki wankewa? Ke kullun sai an tuna miki abu, haka fa kwanaki sai da na rasa wanda zan saka a jikina ƙarshe fita nayi na siya wasu, bafa wanke kayana na tilasta miki ba bayarwa nakeyi a wanke, waɗannan ganin ƙananu ne basu dace a bayar wanki ba na ce ki riƙa wanke su amma abu ya faskara.
Kaima kasan aikin gidan nan yayi mini yawa sannan nayi niyyar wankewa yau, zuwan Anty Wasila ya sa namanta amma gobe In Sha Allah zan wanke.
Allah ya kyauta.
Ya ammata ransa a dagule, Rashida ta yi shuru ta kasa magana tana sosa ƙeya, Zayyad ya ɗago kansa yana dubanta.
Ehen ki daɗi abinda ke ranki.
Dama hmmm me zan dafa maka ne? mu taliya muka dafa na manta ban kira na tambayi me zaka ci ba.
Innalillahi wa inna ilaihir raji’un! Kullun na dawo sai kin tare ni da abinda sai ya ɓata mini rai, yanzu fisabillahi sai na dawo daga aiki ne za a riƙa ɗaura tukunyar abincin da zanci a gidana, duk yunwar dana kwaso saina jiraki kin dafa, wannan matsalar tun kina amarya har yanzu kin kasa gyarawa, duk tsananin son da nake yi miki amma a hankali kinata rage ƙimarki a idona Rashida.
Dan Allah kayi haƙuri yanzu zan dafa ka faɗi me kake so.
Ta faɗa cikin muryan tausayi kamar zata yi kuka. Miƙewa Zayyad yayi ransa ba daɗi dan har idonsa ya sauya zuwa yin ja.
Tabbas ba zaki sauya ba saboda tsawon shekara takwas kenan da aurenmu amma lamarin bai sauya zani ba, Allah ya shirye ki. Amma ina buƙatar wacce zata kula da rayuwata ba dan bana sonki ba, ina fatan zuwan Safna gidan nan ya sauya mini ke.
To ai nima ina maraba da zuwanta Allah ya bamu zaman lafiya Alh. Zayyad.
Ta ambata cikin miskilin murmushi wanda kuma zuciyarta cike yake da zazzafar ƙuna, jikin Zayyad yayi sanyi yana dubanta tare da cewa.
Allah ya gani ina iya ƙoƙarina da haƙuri dake amma naga duk a banza baki gani, kuma ni auro Safna da zanyi ba zai taɓa sanyawa na sauya miki ba domin kece tauraruwata, ina sonki har gobe.
Sauke ajiyar zuciya Rashida tayi sai ta juya ta fice daga ɗakin dan ji take yi kamar ta kurma ihu, zuciyarta a karye yake zata iya yin kuka kota faɗa masa maganar da zai iya dagula musu lissafi, kuma bata so ya gano logonta, Zayyad ya bita da tsantsar tausayawa banda yana matuƙar kaunar Safna da zai iya fasa aurenta, amma bazai iya ba domin Safna wani ɓangare ne na rayuwarsa, yana matuƙar mamakin ma yadda a ‘yan kwanakin nan yake jin son Rashida yana niman dagula masa lissafi sai dai ya bayar da tausayinta da yake ji ne saboda yadda ta nuna dangana da danne kishinta tare da juriyarta akan auren. Falo ya fito ya samu Anisa da su Ilham suna kallo ya wuce Kitchen ya juye ruwan butan da yayi zafi kana ya mayar da wani ruwan ya ɗauki wanda ya juye a bokitin fenti ƙarami ya wuce ɗakinsa. Toilet ya shiga yayi wanka sauri sauri ya fito ya shirya cikin baƙar jallabiya da wando jins ya feshe jikinsa da turare tare da gyara sumarsa na kai dana gemu, sai ya ɗauki flaks da robar fentin ya koma kitchen ya tadda ruwan yayi zafi sai ya juye a flaks ya ɗauka ya mayar ɗakinsa ya ɗauki key, dama wayarsa yana aljihunsa ya fito ya rufe ɗakin da key ya fice abinsa Anisa tana yi masa tsiyar tasan zance zai je ya gaishe da antinsu. Yana fita sai ga Rashida ta fito falon ita da Anty Wasika sun zauna tana kumbure kumbure, Anisa tace.
Ke ya barki da ƙunan zuciya yayi ficewarsa zuwa ga Amaryarsa, wlh ki watsar da shi ki cigaba da lamarinki, shi namiji in kika saka shi a rai sai ya ɗaura miki hawan jini a banza.
Gaya mata dai Anisa, ke gashi baki yi aure ba amma kinsan wannan balle ita, ki cigaba da danne kishinki harta zo a goga ai naji daɗin da zai haɗaki gida ɗaya, kinga sai kuyi zaman kowa ta iya allonta ta wanke, karki yarda wata banza can tazo ta kwace miki miji kina ji kina gani ki zama ‘yar kallo.
Anty ya zanyi? Ƙorafin Zayyad yayi yawa duk ƙoƙarin da nake yi akansa baya gani dan kawai ban yi masa girki ba, shi komai a gunsa ƙorafi ne baya min izuri.
Ki rabu da shi Allah ya nuna mana auren lafiya muga amayar da wacce zata zo.
Nan suka cigaba da hirarsu wanda gabaɗaya ɗebewa maza albarka suke tayi, dama a nan zasu kwana da yawan ‘yan uwanta in sun zo daga wani gari tofa sukan yi kwanaki a gidanta saboda suna samun kayan daɗi da abinci waja waja. Ita Anty Wasila goɗai goɗai da ita gata yaya ce amma haka take shafe kwanaki a gidan in tazo garin, shiyasa Zayyad har ya fara rainawa ‘yan uwanta saboda yadda suke nuna kwaɗayinsu a fili, ƙarin haushinsa muddun in suka zo haka Rashida take banzatar da lamarinsa ta mayar da hankalinta kacokan kansu bata damuwa da buƙatunsa.
Mahaifinsu Zayyad mai suna Ahmad ya rasu sai Hajiyarsu Halima wacce ‘yarsa ilham taci sunanta, Aslam kuma yaci sunan babansu Ahmad, yana da yaya mace Bilkisu suna zaune a Abuja da mijinta Kamaluddeen yaransu huɗu, sai Zayyad sannan Asiya wacce itama tana aure a malali yaranta biyu, sai Mukhtar da yake karatu a KASU.
Ɓangaren Rashida kuma ita ce ta biyu a gidansu, tana da wa Salis, sai Rashida, sannan Haruna sai Anisa sannan Zaliha, ita Wasila yarinyar yayan babansu ce amma a gurin mahaifiyarsu Rashida ta tashi shiyasa suka taso tamkar uwa ɗaya uba ɗaya.
Zayyad da Rashida auren soyayya suka yi kuma Alhamdulillahi a wancen lokacin sun samu fahimtar juna, yaransu biyu Halima (Ilham) ‘yar shekara bakwai sai Ahmad (Aslam) ɗan shekara Huɗu. Babban saɓanin da suka fara samu shine yadda Rashida take da mugun kuiya musamman a gurin yin girki, ta mayar da Zayyad tamkar gauro mara mata kullun abincinsa yana waje, dan sai yafi sati bai ci abincin gidansa ba saboda sakacinta, musamman in ya dawo bata gama ba zai fice yaje rastuarant ko yaje gidan mahaifiyarsa yaci saboda baya ƙaunar jira dan ba yi da juriyar yunwa. Idan kuma aka ce watan azumi ya kama to dama baida abun buɗe baki a gidansa, saboda kwata kwata Rashida bata mayar da hankali ta fara aiki da wuri balle a samu ta gama aci akan lokaci, hatta yaranta tana horar dasu da yunwa tsabar kuiya da yayi mata yawa, ga rashin bawa shinfidarsa muhimmamci saboda shegen saurin barci gareta duk inda aka ce goma tayi to tana nan ta hangame baki ta soma barci, sai ya dawo daga inda yaje bata san ya shigo ba, haka yake yawan azumin litinin da alhamis yana ragewa kansa zafi saboda marabarshi da mara mata abu kaɗan ne. Tarin matsalolinta ya sashi soma kule kulen mata a waje musamman waɗanda suka haɗu a shafin sada zumunta na facebook da Instagram, badan yana sha’awar ƙara aure ba sai dan kawai ya riƙa samun in da sai rage lokaci kafin dare yayi ya shigo guda, ko kuma in ya dawo haka zai ɓata lokaci yana chart da ‘yan mata kala kala tun baya kauce hanya har ya fara biyewa suna irin hirar nan na batsa, duk da shi mutum ne mai matuƙar tsantseni da aikata zina, sharholiyarsa a iya waya yake yi shima bai yarda da tura hotunan tsiraici ba sai dai zantukan batsa dan ragewa kansa zafi. Hakan yasa ya haɗu da wasu natattun ‘yan mata su biyu Zubee da Seema, da yake su yan hannu ne babban burinsu shine su samu damar da Zayyad zai kwanta dasu, duk da suna kawaye amma basu damu ba ko kishin junansu ba tunda rayuwa ce ta bariki.
Matsalolin Rashida sune suka jawo rashin jituwa a tsakaninta da ‘yan uwan Zayyad, tun yana ɓoye damuwarsa har sai da Hajiyarsa tazo ta sani, ita da kanta tasha zuwa tana bawa Rashida shawarwari akan zamantakewa dan ta gyara, saboda tana son Rashida kuma ita irin surukan nan ne masu sauƙin kai da hali sam ba tada takurawa matar ɗanta, amma baisa Rashida ta karɓi gyara ba sai tayi biris da shi taga kamar ma takura mata take son yi, gata sam ba tada kunya bata tauna magana kafin ta yi shi wannan yasa zamansu ya koma zaman haƙuri duk kuwa da irin son da Zayyad yake yi mata bai taɓa tunanin ƙara aure ba a ganinsa har da ƙuruciya zata gyara.
Sai dai kuma tun sa’ilin da yayi tozali da Safna ya kamu da zazzafar soyayyarta yaji yana buƙatarta a cikin rayuwarsa, shiyasa ya yi ƙoƙarin samun zuciyarta har suka kawo gaɓar yin aure, hakan yasa shi ya ja baya da ‘yan matan da yake kulawa a shafin sada zumunta ya mayar da hankalinsa kan Safna kawai. Batun gidansa kuwa dama tuntuni yaƙi mayar da hankali ya gyara side ɗin dake cikin gidansa, wanda a da niyyyarsa zai saka ‘yan haya in kuma ƙaninsa Muktar ya kawo munzalin aure ya tayar da ‘yan haya ya aje matar a ciki, sai gashi ashe da rabon Amaryarsa ce zata tare a ciki, shiyasa ya mayar da hankali har sai da ya kammala gyaran.
Lokacin daya nunawa Rashida zai ƙara aure sam bata ɗauki lamarin da gaske ba, dan tasan yana matuƙar son ta saboda da zai yi mata kishiya da tuntuni yayi irin yadda mutane ke zugashi, amma data ga da gaske ne sai ta kwantar da kanta bata ɗaga masa hankali ba dan tasan tunda yayi niyya sai yayi, kawai dai fargabanta kar ya auro wacce zata kwace mata shi, shiyasa tayi yadda zata yi ta shigewa Safna a jiki dan tasan wacce irin mace Zayyad zai auro mata, tayi sa’a Safna tana da sauƙin kai tana matuƙar girmamata, suna yin waya da chart a tsakaninsu, wannan yasa sosai Zayyad yake ganin zasu samar masa da zaman lafiya a gidansa kuma ba ƙaramin farin ciki yake yi da haka ba, shiyasa yake ƙara kyautatawa Rashida duk abinda tace tana so sai yayi mata domin ya sata farin ciki, amma kuma duk a banza dan har yau ba sauya halinta tayi ba tana cigaba da yi masa riƙon sakainar kashi wanda hakan ke ƙara tunzurashi da ya auro Safna.
*
Gidansu Safnah.
Zayyad yana isa gidan yayi parking yana fitowa sai ga Yaya Mudan ya fito zai je siyo abu, ya isa gabansa suka gaisa kana yace ya shiga cikin gida bari ya kira masa ita, Zayyad yayi masa godiya tare da bin bayan Mudan daya nufi cikin gida, sai da ya fara ɗauko masa tabarma ya shimfiɗa a simintin tsakar gida daga gefe, kana ya shiga kwalawa Safna kira ta amsa daga cikin falo.
To ki fito ga mijinki ya zo, gashinan a tsakar gida.
To tace masa kana ya fice ya nufi inda zashi, ba jimawa Safna ta fito cikin dogon Hijab riƙe da tire a hannunta da jug da kofi biyu akai sai gorar ruwan swan da kuma plate an rufe shi da ɗan uwansa plate.
Rahma Ce.
Ban yarda a juya mini labari ba ko ayi afmani da wani ɓangare na labarin ko kuma satar fasaha, ko a mayar mini da shi Audio a ɗaura min shi a wata kafa na media ba tare da izini na ba, sannan ina gargaɗi ga masu cire sunana a cikin labarina su saka nasu tare da sakinsa a shafinsu, ban hanaku ɗaura labarina ba amma a barmin sunana tare da barin rubutuna yadda yake, da fatan za a kiyaye
Part 3
AMARYAR ZAYYAD
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 3
Safna ta aje tiren a gabansa kana ta zauna nesa kaɗan da shi tana cewa.
Amincin Allah ya tabbata a gareka Sirrin Zainab.
Ameen Wa Iyyaki. Ya mutanen gidan.
Alhamdulillah duk kalau suke.
Masha Allah! Amma kafin mu kai ga hira, ki fara gabatar mini da abinda kika tanadar mini cikina ya ɗauka tukuna.
Murmushi tayi wanda yasa kumatunta lotsawa dimple, tare da matsawa gabansa ta buɗe plate ɗin Samosa data soya shi ɗazun, Zayyad tun kafin tace masa gashi yayi saurin zura hannu a ciki ya ɗauka ya kai bakinsa ya fara ci, yana irin santin nan da mirgina kai dan yayi masa matuƙar daɗi, Safna dai murmushi kawai take zuba masa kana ta ɗauki kofi ɗaya ta shiga tsiyaya masa kunun madara, Zayyad ya yi saurin katse ta da cewa.
Meye wannan kuma ko yoghurt ne?
Sha dai kaji?
Ta faɗa tana miƙa masa, Zayyad ya amsa tare da kai kofin bakinsa ya kurɓa, wani irin garɗin daɗi ne ya shammaci maƙogoronsa bai san sanda ya kafa kofin a bakinsa ba ya shiga kwankwaɗa, sai da ya shanye kafin ya cire kofin yana sauke ajiyar zuciya mai ɗumi, ya kalli Safna cike da tsantsar ƙauna.
Allah yayi miki albarka, yadda kika faranta mini ubangiji ya faranta miki sannan ya cika miki burinki na mallakar Zayyad.
Wannan karan dariya ne ya kubce mata ta shiga yinsa a hankali sautin yana fita.
Ya baki ce Amin ba kina min dariya.
To ai gani nayi kamar sai an sanya maka waigi, wannan irin santi kamar ance maka ga Safna a cikin gidanka an baka halak malak.
To me ya rage nan da wasu ‘yan kwanaki ƙalilan ne komai zai tabbata har abada. Amma batun gaskiya ko miye wannan abun ya mini zallar faɗi, na dai san an saka madara dan ƙamshinsa ke dukan hancina, amma me kyau ki faɗa mini me kika bani ne haka mai daɗi?
Wannan shi ake kira da kunun madara, kuma shi kasha.
Wow amma gaskiya ya kayatar da ni, ban taɓa shansa ba amma ki tabbatar in kinje gidana zaki cikani da salo salon girkinki Ruhieee.
Ya yi maganar yana jan ƙarshen tare da lumshe ido yana saka hannu a gefen zuciyarsa, sosai Safna ta saki dariya, nan dai suka cigaba da hirarsu gwanin sha’awa har misalin ƙarfe tara da rabi kafin suka yi sallama, amma fa saida Safna ta kakkaɓe masa duk wani damuwar da yazo dashi kafin suka rabu ya nufi gidansa cike da bege da ƙosawar son kasancewa da ita.
Ko da Zayyad ya isa gida ya tadda kayan kallo a kunne kitchen a buɗe amma ba kowa a falon, ga plate ɗin abinci da suka ci suka barshi a falon banda ƙamshin taliyar manja babu ƙamshin dake tashi, haka ya kashe soket ya jawo ƙofar kitchen kana ya wuce ɗakinsa, ya cire jallabiyar ya rage ƙananun kaya ke jikinsa ya kwanta tare da jan bargo ya rufe ƙafafunsa, Safna ta riga ta cika masa ciki baida buƙatar abinci, kuma da yake yasan halin matarsa bata girka masa komai ba, da zai kirata ya tambayeta zata ce ta manta, guntun tsaki yaja ya kunna data ya fara duba WhatsApp domin ganin saƙonninsa, dama time ɗin chart ɗinsa kenan dan inya fita aiki ba yida lokacin waya saboda hidima da mutane, nan saƙon Safna ya shigo tana cewa.
Allah yasa mijina ya sauka gida lafiya.
Sai da ya saki murmushi kafin ya bata amsa da lafiya lau sai dai yaga bata online, nan ya fito ya shiga duba saƙonni nan ya samu Seema tana online, sai suka fara chart daga nan kuma suka cigaba da hirarsu na sakin layi, haka ya shagala har kusan sha ɗaya da rabi, ya ce mata zai sauka barci zai yi suka yi sallama tana yi masa mitar itafa ta gaji da ja mata rai da yake yi ya kamata yazo su haɗu su jiyar da juna farin ciki, bai bata amsa ba ya sauka dan yasan ba zata taɓa samun wannan damar ba yana matuƙar kyamar aikata zina, wannana chart ɗin da suke yi shima so yake ya yakice shi ya huta tunda Safna tana gabda shigowa gidansa, Zayyad barci yake ji amma kuma cike yake da buƙatar mace a wannan lokacin musamman yadda yasha kunun madara ya tada masa da maitarsa, dan shi da zarar yasha madara da dare ko yogot to tabbas sai ya motsa masa buƙatarsa, ya duba agogon wayarsa sha biyu saura nan ya shiga wajen kira ya lalubo number ɗin Rashida ya soma kiranta sai dai kash tasa wayar a silent ta saka a jikin chargy a wuta, sannan ma barcinta take yi hankalinta kwance dan tuni tayi nisa dan koda ya dawo tayi barci Anisa ce keta danne danne a waya tana chart, Zayyad sauke ajiyar zuciya yayi mai ɗumi ga mace har mace amma sam hoto ce bata damu da buƙatarsa ba sai nata, dan in abin ya motsa mata tasan ta jira shi ya dawo duk inda yaje, kota dinga kiransa a waya tana jiransa. Zayyad ji yayi kamar ya fashe da kuka ko hakan zai sama masa kwanciyar hankali amma koda yayi kukan ba zai yi masa maganin halin da yake ciki ba, sai ya sauka daga gado ya ɗiba ruwan flaks a marfinsa ya shiga shansa yana kurɓa a hankali har ya shanye farin ruwan ya rufe ya koma ya zauna yana mayarda gumi, daga haka kuma yaji sauƙin ƙullewar marar, sai miƙe ya kashe wuta ya koma ya kwanta ya rufa da bargo ba jimawa barci da ɗauke shi.
Washegari Zayyad sai da ya makara sallar asubahi dan wajen shida da kwata ya tashi, ba ɓata lokaci ya juye ruwan flaks ɗinsa yayi wankan tsarki dan jiya yayi makarfi bar katai kuma ikon Allah da Safna yayi saboda ya kwana da ita a ransa, daya fito wanka ya shirya ya gabatar da sallar asubahi a ɗaki ya cigaba da zama yana jan lazumi har gabanin ƙarfe bakwai, kafin ya kwanta a gado ya kunna data yana duba shafinsa na Facebook, bayi da sauran yin barci dan zai kai yara makaranta ga kuma yana so ya biya gidan mahaifiyarsa ya gaisheta kafin ya wuce shago. Yana a kwance yana jin hirarsu Rashida sai hidimarsu suke yi dan ba tashi take ba, yana matuƙar mamakin sakarcin Rashida tare da ganin wautar yayarsu da ba zata iya ɗaurata a hanya ta gyara ba, ya kula haka rayuwarsu take tun daga gida tarbiyyar da suka samu kenan, tsaki yaja yayi Allah ya kyauta a ransa kana ya sauko daga gado ya shirya cikin ƙananun kaya ya kimtsa ɗakinsa kana ya fito lokacin wajen ƙarfe bakwai da Rabi.
Ina kwana.
Anty Wasila ta ambata.
Lafiya kalau Alhamdulillahi kun tashi lafiya.
Ta amsa da lafiya lau, sai ya wuce zuwa kitchen dan can yaji motsin Rashida, Aslam ya isa ga Abbansa da gudu ya rungume shi yana cewa.
Abbanmu.
Na’am Aslam ɗin Abba, ya naga ba kuyi shirin makaranta ba ina Momynku?
Momy tace uniform ɗinmu yayi datti kuma bamu karya ba.
Ran Zayyad ne ya ɓaci sai ya saki hannun Aslam ya nufi kitchen ya shiga ya tsaya yana ce mata.
Rashida ya naga yaran nan basu shirya ba?
Abban Ilham ashe ka tashi, ina kwana?
Lafiya lau, ina tambayarki baki bani amsa ba.
Rashida ta shiga sosa ƙeya.
Dama uniform ɗinsu yayi datti ban samu damar wankewa ba na manta, amma yanzu nake shirin naje na duba in zai yuwu su saka haka in sun dawo na haɗa na wanke.
Amma nasan uniform ɗinsu kala biyu ne, kuma sun saka ɗaya shekaran jiya monday da jiya talata, yau laraba ya kamata ace ɗayan yana wanke sawa zasu yi tunda sau bibbiyu suke saka kayan friday su saka sport wear.
Wlh ranar Lahadi guda ɗaya na wanke da tunanin washe gari zan wanke ɗayan shiyasa.
Ta faɗa a sanyaye, Zayyad daga hannu ɗaya yayi ya dafe goshinsa dan tsananin takaici, ya sauke hannu yana hura iska mai ɗumi daga bakinsa ya girgiza kai ya fice, a nan ƙofar Kitchen ya tsaya ya shiga kwalawa yaran kira nan suka zo da sauri, ya dubesu.
Kunyi wanka?
Ba muyi ba dama sai mun dawo makaranta muke yi.
Ok kuje yanzu ku sauya kaya masu kyau ku ɗauko jakunanku na makaranta ina jiranku a mota.
To suka ce masa suka isa ɗakinsu da gudu, Zayyad ya koma kitchen ya duba lunch box ɗinsu yaga an aje a gefe ba a jima da wanke su ba, ya isa ya haɗasu cikin kwandonsu ya ɗauka ya fice ya isa ƙofar ɗakinsa ya saka key ya juya ya fita daga falon, a mota ya jira yaran har suka fito suka shiga sai ga Rashida ta fito da gudu.
Abban Ilham basu karya ba ga arish ɗin na gama soyawa yanzu zan haɗa musu tea.
Bai kulata ba ya tayar da motarsa ya ja baya tare da buga hon mai gadi ya buɗe masa ya cilla motarsa waje ya hau hanya ya wuce, Rashida taɓe baki tayi tana jan tsaki ta koma ciki anty Wasila tana cewa.
Wai ke haka kuke rayuwa a gidan nan gabaɗaya bai ɗaukeki a bakin komai ba, anya amaryar da zai aura bata nima shiga tsakaninku ba.
Ke dai anty kya faɗa amma kuma yadda na karanci yarinyar tana da hankali da ilimi bana tunanin zata yi wani abu, halin namiji kawai yake gwada mini.
Amma wlh ke shashasha ce an gaya miki masu ilimin basa shagala ne to su suka fi iskanci ma, dan haka bana tantama yarinyar nan tana niman shiga tsakaninku Allah.
In tayi wani abu ma to kanta ta yiwa ba ni ba, dan Zayyad ɗin ban ɗauke shi a bakin komai ba, bai isa ya wulaƙanta ni ina kallonsa ba ni da shi kar tasan kar.
Allah ya kyauta ni in kin gama haɗa abin karyawa ki kawo muci dan cikina karta yake yi.
Anty Wasila ta faɗa tana yamutse fuska, Rashida tace.
Ai na gama bari na ɗauko.
Sai ta shiga kitchen ta cigaba da aikinta.
**
Zayyad rastaurant ya wuce da yaran ya yi parking suka shiga ciki, yasa aka haɗo musu breakfast mai kyau soyayyan arish da kwai tare da miyar albasa, sai ruwan lipton da kayan ƙamshi, nan suka ci suka ƙoshi daga bisani ya bada lunchbox ɗinsu aka zuba musu abinci jelop ɗin shinkafa da nama duka su biyun ya biya kuɗi suka fito suka shiga mota ya wuce dasu makaranta, ya kashe kusan dubu ashirin a wannan abincin da suka ci. Suna isa makaranta suka ɗauki kajunansu da kwandon abincinsu suka wuce ciki, office ɗin headmaster ya kaisu sun samu ba kowa a ciki sai shi kaɗai, yana ganin Zayyad ya miƙe suka gaisa dan sun saba da juna sosai, suka zauna sai Headmaster ya dubeshi yana cewa.
Ya naga ɗalibanmu da kayan gida Allah yasa lafiya.
Malam kayan nasu ne an wanke musu basu bushe ba, shine naga da suyi fashin makaranta gwara na zo dasu na siya musu wasu, Allah yasa akwai uniform a ƙasa.
Akwai su ai bama bari su yanke saboda masu siye da sabbin shiga. Ina zuwa.
Headmaster yace tare da miƙewa ya shiga cikin wani ƙaramin ɗaki dake cikin office ɗin ya duba uniform ya ciro musu size ɗinsu, nan ya miƙa masa yana cewa.
Gashi nasan zasu yi musu ita bata wuce shekara takwas ko? shi kuma biyar.
Basu ma kai ba, tsayin ƙafa garesu amma wannan zai yi musu.
Cewar Zayyad yana ɗaga kayan yana dubawa, nan ya umarci yaran su cire kayansu su saka uniform ɗin, ba musu suka yi tuɓe suka saka yace su ɗauki jaka da abincinsu su wuce class, suka yi masa bye bye suka fice nan Zayyad ya biya kuɗin uniform suka yi sallama da headmaster kana ya fito ya shiga motarsa ya nufi gidan Amminsu.
Yana shiga falon gidansu ya samu Hajiya zaune a carpet tana ta aikin ɗura dambun Nama a robobi, ta amsa masa sallama tana cewa.
Dan halak kaƙi ambato, yanzu nake zancen Muktar dole ya jira na gama sakawa ya kai muku shago daga can ya wuce makatanta.
Ai tunda nazo sai yayi tafiyarsa. Ina kwana Ammi kun tashi lafiya.
Lafiya kalau Alhamdulillahi ina mutane na su Ilham da fatan kowa lafiya.?
Alhamdulillah yanzu na sauke su a makatanta.
Haba Zayyad meyasa kuke barin yaran nan suke lattin zuwa makaranta, wannan zai iya saka karatunsu yayi ta baya.
Ya zanyi Ammi kema kinsan halin Rashida ba sai na faɗa ba.
Nan ya kwashe komai daya faru da safen ya faɗa mata, Ammi ta girgiza kai tana cewa.
Allah ya kyauta ya shiryata, dama shi mugu bazai cika mugu ba sai yayiwa kansa mugunta, gashi duk abinda take yi ya fara shafar rayuwar yaranta. Shiyasa nake fatan Safna ta shigo ta kula da kai kota fannin Abinci ka huta da zaryar Rastuarant.
Allah yasa mu dace, ashe kinyi dambun naman, kwana biyu masu saye suna ta tambaya.
Ai jiya nace bari na ɗaure nayi nasan za ayi ta tambaya, to jikin namu ne na tsufa yau lafiya gobe ba dama.
Hakane Allah ya ƙara afuwa, Ina Salame mai aikinki bata nan ne?
Ta tafi kula da ‘yarta data haihu, shiyasa aikin ke mini yawa amma tace cikin kwanakin nan zata dawo.
To Ammi ko za a sake samo wata ne su zama su biyu.
A’a itama ta wadatar kuma ai yanada kyau ina motsa jikina. Matso kusa ka zuba dambun a leda roba saba’in ne ba sai ka sha wuyar ƙirgawa ba.
To yace mata ya matso yana sakawa a katon leda.
Part 4
AMARYAR ZAYYAD
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 4.
Sai ga Mukhtar ya fito daga ɗakinsa yana ganin Zayyad ya washe baki yana cewa.
Yauwa shikenan ma bari nayi fijo na wuce inda nafi wayo. Yaya Zey zan samu wani ‘yan chanji a gunka? kasan gaye ba kwabo yawane.
Nan kafi auki ai, kana gama karatun nan shago zan buɗe maka ka fara sanin yadda ake kasuwanci kasan muhimmamcin kuɗi.
Dako ka kyauta Zayyad, dan kam wannan shiryayyen in ba anyi masa da gaske ba malalaci zai zama.
Haba Ammi jifa yadda na tara kwanji, ai ko yanzu zan iya saɓa yaya a wuya nayi yawo dashi saboda ƙarfina.
Zayya ya ɗauki ludayin da Ammi ta gama amfani dashi ya wurga masa, Mukhtar yayi tsalle ya koma gefe yana kwasar dariya suma dariyar suke tayashi, Zayyad yace.
Allah ya shiryeka kowa ma ka mayar dashi abokin wasanka. Ga dubu biyu nasan zata isheka fafa.
Yasin tayi mini kaɗan, ina laifin ka bani dubu biyar a matsayina na autan marigayi Alhaji Ahmad da Hajiya Halima mai dambun nama, ƙanin Bilki da Zayyad da kuma Asiya.
Innalillahi! Muktar Allahu yahadika.
Cewar Ammi tana murmushi, Zayyad ko murmushi shima yayi yana girgiza kai dan ƙanin nasu in dai wajen barkwanci ne lamba ɗaya yake, ya ƙara masa dubu uku ya zama dubu biya ya amsa yana godiya.
Zaka yi Albarka dan gidan Ammi In Sha Allah, Allah ya kawo Anty Safna gidanka lafiya muci rayis.
Yana gama faɗar haka ya fice yana kwasar dariya, suma dariyar suka yi suna yi masa fatan shiriya.
Ammi ta miƙawa Zayyad wani robar takeway.
Ga naka sai ka aje kaci abinka a hankali harya ƙare.
Yauwa nagode, a office ɗina zan aje shi dan inna je da shi gida sai dai naga robar a bola, amma wannan baiyi mini yawa ba? kar in karya jalin.
To Zayyad in ka cinye kaine mai bayarwa, sannan ma Alhamdulillahi na fidda uwar kuɗi da riba. Ɗazun nayi waya da Kamal yace mini jibi Juma’a zai zo.
Eh munyi waya jiya, amma kinyi magana da Yaya Bilki yaushe zata zo ita.
Wai in biki saura sati biyu, zasu fara sauka a gidansu can daga baya su dawo nan ayi bikin.
Allah ya kaimu.
Zayyad ya ambata, Ammi tace amin suka cigaba da tattauna yadda suke fatan bikin ya kasance.
Safna.
Tana zaune a ƙaramar kujera tana wanke wanke sai ga Haajara ta shigo gidan da sallama, da murmushi kan fuskar Safna tace.
Sannu da zuwa ƙawalli na ɗauka sai anjima zan ganki.
Ke gwara na fito kafin rana tayi zafi na kasa fitowa, kin san na fara zama ajebo.
Eh ba shakka ɗan baba ya fara mulki dai, ya nauyin jiki.
Alhamdulillahi, umma fa?
Cewar Haajara tana waige waige, Safna ta sanar da ita taje islamiyya ita ce kawai a gidan kowa ya fita sabgarsa, nan ta zame hannunta a ruwan wanke wanke ta shiga kitchen ɗin tsakar gida ta ɗauko mata kujera ta aje a innuwa tana cewa.
Bisimillah, ina kwana ya Amir da mai gidanki.
Lafiya lau, Amir yana gidan Mamanmu yaje hutu.
Kice ke kaɗai ce a gidan kina buga sarauta.
Ya son ranki Amaryar Zayyad, ya shirye shirye? Wai menene sirrin dana ga kinyi wani kyau kin ciko kamar ba amarya ba, ko ramar fargaba ban gani ba a tare da ke, ga ƙirjinki sunyi Masha Allah kuma keda na sani ba abin ‘yan fiƙil fiƙil.
Dariya Safna tayi mai sauti tana wanke tukunyar data rage bata wanke ba tace.
Ba zaki gane ba madam, an gaya miki haka zanje gidansa kamar wacce aka yiwa aure dole, komai fa sai da gyara aka ce in kana da kyau to ka ƙara da wanka, Sabayar Maman Khadija na siya ya zama abincina na safe da yamma shine yasa na ciko nayi ɓulɓul sannan fatata tayi kyau da sheƙi
Haajara ta tafa hannu cike da farin ciki tana cewa.
Habawa shiyasa gabaɗaya naga kin sauya ƙawata kinyi kyau sosai Tubarakallah, lallai nima zan nima nawa kar a barni a baya.
Ki bari ki juye sai kiyi gyaran da hujja, dan kin san yanzu kin fara nauyi bata gyara zaki yi ba, ta kula da tarbbiyar abinda ke cikinki za kiyi.
Hakane kuma.
Cewar Haajara, nan suka cigaba da hira har Safna ta gama aikinta ta tattare tsakar gidan suka shiga ɗakinta suka yada zango, zancen dai na maganar biki ne, har Safna ta sako mata labarin matar Zayyad, Hajara ta riƙe haɓa.
Ikon Allah, wlh ta burgeni da haka mata suke sauƙaƙa kishi da an zauna lafiya, amma fa ni bazan iya ba kin sanni da zafin kishi.
Niko wlh zan iya, ai yadda Rashida ta nuna mini ya tabbatar mini da za muyi zaman lafiya.
Allah yasa.
Cewar Haajara, Safna tace amin suka cigaba da tattaunawa. Hajara ita ce aminiyar Safna dan tare suka yi makarantar boko har zuwa poly, sun shaƙu sosai tamkar ‘yan biyu duk inda zaka ga Safna to zaka ga Hajara, duk da unguwar su ba ɗaya ba saboda ita Hajara suna ɓangaren geto ne, ita kuma Safna suna GRA, Haajara tayi aure shekara biyu da suka wuce har ta haihu ɗaya Amir yanzu ga cikin na biyu nan kuma duk da tayi aure ba abinda ya taɓa zumuncinsu, suna shawara da juna duk abinda ya shigewa junansu duhu.
Sai bayan La’asar Haajara ta tafi akan sai biki ya rage sati guda zata kuma zuwa taji ya lamarin bikin zai kasance, har titi Safna ta rakata cike da kewar juna suka rabu.
**
Zayyad.
Sai dare wajen sha ɗaya ya dawo gidan, saboda ya biya ta gidan Hajiya sai wajen ƙarfe goma ya baro can, daga bisani ya tsaya shagon abokinsa Saminu tela da yake yin dinkin maza, nan ya ƙarar da sauran lokacin kafin ya nufo gida, falon suru ba kowa hakan ya bashi damar dafawa kansa ruwan wanka yayi kana yabi lafiyar gado ya kwanta. A da yayi niyyar share Rashida amma kuma in yayi haka shine zai cigaba da cutuwa, sannan a wannan gaɓar dole ne yayi mata uzuri ya cigaba da lallashinta tunda laifi zaiyi mata na ƙara aure, sosai maganar Saminu Abokinsa ya tsaya masa a rai da ya bashi shawarar akan ya yi haƙuri ya cigaba da yi mata uzuri tunda har ta iya kwantar da hankalinta bata yi wani abu da zai ɗaga masa hankali ba da ƙarin aurensa, hakan ya sashi sauke gauron numfashi ya dubo number ɗinta ya kirata sai dai bata ɗaga ba, duk da haka bai yi ƙasa a guiwa ba ya sauko daga gado ya nufi ɗakinta ya kwankwasa, ganin shuru ba motsi ya sashi tura ƙofar ya samu tayi ɗai-ɗai tana barci kuma basu Anty Wasila ashe sun tafi ma bai sani ba, ƙila shiyasa tayita kiransa da rana shi kuma saboda haushin abinda tayi masa yasashi ƙin ɗauka, ganin ita kaɗai ce sai ya juya ya wuce ɗakin yara nan ma su biyu ne sunata barcinsa, ya shiga ya gyara musu kwanciya tare da tofa musu addu’a ya kashe wutan ɗakin ya fito ya rufe ƙofar ya koma ɗakin Rashida wacce tun sa’ilin daya buga ƙofar taji amma ta share shi dan yayi mugun ɓata mata rai ɗazun daya ƙi ɗaukar wayarta, ya tura ƙofar ya shiga ya rufe sai ya kashe wutan ya haska da hasken wayarsa ya ƙarasa gadon ya kwanta tare da matsawa kusa da ita ya rungumeta ta baya, kiciniyar kwace kanta ta shiga yi ya saki murmushi.
Dama kina jina kika yi min banza ko.
Ni ka cikani barci nake ji, ko kuma ka jira zuwan amaryarka da zata zo ta kula da kai tunda ni ban iya komai ba.
Kema kinsan duk wata mace a bayanki take sai dai yadda kike hukuntani yana sa mini karaya sosai a zuciyata, sai nake ganin kamar hukunta ni kike yi a fakaice ba tare da kin fito kin nuna zafin kishinki akan auren da zanyi ba.
Haka dai kake gani, amma kasan da zan ɗaga maka hankali da tuntuni nayi, kuma Safna a matsayin ‘yar uwa na ɗauketa duba da yarinya ce mai hankali da tarbiyya.
Gaskiya ne Allah ya ƙara haɗa mini kanku, yanzu dai kin huce ko?
Zan dai huce.
Ta faɗa a dakile, murmushi yayi ya fara yi mata cakulkuli tun tana ture hannunsa har sai da ta saki dariya, daga haka kuma ya sauke nauyin daya kwana biyu bai sauke ba, duk da ba wani dogon kulawa da take bashi yawancin ma nuna ƙosawarsta take yi ayi a gama dan ta gaji, ya saba da haka shiyasa bai wani damu ba, a daren ya tsarkake jikinsa dan yana fatan gobe Alhamis ya tashi da azumin nafila daya zame masa jiki.
Tun daga lokacin Zayyad ya cigaba da lallaɓa Rashida yana haƙuri da jure duk wani shirme da take yi masa, sannan baiyi ƙasa a guiwa ba yana yi mata duk abinda tace tana so daga kuɗi har abin kuɗin, dan hatta ankon Safna data nuna masa ya siyo mata ta bada ɗinki, sannan ya kawo mata akwatin faɗar kishiya kamar yadda yayi niyya guda biyu da kit ya saka kaya masu kyau dai dai ƙarfinsa, suma yara yayi musu ɗinki kala uku uku da takalmi. Duka ɓangarorin shirye shirye suke yi ba kama hannun yaro, dan har an kai akwatin Safna guda huɗu da kit kuma yaji kaya na zamani Masha Allah, sai dai angon da gani yana da kishi dan yaƙi sanya gyale ko ɗaya duka manyan hijabai ya saka, Safna bata damu ba dan bata saka gyale sosai kuma yanzu aure zata yi wa zata yiwa kwalliya in ba mijinta kaɗai ba. Fannin gyara kam ta sashi dan sosai ta sauya har wani haske ta ƙara saboda zaman guri ɗaya ba fita take yi ba, ko rabon kati ta online tayi bata yi yawo ba tunda yanzu zamani yazo na waya. Can gidansu Zayyad suma danginsu sun hallara ana ta shirya shagali, yaya Bilki da Asiya sune kan gaba a komai dan Ammi sakar musu ragamar bikin tayi sai dai in abu yazo na shawara su sameta.
Ana gobe ɗaurin aure sun gama shirinsu tsaf na zuwa walimar da Zayyad ya gaya musu Safna zata yi a babban masallacin unguwarsu, wanda zasu yi a harabar Masallacin, sun gayyaci wani babban malami da zai gabatar da wa’azin aure, hakan yasa danginsa suma suka ce zasu je ayi komai dasu tunda bikin babu wani bidi’a party ko taron raye raye, suka yi sallama da Ammi mota ta ɗibesu ƙananun bus guda biyu suka wuce gidansu Safna. Kyakkyawar tarba suka samu wanda tuni aka ware musu gefensu daban cikin rufar kanofi da kujeru suka zazzauna suna hira ƙasa ƙasa kafin a gama taruwa Malam ya fito dan gabatar da wa’azin, kwatsam sai suka hango Rashida da tawagarta wato ‘yan uwanta mata ƙenne da yayyi na family ɗinsu sun shigo, Bilki da Asiya suka kalli juna cike da tsantsar mamaki, sai dai sun kasa cewa komai suka yi gum da bakinsu, wasu daga cikin danginsu ne suke ambaton ga Rashida sunyi mamakin ganin zuwanta, har suka ƙaraso runfar da suke ciki aka shiga gaisawa cike da fara’a a fuskokinsu kamar ba wani abu a tsakakinsu, suma suka samu guri suka zauna ‘yan uwan amarya suka zo suka gaggaisa kowa ya cika da mamakin ganin kishiyar Safna a gurin taron walimar, wasu na ambaton gulma ya kawota wasu kuma ta burgesu yadda take da sauƙaƙƙiyar kishi, haka dai gurin walimar ya gama cika da mata wasu ma basu zamu gurin zama ba, a haka amarya ta shigo ta zauna a mazauninta da aka tanadar mata ba jimawa malam ya fito ya fara gabatar da wa’azi. An ɗauki tsayin awa biyu ana yi daga bisani aka rufe taro da addu’a malam ya tafi tare da kayan arziki, su Anty Shafa da Haajara suka bi matan dake gurin da kayan sovenears, nan fa aka ga dangin Rashida suma sun miƙe suna nasu rabon a gurin turaren wuta a roba fari ƙarama da sitika a jiki sunan ango da amarya da sunan Ilham da Aslam a ƙasa domin sune suka ɗauki nauyin haka, wannan abu ya ƙara shayar da mutane gubar mamaki wanda da yawa wasu na sambarka da Rashida tare da hango tsantsar kirkinta da mutane suke yi, wasu kuma suna ganin na ciki na ciki wataƙila da biyu tayi hakan, wanda tunanin dangin Zayyad kenan sam hankalinsu bai kwanta ba da yarda da abinda Rashida tayi ba, haka taro ya watse kowa cike da farin ciki tare da kwasar tsarabar tunatarwar da Malam Inuwa yayi akan zamantakewar aure, har gidansu Safna Rashida da ‘yan uwan Zayyad suka shiga tare da gaisawa da su Umma daga bisani suka yi sallama dasu suka fito kowa yaja tawagarsa ya wuce. Dangin Safna sai yabon Rashida suke yi da kyawun halinta, hatta anty Maryam da take adawa da Rashidar ta sauko ta yarda da halinta ne na kirki, haka dai kowa keta yiwa Safna sambarka.
Part 5
AMARYAR ZAYYAD
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 5.
‘Yan uwan Zayyad kuwa suna isa gida suka sanar da Ammi yadda taron ya kasance tare da ƙorafin basu yarda da abinda Rashida tayi ba, Ammi ta kwaɓesu da cewa.
Bai dace kuce haka ba ina ganin farin ciki ya kamata ku yiwa ɗan uwanku daya samu ya shawo kanta, wannan abinda Rashida tayi shine yake nuna za a samu zaman lafiya a gidansa. Ku riƙa kyautata niyya da fatan alkhairi akanta.
Idan zaman lafiyar ya kasance zamufi kowa farin ciki, Allah ya haɗe kansu ya kaɗe fitina.
Cewar ƙanwar babansu Haj. Samira, nan suka cigaba da tattaunawa akai suka saki komai a ransu, wataƙila dalilin auren Rashida ta yi hankali ta gyara kuskurenta, da haka suka bar maganar suka shiga zancen abincin da za a girka goben In Allah ya kaimu ɗaurin aure.
Ɓangaren Zayyad shima ba ƙaramin farin ciki yayi ba da yaji labarin abinda Rashida tayi a gurin walimar Safna, yasha mamaki dan baisan da duk wannan shirin nata ba, hakan yasa daya koma gida da dare ya tareta da zancen, dariya tayi ta zauna a gefen gadonsa tana cewa.
To meye a ciki? ai mun zama ɗaya, Allah ya baka ikon adalci.
Ameen ya rabbi.
Ni ina ganin zan tattara na koma gidan Ammi domin na baku dama keda ‘yan uwanki, sai dai zan rufe ɗakina gudun ayi mini ɓarna.
To shikenan ba damuwa dama a kwai masu kwana a falo yanzu haka dan gidan a cike yake da ‘yan uwana, kaima zaka fi sakewa a can gidan Hajiya, na tabbatar gobe dole ka dawo saboda amarya tunda an gama jere ba kwana.
Dominku gabaɗaya zan dawo zaki ce, ni naga ma sai wani basar dani kike yi hala kin daina sona ne Rashida? ko kaɗan bana ganin kishina a tare da ke.
Ina kishinka mana amma ban isa na hana abinda Allah ya ƙaddara mana ba, sannan da kayi mini kishiyar waje gwara ta gida, dole ne na koyi haƙuri da juriya wata rana sai labari.
Nagode sosai da kika kasance haka, ina fatan koda Safna tazo zamanku ya ɗaure a haka ba tashin hankali.
Allah yasa.
Tace tana guntun murmushi, amin yace ya miƙe ya isa waldrobe ɗin kayansa ya ciro abubuwan da yake buƙata ya saka a wata ƙaramar jaka, ya saka komai a ciki kana ya dawo ya miƙa mata kuɗi dubu hamsin.
Ki riƙe a hannunki koda ana buƙatar wani abu bana kusa.
Godiya tayi masa sai suka fito ta raka shi ƙofar fita falon, ya wuce ya shiga mota kana ya fice daga gidan cike da farin cikin sanyin kishin Rashida.
*
Washe gari duka ɓangarorin anata hidimar girki gidajen sun cika da al’umma, kowa yana cike da farin cikin wannan biki. Bayan sallar juma’a aka ɗaura auren Zayyad da Safna a bisa sadaki dubu ɗari biyu, ɗumbin jama’a sun shaida tare da binsu da fatan alkhairi. Zayyad duk da yana cikin taron mutane bai hana shi komawa gefe ba ya kira Safna, cikin yanayin sanyin jiki ta ɗaga ba tare da tace komai ba.
Zainab an ɗaura fa, daga yanzu kina ɗauke da igiyar aurena uku a kanki.
Wani irin abu taji ya tsirga mata tun daga tsakiyar kanta har zuwa kan babban yatsarta na ƙafar hagu, jikinta ya ɗauki wani irin rawa tare da jin zazzafan sanyi ya rufeta.
Safna kina jina kuwa?
Zayyad ya ambata yana buɗe murya, Safnah ta runtse ido tana ambaton sunan Allah a zuciyarta da kyar tayi jarumta ta haɗiye miyau tace cikin sanyin murya.
Allah ya bamu zaman lafiya.
Safna meke damunki ko baki da lafiya ne?
Zazzaɓi nake ji.
Sannu Allah ya baki lafiya yanzu haka stress ɗin bikin nan ne ki samu kici abinci da panadol, In Sha Allah anjima da kin ganki a cikin gidana zaki warware dan sai nayi yadda zanyi zazzaɓin ya sauka.
Murmushi ta saki mai sauti bata yi magana ba.
To sai anjima, amma da anyi sallar La’asar zamu zo ayi hotunan tarihi.
Allah ya kaimu.
Tace daga haka ta kashe wayar tana duban ƙawayenta.
Yau dai na zama Amaryar Zayyad.
Ihu suka saka suna yi mata tsiya, murmushi kawai take saki sai dai can ƙasar zuciyarta wani irin zullumi da karaya take ji, haka suka cigaba da hira masu bata shawara nayi musamman waɗanda suka jima da yin aure.
Zayyad yana gama yin waya da Safna sai ya kira Rashida amma ta kasa ɗaga wayar, sai ta miƙawa Anisa ta cigaba da tsayuwa tana dubanta dan hankalinta a matuƙar tashe yake, Anisa ta ɗaga wayar tace Rashidan bata kusa, sai Zayyad yace ta sanar da ita an ɗaura, daga haka ya kashe wayar Anisa ta ƙundumo wani ashar ta faɗa tana huci.
Wlh Zayyad mugun ɗan rainin wayo ne, wai ya kira ne ya faɗa miki an ɗaura aurensa.
Rashida da take tsaye kusa da miro wani irin jiri ne taji ya ɗibeta da sauri ta dawo gefen gado ta zauna tana dafe kai da hannu bibbiyu, sai ta cire ɗankwalin dake kanta ta shiga firfita, dan sosai gumi ya gama rufeta jikinta har rawa yake yi, Anty Wasila tace.
Wlh ki ɗaure ki danne zuciyarki a gama bikin nan kar ki karaya, ke ce fa uwargidansa sai abinda kika so zai gudana a cikin gidanki.
Anty wai fa an ɗaura auren, yanzu kenan Safna ta tabbata matar Zayyad, duk wani abu na auratayya zai wakana a tsakaninsu babu tsamaki ina ji ina gani. Na shiga uku bazan iya ba wlh zuciyata zata buga, ina son mijina bazan jure ganinsa tare da wata mace da sunan matarsa ba.
Sai ta rushe da kuka mai ƙarfi da gunji, Anisa ko jingina tayi da jikin waldrobe tana jijjiga cike da takaici, sosai abin ya bata haushi wai ya kira ya faɗa an ɗaura auren, Anty Wasila ce ta dafa kafaɗar Rashida tana bata baki, ana cikin haka ƙanwar Mamansu ta shigo ɗakin, ganinsu ko wanne rai a ɓace ga Rashida na kuka ta shiga rafka salati.
Meke faruwa ne naganku ba yadda kuke?
Zayyad ne ya kira Anty Rashida wai an ɗaura aurensa.
To shine me? Sai ku ɗaga hankalinku akan wannan, Rashida ki ware kiyi shagalinki dan babu abinda za a fasa tunda an ɗaura aikin gama ya gama, karki yarda maƙiyanki su samu labarin karayarki suyi miki dariya, dan ga dangin ubanku can sun hallara kuma kunsan ƙiris suke jira su samu abin yi muku dariya tunda ba ƙaunarku suke yi ba.
Inna zuciyata raɗaɗi take yi mini kamar zai faso ƙirjina ta fito. Shikenan Zayyad ya zama mallakin mu biyu.?
Ehen ya za ayi tunda ƙaddara ta riga fata, dole ki danne ki jure ki bawa mara ɗa kunya, ina ce kece kika bar tarihi akan yadda kika nuna sauƙin kishinki a auren, dan haka jaruma zaki zama tunda an ɗaura ki karɓi ragamar uwargidan Zayyad.
Inna Fati ta faɗa tana share mata hawaye, haka dai suka dinga bata baki da kyar ta daina kukan, ta shiga bayin ɗakinta ta wanke fuska ta fito Anisa ta ƙara yi mata wani kwalliya kana suka fita falo wajen baƙinsu, duk da ana ganin idonta sai an gane taci kuka amma fa haka ta dage tana yiwa mutane dariyar yaƙe sai dai na ciki na ciki.
Kamar yadda Zayyad yaje yayi hotuna da Amarya haka ya dawo gidansa aka yi masa da uwargida harma da yaransu da ‘yan uwanta, daga bisani suka fita can zuwa gidan su Ammi nan ma aka yi masa hotuna da ‘yan uwansa, Alhamdulillahi an ɗaura lafiya tare da yinin biki lafiya kowa ya tafi da farin ciki, sai sauran dangi na jiki ne suka rage. Bayan sallar Isha’i motocin ɗaukar Amarya suka dira a ƙofar gidansu Safna, anyi komai kamar yadda ake yi a al’adan Hausa Fulani, dangin ango sun kawo abincin biko da komai da ake yi. Amarya Safna tasha nasiha da faɗa a gurin ‘yan uwa kafin aka fito da ita tsakar gida, umma har ƙofar gida ta rakata ta kama hannunta duka biyu tana cewa.
Daga ni har babanku munyi miki faɗa tuntuni, dan haka abinda zance miki yanzu shine ki shiga gidanki da zuciya ɗaya ki zauna da kowa da gaskiya, ki riƙe ibadarki ki kuma kula da al’amarin mijinki, ki zama mai juriya da haƙuri da kawaici, kiso duk wani abun da mijinki ke so ki ƙi duk abinda mijinki ke ƙi matsawar bai saɓawa Shari’a ba, addu’a ya zama shine makaminki a duk wani damuwa, ɓacin rai, baƙin ciki da zaki samu kanki a ciki, domin zaman aure akwai jarrabawa kiyi ƙoƙarin kai kanki zuwa ga cin nasara, Allah ya baku zuri’a nagari yasa gidanki ya zame miki hanyar samun aljannarki.
Umma ta ƙare maganar cikin rawar murya kana ta saki hannunta, Safna ta juya tana wani irin kuka mai karya garkuwar jikin duk wani mai tausayi, haka Anty Shafa ta kama hannunta ta jata zuwa wajen mota suka shiga driver ya jasu zuwa gidan Zayyad dake Askolaye.
Da suka isa har cikin gidan motarsu Safna ta shiga sauran ne aka sauke su a ƙofar gate haka suka shigo mata na guɗa, Safna kuwa tunda ta zuro ƙafarta ƙasa sai taji zuciyarta ta kuma tsinkewa tana fidda hawaye mara sauti, Anty Shafa ta kama hannunta ta fito sai suka fara isa ɓangaren uwargida Rashida, suka shiga da sallama matan dake ciki suka amsa kana suka basu guri wasu suka zauna wasu kuma dole tsayawa suka yi domin falon ya cika ba guri, bayan gaishe gaishe sai Mama Najah ƙanwar babansu Safna tace.
To uwargida ga amana mun kawo da fatan zaku yi haƙuri da juna Allah ya baku zaman lafiya, Safna sai ki zama mai biyayya a gareta domin ta girme miki dan ita kika zo kika tadda, Allah ya kaɗe fitina.
Duk matan falon suka amsa da amin, Inna Fati tace.
Ai rayuwar ma gabaɗaya haƙuri ne ku kyautatawa mijinku wajen haɗe kanku, dan in har baku haɗa kai ba to babu yadda za ayi ya samu farin ciki, Allah ya baku juriya da juna. Ga wannan a bawa amarya inji uwargidan Zayyad ba yawa, duk da mun so yi mata tanadi mai kyau amma abun yazo a ƙurƙure.
Wannan ma an gode, Allah ya saka da alkhairi.
Cewar Anty Maryam tare da amsar ledar da Inna Fati ta miƙo, Turmin atamfa ce da kuma turaren jiki na kanti guda biyu duk suna cikin kwalinsu, haka suka ɗan tattauna wanda duk shawarwari ake basu, Safna dake cikin Hijab ta ƙosa su fita saboda zafin da take ji, Rashida kuwa gyale ta saka ta ɗan jawo shi ya rufe mata saman fuskarta ta kasa cewa komai sai matsa yatsunta da take yi, haka su Anty Shafa suka yi musu sallama suka fito da Amarya, wasu daga dangin Rashida suka rakosu tsakar gidan kafin suka koma. Anan ne aka shiga kiciniyar buɗe ƙofar ɗakin amarya, bayan an buɗe Anty Shafa ta kamo hannunta tace ta shiga da ƙafar dama da addu’a, Safna wani irin jiri ne taji ya ɗibeta wanda nan take ta ƙanƙame hannun Anty Shafa tana ambaton sunan Allah.
Anty jiri nake ji.
Ta faɗa cikin sarƙewar murya.
To Safna shiga ciki tukunna sai ki zauna ki huta duk gajiya ce.
Safna ta ɗaga ƙafarta da kyar wacce taji tayi mata nauyi sai ta shiga ciki da sallama tare da koro addu’ar tsari a taƙaice, duk da haka sai da taji kanta ya sara mata, nan take ta saki wani irin kuka wanda ya tabbatar da ba ita ɓace jinnun jikinta sun tashi, Anty Shafa ta kamata ta zaunar da ita a Cushing ta cire mata hijab tana cewa.
Haba dan Allah ya zaku yi mana haka, ace ku rasa lokacin da zaku tashi sai a wannan lokacin.
Gurnani kawai Safna take yi tana kuka, Anty Maryam tace duk matar da ke da aljanu to ta fita saboda gudun damuwa, haka masu shi suka fita can waje, Anty Maryam ta matso kusa ta kama kan Safna da ƙarfi ta shiga tofa mata addu’a, Safna ta fara ture hannunta amma ina taƙi sakinta, ɗan so take su tafi kafin su tona asirin Amarya nada jinnu subar abin faɗe, Allah yasa ango bai riga yazo ba, motocin wasu abokansa ne da suka ɗauko su suna waje suna jiran su fito su mayar dasu, motar su Yaya Bilki ana shigo da amarya gidan suka juya aka mayar dasu domin su isa gida da wuri tunda gobe zasu dawo, shiyasa su Anty Shafa suka ji daɗin ba wani bare sai su danginta, haka Maryam ta shawo kan jinnun suka tafi Safna ta sauke wani nannauyan ajiyar zuciya kana ta kalli Anty maryam tace.
Kayan da suke hannunki ki bawa umma tayi amfani dasu.
Sai ta miƙe tsaye ta mayar da hijab ɗinta Anty Shafa ta miƙe itama ta kama hannunta suka shiga bedroom ɗinta, sauran ‘yan uwa suka cigaba da kallon ɗakin wasu har Kitchen suka shiga suna kallon jere, Maryam ma binsu bayan Safna tayi data same su a gefen gado sun zauna tace.
Safna ki cigaba da amfani da magungunarki karki yi wasa dan gaskiya banji daɗin yadda jinnunki suka tashi ba. Da kinji jikinki ba daɗi ki kira ki faɗa dan ayiwa tufkar hanci bana fatan su hanaki zaman ɗakinki.
In Sha Allah zan kula.
Sannan wancen kayan dama ba amfani dasu zaki yi ba duk da bana tunanin kishiyarki zata cutar dake duba da yadda taketa haba haba da auren nan.
Nima dai haka na gani, amma tunda kin ce a kaiwa umma shikenan duk hukuncin data yanken akan kayan zaki ji.
Cewar Shafa, Safna ta turo baki tana cewa.
To in Umma tayi amfani da su ai kamar nice nayi amfani da shi, kuma ban zargi komai ba wlh.
Masha Allah gwara ki tsarkake zuciyarki. Mu zamu tafi ki tashi ki ɗauro alwala ki zauna da ita a jikinki In Sha Allah wani aljani ba zai sake tashi ba.
Cewar Maryam kana ta juya zata fita.
Ni kaɗai zaku bari? .
Eh mana, to ƙawayenki duk matan aure ne ko wacce tayi gidanta balle su zauna wani siyan baki, koda yake an bar yayin wannan, ki taso ki rufe ƙofar zan kira Zayyad ɗin na faɗa masa mun fito yazo ya sameki.
To tace mata kana Shafa ta miƙe itama suka fita, ba ɓata lokaci suka tattara suka tafi aka bar Amaryar Zayyad ita kaɗai cike da kewan gidansu tare da tunanin sabon rayuwar da zata fara a cikin gidan aurenta.
Part 6
AMARYAR ZAYYAD
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 6.
Safna tana kwance tayi lamo dan har barci ya fara fizgarta sai taji wani irin bugun ƙofa kamar tarar aradu, a razane ta tashi ta zauna dan ƙirjinta saida yayi wani irin bugawa saboda zazzafar tsoro daya dirar mata, jin an cigaba da buga ƙofar ya sata saukowa daga gado ta fito falo, sai ta isa ƙofar ta kara kunnenta dan ji hira sama sama data fito, nan ta tsinkayi muryar wata tana cewa.
Wannan ‘yar iskar amaryar ‘yar rainin wayo ce, ji yadda muke buga mata ƙofa amma taƙi ta buɗewa.
Anisa muje kawai tunda bata buɗe ba dama sai da nace ki bari mu ganta zuwa gobe amma kika nace sai kin zo.
Na ƙosa ne naga wacce tafi Anty Rashida da Zayyad taketa rawar ƙafa akanta, amma taci bashin wannan wulaƙancin data yi mana.
Safna tana jinsu amma taƙi buɗewa dan hirarsu ya tabbatar mata da ‘yan uwan Rashida ne, banda niman fitina taya daga kawota zasu zo suce zasu ganta ai koma miye sabari washe gari tunda yanzu ango ne ya dace ya shigo ɗakin ba wasu ba, imma ganinta ne zasu gaji da ita tunda zamane na dindindin. Sai ta koma cushing ta kwanta tana tunanin su, ashe gwara data rufe ƙofar da Anty maryam ta ce mata, bata san da wanne ma suka zo ba a cikin wannan daren.
Anisa suna shiga falon Rashida ta tsaya tana zagin Safna, Zaliha tana tayata tare da wasu ‘yan uwansu da suka je tare, dan zasu kai kusan su biyar waɗanda suka je sashin Safna da niyyar su ganta, Rashida ta kallesu tana cewa.
To kuma uban waye yace kuje, ai gwara data yi muku haka gobe kwa ƙara.
Amma meye laifinmu dan munje muyi mata hira kafin angon yazo. Wannan ai wulaƙanci ne tana ji ana buga ƙofar tayi banza damu.
Rashida ta ƙanƙance idonta tana cizon yatsa ta miƙe tana faɗin.
Aiko saita san ta wulaƙantaku dan daren yau In Sha Allah ba zata kwana cikin farin ciki ba, sai nayi amfani da wannan damar na bar mata tarihin da har ta koma ga Allah ba zata manta da shi ba. Miko mini wayata na kira Zayyad.
Ta faɗa tana nuna inda ta saka chargy, Nan suka saki shewa Anty Wasila tana cewa.
Yauwa ‘yar gari gwara ki fara nuna ikonki na uwargida, tasan cewa kece da gida bata isa ta samu yadda take so ba sai in kin so hakan ya faru, komai sai da makirci gwara ki hau kan layin dana ɗauraki shima zai miki amfani sosai matsawar kin iya takunki.
Murmushi Rashida ta saki ta koma ta zauna tana ɗaura ƙafar damanta akan center table.
Ai tunda ta yarda ta auri mijina ita da farin ciki sunyi sallama.
Sai ta amsa wayar da Zaliha ta ɗauko mata, dama falon ba kowa sai su dan duk mutane sun watse wasu baƙin kuma suna can ɗakinta sun kwanta wasu kuma sunje gidansu, sai ta shiga wajen kira a wayarta ta danna number ɗin Zayyad, bugu biyu ya ɗauka zata yi magana ya rigata.
Gani nan na kusa ƙarasowa gida ina hanya.
Cikin yanayi na rauni da sanyin murya tace.
To sai ka ƙaraso.
Rashida lafiya kuwa naji muryanki cikin damuwa.
Ka bari dai ka ƙaraso ɗin.
Tana kaiwa nan ta kashe wayar tana sakin wani shu’umin murmuahi, Zayyad kam kasa haƙuri yayi ya shiga kiranta amma taƙi ɗagawa, hakanan ya samu kansa cikin damuwar yadda yaji muryarta, dan sosai yake tausayinta ba ƙaramin jarumta tayi ba da auren nan nasa yana jinjina mata akan haka. Rashida ta kalli Anisa tana cewa.
Ko ki tafi gida yanzu ko ki shiga ɗaki ki ɓoye kanki dan abinda na shirya akanki ne bana so ya ganki.
Wani irin na tafi ai sai dai na ɓoye dan wlh ina gidan nan har sai amarya ta gama kwanakinta kafin mu tattarara muyi gida.
Ta faɗi haka tana wani fari da ido sai ta yi gaba ta shiga ɗakin Rashida ta sanya wayarta silent ta kunna data ta fara chart, nan kuma sauran dake falon suka shiga shewa da cigaba da hira. Lokacin da suka ji dirar motar Zayyad sai duk suka shanye fara’arsu suka yi fuska tamkar waɗanda aka yiwa mutuwa, har ya shigo da motarsa cikin gida yayi parking sai ya ɗauko ledar kazar daya siyawa Rashida yabar nasu a cikin mota, akan in ya fito daga side ɗinta zai tsaya ya ɗauka sai ya wuce. Yana isa ƙofar ya murɗa handle ya shiga da sallama suka amsa masa amma yadda yaga fuskokinsu cikin damuwa yasa shi tsayawa tare da amsa gaisuwarsu, Rashida ta miƙe ta iso inda yake ta amsa ledar hannunsa.
Sannu da zuwa.
Lafiya na ganku haka?
Muje ɗakinka sai nayi maka bayani.
Tace tana wucewa gaba sai ya bi bayanta ya saka makullin ya buɗe ɗakin ya shiga ta bishi a baya tare da rufo ƙofar.
Rashida ya na ganku duk cikin damuwa ko wani abu ya faru ne.?
Zayyad ban so faɗa maka ba saboda ganin yau ranar farin cikinka ne, ka bari zuwa gobe In Allah ya kaimu sai nayi maka bayani.
Kinga Rashida ki faɗa mini kawai dan hankalina bazai kwanta ba ganinki cikin damuwa.
Hmmmm dama su Anisa ce suka je side ɗin Safna domin su yi mata hira kafin ka shigo saboda ‘yan uwanta sun tafi sun barta ita kaɗai, amma abin mamaki sun yi mata sallama sun buga ƙofar shuru bata buɗe ba tayi banza dasu, ban taɓa tunanin Safna zata yi haka ba duba da yadda na ɗauketa, wlh har cikin raina yadda Anisa da Zaliha suke a gurina haka na ɗauketa amma ita ga dukkan alamu da wata manufar tazo gidan nan. Ace yadda na dinga zuzuta kirkinta ga ‘yan uwana amma lokaci guda ta gwasaleni tasa naji kunya, in zata wulaƙanta kowa ai bai dace ace tayiwa ‘yan uwana haka ba kodan yadda na ɗauketa.
Ta ƙare maganar cikin zubda kwalla saboda kasa danne baƙin kishinta daya zo mata wuya, in ta tuna da Zayyad zai kwana da wata ji take yi kamar ta haɗiyi rai ta mutu, Zayyad jikinsa yayi sanyi yana dubanta yama kasa magana saboda tsantsar mamakin Safna dan bai taɓa kawo zata yi irin haka ba, sai ya nisa ya kamo hannun Rashida.
Kiyi haƙuri kuma In Sha Allah zan tsawatar mata dan ba zan taɓa yarda ta wulaƙanta ki ba saboda kina da matuƙar muhimmanci a gareni.
Abinda yayi mini ciwo har nasan dagangan tayi haka, sunce suna jin ƙarar waƙa daga wayarta a falo har ma tana rerawa, hakan ya tabbatar da ta sane daga ɓangarena ne aka je gunta, ashe yadda na ɗauki Safna ba haka ta ɗaukeni ba, nayi haƙuri na danne damuwa da kishina na kwantar da hankalina ganin nasan wacce zaka ɗauko mini, ba zamu samu matsala ba amma daga zuwanta ta wulaƙantani, to eh mana ni tayiwa ba ‘yan uwana ba.
Ta ƙare tana rusa kuka mai cuma zuciya, ran Zayyad in yayi dubu to ya ɓaci dan har ga Allah ya yarda da duk bayaninta, duba da yadda yasan halinta da yadda ta bada haɗin kai ga aurensa. Jayota yayi jikinsa yana buga bayanta tare da bata haƙuri akan zai ɗauki mataki, ɗagowa tayi tana danne kukanta.
Nifa bana faɗa maka bane dan ka yi mata magana ba, kawai na kasa danne abin a raina ne dan ta yi matuƙar bani mamaki banyi zato ba sam, kuma saboda su Anisa sunyi fushi sosai har ta kasa zama a gidan ta wuce gida, dama tun ɗazun da yan uwanta suka kawo ta nan sashinsu bayan fitarsu munji suna ƙananun magana, amma ban kawo komai ba tunda ni da gaskiya zan zauna da Safna.
Haba Rashida meyasa zaki bar Anisa ta tafi, Allah yasa ba zata faɗa a gida ba.
Saida na kwaɓeta nace su bar maganar a iya tsakaninmu dan kar wasu suyi mini dariya.
To shikenan bari zan samu Safnar, wannan kazarki ce kici ɗaya keda yara sai ki bawa ‘yan uwanki suci ɗaya. Bari naje sai da safe.
To Allah ya tashe mu lafiya.
Ta faɗa a raunane, Zayyad ya fito tana biye dashi har ya rufe ƙofarsa ya nufi waje, ta tsaya a ƙofar daki ya isa motarsa ya ɗauki kazarsu da lemu ya wuce part ɗin Safna yana ɗaga mata hannu, murmushin yaƙe tayi masa tana jin wani tuƙuƙin baƙin ciki yana taso mata, bata taɓa jin tsanar Safna ba irin na yau dan ji tayi kamar ta babbaka musu wuta su ƙone akan ya kasance tare da ita, hakan yasa ta saki ƙofar ta fito a hankali ta lallaɓa ta isa windon Safna ta ƙara kunnenta dan jin wainar da zata kaya.
Zayyad kuwa yana isa ƙofar ya buga yana ambaton sunan Safna, dama tana falo sai ta aje wayarta da sauri ta miƙe ta isa ƙofar ta buɗe kanta a sunkuye ta kama ledar hannunsa mai makon ya sake mata sai ya riƙe gam, ya juya ya rufe ƙofar tare da wuceta ya samu kujera ya zauna yana cire hular kansa fuskarsa a matuƙar haɗe, Safna bata ga fuskarsa ba shiyasa bata gane da wani yanayi ya shigo ba, ta samu one seater ta zauna tana matsa yatsunta.
Samnu da zuwa.
Safna!
Ya ambaci sunanta cikin kausasa murya ba tare da ya amsa mata sannu da zuwan ba, yadda taji muryarsa yasa ta ɗago kai da sauri taga fuskarsa a murtuke sai taji gabanta ya faɗi tana dubansa, ya ɗaura da cewa.
Ina so ki sani idan zaki wulaƙantani ko ‘yan uwana ko wani nawa kiyi amma banda Rashida da ‘yan uwanta, Domin banda kamarta macece mai haƙuri da kawaici ta yi matuƙar bani haɗin kai wajen auroki, bazan lamunci cin mutunci ko cin zarafinta ba dan wlh zan iya yin komai akanta saboda ba dan bana sonta bane na auro ki. Haba daga zuwanki zaki fara nuna halin da ban taɓa zatonki da shi ba, ace ‘yan uwanta sun zo gunki dan suyi miki hira kan na dawo amma sunyi miki sallama da buga ƙofa suna jin motsinki a falo kinyi banza dasu, to daga yau karki ƙara bazan ɗauki wulaƙanta mutane ba.
Ya ƙare maganar cikin nunata da yatsa, Safna kam tunda ya fara magana ta sunne kai ta soma zubda hawaye, jikinta har zafi yayi dan nan take taji zazzaɓi take ji, ace a ranar daren amarcinsu su fara da faɗa wanda bata san hawa ba bata san sauka ba, ta san dai wannan makirci ne kawai suka shirya mata amma yadda suke buga ƙofar kamar tarar aradu ba zaisa ta buɗe ba dan ta tsorata dasu, sannan ba suyi mata sallama ba balle tace cikin lumana suka zo. Zayyad ya miƙe ya cire babbar rigarsa ya aje a cushing ya wuce kitchen dan ɗauko plate, bai damu da yanayinta ba ko ya lallasheta dan shima yaji zafin abinda tayi kuma dole ne ya nuna mata kurenta yadda ba zata kuma aikata hakan ba, ya dawo da plate da kofi a hanunnsa ya zauna a carpet ɗin tsakiyar ɗakin ya ciro kazar a leda wanda aka ƙunshe a foil paper ta ɗaura a plate ya buɗe ya fara ci yana cewa.
Ki sauko mu ci abinci.
Ya ƙare maganar ba tare da wata kulawa ba, Safna miƙewa tayi bata ce masa komai ba ta wuce zuwa bedroom ɗinta, tana shiga ta kwanta a can ƙuryar gado tana kuka mai tsuma zuciya, ga mugun ciwon kai daya addabeta ga kuma zazzaɓi da ɓacin rai daya dirar mata a lokaci guda, ta rasa tunanin me zata yi haka ta lumshe ido ta rufe sai ruwan hawaye ne ke zuba. Zayyad a zatonsa ko ta shiga danta yi wani abu ne ta fito amma shuru bata dawo ba, har ya gama cin kazarsa ya naɗe sauran ya aje plate a kan center table da ragowar lemun kwalin, ya miƙe ya ɗauki hula da babban rigarsa ya shiga cikin bedroom ɗin, koda ya ganta a kwance bai kulata ba dan ya kula fushi tayi shi kuma akan Rashida zai ɓata da ita dan ba zai lamunci haka daga gareta ba, ya aje rigarsa ya fito falo ya isa kitchen ya sauko da butar kattle ɗinta da yake cikin kwali ya ciro shi sai ya wanke butar ya zuba ruwa ya jona ruwan wanka, sai ya dawo falo ya zauna yana duba saƙonni a wayarsa wanda duk na mutane ne da suka yi masa fatan Alkhairi da aurensa.
Rashida lokacin data ji Zayyad yana korowa Safna faɗa, wani sanyin taji a ranta dan haka ta bar jikin window ta koma ɗakinta zuciyarta cike da farin ciki, addu’a kawai ta shiga jerowa akan Allah yasa su kwana suna faɗa kar wani abu ya wakana a tsakaninsu, haka ta sake taci kazar daya kawo tare da ‘yan uwanta waɗanda ba suyi barci ba. Sun kai kusan sha biyun dare suna hira kafin daga bisani ko wanne ya nima gurin kwanciya.
Zayyad bayan yayi wanka sai ya zo kan gadon ya kwanta yana duban Safna da take sauke ajiyar zuciya da alama barci ya ɗauketa, ba haka yaso daren farkonsu ya kasance ba, dan ya jima yana mafarkin yadda zai kasance tare da ita da irin kyakkyawar tanadin da yayi musu, sai dai kash Allah bai nufi haka ba dan har lokacin bai yi nadamar abinda yayi mata ba saboda laifinta ya gani, kuma a tunaninsa ta wannan hanyar ne kawai zai magance ɓarakar data ke shirin kunna masa a gida, daga zuwanta zata fara haddasa damuwa wanda bai zaci haka daga gareta ba, da tunani barkatai barci yayi awon gaba dashi.
**
Da asubahi kiran sallar wayar Safna shine ya tayar dasu duka su biyun, dan dama tana da app ɗin da ke kiran sallah duk in time ɗinsa yayi, ta farka amma ta kasa kwakkwaran motsi saboda ciwo da jikinta ke yi mata, ga kuma wannan ciwon kai har yanzu dan a cikin barci ma tana jinsa dan dai barcin yaci ƙarfinta ne, Zayyad ne ya miƙe ya shiga toilet ya ɗauro alwala ya fito yana ambaton sunanta, kamar ba zata amsa shi ba amma ta cije ta amsa tana tashi zaune.
Ki tashi kiyi sallah zanje masallaci na dawo.
To tace masa sai ya fice ita kuma ta sauko ta wuce falo ta shiga kitchen, ta ga yayi amfani da kettle sai ta zuba wani ruwan ta kunna ta jira ya fara zafi sai ta dawo ta ɗauki buta a bayi ta koma ta zuba ruwan zafin a ciki sai ta ƙara wani ruwan a kettle wanda in ta idar da sallah zata yi wanka, ta koma ɗaki tayi alwala da ruwan zafi dan yadda take jin jikinta ba zata iya yi dana sanyi ba, data gama ta fito ta gabatar da sallah.
Part 7
AMARYAR ZAYYAD
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 7.
Safna tana zaune a dadduma tana lazumi, Zayyad ya shigo bedroom ya sameta bisa sallaya, zama yayi a gabanta yana duban fuskarta, ita kuma ta sunne kai ƙasa tana cewa.
Ina kwana.
Bai amsa ba sai ya ɗago fuskarta yaga idanunta a kumbure wanda yasa shi jin ba daɗi a ransa, Safna lumshe ido tayi hawaye ya soma zuba a kuncinta.
Saboda nayi miki faɗa shine zaki hukunta kanki da kuka har idanunki suna kumbura haka.
Kayi haƙuri ba faɗar daka yi mini bane ya sani kuka, kewar gidanmu da su Umma ne yake sani zubda kwalla. Kuma kayi haƙuri da abinda ya faru jiya In Sha Allah zan kiyaye hakan ba zai sake faruwa.
Idan kika yi haka zanfi kowa farin ciki, sannan ki daina zubda hawayenki dan yanzu nine zan maye gurbin su Umma. Safna sonda nake yi miki babu wasa a cikinsa dan Allah ki zauna lafiya da Rashida ki mutuntata dan itama tana sonki.
Ya faɗa yana jawota zuwa jikinsa, Safna bata iya yin magana ba sai ajiyar zuciya da take saki, nan ya kama kanta ya koro addu’ar da duk wani ango ake so ya yiwa Amaryarsa a ranar farko da suka kebe, bayan ya gama ya ɗagata daga jikinsa ya miƙe tare da ɗaukarta cak ya isa da ira kan gado ya kwantar, ya koma ya naɗe daddumar ya kashe wutar ɗakin yaje ya kwanta a gefenta tare da cire mata hijab ɗinta, a hankali Zayyad yaji duk wani haushin daya kwana dashi jiya ya tafi, sai ya shiga yi mata hirar walimar da yayi da abokansa, tare da taɓa sassan jikinta yana shafa fatarta da yake da santsi da laushi, Safna dai ta kasa sake jiki saurarensa take yi kawai amma har lokacin zuciyarta a cunkushe yake, ba tada lafiya ga yunwa da yake damunta wanda rabonta da abinci tun jiya da rana shima ba a nutse taci ba, ganin da gaske yake yi zai rabata da kayan jikinta, sai ta kasa jurewa ta kama hannunsa tana marairaice fuska akan yayi haƙuri ya bari anjima, shima kallonta yayi da rinannun idonsa da suka sauya launi zuwa wata duniya.
Yanzu zamu gama sai ki koma barci nasan akwai gajiya a jikinki.
Shuru tayi bata ce komai dan ba tada wani zaɓi, jikinta rawa kawai yake yi ga fargaba ga kuma rashin kuzari, tana mamakinsa na yadda yaƙi tausaya mata a halin da take ciki tunda ko bata faɗa ba yasan bata jin daɗin jikinta dan har wata rama tayi daga jiya zuwa yau. Haka Zayyad ya biya buƙatarsa ba tare da wani ɓata lokaci ba, babu dogon wasa ko wani abu da zaisa ta samu gamsuwa shi dai nasa ya sani, Allah yasa kayan gyaran data sha ya taimaka mata wajen fitar da lubricant wanda yasa ya samu sauƙin samun hanya, kuka kawai take yi saboda azabar da take ji daga jikinta, gani take yi kamar ma ba wani soyayyarta a zuciyarsa saina matarsa tunda bata ga wani tausayinta a idonsa ba, haka ya miƙe ya fita falo ya shiga kitchen da niyyar ya saka ruwa a kettle na wanka sai ya tadda akwai ruwan zafi har butar ta kashe kanta, haka ya dawo ya ɗauki bokiti ya koma ya juye ruwan ya mayar da wani. Yayi wanka ya gyara jikinsa kana ya koma ya juye mata nata ruwan ya mayar da wani ya kawo mata bayi ya aje ya fito.
Ki tashi kiyi wanka zaki samu ƙarfin jikinki, in kin fito sai mu kwanta zuwa ƙarfe tara saimu karya na fita. Dan nasan ‘yan uwanki ƙila suzo da wuri.
Gyaɗa kai tayi tana cije leɓe ta tashi ta zauna da kyar ta ɗaura zanin kayanta ta sauko tana tafiya da kyar jikinta har ciccira yake yi tsabar zafin da take ji a ƙasanta, haka ta shiga toilet ɗin ta tsuguna da kyar fitsari ya fito mata wanda nan take taga ya gauraye da jini, hawaye ya zuba a kuncinta tasan kuma ta rasa wannan duburcin da ta jima tana tattalinsa, sai dai zuciyarta ta shiga tararradi da kokwanton mutumin data mallak masa shi kamar bai dace daya mallake shi ba, haka ta sirka ruwan da zafi sosai ta gasa HQ ɗinta sosai kusan ruwan anan ya ƙare, Alhamdulillahi taji sauƙin raraɗin da take ji, ta miƙe ta mayar da zanin ta fito akan taje ta dafa wani ruwan na tsarki.
Ina zaki je?
Zayyad ya tareta yana duba wayarsa da alama chart yake yi.
Ruwan ya ƙare zan saka wani ruwan zafin ne nayi wanka.
Ok kawo bokitin na juye miki dama na mayar da wani.
Ya faɗa yana aje wayar a bedside drower ya miƙe ya amsa, ba jimawa ya dawo mata da ruwan ya miƙa mata yana murmushi.
Ki saka ruwan da zafi sosai ki watsa za kiji ƙarfi kinji.
Hummm tace ta karɓa ta koma ciki ta yi wankan, ba jimawa ta fito ta shirya cikin doguwar rigar shadda purpul wanda yasha aiki tun daga sama har ƙasa, ta shafa mai ta saka kwalli ta koma gado ta kwanta, anan ne ya kashe datarsa ya mirgina zuwa inda take kwance ya rungumeta ta baya.
Kiyi haƙuri da duk abinda ya faru jiya wlh raina ne ya ɓaci,vbanso daren farkonmu ya kasance haka ba amma In Sha Allah nayi miki alƙawarin tsawon kwana shida da zamuyi sai ya zame miki daren farko a ko wace rana, saboda tanadin dana yi miki na soyayya ba zai tafi hakanan ba, nagode da kika adana min kanki na sameki cikakkiyar mace, Allah yayi miki albarka yasa a zuwan farkon nan nayi kyakkyawar a jiya wanda zai zame mana sanyin idaniyarmu. Ina matuƙar ƙaunarki Safna ina jinki a can ƙasar zuciya wanda ba zan iya misalta miki yadda nake ji ba, Allah yasa albarka a cikin zamanmu ya kauda dukkan fitina.
Ameen ya rabbi, nima kayi haƙuri da abinda nayi jiyan ban zaci zai zama laifi ba, duba da a wannan lokacin kai kaɗai nake tsumayen jira nayi tozali da annurin fuskarka, shiyasa ban buɗe musu ƙofar ba ganin dare yayi, amma bazan sake hakan ba nayi maka wannan alƙawarin, duk abinda kake so shi zanyi koda raina baya so matsawar bai saɓawa addini ba.
Allah yayi miki albarka Amaryata ya saka miki da gidan aljanna maɗaukakiya, na yarda dake nasan ba zaki zama silar damuwa ta ba. Mu kwanta muyi barci kafin anjima na haɗa mana breakfast.
Kai kuma?
Eh mana, ai tun yau aikina na kula dake zai fara sai na tabbatar miki da gidan Zayyad ne farin cikinki na duk duniya.
Murmushi mai sauti Safna tayi dan sosai kalamansa suka yi tasiri a zuciyarta nan take taji duk wata damuwa ya yaye a ciki ranta, ta kuma yi masa uzuri bisa abinda yayi mata jiya, yadda taji ya ƙara rungumeta yasa ta lumshe ido tana sauke numfashi a hankali, shi kuma a wannan yanayin jinsa yake a wani sabon duniya da bazai iya fasaltashi ba, wani irin so da ƙaunarta ke fuzgarta kamar zai haɗiyeta, haushin kansa yaji akan yadda ya tarbeta jiya da faɗa, sai yake ganin da yayi mata uzuri matsayinta na baƙuwa kuma abar sonsa, daya bi abin asannu to ba zasu kwana jiya kamar wasu abokan gaba ba, a haka barci ya ɗauke shi da tunaninta, itama barcin ya ɗauketa cike da samun natsuwa.
**
Rashida.
Wajen ƙarfe shida ta tashi tayi sallah ta zauna jugum bisa sallaya tana tunanin ko ya Zayyad suka kwana jiya, Zaliha ce ta shigo ɗakin tana cewa.
Anty alale za muyi ko ƙosai?
Ƙosai dai zaifi daɗi da kunu.
To ai mangyaɗa ya ƙare wanda ya rage ba zai ishemu suya ba.
Ok a wanke waken akai niƙa sai na bada kuɗi ku siyo man.
To tace mata sai ta fice ta miƙe ta naɗe sallayar ta adana, kana ta cire hijab ta fito tsakar gida inda suke surfen wake, Wasila ce ta matso kusa da ita tana yi mata rasa.
Yanzun nan naje ɗauko dutsen da zamu haɗa wuta dake can gefen naji ana yin wanka daga sashin Amarya, da alama komai ya kankama abinda kika haɗa bai yi aiki ba.
Wani irin zullo zuciyar Rashida yayi tare da bugawa da ƙarfi har sai da ta dafe bangon da ke kusa da ita, kana ta tsuguna ta zauna a dakalin dake ƙofar ɗakinta ta shiga mayar da numfashi cikin haki kamar wacce tayi gudu, hankalin Wasila ya tashi ta dafa kafaɗarta tana cewa.
Dan Allah ki sausautawa zuciyarki karki yiwa kanki illa, gwara ma kici maganin zama da su dan wlh Namiji ɗan akuya ne ba zai ga sabuwar mace fil a leda ya kasa taɓawa ba gwara ki daina yaudarar kanki, dan aikin gama ya gama tunda an ɗaura, kamata yayi ki zauna ki yiwa kanki linzamin da zai ja ragamar girmanki a cikin gidan nan.
Rashida dai ta kasa magana da kyar ta haɗiye miyau kana ta ɗago kai tana duban Anty Wasila tace a hankali.
Da alama Safna tafi ƙarfina bazan samu yin galaba akan ta ba.
Kama hannunta Wasila tayi ta miƙe sai ta jata suka shiga can uwar ɗaka ta rufe ƙofar da key tana cewa.
Babu gaggawa fa Rashida komai sai a hankali zai tafi, kamar yadda na faɗa miki in wannan bai yi ba to wani zaiyi aiki kar dai ki sare.
Nan ta cigaba da ɗaurata akan mummunar makirci da shawarwari marasa amfani, Rashida sai da ta hau sosai kafin ta ɗan ji hankalinta ya kwanta, sai suka ƙara fitowa waje ta nufi sashin Safna, ta tsaya a ƙofar ta shiga bugawa da ƙarfi kamar wacce tazo amsar bashi. Safna da Zayyad barci bai jima da ɗaukar su ba buga ƙofar da aka shiga yi yasasu suka farka a razane, Safna kam nan take kanta ya rasa mata zuciyarta yana wani irin buguwa cike da tsoro dan har Aljanunta sun motsa, cikin ɓacin Rai Zayyad ya fito falo yazo ya buɗe ƙofar ya fito, bai taɓa zaton ganin Rashida bace, kallon kallon suka yi fuskarta cike da mirmushi.
Ango ango kasha ƙamshi.
Rashida wannan wani irin abu ne da zaki zo ki buga mana ƙofa kamar tarar aradu, barci fa muke yi sannan duk uzurinki ba zaki bari anjima ba in na fito.
Rashida ta marairaice fuska tana cewa.
Wayyo Allah ban zaci barci kuke yi ba ganin ba a jima da asubahi ba, dama mai ne ya ƙare da sugar shine nazo ka bada kuɗin, sannan naji me kuke buƙata a yi muku na karin safe.
Ta gama bayaninta Zayyad yana kallonta fuska haɗe.
Shine ba zaki iya kirana a waya ba zaki zo kina buga ƙofa haka, kin san ai bana kashe wayata in kuma ina da buƙatar kiyi mana wani abu zan kiraki ai. Kuma da kuɗi a hannunki da zaki iya amfani dashi na tabbatar wanda na baki jiya basu ƙare ba, in ma babu saiki ranta a gurin ‘yan uwanki inna fito kya amsa ki basu.
Zayyad har nayi lalacewar da zaka tsaya kana gindaya mini sharaɗin da zan yi magana da kai saboda kayi amarya kaji sabon guri ko, tun ba aje ko ina ba zaka fara sauya mini, babu komai Allah yana gani ni bada wani manufa nazo ba, kayi haƙuri tunda ranka ya ɓaci saboda na tayar da shalelenka.
Ta faɗa tana matsar kwalla tare da juyawa ta wuce, Zayyad baiji daɗin yadda ta fassara shi ba kuma duk maganar daya gaya mata shine dai dai, amma ganin hawayanta ya karya masa guiwa sai ya bi bayanta ya tadda ‘yan uwanta suna hada hadan haɗa abin kari nan suka shiga gaisawa, ya amsa fuska sake sai ya bi bayanta zuwa ɗakinta, ya sameta gefen gado tana matsar kwalla, Zayyad ya zauna tana dubanta.
Rashida na faɗa miki kina da matsayin da babu macen da zata saka na wulaƙantaki, ni banji daɗin yadda zaki je kina buga ƙofar mu da kanki ba, domin ina duba miki kar ki zubar da girmanki ne, dan in da Sadfna ce ta buɗe ƙofar bansan da wani irin kallo zata yi miki ba, kinga girmanki zai zube a idonta.
Sai dai in kaine zaka bata damar ta raina ni, amma daga zuwa in yi magana da kai shine zai zama laifi da zubda girma, tun ba aje ko ina ba kana nuna mini iyakata da kai bayan tare ta zo ta ganmu.
To shikenan kiyi haƙuri ni bana son ganin wannan damuwar akan fuskarki, yanzu bari naje na ɗauko kuɗin saiki aika a siyo miki duk abinda babu. Haba uwargidan Zayyad ai babu macen da zata kaiki matsayi a zuciyata.
Hmmm Allah yasa.
Ta faɗa tana miƙewa shima miƙewa yayi sai ya kamo ta ya rungume ta tare da manna mata kiss a goshi sai ya saketa ya fice. Yana isa ɗakin Safna ya sameta jingine da filo tana duban ƙofa, murmushi ya sakar mata yana cewa.
Kiyi haƙuri an tasheki a barci yara ne suka zo suna bugawa wai an aiko su su amsa kuɗi za a siya man suya.
Zayyad ya samu kansa da zabga mata ƙarya, bayan lokacin daya fita ta isa windonta na uwar ɗaka taji duk maganarsu da Rashida, murmushin yaƙe tayi masa tana cewa.
Ba komai dama kaina ke mini ciwo kuma buga ƙofar ya razanani, amma ina da sauran panadol zan haɗa tea nasha sai na sha maganin.
To kiyi haƙuri kuma na tsawar musu, bari nayi sauri na fita na haɗo mana kayan tea danni na riga na tashi kenan bazan iya komawa barcin ba.
To sai ka dawo.
Tace, Zayyad ya isa inda ya aje kayansa daya cire jiya ya ɗauki kuɗi ya fice daga ɗakin, da kallo ta bishi tana mamakin yadda yake rawar ƙafa akan Rashida, da alama duk wannan soyayyar da ta nuna mata ashe shigo shigo ba zurfi tayi mata, dan makircin data haɗa mata jiya da kuma abinda ya faru yanzu ya tabbatar mata da wuya suyi zaman lafiya, da akwai mugun nufi a zuciyarta ba soyayyar gaskiya take yi mata ba, haka ta runtse ido tana fatan ko yaya barcin ya ɗauketa amma ina, hirar da ‘yan uwan Rashida suke yi a waje ya hanata dan hira suke yi sosai da shewa kamar ba safiya ba.
Haka zayyad ya dawo ya shiga kitchen ɗinta, da kansa ya haɗa musu abin kari, ya haɗa musu tea ya soya kwai tare da gasa biredi da butter a toaster kana ya aje musu a falo, ya je ya kira Safna ta fito suka karya, dama da yunwa a cikinta bata yi wasa ba ta ci sosai, ya kalleta yana cewa.
Kinga kazarki baki ci ba, na manta dana sarrafa miki kin ci shi amma karki damu anjima zan siyo miki wata.
Wai in tambayeka mana.
Ta faɗa tana murmushi, ya kalleta da kyau yana ‘yar dariya.
Ina jinki Amaryar Zayyad.
A ina ka koyi girki ne?
A gurin Amminmu, dan lokacin da muke matasa ba abinda ban iya ba da aikin gida, kin san ita duk wadatar Abbanmu bai sa ta yarda da masu aiki ba muke yin komai a gidan.
Yanzu kace har Mukhtar shima ya iya aikin gida?
Sosai kuwa sai dai in hakan bai taso ba.
Nima In Sha Allahu haka zanyi training yaranmu.
Ta ƙare maganar tana rufe fuska cike da jin kunya, Murmushi Zayyad yayi yana girgiza kai ba tare da yace komai ba, haka suka gama karyawa cikin nishaɗi kafin suka miƙe zuwa Bedroom, Zayyad ya shirya cikin manyan kaya yasa hula tare da feshe jikinsa da turare ya juyo yana dubanta.
Na haɗu kuwa.?
Irin soaai ɗin nan kayi, sai dai kar ‘yan matan waje su gama kalle mini kai.
Ko sun kalla kwalelensu, ni wa Rashida da Safna ne aka halicceni kaɗai.
Murmushi tayi masa tana jin kishin ambaton sunan Rashida da yayi, ya ɗauki key mota da waya.
Anjima zan aiko da cefane ina so na fara cin girkin Amaryar Zayyad, kiyi tuwon semo miyar kuɓewa ɗanya.
An gama Sirrin Ruhu.
Ta ambata tana murmushi, shima dariya yayi tare da wucewa ta bishi a baya har zuwa ƙofar ɗaki, ya wuce ta rufe ƙofar da key ta ciki ta koma dan ta gyara inda suka karya da turare ɗakin kafin ‘yan uwanta su ƙaraso. Tana jin fitar motarsa wanda baifi da minti biyar ba taji an zo ana buga mata ƙofa da ƙarfi, wanda ya sanyata faɗuwar gaba har kofin dake hannunta ya faɗi ƙasa dan razana.
Akwai ƙura a wannan tafiyar
Part 8
AMARYAR ZAYYAD
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 8.
Safna daidaita natsuwar tayi da addu’a kafin ta isa ƙofar ta buɗe saboda karta ƙara yin wani laifi, tana buɗewa taga mata kusan su biyar kuma babu wacce ta sani daga ciki sannan ba mai mayafi, hakan ya tabbatar mata daga sashin Rashida suke, matsa musu tayi suka shiga sai ta koma ciki ta zauna a one seater tana cewa.
Sannunku da zuwa.
Yauwa Amarya ina kwana ya baƙunta, kiyi haƙuri mun sake dawowa Allah yasa bamu dameki ba, kin san amarya farin jini take da shi mun ƙosa mu ganki shiyasa tun jiya muka zo sai kuma baki buɗe ƙofar ba.
Cewar Anisa da ta nace sai ta ga Amarya, Zaliha ta matsa kusa da center table ɗinta ta buɗe sauran kunshin naman kazar jiya da Zayyad ya bari a gurin.
Anty Anisa ga mutumiyar fa, da alama mune za muci sauran kazar amarya, Amarya sai dai kiyi haƙuri damu dan gaskiya bama ganin Dajaja bamu sanya mata albarka ba.
Ta faɗa tana yago tsoka ta saka a baki.
Kuma wlh bata yi komai ba da yake a rufe aka aje shi.
Ta ƙare maganar tana taunar kazar kamar mayya, nan fa sauran suka taso duk suka saka hannu amma banda Anisa da ita wajen da suka karya ta nufa, ta zauna tana shan sauran tea data gani a kofi ga kwai da suka rage shima, nan ta gyara zama ta yaga biredi ta soma ci hankalita kwance, Safna tsabar gubar mamakin da ya bugar da ita rungume hannu tayi a ƙirji ta tsaya kallon ikon Allah, hankalinsu kwance suke ci suna hira tamkar dama sun daɗe da saninta, bata iya cewa komai ba banda ido data zuba musu har suka gama cinye komai tas dan hatta biredin saida ko wacce ya yagi rabonsa ba subar komai ba, Anisa ta miƙe tana guntun gyatsa.
Aiko ysnzu na rage hanya dama da guntuwar yunwata na tashi, idan an soma suyar ƙosai na ƙara cika ƙuiɓa ƙuiɓa na da shi. Amarya kiyi haƙuri damu domin mu ƙannen Anty Rashida ne in da ƙara kuma kema kin zama yayarmu.
Wlh kuwa ai a hankali zata wayemu, gaskiya ɗakinki ya tsaru gwanin burgewa Allah ya nuna mini aurena haka.
Cewar Amina ɗiyar ƙanwar mamansu Rashida, nan suka cigaba da zama suna hira cikin sakewa kamar ɗakin uwarsu, Safna ganin abin nasu bana ƙarau bane gashi tana fama da ciwon kai ga barci na damunta, tasan kuma har zata runtsa kafin ‘yan uwanta su zo hakan yasa ta ari jarumta tace.
Dan Allah kuɗan yi mini haƙuri zan kwanta ina fama da ciwon kai zuwa anjima sai ku dawo muyi hirar.
Kallon juna suka shiga yi ko wacce da magana akan fuskarta, Zaliha da yake ba kunya ke gareta ba ta miƙe tana cewa.
Sai ku tashi mu tafi tunda bata yi farin ciki da ganin ba, dama tun ɗazu naga sai wani haɗe rai take yi, wannan amaryar da gani sai Anty Rashida ta sha fama da ita dan alamu sun nuna ba kirki zata yi ba ni kunga tafiya.
Ta ƙare maganar tana yin hanyar ƙofa, suma sauran duk suka miƙe suna ƙananun magana.
Allah ya baku haƙuri bani nakar zomon ba, amma kam ina buƙatar na kwanta bazan kuma tauyewa kaina hakki ba dan na faranta muku, da alama baku san kawaici ba.
Ta faɗa tana bin bayansu tare da rufe ƙofarta garam ta ɗan ƙarfi sai tasa key, su Anisa tsayawa suka yi suna kallon ƙofar tare da mamakin maganar data yi musu basu zata tana da baki haka ba, hakan sai ya ƙara wutar tsanar da suke yi mata dan sosai suke taya yayarsu kishi, gashi Rashida ba zata gwadawa Safna komai ba illa ta fita ƙiba da haske, amma batun kyau Safna itace matar nunawa sa’a gata ba tada ƙiba sai kumari da dan tsayi kaɗan, tana da hips da mazaunai wanda nan gaba in taji daɗin auren zasu ƙara bayyana, ga boobs ɗinta Masha Allah ba irin na Rashida ba da suke ƙananu kuma duk sun kwanta. Ita Rashida hasken fata gareta ga tayani muni da idanu ƙanana kamar an tsomawa teba tsaya, sauƙinta tana da ƙaramin baki da hanci wanda sune suka ɗan ƙarawa fuskarta kyau kaɗan, haka suka nufi sashin Rashida suna surutai, suna shiga falo suka ga su Rashida a zaune Amina ta fara da cewa.
Anty Rashida Wlh kishiyar nan taki saikin tashi tsaye da ita dan wlh idanunta a tsastsaye suke da gani ba tada mutunci balle kunya, wai fa koromu tayi ita zata yi barci.
Aini ta gama shayar dani mamaki yadda naganta a fuska kamar ba zata yi surutu ba, ashe kallon kitse nakewa rogo, ni ai ta sagar mini da duk wani kwarin guiwa ta, shegiya gata da kyau na ɗauka mummuna ya kwaso.
Cewar Anisa data samu guri ta zauna tana cika tana batsewa, nan fa suka cigaba da zagin Safna, Rashida dai ta cika tayi fam kamar zata fashe, tunaninta Allah ya bata damar da zata nakaɗawa Safna dukan tsiya ko ƙila ziciyarta zai rage mata raɗaɗin abinda take ji dangane da ita, ta cigaba da lissafin yadda zata hana mata kwanciyar hankali a gidan har sai ta bar mata gidanta.
**
Safna.
Tana rufe ƙofar ta dawo ta zauna a cushing ta tallabe kuncinta da hannu biyu tana mayar da numfashi, dan sosai taji fargaba da maganar da tayi musu bata ma san tana da jarumta har haka ba, koda yake tunda taji zuciyarta da numfashinta yana wani iri tasan mutanen jikinta sun motsa, wata ƙila suna ɗaya daga cikin taimakon da suka bata ta samu damar korasu, ta sauke hannu tana cewa a fili.
Allah ka haɗani da dabbobin mutane wanda basu san zuru ba, aiko wlh su kai ƙarata gurin Zayyad ɗin in yaso yayi min faɗan, duka ne dai bai isa ba wlh sai dai ya tsaya a bambami, dan bazan ɗauki wannan rashin hankalin nasu ba ina dai dai da lissafinsu.
Tana gama faɗar haka tayi ƙofa ta miƙe ta haɗa kayan gabaɗaya takai kitchen, sai ta tattara datti ta saka a dustbin ɗin da suka aje mata a kitchen, ta wanke kayan da suka ɓata ta dawo falo ta gyara, kana ta kunna turaren wuta na tsinke ta aje shi a cikin ƙarfensa, sai ta koma ɗaki ta cire kayanta ta saka na barcin da ‘yan uwanta suka ciro mata akan tayi amfani dasu jiya, tabi lafiyar gado tana mai koro addu’ar safiya da bata samu yi ba tana kammalawa ta rufe ido, cikin ikon Allah sai barci ya ɗauketa ba jinawa.
Itace har kusan ƙarfe sha ɗaya da rabi tana barci, wanda kiran wayarta ne ya farkar da ita tana dubawa taga yaya Mudan ne, bata ɗauka ba ta tashi ta fito falo ta shiga kitchen ta kunna gas ta saka ruwa a tukunya dan tuni aka ɗauke wuta, kana ta dawo ta zauna bakin gado ta kira Yayanta, koda ya ɗauka suka gaisa ce mata yayi.
Dama Maryam ce ta kiraki da wayata nata wayar ba kuɗi, ina ga sun kamo hanya zasu zo dama tambayarki za suyi ko a tawo miki da littafan makarantarki, nace su barshi tukuna ko daga baya Yusuf ya kawo miki.
Allah sarki to ba damuwa ka gaida su Umma.
Zasu ji Allah ya baku zaman lafiya kanwata ayi ta dai Haƙuri.
Murmushi tayi tace amin kana ta yi masa godiya suka yi sallama. Ko kafin su anty Shafa suzo tayi wanka ta mayar da rigar shaddarta, sosai taji ƙarfi a jikinta dan dama ta kula rashin barci mai kyau da gajiyar jiya shine ya saukar mata da zazzaɓi, sai dai ciwon kai ne yana yi mata kaɗan kaɗan amma shima a hankali zai tafi in dai zata samu barci isasshe. Da su Anty Maryam suka shigo basu ga kowa a tsakar gida ba sai suka nufi sashin Safna, suka buga mata ƙofa ta buɗe kana suka shiga tana murna da ganinsu, Anty Zainaba matar ƙanin Umma tace cikin kulawa.
Ayya takwarata har kin faɗa wlh, aure akwai saka damuwar rabuwa da iyaye ba sauƙi saina Allah, Allah yasa gidan zamanki ne.
Suka amsa da amin sai duk suka samu guri suka zauna, nan ta gaishe su suka amsa fuska sake anty Maryam tana cewa.
Ya kewar gida da baƙunta, naga ma komai tsaf ba wani gyara da za muyi ƙilan dai zaman hira za muyi yau.
A’a fa ina so ku sauya mini zaman kujerun nan sannan ɗayan ɗakin baku gama haɗa gadon ba, ina so ya zama ɗakina wanda muka kwana ya zama na Zayyad.
Safna tana faɗa cikin shagwaɓa, Anty Shafa ta fara dariya.
Iye Safna masu miji anyi gidan kai fa sai iya yi da tsurfa kala kala, to dama ba zamu bar gidan nan sai mun gyara miki ko’ina dan Umma tace kar mu bar miki aiki.
Allah sarki abar ƙaunata Ummata nayi kewarta da Abba wlh sosai.
Ai Safna haka saki saba dan zama in yayi zama dole rashinsu yabi jikinki.
Cewar wata dangin babansu, nan dai suka cigaba da hira wasu kuma suka miƙe suka fara gyara ɗayan ɗakin, dama daki ciki uku ne a cikin falon kuma ko wanne da bayinsa sai kitchen da store a haɗe a falon. Bayan sun shiga ɗakin Safna dan su aje mata akwatinanta da kayan gara na cincin da diblan, anty Maryam ta zauna a gefen gado tana cewa.
Safna babu wata matsala ko?
Safna ta sauke ajiyar zuciya kamar ba zata faɗa musu abinda ya faru ba, amma kuma tana buƙatar shawararsu dan lamarin ba zata iya ita kaɗai ba, nan ta gyara zama ta basu labarin abinda ya faru tun daga jiya har yau sai dai ta ɓoye kusancin aurayyarsu da Zayyad dan wannan sirrinta ne, Anty Maryam ta kalli Shafa tana cewa.
Kinji ba ai wlh biri yayi kama da mutum dama wannan shige matan da tayi da akwai manufarta, dan haka wannan turarukan da Umma tace a dawo mata dasu tayi amfani dasu to ba zata yi ba, dan mutum mai fuska biyu baka iya sanin alƙiblarsa.
Gaskiya kam Maryam ko atamfar da umma tace mu ɗinkawa yara shima ba zamu yi ba, ajewa zata yi a hannunta in wata ta haihu a dangi tayi biki da shi, Allah yace tashi in taimakeka.
Cewar Shafa tana mamakin sauyawar Rashida, Safna tace.
Nifa dama ba zanyi amfani dasu ba, balle ma yadda ta nuna makircinta a kaina ƙiri ƙiri gwara na kama kaina nasan irin zaman da zanyi da ita, ɗan wlh ta tsoratani da halin ɗan Adam.
Ai mun ɗauka soyayyar gaskiya take nuna miki shiyasa umma tace sai dai mu ɗinkawa Hafsa ɗiyar Anty Shafa da kuma Labeeba ‘yar wajena atamfar, In yaso turarukan kuma mu kawo miki kiyi amfani da abinki, amma yanzu shawara ta sauya dan mugu baida kama.
Cewar Maryam, nan dai suka tattauna suka bata shawara akan yadda zata yi taka tsantsan da duk wani rikici da Rashida zata kunno mata, ta kuma kama azkar da yawaita karatun Alqur’ani da addu’a, tunda har ta fara nuna mata haka to lallai itama ta iya takunta.
**
Zayyad.
Wajen abokinsa Saminu ya nufa yayi sa’a ya same shi a ƙofar gidansa ya fito shan hantsi, nan suka zauna suka gaisa yana tsokanarsa amarya, tare da cewa.
Yanzu fa shikenan kayi mana zarra, da muna da ɗai ɗai yanzu ka ƙara ka barmu a baya, nima dai dana samu wasu kuɗi Allah auren nan zan ƙara kasan matanmu sai sunga anyi musu kishiya suke gyara wasu ɗabi’unsu. Yanzu yaushe zaka saka mana rana muje muci girkin amarya.?
Haba abokina sai kace wani auren fari, ba wani girki da zaku ci tunda kunci na Rashida ya wadatar, sannan wlh abokina in ka samu dama kayi auren nan dan kuwa gida biyu maganin gobara, kaga kuwa yau ɗin nan zan fara cin girkin amarya dan nace tayi mana na dare.
Haba abokina baiyi wuri ba, ai bata gama hutun gajiyar biki ba, kuma da alama zaka fara yiwa mutane rowa dan kayi sabuwa.
Hmmm Samuni kasan matsalata bana samun abinci a gidana sai na fi sati banci ba, shiyasa naketa ɗokin na amarya wlh, nasan In Sha Allah tanan na huta da cin abincin waje, Rashida zata san yanzu duk abinda zata yi mini ba zai bani haushi ba tunda ina da madafa.
Gaskiya ne kuma, amma duk da haka daka ɗaga mata ƙafa zuwa jibi.
Ina da mata biyu in cigaba da cin abincin waje, nasan Safna tana da juriya zata yi kuma iya na dare ne, sannan da safe ni zan riƙa yi mana kafin na fita.
Zama da masoyi daɗi in andacewa… Wani waƙar ‘yan hausa film, banga laifinka ba dan duk wanda ya samu rana dole yayi shanya, Allah ya saka mu a danshinku.
Saminu ya faɗa yana ɗan murmushi, Zayyad yace Amin suka cigaba da hira sai wajen ƙarfe goma kafin suka rabu ya wuce gidan Amminsu.
Kuyi haƙuri rasuwa aka yi mana shiyasa Allah ya jikan dukkan Musulmi ya gafarta musu. Mutanen Maiduguri ina miƙa saƙon jaje gareku Allah ya shiga lamarinku ya kawo muku agaji ya mayar muku da alkhairi. Ameen
Part 9
AMARYAR ZAYYAD
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 9.
Zayyad koda ya isa gidansu ya tadda suna ta hada abin karyawa sai ya wuce sashin Ammi ya sameta da ‘yan uwanta ya gaishe su kana ya fito ya wuce ɗakin Mukhtar ya samu baya ciki sai ya rage rigar jikinsa ya kwanta a gado dan ya huta, dama ya bawa yaran aikinsa hutun kwana biyu sai monday zasu koma aiki. Dangin Zayyad sai wajen ƙarfe ɗaya da rabi suka isa gidansa, sashin Rashida suka fara isa sai dai basu samu tarba mai kyau ba, dan gaisuwarsu ma sama sama matan dake falon suka amsa kuma babu wacce ta basu gurin zama, hakan yasa suka fito suka nufi sashin amarya nan suka tadda karamci dan an yi musu tarba mai kyau kamar sun jima da sanin juna, haka suka saje suka shiga hira dama sun tawo da abinci a ƙaton kula dafadukan shinkafa da naman rago soyayye a sama kuma da ɗan yawa, haka suka ci abinci suka ƙoshi, Safna dai tana bedroom ɗinta da aka gyara mata tare da ƙawayenta su Haajara sunata hira, anan ne ma Haajara take cewa Saleema ƙawarsu.
Kin ce in mun zo zaki amsa number ɗin mai maganin gyaran nono da ƙarin kumarin da Safna tasha, gatanan a kusa sai ta ƙara yi miki bayani, dan kinga ramarki tayi yawa ga shi kince kin kusa yaye Ammar.
Saleema ta muskuta da yake an sosa mata inda yake yi mata ƙaiƙayi.
Yauwa Safna bani sirrin gyaran da kika yi dan wlh har baban Ammar ya fara mini ƙorafi, cewa yake ko nawa ne zai bani nayi gyara dan yana son ya ganni nayi dumur dumur.
Maza mutanenmu yanzu fa akan wannan sai kiji yana zancen ƙara aure.
Cewar wata daga cikinsu Hafsa, nan Safna ta ɗaura da cewa.
Sabayar Maman Khadija nasha ya ciko mini da komaɗa, shine sirrin kyau na.
Aiko ba Saleema kaɗai ba hatta ni zan yi ƙoƙarin nimansu dan na kwashi garaɓasa, kin san mace sai da gyara ballw mazanmu na yanzu suna son ganin mace kullun ‘yar cakaras.
Cewar Hafsa, sai duk suka saka dariya haka suka cigaba da hira gwanin sha’awa. Zuwa yamma lis mutane sun fara watsewa waɗanda suka rage suka gyarawa amarya ɗaki suka saki turare, su Anty Maryam suka ɗiba kayan gara suka kaiwa uwargida nata, daga bisani sai ga Zayyad yazo da mota ya ɗibesu harda Safna zuwa can gidan Ammi, sun samu tarba mai kyau nan suka danƙa amanarta ga mahaifiyarsa tare da kayan gara da atamfa mai kyau da turaren wuta haka suma dangin ango suka haɗawa amarya kuɗi dubu goma sha biyu kamar dai yadda ake yi a al’adar malam Bahaushe, sai gabda magrib Zayyad ya mayar dasu suka yiwa Safna sallama suka tattara yanasu yanasu suka koma gida. Ɗaki ya rage daga ita sai halinta, a sannan ne na tuna da miyar tuwon da bata yi ba, dan tuwon ma Haajara ce tayi mata, miyar ne tace in an watse sai ta ɗaura, ba ɓata lokaci ta shiga kitchen ta soma aiki data gama ɗaura sanwa sai ta fito ta yi alwala ta gabatar da sallar magrib kana data idar ta koma kitchen ta ƙarasa miyarta, ta sauke ta ɗumama miyar stew da umma ta aiko mata dashi wanda yaji tsokar naman sa a ciki, ta sauke ta kashe gas, sai ta juye ruwan wanka ta mayar da wani taje ta yi, da ta fito ta shirya cikin wani leshi riga da siket ɗinkin ya zauna a jikinta, duk wani saƙo da lungu ta saka turare sannan ta yi kwalliya a fuskarta tayi kyau, a lokacin an kira sallar isha’i sai da ta gabatar da shi kafin ta ɗauki wayarta ta fito falo ta zauna ta fara kallo a tv, ba jimawa Zayyad ya ƙaraso gida yayi parking mota, da gudu yara suka isa gareshi suna yi masa oyoyo ya fito ya kama hannun Aslam suka wuce sashin Rashida, ya samu guri ya zauna a falo dan baƙin sun tafi sai Anisa da Zulaiha ne suka rage suma suna ɗakin yara suna danna waya, Rashida ta fito daga ɗakinta sanye da ƙananun kaya riga da wando sun matseta, da fara’a ta ƙaraso ta zauna kusa da shi tana ƙamshin turare.
Madam kinyi kyau fa, yaushe rabon dana ga kin saka waɗannan kayan.
Kai Abban Ilham banda sharri, ina sawa fa Allah.
To shikenan yanzu kije ki saka hijab muje sashin amarya na haɗa kanku.
Ko dai ita tazo ta same ni ba, haba Zayyad ya kake abu sai kace baka san yadda ake yi ba, ai nice babba.
Afwan ganin ita baƙuwa ce yasa nace muje amma bari naje na yi mata magana ta zo.
Da dai yafi, dan wutsiyar raƙumi yayi nesa da ƙasa.
Ta faɗa tana cuno baki, girgiza kai Zayyad yayi yana dariya ya miƙe suka fita tare da yaran zuwa sashin Safna, sallama ya fara yi kafin ya buga ƙofar a hankali, da sauri ta miƙe ta isa ƙofar dan tasan shi ne ta buɗe, ƙamshinta ya gauraye da iskar shaƙarsa kallonta ya tsaya yi cikin wani irin shauƙi, dan sosai tayi masa kyau ga ƙamshinta da ya soma gigita tunaninsa.
Sannu da zuwa Sirrin Safna.
Yauwa Ƙaunata. Ɗauko hijab muje sashin Rashida na haɗaku.
To tace masa kana ta juya zuwa bedroom ɗinta ta ɗauki hijab ta saka ta fito, ta samesu a kofar ɗakin suna jiranta ta rufe ƙofa suka wuce gaba tana binsu a baya. Da sallama suka shiga falon sun tadda Rashida ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya kai ba ɗankwali ko hula tayi parking gashi, kallo ɗaya Safna tayi mata ta kawar da kai ta samawa kanta gurin zama shi kuma Zayyad ya zauna kusa da Rashida yana cewa yara suje ɗakinsu suka wuce.
Ina yini maman Ilham.
Lafiya lau antynsu Ilham ya baƙunta da rashin sabo.
Alhamdulillah.
Safna ta bata amsa a taƙaice, sai Zayyad ya ɗaura da nashi bayanin, nasiha yayi musu sosai da kuma irin yadda yake so su haɗa kansu, ya ɗaura da cewa.
Rashida kece babba idan Safna tayi miki ba daidai ba ki sameni ki faɗa mini In Sha Allah zan tsawatar, haka kema Safna ki yiwa Rashida biyayya saboda ta girme miki sannan itace uwargida kafin ke, matsayi ne da Allah ya bata nasan kuma zaki bada haɗin kai. Batun girki ko wacce zata riƙa girkinta wacce keda miji tayi da shi wacce kuma ba ita ce da miji ba ta girka abinda zata ci, cefane da abinci duk ko wanne da shi nasan wannan In Sha Allah zai kawo zaman lafiya, sannan na yanke kwana biyu biyu zan riƙa yi a kowani ɗaki, da fatan wannan tsarin yayi muku, in da mai tambaya ko magana sai yayi.
Ni dai ba abinda zance domin tsarin yayi, Allah ya bamu zaman lafiya.
Suka amsa da Amin Zayyad yace.
Bari muje sai zuwa anjima zan sake shigowa.
Ya ƙare maganar yana miƙewa Safna ma ta miƙe suka wuce, da dogon harara Rashida ta bisu dan bata amsa saida safen da Safna tayi mata ba, suna fita ta ja tsaki tana cewa.
Munafukan banza kawai.
Ta miƙe ta mufi ɗakin yara dan ta faɗawa su Anisa yadda suka yi. Koda ta basu labari maganganunsu suka yi suna cewa ta tashi tsaye karta ɗauki raini, daga bisani Zuliha tace.
Anty kin aika musu da abincin kuwa?
Ohhh kinga na manta bari na haɗa sai ki kai musu.
Tana faɗa ta isa kitchen ta haɗa kulolin abinci guda biyu shinkafa da miya sai kosilo a ƙaramin faranti ta fito dashi falo tana kwalawa Zuliha kira, ta fito ta amsa tiren ta wuce ta fita zuwa sashin amarya.
Safna kuma suna shiga Zayyad yace ta kawo musu abinci, ba musu taje kitchen ta haɗo komai a babban tire tazo da dire a carpet nan suka zauna suka ci abinci tare da Zayyad yana zuba mata santi, suna tsaka da ci ne suka ji bugun ƙofa wanda duk in aka buga sai ƙirjin Safna ya faɗi, Zayyad ya miƙe ya isa ƙofar ya buɗe ganin Zaliha da tire niƙi niƙi da abinci yasa shi mamaki kafin yayi magana tace.
Anty Rashida ne tace na kawo muku.
Ikon Allah ai yau amarya ta fara girki yanzu haka abincin muke ci ki mayar mata dashi, dana san zata yi ma dana ce ta bari.
To Zaliha tace cike da talaici ta juya, shi kuma ya rufe ƙofa ya koma ciki yana mamakin wai Rashida ta yi musu girki, matar da sai ya dawo daga shago bata ɗaura komai ba sai a lokacin ne zata ce masa me zata dafa, girgiza kai yayi bai cewa Safna komai ba dan yasan taji maganarsu suka cigaba da cin abinci. Bayan sun kammala Safna ta mayar da kayan kitchen ta gyara gurin kana ta juye masa ruwan wanka ta kai masa bayin ɗakinsa, ya bita a baya ya shiga yayi wanka ita kuma tana zaune a gefen gadonsa, ya fito ya shafa mai ya saka jallabiyar data ciro masa ya saka yana cewa.
Nan ɗakin ya zama nawa ni kaɗai kenan?
Namu dai amma kuma komai naka yana nan, in ba ni bace da girki zan kwana a ɗakina, in kuma na amsa zamu kwana tare.
Na ɗauka tunda ya zama nawa ni kaɗai zan kwana a ɗakin.
Uhum ni dai ba haka na tsara zan rayu a gida sirrin ruhina ba, in dai yana tare dani to tabbas numfashina da nashi zasu riƙa gauraya guri guda.
Ashe ni ɗan lelenki ne.
Ya faɗa yana tsayawa a gabanta ya kamo hannunta ta miƙe suna fuskantar juma, yadda yake jifanta da wani kallo yasa ta sunne kai ƙasa tana ɗan murmushi.
Da alama wannan kunyar sai na kakkaɓe sauran daya rage, dan naga zai riƙa kawo mini cikas.
Ni dai kaje ka dawo dan ina buƙatarka kusa dani a irin wannan lokacin.
Ta faɗa tana cire hannunta a nashi, murmushi Zayyad ya saki sai ya wuce ya fice kwakwalwarsa yana maimaita masa maganganunta da suka yi tasiri a zuciyarsa, sosai yaji daɗinsu tare da hango tabbas farin cikinsa yana tare da Safna. Yana shiga falon Rashida ya samu ba kowa sai ya wuce ɗakinta ya tura ƙofa yaga tana zaune a gefen gado tana tsare hawaye, da sauri ya isa gareta yana tambayarta ba’asi, banza tayi masa tana ƙara haɗe girar sama da ƙasa.
Rashida saboda kin san zubar hawayenki yana ɗaga mini hankali shiyasa kike hukuntani dasu ko.
Zayyad tun ba aje ko ina ba kana niman wulaƙantani, yanzu fisabilillah ya dace in aika muku da abinci kasa a dawo mini sash, wannan ai cin fuska ne.
Zayyad ko da ta kai aya a maganarta kallonta yake yi yana mamakinta, ta ɗaura da cewa.
A gaban amaryarka kasa a dawo mini da abinci ai wannan raini kawai kake son jawo mini, koda ba zaku ci ba ai yaci ace ka amsa kun saka albarka in yaso sai ka dawo mini da sauran, kaga ka mutuntani a gunta.
Hmmmm dana san zaki aiko da abinci zan ce ki barshi domin na riga na sata ta yi mini girki, kuma cikin ikon Allah koda na dawo ta kammala tana jirana, tayi wanka ta tsaɓa ado jikinta da ɗakinta ko ina yana ƙamshi, wannan ya tabbatar mini da na samu mai sharen hawaye na, kuma in da ace naso kiyi mana girki ai zan kiraki nace ki girka, dan haka banga abin kuka ko jin haushi ba dan nace a dawo miki da abincinki ba, in kinyi dan ki burgeni ne to wlh ba kiyi ba, tuntuni haka na so ki riƙa yi amm ba kiyi, kin nuna ke ga yadda kike so shiyasa na rabu dake ban takuraki ba, ɗan haka ki sani ni yanzu babu abinda sa kiyi ya bani haushi dan ina da wacce zata faranta mini.
Abinda zaka ce ma kenan? Zayyad duk son da kake ikirarin kana yi mini ashe daɗin baki ne, ba aje ko ina ba kana son nunawa banda sauran amfani a gunka.
Ta ƙare maganar tana dubansa idanunta suna zubar da kwallar baƙin ciki, Zayyad ya taɓe baki yana ɗage kafaɗa.
Kece dai kika yiwa maganata fassara amma ai gaskiya na faɗa, dama ce nake baki domin ki gyara kuma da bana sonki bazan kawo iyanzu ina zaman aure dake ba, soyayyar yasa nake ta haƙuri da matsalolinki, kuma ko yanzu auren da nayi ba zai sa na juya miki baya ba kina nan a matsayinki a zuciyata.
Hmmm kawai ta iya cewa ta cigaba da matsar kwalla, Zayyad jin tayi shiru yasa shi shima yin shuru sai ma ya ciro wayarsa ya shiga facebook yana duba pages ɗin mutane, shi dai yasan gaskiya ya faɗa mata in taso ta gyara in taƙi karta gyara shidai yanzu ya samu wacce zata faranta masa, ganin ya kai kusan minti ashirin a ɗakin ya sashi miƙewa.
Ni zan je na kwanta sai da safe, in kuma da abinda kuke buƙata ki faɗa mini dan bana son buga ƙofa da sassafe.
Yanzu kena duk uzurin daya taso mini ban isa in zo in tashe ku ba sai na jira ka fito, wato haka amaryar taka ta tsara maka kenan.
Kina so ki tsuro da halin da ban taɓa tunan kina dashi ba, meyasa ina yabonki sallah amma zaki kasa alwala.
Ni ban sauya ba kaine dai amarya ta soma sauyaka, da alama bani da ta cewa sai abinda ta tsara maka, Allah dai yana ganin komai.
Ta ƙare maganar cikin kuka, wannan karan tsaki Zayyad yaja ya juya ya fita dan in ya biye mata ɓata masa rai zata yi, ya kula lallaɓata da yake yi ne yasa take niman wuce gona da iri, duk da baya jin daɗin ganin tana kuka amma ya zama dole ya rabu da ita dan ba zata caja masa kai ba cikin daren
Part 10
AMARYAR ZAYYAD
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 10.
Rashida da kyar barci ya ɗauketa a wannan ranar sosai ta kuma ƙullatar Safna da zayyad ɗin, hakan yasa ta yi fushi dashi bata kula shi iya gaisuwa kawai ke shiga tsakaninsu, har Safna ta gama kwana bakwai na amarcinta, a ranar Safna da kyar ta bari Zayyad ya fita aiki dan sosai ta langwaɓe masa akan kewarsa da zata yi, koda ya fito sai ya wuce side ɗin Rashida ya samesu a falo, ya zauna yana amsa gaisuwar su Zaliha suka miƙe suna cewa in zai wuce ya rage musu hanya zasu wuce gida, yace to kana suka wuce ɗakin yara dan fito da jakar kayansu. Zayyad ya kalli Rashida fuskarsa sake.
Uwargida har yanzu fushin ake da Zayyad ne? Ya kamata a sausauta masa haka tunda yau kece da shi, da fatan zai samu kyakkyawar tarba.
Kai da kace duk abinda nayi ba burgeka zanyi ba ai babu wata tarba da zaka samu.
Nifa ba haka nake nufi ba, meyasa kike da nacin magana ne da yawan ƙorafi, to kiyi haƙuri komai ya wuce, ki rubuta mini abinda babu ta text anjima zan aiko Jamilu ya kawo miki.
To adawo lafiya dama naso zan je gida kafin yamma na dawo.
A’a ba zaki ko ina ba ki bari sai wani satin.
Dan Allah ka barni na tafi kusan wata kenan ban leƙa ba, bazan jima ba zan dawo.
Amma ki rasa ranar da zaki fita sai ranar girkinki, meyasa haka ne? sannan yara in sun dawo fa.
To baga antynsu ba sai su zauna a gunta kan na dawo.
Hmmmm ba zaki je yau ba, ki yiwa su Zaliha magana su fito mu wuce.
Ya ƙare maganar yana miƙewa ya fice zuwa waje, Rashida cike da takaici ta kwalawa Anisa kira suka fito sai ta rakasu har mota tana cewa.
In Sha Allah ina nan zuwa gobe in Allah ya kaimu ku gaida su mama.
Suka amsa da to kana Zayyad ta tayar da mota ya wuce. Ta koma ɗaki ta zauna tana jin ba daɗi saboda ba kowa sai ita kaɗai, su Ilham sun tafi hadda sai wajen biyu na rana zasu dawo ga duk baƙinta sun tafi, a wannan lokacin ne taji sha’awar son ta ƙara wani haihuwa, dan tun bayan data haifi Aslam ta saka implant na shekara biyar, to gashi Zayyad ya ƙara aure ya kamata ace ta cigaba da haihuwa kafin amarya tazo ta fara nata, burinta ace tafita yawan yara, dan haka tunanin ya tsaya mata a rai da nufin dole ma taje gida gobe daga nan ta wuce asibiti a cire mata implant ba tare da ta sanar da Zayyad ba, dan tasan in ta sanar dashi bazai bari ta cire ba tunda ba son haihuwar yake sosai ba, in kuma ta biye masa itace zata kwan ciki har amarya tazo ta fita haihuwa gwara ace nata yaran sun fi yawa, da wannan tunanin ta miƙe ta nufi ɗakinta ta zauna ta ɗauki waya ta kira ƙawarta Kubura, koda ta ɗauka suka gaisa take ce mata.
Nayi baƙin cikin bikin nan bana nan, amma da zarar na diro gari zaki ganni, wai Rashida kina miye ne har kika bari auren nan ya tabbata?
Ya zanyi to Kubura ƙaddara ta riga fata, gashi ba aje ko ina ba Zayyad yana son nuna mini halinsu na maza saboda yaji sabon guri.
Hmmm ai wlh kece kika yarda amma kin ganni babu wata ɗiya da zan bari ta shigo mini gida wai sunan kishiya, ga Aliyu nan yasha gwada yin auren da magana ta taso za kiji ta kwaranye to an gaya miki zama zanyi, ai ba zan bari ma magana tai kwari ba balle ayi aure, kema tuntuni naga kinyi sakwa sakwa ne amma ko yanzu bata ɓaci ba.
Ni gwara dai ki dawo muji ta ina zamu ɗaura, dan wlh inna cigaba da ganin Zayyad da wata za’a wayi gari aji nayi mushe zuciyata tayi bunga.
Hmmm kisha kuruminki, akwai wani magani ɓata gaban kishiya zan haɗo miki su ki tsuma kanki, ta yadda idan ya kusanceki wlh ita da shi sai rabo in ya tsaga, sannan batun sauran mallakan suma zan sa yayana ya haɗa miki, kin san mu gidanmu yayi ƙaurin suna da malinta.
Kamar nawa zan turo miki? dan ina buƙatar maganin matan nan sosai, da dai bana sha amma yanzu kuwa ba sanya.
Zan je gidan innata itace ke sayarwa duk yadda muka yi anjima zan faɗa miki, har da mallakan da zan amsan miki guri yayana.
Rashida cike da farin ciki ta soma zuba mata godiya tana cewa in ma bata kira ba ita zata kirata tunda itace ke buƙata, haka suka yi sallama tana sauke numfashi cike da tsantsar farin ciki, dan kam a yanzu bata ga zama ba burinta ace ko Zayyad bai saki Safna ba amma ta zama hoto a gurinsa ta yadda ko dabba sai ta fita daraja.
Bayan sallar isha’i.
Safna ta fito wanka duk jikinta ba kwari duba da yau ita kaɗai zata kwana sai duk take jin kewar ‘yan gidansu, kamar ta buɗe ido ta ganta a cikin gidansu tare dasu yaya Mudan suna tsakusawa. Zama tayi a gaban madubi tana sanye ta siket underwear ta daga shi sama zuwa ƙirjinta da yake yana da ɗan tsayi ya kai mata rabin cinya, kuma shi kaɗai ne a jikinta ba pant ba bra, ta shafa mai ɗinta mai kyau wanda yake ƙaramata laushin fata, data gama ta ɗauki turaten humra tana bin fatar jikinta tana shafawa tare da duk wani joint na jikinta hatta bayan kunne ta shafa, kana ta miƙe ta ɗauki body spray ta fesa a hammatarta bayan ta saka asalin turaren hammata wanda yake ɗauke gumin zufa, sai ta tuna da indimie ɗinta data ɗaura a gas a low heat, da sauri ta fita kitchen ta duba taga da sauran ruwa sai ta ƙara gas ɗin ta fito falo, a lokacin mbc max sun saka wani action film daya ɗauki hankalinta, sai ta zauna hannun kujera tana kallo dan dama taso taje ɗaki ne ta saka kayan barcinta. A lokacin taji dirar motar Zayyad tasan ba ita ke da girki ba shiyasa bata damu ba ta cigaba da kallo, bayan kamar minti goma ta miƙe ta isa kitchen ta juye indimie ɗinta da dafaffe kwai guda biyu data ɗora a sama ga kuma naman kaza data saka a ciki guda daya, ta fito falo ta aje a center table dan ya sha iska ta ci.
…
Zayyad yana shiga falo ya tadda yara suna kwance kamar marasa lafiya babu wani karsashi a jikinsu, ko dan oyoyo da suka saba yi masa bai gani ba, ya zauna yana cewa.
Mamana me yake damunku na ganku haka, Abbana yaya lafiya kuwa?
Ya faɗa yana dubansu, kafin su bashi amsa sai ga Rashida ta fito daga kitchen tana cewa.
Yunwa suke ji shine ka gansu kamar anyi musu mutuwa.
Meyasa baki basu abinci ba gashi har takwas ta wuce.
Kasan wake wahalar dahuwa yake mini, har yanzu yana kan wuta ban ma saka shinkafar ba.
Da kallo Zayyad ya bita har ta ƙaraso ta zauna a cushing cike da takaici.
Kina nufin baki gama kirgin ba? Tun yaushe kika ɗaura? Ko gas ya ƙare ne?
Akwai gas miya na ɗaura anan itama ta kusa yi, waken yana kan electric.
Da yaushe kika ɗaura girkin nan Rashida?
Wlh barci ne ya shammace ni da yamma sai bayan magrib na samu damar shiga kitchen, yanzu ma nake shirin yin sallar isha’i.
Zayyad shuru yayi ya mike yana duban yaran.
Ilham ga kankana da lemu ku fara sha kafin ta gama muku abincin, ina zuwa.
Ina kuma zaka je?
Zan kaiwa Safna nata kankanar.
Ya bata amsa a takaice, Rashida ta miƙe tana cewa.
Ka aika Ilham ta kai mata mana, ko ka bari anjima in zaka shiga gabaɗaya ka bata.
Saboda ke haka nake yi miki ko, inna shigo da abu yara nake kira su kai miki ko kuma in zan zo na ganku gabaɗaya shine zan kawo miki. To baki isa ki tsara mini yadda zanyi a gidana ba.
To ba sai ka bari in kaci abinci ka shiga ba.
Hmmm kawai ya ce ya fice riƙe da ledar fruit ɗin Safna, yana isa ƙofar ya buga mata tare da yin sallama da sauri ta aje cokalin data fara cin abinci ta isa ƙofar ta buɗe masa, ta ɗauka miƙa mata saƙo zai yi dan tasan haka yake yiwa Rashida amma sai taga ya raɓeta ya shigo ita kuma ta mayar da ƙofa ta rufe tana yi masa sannu da zuwa, ko kafin ta yi aune ya fizgota zuwa jikinsa ya rungumeta yana shaƙar ƙamshinta, ita sai yanzu ne ta tuna daga ita sai underwear, Zayyad ya ɗago fuskarta cike da tsantsar kewarta.
Kaunata ƙamshin ki ya gigitani, ji nake yi kamar zan suma dan daɗi.
Siirin Ruhi shifa nake shafawa in zan kwanta.
A’a wannan ya bambanta dana kullun ban yarda da guda ɗaya kike amfani ba, gaskiya zaki tsammini wannan ƙamshin daga jikinki yadda zanyi barci cike da begen ki.
Ka rufa mini asiri kar Anty Rashida ta ji ba daɗi, ni cikani ka tafi anjima ka dawo.
Korata kike yi saboda kin daina sona umm?
Ya ƙare maganar cikin marairaicewa, Safna ta saki dariya ta wuce zuwa cushing ta zauna tare da ɗaukar cokali tana cewa.
Ni ɗin banzana zan kori Ruhina, kawai dai bana son shiga hakki ne.
Amma ai ke halas ɗina ce zan iya aikata komai dake ba haramci. Sannan da in fita waje in nima a gurin wata banza fa bayan ina da ke.
Gamu dai zaka ce dan Anty Rashida itama macece.
Na kula kina mugun ji da yayar nan taki.
Ya fada yana ƙarasawa gaban center table ɗin ya zauna gefenta ya jawo shi gabansa ya amshe cokalin ya fara ciki yana cewa.
Cin abincin ba tayi saboda kin fara koyan rowa ko, to wallahi wannan rabona ne ki tashi ki shiga kitchen ki dafa wani.
Haba Zayyad ya zaka yi haka wlh bazan ji daɗi ka ci abinci anan ba bayan kasan bani ce da girki ba.
Safna kiran sunana gatsai haka ba ko sirki, gidana kuma ɗakin matata babu wanda ya isa yayi mini sharaɗi akan duk abinda zan aiwatar.
Yana gama faɗar haka ya cigaba da cin indomie ɗinsa, Safma dai shuru tayi ta rasa me zata ce masa sai tunanin zucci, amma har ga Allah bata ji daɗin haka a ranta ba dan ba zata so a ranar girkinta yayi mata haka ba, Zayyad ya kusa cinye abinci sai suka ji bugun ƙofa da mugun ƙarfi wanda yasa Safna sai da ta miƙe tsaye a tsorace tana dafe da ƙirjinta dan ba ƙaramin tsorata tayi ba kuma dama da tunanin Rashidan a ranta, Zayyad ya dubeta yace.
Koma ki zauna.
Ba musu ta koma ta zauna, ya cigaba da cin abincinsa kuma Rashida bata fasa buga ƙofar ba, sai da ya gama tas ya cinye komai dan hatta kwai da naman bai ragewa Safna ba, ya kora da ruwa ya miƙe yana dubanta.
Allah yayi miki albarka sai na shigo anjima.
Yana kaiwa nan ya juya yayi hanyar ƙofa ita dai Safna da kallo ta bishi dan sosai buga ƙofar nan ke razanata, ya buɗe ya fita tare da jan ƙofar, nan ta tsinkayi muryar Rashida tana cewa.
Zayyad ni zaka wulaƙanta kana ji ina buga ƙofa baka buɗe ba, sannan daga zaka miƙa mata abu shine zaka yi zamanka wannan adalci ne.
Bai kulata ba ya wuce abinsa.
Na rantse da Allah ban yafe ba kuma wlh sai ka faɗa mini mai ka tsaya yi?
Bata rufe baki ba ya juyo a fusace ya wanke ta da mari ya ɗaura da cewa.
Abinci na tsaya ci ko kin isa ki hanani ci ne, idan ke bakya buƙatar lada ita tana buƙata kuma tasan daraja na, wlh daga yau muddun na dawo baki gama girki ba to a ɗakin Safna zanci abinci baki isa ki cigaba da jana a ƙasa ba saboda kin raina ni, na wuce zama da yunwar da kike hukunta ni dani da yarana, ni yanzu ina da madafa. Idan kinyi zuciya ki gyara.
Yana gama faɗar haka ya wuce abinsa.
Ni ka mara akan hakkina, Wlh bazan yafe wannan ba.
Rashida ta faɗa cikin kuka ta bi bayansa, Safna dake jikin window duk taji komai jikinta ba bubu inda baya rawa, daga zuwanta ace sun fara samun matsala, ba zata so ace ita ta zama sila ba, ta koma jiki ba kwari ta zauna a cushing.
Dama ya auro ni ne domin na zame asa sanyin idaniyarsa, ashe Rashida bata cika macen da ake buƙata ba, taya zai dawo iyanzu bata gama girki ba wannan ai sakarci ne, ni dai bana so ta ƙullaceni wlh.
Duk wannan maganar a zuciya take yinsa, data ga ba zai fissheta ba ta miƙe ta isa kitchen ta ɗaurawa kanta wani indomie zuciyarta sam babu daɗin abinda ya faru.
…
Rashida tunda suka shiga falonta ta shiga surfa masa masifa tana yi tana kuka, Zayyad bai iya ce mata komai ba yayi shuru yana saurarenta har sai da ta gaji dan kanta kafin ta wuce kitchen ta duba girkinta, a lokacin Zayyad ya miƙe ya kamo hannun Aslam ya cewa Ilham ta tashi, ya kama hannunsu suka fito suka shiga mota, sai dai Rashida da Safna suka ji tashin motarsa mai gadi ya buɗe masa gate suka fice daga gidan.
Bai zame ko ina a sai wani joint na masu sayar da tsire ya siyawa yaran, kana ya wuce suka siya yoghurt sai ya samu wani guri a cikin wani layi yayi parking yace yaran su ci, haka suka riƙa ci a yunwace dan rabonsu da abinci tun da rana a makaranta, dan ko da suka dawo gida basu samu abinci ba sai cake data basu suka ci. Sai da suka cinye komai tas suna gyatsa ya tabbatar da sun ƙoshi kana ya tada mota suka kamo hanyar gida, ko kafin su ƙaraso yaran sunyi barci, da ya shigo da mota yayi parking ya tashi Ilham sai ya ɗauki Aslam suka wuce ciki, a falo suka tadda Rashida ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana girgiza ƙafar data ɗaura a cinya.
Part 11
AMARYAR ZAYYAD
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 11.
Zayyad ko da ya shiga ɗakin yara sai ya kwantar da Aslam, Ilham ma ta kwanta a gadonta yayi musu addu’a ya kashe musu wuta kana ya fito ya nufi sasshin Safna, duk Rashida tana falo ya fice basu tanka juna ba, haka ya yi minti sha biyar a sashin Safna kana suka yi sallama ya fito ya dawo, bai ga Rashida a falon ba sai ya rufe ya shiga ɗakinsa ya kwanta tare da kunna data, yasan halinta in tayi fushi to sai ya bita yana rarrashi, yanzu ko rabuwa yayi da ita tunda ba wani abu yake nima a gurinta, dan yana da Safna koda yaji shi a matse zai je can ya sauke nauyi ya dawo dan bata isa ta juya shi ba.
Da safe bayan ya kai yara makaranta kasantuwar Sunday ne baya fita sai da rana, haka ya dawo ya shiga kitchen ɗin Rashida ya tadda bata yi breakfast da shi ba sai ya shiga fere dankalin turawa yana yankawa har ya kai yadda zai iya cinyewa kana ya ɗaura mai daya gani a fan a gefe, ya soya dankalinsa ya fasa kwai shima ya soya sannan ya haɗawa kansa ruwan tea, daya gama ya fito falo ya zauna ya cinye kayansa, sannan ya mayar da kayan kitchen ya wuce ɗakinsa ya shirya dama tun asuba yayi wankansa saboda ya saba da yi koda bai yi wani mu’amalar aure ba ko mafarki, wajen goma saura ya fito ya nufi sashin Safna bai nima Rashida ba kamar yadda itama bata nimeshi ba, tana ɗaki tana jin motsinsa amma fushi yasa ta watsar da shi. Ya samu Safna cikin kwalliyar doguwar riga ready made kanta ba ɗankwali tayi parking gashinta, ya zauna suka gaisa yana dubanta.
Ya kamata kannan kiyi kitso.
Ban san ina zan samu mai kitso ba a unguwar nan, nima kan ya isheni amma nafi so saina ƙara wankewa.
Ya kamata, kuma can saman titi akwai wata mai saloon kamar har da kitso suke yi sannan musulma ce.
In ka lamince mini za je nayi In Sha Allah amma sai zuwa goben.
Allah ya kaimu ni zanje gidan Ammi daga can zan wuce shago.
Ka gaisheta, ni yaushe zan fara fita ne?
Sai kinyi wata uku.
Ido Safna ta waro waje, tana ‘yar dariya.
Sai kace auren mutanen da, ina laifin in nayi waya guda dai na je gida ina son ganin su Umma.
Uhum tukuna dai bari muga zuwan lokacin, anjima ki dafa abinci dani.
Kallonsa tayi sheƙeƙe alamar tambaya, sai ya kanne ido ɗaya yana murmushi.
Eh kin ji me nace ai, kiyi abinci dani ko miye zanci sai na dawo.
Ya miƙe yana gyara zaman hularsa tace Allah ya tsare sai ya amsa da amin kana ya wuce ya fita, taje ta kulle ƙofarta da key dan sosai take jin tsoron Rashida bata son abinda zai haɗasu domin bata son faɗa. Zayyad ya kunna mota kenan Rashida ta fito da sauri ta isa window motar ta tsaya tana cewa.
Nifa zan je gidanmu ka bani kuɗin mota.
Bai ce mata komai ba ya ciro kuɗin motan dubu ɗaya ya bata, tana amsa ya ja motarsa ya fice ita kuma ta koma ciki ta sauya kaya dama tun ɗazu tayi wanka, bata tsaya gyara gidan ba sannan ko wanke wanke bata yi ba ta shirya ta fito ta rufe ƙofar ta kama hanyar gidansu.
Koda ta isa gida ta samu Zaliha tana nan amma Anisa ta fita, ta zauna a falonsu tana duban Mamansu da suka gama gaisawa.
Mama na gaji da auren Zayyad wlh wulaƙantani kawai yake yi saboda yayi auren nan.
Hauka kike yi halan da kaka ce kin gaji da aurensa, to me akayi da ‘yan maza ai zama ba fashi.
To ya zanyi Mama? gabaɗaya na rasa ta ina zan karkato da hankalinsa kaina.
Har yanzu da sauranki Rashida shi namiji ai sai annuna masa da gaske ana sonsa shine za a zauna lafiya, dan haka zama bai ganki ba.
Shiyasa nazo dan naji ta ina zan shawo kan matsalata, sannan ma ina so naje asibiti a cire mini implant ɗin nan.
Ba dai kin biye masa ba kina wani tsarin iyali, aiko ga amarya nan tana fara zuba kwai zata kamo ki, dafa yanzu kinyi haihuwa ya kai huɗu zuwa biyar amma saboda kin biye masa gashi ba a je ko ina ba ya yi aurensa, kuma in baki wasa ba haka zaki cigaba da zama ‘yar kallo.
Cewar mamanta tana taɓe baki, Rashida tayi kwaɓa kwaɓa da fuska kamar zata fashe da kuka.
Mama ya zanyi?
Bari in shiga bayi inyi wanka ina zuwa.
Maman ta bata amsa tana miƙewa ta wuce, Zaliha ta muskuta gurin Rashida.
Anty wlh sai kin cigaba da haɗa mata makirci kamar yadda Anty Wasila tace dan na kula wannan kishiyar taki a tsaye take.
Rashida ta tallabe haɓarta tana jin wani tuƙuƙin baƙin ciki a cikin ranta, tama kasa magana dan takaici.
**
Safna.
Tunda Zayyad yayi mata maganar kitso sai ta fara shirin wanke kanta dan sai ta wanke tayi driying ɗinsa gobe In Allah ya kaimu sai taje kitso, duk da tana da shampoo amma bata yarda tana wanke kai da ruwa mai haske ba sai da ruwan haɗin kayan islamic, shiyasa tun kafin aurenta taje ta siyo kayan buƙatarta ta adanasu dan tafi gane ta riƙa yin gyara dakanta, hatta hand dryer ta saya sabo wanda zata riƙa busar da gashinta koda ya jiƙe, shiyasa kullun kanta yake fidda ƙamshi tunda aka kawota to tana kula dashi tare da shafa masa mai da busar dashi. Ta shiga ɗaki ta ɗauko Ganyen magarya, Ganyen dalbejiya, Habbatus sauda ‘ya’yan Hulba, ta shiga kitchen tayi giretin albasa da tafarnuwa, sai ta haɗa wannan kayan duka a babban tukunyarta ta ɗaura a gas ta kunna tare da zuba ruwa mai yawa ta barshi domin ya tafasa. Sai ta kuma yin giretin albasa ta tace ruwan ta zuwa a ƙaramin kofi ta fito ta shiga ɗakinta ta samu kibiya tana tsaga kanta tare da yayyafa ruwan albasan a ƙasan gashinta, tana cuɗawa har sai da ta tabbatar da ruwan albasan ya gauraye kanta sai ta samu leda ta saka akan, ta ɗauki kofin ta mayar kitchen ta wanke kayan data ɓata kana ta dawo falo ta kunna kallo tana yi tana charting, har sai da ruwan nan data dafa ya tausa dan taji ƙamshinta har falo, taje ta sauke ta kashe gas, kana ta dawo dan ruwan ya huce. Ta ɗauki kusan awa biyu a haka kafin ta ɗauko bokitin bayi ta juye ruwa nan tare da tace shi, ta ɗauka ta wuce toilet ta cire ledar data rufe kanta da shi ta ɗauki shampoo ta soma wanke kan da wannan ruwan maganin, har ta gama tas kafin ta samu ƙaramin towel ta ɗaure kanta dashi ta mayar da komai inda yake ta wanke bayin, sannan ta fito falo ta zauna towel ɗin ya tsane ruwan kanta sai ta fito ƙofar ɗakinta da kum ta taje kan, sannan ta koma ɗaki ta ɗauki hand dryer ta jona a wuta ta busar da gashin, sai ta samu haɗaɗɗen manta mangyada pure one wanda bana gida ba, da man kaɗe data gaurasu ta haɗa su sosai shiga shafawa akan, ta kuma ɗauko man kitsonta da aka saka mata a akwati ta ɗauka ta saka a kai, wanda shima ta saka masa haɗin mangyaɗa da man kaɗe a ciki ta gaurayasu, ta shafa kan yaji mai sai ta kuma saka hand dryer ta narkar da man ya gauraya gashin sai ta taje ta yi parking ɗinsa sai sheƙi yake yi, wannan shine sirrin sumar Safna tana ɓata lokaci gurin gyaransa, wannan haɗin data yi yana taimakawa wajen maganin amosanin kai da dandrop da kuma maganin karyewar gashi ne da kuma ƙarin tsayin sumanta. Ta dawo ta zauna tana tunanin me zata ci da rana, a lokacin ne aka kira sallar azahar ta miƙe taje ta gabatar ta fito ta shiga kitchen ta ɗaura sanwar taliya dan taci da sauran miyarta, ta dawo kenan taji sallama a ƙofarta taje ta buɗe sai taga wata mata ce baƙuwar fuska, da fara’a ta tarbeta suka shiga ciki suka zauna tare da gaisawa.
Ni maƙociyarku ce nace bari na leƙo naga amaryar Rashida.
Allah sarki nagode ya yaran.
Lafiya lau sai naga kamar Rashida ta fita ko, dan nata sallama ba a buɗe ba.
Gaskiya ban sani ba amma da alamar ta fitan tunda har bata buɗe ba.
Safna ta faɗa tana miƙewa ta wuce kitchen ta ɗauki plate ta fito zuwa Bedroom ɗinta da ta aje cincin da diblan ta ɗibo mata sai ta fito taja mata center table a gabanta tana cewa bisimilla, matar tayi mata godiya.
Ai yara ma sun shigo an basu, da alama anyi miki kayan gara da yawa, ace har yanzu bai ƙare ba duba da wannan rayuwa da muke ciki.
Aiko dai da yake ba mutane sosai da suke shigowa shiyasa.
Nan a miƙe dai ta koma kitchen ta saka taliya a ruwan daya tausa, ta fito ta zauna matar tana cewa zata tafi, Safna tace ta tsaya ta shiga ɗaki ta ɗauko leda ta juye mata cincin ɗin ta bata ta yi mata godiya ta fice bata tsaya tambayarta wani gida take ba, dan ba lallai ta shiga ba tunda ita tun asali ba mai son mutane bace kuma tasan duk suna mu’amala da Rashida bata son damuwa. Lokacin da taliyar tayi ta saka ta fito ta zauna tana ci, a lokacin ne su Ilham suka dawo direct ɗakinta suka nufo dan dama Rashida ta faɗa musu in sun dawo su je sashin Safna, suka shiga buga ƙofa tayi sauri ta miƙe ta buɗe, ganin su ne ta ce cikin kulawa.
‘Yan makaranta kun dawo, kamata yayi kuyi sallama ba buga ƙofa ba koda ina bedroom zanji ku.
To suka ce mata sai ta matsa suka shiga ciki, Aslam yana ganin abinci ba magana yaje ya zauna ya soma ci, da kallo Safna ta bishi tana mamakin wannan lamari, sai ta isa gurin plate ɗin ta ɗauka tana cewa.
Ka bari ayi maka tayi mana malam Aslam, ina zuwa.
Ta wuce Kitchen ta zuba musu sauran taliyar data rage akai ta juya musu ta ɗaukowa Ilham cokali ta fito falon ta aje musu a carpet tace suje su ci, sai suka sauko suka soma ci ta ɗauki plate ɗin data zubawa matar nan cincin ta je ɗaki ta ɗibo ta aje a hannun kujera, sai ta shiga kitchen ta haɗa tea ta fito ta zauna ta ci badan ranta yaso haka ba, yunwa take ji kuma ba zata iya jiran ta dafa wata taliyar ba haka ta tusa cincin da tea kuma ta ƙoshi, yaran da suka gama suka bar mata wanda suka zubar a caepet ko wanne yaja kujera ya zauna yana mayar da numfashi dan sun ƙoshi sosai, da kallo ta bisu bata ce komai ba ta miƙe ta tsince wanda suka zubar ta ɗauki plate ta mayar kitchen ta tsaya wanke kayan, a lokacin ne Aslam da Ilham suka miƙe suka wuce bedroom ɗinta suka ga robar cincin a can jikin bango, suka isa gurun suka cicciko hannunsu suka fito falo suka zauna suna ci, Safna data fito ta gansu da cincin sai ta tsaya ta kama ƙugu.
Kai waye ya baku cincin?
Mun shiga ɗakinki mun ɗiba ne.
Da izinin waye kuka shiga har Sakina kuka ɗiba? Ina wasa da ku ne, taya zaku ɗiba abu ba tare da ance muku ba, wannan wani irin tarbiyya aka baku? to bazan ɗauka ba matsawar kuka ga abu ban baku da hannuna kuka ɗaukar mini Allah sai na bigeku.
Ta ƙare maganar ta wuce bedroom ɗinta, nan taga marfin robar akan gado suka barshi ba su rufe ba, tayi ƙofa ta je ta rufe kana ta dawo falon ta zauna tare da shan kunu, ta kula yaran basu samu tarbiyyar daya ishe su ba dan haka dole ne ta ɗauki matakin da kar raini ya shiga tsakaninsu, ba zata ɗauki wannan shashancin ba dole ne ta seta su kuwa, yaran kuma tunda tayi musu faɗa suke cin magani sai wani turo baki suke yi bata bi ta kansu ba har zuwa la’asar, a lokacin ne Ilham ta ɗauki jakarta tana cewa Aslam suje ƙofar ɗaki su jira Mamansu daga nan suyi wasa, kanzil Safna bata ce musu ba suka fice ta mayar da ƙofa ta rufe, sai da ta gabatar da sallah kafin ta shiga kitchen ta ɗaura wake dan tana son cin shinkafa dawake da mai da yaji ne, ta dawo ta kunna data ta soma chart, anan ne taga Zayyad online sai ta tura masa da saƙo kamar haka.
Farin Masoyi ina cike da tsantsar kewarka ya sanda mai ruwa, ya fama da mutane Allah yasa albarka a cikin nemanka.
Ta tura masa, Zayyad ya yi murmushi lokacin daya karanta sai ya bata reply kamar haka.
Sanda mai ruwa gashi nan ya cika taf yana niman inda zai yi ban ruwa, na tabbatar Ƙaunata a kullun tana maraba da shi dan haka ki yi masa tanadin gaggawa dan yana gabda….
Hahaha gabda me? Ƙaunarka tanadin gobe ko jibi take yi maka.
Kinma isa ai wlh sai dai in banyi niyya ba, ko so kike yi na samu wata ‘yar fara a waje ina rage zafi.
A’a wlh ban yarda da wannan mugun wasan ba.
Ta tura masa tare da imoji mai hoton hawaye ɗaya, Zayyad yayi dariya dan yasan ya tabo inda bata so, yasan Safna akwai kishi sai dai yadda take burgeshi bata nuna kishinta akan matarsa ko ta nuna jin haushinta, wani sa’ilin har tare mata take yi.
Ruhin Zayyad kema kinsan ni ɗin wa ku biyu ne kawai In Sha Allah, yanzu me kike dafa mana dan nasan kin ɗaura sanwa baki wasa sa kammala girki da wuri.
Nan ta sanar dashi abincin da zata yi, yaji daɗi domin ya kwana biyu bai ci ba, dan haka yace sai siyo musu latas suci dashi sannan ta dafa musu kwai, to tace masa kana suka cigaba da hirarsu na sakin layi wanda tun aurensu ya fara koya mata, tun tana jin kunya har take biye masa suna yi dan gwara yayi da ita da ace da wata can manza ‘yar kwalta suke yi.
*
Rashida sai gabda magrib ta dawo gidan ta tadda yara a tsakar gida suna buga kwallo, suka yi mata oyoyo Ilham tayi kwaɓa kwaɓa da fuska tana cewa.
Anty ta yi mana masifa sai faɗa take yi mana har da cewa wai bamu da tarbiyya, ni bazan sake zuwa gurinta ba.
Nima bazan je ba, gwara kice mu shiga gidan maman Walida mu jiraki.
Cewar Aslam, Rashida maganar yaran yazo mata wuya wato Safna zaginsu tayi da faɗa, saboda son kai bata tambayi yaran me suka yi mata ba har tayi musu faɗa, sai ta yanke mata hukunci akan bata son su ne, tayi ƙofa ta jasu suka wuce ƙofar ɗaki ta buɗe suka shiga, a sannan ne taga ɗakin ba yadda yake, to bata yi komai ba ta fita, a lokacin ne kuma Zayyad ya dawo dan ranar Lahadi baya fita da wuri kuma yana dawowa gida da wuri, sai duk ta daburce ta rasa ina zata fara gyarawa.
Part 12
Buy Data here Sme data and cable subscription
AMARYAR ZAYYAD
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 12.
Rashida da sauri ta ɗauki tsintsiya ta fara sharar falo a lokacin Zayyad ya shigo da sallama, ta amsa tana ɗan sakin murmushi domin mamansu sosai ta yi mata huɗuba fushin da tayi da shi, shiyasa ta ɗauki aniyar sauyawa domin ta sauya salo, tayi masa sannu da zuwa ya amsa tare da yin hanyar kitchen dan ya saka ruwan wanka saboda yasan bata saka masa a flaks ba, yana shiga yaga yadda ya barshi ɗazun haka ya same shi hakan ya tabbatar masa da Rashida bata daɗe da dawowa ba kuma bata gyaran gidan ba kafin ta fita, hakan ya ƙona masa rai amma in da sabo ya saba, dan haka juyawa yayi ya wuce zai fita ta dakatar dashi da sauri.
Ina kuma zaka je? Me zan dafa mana ne.?
Zayyad ya juyo yana dubanta da kyau.
Rashida bana buƙatar komai kuma ki daina yi mini tambayar ina zani tunda ni ba ɗanki bane.
Amma ai naga yanzu ka dawo kuma nice da girki.
Ashe ma kin san ke ce sa girki shine zaki je kiyi zamanki baki dawo da wuri ba, sannan kin fita baki gyara gidanki ba wannan wace irin rayuwa ce.
To ai yanzu zan gama komai In Sha Allah, bari na saka maka ruwan wanka a kettle.
Ki barshi kawai dan kinsan bana son jira, kuma yanzu ba ke kaɗai bace ina da damar da zanje inda zan samu farin ciki. Aslam zo muje ɗakin antynku.
Ya ƙare maganar dasu Aslam, Rashida tayi saurin dakatar dasu.
Ba inda zasu je, Matarka bata son yaranka dan cewa suka yi tayi musu faɗa har tana ce musu ba su da tarbiyya.
Safnar ce zata ce haka me suka yi mata? Ilham me kuka yi mata har tayi muku faɗa.
Wai daga Aslam yaga abinci a center table ya fara ci, sai kuma muka shiga bedroom muka ɗiba cincin, shine wai ba mu da tarbiyya har take mana faɗa meyasa zamu ci bada izininta ba.
Eh mana Abba faɗa tayi mana shine mu kuma muka yi fushi muka bar mata ɗakinta, dama mamanmu tace duk abinda tayi mana in ta dawo mu faɗa mata shine…
To faɗi ba a tambayeka ba, fara rattafo zance rarara kamar wanda ya haɗiyi radio.
Cewar Rashida data katse shi cikin faɗa, Zayyad ya gyara tsayuwa yana ƙara haɗa maganganun yaran a kansa ya tabbatar tunda Aslam ya faɗi haka to Rashida zata aikata.
Kin kyauta kin ji, da kanki kike son ɓata tarbiyyarsu, na tabbatar baki ji ba’asin faɗar data yi musu ba kike niman yanke mata hukunci.
Ato yara da gidan ubansu sannan ta san kana da yara ta aureka dole ne tayi musu uzuri matsayinsu na yara.
To amma tarbiyya ce kice musu duk abinda tayi musu su faɗa miki, wannan ai sakarci ne kina so ki ɗaura raya a turban da bai da kyau, Rashida ban san me yasa kika sauya ba wlh, da farko kin nuna kina tare da Safna amma tunda tazo gidan nan kike ta abu daban daban masu cike da mamaki, ban taɓa zaton haka daga gareki ba, dan haka ki sauya hali in ba haka ba ke ce zaki wahala.
Dama ai komai nayi laifi ne yara ne kuma In Sha Allah ba zasu ƙara zama a gunta ba in yaso sa riƙa jirana a maƙota, itama zata haihu ai zata san zafinsu, tarbiyya dai dai gwargwado ina basu Allah ya sani ai.
Ban da lokacinki, Ilham zamu je gurin antynku ku bata haƙuri.
Ba in da zasu maza ku wuce kuje ɗaki ku cire uniform.
Sum-sum yaran suka wuce Zayyad ya girgiza kai ya fice. Da Safna ta buɗe masa da farararta tace.
Sannu da zuwa farin masoyi yau ka dawo da wuri Allah yasa dai lafiya.
Alhamdulillah dama duk sunday ina shigowa da wuri, kina da ruwan zafi.?
Eh akwai a flaks sannan akwai wani a kettle.
To juye mini zanyi wanka.
To tace masa ta wuce ɗakinsa ta ɗauko bokiti daga bayinsa ta isa kitchen ta juye ruwan kana ta fito ta kawo masa gabansa, da kallo ya bita yana cewa.
Ki kai mini bayi anan zanyi.
Ai na ɗauka zaka je can kayi dan naga ba nan kake ba.
Safna ki wuce dashi ki sirka mini.
A’a Abban Ilham kaje dai dashi ka yi acan tunda ta dawo, da dai bata nan ne sai kayi anan.
Ɗaure fuska yayi ya miƙe yana cewa.
Ki bar ruwan bana so.
Afwan mijin so wlh ba korarka nake yi ba, haƙƙi ne bana son shiga.
To daga yanzu karki ƙara yi mini musu inna saka ki kiyi mini abu.
Yana kaiwa nan ya ɗauki ruwan ya fita. Rashida tana kitchen amma data ji ya shigo ta ganshi da bokiti da ido ta bishi ya isa ɗakinsa ya buɗe ya shiga yayi wankansa kana ya shirya cikin jallabiya ya fito da bokitin Safna falo akan in zai je masallaci zai mayar mata, sai dai kuma da aka kira ya manta da shi ya tafi masallaci tare da kama hannun Aslam, Rashida tana ganin fitarta ta ɗauki bokitin da fita tsakar gida tayi wurgi dashi, Allah yasa robar mai kwari ce da ya fashe, Safna tana bedroom ɗinta taji ƙarar robar jikinta ya bata bokitin ta ne sai ta fito da sauri, tana zuwa tsakar gida a side ɗinta nan taga bokiti anyi jifa dashi, guntun murmushi tayi dan tasan za ayi haka ganin yadda Rashida take bayyana zafin kishinta, ta ɗauka ta koma ɗaki bakinta alaikum.
Zayyad bayan sun dawo Aslam ya wuce ɗakinsu shi kuma ya nufi ɗakin Safna ya zauna a falo yana cewa.
Kinga nayi mantuwar latas ɗin nan, zuba mini abincin ki yanka albasa da tumatur yunwa nake ji.
To tace masa taje ta zuba masa abincin ta haɗo komai a babban tire ta kawo masa kan center table ta ajiye, nan ya aje wayarsa ya soma cin abincin dan sosai yake jin yunwa, can ba jimawa sai ga Ilham ta zo tana buga ƙofa Safna taje ta buɗe ta shigo tana cewa.
Abba Mamanmu tana kiranka.
Ki ce ina zuwa.
Ya bata amsa sai ta fice zuwa sashinsu ta samu Rashida a kitchen tana fere doya zata yi musu faten doya.
Mama naga Abba yana cin abinci a ɗakin Anty.
Abinci ko?
Ilham tace eh, sai ta saki abinda take yi ta fito ta nufi sashin Safna, dama fitar ilham basu rufe ƙofar ba aiko haka ta murɗa handle ta samu a buɗe nan ta tsaya a bakin ƙofa tana yi musu kallon uku saura kwata.
Wlh Zayyad bazan taɓa yafe wannan ba taya ranar girkina zaka zo ka zauna kana cin abinci anan, ke kuma shafaffiya da mai kin kyauta Allah saiya saka mini.
Safna mukus tayi bata ce komai ba, Zayyad ya miƙe yana nunata da yatsa.
Ki ɓace mini daga nan tun kafin raina ya gama ɓaci.
Zaka zo har ɗaki ka same ni.
Ta faɗa a fusace ta juya ta wuce ranta in yayi dubu to ya ɓaci, Zayyad yayi ƙofa ya koma ya zauna ya cigaba da cin abincinsa, Safna ko bata ce kala ba dan ita lamarin ya fara isar ta, da zai taimaka mata ya daina ci a gunta daya fi mata dan bata son rigima. Sai da ya kammala cin abincinsa tsaf kafin ya miƙe yace mata yana zuwa ya fita. Safna ta miƙe ta rufe ƙofar tana jin ba daɗi a cikin ranta bata so ace ita ce sanadin rikicinsu.
Zayyad yana shiga sashin Rashida ta miƙe a fusace ta fara zazzaga masa masifa, wannan karan bai yi shuru shima ya fara mayar mata, wanda har sashin Safna tana jin wannan faɗar da suka yi, ga yara suma suna kallonsu sai dai suka kame a kujera ko wanne ya natsu, Rashida garin masifa ta zageshi Zayyad ya yo kanta ya zabga mata mari ta fashe da ihun kuka tana Allah ya isa tare da zaginsa, ganin ya ƙara yo kanta ta ruga ɗaki a guje ta rufe dan yadda ransa ya ɓaci to fa zai iya rufeta da duka, ya koma ya zauna zuciyarsa sai tafasa yake yi, daga bisani fitowa yayi ya shiga mota ya bar gidan. Sai a lokacin Rashida ta fito daga ɗakinta ta kira wayar Mamansu, koda ta ɗauka tana rusa kuka ta faɗa mata komai, ran maman ya ɓaci ta shiga zazzaga masifa, daga bisani ta bata haƙuri tace zata yi magana da babansu dan abin ya fara yawa, bayan sun gama waya ta kuma kiran ƙawarta Kubura itama ta bata labari.
Karki ji komai cikin satin nan zan dawo In Sha Allah matsalarki tamkar anyi miki maganinta.
Dan Allah da kin shigo gari ki sanar dani, har gida zan zo dan wlh sai nayi maganinsu.
Cewar Rashida tana hucci, haka suka jima suna maganar daga bisani suka yi sallama ta koma kitchen ta gama haɗa musu sanwar abinci.
Zayyad sai dare kusan goma da rabi ya dawo gidan, ya fara zuwa sashin Safna ya zauna a falo babu wani hira da suke yi domin har lokacin fuskar Zayyad ba walwala, ganin haka yasa Safna kame bakinta ta cigaba da kallo, bayan kamar minti goma da shigowarsa ya kira sunanta ta amsa tana kallonsa.
Daga yau duk abinda su Ilham suka yi miki karki ƙara yi musu faɗa ki sanar dani ni zan ɗauki mataki, sannan banji daɗin yadda kika yi musu ba a matsayinsu na yara har kina ambaton ba suda tarbiyya, to yarana suna da tarbiyya kawai dai akasi aka samu duba da suna yi miki kallo kamar mamansu ne shiyasa suka yi miki abinda suka aikata, dan haka ko me suka yi miki karki ƙara yi musu hukunci ki sanar dani.
Kenan kana nufin ban isa na tayaku tarbiyyarsu ba, ina ce nima ina da haƙƙin kula da tarbiyyarsu matsayina na matarka kuma wacce take zaune a cikin gudanka, duk abinda naga sunyi ba daidai ba kar nayi musu faɗa kenan? sannan ni ban kira su marasa tarbiyya ba sai dai in juya maganar aka yi Allah shine shaidata. Kuma In Sha Allah daga yau bazan sake shi lamarinsu ba tunda hakan ya zama damuwa.
Safna ni kike faɗawa magana haka?
Haba Zayyad ya kake so nace maka, ni abinda naga yaran nan sunyi har nayi magana ganin bai dace su riƙa ɗaukar abinda suka san ba nasu bane gudun kar suje wani guri suyi, amma tunda ya zama laifi bazan sake saka baki a lamarinsu ba.
Tana kaiwa nan taja bakinta tayi shuru, nan Zayyad ya shiga yi mata faɗa ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, wato duk haushin Rashida sai ya gama saukewa akanta, da yake ita tasan darajarsa bata kuma cewa komai ba har ya gama faɗarsa kafin tace.
Allah ya huci zuciyarka kayi haƙuri zan gyara da yardan Allah.
Bai ce mata komai ba ya miƙe yana ce mata sai da safe, amma har cikin ransa yaji daɗin yadda ta bashi girmansa, ko anan yaga akwai babbancin tarbiyya tsakaninta da Rashida, yana fita Safna ta rufe ɗaki ta dawo ta zauna a cushing tare da tallafe kuncinta.
Allah kasa naci jarabawarka, domin na samu kaina a cikin wani irin ƙaddara mai wuyar misali, duk yadda nake hangen gisan Zayyad zai zame mini farin ciki ba haka na samu ba, sai tarin matsaloli da suke kunno kai Allah ka ƙara mini juriya.
Ta ambata tana jin wani rauni a zuciyarta dan har hawaye ya cika mata ido, haka ta shanye shi ta miƙe ta kashe kayan kallo da wutar falon ta wuce ɗakinta, ta yi shirin barci ta kwanta.
**
Tun daga wannan ranar zama yaki daɗi tsakanin Zayyad da Rashida, Safna tana iya ƙoƙarinta wajen kyautatawa Zayyad duk da barazanar da take gani a cikin idanun Rashida, dan ko ta gaisheta bata amsawa sai mugun kallo da harara, haka ‘yan uwanta in sun zo wani lokacin a ƙofar sashinsa suke yada zango suci hira suna yada mata habaici, haka take maƙalewa a ɗaki ta rufe kanta bata sakewa har sai in Zayyad ya dawo. Sannan batun buga ƙofa da safe har abin ya fara bin jikinta, duk da in anbuga yana sakata faɗuwar gaba, akan abin Naira ashirin Rashida takan buga musu ƙofa ko ta aiko yara su buga, da safe ko da daddare duk kuma a cikin girkin Safna take yin haka muddun In Zayyad yana cikin gidan, yayi faɗar amma duk a banza dan da alama tayi mugun raina shi bata shakkarsa. Safna bata taɓa faɗawa wani matsalar da take fuskanta ba a gidan, dan ko ‘yan uwanta da iyayenta in sun kirata suka tambaya komai lafiya to lafiya lau take ce musu, haka ma ɓangaren ‘yan uwan Zayyad ko sun tambaye ta lafiya take ce musu, domin tana yawan magana dasu a online, Amminsu kuwa suna waya kota kirata ko ita Safna ta kirata, haka rayuwa ya cigaba da gudana a cikin gidan Zayyad har aka ɗauki wata guda da sati ɗaya wanda ya kama kwanakin Safna a gidan wata ɗaya da sati biyu.
Akwai ƙura kam Allah yasa mu dace. Ina godiya da addu’ar ku da kuma comments dinku Allah ya saka da alkhairi Ameen.
Part 13
AMARYAR ZAYYAD
Na
©️®️Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 13.
Safna tana kwance a cushing a falo ita kaɗai, Zayyad a sashin Rashida ya kwana shiyasa bata damu da haɗa abin karin safe ba sakamakon ta wayi gari da ciwon kunne duka biyun, ita kaɗai tasan irin azabar da take ji dan gane da kuɗar da yake yi mata, dama tana da history akan ciwon kunne shara uku da suka wuce tayi fama da shi sai da suka dage da magani sosai daga na asibiti har na islamic kafin ta samu lafiya, abinda ya fi damunta a yanzu shine yadda kunnenta na hagu ya toshe bata ji sosai da shi har ya sakar mata da ciwon kai. Sallamar da Zayyad yayi daga ƙofarta shine yasa ta miƙe jiki ba kwari ta isa ta buɗe masa sai ta juya ta dawo ta zauna a cushing, da ido Zayyad ya bita ganin ba ta da walwala da kuzari, ya tura ƙofar ba tare da ya rufe ba ya zo ya zauna yana cewa.
Madam Zainab barka da safiya, amma lafiya na ganki wani iri.?
Safna ta miƙe ta isa gareshi fuska kwaɓa kwaɓa kamar zata fashe da kuka ta zauna a cinyarsa tana dubansa.
Sirrina kunnena ke mini ciwo duka biyun, na hagun nan ma ya toshe bana ji sosai da shi.
Ta ƙare maganar hawaye yana sauka a kuncinta, Zayyad y tallafo fuskarta da duka hannunsa cike sa tsantsar kulawa.
Subhanallahi ciwon kunne kuma, sannu ƙaunata Allah ya ƙara sauki. Ina ganin ki shirya yanzu mu fita tare inna sauke yara a makaranta sai mu wuce asibiti likita ya duba ki dan abinda ya shafi kai ba a wasa da shi.
Ya ƙare maganar yana manna mata kiss a leɓenta tare da share mata hawayen da hannu. A lokacin ne Ilham ta turo ƙofar ta shigo kamar an korota ba ko sallama, cikin tsawa Zayyad ya dakatar da hanzarinta.
Wannan wani irin shashanci ne zaki faɗo ba sallama.
Mamanmu ce tace in kiraka mun shirya.
Ai nasan kun shirya wuce ki bani guri, kuma ki ƙara shigowa ba tare da sallama an baki izinin shigowa ba, sai na gauraya ni da ke.
Ilham ta fice da sauri tana turo baki dan bata son ayi mata faɗa, Safna tace cikin sanyi.
Da ka yi mata haƙuri, kasan yara in sun shirya zuwa makaranta nan hankalinsu yake tafiya.
Hmmm Ƙaunata kenan, nafa tuna malamar makaranta ce ke, ya kamata ki ware lokaci kina yiwa yaran nan lesson a gida.
Sai ka sanar dasu tare da mahaifiyarsu su sani, dan ni ko wani lokaci suka zo banda damuwa.
Godiya muke Amaryar Zayyad, yanzu jeki shirya da sauri Allah yasa ma kin karya.
Bana jin yunwa sai mun dawo na samawa kaina abinda zanci.
Shiyasa naganki ba kuzari ai, da yanzu zance mu shiga daga ciki ba zaki taɓuka komai ba.
Waye ya gaya maka? ai kasan bana taɓa yarda ka ƙure mini gudu sai dai mu jera, kuma ko a yanzu zaka sha mamakin karatun da zan biya maka.
Safna ta faɗa tana ‘yar dariya ta nufi ɗaki zata shiga, Zayyad ya yi dariya shima.
Iye lallai na auri daidai ni, Ko dai zamu gwada ne mu ga waye gwarzo a yanzu.
Ban yarda ba.
Ta faɗa tana shigewa ɗaki, Zayyad ya saki murmushi yana girgiza kai wato Safna ce daidai shi in dai a wajen sakin layi ne tana bashi haɗin kai yadda ya kamata, hakan kuma yana sawa tana ƙara samun gurbi a zuciyarsa, duk wani hanya da salo na kula da miji tana ƙoƙarin yi, wanda da ace ita ya aura tun farko baya jin zai iya ƙara aure sai dai in yana cikin ƙaddararsa, duk da bata gama gwanancewa a harkar gado ba amma tana iya ƙoƙarinta ganin ta faranta masa, abin burgewa duk yadda yazo mata da salon kwanciya tana jure masa ba tare da ƙorafi ko raki ba, saɓanin Rashida da komai nata bata mayar da shi mai muhimmanci, ya rasa wani iri tunani Allah ya ɗaura mata, ita baga girki ba baga shimfiɗa ba komai nata ci baya ne, ga rashin iya magana da rashin kunya dan sosai ta raina shi, ya tabbatar tarbiyyar Safna da bambanci da Rashida, hakan yasa Safna ta soma samun babban gurbi a zuciyarsa sama da Rashida. duk da yana sonta amma Safna ta fara cin galaba a zuciyarsa da babban matsayi.
Safna bata tsaya ɓata lokaci ba ta saka doguwar riga baƙa da aikin farin duwatsu, ta saka hijab har ƙasa kana ta ɗauki glass ɗinta ta saka wanda ya ɗan cika mata fuska, ba kwalliya a fuskarta amma tayi kyau Masha Allah, ta saka turare mai sauƙin ƙamshi a jikin kayanta ta fito riƙe da waya, Zayyad ya kura mata ido har ta ƙaraso tana cewa.
Na shirya mu tafi.
Zuwa asibiti har da tabarau matar Zayyad, anya kuwa zan yarda da wannan mugun wasan, salon wani ya gama kalle mini ke gaki dai ba kwalliya amma kinyi kyau sosai, gaskiya kin san sirrin ado yarinyar nan.
Matar nan dai zaka ce, kuma ina cikin mota waye zai ganni? kasan tun ina gida ina ƙaunar tabarau dan Allah karka hanani sawa.
Ta ƙare maganar cike da shagwaɓa, banko ƙofar da aka yi yasa duk suka juya, ita dai Safna sai da gabanta ya faɗi, Rashida suka gani a tsaye fuska a ɗaure tana dubansu.
Zayyad amma abinda kake yi kana kyautawa, yara sun shirya zasu tafi makaranta kazo nan ka shagala, idan ban shiryasu da wuri ba kayi ta faɗa da mita, amma gashi kusan minti nawa ka ɓata anan, ke kuma saboda baki san zafin haihuwa ba balle kisan darajar karatun yaran shiyasa kika tare shi saboda mugunta da son kai, ki cigaba da abinda kike yi.
Tana gama faɗar haka ta juya ta wuce kamar guguwa, Zayyad da Safna suka kalli juna.
Mu tafi kuma bana so ranki ya ɓaci akan maganganunta.
Haba Ruhi bakomai, nasan rashin fahimta ne kuma ita muka yiwa laifi sai ka bata haƙuri.
Ta ƙare tana ɗan murmushi, sosai maganarta ya burge shi wanda ya nuna tsantsar tarbiyya a ciki, tayi shi cikin tauna harshe da kuma kawaici da haƙuri, hakan yasa shi kasa magana ya wuce gaba ita ta bishi a baya har suka isa wajen mota. Sun samu yaran suna tsaye yace su shiga baya su zauna, sai Safna ta shiga ta zauna a gefen driver, Zayyad ya zagaya zai shiga gurin driver ya hango Rashida ta rungume hannunta a ƙirji tana kallonsu, saboda ya wanke kansa daga zargi sai ya wuce sashinta ya tsaya a gabanta yana cewa.
Safna ba tada lafiya tana fama da ciwon kunne shiyasa zamu fita tare, inna sauke yara na ƙarasa da ita asibiti.
Hmmm sai ku jira ni mu tafi tare nima nayi muku rakiya.
Yadda tayi maganar cikin haɗe fuska yasa shi yin shuru bai tanka ba sai ya juya ya koma ya shiga mota, ita kuma ta shiga ɗaki tana ciwon yarda da jin wani raɗaɗin zafi a ƙirjinta wanda tun sadda Ilham ta koma ta sanar da ita Zayyad ya korota kuma taga Safna zaune a cinyarsa, ba ƙaramin dukan zuciyarta maganar tayi ba, tsabar kwazzaba jiya ya gama naniƙarta har da sambatunsa amma kuma yaje yana mannewa Safna, bayan tasan magungunan da ta sha ba ƙaramin aiki suka yi mata ba dan sosai taga sauyawarsa saboda tuni duk wani fushi da yake yi da ita ya daina, dama rabonsu da juna tun kafin bikinsa da Safna sai jiya ta sauke kai taje ɗakinsa ta bashi dama, ta ɗauka zaita rawar ƙafa akanta duba da lokacin da suka ɗauka ba mu’amalar aure, duk da yana samu a gurin amaryarsa amma ta zaci irin da ne da yake yawan nane mata, shiyasa ta dage da yin gyara musamman magungunar da ƙawarta Kubura ta kawo mata daga niger, amma wai ya je sashin Safna ya shantake kamar an aiki bawa garinsu, tayi kwafa tare da ɗauko hijab ta ɗaura akan riga da siket ɗin atamfar dake jikinta, ta fito ta rufe ƙofa ta isa motar ta tsaya a ƙofar da Safna take zaune.
Malama sai ki fito ki bani guri na zauna.
Rashida miye kike yi haka ne? ki shiga baya mu wuce tunda ta riga ta zauna.
Amma kasan dai uwargida ce ke da gaban mota.
A naki ƙaulin ba, amma ko wacce tana da damar zama a gaba in dai mace tana da girki, kije ki ƙara tambaya.
To ai nice da girkin.
Ta faɗa tana tsuke fuska, Safna ba musu ta buɗe ta fito ta zaga ta zauna a baya ta gefen Zayyad, Rashida ta shiga ta zauna Zayyad ya tada mota suka wuce cike da takaicinta.
Bayan ya sauke su Ilham sai ya juya alakar motar zuwa asibiti, sun hau kan titi sosai Rashida ke cewa cikin sakin fuska.
Abban Ilham yaushe rabonmu daka fita damu unguwa a mota har na manta, ya kamata ace nima yanzu ka saya mini mota, kaga kaima ka huta da jigilar kai yaran nan makaranta.
To kai ki unguwa Rashida ai kamawa take yi, mota kuma a yanzu banda halinta sai dai kiyi mini addu’a Allah ya hore mini nan gaba na siya muku keda Safna.
Amma ai zaka iya siyan mini daga baya ka siya mata, ba dole sai lokaci ɗaya ba.
Hakane sai ki taya ni da addu’a.
Ya faɗa a takaice tare da gundura da maganarta dan ya kula Rashida tana da son kanta, Zayyad ganin Safna tayi shuru ya kalle ta yana cewa.
Safna kin yi shuru kamar ruwa ya cinyeki ko ciwon kunnen ne?
Uhum da sauƙi Alhamdulillahi.
To ko kina tunanin Allura ne.
Ni bana tsoronta saboda ni jaruma ce.
Allah ko? kar dai sai kin ganta ki saka mana kuka.
Ni ɗin? haba dai Sirrin Ruhi gaka a kusa dani mai zai saka ni kuka, na tabbatar har ayi a gama ba zanji zafinta ba, kuma kamata yayi a raba ruwan allurar biyu a yi mini rabi a maka rabi nasan zanfi samun sauƙi akan lokaci.
Taya za ayi mini rabi bayan ni ƙalau nake.
Ka manta da cewa wanda aka yi maka zai dawo yayi aiki a jikina.
Zayyad sai da ya kalle ta ta madubin saman kansa, ya ga shi take kallo tana sakar masa murmushi.
Na yarda amma da sharaɗi.
Ya bata amsa yana nuna mata yatsun hannun damansa guda huɗu.
Naƙi wayon.
Ta bashi amsa tana maƙe kafaɗa, Zayyad ya saki dariya har yana dukan sitiyarin mota, gabaɗaya sun shagala kamar su kaɗai ne a motar, Safna murmushi ta dinga saki ta mayar da dubanta gefen hanya, dan tuni ta gano jirginsa akan nuna mata yatsunsa guda huɗu da yayi, hakan yana nufin kusancin aure zai yi sau huɗu a dare ɗaya, karatu ne daga shi sai ita suka san kansa, Rashida kamar ruwa ya cinyeta dan ba ƙaramin ƙular da ita suka yi ba, hakan yasa ta kunna data ta hau online zuciyarta kamar zata fashe, sai ta koma tana dana sanin biyo su da tayi, dama gulma yasa tace zata je dan bata yarda asibiti zasu ba duba da bata ga Safna a wahalce ba balle tayi kama da mara lafiya.
Part 14
AMARYAR ZAYYAD
Na
©️®️Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 14.
Suna isa asibiti suka zauna a reception suna jiran likita da aka ce yana ward round, tuni aka tura file ɗinsu zuwa system ɗin doctor. Bayan kamar minti goma sha biyar sai gashi likitan ya ƙaraso, yana ganin Zayyad ya isa gareshi shima ya miƙe cike da fara’a suka yi musabaha.
Alhaji Zayyad Barka da safiya, kai ne da iyalin duka waye ba lafiya.?
Amarya muka rako.
To madallah Bisimillah.
Likita ya ambata ya juya zuwa office ɗinsa, Zayyad ya kalli Safna yace mata su shiga sai Rashida ta miƙe da nufin binsu.
Maman Ilham ki jiramu mu fito.
Cewar Zayyad daya katse mata hanzarinta, ya rasa wannan wani irin binbini take yi musu ko wace mace tana buƙatar sirri amma yaga Rashida sam bata da wannan tunanin. Da suka shiga likita ya tambayi Safna meke damunta, sai ta faɗa masa daga nan ya ɗaura da tambayarta yadda take ji a jikinta harma da yaushe rabon data ga jinin al’adarta, duk ta faɗa masa dan bikinsu saura sati ɗaya tayi wanka kuma bata ƙara ganinsa ba dan har ta soma ɓace lissafi, likita yayi rubuce rubucensa kana ya miƙa musu wata takarda yace suje lab za a ɗiba jininta ayi gwaji da kuma fitsari, Zayyad ya amsa kana suka fito yana gaba Safna tana binsa a baya har suka isa lab, ba ɓata lokaci aka ɗiba jininta tare da bata wata ƙaramar roba akan taje tayi fitsari, suka nuna mata bayi ta shiga ba jimawa ta fito ta basu suka amsa tare da cewa suje su jira zasu kawo result office ɗin likita. Bayan sun dawo suka zauna zuna jiran sakamako, Safna hankalinta yana kan tv Rashida kuma tana ta danne danne a waya haka shima Zayyad. Bayan wani ɗan lokaci sai ga nurse tace su shiga ɗakin likira dan har an kawo result ɗin, suka miƙe suka shiga tare da zama suna fuskantar likita.
Alhaji Zayyad ina tayaka murna da samun ƙaruwa dan sakamako ya tabbatar da Amaryarka tana ɗauke da juna biyu, dan haka zuwa nan da sati biyu zaku dawo dan tabbatar da kwanaki nawa yake. Wannan ciwon kunnen alamu ne na laulayi yazo mata a haka, Allah ya raba lafiya.
Ameen nagode likita sai a ɗaurata akan magani dan samun sauƙin ciwon kunnen.
In Sha Allah gasu zan rubuta sai kuje gurin biyan Kudi ka biya sai ku amsa magungunan a pharmacy.
Zayyad yayi godiya sosai, Safna kuwa taji daɗi sai dai abin yazo mata a ba zata bata taɓa kawo ciki yanzu ba, balle babu wani laulayi kamar amai zazzaɓi kamar yadda sauran wasu mata ke yi. Bayan sun fito Zayyad yace su jirashi a mota ya wuce gurin biyan kudi, daya gama dasu ya amsa magani kana ya fito suka kama hanyar gida.
Bayan sun ƙaraso gida Rashida kamar abin arziki ta juya tana cewa Safna.
Allah ya ƙara sauƙi yasa kaffara ce, zaki iya ɗiga Zaitun a kunnen shima yana maganinsa sosai.
Ameen ya rabbi nagode maman Ilham In Sha Allah zan saka.
Malama ba abinda zaki saka tunda likita yace ciwon kunnen da akwai dalili, ga maganinki ki tabbatar kin karya kin shasu, ina zuwa.
Ya ambata tare da miƙa mata ledar maganin, Safna ta amsa ta wuce, shi kuma suka jera da Rashida tana cewa.
Ya zaka ce kar ta ɗiga bayan kaima kasan yana maganin ciwon kunne, ko ba kaine ka taɓa siyowa ba lokacin da Aslam yayi fama da shi kace Hajiya tace a saka masa.
Hakane amma ita fa laulayi ne yazo mata a haka.
Dumm Rashida taji akanta kamar an buga mata guduma, nan take taji wani gumi ya soma damunta amma haka ta shanye yanayin da take ciki ta ƙaƙalo murmushi.
Ayyiriri kace har ta ƙunsa, Allah ya raba lafiya, lallai fa Zayyad ka zama Sharp shooter wannan abu da wuri haka.
Bana son sharri Malama, kema ina ce daga zuwanki wata guda kika ƙunsa, dan haka kin tabbatar da ni ɗin jarumi ne ina da lafiya.
Aiko ni shaida ce. To Allah ya inganta. Zaka karya anan ne ko kuwa?
Ta ambata tare da cire hijab ta aje saman kujera, Zayyad ya zauna yana cewa.
Ki haɗa tea mai kauri ki kawo mini arish da biredi, bana ma jin wani yunwa sosai.
To tace masa ta isa kitchen ta haɗo masa dan dama tun ɗazu ta soya arish ɗin haɗe dana ‘yan makaranta, ta kawo masa ya karya suna hira kamar wani rikici bai shiga tsakaninsu ba, sosai Rashida taji daɗin yadda komai ya soma zama dai dai a tsakaninsu, tun dai jiya data ba shi haɗin kai, bayan ya gama ya ciro dubu ɗaya ya miƙa mata yana cewa.
Ki riƙe ko da kina buƙatar siyar wani abu.
Hmmm yaushe rabon da ka bani kuɗin kashewa sai yau, kodai duk murnan samun ƙaruwar ce.
Ki amsa kiyi godiya ba niman ba’asi ba, imma shine ai ya kamata dan haihuwa Alkhairi ne, balle ma kuma ba shi yasa na baki ba ra’ayi nayi.
To nagode a dawo lafiya.
Ta amsa ya wuce ɗakinsa ya ɗauki abinda zai ɗauka kana ya fito ya wuce sashin Safna wanda Rashida da harara ta bishi, kamar tana jira ya fita ta ɗaga waya ta kira mamansu tare da shiga ɗakinta ta rufe ƙofar ta ciki, bayan ta ɗauka suka gaisa ta ɗaura da cewa.
Mama wai Safna ciki gareta, yanzu muka dawo asibiti bata jin daɗi.
Ikon Allah abu da wuri haka to Allah ya inganta.
Mama ya zaki ce haka.
Rashida ai tunda aka ɗaura auren nan kema kin san ƙaddara ta riga fata dan haka kiyi haƙuri ki karɓi ƙaddara, sannan ke ya batunki har yanzu shuru ko.
Mama yaushe na cire implant din, ai da saura tukuna.
Gobe kya sake biye masa ai, gashi Amarya tana fara zuba ɗaya to ɗaya ne zai rage ta kamo ki, in kuma ‘yan biyu ne to kun yi daidai kenan.
Mama madadin ki lallashe ni sai ki ƙara mini zafi.
Rashida ta faɗa cikin rawar murya, Maman tayi ɗan murmushi.
Ya kike so nace miki, to kiyi haƙuri in kin samu lokaci sai ki sake kira muyi maganar can da na fara yi miki jiya.
Yanzu ma ina da lokaci, kuma ina da kati muyi kawai ina jinki.
Rashida ta faɗa tana zama a gefen gadonta tare da tattaro duk natsuwarta suka shiga hira.
…
Zayyad yana shiga ɗakin Safna ya tadda falon ya ɗauki Ƙamshin turaren wuta, ya zauna yana shaƙar numfashi tare da fitarwa cike da samun natsuwa, Safna ta iya kula da sashin ta sosai ya ambata a cikin ransa, fitowa tayi daga ɗakinta tana murmushi.
Farin Masoyi har ka fito.
Eh amma kin karya kuwa?
Yanzu na gama gyaran ɗaki zan shiga kitchen.
To kin san dai ba ke kaɗai bace yanzu, ki kula da cin abinci dan Allah, sannan duk abinda kika ji kina son ki ci ki sanar dani zan aiko miki.
Nagode da kulawa ina Ƙaunarka masoyi.
Kamar yadda nima nake ƙaunarki, ga dubu ɗaya ki aje saboda tsaron lalura koda sa kati ko wani buƙatar in ta taso miki da gaggawa.
Ta ƙaraso in da yake zaune ta ɗago haɓarsa ta sakar masa kiss a goshi.
Yadda kake faranta mini Allah ya cigaba da faranta maka, ya ƙara maka buɗi da yalwar arziki mai albarka ya kuma tseratar da kai daga Haram.
Zayyad miƙewa yayi yana kallon kwayar idonta cike da tsantsar so da farin cikin kasancewarsu tare a inuwa ɗaya.
Ameen ƙaunata ina alfahari da samunki a cikin inuwa guda, Allah yayi miki albarka tare da abinda ke cikinki.
Ameen tace tare da rungumeshi tsam a ƙirjinta, shima runguneta yayi sosai kamar zai mayar da ita cikin jikinsa, suna jin bugun zuciyar junansu tare da shiga wani daular duniya wanda sai tsantsar masoya sune kaɗai suka san yadda yanayin yake, Safna ta sauke ajiyar zuciya ta sake shi shima ya saketa suna kallon juna.
Badan badan ba dana ƙi fita aiki yau na cigaba da kasancewa da ke, Safna kina yalwata mini duniyata da farin ciki Allah yasa zamanmu ya ɗaure a haka.
Ameen ta ambata ta kama hannunsa ta jashi suka fita har mota tayi masa rakiya, ya shiga ya zauna suna jifar juna da shu’umin kallo wanda su kaɗai suka sai irin karatun da suke aikawa junansu, ya tada mota ya wuce suna dagawa juna hannu, sai da ya fita da motan kafin Safna ta koma cikin ɗaki ta soma shirin haɗawa kanta abin karyawa.
**
Bayan sallar La’asar Rashida ta ɗaura sanwar abinci da wuri, dan haka ta fito tsakar gida tana wanke uniform ɗin su Aslam, su kuma suna wasa da kwallo, tsautsayi yasa Ilham ta buga kwallon ya daki window ɗin Safna da ƙarfi, Safna dake bedroom a kwance a razane ta farka daga barcin data samu ya ɗauketa, dan jiya bata samu barci mai kyau ba, ta tashi cike da ɓacin rai sai ta saka hijab saman rigar barcinta ta fito tsakar gida tana cewa su Ilham.
Wanene ya buga mini window? Ilham meyasa bakwa yin abu cikin natsuwa ne ina barci kun tashe ni.
Malama dakata! ta yaya zaki hana yara sakewa suyi wasa saboda karsu tashe ki a barci, wannan ai ba magana bace.
Cewar Rashida data ɗago cikin faɗa, Safna ta cigaba da kallonta cike da mamakin ta.
Amma kin san ya kamata ayi musu faɗa karsu sake, duba da window ɗin glass ne karsu fasa, sannan ban hanasu wasa ba amma suyi shi cikin natsuwa.
Ba za suyi ɗin ba, yara da gidan ubansu ki nima saka musu dokar yin wasa, in ma sun fasa window ɗin babansu ne ya saka kuma shi zai gyara bana son takura.
Hmmm Safna tace kana ta koma ɗaki dan sosai taji kanta na sara mata ga bugun kirjinta yana yi da sauri da sauri, saboda jinnun jikinta sun motsa shiyasa ta wuce kar ayi rikicin da bai dace ba. Rashida ta bita da ƙananun magana tana jan tsaki tare da cewa yaran suyi wasa son ransu ba wanda ya isa ya hana su, sai ta cigaba sa wankinta, Safna kuwa tashar karatun Al-Qur’ani ta saka tana saurare ga wani hawaye mai zafi yana sauka daga gefen idonta na hagu kuma tanan kanta ke ciwo, ta jima a haka kafin daga bisani ta shiga fidda numfashi mai nauyi tare da zufa daga goshinta, alamun aljanun sun tafi sai ta miƙe jiki ba ƙarfi ta wuce kitchen ta ɗauko ruwa a fridge tasha kana ta samu sauƙin zafin data ke ji a ƙirjinta.
*
Da dare.
Bayan sallar isha’i Zayyad ya dawo, ya riƙo musu nama tsire tare da fruits ya aje nasu sai ya wuce sashin Safna ya buga ƙofa tazo ta buɗe masa, ya bita a baya ya zauna yana tambayarta jiki tace da sauƙi, ya ɗaura da cewa.
Na sanar da Ammi ba kya jin daɗi shine tace ko zata aiko yarinyar yaya Hauwa tazo ta zauna miki na kwana biyu ta taya ki aiki.
Ikon Allah, ba dai ka gaya mata ciki gareni ba kasa naji kunyar zuwa gidan.
A’a ban faɗa ba nace dai kunne kike fama da shi.
Ai tun ɗazu naji sauƙinsa sai dai toshewar ne har yanzu kuma ni bazai hanani aiki ba, kar a takurawa yarinya.
Ba wani takura ta kammala secondary ne tazo zan nima mata admission anan KASU.
Kace ta dawo Kaduna da zama kenan to Allah yasa a dace.
Ameen. Ina ganin wannan juma’ar zaki je can gidanmu kiyi musu wuni in wata juma’ar ta zagayo sai ki je gidanku.
Wato dai sai da nayi wata biyu kan zan fara fita.
Banda Ammi tace in barki da ba zaki je ko ina ba sai kinyi wata uku.
Buga ƙofarta ya dakatar da hirarsu, ya miƙe yaje ya buɗe yaga Aslam ne.
Mamanmu tace kazo.
Wuce kaban guri.
Ya faɗa a tsawace.
Yaron ya tafi da gudu, Zayyad ya juyo yana ce mata yana zuwa, sai ya wuce sashin Rashida yana shiga ya soma cewa.
Bana son irin abinda kike yi mini wlh, taya zaki dinga aika mini yara in zo.
Gani nayi dole sai ina tuna maka da girki na ne, dan na kula mancewa kake yi dani.
Amma ke bana zuwa ɗakinki na daɗe kafin in koma can, wani lokacin sai na fara zuwa nan na ganku kafin in je ɗakinta kuma itace da girki, sannan bata taɓa yi mini ƙorafi ko nuna damuwa akan haka ba, wlh zan ɓata miki rai in baki bari ba.
Ato daga faɗar gaskiya sai kuma ya zama laifi. A saka abincin ne ko sai anjima.
In kin gadama zaki iya sakawa.
Zayyad ya bata amsa yana samun guri ya zauna, Rashida ta taɓe baki da ɗage kafaɗa ko a jikinta sai ta miƙe ta wuce Kitchen ta haɗo masa abinci ta kawo masa, dafadukan shinkafa da wake na mangyaɗa tayi, gashi nan fari bai ji kayan haɗi ba, ba kayan miya sosai balle curry, Zayyad yana kai loma ɗaya yaji baiji gishiri bane ko maggi oho, ya haɗiye yana kallon Rashida.
Ɗauko mini yaji.
Aiko yaji na ta ƙare ban daka wani bani.
Ke Ilham jeki ɗakin antynku ki amso mini yaji.
Yayi maganar yana kallon Ilham, ta miƙe da sauri ta fita, ba jimawa sai gata ta dawo da yaji a cikin ƙaramin kwano plastic ta miƙa mishi, ya amsa ya zuba ya cigaba da cin abincinsa, Rashida cikin ƙufula tace.
Yanzu dan Allah miye na amso yaji a gurinta, komai dai sai ka nuna mata ni ban iya ba, ai da sai ka bada kuɗi yanzu na saka hijab na amso nan maƙota suna sayarwa.
Zayyad abincinsa ya cigaba da ci bai tankata ba, ya kula Rashida abin ƙorafi baya yi mata kaɗan, a dalilin yajin kuwa yaci abincin sosai ya kora da ruwa tare da kankana kana ya miƙe ya bar mata kayan a gurin ya wuce ɗakinsa dan yayi wanka, Rashida ta ɗauke kayan abincin ta mayar kitchen ta samu leda ta juye sauran yajin ta ƙulle, kana ta kife kwanon a ƙasa ta ɗauko taɓarya ta bugawa gefen kwanon, nan take ya tsage dan kaɗan ya rage ya rabe biyu, ta ɗauka ta adana da nufin da safe in Zayyad ya fita zata aika yaran da shi su kaiwa Safna.
Part 15
AMARYAR ZAYYAD
Na
©️®️Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 17.
Bayan sun shiga falo kowa ya zauna kukan Safna ne ke tashi a ciki, babu wanda yace tayi shuru ko ya tambayeta abinda take yiwa kuka, har ta gaji dan kanta ta yi shuru tana ajiyar numfashi, a lokacin ne Yusuf ya shigo ya miƙawa Umma sugar ta amsa ta saka a cikin kunun tsamiyar data dama musu, data gama juyawa ta zubawa babansu a kofin jug tasa Yusuf ya miƙa masa tare da kular ƙosai data zuba masa, daga nan ta sakawa Mudan sai Yusuf, a lokacin ne ta kalli Safna da take zaune a takure a carpet.
Kin karya?
U-um ta bata amsa haɗe sa girgiza kai, umma ta zuba mata a wani kofi da ƙosai a plate tasa Yusuf ya miƙa mata sannan ya koma ya cigaba da karyawa, falon ya ɗauki shuru sai cin abincinsu suke yi sai dai ko wanne zuciyarsa cike yake da damuwar ganin Safna, amma da yake sun san dokar Abbansu yasa kowa yayi shuru har sai shi ya buɗe baki ya fara magana, Umma ma dauriya kawai take yi tana tusa abin karin ba dan tana jin daɗinsa ba, ace yarinya ko wata biyu bata cika a gidan aurenta ba amma matsaloli suna biyowa baya irin haka, duk ta ƙosa taji meke faruwa, ɓangaren Abba kuwa yana sane yaƙi cewa kowa har sai ya karya tukuna, shiyasa daya kammala ya miƙe ya shige ɗakinsa ya shirya cikin manyan kaya har da malum malum kafin ya fito yana gyara zaman hularsa ya samu guri ya zauna, wanda a lokacin duk sun gama karyawa Safna ce dai data kasa cin komai tana wasa da yatsunta babu kuma wanda yace taci dole, Abba yayi gyaran murya yana dubanta wanda yasa Safna tattaro duk natsuwarta.
Mamana meya kawo ki gida a irin wannan yanayin? Bana so kiyi mini karya ki faɗi duk abinda ke faruwa muna saurarenki.
Safna bata taɓa zaton Mahaifinsu zai tambayeta cikin sassauci haka ba, hakan yasa ta samu damar sauke ajiyar zuciya abinda take ji ya tokare mata a wuya ya sauka, sai ta shiga basu labarin irin matsalar data fara fuskanta da Rashida har kawo abinda ya faru yau, sai ta ja fasali tare da sauraren me zasu ce, umma tace cikin damuwa.
Ban zaci haka daga gareki ba Safna ina yabonki da haƙuri ashe ba kida shi, meyasa zaki biye mata? Kenan duk jan kunne da faɗar da muka yi miki ya tashi a banza ko, wannan ba shine tarbiyyar da muka baki ba, sai ki biye mata kunyi faɗa keda nasan aljanunki bama sa tashi. Me yasa sai yanzu zasu yi haka kuma anata magani.
To mugunta suka shirya mata mana, ace anyi maganinsu sai da aka yi aure zasu riƙa tashi, ashe maganin ya zama aikin banza. Sannan Safna meye dan sun fasa miki plate, saiki rabu dasu in ma kina buƙatar wasu ne saiki kira ki faɗa a siya miki, kuma bai dace ki hukunta yarinya ba tunda har uwarsu tanuna ki daina takurawa yaranta, wataƙila da su zata riƙa amfani dan ganin tana tunzuraki aljanunki na tashi, kinga in hakane to ta samu nasara akanki tunda gashi tayi sanadin da Mijinku ya koro ki gida kuma ko wata biyu baki rufa da aure ba, wannan kinga ya zama kin zubar mana da mutunci da ƙima, dan haka daga yau wannan ya zama na farko da ƙarshe, na rantse da Allah idan har kika sake biye mata kuka yi faɗa koda ta baki ne Zayyad ya koroki gida to ki sani sai na yi miki dukan da tunda kika zo duniya ba ayi miki irinsa ba. Idan ma tayi miki wani abu ki jira ya dawo ki faɗa masa shi ya ɗauki mataki, amma zanfi so karki zama mai kai ƙara ki zama mai haƙuri juriya da kawar da kai, ki tashi cikin dare ki faɗawa Allah ki sata a addu’a akan Allah yayi miki ganinta ya kawar da saɓani a tsakaninku, in kinyi haka In Sha Allah zaki ga kyakkyawar sakamako, dan haka yanzu zan fita bazan jima ba zan dawo ki shirya zan mayar dake gidan mijinki. Ke kuma sai ki ƙara ja mata kunne dan wlh bazan ɗauki wannan shegentakar ba.
Abba ya ƙare maganar akan umma, to tace masa kana ta yi masa a dawo lafiya ya wuce ya fita, a lokacin Mudan ya soma magana.
Gaskiya idan kika ƙara faɗa da kishiyarki wlh har gida zan zo in miki shegen duka, haba Safna ya za ki biye mata kuyi abu sai kace a zamanin jahiliyya, karki kuma aikata haka dan ban sanki da rikici ba, yau da Maryam ce aka ce tayi haka bazan musa ba dan ita tana da zafi da gatsali.
Faɗa mata dai danni wlh mamaki ma ta bani, in ance min Safma ce tayi haka zan karyata amma da yake da bakinta tayi bayani shiyasa na gasgata. Nasan baki san ya zaman kishi yake ba tunda nan ba ita gareni ba, kuma suma ‘yan uwanki ba mai kishiya amma kuma mun baki tarbiyyar da zaki iya zama da kowa duk mugun halin mutum, karki biyewa zuciya Safna dan ba tada ƙashi ƙarshe ya sauke ki a tudun dana sani. Ko wannan koroki da yayi ai ya zama cin mutuncin gidan nan dan haka karki ƙara, tunda har ta nuna miki halinta na son rashin zaman lafiya sai ki tura mata aniyarta ki zuba mata ido, ki kama kanki ki kula da mijinki kawai, yaranta in kin kinji zaki iya kyautata musu kiyi amma ki kauce duk wani abu da zaisa yaran su samu abin faɗawa Mamansu kinyi musu dan a zauna lafiya.
In Sha Allah Umma zan kiyaye nima wlh ba a son raina hakan ta faru ba.
Ki dai kiyaye, sannan In Sha Allah za a kawo miki wasu magungunar kina amfani da su dan su daina tashi. Ki kuma cigaba da kyatatawa mijinki iya iyawarki. Sai hankalinki ya kwanta yanzu, ki samu ki karya kafin babanku ya dawo.
Safna tace to tana mai sauke ajiyar zuciya dan bata taɓa zaton zasu yi mata da sauƙi haka ba, kunun ta iya sha bata ci ƙosai ba. Bayan ta gama umma ta jata ɗakinta ta cigaba da bata bayanai na yadda zata zauna da Rashida lafiya, Safna ta baza kunne tana saurare kuma sosai ta gamsu da kuma ɗaukar alƙawarin aikata hakan.
**
Bayan sun isa gida nan Zayyad ya barsu maman Rashida suka shiga hidima da ita da magani, ya fito ya nufi sashin Safna sai ya tadda bata nan, shuru yayi yama rasa tunanin da zaiyi daga bisani ya fito ya shiga motarsa sai ya wuce gidan hajiyarsa danya shaida mata abinda ke faruwa. Yana fita Rashida ta miƙe da gudunta ta nufi ɗakinta ta faɗa tiolet tayi fitsari, data gama ta fito tana sauke numfashi sai ta samu guri ta zauna tana cewa.
Tun ɗazu fitsari ya matseni amma ina tsoron na motsa na ɓata shirinmu.
Ai magana ma ta ƙare tunda mun je gurin magani kuma yaji komai da kunnensa, ko zuwa anjima zaki iya yin tafiya sai dai kiyi shi a hankali tunda sauƙi bai samuwa lokaci guda sai a hankali, kuma kinga wannan abinda ya faru shine abinda zan iya ɗauraki akai da zaki samu sassauci daga Zayyad ɗin, kuma na tabbatar dole hankalinsa yafi karkata akanki saboda jinyar da zaki yi, to sai ki san yadda zaki ja ragamar zaren ki kama shi a hannu, ni zan wuce su Anisa sai su zauna miki Allah yasa daga can ya bita da takardan saki.
Cewar maman su, Zaliha suka amsa da amin kana ta miƙe, Anisa ta tareta da cewa.
To yanzu malam yaci dubu ɗari kenan a bilis.
Rabonsa ne ya tsaga mu dai buƙatarmu ta biya shine kawai, ko bai yarda da kishiyarta zata yi mata asiri ba mun dai saka masa shakku da kokwanto a zuciyarsa, kuma daga haka komai zai kankama.
Tana kaiwa nan a maganarta ta yi hanyar fita suka rakata har mota ta shiga suka wuce kafin suka dawo ciki suka tadda Rashida zaune ta ɗaura ƙafa daya kan daya tana danna waya.
Sai kinyi ko ba fosta uwargidan Zayyad, duk wanda ya shiga gonarki sai kin ga bayansa da izinin Allah.
Cewar Zaliha, Rashida ta saki wani shu’umin murmushi.
Ai yanzu wasan zai fara, ba dai ta yarda ta auri mijina ba hmmm, cikin ruwan sanyi zata bar gidan nan da ƙafafunta, dama hanya nake nima kuma mama ta ɗaurani a kai.
Ta ƙare maganar tana turo ɗankwalinta gaban goshi, Zaliha ta miƙe ta nufi ƙofa ta saka key ta dawo ta zauna.
Saboda tsaro kar muna cikin hira muga Zayyad ya dawo ido ya raina fata.
Ta ƙare tana ‘yar dariya, nan suka cigaba da hirarsu Anisa ta miƙe ta shiga kitchen dan haɗawa Rashida abin kari saboda tace yunwa take ji bata karya ba.
Zayyad yana isa gidansu ya samu Hajiya a baranda bisa tabarma ta kishingiɗa da filo, tana ganinsa ta miƙe ta zauna tana murmushi har ƙaraso ya zauna ya shiga gaisheta, ta amsa tare da tambayarsa iyali, Zayyad yace lafiya lau kafin ya soma bata labarin duk abinda ya faru, hajiya ta riƙe haɓa cike da mamaki.
Amma banji daɗin wannan labari ba, meyasa Safna zata biye mata ina yi mata kallon mai hankali da tarbiyya.
Wlh Ammi abinda ya bani haushi kenan nace ta tafi gida. Kuma abinda yake bani mamaki yadda aljanunta suka tashi dan tace lokacin tana gisa basa tashi saboda suna magani kuma har yanzu ma ana aiko mata da magani daga gida.
Zai yuwu ɓacin rai ya kawo su, tunda da yawan masu aljanu in ana faɗa ko tashin hankali yana saka su tashi, amma ni maganar da kace wai asiri aka yiwa Rashida shine hankalina bai ɗauka ba, taya daga faɗa sai kuma ta zube ace wai asiri ne, sai dai in itama tana da aljanun ba a sani ba.
Wlh Ammi nima abinda na gani kenan shiyasa naso muje islamic chemist, amma mamanta ta ce can gurin malam na kan kwana zamu.
Ai tunda sune suka zaɓi haka shike nan sai a jira a ga aikin maganinsa tunda an zuba kuɗi har dubu ɗari, Allah ya kyauta gaba amma banji daɗin da kace su tafi gida ba kaga iyayen Safna ba zasu ji daɗi ba dan ba a kyauta musu ba, tunda har ka iya haƙuri da matsalolin rashi meye zaisa ba zaka yi mata uzuri ba tunda wannan ne na farko kuma faɗan bada ita aka yi ba da aljanunta suka yi. Gaskiya karka sake yin haka ko nan gaba domin hakan ke nuna baka fi ƙarfin gidanka ba ka kaza tsawatarwa.
In Sha Allah zan gyara kuma nima sai daga baya naga bai dace data tafi ba, na duba ta a ɗaki naga ko tana nan muyi magana sai na tadda ta tafi.
To ba dole ta tafi ba tunda kai kace hakan, Dan Allah Zayyad ka zama tsayyen namiji a gidanka, kasa a ranka irin haka zai faru koma fiye da haka tunda ka haɗa mata biyu a gidanka, idan kuma zaman lafiyar bazai samu ba ina ga gwara ka raba musu gida hankalin kowa ya kwanta.
In Sha Allah zan kula sosai, kuma ni yanzu inna ce zan raba musu gida hayar ne bana so tunda Allah ya rufa mini asiri da gidana. Zan cigaba da lallaɓawa haka.
To shikenan Allah ya shiga lamarin ya baka ikon Adalci a tsakaninsu, bari na kimtsa sai ka kaini na duba jikin Rashida.
Ameen ya ce mata sai ta miƙe ta shiga ciki ba jimawa ta fito cikin shigar doguwar rigar atamfa da hijab suka wuce suka shiga mota sai ya jasu. A hanya Ammi ke ce masa lallai zuwa yamma yaje gidansu Safna ya bawa iyayenta haƙuri ya maido da matarsa, yace mata to, nan dai ta dinga yi masa faɗa da shawarwarin yadda zai zauna da su cikin hikima.
Lokacin da suka isa Zayyad yayi parking a ƙofar gida kana suka nufi sashin Rashida, sai da suka buga ƙofar dan sun tadda shi a rufe, Zaliha tazo ta buɗe musu suna ganin Hajiyarsa ce suka shiga yi mata sannu da zuwa har suka ƙarasa cikin falon suka zauna, suka gaishe da Ammi ta amsa tana yi musu ya mai jiki.
Da ɗauki bata jima da samun barci ba.
Cewar Anisa, Ammi ta shiga yi mata addu’ar samun sauƙi cike da tausayinta, dan shimfiɗa suka yi mata akan carpet suka ɗaura kanta bisa pillow, duk tana jin hirarsu dan idonta biyu suka yi karyan tana barci, kiran daya shigo wayar Zayyad shine yasa shi miƙewa ya fita danya amsa, ya barsu da Ammi tana tambayarsu yanayin jikin nata.
…
Safna.
Abba bai jima ba ya dawo nan yace ta fito su wuce, ba musu ta fito har waje umma ta rakota tana ƙara ja mata kunne, suka shiga motar Abban suka wuce, shima a mota faɗa da nasiha ya dinga yi mata har suka ƙaraso ƙofar gidanta, yayi parking a waje yace ta shiga ta kira Zayyad in yana ciki in kuma baya nan ta shiga ɗakinta ta zauna anjima zai dawo, Safna tace to kana ta sauko a motar ta buga gate mai gadi ta buɗe mata ta shiga, wanda a lokacin ne Zayyad ya fito ya amsa waya, yana jin buga gate ya mayar da hankalinsa can sai ga Safna ta shigo ya ganta, nan take yasha kunu dan har lokacin bawai ya sauko daga fushin daya ke yi da ita bane, har inda yake tsaye ta ƙaraso ta tsaya a gabansa ya gama wayar kafin ya dube ta.
Dama ashe kinfi son ki tafi gidan, kika sa ƙafa kika tafi ko.
Bani kaɗai bace tare da babanmu nazo yana waje yana jiranka.
Ta bashi amsa tare da kaucewa maganarsa, dan itama har lokacin haushinsa take ji saboda ya raina mata wayo shi yace ta tafi amma yana ƙorafin ta tafi, Zayyad bai ƙara magana ba ya nufi gate ya fita, sosai yaji kunyar ganin babansu Safna dan baiyi zaton zai dawo da ita ba, ya isa inda yayi parking ya risina yana gaida shi, Abba da yake jikin motarsa a tsaye ya miƙa masa hannu akan su gaisa, Zayyad yaji kunyar miƙa masa hannu sai ya noƙe, haka suka gama gaisawa Zayyad ya shiga bashi haƙuri akan abinda ya faru tare da faɗin dama ya bari anjima yaje ya dawo da ita, Abba yace ba komai nan shima ya bashi haƙuri ya kuma tabbatar masa da za a cigaba da nima mata maganin aljanunta, sannan sunyi mata faɗa sosai ba zata kuma aikata abinda ya faru yau ba, sosai Zayyad yaji kunyar Abba kamar ƙasa ta buɗe ya shiga, sai yanzu ya gane bai kyauta ba daya turata gida, daga bisani Abba yace zai tafi Zayyad yayi masa godiya yaje jikinsa yana rawa ya buɗe masa mota ya shiga ya tuka yana tsaye har ya bar unguwar, a lokacin ne ya samu damar sauke ajiyar zuciya kana ya juya ya shiga gidan cikin sanyin jiki.
Part 16
AMARYAR ZAYYAD
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 18.
Ght products me Maida Bora mowa💃🏻💃🏻💃🏻 Mai maida mazaje jarumai uwar gida da Amarya suyi ta alfahari da shi shima na alfahari da su🙈😂
Wai haryanzu kina zaune baki gwada ba? Kaima kana zaune baka gwada ba? mata da Maza nata k’ara martaba da kima adalilin ght products, wai kun tsaya kallo? Shin ko sai gwad’o yayi muku k’afa ne?🤔🤥
Yar uwa da d’an uwa ku garzayo in hada muku kayan gyara iya kudinku iya shagalinku.
Mrsjmoon bata tsauwalawa ku dai ku zo musa labule in gyaraku ciki dawaje kuyi tsaf tsaf kuyi cif cif kuyi zaqwai zaqwai kunsan dai zaki na zuma baya illah😋 hakkun duk wanda bai tab’a amfani da kayan GHT ba anbarshi a baya Maza da Mata kada ku bari a barku a baya dan dan Allahb👏🏻 ku ka sance a kan gaba wurin mallakan naku ba jiran ana baku labari ba😍🏃♀️🏃♀️ Mai so zai iya tuntubar wannan number 08132166848 a Whatsapp ko kira. Nagode sosai.👏🏻👏🏻 Indiawa suka ce bahut bahut shukhriya🥰🥰
Safna koda ta shiga ɗaki ruwan wanka ta fara sakawa domin ta samu ta watsa ko zata ji daɗin jikinta, sai ta ɗauko maganinta a ɗaki ta fito falo ta zauna a cushing ta sha, a lokacin ne Zayyad ya shigo falon dan ta barshi a buɗe, yace ta fito suje part ɗin Rashida Mahaifiyarsa tazo tana ciki, daga haka ya fice sai ta miƙe ta mayar da hijab ɗin data cire ta fito ta nufi sashin Rashida. Da sallama ta shiga wanda idonsu Zaliha ya dawo kanta harta ƙaraso ciki ta zauna a carpet tana gaishe da Ammi, a lokacin Rashida ta farka ta soma zaro ido tana nuna inda Safna ke zaune tana fuzzar da miyau, su Anisa suka yi kanta suna salati, haka shima Zayyad miƙewa yayi ya isa gareta yana tambayarta lafiya, bata iya cewa komai ba sai nuna Safna, wanda ita kuma kallonsu kawai take yi tana jin wani hayaƙi yana yawo a kanta, sarai ta fahimci meke maruwa amma har cikin ranta bata yarda da Rashida ba sharri kawai take so ta yi mata, Ammi ma tana zaune tace su kawo ruwa su shafa mata a fuska dan itama kallon lamarin take yi kamar a drama, bayan sun shafawa fuskarta ruwa sai ta shiga sauke ajiyar zuciya ta dawo hayyacinta, Anisa ta miƙe cikin faɗa.
Gaskiya Safna ki tashi ki fita mun samu ta fara dawowa hayyacinta karki ɓata mana maganin da muka fara yi mata, kuma In Sha Allah aniyarki zata biki.
In Sha Allah aniyar kowa kuwa zata bishi, kuma Allah baya barci.
Cewar Safna cikin kwarin guiwa dan sosai taji zuciyarta a dake babu fargaba ko tsoro. Zayyad ya dubeta rai ɓace.
Tashi ki fita bana son tashi hankali.
Babu inda zata je ta zauna zanyi magana daku duka.
Cewar Ammi cikin haɗe rai, ba wanda ta ƙara magana ta cigaba da cewa.
Anisa da Zaliha dole zasu bar gidan nan a samo wata wacce zata yi jinyar Rashida, dan na kula in dai kuna gidan nan ba zaku bari a zauna lafiya ba, ko kuma su ɗauki Rashidar su koma gida ta yi jinya a can bana son tashin hankali. Sannan wannan ciwon nata alamu ya nuna Aljanun dake jikin Rashida basa shiri dana Safna dan haka sai an tsaya tsayin daka wajen yin maganinta, itama Safna a dage mata, na rasa wannan abu ace girki ba ɗaya ba ko wacce da side ɗinta ba ruwan wani da wani amma ku kasa sakawa zuciyarku salama akan kishi, to gaskiya ba zai yuwu ba duk wacce ba zata zauna lafiya ba to zata tafi gidansu.
Amma Hajiya ita Safna da Anisa tayi magana meyasa zata biye mata, ba sai tayi shuru taga hukuncin da zan ɗauka ba.
Tunda na zo gidan nan mutanen nan suke bina da rigima, na kawar da kai nayi haƙuri amma ba zasu fasa ba, yayarsu tayi mini suma suyi mini, ina ce a ranar da aka kawo ni cikin gidan nan bayan ‘yan uwana sun watse sai da suka haɗani faɗa da kai, buga ƙofa da sassafe bani da sukuni a cikin gidan nan, Rashida ta takura mini bayan ni bana shiga lamarinta, yarinya ta fasa mini kwanon dana saka maka yaji jiya ta kawo sai naja mata kunne akan karta ƙara, saboda sau biyu kenan suna fasa mini kwano, amma ba halin na yiwa yaran nan faɗa Rashisa zata zo har ɗakina tana gaya mini maganar da yayi mata, ya kake so nayi.
Safna ta ƙare maganar tana matsanancin kuka, daga bisani miƙewa tayi ta bar ɗakin da gudu ta wuce ɗakinta, nan ko Ammi ta shiga surfa musu masifa tayi musu tatas tare da jawa su Anisa kunne akan in dai zaman lafiya bazai kawo su ba to karsu ƙara zuwa gidan, dama tasan duk abinda ya faru laifin na Rashida ce kuma in taso ta gyara in taƙi kanta zata yiwa, ta miƙe rai ɓace tayi mata Allah ya sauƙe kana ta fito zuwa sashin Safna.
Koda ta shiga ta sameta tana ta kuka Ammi ta zauna ta shiga yi mata faɗa, tace daga yau in yaran sun yi mata abu ta riƙa faɗawa Zayyad ne tunda in ta yi musu magana ita yana zama rikici, tayi faɗa sosai tare da nasiha tace in har Rashida ko ‘yan uwanta sun sake yi mata wani abu ta kira ta faɗa mata ita da kamta zata zo ta ɗauki mataki, tayi mata nasiha sosai da shawarwari wanda yasa Safna ta ji sanyi a ranta, ko ba komai tasan Hajiya tana sonta dan haka ta share hawayenta, Ammi ta miƙe akan zata tafi Safna ta rakota har waje kana ta koma cikin ɗaki ta rufe dan sosai Zayyad ke bata mamaki yadda ƙiri ƙiri yake niman ɗaura mata laifi. Ammi ta leƙa tace ya fito ya mayar da ita gida yace to kana ta wuce waje shi kuma ya cigaba da bawa Rashida haƙuri, dan tun fitar Ammi take kuka akan ta nuna mata bata sonta ƙiri ƙiri dan tafi ƙaunar Safna da ita, dan haka ita gidansu zata koma da jinya, ganin ta rikice masa yasa ya susuce ya dinga lallashi kana ya bawa su Anisa haƙuri yana cewa ba inda zasu je sune zasu kula da Rashida ran Ammi ya ɓaci ne kuma zai fahimtar da ita, haka ya fito ya ɗauki hajiya a motarsa, ta cigaba da yi masa faɗa dan ta kula hankalinsa yafi karkata akan Rashida wanda hakan bai kamata ba, tunda a zahiri itace ba tada gaskiya amma saboda ta langwaɓe yake rawar ƙafa akanta, ita sam ma bata yarda da ciwon da Rashidan ke yi ba gani take yi duk makirci ne, Zayyad haƙuri yake bata da alƙawarin zai daidaita gidansa, har ya sauketa a ƙofar gida tana ƙara jaddada masa akan ya kamanta adalci, yayi mata godiya ta shiga gida shi kuma ya koma gida kansa a cunkushe yama rasa tunanin da zai yi, duk da yasan Rashida ce ba tada gaskiya amma ya zama wajibi ya tausaya mata kodan lalurar da take fama da ita, kuma da Safna bata biye mata sunyi faɗa ba da duk haka bai faru ba, shiyasa yake jin hauahinta sosai tunda yace mata duk abinda yaran suka yi mata ta faɗa masa ya yi musu hukunci da kansa amma bata ji ba.
Koda ya dawo sashin Rashida ya shiga ya samu tana kwance kan kujera, ya cigaba da bata baki akan komai zai yi daidai kana ya tambayi me suke buƙata, ta faɗa masa sai ya yi mata sallama ya wuce ya fita ba tare da ya shiga sashin Safna ba. Bayan fitansa Rashida ta tashi ta zauna tana ɗaukar alwashin saita ci uban Safna cikin ruwan sanyi, kuma Hajiyarsa sai tasan ta nuna mata ƙiyayya, su Anisa banda zugata ba abinda suke yi, har mamansu sai da suka kirata suka bata labarin abinda ya faru, cewa tayi ta kwantar da hankalinta tunda ko a yadda Zayyad ke rawar ƙafa da ita sun fara samun galaba ta fita batun mamanshi.
*
Safna
Shiru shuru tana jiran Zayyad ya shigo amma bata ganshi ba, har ya dawo daga kai Ammi ya kuma fita bai leƙo ba, abin yayi matuƙar ɓata mata rai amma ya zata yi dole ta sauko tunda ita ce ranar zata amsa girki. Wajen ƙarfe uku na rana ta kirashi ya kai sau uku amma yaƙi ɗauka, hakan yayi matuƙar baƙanta mata rai amma saboda ta fita haƙƙinsa kuma ta saba tambayarsa abincin da zata girka yasa ta tura masa text kamar haka.
Assalam na kira shuru baka ɗauka ba Allah ya huci zuciyarka, dama ina so naji me zan dafa mana anjima.
Ta tura masa amma ba reply, ganin har bayan La’asar bai kirata ba kuma bai tura mata saƙo ba yasa ta shiga kitchen ta ɗaura tuwon shinkafa miyar kuka da busasshe kifi dan tasan yana so, harta kammala ta zuba taci ta ƙoshi dan ba wani abincin kirki taci ba a ranar, wajen gabda magrib ta yi wanka ta shirya cikin ƙananun kaya riga mai guntun hannu da siket iya rabin cinyarta, ya kama jikinta duk wani halittarta ta fito, dan ranar ne farkon data fara saka kayan duk dan tayi amfani da wannan damar ne wajen jawo hankalin Zayyad ya daina fushi da ita.
…
Bayan sallar magrib Zayyad ya dawo daga shago, ya yiwa Rashida siyayyen kayan marmari da kuma nama tsire, sashin ya fara shiga ya taddata tana zaune ƙafafunta suna ƙasa ta jingina bayanta da jikin kujera, da sauri ya ƙarasa ya aje ledojin hannunsa akan Center table yana duban Rashida cike da fara’a a fuskarsa.
Alhamdulillah kice sauƙi ya fara samuwa.
Wlh kuwa ka ganni ina motsa jikina tafiya ne ya rage mini, gaskiya maganin mutumin nan yana da kyau.
Sosai kuwa dan ga alamu mun gani, saboda har abinci taci fa sosai.
Cewar Zaliha data fito da plate a hannunta daga kitchen tana cin abinci, Anisa ta fito da ƙaton tire da abinci a kai da ruwa ta dire a center table tana cewa.
Abban Ilham ya aiki, nasan ka shigo da yunwa ga abinci ka rage hanya kafin ka isa gurin Amarya.
Wlh kamar kin san yau haka na yini banci abinci ba sai drink da cincin ne a ciki na.
Ya faɗa yana samun guri ya zauna, Anisa taja center table ɗin a gabansa ta buɗe masa abincin fried rice ne data girka dan ba laifi ta iya girki, Zayyad ba tunanin komai ya soma cin abincin, su kuma suka shiga shan kayan fruit ɗin daya shigo dashi, ya ɗiba tsiren ya saka a saman abincinsa yana ci su kuma suka raba sauran tare da ɗibarwa Rashida nata, haka Zayyad ya shagala har aka kira sallar isha’i kafin ya miƙe dan ya kammala cin abincin, ya kama hannun Aslam suka fita masallaci, Anisa ta kalli Rashida tana sakin dariya.
Anty fa ga dukkan Alamu kin samu akalar Zayyad, dan gabaɗaya ma ya mance da cewar ba ke ce da girki ba.
Hmmmm ba kuga komai bama dan yanzu aka fara wasan.
Cewar Rashida cike da tsantsar farin ciki, haka suka dinga hira cike da nishaɗi dan ko ba komai yadda Zayyad ya share Safna yayi matuƙar faranta musu rai.
….
Safna tun tana duba lokaci har ta gaji ta koma ta zauna a cushing ta rafka tagumi tana tsumayen shigowar Zayyad, saboda taji ƙarar shigowar motarsa sannan yanzu ma da zai tafi masallaci taji yana cewa Aslam yayi sauri, faɗar damuwar da ta shiga ɓata lokaci ne haka ta miƙe jiki a sanyaye ta shiga bedroom ɗinta ta gabatar da Sallah, tana zaune a dadduma taji dawowarsu da saurinta ta miƙe har tana haɗawa da gudu danta buɗe masa ƙofa saboda tasan yanzu dai dole ya shigo ɗakinta, amma ga mamakinta sai taji shuru har saida ta buɗe ƙofarta ta fito tsakar gidan ta tsinkayi maganarsa a falon Rashida, kamar zata je ta same shi sai kuma wani zuciyar ya gargaɗeta akan kar ta kuma wani laifin, sai ta juya ta shiga ɗaki tana matsar kwalla, tabbas Abin da ciwo a zuciya dan babu wanda zai fahimci ya Safna taji a wannan lokacin sai wacce ta samu kanta a irin wannan halin, ace kina da kishiya kuma ke ce da girki amma namiji ya nuna baisan da ruwan halittarki ba, zama tayi a carpet tana wani irin kuka saboda wani abu mai nauyi daya tokare mata maƙoshi, a buɗe tabar ƙofar amma har kusan goma saura Zayyad bai shigo ba, haka ta miƙe da kyar ta wuce bedroom ɗinta ta kwanta tana ambaton sunan Allah, duk addu’ar data faɗo a bakinta shi take yi domin kawai ta samu sassaucin halin da take ciki, a haka har taji zuciyarta tayi sanyi sai dai damuwar yana nan daram, hawaye kuma da kanshi ya ƙafe ya daina zuba dan kansa, har barci ya fara ƙoƙarin ɗaukarta.
Zayyad ko tunda ya shiga falon Rashida ya tadda suna cuku cukun ɗaukarta su shigar da ita ɗaki akan zata yi wanka, sai ya ce su bari shi da kansa ya ɗauketa ya kaita bayi yayi mata wanka ya fito da ita ya kwantar a gado, ya shirya ta cikin kayan barci kana ya gyara mata kwanciya ya miƙe da nufin tafiya yana ce mata sai da Safe, Rashida ta marairaice fuska ta kamo hannunsa.
Ji nake yi in ka tafi kamar ba zan sake ganinka ba sai dai na ganni a kushewata.
Dan Allah ki daina wannan maganar.
To ka zauna kayi mini hira in samu barci sai ka tafi.
Ba musu Zayyad ya zauna ya cigaba da yi mata hira, har saida barci ya kamata kusan ƙarfe sha ɗaya kafin ya miƙe ya fito lokacin su Ilham suma sunyi barci, sai su Zaliha da suke kallo a tv yayi musu saida Safe kana ya wuce sashin Safna. Yana shirin buga mata ƙofa sai ya tadda ƙofar a buɗe yake ya shiga da sallama ya wuce ɗakinta ya cire kayan jikinsa, Safna duk tana jin motsinsa koda ta fito ta shiga ɗakin ta samu ya shiga wanka, sai ta ciro masa kayan barcinsa ta aje a gadon ta koma ta zauna, harya fito ya taddata, tace masa sannu da zuwa ya amsa a daƙile, sarai yaga kayan data ciro masa amma sai ya wuce wardrobe ya ciro wasu ya saka, Safna ta miƙe tana cewa.
In saka maka abincin ne?
A ƙoshe nake, zaki iya zuwa ki kwanta dan barci zanyi.
Daga haka ya ƙarasa saka kayansa yabi lafiyar gado ya kwanta, Safna da jikinta ya ɗauki rawa bata ce masa komai ba ta fice daga ɗakin, ta koma ɗakinta ta kwanta tare da jan bargo dan zazzaɓi taji ya rufeta. A wannan daren wani irin ƙunci Safna ta samu kanta a ciki wanda ƙiri ƙiri barci ya kauracewa idonta, sai gabda kiran sallar farko ta samu ya ɗauketa.
**
Washe gari wajen bakwai saura ta farka taga gari ya yi haske, da sauri ta sauko ta shiga toilet ta dauro alwala ta gabatar da sallar asubahi, data idar ta fito ta duba Zayyad amma baya ɗakinsa kuma baya falo hakan ya bata yana sashin Rashida, hawaye taji ya sauka a kuncinta sai kawai ta wuce kitchen ta shiga haɗa musu breakfast. Wajen takwas saura ya shigo ya sauya kayansa tana sauri ta cimmasa a ɗakinsa sai gashi ya fito falo yana saka links ɗin hannun rigarsa.
Ina kwana.
Lafiya, ni zan kai yara makaranta daga can zan wuce shago.
Na gama haɗa breakfast ba zaka dawo kaci ba.
Kici kawai dan sauri nake yi.
To anjima me zan dafa?
Ki dafa abinda ya sauwaƙa.
Yana kaiwa nan ya juya ya fice, da ido Safna ta bishi har ya fita tamkar wani baƙon mutum haka ya zame mata, dan fuskarsa a tamke yake yi mata magana, sosai Zayyad ya shayar da ita gubar mamaki bata taɓa zaton haka yake ba, jiki a sanyaye ta koma kitchen ta ɗiba breakfast ɗin soyayyen arish da kwai ta fito ta nufi wajen maigadi Zayyad yana tsaye tazo ta wuce, ta miƙa masa yana zabga mata godiya, Safna tace.
Anjima akwai sauran tuwo zan kawo maka, sannan in ka samu almajiri ka yi mini magana shima na saka masa dan yana da yawa kuma kar ya lalace.
To ‘yar baba nagode Allah ya saka a mizani.
Ta amsa da amin ta zo ta wuce su lokacin yaran sun fito sun shiga mota ga Anisa tana yi musu bye bye, ta shiga ɗakinta ta rufe da key ta ɗauko sauran abin karin tazo ta zauna, da kyar ta iya cin kaɗan ta mayar da sauran ta koma ɗakinta ta kwanta ta shiga karanta wasiƙar jaki.
A takaice haka Safna ta fita girki Zayyad bai ci abincinta ba, sannan tunda Rashida ta amsa girki in ya leƙota da safe to bata sake ganinsa sai wata safiyar, tayi kuka har ta gode Allah ga ciki ga ciwon kunne da har lokacin yana mintsilinta ga damuwar Zayyad, bata iya cin abinci sai ta tilastawa kanta sai yawan shan ruwa, nan da nan ta rame ta yi wani haske, taƙi faɗawa kowa halin da take ciki face Allah dan shine kaɗai gatanta.
**
Bayan kwana biyar.
Wanda ya kama ta amsa girki ta fita, Rashida ma ta amsa hatta fita itama, Safna ta kuma tq amsa har tayi kwana ɗaya jiya, kuma har lokacin Zayyad bai daina fushi da ita ba kusan mako guda suna abu guda, a ranar ne ta yanke shawarar tunkararsa da maganar dan ta bashi haƙuri su shirya, saboda ita ce ke cutuwa saboda shi yana walwalarsa a sashin Rashida wacce har ta ji sauki Anisa ta tafi gida sai Zaliha ce ta rage tana ɗan tayata aiki. Ranar ta tura masa text akan tana so a kawo mata fulawa zata yi ɗan wake, duk da in ta tura saƙo baya yin reply amma yana aikowa. Can wajen ukun rana ya aiko da fulawa haɗe da kwai da mangyaɗa, nan ta soma haɗa ɗan waken saboda bata ci komai da rana ba shi take jira, kafin La’asar ta gama dan haka ta zuba taci haɗe da kayan miya data yanka da kwai data dafa, taci sosai kuwa dan ta jima bata ci abinci haka ba, ta tsame sauran a matsami akan anjima zata ci in kuma yace zaici duk sai ishesu tunda har lokacin baya cin abincinta, ta samu ta gabatar da sallar La’asar sai ta zauna a adduna tana jan hasbulallahu wa ni’ima wakil ƙafa 450, Ya hannu Ya mannanu ya bidi’assamawati wal ardi ya zaljaluli wal ikram shima ƙafa ɗari, tare dasu salatin annabi dubu da Bisimillahi dubu, haka ta kai kusan ƙarfe biyar tana lazumi daga bisani ta yi addu’a ta miƙe ta fito falo ta kwanta a doguwar kujera ta soma kallon MBC bollywood.
Yauma kamar kullun Zayyad bai shigo sasshinta ba koda ya dawo sai wajen ƙarfe tara da rabi, ya shigo ya sameta a falo tana kallo tana ganinsa ta miƙe tana yi masa sannu da zuwa, ya amsa ba yabo ba fallasa sai ya wuce ɗakinsa ita kuma ta wuce kitchen dan shirya masa abinci, ta gama haɗa komai a babban tire ta fito dashi falo ta ɗaura a table sai ta wuce zuwa ɗakinsa, koda ta shiga taji saukar ruwa alamar ya fara wanka, sai ta zauna gefen gado tana jiransa amma me? ƙarar saƙon WhatsApp ya cika mata kunne dan datarsa a buɗe yake, kamar ance ta ɗauki wayar taga saƙonni yana shigowa ta sama, abinda idonta ya gani na saƙon Saima sai da taji kamar anbuga mata guduma a kai, wanda yasa aljanunta motsawa saita samu kanta da danna PIN ɗinsa wanda ita bata sansu ba amma aljanunta sun yi amfani da hannunta sun buɗe mata, ta shiga WhatsApp ɗinsa tare da shiga number ɗinta Saima nan taga hirarsu na batsa da yawa, sai ta fito ta shiga duba sauran numbers ɗin, nan taci karo da Zuby itama dai kusan hirar da yake yi da Saima suke yi, sai dai yadda suke roƙonsa da magiyar yazo su haɗu ya bata mamaki, kuma a hirar taga yasha tura musu kuɗi, sosai gumi ya gama rufeta dan hankalinta yayi mugun tashi. A lokacin ne Zayyad ya fito daga bayi ɗaure da towel ga wani ƙarami a hannunsa yana goge kansa, Safna ta ɗago tana kallonsa cike da tuhuma shi kuma wani faɗuwa gabansa yayi ganin wayarsa a hannunta, da sauri ya yarda towel ɗin hannunsa yazo ya kwace wayar yana hucci.
Uban waye yace ki taɓa mini wayata.?
Ya ƙare maganar yana kifa mata mari cike sa borin kunya, Safna ta miƙe jikinta babu inda baya rawa tama kasa magana, ta fashe da matsanancin kuka tare da dafe mararta data ɗaure mata, nan take kuma jini ya ɓalle mata.