Nama ya hadu romo danye Book
NAMA YA DAHU….
ROMO ƊANYE
LITTAFI NA UKU
GAWURTATTU UKU
NA.
BADI’AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
SHAFIN FARKO (1)
IYABO:.
Buy Data Here SME data and Electricity bill Payment
“Iyabo da wuya ta kasheki gara daɗi ya kasheki. Ki tuno da irin taimakonmu da Saleem yayi mana a lokacin da muke da buƙatar taimakon . Dubi Ahalinshi yadda suka karɓeki duk da kina matsayin baƙar fata, beyerabiya. Ki duba kuɗi da Saleem ya kashe miki. Kayanmu gashi sun iso suna gidana. Ki duba Saleem ya baro ƙasarsu yazo gareki Iyabo. Irin sakayyar da zaki mishi a ƙasar taku kenan?” Uwani ta ɗaureni tamau da dukkan jijiyoyin jikina. Illahirin jikina a mace yake murus.
Gaskiya Saleem bai cancanci irin wannan tarbar daga gareni ba. Ɗan murmushi nayi na dubeshi. Ya riga da ya gane akwai matsalane, dan yanayinshi ya sauya, jikinshi kuma yayi sanyi.
“Zuwana ya haifar da matsalane Zauja? Ya tambayeni da larabci.
A’a Saleem. Ya hanya ina fatan kazo lafiya?” Murmushi yayi tare da sauke ajjiyar zuchiya har yana dafe saitin zuchiyarshi.
Hararata Uwani tayi, ta miƙo mun wata jakar kwali wadda sabida ruɗu ni ban ganta tare da jakarnan ba sai yanzu.
“Gashi wannan tsarabarki ce daga surukarki”
Fizgewa nayi dan a wuya nake da Uwani. Dariya tayi kawai tace.
“Iyabo kenan. Baƙin halin naku na yarbawa masu kwalo_kwalo ya motsa kenan?”
Banza nayi mata, na mayar da hankalina ga Saleem tare da yi mishi godiya da tsaraba, na tambayi lafiyar mahaifiyarshi da danginshi duka.
“Duk suna lafiya kuma sunce a miƙo miki saƙon gaisuwarsu gareki. Kuma sunyi mun fatan nasara. Meke damun Mamane haka, sannan me yasa aka kawota wannan asibitin, kuma ɗakin duk mutane.” Ɗan murmushi nayi. Duk wannan abun fa hankalina yana ga Hamma.
Babu komai asibitin yana da kyau. Kuma jikinta ya warware an kusan a sallamemu mu koma gida in sha Allah.”
“To Shikenan zanje in yi sallah inna dawo sai mu tattauna, kuma a gabatar dani ga magabata ayita ta ƙare ko zan samu nutsuwar zuchiya.”
Kwatancen hanyar da zaiga masallaci nayi mishi. Yana tafiya na dubi Uwani nace.
Yanzu Uwani yaya zanyi? Ni da Hamma lokaci kawai muke jira, ina tabbatar miki da ba dan ciwon Dada ba da yanzu wata maganar akeyi ba wannan ba. Wallahi Uwani ni zuchiyata tafi nutsuwa da Hamma fiye da Salim batun ƙauye ko ƙauyanci kuma ni naji na gani zan rungumi aurena in zauna a ƙasata ni yafi mun rufin asiri. Ki tuno irin baƙar azabar da muka sha a hannun larabawa. Shi Salim ɗinnan kinsan mazinacine gangaran, tantirin mazinaci ma kuwa, dani dake da Faty duk fa mun sani. To ina sane bazan auri mazinaciba, ni abun hannunshi bai tsole mun idoba, Uwani kiyi tunani. Zina yaɗo take yi ta lashe zuriya, ki duba mazajen larabawa da yawansu kamar Ayu suke dan tsabaragen son mata”
Jim Uwani tayi can ta dubeni tace.
“Yanzu ke dai kinji kin gani Hamma dai kike so zakiyi haƙuri da duk abinda in kika shiga zaki gani, shin tunda kin kawo hujjojinki na ƙin auren Saleem shin Iyabo me zai hana ki nutsu ki yi kasuwancinki da sannu Allah zai ɓullo miki da wani, shin ko a matse kike?”
Sosai kuwa, muna fatan ganin alkhairi. Nifa na tsorata da sha’anin larabawa ko karen hauka ya cijeni bazan auri Salim ba. Uwani ki mishi bayani an riga an haɗani auren zumunci da ɗan uwana wanda suka gaisa saura sati ɗaya ma ayi bikin in samu mu rabu lafiya” Mun daɗe muna tattaunawa, Uwani ta jima tana bani baki akan nayi nazari kafin yanke hukunci. Ita a tunaninta dan gudun dana sani. Ni kuma babu dana sani a soyayyata da Hamma. Har Salim ya dawo bamu tsaida matsaya ba. Ciki na shiga na kawo mishi madarar shanu a gora yasha sosai sai santi yake yi mana. Uwani ce ta nutsu ta soma yi mishi bayani da larabci kasancewar ta fini ƙwarewa a yaren. Salim hankalinshi ba ƙaramin tashi yayi ba har ƙwalla saida ya zubar wallahi.
“Allah shine shaidar son da nake yi miki. Ni nasan harda tsoro yasa kika ƙi aminta dani Iyabo. Yaya zanyi da sonki, kinsan sonki zai iya zautani kuwa?”
Wasu siraran hawayene suka gangaro a kumatuna. Salim duk ya birkice abinka da farin mutum har fuskarnan tashi ta Zama jawur da’ita haka ma idanunshi.
Salim kayi haƙuri bazan iya saɓa ma iyayena domin faranta nawa ran ba. Yayana suka zaɓa mun. Ina mai baka haƙuri , Allah ya ɓillo maka da wacce ta fini alkhairi a rayuwarka da addininka. Na yaba nayi godiya da soyayyarka a gareni kayi haƙuri ” murmushi yayi mun yace.
“Ina sonki Allah. Amman na haƙura har ga Allah kuma ina roƙon Allah ya baki zaman lafiya da mijinki ya baki zuriya ɗayyiba. In na haifi yarinya zan saka mata sunanki Iyabo”
Sai zuchiyata naji ta tsinke ainun. Babu shiri hawaye ya shiga gudu a kumatuna. Billah da zan iya amsar son Salim da zan amsa. Amman kash ko wacce zuchiya da abin sonta, kuma ko wacce ƙwarya tana da abokin burminta.
Jabu zaka saka ma yarinyar taka. Sunana kenan ta ɓangaren mahaifiyata.” Dariya yayi yace.
“Jabu what a nice name” Miƙewa yayi tsaye hannayenshi a cikin aljihun jallabiyarshi yana kallona yana nazartata, ko kuma karanta wasiƙar jaki.
“Zan koma Kano. Jibi zan koma inda nafi wayau. Zaki ga saƙona inna koma ga wannan gudunmawatace ki sai gadon da angonki zai hau ku raya sunnah nayi imani zan samu lada. Kiyi alƙawarin siyan gadon kar ki saɓa Jabu.’
Kuɗi masu kaurin gaske ya bani, wanda a wannan lokacin inna canja kuɗin zasu iya kaiwa dubu ɗari biyar irin ta da bata wannan zamanin na tinubu ba.
Godiya nayi mishi har tashar mota ni da Uwani muka rakashi dan ita tace zata kwana biyu ta tayani jinyar Dada. Sai da muka ga tashin motarsu yanata ɗaga mun hannu idanunshi fal ruwan hawayen bankwana.
Kuka na saka rikitaccen gaske na runtse idanuna tsigar jikina sai tashi take yi. Tausayin Salim ya dirarmun sosai.”
“Ki dena kuka Iyabo, na fahimci ke kanki bawai son Saleem bane bakya yi ba A’a. Son da kike yima wancan figaggen ne yafi na Saleem. Kamar yadda Hamma yake sonki fiye da Saleem ɗin. Muje magriba ta kawo kai, kiyi haƙuri ki fuskanci yadda zaki fahimtar da gogan naki naga ya ɗauki zafi, fulani dama suna da tsantsar kishi gaskiya. Nifa mamaki iskancin Hamma yake bani “
Wallahi Uwani ni tausayi ya bani. Jibi yadda yake kuka kamar ƙaramin yaro fa. Uwani ni nasan raɗaɗin son maso wani. Sannan ni ina gujema matsaltsalun rayuwane. Na tsorata da auren mijin da ba yarenku ɗaya ba. Fulani da yarbawa kuma suna da daɗaɗɗen tarihi na zamantakewa da auratayya. Bugu da ƙari Hamma jininane, ina tsoron kada son abin duniya yasa in zaɓi Saleem harga Allah Hamma nake so” Uwani ta ja gwauron numfashi tace.
“Iyabo na fahimta, ni kaina waɗannan tunane tunanenne du banyi su ba. Duk da dai masu iya magana suna cewa abinda aka gasa shi yaji wuta”
Fitowa mu ka yi daga tasha muka tari abin hawa zuwa bakin asibiti. Gogan yana tsaye a bakin asibiti da halama ya kafane ya tsare yana son ganin ta inda zan ɓullo. Gabana ya yanke ya faɗi ganin irin kallon tuhumar da Hamma yake yi mun.
“Uwani baƙon ya tafi ne?” Ya tambaya yana kakkafe ita uwanin da ido.
“Ya tafi Hamma. Dama dai ya matsa ne yana son yaga Jabune, sabida kayan da yawa bazai yiwu ace ya tafi ba tare da ya ganta ba.” Murmushi yayi kawai ya kalli tsakiyar idanuna, saiya soma kallon ƙwayar idona da ɗaya da ɗaya. Ta gefena Uwani ta shige.
“Wannan soyayyar taku inna tsaya anan Hamma sai zuchiyata ta buga” Cewar Uwani data yi shigewarta ciki.
“Me yazo nema a wajenki, kuma me yasaki kukan da har fuskarki da idanunki suka sauya launi?”
Wannan tambaya tashi ta sake rikitani, bansan me zance mishi ba.
“Ki shiga ciki su Hama da Daso suna ciki. Ni zanje masallaci inna dawo zan raka Hama gida”
To Shikenan sai ka dawo”
A gurguje na wuce tare da sauke ajjiyar zuchiya a haka dai kamar fishin nashi ya sassauto.
A wajen gadon Dada kuma su Daso suna zazzaune a tabarma suna fira ita da Hama ƙawarta. Gefensu kwanukan abincine da suka kawo. Uwani kuma tana zaune a kujerar roba inda nake zama. Ina isowa Hama ta dena hira ta haɗe girarta ta ƙasa data sama. Ita kanta Daso na ga canji sosai a yanayinta. Nasan yana da nasaba da tsaida lokacin aurenmu da Hamma.
Sannunku Daso ashe kunzo, ina wuninku?” Daso ce ta amsa babu yabo babu fallasa dai, Hama kuwa bata ce um ba, wasa take da hannun ɗiyarta dake kwance a cinyarta.
Uwani wannan itace Daso yarinyar ƙanwar Dada Yafendo Jabu me sunana. Wannan kuma Hama ce matar Yaya Hamma “
“Ayya, ai mun gaisa kice itace uwargidanki. Hama Allah ya sanya alkairi Allah ya haɗe kawunanku.”
“A gaskiya baiwar Allah baki kyauta ba ai ba’ayin haka. Sanin kanki ne babu macen da take son kishiya, ita kanta Jabun da ita za’aima kishiyar aka mata haka ba zata ji daɗi ba”
Daso ce tayi maganar cikin fishi da fishin Hama. Sanin halin ƙawata Tabalbalin yasa nace.
Kuyi haƙuri itama bata faɗa da niyya ba” Tsaki Hama tayi, Uwani tace.
“Allah sarkin girma inji kishiyar mai Ɗuwayya. Allah ya baku haƙuri ni ba baƙuwar zafi bace. Amman fa ku iya bakunanku in kuma ba haka ba sai dai kuji jini na zuba, ƴan iska ƙauyawan banza duk kun cika waje da ƙarni.”
Duk wannan abun da akeyi Dada bacci take yi. Fulatanci da Hama ta soma zazzagowane ya farkar da’ita. Nasan dai ba alkhairi Hama take faɗi ba. Ɗiyarta ta goya tana ta huci.
“Daso meke faruwa ne?” Dada ta tambaya.
“Babu komai Dada” Amsar da Daso ta bata kenan. Ana cikin haka sai ga Hamma ya iso.
“To muje ko dare nayi. Dada saina dawo zan kaisu gida”
“To dama ka zauna a gida. Jabu da ƙawarta zasu kwana anan. Kaima ka huta. Ka sanar da Baffa Musa, inason ganinshi gobe da sassafe.
“Haba Dada. Kona koma gidan ma ni bazan iya bacci ba. Likita ma ya tabbatar mana zuwa gobe ko jibi zai sallamemu mu koma gida. Hama muje”
Fuuu Hama ta fice ko sallama batai mana ba, Daso ce kawai taima Dada sallama ni ko da uwar harara ma ta bini. Ni kuma nayi mata murmushi kawai nasan kishin rashin Hamma ke damun Daso, ba taya Hama kishi ba. Tunda data samu dama itace zata zama kishiyar Haman.
“Ga abinci kuci Jabu. Baƙon ya tafi ko?”
E Dada ya tafi”
Matashin kanta ta ɗan ɗaga ta gefe ta zaro kuɗin da Saleem ya bata ta miƙo mun.”
“Ki riƙe a hannunki, ni bansan ma nawa bane. Jabu su Yusufu har yanzu basu zo sun dubani ba” Murmushi nayi mata nasa hannu na amshi kuɗin
Dada nice na hanasu zuwa, kiyi haƙuri an kusa sallamarmu mu koma gida”
Maimakon naga tayi farin ciki. Sai naga saɓanin hakan damuwa ta bayyana a fuskarta. Babu shiri na ƙarasa wajen gadon na zauna a gefe guda.
Dadana na siya miki gidan da zaki zauna ki huta ki mori haihuwa kema. Kuma in sha Allah zan zuba miki kayan alatu da zaki more tsufanki. Kulawarki ta dawo hannuna Dada. Su Cubu zasu zauna tare dake, na ɗauke miki nauyin komai Dada. Nasan ƙila tunanin inda zaki zauna kike yi” Hawayene ya gangaro ta gefen kuncinta, sai ta runtse idanunta tace.
Ubangiji Allah ya kai haske kabarinka Akintoye. Haƙiƙa kabar baya me kyau. Jabu kamar yadda sanadiyyarki matsalolin rayuwata suka gutsire. Ina roƙa miki Allah Hamma ya zama silar goge miki damuwar rayuwarki. Sannan inaso in faɗa miki kibi Hama a sannu, sannan kibi Daso a sannu. Ɗazu ba bacci nake yi ba duk abinda suka tattauna duk a kunnena. Dansu a kuɗirinsu shine aurenma bazai yiwu ba. Bokaye sosai Hama take bi duk dan a raba soyayyarku. Ke kuma saiki dage da roƙon Allah yai miki tsari da sharrinsu. Nayi imani da Jabu uwar Daso zata san abinnan da Daso tayi zata iya yi mata baki. Dan haka kija bakinki kiyi shiru komai ma yazo ƙarshe daga gobe za’a yita ta ƙare” Hannun Dada na damƙe na lumshe idanuna. Na lura a wannan tafiyar kamar da jarabawar kishiya kuma zan jarabtu na tsallake rijiya da baya akan uwar miji, ga kishiya kuma jama’a tana neman rayuwata.
Babu komai Dada, Allah shi ke da iko akan komai. Ki tayani da adda’a nima zan zage damtse. Ki kuma dena kuka Dada, Allah ya jiƙan Baami”
Dawowa nayi kusa da Uwani a tabarma. Na zuba ma Dada jallof ɗin shinkafa dasu Daso suka kawo, har zan miƙa mata sai naga kamar yayi kaɗan sai na saƙa cokali zan ƙara mata. Wallahi saiga dunƙulen magani a cure a waje ɗaya bai idasa cakuɗuwaba.
Subhanallaah Uwani duba” Na nuna ma Uwani. Haɓa ta kama tare da zaro idanu.
“Iyabo wannan ai dunƙulen maganine, hala kishiyarkice ta kawo abincin?” Da kai na amsa mata. Juye abincin nayi na rufe, na jawo kular Karima matar Amaduyal na zuba ma Dada abincin ciki. Shinkafa da miya da kifine. Na miƙa mata na bata ruwa. Na saka mana cokula biyu a cikin kular zamuci dan sabida ƙauyanci a kan shinkafar ta kyaɓo miyar.
“Iyabo jikina yayi sanyi tsoron Allah kuma ya kamani. Tofa wata sabuwa inji ɗan caca. Shi kuma wannan auren na lura da kishiya za’a fafata. Nifa duk harkar asiri bana ciki. Ko kishinne nafi son muyi na kirsa duk wacce ta biya allonta saita wanke. Amman tun kafin ki shigo ciki an soma binki da bita da ƙulli?” Ni dai ko magana wannan na kasa yi. Sai cin abincin nake yi. Abincinma sharkab da mai dan masifa sai tea na haɗa mana muke danne man dashi. Wajajen bayan isha Yaya Hamma ya dawo. Leda ya miƙo mun ɗaya cike da tsire, ɗayar kuma lemun kwalba ne montin dew. Dada ta ɗan jima da bacci sabida magungunanta kamar akwai masu saka bacci.
“Ni kam me ya haɗaku da Hama da Daso Jabu”
Kallonshi nayi, sai na fahimci ranshi a ɗan ɓaceyake sai nace.
Babu komai wani abun suka ce maka anyi?”
“E Hama tace mun wai kince kinfi ƙarfin kiyi kishi da’ita dakin shigo zaki kaɗata. Maganganu dai marasa daɗi Daso tace har mahaifiyar Hama kika zage tas. Dan Allah meye gaskiyar wannan lamarin?” Kallon kallone ya shiga wanzuwa tsakanina da Uwani.
Tab wata sabuwa inji ɗan caca, ni Iyabo gidan da zan faɗa kuma kenan? Ga asiri ga makirci anya kuwa? Uwani ce naji tayi mishi bayanin abinda ya faru. Sai yayi dariya kawai yace.
“Kishi ne yake damunta sosai shi yasa ita da Dason suka ƙirƙiri wannan maganar. Amman zan ɗauki mataki akan ita Haman ni na isa da gidana.
Jabu ina jiranki a waje domin ki bani amsar tambayoyina”
Yana idasa maganarshi ya fice hannunshi riƙe da sandar da ba’a fiye raba bafulatani da’ita musamman ma masu fita kiwo. Idanuna na lumshe kaina sarawa yake yi sosai.
Uwani ci namannan bari inje in kashe wutar da kika kunnamun. Inna dawo zamu tattauna matsaloli Uwani”
Nan na bar Uwani tana cusa tsire da albass a bakinta. A inda yake kwanciya na sameshi kanshi a ƙasa yana bubbuga sandarshi a ƙasa. Harna zauna bai ɗagoba, ko salllamata yaƙi amsawa lallai ran maza ya ɓaci.
Angona masoyina wanda ya zama zaɓina abun begena. Lafiya ka kasa amsa sallamata, ko dai maganganun da Hama tace na faɗa mata ne suke damunka?” Shirune ya biyo baya na daƙiƙu kana ya ɗago idanunshi ya saukesu a kaina. Na kasa karanta haƙiƙatan ɗin abinda ke cikin idanun nashi, na hango kishi, da so mai wuyar fassarawa. Ajjiyar zuchiya na sauke tare da yin ƙasa da idanuna, ina jiyo yadda idanunshi ke yawo a fuskata.
“Wallahi Allah ina da mugun kishi akan duk abinda nake so. Wannan dalilin yasa na kusan kashe ɗan uwan Hama a filin shaɗi a lokacin da ya zama daga cikin gwarazan da suka fito neman aurenta. Jabu kafin ki tafi saida na damƙa miki amanar rayuwata nasa kikai mun alƙawarin babu wani ɗa namiji da zaki bashi damar shiga rayuwarki. Kaico ashe ke soyayya kiketa ta yi. Ni kin barni da dakon sanki, kewarki duk ta hanani sukuni, hatta bacci me kyau ina samune duk ranar da nayi mafarkin na aureki jibi yadda na fita hayyacina Matata da abokaina kullum a cikin surutun lalacewata suke. Amman ke ashe mu biyu kika ajjiye a gurbin zuchiyarki, kin ban mamaki sosai Jabu.
Meye matsayin Saleem a wajenki, kuma me yazo yi wajenki, Allah yasa ba kukan sonshi kika yi ba?”
Shiru nayi kamar ruwa ya cinyeni tunda ya soma maganarshi harya dure. Akwai taushi da zafi cakuɗe da muryar tashi.
Yaya Hamma ka yarda dani kai ɗaya tal ne a zuchiyata ban haɗa soyayyarka data kowa ba. Ko uban Ƴaƴana ban soshi irin son da nake yi maka ba. Gaskiya dai ɗaya ce Saleem ya taimakemu a zamanmu na saudiyya. Dan shi yai mana hanya muka dawo Najeriya. Bamu yi soyayya ba, amman ya soni sosai. Dalilin zuwanshi kuma neman aurena yazo yi, kuma na faɗa mishi gaskiyar lamari. Batun kuka kuma ka gafarceni tausayi ya bani ne”
Ƙur idanunshi a kaina yana kallona irin kallo mai fassarar ban yarda dake ba. Idanu na lumshe na buɗe a kanshi.
Yaya Hamma”
Yayi saurin ɗaga mun hannunshi. Yayi magana da wata murya a ciki.
“Ya’isa haka dan Allah. Kar kiyi sanadiyyata inje in rataya a wuyanki. Ki koma ciki (🤣🤣) Uwani na jiranki saida safe”
Nayi yinƙurin fahimtar dashi tare da rarrashinshi. Amman bai bani wannan damar ba sam. Haka na miƙe jiki da zuchiya babu kuzari na shiga na samu Uwani tana waya.
Jagwab na zauna a gefenta ina ambaton Allah.
“Lafiya na ganki haka Jabu, an samu tsabanin fahimta da Hamma kenan ko?”
Ke dai bari yaƙi fahimtata akan zuwan Saleem Uwani. Amman zan bashi lokaci inya huce zai fahimceni. Ni wallahi komai ya fice mun arai, Hama lamarinta ya kashe mun jiki. Tsorona Allah tsorona hulɗa da mai mu’amala da bokaye Uwani. Wannan wanne irin zama zamuyi kenan, da wanne irin bita da ƙullin zata bini in mijin ya zama namu mu mu biyu?” Uwani ta muskuta kana tace.
“Adda’a takobin mumuni, bacci da barin bakinki shiru ba naki bane. Ni a tunanina da ai miki kisan mummuƙe aita gabza miki asirinma baki sani ba. Ai gara kin sani zaki san irin zaman da zaki yi da’ita. Ke dai ki zama me lura sosai. Kar ki sake kici duk abinda zai fito daga hannunta shine kawai tunda kin nace. Abinne Allah cuta Allah magani, tunda ko kai akazo aka tarar bakasan irin wacce za’a kwaso maka ba. In kinga irin yadda amaryar Hafizu take tata ɗiban albarka irin nasu na ƴan ƙauye Iyabo zaki riƙe baki. Kinsan akace shege na ƙauye.”
Dariyar dole Uwani ta bani, duk da labarin da take bani mai ciwone a gareta itama saida ta dara.
Bani labarin yadda ta kaya a tsakaninki da Hafizu ranar da kika koma”
“Hahahahhh baki da kyau Iyabo.
A daren ranar ni ban barshi ya shigo mun ɗaki ba. Kafin ya dawo na garƙame ɗakina. Bugun duniya banbi ta kanshi ba, sai matarshi ce tazo ta jayeshi tana cewa wai ya barni ƙila bacci nake yi.
Sai da safe dana buɗe ɗakina ya shigo muka gaisa sama_sama, ni dai naƙi sakin fuskata sai jana da hira yake yi nayi biris dashi. Ke saiga wani dumamen tuwo da wani ƙazamin ruwan kokko harda dogon gashi a ciki matarshi ta shigo ta dure mun.
Ke dai kinsan banda daɗi Iyabo, a taƙaice dai na sai gida a can saman layin ta titi, ɗakuna ukune sai banɗaki da kitchen harda shago a ƙofar gidan, nayi komawata. So nake inna nutsu a gyare mun shagon in soma kasuwanci a ciki, in Allah ya dafa mun shikenan fa Iyabo. In Hafizu yazo miji, in baizo ba shi da banza basu da maraba. Bazan kashe kaina ba wallahi sabida rijalu. Ko yanzu ya tafa mun takaddar sakina cafewa zanyi in cashi zawarci”
Kai na jinjina ina dariyar furucinta na kusa da ƙarshe da tace in yazo miji, in baizo ba shi da banza duk ɗaya.
Uwani ta balbalin duniya. A irin zafinki kam zama gida ɗaya da kishiya ba naki bane, raba gidan yafi. Koni da ace Hamma zai amince mun da saina sai waje na gina inyi zamana a gidana da saina fi samun nutsuwa. Amman kinsan ƴan ƙauye su gidan gandunnan shi suke yi, kowa dai da ɓarayinshi.”
“Amman dai zaki gyare ɓangaren naki yadda zaki ji daɗin zaman wajen ko? Ina tausayinki Iyabo baki san sharrin rijalu bane hmm” Murmushi nayi nace.
Sai dai in gyara cikin ɗakin nawa, wallahi Uwani bana son inyi wani abun da zai haskoma Hamma kamar na raina arzikinshi. To iyakar gyara zan yishine a cikin ɗakina”
Harara ta watso mun taja dogon tsaki ta jiya baya ta kwanta.
Uwani meye haka?” Cikin masifa tace.
“Da Allah Iyabo mu bar zancannan ni bacci nake ji naga kamar kin zama majuniniyane akan Hamma”
Dole haka zancan ya tsaya. Ni kuwa na jima cikin tubka da warwara da ƙyar bacci ya ɗaukeni cike da mafarkai marasa daɗi masu tada hankali. Gabaki ɗaya saina wayi garin cikin damuwa da fargabar data haifarmun da zazzaɓi.
Da sassafe saiga Yafendo Kaɓoji, da Baffa Musa sunzo.
Dada tace mu basu waje, me suka tauna oho basu jima ba suka kama hanyarsu. Muna komawa ciki saiga takaddar sallama da ragowar kuɗaɗen da ake binmu. Gashi yau tun sassafe Yaya Hamma ya bar asibitin. Uwani ta zauna da Dada ni kuma naje na biya kuɗin da ake binmu. Ina dawowa na tarar da Amaduyal shi da Kari matarshi. Kari ce ta tayani tattare kayayyakinmu tsab, Amaduyal kuma nace ya fita ya nemo mana ƙaramar mota zuwa Girai.
Ai kuwa hakan akayi motarnan ta saukemu a Girai muka hau akori kura zuwa Banyo, daga Banyo muka ƙarasa jaɓɓi. A sabon gidan Dada muka sauka. Ta kalli gidan ta kalleni saita saki kukan farin ciki ta dubeni tace.
“, Jabu Allah yayi miki albarka. In sha Allah Kamar yadda kika sani zubar da hawayen farin ciki. Rayuwarki zata yi albarka. Allah ya jiƙan Adetoye da rahama.”
Ameen Dada nagode sosai mu shiga ga ɗakinki nan. Wancan nasu Cubu ne, sai na su Yusufu gashi can.” Ɗakin muka shiga daga gado sai wata kujera doguwa guda ɗaya, sai kafet malale a ƙasan ɗakin da labule, sai akwatin kayanta guda ɗaya. Kayan ciki sababbi nasa aka ɗinko mata da hijabinta biyu da takalma biyu sai dadduma. Kan kace me labarin sallamomu ya kareɗe ƙauyen nan mata suka cika gidan ana ma Dada Yaya jiki ana mata barka da arziki.
To nima anan nake cewa mu tara gobe in Allah ya kaimu….
MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
Part 2
NAMA YA DAHU…
ROMO ƊANYE
BADI’AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
LITTAFI NA UKU (2)
Ni da uwani kuma muna madafa na hura kara ina kiciniyar ɗaura girki ta dubeni tace.
“Iyabo yanzu kema da karar zaki dinga girki in kunyi auren ko? Ni wallahi Iyabo ba wai ƙin Hamma nake yi ba, ba kuma ƙyamatar rayuwarsu nake yi ba.
Ke nake jiye ma, kece baki saba da irin wannan rayuwarba, su fes suke jin kansu ba wata matsala, ta ina ke zaki soma Iyabo?”
Murmushi nayi mata ko a jikina nace.
Nifa babbar nasara shine in zama mallakin Hamma kawai, kuma inason in zauna da Dada, aurenta fa ya mutu faɗa miki ne banyi ba uwani. Uwani zuchiyata tayi nisa da sonshi, idanuna ya rufe bana hango komai. Bini da adda’a ƙawata kawai, ki dena damun kanki. Da birni da ƙauye duk rayuwar ɗayace, ita mace kwanciyar hankali take buƙata a gidan aure ba birni ko ƙauyeba, sannan inason in koya ma ƙannena yadda zasu bautama Allah. Hatta Dada daga iya alwalarta akwai gyara ina ga karatun Sallah kuma.”
Dariya tayi kafin tayi Magana kawai sai muka jiyo guɗar su Boɗɗo da su Cubu, harda Yafendo Jabu. Kuma wajenmu suke nufowa. Suna shigowa Baɗɗo tace.
“Adda yau dai kin zama matar Yaya Hamma an ɗaura aurenku babu jimawa” Farin cikine, a’a ruɗewace sai kawai naji gudawa ta kamani. Kafin in miƙe sai Yafendona tace.
“Munyi farin ciki da wannan Aure. Muna fatan mutuwace zata rabaku. Adda Daso sai kukan farin ciki take yi”
Ni dai da jin wannan labarin saida nayi gudawa sau biyar cikin awa guda.
Ina cikin wannan zuruftu saiga Hamma da abokanshi biyu sun kutso kai gidan. Nayi maza na shige kitchen dan yafi kusa dani. Idanu na lumshe inajin wani farin ciki na cikar buri na lulluɓeni. Amman sun sammaceni, babu shakka wannan shine dalilin zuwansu Baffa Musa da safe asibiti, kuma shine dalilin Dada na cewa za’ayita ta ƙare, ashe tana nufin auren za’a ɗaura kowa ya huta. Uwani ce ta dafani nayi saurin buɗe idanuna.
Sun tafine uwani?” Na tambayeta ina dariya. Itama dariyar take yi tace dani.
“Sun tafi, dake da Hamma bansan wanda yafi wani farin ciki ba. Bakiga bakinshi ba yaƙi rufuwa sam. Ina miki fatan alkhairi Allah yasa ki samu farin ciki ɗorarre na zubar da makaman yaƙina iyabo, Allah ya ƙadarto miki rayuwa a rugga”
Ameen Uwani ko ke fa. Yanzu dai me ake ciki dangane da kayan ɗaki? Ni a kano naso sayen gado da kayan kujeruna gaskiya, to yanzu ba lallai lokaci ya bamu damar hakan ba”
Baɗɗo ce ta shigo tace.
“Adda kizo Baffa na son magana dake”
Uwani ki dinga duba girkinnan kafin inzo’
Nasa kai na shiga ɗakin Dada da sallama. Dukka ƴan uwan Dada suna ciki. Yafendo Kaɓoji tace.
“Tawo ki zauna a kusa dani ƴata”
Cike da kunya na ƙarasa na zauna a gefen ƙafarta. Baffa yace dani.
“Ungo nan Jabu sadakinkine nera dubu biyar. Ɗazu aka ɗaura aurenki a ƙofar gidan mai gari ke da Hamma. Amman kasancewar auren yazo babu wani shiri, inda zai saki ma bai gina ba tukunna zaki zauna a gida kamar na sati biyu kafinnan ya gama ginin ya kuma gama haɗa lefe sai ki tare”
Hannu nasa na amshi sadakin. Na kuma ji daɗi sosai da akace mun sai nanda sati biyu zan tare. Har zan shiga Kano inje inyi gyaran jiki in kuma siyi kayan ɗaki irin wanda raina yake so” Yafendo Kaɓoji tace.
“A’a Yaya sati biyu yayi yawa. Ginin yau zasu soma da abokanshi zasu iya gamawa yau. A bar dai tariyar rana ita yau zaifi” Dada tace.
“Allah ya nuna mana rana ita yau ɗin. Amman ita Jabu gobe zata koma kano kamar yadda na sanar daku, acan za’aje a ɗakko Amarya a wajen dangin mahaifinta suna da hakki. Da ace lafiya nake da ni da kaina zan kaita inyi ma Toyosi ɗin bayani a nitse dan gudun kar suga kamar anyi musu fin ƙarfine.” Baffa Musa yace.
“Hakanma yayi, babu damuwa ku zaku tsara yadda tafiya ɗakko Amaryar zai kaya. Allah ya sanya alkhairi. Jabu zaki iya tafiya sai ki kwana da shirin tafiya kanon gobe. Duk abinda zaki kintsa saiki kintsa rana itayau za’a zo ɗaukar taki, ki sanar musu suma acan.
To Baffa “
Iyakar abinda na iya cewa kenan. Na fita na samu Uwani na labarta mata duk yadda mukayi.
Haka dai muka wuni tarbar baƙi masu zuwa dubiya. Su Yusufu duk suna gidan sun shige ɗakinsu da abokansu. Sai da daddare Hamma ya samu zuwa muna tsakar gida mun gama cin abinci munyi sallar isha anata hira ina jin daɗin kasancewata tare da ƙannena, sai gashi ya shigo da sallamarshi.
“Ango kasha ƙamshi lale da zuwa”
Cewar Uwani kenan tana tsokanarshi. Hannunshi riƙe da ledoji biyu. Sai ya miƙa ma Cubu leda ɗaya yace ta kaima Dada. Ɗayar kuma yace ta Uwani ce, na karɓa na miƙa mata.
Watsewa sukayi suka barmu mu mu biyu a tsakar gidan. Ni ina kan tabarma shi kuma yana kan jarkar ruwa yana fuskantata.
Ina wuni Yaya Hamma?
Na faɗa a sanyaye da sabuwar muryar da baisan na mallaketaba. Wata iriyar muryace mai kama da busar sarewa.” Sai da ya sauke ajjiyar zuchiya nannauya kana ya dubeni muka haɗa idanu sai yace.
“Faɗa ya ƙare Hamma yayi nasarar samun Jabu na kayar da mutan birni.”
Dariya ya bani sosai.
Yaya Hamma kenan. To Allah ya bamu zaman lafiya. Allah ya baka ikon yi mana adalci a tsakaninmu”
“Ameen nagode da wannan adda’ar taki. Sai batun tarewa Dada tace an tsayar da maganar tarewa sati me zuwa. Kuma a Kano za’aje a dakkoki ko?”
Kai na gyaɗa mishi. Sai yace.
“Maganar kayan lefe zan baki kuɗinne ki siyo abinda kikeso a Kano harda fantimoti ko yaya kike ganin za’ayi?”
Duk yadda kayi daidaine na baka wuƙa da nama”
Kai ya girgiza yace.
“Ni kinga bansan kalaba. Sannan Hama ma ba sanin kala tayi ba bare in bata ta haɗo komai”
To ka tuntuɓi su Dada ko su zasu haɗa ni basai na haɗa lefe ba”
“To Shikenan Amarya yadda kikace haka za’ayi. Zan tuntuɓi matar ogana na birni naga kamar kayayyaki take siyarwa in yaso sai in bata ta haɗamun duk abinda ya dace. Yanzu nawa kike buƙata na gyare_gyarenku na Amaren birni?” Dariya nayi mishi. Shima dariyar yayi.
To kuɗin gyaran jiki, sai kuɗin ƙunshi, da kuɗin kayan fitar biki Shikenan abinda nake buƙata”
Hannu yasa a ajjihu ya zaro nera dubu goma sha biyar Murtala _murtala ya miƙo mun, nasa hannu na karɓa nasa musu albarka.”
“Gobe zanzo in kai ku tasha, dama inason zan sai fenti a birni mun gama gina miki ɗakinki. Duk da dai ban samu yadda nake so ba lamarin yazo mun babu shiri”
Zamu rabu kamar ba zamu rabu ba a wannan dare mai cike da ni’ima iska sai kaɗawa take yi hadari na rugugi a sararin samaniya. Ganin an soma yayyafi yif_yif yasa ba dan rai ya so ba muka rabu da juna cike da shauƙin junanmu.
Washe gari sassafe muka shirya tsab Yaya Hamma yazo ya kaimu tasha har sai da motarmu ta bar tasha suka tafi shi da aminanshi.
Bayan la’asar sakaliya muka shiga gida. Su Iya duk suna tsakar gida suna murnar haihuwar Bose muka tarar dasu. Nan murna ta zama bibbiyu.
Sai da muka nutsa muka rama sallolin da aka boyomu, Uwani tai ma Iyaa bayanin duk abinda ke a kwai.
Da jin wannan bayani sai Iyaa ta miƙe tsaye tana buga cinyoyinta tana faɗin.
“Mo ti pari mo ti pari ah ah ahh.. ( na gama yawo, na gama yawo) Iyabo aure a ƙauye a wannan garin zaki zauna kiyi zaman aure? Kin kashe rayuwarki, kin kashe kanki”
Kafin kwabo Sai gasu Iyaa Beji da su Iyaa Kokodeen sun shigo. Bata sauya zane ba. Ita dasu duk kanwar ja ce, sukaita kwakwazo har sai da Alfa ya shigo shine ya tsawatar musu. Iyaa kuwa du hannuwanta aka ta ɗorasu tana jijjiga harda hawaye shaɓe_shaɓe tana ta ambaton
Ah ah ah….” Wanda indai kaji beyerabiya nata maimaita wannan kalma to fa abu yayi abu. Alfa ya tambayi Iyaa Kokodeen meke faruwa. Kafin tayi magana Iyaa Debisi ta soma magana da yare ta bashi labarin abinda Uwani tace mata. Jimm yayi sai halamun tsoro suka bayyana a fuskarshi muraratan.
“Je otito Iyabo?” ( Da gaske ne Iyabo) Ya tambayeni idanunshi kakkafe a kaina.
Beeni ( Eh)”
Itace kalmar dana furta a sanyaye. Shima jikinshine ya kuma mutuwa mus. Gwauron numfashi ya sauke yace.
“To Allah ya sanya alkhairi. Tunda rayuwar da kika zaɓama kanki kenan mu bamu da abinda zamu ce dake. Toyosi kiyi haƙuri ki bita da adda’a a wannan karon kar ku juya mata baya.”
Da ƙyar ya rarrashi Iyaa ta haƙura. Ni da Uwani dai duk mun takure, Uwani taso tafiya ma, amman ganin irin faɗan da Iyaa ta dinga yi mun yasa dole muka kwana tare.
Washe gari ragowar samari da magidanta gidanmu duk labarin aurena ya ruskesu. Kowa sai jimantamun yake yi. Burodami Debisi kuwa kamar zai yi hauka da yazo gidan yaji labarin abinda ake ciki. Ƙasa zaman gidan yayi ya fice. Nan Iyaa ta sake saka ɗambar faɗa tana faɗin.
“Ai duk Debisi ne ya ja wannan abun. Tunda tun farko dashi ya auri yarinyarnan da sai dai mutuwace zata rabasu. Gashi yanzu ta kashe rayuwarta a banza, wawuyar yarinya wadda batasan meke mata ciwo ba. Ko da yake Daso ce ta zuga ta shi yasa ta jayeta su je su sha wahalar tare”
Iyaa ta dinga jero zance babu arziki muka shirya tsab muka bar gidan. Da gidan Bose muka soma, sai muka nufi gidan Uwani data siya. Hafizu yana zaune a kan benci a ƙofar gidan sai gamu.
“A’ah Alaja Iyabo rakiyarce kuma har Kano? Lallai wannan ƙawance naku da girma yake” Ya ƙarashe yana dariya sai kace wanda yaga wawan zama. Uwani kuwa girar sama ta haɗe data ƙasa, ta buɗe gidanta tayi shigewarta ta barmu muna gaisawa dashi.
A tsakar gida na sameta tana kiciniyar buɗe ƙofar ɗaki.
“Taho ki soma ganin dilolin kayan. Da mun gama hidimar biki zan buɗe dila amman nafi son in gyare shagona tsab.”
Ta buɗe ɗakin muka shiga, ga dilolinan masha Allah, wani kan wani dukiya akwai daɗi ganin dilolinnan sai ya sharemun ƙuncin da su Iyaa suka dasamun a raina. Ɗakin uwani muka koma, ɗaki masha Allah har kayan kallo Uwani ta saka ga firjinta ƙatoto.
Kinyi gyara gaskiya Uwani. Kuma gidan yayi kyau babu laifi”
“Wallahi kinga ga wani gida na jikin nawannan daga hannun hagu, shima da shago babbane dan yafi nawannan girma. Ni dai da zaki siya ko haya sai ki zuba Iyabo, ki ɗan dinga karɓar kuɗinki, kuma ko babu komai kin ajjiye kadara. Gidan a hannun dillalin dana siya wannan gidan ta hanyarshi yake. Yana ta mun tayi gidanma akan in siya in haɗe da nawa. Ni dai ki siya Iyabo. Ina da kuɗin siya amman ke naima sha’awar gidan “
To Uwani naji shawararki zan siya babu matsala, dan dama shanu naso in siya ayimun kiwo. Ammam bazai gagaraba zan sai gidan”
Uwani bata ƙyaleni ba har saida ta kaini ofishin dillalinta muka tsayar da magana harda rabin kuɗi na ajjiye mishi mun tsaya akan gobe inzo da shaiduna insa hannu a takadda a mayar da sunan gida nawa a bani takadduna, in cika kuɗi a bani ɗan makulli.
Hakan kuwa akayi Burodami Kokodeen da Lekan sai Uwani su su kaimun shaida akayi aka gama komai aka bani takaddun gidana da ɗan makulli.
Ɗakuna shida ne falle falle, sai ban ɗaki da kitchen, da shago a waje kamar dai gidan Uwani.
Daga haka muka shiga sha’anin gyaran jiki, magungunan mata daga wajen Anty Ramlex, shiga kasuwa, kai dinki. Kafin dai sati guda duk abinda zan siya na siya na jibge a gida har dilolin kayana nasa mota ta ɗaukarmun ta kaimun gida. Na buɗe jakar tsaraba naba duk wanda ya dace.
Ranar laraba sai ga mutanen Banyo da yamma sakaliya mota ɗaya duk mata, sai direba namiji.
Sun samu tarba ta girmamawa sosai dan ni banyi tunanin hakanba ma. Sun tawo harda akwatinsu mai taya guda biyu. Kayan ciki babu yabo babu fallasa ga bazawara kamata dai. Wasu a ɗakin Iyaa Debisi suka kwana, wasu kuma a ɗakin Iyaa Kokodeen suka kwana. Ni da Uwani muka kwanta a ɗakin su Lekan.
Washe gari sassafe muka ɗauki hanya. Motar da suka tawo da’ita ɗaukar Amarya muka shiga mu biyar. Ni da Uwani, sai Anty Ramata, da Iyaa Kokodeen. A gaban mota kuma Burodami Kokodeen ne sai direba. Motar kaya kuma aka lode kayayyakina hardasu dilar kayana aka rufe da tampol dan hadarine baƙi ƙirin a garin motar kayan ta daɗe da kama hanya ita kafin mu. Muka kama hanyar Adamawa. Tun kafin mu fita daga cikin garin Kano aka soma yayyafi sama_sama. Da muka soma shaga ƙauyuka ruwan yanata ƙaruwa, duk ƙauyan da aka wuce ruwa akeyi sosai. Sai tafiyar ta zama me daɗi babu zafin rana sam sai sanyi dake ratsawo ta ƙasan motar. Su Iyaa Kokodeen tuni sukai baccinsu sai gwara kai suke yi. Idanu na lumshe inata tunani, tare da adda’ar Allah yasa kada Yaya Hamma ya bani kunya ya tozarta zumuncinmu.
Yanzu Shikenan rayuwata ta koma ƙauye nima zan zama baƙauya kenan?
Wasu siraran hawayene suka gangaro a kumatuna wanda ni kaina bansan na meye ba.
Haka mukaita gudu har muka isa Adamawa ruwa akeyi sai tsurarun ƙauyuka da basu wuce uku ba da muka wucesu ba’a ruwa. A Girai motocinnan suka tsaya gashi ruwa akeyi sosai. Haka dole muka fita daga cikin motar muka fake a ƙasan wata bishiya mai yalwar ganye. Maza da mata duk muna fake mota ake jira. Munfi awa guda ana zabga ruwa daga bisani ruwan ya tsagaita mota ta tawo duk ta kwashemu. Kowa a takure yake sanyi ga jikewa da mukayi amman ba sosai ba. Hanyar tafi ta kullum muni, ko ina ruwa camɓal a kwance, ga laka sai riƙe motar take yi a haka dai har muka iso masauki. Daga nan muka tari mashina suka shigar damu. Gidan Dada kai tsaye nace su wuce dani dan ina buƙatar in sake kayan jikina, ba a kai amarya a jike sharab ba. Dada da Yusufu ne kaɗai a gidan tana ganin su Iyaa Kokodeen ta soma murna tana musu yare.
“Daso ciwo kikayi haka naga duk kin ƙare sai wuya?”
Dada ta dubi Iyaa Kokodeen tace.
“Zauna tukunna manyan baƙi nayi farin ciki da ganinki. Yau gaku a garinmu.”
Zazzaunawa sukayi Jikkunansu duk a mace. Sai jimantamun suke yi.
“Ni ina mamakin abinda Iyabo ta gani da har ta amince da rayuwar ƙungurmin ƙauyen nan. Rayuwar ƙauye a wajen ɗan birni takota ina cutarwace. Jibi nisa da wuyar da muka shawo. Ohh ke kuma haka kikeson kaddararki ta kasance” Cewar Iyaa Beji kenan. Iyaa Kokodeen ita kam hawaye take ta sharewa. Take nima na fashe da nawa kukan sai shessheƙa nake yi. Ni wannan maganganun duk sun isheni. Ni ba yarinya ƙarama ba, kuma ni nace naji na gani ba sai su sa albarka su bini da ido ba? Haka aurena da Gwadabe akaita koke_koke da tashin hankula iri daban_daban gashi a aure na biyu dana auri jinina bata sauya zani ba. Ko babu komai ni inaso in zauna a kusa da kannena da mahaifiyata. Tunda da tun farko an barni a hannunta da a wannan ƙauyen zan rayu, kamar yadda itama ta rayu.”
Kaya na sauya, akwatin kayan sawata dama yana tare damu. Ruwa daya tsagaita Yusufu yai mana jagora bayan mun rama sallolin da ake binmu har magriba munyi, an kawo mana jallof ɗin shinkafa da Dada tasa aka dafa domin tarar baƙi. Yafendona Dada ta aika aka kira duk suka haɗu aka rankaya kai Amarya da ƙafa.
A kacame gidan yake sosai anata kacaniyar biki. Tsakar gidannan ta damalmale da ruwa da abinci da yara suka zubar. Rumfunan gidan cike da mata da yara anata haya_haya. Ɗakin Yafendo Kaɓoji aka wuce dani kai tsaye. Anan muka tarar da su Yafendo A’i da yaransu mata dake gidan aure.
“Lale lale. Amaryarmu tazo gida.
Sannunku mutanen Kano”
Waje aka basu na zama aka taresu da lafiyayyen tuwo miyar ta wadatu da naman saniya da man shanu. Yafendo A’i tace.
“Ga abinci kuci, ayi sallah sai a shiga da Amarya ɗakunan matan gidan kafin a shiga da’ita ɗakinta. An gama jera mata komai. Tun ɗazu mata suke zuwa kallon ɗakin Amarya tubarkalla masha Allah” Ɗan dariya Iyaa Kokodeen tayi a matsayin amsa kawai.
A nan mu kai Sallah, Baɗɗo ta shigo ta sameni.
“Adda ragowar wasu muhimman kayanki duk suna ɗakina gudun kar a ɓarnatar miki. Akwai ƙunshi wasu buhunhuna duk na shiga dasu ɗakina”
Yauwa Baɗɗo su waɗannan buhunhunan ki barsu a ɗakinki zuwa gobe zamu ware kayan amfanina ragowar gidan Dada za’a Kai mun.”
Raɗa naima uwani a kunnenta, ta miƙe suka fita ita da Baɗɗo. Yafendona tace.
“Iyayen Jabu ku taso mu kai amarya ɗakunan matan da tazo ta tarar a gidan bisa ga al’ada kafin a kaita ɗakinta”
Gaba suka tusani Yafendona da Iyaa Kokodeen. Ragowar kuma aka nuna musu ɗakina suka kama hanya.
Da ɗakin Hama muka soma, ɗakin ma cike yake da ƙawaye babu masaka tsinke. Duk sun tarune domin suna son ganina, ance musu daga Saudiyya na dawo. Sai da wasu dole suka fita kafin mu muka samu waje. Yafendona ta nuna mun gefen gadon Hama tace.
“Jabu ga bakin gado zauna muyi a gurguje ki samu ki shiga ɗakinki sanyin yayi yawa” Ɗofanuwa nayi a bakin gadon, fuskata ba’a rufe take ruf ba ina iya ganin kowa da komai, duk wanda ya kalleni zai iya ganin fuskanta.
Hama fuskarta ta kumbura tayi jawur da halama taci kuka ta gode Allah. Dan ina zama ta bani baya sai jijjiga ƙafarta take yi. Ga Daso a gefenta sauran manyan ƙawayen nata suna tsakiyar gadon sai ƙaremun kallo suke yi. Ni ko ina lure tsab da motsin kowa.
“Hama ga ƙanwarki mun kawo miki. Duk da dai zata iya girme miki amman dole kece sama da’ita tunda ke ta shigo ta samu. To Jabu dai ba baƙuwa bace ku daure ku haɗe kawunanku domin a zauna lafiya. Jabu dai ƴar uwa take ga Hamma da mahaifiyarta da mahaifiyar shi uwa ɗaya suke uba ɗaya kin sani. To ayi haƙuri a martaba wannan halaƙar” Hama dai taƙi buɗe bakinta tayi magana har saida Daso ta zungureta kana tace.
“Allah ya bada zaman lafiya ya sanya alkairi ” Yafendona tace.
“Ameen to Jabu muje a kaiki ragowar ɗakunan”
Haka mukaita shiga ɗakunan matan ƙannen Hamma daga ƙarshe suka wuce dani bukkata dake wata ƴar kwana can ƙarshen gidan sai an shiga lungu. Tun daga ƙofar lungun akayi blue ɗin fenti har cikin bukkarnan data kasance ɗakina. Da bismillah na shiga ina karanto adda’a duk wacce tazo bakina.
A takure bukkar take sosai kasancewar kayana da yawa sai ya zamana babu ko wajen da zan iya sallama. A kujera aka zaunar dani. Uwani da Baɗɗo sai gyare_gyare suke yi mini. Anti Ramata tace.
“Allah me iko. Yau wannan shine ɗakin auren Iyabo”
Sabida rashin waje ishasshe basu jima ba duk suka fice, ɗaki ya rage daga ni sai su Uwani.
“Iyabo kujerunnan dole ki rabu da wasu gaskiya. Ni ina ganin waccan 2 sitter ɗin kawai za’a bari in kinaso ki samu fili. Sannan kayayyakin kitchen ɗinki fa duk mun lode miki a sib ɓangare ɗaya baki da kitchen, da kitchen da banɗaki duk na gandune, kinga ai ba zamu yi miki jere a kitchen ɗin gandu ba.
To Uwani duk yadda ya dace ayi kawai”
Nace da’ita ina takure a kujera”
“To yanzu dare yayi zuwa gobe da safe duk saimu gyara komai ni da Baɗɗo. Kun haɗu da angon naki kuwa Iyabo?” Idanu na lumshe nace.
A’a bamu haɗu ba, ƙila ma sai gobe dare yayi, gida kuma haɗe da iyaye”
Mayafina na cire na koma kan gadona da yasha lafiyayyen zanin gado mai laushi. Fentin ɗakin nabi da idanu, bai biyu ba yayi wani roɗi_roɗi. Na ɗaga kaina azara tana kallona ina kallonta. Ajjiyar zuchiya na sauke na dubi Uwani nace.
Uwani wannan azarar babu yadda za’ayi a rufeta?”
Dariya ce ta kama Uwani sai da tayi mai isarta sannan tace.
“Zamu rufeta zuwa gobe ko da zanin gadone, dan dama nace zan shiga gari in siyo cottin a zagaye miki ɗakin dashi zaifi fasali fiye da wannan fentin ƴan ƙauyen a hakanma naga ke kaɗaice mai fenti me kala duk farar ƙasace a shafe a nasu bukkar, azara ai ke kika siya da kuɗinki Iyabo. Ke dai zuwa goben dai ki kwantar hankalinki Amarya a gidan Hamma.”
Dariya muka saka dukkanmu nace.
Baki da dama Uwani Uwargida a gidan Hafizu, Hafizu ikon Allah”
Wata uwar harara ta watso mun. Na sake fashewa da dariya. Baɗɗo tace.
“Bari in kawo muku fura da nono Adda” Ta fita sai gata da Fura da nono cikin ƙwarya, tayi mana sallama ta fita dan a lokacin goman dare zai iya yi. Muna daga gado muna hira da Uwani muna shan fura.
“Iyabo nifa harna hango miki alkhairan kasuwanci. Wallahi in Allah ya dafa miki me kuɗi zaki zama, kita sare_sarenki. Nima kafin in tafi zan sari man shanu. A hannun Baɗɗo tunda yanzu lokacin arharshi ne.”
Mun daɗe sosai muna tattaunawa kafin bacci yayi awon gaba damu.
Washe gari aka kuma tashi da hatsaniyar biki. Uwani tun wurwuri suka shiga gari ita da Baɗɗo. Daga ni sai Anti Ramata a ɗakin, sai wajajen takwas na safe matar ƙanin Hamma ta kawo mana shayi ruwan bunu da ƙaton biredi sai ƙosai cikin kula.
Ni banci biredin ba ma, ƙosai biyu naci sai ruwan bunun dana sha. Cubu ce ta leƙo ɗakin tace.
“Adda na kai miki ruwan wanka ki je ki watsa”
Dama tuntuni wankan nake son yi inje mu gaisa da Yafendo, da ragowar matan gidan.
Hijabi na saka na fita hannuna riƙe da kwandon soso da sabulu.
Ruwan wankan yana cikin sabon bokitin ƙarfe in leƙa ruwan sai naga wani garin magani yana yawo a cikin ruwan. Baki na buɗe ina mamaki, ba shiri na kelayar da ruwan na fito da bokitin a hannuna. Da hannu na yafito Cubu dake gindin murhu. Tana ƙarasowa na damƙa mata bokitin.
Ungo ki zubo mun wani ruwan zafin. Kafin ki zubo ki ɗaurayo bokitin sosai. Wancan zamewa nayi ya zube”
Karɓa tayi ta zubo mun wàni ruwan nayo wanka zuchiya cike tab da fargaba.
Ina fitowa na kintsa cikin riga da siket na atampa, na yi kwalliya sama sama na yafa mayafina wanda na bishi da turaren feshi.
Ina fitowa tsakar gidan ido ai sai ya dawo kaina.
Anan zan dakata sai Allah ya kainmu gobe.
MRS BUKHARI
Part 3
NAMA YA DAHU…
ROMO ƊANYE
BADI’AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
LITTAFI NA UKU (3)
Kunsan masu ƙiba yadda sutura take amsarmu, haka kwaliyarma take amsarmu. Abunka kuma da Amaryar birni a ƙauye. Ni dai harna iso gun_gun matan dake kallona basu dena ba.
Ina kwananku” Nai musu jam’u dan Hama ma tana cikinsu. Tsirari daga cikine suka amsa, na yi wucewata na bar musu ƙamshin turarena a iska.
Danƙari na ji wata baƙuwar murya ta faɗa ko me take nufi da hakan oho.
Sallama nayi a ƙofar ɗakin Yafendo na shiga. Duk ƙannen Dada suna ciki karyawa suma suke yi, su Iyaa Kokodeen ma suna ciki.
A ƙasa na zube na bisu ɗaya bayan ɗaya na gaishesu. Ko wacce da fara’a ta amsani. Saina nemi gefen gadon bono na takure kaina a ƙasa nayi shiru kamar ruwa ya cinyeni. Can Yafendo A’i tace.
“Jabu sai kin ƙara da haƙuri dan zama da kishiya ba abu bane mai sauƙi ba. Musamman ka haɗa miji da bafulatana, bafulatanar ma ta Camaron basu ɗauki kishi da wasa ba. Mu ma da kika ga mun yi ƙarko har zuwa yanzu, haƙuri da kawaicine, da ƙarfin adda’a.
Kema ina baki shawarar ki riƙe wannan abubbuwan zaki samu riba duk daren daɗewa. Ki zamto mai kawo haɗewar kai ba mai ƙoƙarin ganin an samu rabewar kai ba. Hamma dai ɗan uwankine jini ba ruwa bane, kar ki bari wata ta kutso kanta cikin rayuwar aurenki ki kula sosai. Kuma kin nuna mana soyayya, kin yi abun a duba Hamma zai nuna miki shi ɗan halak ne”
Ta jima tana nusar dani tare da bani satar amsa dangane da yadda zafin kishin fulani yake mazansu dama matan nasu. Daga ƙarshe tace inyi komawata ɗakina”
Sallama nayi musu na fito. Kaina a ƙasa na wuce matan da suke tsaye cirko_cirko dan son sake ganina. Uhm bance dasu ba nayi kwanar lungun ɗakina nayi shigewata.
Uwani na gani akan turmi tana ta faman zagaye mun ɗaki da farin citton me les les. Yayi matuƙar kyau sosai.
Ashe kun dawo Tabalbalin? Sannunku da ƙoƙari”
“Mun dawo har mun shiga aiki. Ance yau ango zai shigo ɗakin Amarya ai gara mu samu mu kammala komai a nitse. Kinga wasu fararen labulaye masu kauri dana siyo inaso ko yayane mu raba ɗakin biyu ta yadda ko an shigo ba za,a ga wanda ke kwance a gado ba ko ya kika gani?”
Lallai wannan dabarace mai kyau na kuma ji daɗinta sosai na baku wuƙa da nama”
Anti Ramata da Cubu kuma kujeruna suka fitar dukka waje muka haɗu muka sake ma ɗakin fasali babu laifi yafi na farko kyau. Kujerar doguwa guda ɗaya kaɗai aka mayar, sauran nace Baɗɗo ta ɗauki 2 sitter ɗin sauran 1_1 ɗin akai gidan Dada a ajjiyema Cubu in aurenta ya tashi sai a kai mata. Muka gyara komai abincin gara na ɗebi wanda zan ɓoye na tura ƙarƙashin gado, dama na sai maggi dunƙule katan guda, na daka yajin barkono da yajin daddawa, na sai kayan tea na dayawa, na sai tocilolina masu batura hatta baturan na sai abina, Uwani tayo mun miya, mun tawo da risho da kalanzir, ƙananun abubbuwan buƙata dai wanda nasan zanyi amfani dashi duk na sai kayana na adanasu. Cikin awa uku ɗaki yayi shar dashi gwanin ban sha’awa. Mata masu zuwa ganin ɗaki har daga maƙotan ƙauyan zuwa sukaita yi basu taɓa ganin kaya irin nawa ba, yadda aka raba ɗakin biyu shima ya burgesu sosai.
Haka dai aka wuni cur ana sha’anin biki. Wuninnan cur kuwa ruwa akaita makawa. Sai magriba ruwannan ya tsaya na samu nayi wanka na sake kwalliya. Anayin isha su Uwani suka watse suka barni ni kaɗai a ɗakin ƙwalam akan kujera na ƙurama tocila idanu. Ɗaga kai nayi na kalli yadda su Uwani suka rufe azarar saman ɗakin da farin labule cikin hikima. Na daɗe a zaune ina karanta wasiƙar jaki ga turaren tsinke sai ƙamshi yake fitarwa daga saudiyya na siyo. Wajajen goman dare har bacci ya soma surata akan kujera na jiyo shigowar Yaya Hamma. Da sauri na buɗe idanuna dan na tsorata sosai.
“Tsoro kikaji ne Jabu naga kin tashi a zabure?”
Saye yake da wani yadi green yala_yala ɗinkin ƴar shara, kanshi babu hula sai suma data zame mai ado ta kwanta ta laɓe a dogon wuyanshi. Sai ƙamshin turaren sasarobia yake yi, hannunshi riƙe da leda mai zane”
Da sauri na miƙe tsaye ina shirin amsar ledar hannunshi. Saijin hannunshi nayi ya riƙe ƙuguna ya jawoni na faɗa jikinshi. Ƙam ya riƙeni, nima na riƙeshi ta baya riƙo na ƙwarai. Munkai kamar minti biyu cur muna shaƙar numfashin junanmu. Ni dai wani abune ya shiga yi mun yawo tun daga dunduniyata har zuwa kaina.
Ji mukayi an bankaɗo labulen ɗakin an shigo. Ga wani irin kukan jinjira na fitar hayyaci. Da sauri muka saki juna. Hama ce a tsaye riƙe da jaririyarta dake canyara kuka. Wuf Hamma ya amshi yarinyar yana tambayar Hama meke damunta.
“Baccinta take yi lokaci ɗaya saita soma firgita tana zabura tana miƙewa, sai kuka ka dai ganta” Jijjiga yarinyar ya dinga yi, amman yarinyarnan kamar ƙara zugata akeyi sai canyara ihu takeyi bakinta na rawa. Kafin kace me matan gidan duk suka yo ƙofar bukkata suna tambayar ba’asin wannan kukan.
Hamma ne ya fita da yarinyar rataye a kafaɗarshi.
Ina jiyoshi yana musu bayanin da Hama tayi mishi da fulatanci.
Ni kuwa ina tsaye a inda suka fita suka barni, ga ledar kaji tarwatse a ƙasa. Tun inajin muryoyinsu harna dena jiyowa, kukan yarinyar yayi nesa sosai.
Wallahi saida nayi awa guda cur a tsaye in kai mari in kai gwauro ina tubkewa da warwarewa.
Labulena aka ɗaga Hama ce fuskarta a sake tace.
“Amarya sai haƙuri auren mai mata angone yace in sanar miki zamu kai yarinya gidan magani, wai ki kwanta kiyi baccinki, in mun dawo zai kwanta a ɗakina sabida jikin yarinyar” Numfashi naja sama nace.
To Ubangiji Allah ya bata lafiya, gaskiya ya kamata ya zauna tare daku har sai ta samu sauƙin jikin nata”
Labulen ta sake. Ni kuma wasu siraran hawaye suka gangaro a kumatuna lumshe idanuna nayi na kaɗa kaina na zauna a kan gado ina karanta wasiƙar jaki. In ƙulla fari in ƙulla baƙi zuchiyata bata gamsu da kukan yarinyarnan ba wallahi. Duk da naga yadda take kukan fitar hayyaci. Amman babu komai ai hama ba zata dauwama tana cin nasara a kaina ba. Wannan dai ta shammaceni. Bari mu gani gobe kuma dame zata zo. Kwanciya nayi ina kallon sama sanyi na ratsani. Irin wannan weda ta ma,auratace, naso yau yadda wedarnan ta bada haɗin kai mu raya wannan dare. Amman babu damuwa gobe ma ranace.
Da tunane_ tunane bacci yai awon gaba dani mai cike tab da mafarkai marasa daɗi. Ƙarfe ukun dare na miƙe a bahun na ɗaura alwala na soma sallar nafila har zuwa ketowar alfijir. Saida na sallaci asuba na kwanta a kujera dan tsabar bacci kaina kamar zai fashe.
Kamar a mafarki nake jiyo muryar Baɗɗo da Uwani a kaina. Ina buɗe idanuna ilai kuwa sudinne. Uwani riƙe da takaddar kajin da Hamma yai watsi dasu.
“Iyabo ya kaza haka a yashe a ƙasa ga Amarya kuma akan kujera, Allah yasa lafiya?” Uwani ta tambayeni. Sai da nayi Ajjiyar zuchiya kana nace.
Ina kuwa lafiya Uwani. Har ɗaki aka shigo aka janye ango har yanzu banma sashi a idanuna ba. Ke jiya ni naga bariki.” Shewa Uwani tayi, ta nemi waje ta zauna niko na labarta mata halin da ake ciki. Hararata tayi tace.
“Kin bani kunya. Karfa ki bari zaman saudiyya da kikayi ki bari ya tashi a banza. Wacce yaudarace baki gani ba. Ga zaman gidan Gwadabe wanne siraɗine baki tsallakeba? Ko da yake nifa Hama burgeni tayi, ai baki ga komai ba Iyabo”
To Uwani ya zanyi ni mamakine ya hanani kataɓus. Amman bawai zan bari ta takani yadda taso bane sam. Jiyanma ta shammacenine wallahi. Na kuma barta ne kawai in halinta ne zata sake. Zigata akeyi shi yasa duk take wannan abubbuwan.”
“To gaskiya karki sake bari hakan ta faru. Yanzu dai wannan kajin ai sai mu zauna muci mu kora da lemu rabonmu ne”
Wanke bakina na fito nayi a ƙofar ɗakina na koma ciki, muka zauna mu uku saida muka ta da kajinnan biyu ƙananune sosai muka kora da lemun kwalba.
Ko da aka kawo mana ɗumamen tuwon masara bamu ci ba mayarwa mukayi. Rishona na fitar ƙofar ɗaki na dafa ruwan wanka nayi, na sha kwalliyar les fari tas.
Su Anti Ramata ne suka shigo da shirinsu na komawa gida tsab. Nasiha suka sake yi mun dai a gurguje. Burodami Kokodeen ma ya shigo yai mun nasiha suka kama hanya.
Haka dai muka wuni a ɗaki maƙota sai shigowa ganin Amarya suke yi ba ƙaƙƙautawa. Da rana Hama ta girko shinkafa da miya aka kawo mana, miyarnan baƙi sosai kamar anyi sauwarta da ruwan rubutu.
Daga ni har Uwani bamu ci ba. Yafendo ce ta aiko mana da fura da yawa. Dada kuma ta aiko mana da farfesun kaza, shi muka ci muka ƙoshi. Wajajen azahar yaran Baffa Musa, da yaran Yafendo A’i, da su Karima harda Daso duk suka taru akaita hirar zumunci. Mafi yawan hirar da fulatanci suke yi sai hausa jifa_jifa. Daso dai ba komai take sa musu baki ba, niko na sake sosai a cikin ƴan uwana. Sai da sukai sallar la’asar sannan ko wacce ta kama hanyar gidanta. Ritsona na fitar gefen ɗakina na ɗaura ruwan zafi. Uwani ta shiga gyara mun ɗakin dan duk ya hargitse. Ruwan zafin na tafasa na cika filasaina du biyun na sake mayar da wani ruwan na wanka. Kafin ayi sallar magriba na fito daga wanka.
Saida nayi salla kana nayi zaman dirshan na shafe jikina da mai, nayi kwalliya mai sauƙi na sanya doguwar rigar yadin boyel me ruwan baƙin bulu ( blue black). Na saka ɗankunne da sarƙata fashion ja kasancewar akwai ƙaramin keb a wuyan rigar boyel din anyi da jan zare. Na feshe jikina da turare shar.
“Bari in nemo miki gaushi ki soma amfani da turaren wutanki ɗan saudiyya wallahi ba dai ƙamshi ba.”
Fita tayi da kaskon turaren wutan. Tana fita Safiya matar ƙanin Hamma ta yo sallama ta shigo hannunta riƙe da langar tuwo da miya ta ajjiye.
“Ga abinci Adda Jabu. Baɗɗo har yanzu bata gama girki ba shine nace bari in kawo miki” Murmushi nayi mata nace.
To Nagode kwarai Safiya” Tana fita uwani ta shigo da gaushi.
“Gashi kishiyarki ce ta bani. Kinga wata yaluwar atampar data saka wai ita tayi kwalliyar yamma? Wuyan rigar baya ko zama tsabar yadda yayi mata yawa, ta ko rambaɗa jar hoda fuskarnan tayi jawur.”
Dariya muka tuntsire dashi. Baɗɗo ce ta shigo da tiran abinci. Shinkafa jallof tayi da kifi, sai fura da dambu cikin jug ɗin silba.
“Adda wannan nono da Dambun na Yaya Hamma ne. Kullum sai ya sha babu fashi nasan baki sani ba shine nayi miki. Ga abincinku. Adda Uwani muje muci namu Yaya Hamma ya dawo yana wajen shanu”
Kwanukan abincin Safiya na mika ma Baɗɗo.
Ungo ko yaranki sa ci, wannan ya isheshi ni a ƙoshe nake”
Ta karɓa suka fita. Suna fita na ta da sallar Isha. Ina zaune ina lazimi Yaya Hamma ya shigo da sallama hannunshi riƙe da baƙar leda babba.
Da sauri na miƙe na amshi ledar hannunshi na ajjiye a gefe.
Zama yayi a kujera yana sauke ajjiyar zuchiya da gani a gajiye yake dan idanunshi sun lumshe da ƙyar yake buɗesu.
A gefenshi na zauna.
Sannu da dawowa Yaya Hamma ” Hannuna ya riƙo ya matse a nashi, ya zuba mun idanunshi da yake lumshesu.
“Amarya kinyi kyau. Ɗakinki yayi kyau sosai, tsarin ya burgeni”
Murmushi nayi mishi kawai.
Ina ka shigane tun jiya rabona dake.
Murza hannuna yayi yace.
“Ke dai bari, yadda naci burin daren jiya bai kasance yadda na tsarashi ba. Yarinya ba ita ta samu bacci ba sai asuba, ina dawowa masallaci kuma na wuce gidan Baffa Musa yana nemana. Acan na daɗe daga nan kawai saina wuce wajen aiki dan nasan gidan cike yake da mata. Aimun afuwa in ran gimbiyata ya ɓaci, ba da nufi komai ya faru ba. Su Inusa ma ƙorafi suke yi mun wai ban kawosu sunci tuwon Amarya ba”
Ɗan murmusawa nayi nace.
Ai babu komai. Ciwo ya doke komai ai, ciwonma na yarinya ƙarama. Su Iyaa sun tafi yau, uwani kuma sai jibi so take tabi Baɗɗo suje cin kasuwa akwai abubuwan da take son ta sassarane”
“Uwani baiwar Allah. Wannan ƙawancan naku yana bani sha’awa gaskiya. Ina muku fatan ya dore har ku haɗa ƴaƴanku auratayya”
Ameen. Yanzu dai me kake son ka soma, wanka, ko cin abinci? Naji sai warin rana kake yi”
Duk wannan hirar a shingiɗe yake a kujera hannuna yana cikin nashi yana murzawa.
“To wanne kika ga ya dace dani? Ni wanka ai sau ɗaya nake yi, wani sa’inma sai in kwana biyu gaskiya banyi ba, sabida yanayin aiki da kiwo”
Dariya nayi, shima dariyar yayi yace.
“Sai kinyi haƙuri mijin naki ƙazami_ƙazamine”
A’a ba haka bane. Kar ka damu wannan duk ya kau daga yau. Wanka sau biyu safe da dare in sha Allah. Bari in kai maka ruwan wankan ka watsa sai kazo mu ci abinci, ga nono da dambu yana jiranka”
Ina faɗin haka na miƙe na juye ruwan filas ɗaya a bokitin ƙarfe, na fita waje randata tana bakin ƙofata na surka mishi ruwan, na haɗa mishi da soso da sabuluna na kai mishi.
Yaje yayo wankanshi tsab, na dangwalo mishi dakakken gawayi wanda aka cakuɗa da alim nace.
Goge bakinka tas Yaya Hamma “
Murmushi yayi ya amsa ya tsugunna a ƙofar ɗakina ya jima yana goge bakinshi. Ni kuma ina ciki na haɗa mana tea na zuba mana abincin Baɗɗo. Na zuba miyar stew da uwani tayi mana taji soyayyan kifi sukunbiya.
Tare a plate ɗaya muka ci abincin, kaɗan yaci ya ɗauki nono da dambu ya sha, ni kuma na sha tea.
“Akwai kazar amarci a ledar dana shigo da,ita ki ɗakko”
Ai sai dai da safe mayi karin kumallo da’ita a yanzu gaskiya na ƙoshi.
Gaga_gaga muka kammala duk abinda ya dace, muka ɗauro alwala muka yi sallar nafila bisa Shari’a. Daga nan al’amura suka soma sauya salo, daga ƙasa zuwa kan gado. A hankali abubbuwa masu daɗi da wuyar fassaruwa sukaita gudana. Har abinda aka daɗe ana mafarki ya tabbata a tsakaninmu. Abinda ya curemu muka zama guda kenan. Abinda ke ƙara soyayya da shaƙuwa a tsakankanin ma’aurata. Yaya Hamma yayi mun bazata, dan banyi tunanin tattali irin wacce na samu ba, asalima ban kawo irin wannan tattalin ga mutumin ƙauye ba, sai gashi ya kere tunanin Iyabo. Dan wallahi Gwadabe da wasa bai taɓa kaini irin wannan duniyar ba. Shima kuma na fahimci na kaishi duniyar da babu fulani a cikinta.
Wannan yanayin ya ƙara mana so da shauƙin juna sosai. Bayan komai ya lafa muna kwance muna mayar da numfashi, Yaya Hamma ya juyo ya zuba mun idanunshi masu haske kamar madara. Abu ɗaya da ya bani tsoro shine na fahimci Yaya Hamma kamar baya aski ko ince baima taɓa yi ba irin yadda na fahimci yawan gashin. Amman nasa a raina zuwa washe gari zai aske shi tas.
“Jabu soyayyarki ta kasance ta daban a zuchiyata. Kin kafa babban tarihi a wannan daren mai ɗumbun nasara da tarihi. Allah yayi miki albarka. Nagode da kika tallafi soyayyata baki hofantar dani ba. Wallahi Allah shine shaidata da ban sameki ba, komai zai iya faruwa dani, ina nufin komai.
Ina roƙonki komai sauyin yanayi dana zamani kar ki gujemun, kar ki juya mun baya”
Mun jima a wannan daren muna ma junanmu alƙawarurruka masu nauyi da girma. Daga ƙarshe tare dashi muka je banɗaki mu ka yi wankan Sallah. Duk da yana noƙewa tare da jin tsantsar kunyata, har rufe idanunshi da tafukan hannunshi ya dinga yi. hakan bai hanamu yin nishaɗi ba. Yanayi ne mai kyau, irin yanayin da na jima ina mafarki kenan Allah baisa na samu tare da Gwadabe ba, sai gashi na samu a wajen Yaya Hamma.
Bacci mu ka yi mai daɗin gaske, baccin da saura ƙiris Yaya Hamma ya rasa sallar asuba. A gurguje ya zura rigarshi mai warin hammata da warin awaki ya fita. Idanu na lumshe tunanina yana mayar dani daren jiya da ni’imomin dake kewaye da daren. Marata na shafa ina fatan Allah yasa Yaya Hamma yayi ajjiyar jininshi a marata in haifa mishi kyakkyawan santalelen saurayi me kama dashi ya samu abokin shawara.
Da ƙyar na fito nayi alwala wani irin muƙu_muƙun sanyi ake busawa sosai.
Ina idarwa na kunna risho na dafa ruwan tea na zuva a filas na ɗakko wannan kaza na ɗorata akan plate. Na mayar ma da Yaya Hamma ruwan wanka.
Yana shigowa na kai mishi ruwan wanka, ya tafi ya yo wankan. Ni kuma na shiga cikin gidan.
Matan gidan duk suna kitchen ɗin tsakar gidan ko wacce girki takeyi a murhunta. Wani irin murhu garesu ginanne mai kyau, da laka ake ginashi, sai ɗan ramin dora tukunya. Duk ramuka bibiyu akaima ko wanne murhu, nawa yana kusa dana Hama sabo dal dashi har fenti akeyi mishi.
Ɗakin Yafendo na shiga muka gaisa sannan na fito na nufi kitchen din. A dokin ƙofar kitchen ɗin na tsaya. Hama na dafa madarar shanu ta ɗago muka haɗa idanu. Ta wani turɓune fuska wuyan rigarnan nata a sauke nonuwanta rabi da kwatansu duk a waje. Wani tsohon kitsone a kanta duk ya furje. Ga gashi dai yala_yala amman babu gyara duk abun katifa ya rirriƙe gashin haka ma kan yaranta yake. Babbar ƴarta me sunan Yafendo tana gefenta riƙe da kofi hancinta sai yoyyo yake yi. Duk sanyin da akeyi kan yarinyarnan ba ɗankwali, ƙafarta babu takalmi ba suturar arziki.
Maman Dada ina kwananku?
Hama ta juya kai ta mayar da hankalinta akan madarar da take dafawa. Sai su Fatu da Safiya ne suka amsa muka gaggaisa. Baɗɗo ta gaisheni tare da cewa.
“Yanzu nake son in kawo muku madara ku karya”
To sai in tafi da’ita. Maman Dada kayan Yaya Hamma zaki bani yayi wanka yana son sauyawa”
Sai ta saki muciyar da take juya madara ta juyo a fusace.
“Shine ya aikoki ko zuwa kikayi ki sanar dani ya kwanta dake kome kike nufi Jabu? To bazan bayar da kayan ba shi bashi da ƙafar da zaizo ya ɗauki kayanne.”
Taja dogon tsaki ta fice fu a kitchen ɗin, saida taso bangazata na matsa da mugun sauri.
Dariyar Uwani na jiyo daga bayana. Harda tafinta Uwani ƴar duniya kenan. Nima darawa nayi kawai.
“Sai haƙuri Jabu. Yanzu Maman Dada a cikin fishi take” Cewar Safiya wacce na lura tana da hankali.
Ba komai Safiya komai zai daidaita. Baɗɗo bani madarar”
Madara ta miƙomin cikin kofin silba na nufi inda Uwani ke goge bakinta.
“Wannan kishiya taki sai kinyi da gaske. Irin wannan daga miki murya da take yi haka, sai kace uwarki?”
Ke dai bari Uwani. Bari in sallami Yaya Hamma zan zo in sameku, ƙila ma muje kasuwar tare in ya barni dan inason in yi siyayyar kayan miya da abinda ba za’a rasaba ƙila yau muna da baƙi masu cin tuwon dare.
“To Shikenan sai kin shigo maza aje a kula da megida”
Komawa nayi ɗaki na tarar da Yaya Hamma yana karyawa.
Harka soma karyawa Yaya Hamma?
Murmushi yayi mun.
“Na gama ma. Inaso in fita kiwone yau nama ɓata lokaci sosai.”
Kallonshi nayi ya miƙe tsaye nace.
To Allah ya tsareka ya dawo da kai lafiya.
Yauwa Yaya Hamma nace abokan naka su nawa ne zasu zo zan musu girkinne?”
Hularshi ya mayar kanshi kana yace.
“Mu shida ne.”
To dan Allah inaso zan raka Uwani kasuwa siyayyarta da yawa kuma nima ina buƙatar zan ɗan yi siyayya”.
Jim yayi kamar bazaiyi magana ba dai. Sai yayi dariya kuma yace.
“Da ƙafa suke zuwa cin kasuwar fa, mota wuya take yi sosai in zaki iya to kuje sabida dai Uwanine amman da bazaki ba”
Nera ɗari biyu ya bani yace.
“Ga kuɗin cefananki nan sai ki sai abinda zaki siyo acan yafi arha. Ki karɓi garin tuwo da ɗanyan man shanu a wajen Hama zan mata magana ta baki”
A gurguje mu kai sallama ya fice. Kayan karin na tarkata na fito na nufi tsakar gidan. Yaya Hamma yana ƙofar ɗakin Hama da sandar kiwonshi, mijin Baɗɗo kuma yana kaɗa shanun waje.
Bance musu um ba na wucesu kamar ma ban gansu ba.
Tare da su Baɗɗo muka ci kazarnan da tea muka kora da dafaffiyar madara.
“Bari inje in harhaɗa kayan nonona sai inzo mu tafi Adda Uwani”
Fita tayi, fitarta ke da wuya uwani ta soma zolayata. Da dariya na bita kawai. Baɗɗo ta gama haɗa ƙorenta na Nono ta leƙo tai kiranmu akan muje. Muna fitowa Hama na ɗaura ƙoren nononta a ka, ta fice tana tsaki.
Yafendo muka je mu kaima sallama.
“Jabu har da ke za’aje?”
E Yafendo inaso inga kasuwarne” na bata amsa ina sauke kai ƙasa.
“To Shikenan. Nima yanzu ina gamawa zan biya ta wajen Adda Daso kafin in wuto kasuwar.”
To Yafendo muma in muka dawo zamu biya can uwani zata maata Sallama.
A wannan kasuwar naga tarin ƙauyawa iri da kala. Ga masu tuyar ƙosai da masu saida burodi, komai akwai a wannan kasuwar gasu da arhar nama, ga kayan hatsi, gasu nono, mam shanu, madara, suturu, harda shanu da tumakai, kaji, zabbi, rediyone tocila, su kayan miya ɗanye da bushasshe babu fa abinda babu. Ga maza da matan Fulani damƙam wasu sunzo siyayyane irinmu, wasu kuma kasuwanci ya kawosu irinsu Hama da Baɗɗo. Haka mu ka shawo siyayya nan muka baro Baɗɗo.
Bayan mun dawo muka ya da zango a gidan Dada anan muka tarar mai nagge yazo ya tusa ƙeyar su cubu yace ba zasu zauna a hannun Dada ba. Su Baffa Musa suna zazzaune ana mayar da zancan Dada sai hawaye take yi muka shigo.
Baffa ne yai mun bayanin halin da ake ciki, da korar Amaduyal da yayi a gidan nashi kan yace bazai iya dena zuboma Dada abinci in matarshi ta dafa ba. Shine ya ƙwace shanayen dake hannun Amaduyal ɗin ya fito musu da kayansu. Ajjiyar zuchiya na sauke bayan na gama jin komai nace.
To babu damuwa, su Cubu su je su zauna wuya bata kisa. Amaduyal kuma ga ɗakinan ku share kai da matarka ku zauna.
Shanu dama ina da burin siya ko babu yawa zan danƙama ka dinga yi mun kiwonsu, a jiki ku dinga samun madara, nono da man shanun da zaka kula da iyalanka da abincin da Dada zata ci. Dada ki dena kuka Allah zai rufa mana asiri.” Baffa Musa ya sauke ajjiyar zuchiya yace.
“Shikenan an samu masalaha. Jabu sannu da zumunci Allah ya baki waɗanda zasu yi miki kema. Mai Nagge kuma ina ƙara jan kunnenki kar ki kuskura wani abun ya shiga tsakaninku, ko bayan raina kar ku tayar da maganar shanun Daso daya danne ya zama mallakinshi mugun mutumne wanda zai iya kashe duk wanda zai tayar da wata magana akan shanunnan. Duk shanun da kikaga yana gadara dasu na Daso ne wanda ta samu a gado, labari aka bani rugga_rugga sai yawon bin bokaye yake yi kuma duk akan a rufe bakinmu kar mu tada zancen Shanu ne. To mun yi shiru zamu haɗu a gaban Allah”
Ba komai Baffa mun bar maganar in sha Allah. A dai nema mana shanu sai mu siya manya da ƙanana sabida shi Amaduyal ya soma fita kiwo, duk da gidan babu inda za’a iya garke.
To anan nake cewa daku mu tara ranar monday in Allah ya kaimu.
To ina ƴan team Hamma goga dai ya ciri tuta.
Ina masu ƙin Hamma me zaku iya cewa ina sauraren ra’ayinku.
Mrs Bukhari
Part 4
NAMA YA DAHU…
ROMO ƊANYE
GAWURTATTU UKU
BADI’AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
LITTAFI NA UKU (4)
Maraɗi.
Robar ƙarin ruwane ɗaure a hannun malam, numfashinshi yana sauka da hawa a gurguje sosai.
Daktar ne tsaye a kanshi yana ma ƙarin ruwan dake ɗaure a hannun malam allura. Tasi’u da Jamilu ne a kusa da malam kusan a tsaye suka kwana akan malam. Iyayensu kuma a zaune a ƙofar ward ɗin suka kwana ciki harda Baba Suwaiba wacce ta zama itace ummul aba’isin faruwar komai.
Kafin ƙarfe bakwai na safiya iyalan Malam kab sun hallara, ko wacce uwa na zaune a gefe guda da bataliyar yaranta a gefenta. Tsakanin Amaryan malam, Baba Suwaiba, Baba asshi babu komai face harara da jan dogayen tsaki. Yaran maza da mata sunyi tsit kamar ruwa ya cinyesu kowa da tunanin da yake yi.
Buɗe ƙofa akayi gadon jan marasa lafiyane ya fito malam na kai baisan a wacce duniyar yake ba.
“Ina za’aje dashi wannan yaron?” Baba Fhatsima ta tambaya a tsorace. Hawaye Yaya Tasi’u ya share yace.
“Na nemi a sake mishi ɗakine, sannan Malam yana bukatar adda’ar matanshi da yaranshi. Auwala ku haɗu dukkanku ban ware kowa ba aje a sauke ma malam Qur’ani ayi sadaka.”
Hawayenshi ya kuma sharewa yabi bayan ma’aikatan jinyar a baya. Jamilu kuma ya tsaya tattsunawa da uwarshi da ƙannenshi.
“To ai kowa yaji abinda Babban wa uba yace. Sai mu tafi ai ko?” Cewar Auwala kenan. Buɗar bakin Muntari sai cewa yayi.
“Ni babu inda zani, ku dai da kuke tunanin Malam ku kaɗai ya haifa, kuma uwarku mowace sai kuje kuyi mishi”
Yinƙurowa Auwala yayi kan Muntari da zafin nama. Da sauri Baba Suwaiba ta miƙe ta shiga tsakankaninsu.
“Kul Auwala karka sake ka tayar mana da fitina a wajennan. Ka barmu muji da bala’in da uwarku ta jefani a ciki. Saukace dai yace bazaiyi ba ku da kuke jin zaku iya kuje ga hanya”
Saroro yaran suka yi suna kallon Baba Suwaiba. Ɗaya bayan ɗaya suka shiga zamewa suna ficewa. Banda yaranta su suna zaune tare da’ita.
A mota Hadiza sai kuka take yi na baƙin cikin irin zaman da akeyi a gidansu. Wannan rayuwa da muni take, Malam na da rai ma kenan kai yaƙi haduwa ina ga Malam ya bar duniyar kuma, yaya gidan zai kasance ina makomar zumunci tsakankanin ƴan uwan junan?”
Gwadabe ya dafata yace.
“Hadiza wannan kukan ya isheki haka. Malam adda’a yafi buƙata, Allah zai tashi kafaɗunshi.”
Auwala dake gaba a zaune ashe shima hawayen yake yi yace.
“Ka barta ta koka irin rashin haɗin kan gidanmu Gwadabe. Nima kukan nake yi, ace mahaifinka yana kwance rai a hannun Allah. Amman kai bata lafiyarshi kake yi ba. Kaji fa abinda Muntari yake faɗi. Kaji irin goyon bayan mahaifiyarshi. Me Malam yayi daya cancanci irin wannan hukuncin daga diyoyinshi?”
Idanu Gwadabe ya lumshe, rayuwar gidansu na haskawa a kwaƙwalwarshi da irin tsanar da ƴan uwanshi suke mishi,hatta Babala bata fatan ta buɗe ido ta ganshi.
Ai halin da yake ciki akan danginshi yafi nasu ciwo. Matsalolin ƴan uba abune sananne wanda yazo a cikin tarihin Annabi Yusuf da ƴan uwanshi suka zaɓi jefashi rijiya, sabida ƴan ubanci, da zafin nuna fifiko”
Amman tashi matsalar mai rikitarwace sosai”
“Auwala ayi haƙuri komai ai mai wucewane wata rana sai labari. Duk daren daɗewa abubbuwa zasu zo suyi sanyi kuma su warware. Fatanmu Allah ya ba Malam Lafiya”
Haka suka ci gaba da tattauna manyan matsalolin gidan har suka iso gida.
Ayau dai su Sabitu babu fitina har aka kammala saukar Qur’ani kasancewar tare da manyan gardawan malam aka haɗu akayi sai abun bai ja lokaci ba aka kammala.
Su Auwala ana gamawa suka sake komawa Asibitin. Su Hadiza kuma suka tsaya girkin abincin da zasu kai asibitin.
Sha biyun rana Hadiza ta gama lafiyayyen tuwon shinkafarta miyar kabewa yaji naman rago. Ta jera komai a babban basket ta fito.
Daidai fitowar Shafa itama a shirye take tsab tanaso zata bi Hadiza asibitin taga halin da me jikin yake.
Tare da Anti Badi’a suka dunguma suka tafi.
Acan suka tarar da Matar Jamilu.
A wajen wata baranda suka shinfiɗa kapet huɗu, ko wacce mace da yaranta mata da ƴan uwanta. Haka abinci ma kowacce nata dana jama’arta daban sabida tsabaragen rashin haɗewar kai.
Sai da yamma Yaya Tasi’u ya leƙo yace.
“Baba kizo Malam ya farka sai ambaton sunanki yake yi.” Da sauri Baba Fhatsima ta miƙe, Baba Asshi ma ta miƙe ta bi bayan Baba Fhatsima”
“Baba kaɗai yace yana son gani. Dan Allah Baba Asshi ki koma kar ganinki ya ɓata mishi rai” Cewar Yaya Tasi’u, cikin girmamawa yayi maganar. Ita kuma cikin hargowa tace.
“Ko tare da uwarka kake yawo baka isa ka hanani shiga ɗakin mijina ba. Kisa ya sakeni kamar yadda kikai sanadin fitar Suwaiba”
Ta dubi Baba Fhatsima tana harararta.
Murmushi tayi kawai. Ta girgizama Yaya Tasi’u kai halamun yai shiru. Tare su ukun suka shiga ɗakin da Malam yake kwance.
“Asshi kar ki shigo inda nake. Ban kiraki ba bana buƙatar ganinki. Tasi’u ka fita da’ita in dai ba kana daga cikin masu son in mutu suci gadona bane”
Turus Baba Fhatsima da Baba Asshi sukai a tsaye a ƙofar ɗakin. An rasa me shiga, da me fita.
“Bakomai Malam, ba dai ni ka jefa da wannan furucin ba? Daga ni har ƴaƴana babu wanda zai sake tako ƙafarshi yazo dubaka. Da sakina kayi na huta da baƙin cikin Fhatsima data kwashe shekaru tana ƙunsa mun”
Tana gama faɗar haka ta fice da kuka nan ta tattare kan yaranta tana kururuwa suka fice daga asibitin. A ranar ta sanar ma ƴaƴanta duk wanda ya sake shiga harkar Baba Fhatsima da yaran ɗakinta bata yafe mishi ba. Wannan dalilin ya zama tsani na ƙullatar Baba Fhatsima da yaran ɗakinta. Baba Asshi ta haddasa gaba mai ƙarfi a tsakankanin yaranta da ƴan uwansu. Ƙafarsu bata sake taka asibitin ba har Malam ya kwana shida a asibiti jikin yayi kyau aka sallamoshi. Ko da aka sallameshi Baba Asshi da yaranta babu wanda yaje ya duba malam da jiki harkokin gabansu kawai suke yi.
Ta ɓangaren Baba Fhatsima da Malam kuma. Haka taita tausarshi tana kwatanta mishi ba’a gyara ɓarna da zafi. Matakin daya ɗauka ba matakin gyara bane. Da ƙyar tun yana asibiti tasa ya dawo da Baba Suwaiba, da matar Malam ɗakinsu, kuma suka tare kafin a sallamo Malam ɗin. Zaman gida ba daɗi matar malam take ji ba. Baba Suwaiba kuwa sai yawo take yi a tsakankanin gidajen yaranta.
Ta bangaren gidan Yaran Malam kuwa, babu jituwa a tsakanin matan gidan, sakamakon rashin haɗin kan dake a tsakanin mazajen nasu. Zuwa kwsnciyar Malam a asibity da sallamoshi suka san duk abinda ke gudana a tsakanin ahalin gidan. Lamarin sai ya zama yau in ba’ai hayaniya akan shara ba. Gobe akan wanke bayan gidan tsskar gidan za’ayi, gidan ya zama tamkar masu ganin hangin junansu. Ga gasa, ds yin bajinta a ƙoƙarin ko wanne ɓangare na son nuna shi ɗin shine. Malam ya ɗauki ido ya zuba, ya hana Yays Tasi’u cewa komai yace a barsu yana son ganin iyakarsu.
Ta ɓangaren Hadiza da Shafa kuwa, babu yabo babu fallasa. Da safe kafin dukkanninsu su fita aiki suna haɗuwa su gaisa. Haka da daddare suna haɗuwa a ɗakin wacce bata da kwana aci abinci a ɗan taɓa hira kuma sai ku ma wacce akayi hira a ɗakinta sallama.
Hadiza basa rabo da faɗa da Gwadabe dan ƙes ta gani wanda baiyi mata ba saita sashi gaba da maganar, hakan yasa ta zama mai yawan ƙorafi da yawan fishi. Saɓanin Shafa da take danne abubbuwa da yawa, kafin tayi ƙorafi sai abun yaci tura.
Kwatsam wata ranar juma’a tun a makaranta Hadiza tai ta faman sheƙa amai dama kwana biyu bata gane kanta ba. Ya tabbata zargin tana da ciki ya tabbata.
Ana tashi tayi gida dan zazzaɓi ne ƙaƙas ya rufeta. Tana zuwa gida ta kwanta gashi a ranar ita ke da girki, ta tashi ta dafa ta kasa, ta ce Shafa ta dafa kishi ya hanata. Sai ɓarayin Yaya Tasi’u taje Anti Badi’a ta cika mata babbar kula da farar shinkfa da romon gandar naman kan rago.
Har Gwadabe ya shigo bata iya yin wanka ba, ɗakin nata ma bata yi shara ba, a haka ya shigo ya taddata a kwance a ƙasa.
“Lafiya kike kwance a ƙasa Hadiza, ko dai babu lafiya ne?”
Ya tambayeta bayan ya ajjiye mata kayan marmarin da ya zamar mata jiki shansu.
“Wallahi jikinne sam babu daɗi. Kaga abincima sai ɓarayin Yaya Tasi’u naje na karɓo bazan iya girkawa ba” Kallonta yayi da kulawa, duk da yaji babu daɗi akan maganarta ta ƙarshe sai bai nuna ba yace.
“Inane yake miki ciwo, kin kuma sha magani?” Dariya tayi tace.
“Ciwon bana shan magani bane, ƙaruwa muka samu, ina nufin nan da watanni ƴan biyu zasu samu ƙani ko ƙanwa”
Kabbara yayi tare da rungumeta cike da farin ciki yace.
“Alhamdulillah dake da ƴar uwar taki ƙila babu nisa a tsakaninku. Itama kwanaki bata ji daɗi ba, sai ta shiga asibitin da take ba da kati aka mata gwaje_gwaje aka tabbatar mata tana da ciki”
Sai Hadiza ta ɗan rage fara,arta. (Ku fahimta da Hadiza, da Baba Fhatsima wasu irin matane masu kishin sunfi son komai ace sune gaba. Bawai kishi take kar Shafa ta samu ciki ba, ta dai fi so ace itace ta soma laulayin kafin ita Shafar. Sai gashi a bayanin gwadabe da halama ɗanta ko ƴarta sai dai su biyo na Shafa, in ba wani ikon Allah ba.)
Gaga_gaga lokaci yaita shurawa abubbuwa marasa daɗi sukaita faruwa, dambe tsakanin matan wannan gida, haka mazan dambe a tsakankaninsu. Zaman sulhu anyi yafi sau a ƙirga, haka zaman meeting ba’a denashi ba. Rarrabuwar kai sai sake ta’azzara yayi kamar yadda Baba Fhatsima da Yaya Tasi’u sukai hasashen haɗuwar ba lallai ta haifar da Alkhairi ba alai kuwa abinda ke faruwa kenan. Ƴan unguwa sunsa ma gidajen suna kusan kashi uku tsabaragen yadda suke shiga rabon faɗa a kullum.
A haka dai akaita tafiya ranaku a cikin watanni. Har matan wannan gidan masifa suka soma haihuwa, duk taron suna sai anyi uwar watsin da kowa zai tafi rai babu daɗi. Jikin Malam kullum a cikin tashi yake, dan ashe a baya ba tashin hankali akayi ba, yanzune akeyi kunsan abu dama in aka haɗa da mata.
Ana cikin haka wata safiyar talata Shafa ta haifo ɗanta namiji santalelen gaske, ta haihu da kwana biyu matar Auwala ta haihu itama, sai akace za’a haɗe bikin sunan. Hadiza kuwa jiki yayi nauyi sosai sai turawa take yi tana lallaɓawa a hakan ita take ɗorama Shafa ruwan wanka, Baba Fhatsima kuma ita ke ma jaririyar wanka Anty Badi’a kuma ita ke ma Shafa wanka, da ɗora ruwan wankan yamma, ana jibi suna ƴan takai suka iso harda Sakina da Toye akazo. Aka haɗu harda Hadiza akaita sha’ani tare da tsare_tsaren yadda sunan zai kasance.
Ranar talata Yaron Gwadabe yaci sunan mahaifinshi aka mishi alkunya da Abba. Yaron Auwala yaci sunan Malam ana mishi alkunya da Magaji kamar yadda shima malam ake mishi alkunya da wannan suna.
An gudanar da bikin suna lafiya za’ace kasancewar ba’ai wani taro mai yawa ba Shafa bata da dangi a ƙasar. Gwadabe yayi ƙoƙari ƙaton rago ya yanka ma mai jego, ga naman ƙauri saida ya kwana biyar yana kawowa ba tare daya gajiya ba.
Kayan fitar suna Shafa kawai yayi ma kala biyu, ita Hadiza yace inta haihu zaiyi mata. Ita kuma atampa da rigar yaro mai tsada ta ba Shafa.
A ranar suna da daddare gaga_gaga sai Hadiza ta kama ciwon naƙuda. Wasane gaskene taita abu guda Anty Badi’a na kanta har saida akai sallar asuba kana ta haifo ɗiyarta mace mai kama da’ita tamkar an tsaga kara.” Da uwar da ɗiyar suna cikin ƙoshin lafiya. Hadiza tana yin wanka tasha tea sai bacci.
Su Anty Badi’a da Ene data bugo sammakone suka kintsa wajen akaima jaririya wanka ta fito tubarkalla a cikin farin seti sai bacci take yi.
Matan Auwala da Mammadane suka shigo barka, me jego tana kwance tana baccin wahala, har su Auwala suka shigo da angon ƙarni Gwadabe bata tashi ba.
“Gwadabe an sake zama angon ƙarni. Gata ku ganta”
Anti Badi’a ta miƙama Gwadabe yarinya ya amsheta da bismillah ya shiga yi mata adda’a, sai ga Ayashe da Sakina harda Shafa mai jego tana riƙe da jaririnta. Taiwo da Kahinde, da Toye suna biye dasu. Yaran da suka zamema Gwadabe sanyin idaniya, yaran da yake jinsu a ranshi fiye da komai da kowa. Baya jin akwai wani ɗa ko ƴa da matanshi zasu haifa mishi da zai sosu sama da nasu Toye sai dai ƙasa. Soyayyar babarsu tana nan a ƙasan zuchiyarshi. Yanayin jini da ya ga Taiwo sai yaga Iyabo sak, kuma dama yarinya jikinta irinna Iyabonne dan ƙiba gareta.
“Shafa har dake a fitowa? Ai da kin zauna kema ba jegon kike yi ba”
“A’a Anty ai babu komai nazo inga ƙanwar Abbane, in ma Maman Abban barka” Ta faɗa da fara’arta. Anty Badi’a ta karɓi Abba a hannunta. Aka gaggaisa duka su Sakina duk sukai ma Gwadabe da su Anty Badi’a barka. Me jego bata san wainar da ake toyawa ba tana uwar ɗaku.
“Me jegon bacci take yi. Amman inta tashi zan faɗa mata” Cewar Anty Badi’a.
Gwadabe yace da Sakina.
“Sakina zaman maraɗi ya ƙara kamaki dan sai anyi suna zaki tafi” Dariya tayi tace.
“Ai nima haka nace. Duk da su Toye zasu koma makaranta, amman zamu zauna ayi suna damu”
Aka ɗanyi wasa da Dariya dai, su Gwadabe suka tafi aiki. Mata kuma suka ci gaba da zuwa barka.
Gaga_gaga haka akaita jego, kullum Gwadabe na siyo naman ƙauri itama yai mata na kwana biyar. Har ana jibi suna gwadabe bai sanarma Hadiza sunan da yaima yarinya huɗuba dashi ba. Da daddare bayan sun gama komai suna kwance suna hirar ma,aurata sai tace.
“Nifa har yanzu baka sanar dani sunan yarinyarnan ba, ko nima sai ranar raɗin sunan zanji?” Ta ƙarashe tana dariya. Shi kuwa duk saiya koma kalar tausayi.
“Dama tun ranar da nayi mata huɗubar nake ta tauna yadda zan tunkareki da zancan”
Ai saita miƙe zaune ta ƙanƙance idanunta tace.
“Kar kace da sunan tsohuwar beyerabiyar matarka kaima ɗiyata takwara?”
Dama yasan za’a rina, baiyi mamaki ba.
“E da sunanta nayi huɗubar ina fatan zaki amshi hakan. Nayi alƙawarin saka sunan nata ga ɗiya macce da zan samu ta fari…..”
“A’a Gwadabe mu bar zancannan dan narantse da Allah ba zaka ma ƴata huɗuba da sunan wata ba. Uwata na da rai ba’ai mata taƙwaraba sai tsohuwar matarka daka kasa mancewa da’ita”
Take ranshi ya ɓaci nan suka haura shima ya farfaɗa mata maganganun da yasan dole ranta ya sosu. Ya suri fulo yayi ficewarshi zuwa falo.
Ya barta a gado tana risgar kuka wiwi kamar wacce aka aikoma da saƙon mutuwa. Wani irin muƙu_muƙun kishin Iyabo yaita fisgar ranta.
Washe gari ta tashi cikin fishi da ƙuncin zuchiya. Haka ta wuni sukuku, zuchiyarta cike da fargaba kasancewar Gwadabe a ɗakin Shafa ya kwana sai su Sakina ne suka tafi ɓarayin Yaya Tasi’u suka kwana. Bata san ya canja sunan yarinyar ba ko yana kan bakarshi nasa mata sunan matarshi?
Haka gari ya waye, ga mai jego taci kwalliya ta fito shar cikin shadda bazin wacce ta siya da kudinta irin adashennan da malaman makaranta ke kafawa, ta fito tayi ɗan karen kyau yarinya ma tasha ƴar kanti me riga da siket.
Tsakar gida ta fito tanaso tayi magana da Anti Badi’a, nan kallo ya dawo kanta. Su Sakina suna bakin magudana suna aikin kayan ciki, Gwadabe ya shigo da ƙaton rago, Mammada na biye dashi da ƙatuwar tinkiya duk aka rataye mata a barandarta. Saita shiga mamakin shin rago biyu ya yanka mata kenan sabida yasa sunan tsohuwar matarshi? Ita kuwa taci alwashi in sama da ƙasa zata haɗe ɗiyarta ko sunan Shafa ba zata ci ba balle sunan tsohuwar matar mijinta, alo tsiya alo danja.
Shafa ta fito daga ɗakinta da kayan Ƴan biyu itama sai taga raguna biyu a ƙofar Hadiza a rataye ga kayan ciki cikin ƙaton bawo su Ayashe sunata gyarawa. Masu yanka kabeji,da masu yanka kaji nayi gidan ya kacame da aiki da halama sunan na dabanne. Dan matan gidama sai ɗan fitowa suke yi gulma. Matar Mammada da Matar Auwala dake ɗauke da ciki na wata shida suma suna tsakar gidan suna aiki, banda ƙannen Hadiza da kawayenta duk kowa aiki yake yi, ga Hadiza ta sha Bazin asalin babbar me geza. Ƴan biyu dake guje_guje a tsakar gida Shafa ta kira da hannu, a guje suka isa gareta, ta jasu ɗaki Gwadabe ya bita da kallo dan yaga kamar akwai ɓacin rai tattare da’ita bazai wuce akan raguna biyu data gani ba, da suturar jikin Hadiza ba.
Yana gama ratayewa ya nufi ɗakin Shafa ko kallon Hadiza baiyi ba.
“Gwadabe mufa har yanzu ba’a sanar damu sunan wannan jaririya tamu ba” Anti Badi’a ta katse mishi hanzarinshi.
“Sunanta Fhatsima. Alkunyarta Ummi”
Ajjiyar zuchiya Hadiza ta sauke ranta yayi fes. Anti Badi’a ta saki guɗa tana faɗin.
“Baba Fhatsima dole tayi mana fantimoti na takwara. Bari in shiga cikin gidan in sanar.”
Dariya Mammada yayi yace.
“Sun rigaku jin sunan tun asubar fari ai. Sai dai in akwatin zaki karɓo”
Dukkansu suka saka dariya. Gwadabe a bayan gidan Shafa yayi wanka ya kintsa, ya fito ya sameta tana wasa da ƴan biyu.
“Shafa” ya kira sunanta, ta ɗago ta zuba mishi idanu ba tare da tace komai ba.
“Raguna da kika ga biyu. Yaya Tasi’u ne ya ba Hadiza ragon ni tunkiyar na siya. Kar kiga tafi taki girma wallahi yanayine kawai duk da nasan tafi taki tsada. Suturar jikin Hadiza da hidindimun da kikaga anayi, wasu ita da kuɗinta tayi, wasu matar wanta Anti Badi’a mace mai karamci ce tayi mata. Kiyi haƙuri kinji ko, umman Abba?”
Murmushi tayi, shima murmushin yai mata.
“Babu komai Allah yasa mu dace.
Haka dai akaita girke_girken suna a gidan abinci saida akayi kusan kala uku, ga cincin da alkali, harda soɓo da kunun gyaɗa duk saida akayi. Me jego da yarinya kuwa sunga gata sosai. Dan hatta Gwadabe kayan da Yaima ummi baima Abba ba, sai haƙuri ya ba Shafa akan zai ƙaro musu in ya samu kuɗi.
Washe garin suna tun sassafe aka kafa kaskon suya. Su Sakina suka shiga shirin komawa najeriya, Hadiza ta ɗeba musu nama mai yawa sosai da cincin da dubulan. Baba Fhatsima kuma ta musu tsarabar lalle ɗan nijar mai mugun kamu da yankan salateb harda gishirin lalle wanda ake kwaɓawa da toka a shafa sai lalle ya dawo baki wudik. Har sun fita Gwadabe zai rakasu tasha sai ga wayar Tamu yana roƙon a bashi Shafa tazo tayi wankan gida.
Tamu ya wuce ya nemi abu ya kasa samu a wajen Gwadabe. Babu shiri suka ɗaga tafiyar zuwa washe gari. Shafa saita shiga murna tana haɗa kaya. Gwadabe ne ya kai zancan gaban uwar ɗakinshi Baba Fhatsima.
“To ai babu lefi tunda ka amince, kaga sunyi kawaici ma dan da wasu ne kafin ta haihu zasu zo su tafi da’ita. Babu damuwa Allah ya tsare”
Ita ta sanar ma Malam washe gari suka kama hanya sai Najeriya. Kan Gwadabe ya ɗauki zafi dan a ranar yana da zuwa wani ƙauye cin kauwa zai kai magani ba ƙaramin ciniki yake yi ba. Sai ya sha’afa bai sanar da Hadiza batun zuwa wankan shafa ba sai a bakin Shafar taji da taje mata sallama.
Alhamdulillah sana’ar saida magani tana kai mishi sosai babu laifi, har magungunan ƙarfin maza da su yaji dakan maza yake siyarwa, abu kamar wasa saiya soma haɗawa da ƙwayar bature duk dai na mazan. Kuma yana zaga ƙauyuka dan cin kasuwa, yana ciniki sosai babu abinda zaice da Allah sai godiya.
Koda ya dawo ga gajiya, ga hayaniyar kasuwa saida Hadiza ta tareshi da ƙorafinta.
“Ashe kasan Shafa ba zama tayi ba za’a tafi da’ita wanka shine baka faɗa mun ba.” ( Mata mu dinga lura da lokacin daya dace mu shigar da ƙorafinmu ga miji. Kuma mu sani mu tsaya a iyakar matsayinmu dan kare mutuncin kanmu, musamman in kina da abokiyar zama) A faɗace yace.
“Ai ba huruminki bane dan Shafa zata wankan gida saina sanar dake ba. Tunda ta miki sallama ai Shikenan. Da dawowata kin tarbeni da ƙorafi'”
Yana faɗar haka ya shige ɗaki yana ta tauna al’amura lamarin Hadiza ya soma isarshi gaskiya mace sai shegen ƙorafi shi kenan kullum shi a cikin yin ba daidai yake ba kenan?”
Tsaki yaja kawai.
Gaga_gaga haka rayuwar taita turawa kwanaki cikin kwanaki. Har Shafa tayi arba’in. Ana gobe Hadiza zatayi arba’in Gwadabe ya dawo daga cin kasuwa can garin Tawa yace.
“Ki shirya jibi zamu je Najeriya. Zamu je mu gaishe da su Babala da abokaina. Shafa ma jiya suka shiga Takai ɗin.”
“To Shikenan Allah ya nuna mana. Dan Allah kayi haƙuri a bisa laifin da nayi maka jiya. Wallahi zuchiyata ce ta kasa jura naga daka dawo a madadin ka mayar da hankalinka a kanmu ni da Ummi. Sai inga damuwarka Shafa dai da Abba.”
Ƙur ya zuba mata idanu kamar bazaice komai ba dai sai yace kawai.
“Bakomai Hadiza. Gobe ma da ƙorafin da zaki kawo. Kinga ita ko Shafa bata taɓa mun ƙorafin komai a kanki ba. Hadiza baki gane bane kinci babban kaso a zuchiyata mai girma. Ya kamata ki kwantar da hankalinki”
Murmushi tayi taji daɗi har a cikin ranta. Kuma ta gamsu da hakan. Tana girmama yadda Gwadabe yake ɗaga mata ƙafa. Har cikin ranta tasan kishi da ƙorafi shine matsalarta, tayi imani Shafa ma nada nata matsalar.
“Na haɗa harda kason tsohuwar matarka na kwakwushe Iyabo?”
MRS BUKHARI
Part 5
NAMA YA DAHU…
ROMO ƊANYE
GAWURTATTU UKU
BADI’AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
LITTAFI NA UKU (5)
Iyabo
Baffa Musa yace.
“Wajen kiwo ba damuwa bane. Ko nan gidanku zai dinga zuwa yana garkesu. Ko gidana, ko gidan me sunanki Jabu.
Zamu bari ranar Talata ranar kasuwa sai muje akwai shanu na siyarwa da ake kawowa. In ma ba haka ba akwai inda zamu je da Amaduyal din mu samo miki. In yaso ko tunkiya da rago sai ke ki siya ki watsar a tsakar gida, suna cin ƙanzo da ciyayi sai kiga kin ta da garke, in wata matsuwa ta kamaki sai ki ɗaga abinki ki siyar.
To Shikenan Baffa zuwa gobe Amaduyal zai kawo maka kuɗin in sha Allah. Duk yadda kudin suka yi sai ayi abinda ya dace dashi kuma zuwa jibi zan buɗe kayana in soma siyarwa, abinda na kuma gagganɗawa sai a sake siyowa, har kaji da zabbi inaso in saka, naga su Baɗɗo duk suna kiwonsu”
Baffa Musa yayi mun dariya yace.
“Jabu mutanen birni, ta dawo matar ƙauye”
Nima dariyar nayi. Nan dai muka gama abinda zamu yi, zuwa bayan la’asar Uwani taima su Dada sallama akan gobe zata wuce, daga haka sai muka koma gida.
Babu kowa a gidan, sai awaki da kaji da suketa shaƙatawarsu. Tsakar gidan duk datti da tarkacen bokatai da tukwanansu na dafa nono ƙudaje sai fareti suke yi. Mayafina na rataya a saman bishiyar gidan na ɗauki tsintsiya tun daga kitchen na zakulo shara, a iyakar kitchen kawai saida na fitar da tarkacen ledoji da toka ƙaramin buhu. Duk girman tsakar gidannan na share tas, na haɗe musu kayan kazantarsu a bakin rijiya inda suke wanke’wanke da wanki. Lokaci guda gidan yayi fes ras dashi.
Karar girki dana gani a jibge a kusa da ɗakin Baɗɗo na ɗebo Uwani ta tayani muka hura wuta abu kamar wasa wuta ta kama na tsayar da sanwar miyata. Uwani tayi mun jajjage a babban turmin gidan, su citta, tafarnuwa, diyar miya duk muka daka na wanke naman rago na sashi a ɗayan gefen na murhun na sanar muku baki bibbiyu suke gina murhun, saina ɗaura tafashen nama a ɗaya, ɗayan kuma na tsayar da sanwar miyar karkashi. Awa uku cir muka yi a kitchen kafin na kammala tuwona na shinkafa miyar karkashi yaji nama. Soyayye Tuwon na ƙuƙƙula a leda na cika babban flaks, na bare sabon filas tuwo da miya na zuba na kai ɗakin Yafendo da dawowarta kenan.
“Sannu Jabu gida yayi kyau sosai. Allah yayi albarka ya baku zaman lafiya”
Ameen Yafendo nagode.
Ina fitowa daga ɗakin Yafendo sai ga matan gidan sun dawo zuga guda da goyo da ƙananun yara raɓe_raɓe ga siyayya iri_iri sunyo. Suna ganin yadda gidansu ya sake sunsan aikinane.
Sannu da zuwa nayi musu na shiga binsu da tuwon girma ɗaki_ɗaki. Da nazo kan Hama bari kuji abinda samodarar tace dani bayan taƙi amsar tuwon fur.
“Au a rabe zamu dinga yin girkin? Aina ɗauka duk wacce miji yake ɗakinta ita zata girka abincin ?” Murmushi nayi mata.
A’a ko wacce girkinta zata dinga yi, in ranar girkinki tazo kina wajen tallar Nono ni ina gida bazanci abinci ba kenan?” Ai saita zabura tace.
“Ai kema zakiyi tallar nononne, wallahi ban yarda a raba girki ba” Dariya nayi mata na wuce da tunowa na ƙarama Baɗɗo.
Bayan na fito wanka na zuba tuwon na aiki yaro ya kaima Dada dan nayi alƙawarin ko ƙasa na dafa tare zamu ci da Dada, kuma nasa Baɗɗo ma ta roƙi mijinta ta dinga aikama da Dada abinci duk a haɗu a rufa ma kai asiri.
Yaya Hamma basu suka shigo ba shi da abokanshi sai bayan isha sai gasu. Naci dariya, sunyi santin tuwo sosai ɗaya daga cikinsu ma cewa yayi abincin ƴan aljannah ne. Sai tara da rabi suka yi mun sallama suka tafi suna faɗin zasu turo matansu koyon girki. Ni kuma sai nayi amfani da damar wajen tallata musu kayana tare da sanar dasu jibi zan buɗe dilar. Duk sunce zasu ba matansu kuɗi su zo su sai zanin gadon makka, kunsan dai kayan makka da farin jini.
Bayan Yaya Hamma ya shigo mun kaɗaita komai ya lafa sai nake labarta mishi duk yadda muka yi da Baffa. Shima ya goyi bayan ayi hakan babu damuwa. Sai naji nasamu nutsuwa sosai. Washe gari sassafe Uwani tai mana sallama ta kama hanyar kano harda ƙaton zakaranta da Baɗɗo ta bata.
Muna dawowa daga rakata ni da Yaya Hamma, yana shirin fita sai muka jiyo sallamar Amaduyal. Kuɗaɗen dake hannuna na tattare dubu ɗari ukku na bashi su a baƙar leda, ragowar kuɗaɗen dama nayi musu mugun ɓuya ƴan kuɗin hannuna bai wuce dubu saba’in ba haka wanda suke fili ɗan na zara a kashe wutar data taso.
“To ni zan tafi aiki. Akwai abinda kike buƙatar in siyo miki a birni ne?” Ya tambayeni na girgiza mishi kaina.
A’a babu sai dai in maka fatan dawowa lafiya. Amman kafin ka fita ya kamata ace akwai kayanka ko kala biyune anan ɗakin bawai kullum in kayi wanka zaka fita sai dai kaje ɗakin Hama ka saka ba” Dariya yayi ya shafa fuskata.
“Hakane Jabuna. Zan ɗebo inna dawo. Kar ki manta kafin Hama ta fita ki je ki karɓo garin tuwo da man shanu. Inna dawo zan nuna miki naggenki da zaki dinga tatsar nono a jikinta, kinga sai Baɗɗo ta koya miki yadda ake fitar da man kya dinga fitarwa da kanki kin samu na girkin ki ko, madarar da Nono sai ki ta sha tunda kinƙi tallar nono ” Dariyar soyayya mu ka yi ma junanmu. Na dinga ragargazo mishi adda’a yana ameen_ameen harya fice daga lungunmu.
Sai da naga tafiyarshi ina rakuɓe a bakin lungun harya fita Hama ta bishi da gudu raɓe_raɓe da nononta guda ɗaya ta ciroshi ta wuyan riga. Ga Yuguda mijin Baɗɗo a wajen Hama ko a jikinta.
Da ganin yadda take magana faɗa take yi ilai kuwa sai naga tana share hawayenta. Kaina na girgiza nayi komawata ɗaki nayi ɗaiɗai a ƙasa ina tura wainar ƙwai ina danne maiƙon da ruwan tea na me madara.
Saida na gama karyawa na fita tsakar gidan, tun sassafe na kaima Yafendo nata abun karin.
A zaune a ƙasa durshan na samu Hama tana jijjiga madara kwananniya dan fitar da man shanu. Kanta babu ɗankwali ya ilahi zo kuga gashi wallahi kamar a india amman annakiya zata kashe shi, wani irin dattine a daddanƙare akan da ciyayin katifa.
Ina kwana Hama ya kwanan yaran?” Baki ta taɓe tace.
“Lafiya”
Dama Yaya Hamma ne yace ki bani garin tuwo da ɗanyan mai” Dariya tayi harda shewa tace.
“Ai Hamma ya gama kwanaki ukkun da zaiyi a ɗakin ki, kinga harya faɗamun kalar miyar da zan kaɗa ta dare. Saiki bari in kwana ya zagayo kanki sai kizo in baki” Ta ƙarashe da Dariyar ƙeta harda sakin waƙa da fulatanci.
Turus nayi a tsaye ina jujjuya kalaman nata. Taya akayi kwanan suka zama uku. Kenan harda darena na farko da tazo ta jaye shi harda daren a lissafi kenan? Wata bazawarar dariya nayi dan wallahi yau sai Hama taga bariki zan nuna mata nayi zaman gidan karuwai a saudiyya.
Kaina kaɗa nayi tafiyata, matan gida sai kallona suke yi, Baɗɗo har ɗaki ta biyoni tana bani haƙuri ta kawo mun man shanu ƙwarya guda da garin jar masara nata.
A’a ki koma da masarar, man shanun dai na karɓa.”
“Adda sabida ke fa ko gaisuwata Hama bata amsawa, ta hana yaranta wasa da nawa yaran. Ko a mota muka haɗu ta dinga tsaki kenan. Kuma ƙawayenta ke zugata wallahi baranma Daso. Jiya a kasuwa sun haɗu da Daso naga ta bata ƙunshin wani magani naji ana cewa da tayi amfani dashi Shikenan. Ni dai iyakar abinda naji kenan. Adda kiyi a hankali Hama hatsabibiyace” Dariya nayi ina mamakin Daso, ita da take ƴar uwata amman da ita aka haɗe kai ana son sai anga bayana. Ni zancan asiri_asirinnan na Hama zancan gaskiya yana tsoratani duk da na dogara da Allah, amman bansan wacce iriyar illa zatai mun ba a kwana a tashi. Numfashi naja nace ma Baɗɗo.
Da izinin Allah asirinsu bazai yi tasiri a kaina ba. Bari in baki tea da ƙwai ki kaima Dada, kullum kafin ki fita ki leƙo ki tafi mata dashi.
Itama saida taci nata ta fita dana Dada da garin tuwonnan. Suna fita na nufi ɗakin Yafendo na tsiri yi mata kwalima na gyare mata ɗaki tas na fito da wankinta na haɗe da nawa na wankesu tas. Na wanke ƙazamin bayan gidan tas da toka, na tusa sharar tsakar gidan. Sai gidan ya dawo abun sha’awa har wani fili ya sake yi gidan yana da yalwa sosai da sosai.
Da rana na dafa mana farar shinkafa ina da miyata a ɗakin Yafendo naci nawa, yaran gidan duk da iyayensu suna ajjiye musu abinci a ɗaki na harhaɗa kansu na zuba musu a tire suka daka wawar abincin.
Can sai gasu Yusufu da Kari sun shigo, a ɗakin Yafendo suma suka yada zango aka gaggaisa na zubo musu abincin. Kari na cin abincinne take sanar dani.
“Dama Dada ce tace mu zo mu sanar miki an siyo shanun, harda tumakai biyu da akuya. Zuwa anjima Amaduyal zai kawo su nan gidan shanu sunyi kyau”
Murna ta kamani sosai, Yafendo ta sanya mana albarka ta riga tasan komai a wajen yayyenta. Na tambayi Yusufu ya suke suna dai samun abinci ko?
“Wallahi a’a Adda ana bamu dai na safe. Amman na dare wata rana sai dai Cubu ta siyo rogo a ɓoye ta kawo mana muci, ko ƙosai, ko ƙarago. Dama Kari ce ke sa mana abinci kafin Baffa ya koresu.
Shiru nayi idona ya cika da hawaye Yafendo tace.
“Yanzu su Hassana sai su hanaku abinci dan basu da imani bayan taƙamar tasu dukiyar ta Daso ce akai mata fin ƙarfi?. Babu komai ke Jabu aiki ya sameki sai ki ƙara sanwa su dinga zuwa suna ɗaukar abincin a wajenki. In yau kin basu, gobe sai Baɗɗo ta basu. Mu ba ma bari su tagayyara ba, watarana sai labari.’
Godiya nayi ma Yafendo sosai, Yusufu shima yayi farin ciki sosai da wannan bayanin.
Hakan kuwa akayi dan su Yusufu basu tafi ba har saida na gama abincin dare, shi ya tafi musu da nasu, Kari kuma ta tafi dana Dada bayan taci nata. Yafendo ma na miƙa mata nata. Nan na shiga hidimar tarbar miji, ina jiyo hayaniyar dawowar su Baɗɗo masu tuwon dare, sai su kai goman dare basu gama tuwo ba.
Takwas dai-dai Yaya Hamma ya shigo dan naji muryarshi abun mamaki sai naga har minti talatin bashi ba dalilinshi, ni gashi naci kwalliya kuma naci alwashin saina nuna ma Hama shiru_shiru ba tsoro bane. Ai saina ɗauki mayafina na yafa na fice. Hama na kitchen nayi shigewata ɗakinta ga zahiri yana ciki ga takalmin robanshi nan a ƙofar ɗakin. Cusa kai nayi da sallamar da buɗe labulen a tare.
Yana zaune babu riga daga shi sai dogon wando, ba laifi yau ɗakin ba a hargitse yake ba anyi mai gyara buja_buja. Yana riƙe da yarinya yana mata waƙa da fullanci.
“Jabu irin wannan ƙyalli da kikeyi kamar wata ɗan dare sha biyu?” Wata basarakiyar murmushi nayi mishi na nemi daf dashi na zauna jikina da nashi na gugar juna, na wani narke mishi duk na sukurkutashi da kallo masu fassararo. Da shawaba nace.
Naji shigowarka tun ɗazu sai naji ka shiru. Nazo na ganka a tuɓe ka manta kwananane?” Idanunshi har sun ƙanƙance, hannuna ya kama ya ɗan matse a nashi ni dashi du muka lumshe idanu na sake shigewa jikinshi. Yayi daidai da shigowar Hama da tiranta na silba. Ba shiri ta saki tiran komai ya watse ji kukeyi rakwacam.
Tasha kwalliyarta harda janbaki. Atampar jikinta ta amsheta ban ɓoye muku ba Hama a fulaninma ita kyakkyawace wallahi saida gabana ya faɗi data shigo dan koni tayi mun kyau, damma dinkin yayi mugun yi mata yawa rigace a mugun ɗangale har cikinta ana gani wuyan rigar kuwa baya ko zama. Amman dake atampar ja ce sai ta haska.
“Me zan gani wannan Hamma. Baka sanar mata yau kwanana bane da zata ci kwalliya ta shigo mun ɗaki sabida neman fitina. Da nice nayi haka ace ban kyauta ba. Jibi yadda ta matseka har kana riƙe hannunta sabida rashin kunya”
Da fullanci take du wannan maganar, tanayi tana hawa tana sauka, dan masifa har hunhuna hancinta yake yi.
“Shigowarta kenan kema kika shigo. Meye laifi danta shigo ɗakinki, da kike maganar ta zauna kusana na riƙe hannunta. Matatace halaliyata ai kin sani” ya faɗa mata haka, ai saita sake hawa tace.
“Sai ku bari kuje ku karata ranar girkinta bawai ranar girkina tazo har ɗakina ta nuna mun ta fini iya kwanciyar Aure ba. In banda Hamma kana da kamata kyakkyawa wanke hannu ka taɓa me yasa ka auro Jabu oho..”
“Kiyi mun shiru baki da hankaline” Ya daka mata tsawa, ni kuma nayi murmushi na miƙe. Hama gadararta kyaune, ni kuma ina gadara da ƙirar da Allah yaimun musamman mazaunaina wanda nasan yana rikita kan maza, kuma shi kanshi Hamman mazaunan suna daga cikin abinda suka fi fisgarshi game dani. Ba yabon kaiba ina hamdala da irin dirin da Allah ya bani, ko a fuskar ni ba mummuna bace, na yarda a fuska Hama ta kereni ovar, amman baya ga haka na fita kayan alatun more rayuwa sau dubun dubata.
Saida na yi taku na kaɗa mazaunaina sosai kana na juyo.
Yaya Hamma ina jiranka karka daɗe. Bazawara kwana uku take dashi, a iyakar sanina kwananka biyu a ɗakina. Bazan iya sarayar da kwanana ba, dan na fita buƙatar kwanan”
Ina dasa aya nasa kai na fice.
Wane tudu wane gangare sai ga Yaya Hamma ya biyoni. A wannan daren na wanke mishi kai tas, abubbuwa da yawa sun faru masu tsaiwa daram a zuchiyoyi, muka wayi gari cikin farin ciki da shaƙuwa a tsakankaninmu, na jefa Yaya Hamma a duniyar da nayi imanin bai santa ba kafin ni. Wannan saiya zama matattakalar ƙara buɗe sabon faifayin sona a zuchiyar Yaya Hamma, yana ji dani sosai, wallahi baya son ganina a damuwa ko ɓacin rai.
Tun asuba Hama ta wayi gari da dukan yara da zaginsu a nufinta na hucewa a kansu. Ina jiyota Yafendo na mata faɗa, shima uban gayyar bayan ya gama shan soyayyarshi daya fita ina jiyoshi yana mata faɗa.
Ni ko a safiyar ranarma bata ganni ba har ta gama dafa madara suka kama hanyar tallah.
Bayan na gama aikin shara da wanke bayi dana ɗaurama kaina , na dafa abinci mai yawa, na kaima Yafendo nata.
Yafendo zanje gida, yau nake son buɗe kayana na siyarwa. Daga nan duk zan leƙa maƙota in sanar musu” Murmushi tayi tace.
“Ƴar albarka. Yi tafiyarki zan shiga da kaina duk in sanar musu zaki kuwa kwanɗa ciniki mu nan mata suna da kuɗaɗensu babu laifi. Bari mu fita tare”
Abun sha’awa a tare muka fita, ni na tafi gida ita kuma ta dinga zagaye gidajen wannan gunduma tanai mun tallah.
Ina isa gida na tarar da Dada da Kari a tsakar gida, Dada na kwance Kari na wanke_wanke.
Ganin Dada na hutawa shine farin cikina ko iya haka burina ya gama cika sanadiyyata Ƙaddararren aurenta ya mutu, sannan sanadiyyata ta dena yawon wahalar talla itama ta soma morar haihuwa ai bata ga komai ba in sha Allah saina biya mata makka taje kafin rai yai halinshi.
Muna haɗa idanu tayi mun murmushi mai kyau. Danma bata sakewa dani kundai san halin fulanin daji. Amman murmushinta shi ya nuna taji daɗin ganina.
Gaga_gaga na shiga buɗe kaya na soma da buɗe zannuwan gado. Wasu ƙananan zannuwan gadone masu ɗawisu suna da santsi, na kwasosu da yawa gaskiya sabida suna da sauƙin kuɗi. Masu tsadar ɗan jejjefosu nayi. Dogayen riguna kuwa gaskiya masu kyaune giredi wan baƙaƙe sunfi yawa. Ina kam ciccira rigunan na soma jin sallamar mata Yafendo na ta tawo mun su. Allah cikin ikonshi wannan zannuwan gado sai suka tafi dasu, a ƙauyan kab su basu taɓa ganin irin wannan zannuwan gadon ba. Du mata gomannan da suka zo ganin kaya saida ko wacce ta sai ganin gado nera ɗari dubu ɗaya kuɗinsu. Dogayen rigunan kuma ɗari biyar biyar ko wacce ƙulle da gyalenta. Hayaniyar matannan ita ta jawo mun hankulan matan maƙota gida fa sai ya ɗinke da mata. Alhamdulillah zannuwan gadonnan an kwashesu duk da dogayen rigunanma an jidesu na kama ƴan ƙudaɗena na ɗaure. Wajajen azahar gidan ba kowa, bayan nayi Sallah saina zuba ma Dada abincinta na zuba nawa, wanda yayi ragowa na miƙama Kari da yaranta. Yafendo dama ko zama batai ba rako wannan mata kawai tayi ta koma ta bar yara ƙanana a gida.
Zuwa bayan la’asar saina ɗau haramar komawa gida. Na bar riguna ashirin, da zannuwan gado ashirin na danƙa a hannun Kari akan in wasu matan sun shigo siyan kaya saita nuna musu. Na bata doguwar ruga biyu nata da zanin gado. Na ɗan tsinci digayen rigunan da zanin gadon na sa a leda. Naima su Dada sallama na koma gida.
Abinci na ɗaura na shiga aikin shara duk da ɗakin a share yake amman so nake in ganshi ƙal_ƙal.
Ina gama sharar saiga ƴan tallah sun shigo. Bayan sun nutsa na fitar musu da kaya suka kwashe, har Hama saida ta sai doguwar riga baƙa da zanin gado. Rai a turɓune ta kunce gefen zani ta ƙirgomun kuɗina na dafe. Banyi tunanin zata ko kalli kayan ba, dan dana je wajen nai musu sannu tana wanke_wanke bata ko ɗago kai ta kalleni ba. Jin yadda ake kururuta zannuwan gadonne yasa ta wanke hannunta tazo kashe ƙwarƙwatar idanunta.
Da magriba Yusufu yazo ya ɗaukar musu abinci, na haɗa mishi dana Dada. Amaduyal ma da yazo ɗaure shanu saida ya shigo na cika mishi kwano da abinci ya cinye.
Ni dai ina yin sallar isha nayi kwanciyata dan nasan yau Hama ba zata barshi yazo ko gaisawa mu yi ba.
Ai kuwa wajajen sha ɗayan dare ina bacci naji ya faɗo ɗakin. Da sauri na farka dan tsoro ya bani ma.
“Gimbiya har kinyi bacci ba tare da kin sani a idanunki ba? Ni inacan gangar jikinace acan ruhina yana tare dake”
Yayi maganar yana shafa fuskata. Lumshe idanu nayi nace
Nasan ƴar rigimar matarka ba barinka zata yi kazo ba, kaga shi yasa nayi baccina amman kana ƙasan zuchiyata can ciki”
“To da fatan kina lafiya?”
Sai alkhairi ya aikin, da fatan ka dawo Lafiya?” Murmushi yayi yace.
“Lafiya lau wuni nayi ina tunaninki. Nayi kewarki sosai. Yanzu dai da safe ki shirya zan kaiku gidan ogana matarshi ta haihu gobe suna zaku je mata dan ta dameni da gori”
Nan mukai sallama ya fita. Lumshe idanuna nayi bacci mai cike da mafarkai yayi sama dani.
Washe gari kamar kullum na gama duk abinda ya dace da sauri dan Yaya Hamma ya turo Hama yace inna gama in samesu a ɗakinta.
Kwalliyar leshi nayi fari sol mai kyau da tsada, takalmina da jakata masu ruwan zuma na ɗauko ɗankunne da sarkar gwal na saka, da awarwarona da zobunan zinare, turare mara ƙarfi na fesa a hammatata dan gudun yin warin zufa kunsan mu masu ƙiba gaskiya ba wuya munyi zufa, daga zufa sai warin hammata yanzu saimu gume waje. Shi yasa ko wankana yana ɗaukar lokaci ba laifi dan sai nayi cuɗa da ɗauraya sosai.
Zanin gado ɗaya na ɗauka na sa a jakar leda ta ƴan gayu zan kaima mai jego. Tun sasssafe na aiki Amaduyal da yazo kaɗa shanu gida ya kwaso mun kaya na loda a wata babbar jaka.
Fitowa nayi tsakar gidan ba kowa, sallama nayi ƙofar ɗakin Hama suka fito muka kama hanya.
Babu laifi Hama tayi kyau kunsan farar mace akwai haskawa atampa koddibuwa ce mai ruwan kore da ruwan madara. Sai dai fa mayafi mai ruwan bula ta saka sai takalminta baƙi, da wata cinyayyar jakarta ja abunta. Kuma ita da gaske ta kece raini haka take ji dan taƙu ɗaiɗai take yi.
Haka dai muka shiga cikin gari Yaya Hamma ya kaimu gidan oganshi anguwar masu kudi tabkeken gidan sama. Har falon gidan ya shiga damu, yasa masu aiki sukai ma Hajiyar gidan magana.
Mace mai karamci da faram_faram sai gata ta fito tana walƙiya.
“Ah Hamma masha Allah wannan mata zuƙa zuƙa haka ga siririya ga duma_duma. Bayin Allah sannunku da zuwa kuzo mu shiga ciki”
Nan Yaya Hamma yai mana sallama akan da yamma zai zo ya ɗaukemu. Hajiyannan har uwar ɗakinta ta kaimu muka zauna a cikin ƙannenta. To kunsan mu yarbawa bamu da son jiki, saina sake na shige dangin Hajiyannan mukaita aikin girki, muka gama kuma na wanke musu wajen tas. Hama kuwa tunda ta zauna saita noƙe ta sake takurewa.
Kafin a taru na ba Hajiyarnan zanin gadonnan gudunmawata, Hama kuma ta miƙa mata omo data ƙunso a jakarta, kafin Hamma ya tafi ya bamu ko wacce dubu akan ta bada gudunmawa. To tunda ko wacce na da abin bayarwa saita miƙa ta soke dubunta.
Da naga taro yai taro an cika an batse saina kunce haja. Allah cikin amincewarshi wallahi kaya suka ƙare kab har ana nema saida nayi cinikin nera dubu arba’in ku kunji rabo. Wannan Hajiyarma tace in kawo mata zanin gado amman in bata sari tana da shago a kasuwa na zannuwan gado da su ledar tsakar ɗaki da kafet. Wata baiwar Allah ma tace in mata kwatancen gidana zata zo sarin riguna tana shiga ƙauyuka cin kasuwa. Na mata kwatance, gidana ta sanar dani gobe zata shigo.
Haka wunin sunan ya kasance dai, akwai wata baiwar Allah ita kuma magungunan mata ta kawo, nima har na sai wani magani da naji anata yabon kyanshi. Hama ta kalleni ta kawar da kanta.
Amman dana juya baya saida ta miƙa dubunnan ta kwashi kaya itama.
Da yamma da Yaya Hamma yazo kwasarmu Hajiyannan ta cika mana kuloli biyu da abinci babbar kular farar shinkafa ce, ƙaramar kular kuma miyar naman saniyace a ciki, banda lemo da ruwan roba, da cincin duk saida ta haɗa mana.
Mu tara gobe in Allah ya kaimu
MRS BUKHARI
Part 6
NAMA YA DAHU…
ROMO ƊANYE
BADI’AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
LITTAFI NA UKU (6)
Sai yaushe Hamma zaka sake kawo mun Jabu zuwa na musamman? Na yaba da’ita sosai, kaga har Halima ƙanwata tace tana sonta da ƙawance naga har adireshin juna suka karɓa, ita tana aure a Girei ne” Ɗan murmushi Yaya Hamma yayi ya sauke kai. Hama ai saita haɗe fuska tai kicin_kicin.
“Hajiya zan kawota duk ranar data shirya in sha Allahu”
“To to Shikenan. Jabu zannuwan gadon zasu kai guda nawa wanda ya rage miki?” Ta tambayeni.
To gaskiya da yawa dila guda na buɗe, sai dai ki faɗi guda nawa kike so”
“Kice Hajiya ce. Ko da yake Hamma ya ba Alhaji labarinki lokacin baki dawo saudiyya ba. To a ba Hamma guda talatin ya kawo mun, zai tawo miki da kuɗin”
Faɗin da Hajiya tayi Hamma ya sanarma Alhaji oganshi labarina ba ƙaramin kura Hajiya ta kwanto ma Yaya Hamma ba, dan sai kallon Hama yake yi a ido_a_ido. Tako turɓune fuskarta, daga ƙarshe ma wajen ta bari sai a bakin get muka taddata, muka koma gida duk a gajiye, ni dai da nasan ba kwanana bane, ɗakin Yafendo na leka nai mata sannu da gida nayi shigewata ɗaki. Nasan masu jiran abincina dole suna can suna jira, dole na kunna risho na ɗaura macroni fara. Ina kan dafawa saiga me sunan Yafendo ta shigo bako sallama da roba a hannunta an shaƙo shinkafa an camɓala miyar akwai. Hancin yarinyar du majina, kayan jikinta kuwa du ƙura. Kije kuci ke da ƙannenki kinji yarinyata” Bata jin Hausa ni kuma fillancin nawa baikai yadda zan mata bayani ba. Ta dai fita da abincin ta mayar. Ina zuba ma Yusufu da yazo yanzu abincinsu dana gidan Dada sai Hama ta fado ɗakin bako sallama har tana tuntube da ƙafar Yusufu, daga ita sai ɗaurin ƙirji. “Na aiko yarinya kin dawo da’ita ina cin abinci kinsa an tasoni” Tana magana sakaka kamar goyon kakannin. Murmushi nayi nace. Na riga da nayi girki ki karama yaran suci” Saita fice fuu. Washe gari sai rigima ta kaure tsakaninta da Hamma. Ashe tunda aka kawoni aketa faman rikicin dole sai dai mu dinga yin girki ɗaya kamar yadda mijin yake ɗaya. Kunsan ƙauye suna da riƙo da al’ada, rikici har gaban Yafendo ita kuma a ƙoƙarinta na son a zauna lafiya sai tace. “Tunda dama hakan akeyi, kuma daga yau kuyi hakan banason wata magana kuma. Ke Jabu ki soma girki da abokiyar zamanki tunda girkin naki ne yau. Ke kuma ki sani akwai kwanon ƙannenta dana mahaifiyarta da ake sama abinci saiki dinga sa sanwa dasu. Banason ƙara jin wata fitina.” Inaji ina gani haɗa girki ya tabbata. A ranar ansha waƙe a tsakar gida kafin su fita tallar nonon. Na shige ɗaki naci kukana na share hawayena ni bansan ta yaya zan iya ɗanɗana girkin Hama ba. Mai gayyar ya dinga rarrashina kafin ya tafi aiki. Da zai fita sai Hama sai taga mun fice tare, sai hankalinta ya tashi. Ina ganinta har ƙofar gida ta fito bata koma ba saida muka yi kwana. Ni kuma zannuwan gado na kwasa a gidan Dada na bashi zai tafi ma matar Oganshi. Na jido kaya Kari ta tayani muka kawo gida, daga haka sai muka ɓige da hira har wannan baiwar Allah mai sarin dogayen riguna ta iso. Tako sari riguna sosai ta caskemun kuɗaɗena kuma tace. “In sun ƙare gobe ma zaki iya ganina na dawo. Yola zan kai kayan gobe akwai cin kasuwa, ko mai mutum yakai ƙarewa yake yi.” Nan tai mana sallama dai Gaga_gaga haka ranaku sukaita zama wata, al’amura sunata sauyawa. Tunda muka haɗa girki, duk ran girkin Hama su Dada basa samun abincin arziki. Sannan karfa ku mance ita Hama abincin dare dana safe kawai take yi da rana dole ni in ɗaura tukunya in girka, daga baya ne na dena girkawa sai dai in dama mana nono da fura musha, ni da kaina nake tatsar madarar in mayar da’ita nonon. Duk kwanan Hama abincin da take kawo mun saita bado magani a ciki. Ni dai ban taɓa ci ba, hatta banɗaki in zan shiga saina sake wankewa sai inga garin magani a kasan bayan gidan an barbaɗa mun. Har wata baƙar laya na tsinta a tsakiyar gadona, na ɗauketa da bismillah. Karambani irin nawa maimakon in cillar saina buɗe layarnan. Zanen mace na gani a jiki, an caccaka mata abu a mararta, sai gashi silli ɗaya, da ƙwayar barkono guda bakwai. A shara na cillar na ja bakina nayi shiru. Ta ɓangaren Yaya Hamma kuwa ina ganin soyayya ta haƙiƙa na fahimci ɗakina ya mayar dandalin nishaɗi da nutsuwa, dan kullum sai yayi mun waƙar soyayya. Soyayya ta yi soyayyar da duk ran asabar da lahadi ina rakashi kiwon shanu, sai in dafa mana abinci insa a wata jaka da ruwa da komai in bishi mu kutsa jeji muna tafe muna hirarmu ta soyayya. Da wannan soyayyar na jawo ra’ayinshi na askeshi tas yana noƙewa ni dai ina sara. Kunsan Allah sai da yayi zazzaɓin wannan aski da nayi mishi, wajen har kumbura yayi na kwana biyu kafin ya saɓe. Wanka kuwa Alhamdulillah yana yi, yana goge bakinshi, kayanshi na ɗakina suna samun wanki mai kyau har turare nake fesa mushi. Kayayyaki kuwa sai karɓuwa suke yi a hankali a hankali kaya nata tafiya. Harna sake sayo Shanu, na sake siyo tunkiya inata kiwon abina, Kari kuwa ta koma tallar Nono tana girkinta ita da Dada, amman hakan baisa an dena zuba ma Dada abinci daga gidana ba, haka su Cubu.
Matar ogan Yaya Hamma kuwa ya kaini naje na wuni mata, da zan dawo ta hadoni da goma sha tara na arziki. Ƙanwarta Halima naje mata itama tazo mun. Ashe layin su ɗaya da layin da Daso take aure. Gidanta yafi ko wanne gida kyau a unguwar. Dake Yaya Hamma ne ya kaini shine yake nuna mini gidan Dason. Da yamma da yazo ɗaukata sai muka ratsa bata dawo talle ba. Gaga_gaga dai anata tafiya ana ƙarawa da haƙuri da kawar da kai. A cikin matan ƙannen Hamma Safiya ce kaɗai muke shiri, duk sauran basa shiga harkata bana shiga tasu harkar, sun haɗe ma Baɗɗo kai ta dena jin daɗin zaman gidan. Ba dama tazo ɗakina ko ni in shiga nata ɗakin sai tsogumi a tunaninsu sai gulmace zata haɗamu. Dan a zauna lafiya sai nace da’ita tayi zamanta ma dinga haɗuwa a gidan Dada. Amman in na ɗan dafa abin ɗaukani ina zuba mata, harsu matan gidan ina basu kuma su lashe, amman saidai in ɗauki kwanono a bakin rijiya an yasar mun dashi.
Wata ranar juma’a nice da kwana, gaga_gaga na gama aikin tuwon dare na sallami kowa, Hama na bar mata nata a kitchen dama anan nake ajjiye mata inta dawo ta ɗauka. Na shalla wanka, jiki ƙamshi ɗaki ƙamshi ina harɗe misalin tara na dare Yaya Hamma ya shigo. Me zai faru, kamar yadda na saba tarbarshi da gudu in rungumeshi haka naje, duk da yana tsantsar jin kunyar hakan amman yanaso dan bai taɓa hanani ba.
Ina isa wajen sai ya ja da baya yace.
“Dakata karki taɓani” Ai sai nayi dariya a tunanina ko zolayace ashe da gaske yake, saida na rungumeshi sai ya ɓanɓareni a jikinshi harda jan tsaki.
Da ƙyar na juyo na zauna a gefenshi ba guiwa.
Lafiya wani abun nayi, ko wani ne ya ɓata maka rai a waje?”
“Ba wanda ya ɓata mun rai, dan Allah ki rabu dani banason surutu”
Yana faɗar haka saiya koma kan gado yayi kwanciyarshi.
Banfa daddaraba na juye ruwan wankan dana sabar mishi na kai mishi banɗaki.
Yaya Hamma na kai maka ruwan wankan” Ba sai ya kawo mun mari ba, nayi maza na kauce ya mari iska. Ai sai hawaye shar_shar_shar.”
Sai ya shiga faɗa yana zage_zage ni bana sanin ma abinda yake cewa. Wallahi Allah ana cikin haka sai firit Hama ta shigo itace harda zama a bakin gadona.
“Menene nake jiyo hayaniyarka, wani abunne?” Ai saina zama ƴar kallo suka zame mun sinima su kuma.
Sai ya shiga jero mata bayani, wai daga shigowarshi na ɓata mishi rai, kuma yace in rabu dashi saida na sake yi mishi magana”.
Uwar kusasu ta samu abinda take so. Saita shiga rarrashinshi, kunga har ƙirjinshi take shafawa. Bantaɓa sanin haka kishi yake da zafi ba sai yau. Dan har wani duhu_duhu nake gani, ji nake kamar in dira a wuyan matsiyaciya. Sai idanu na runtse wata gobara na ruruwa a zuchiyata. Tunda na runtse idanuna inaga tun tara da rabi, bani na buɗe ba sai goma da minti goma,minti arba’in tim nayi. Wannan rufe idanun da nayi Allah kawai nake ambato dan nasan shi kaɗaine zai kawo mun agaji, har ita alkinkimar ta fita ni banma sani ba.
Shiko Yaya Hamma yayi bacci abinshi harda minshari, niko ina zaune ga kayan abinci a gabana inata tubka da warwara, amman na kasa gane dalilin fishin daya zama sababin wannan tashin hankalin.
A zaune a wajen bacci yayi gaba dani. Cikin dare na tashi naita adda’a ina roƙon rabbissama wati war ardi ya kawo mun ɗauki na shiga tsaka mai wuya. Ina zaune ina salatin Annabi har aka kira assalatu. Abinda yafi bani mamaki har ana niyyar shiga sallah Yaya Hamma baiko motsa ba. Abinda bai taɓa yi ba, ana kiran assatu yake miƙewa.
Yaya Hamma, Yaya Hamma lokacin sallah yayi za’a shiga Masallaci “
Hmm kunsan daya tashi a zabure me yace dani? Abun da ciwo cewa yayi.
“Ke mahaukaciyar inace, haka a gidanku aka koya miki tashin miji marar tarbiyya” Haka fa yace mun
Ita zuchiya bata da ƙashi, raina ya ɓaci idanuna sun rufe sai nace.
Ni ina da tarbiyya Allah dai ya baka haƙuri naga zuchiyarka a kusa take, ko lefin me nayi oh….”
Ba sai jini ba, a ina?
Naushi ya kaimun a bakina, zafin ya ratsani kau. Kafin in tare naji yana dukana takota ina ya samu tsoka. Niko bakina na toshe da hannayena bibiyu ina gudun kar kishiya ta jiyo ihun ana jibgarka taji dadi. Saida ya dokeni iya iyawarshi ya fice.
Saina durƙushe na saki kuka marar sauti. Idona a kumbure, guda ɗaya, dishi_dishi nake gani dashi, dan mugun naushi Yaya Hamma yaima idon. bakina na ma haka, jikina yayi laushi, gashi zuchiyata tana cikin ƙunci.
Yau nice miji yasa hannu yaimun shegen duka haka? Babu komai akwai Allah”
Hawayena na share, na ɗauki mayafina daya faɗi garin duka na yafa na fito hannuna ɗauke da tiran abincin jiya da daddare. Ina fitowa naga gilmawar Hama ta fice a guje daga lungunmu, nayi imani laɓe tayi mun. Ba yau bane kaɗai ba, ina zarginta sai dai yau ta tabbatar mun da zargin.
Ko a zuchiyata na tuna Hama ita ta shiga ta fita tayi asirin farraƙani da Yaya Hamma. Amman sai nayi saurin tuba bisa furucina. Ba mai yi sai Allah.
Hawayen daya cicciko a idona na mayar da dabara na fito tsakar gidan gabana na faɗuwa. Sai nake jin inama ƙasa ta tsage in faɗa da wannan abun kunya.
Aiko da Hama na soma cin karo ta kafa ta tsare.
Banko bi ta kanta ba, na dai jiyo tana waƙar fulani. Ni dai ta kaina nake yi, wani irin mugun sarawa kaina yakeyi, idona inaji kamar zai zazzago. Ina hura wuta Baɗɗo ta shigo. Tana kallona ta riƙe mun hannu. Sai hawaye shar_shar a idanunta. Cikin jarumta nace.
Ki dena kuka babu komai Baɗɗo. Bari in gama dumamennan ki sameni a bayan layi sai muyi magana.” Tukunyar tuwon dana yayyanka na ɗaura, ɗaya gefen na ɗaura miyar. To ni a gaskiya inna ɗaura abinci a wuta bana ko motsawa ina zaune har saina raba. Dan gudun kar a cutar dani, irin magungunan da Hama take sassakamun yayi yawa.
Saida na raba dumamen matan gida suka soma shigowa. Da suka ga yadda halittata ta sauya, sai wannan ta kalli wannan, wannan ta kalli waccan. Haka kuma ina jiyota da Yaya Hamma a tsakar gida sai dariya takeyi. Ni dai na gama abinda zanyi na ɗakko namu abincin na fito. Amman me Yaya Hamma harya fice abunshi. Na gyaɗa kai tare da haɗiye yawu mai ciwo.
Koda na shiga saina sau kuka kawai. Ina cikin rera kukannan sai ga Baɗɗo da Amaduyal a guje sun shigo”
“Adda Adda shanu sunata mutuwa kizo ki gani”
A guje ni dasu muka fita. Allahu Akbar lallai an sabautani dan duk manyan shanun sun faɗi sun mutu sai kumfa ke fita a bakunansu da halama wata gubar aka saka musu. Ragowar ƴan madaidaitan da basu ƙarasa mutuwa ba Amaduyal yasa kansu gabas ya yanke. Matan gida dana maƙota duk suka cika gidan tam anata tayani jaje, ga gulmar ganin bakina da idanuna da suke ta tayi. Ana cikin haka saiga Yafendo ta kutso ta iso. Ga shanaye a kwance riɗa_riɗa sun mutu shanaye masu tsada ƙosassu.
“Ko wani abun suka ci a wajen kiwo Amaduyal? Wannan lamarin da girma yake, shanu manya haka?
Maza je ka kirawo Baffanku”
Da sauri Amaduyal ya fita, Yafendo tana kalloni taga a halin da nake. Sai ta dafani”
“Jabu me ya samu idanki duk ya kaɗe jini ya taru, ga bakinki a fashe?”
Munafurci irinna matan ƙauye duk sai su kayi tsit suna jiran amsata.
Faduwa nayi a banɗaki na taka sabulu” Hama najin haka ta saki murmushin da karaf a idona tayi wucewarta. Hannuna Yafendo ta ja izuwa ɗakinta ta zaunar dani a gado.
“Kuna faɗa da wannan yaron ne Jabu, ki sanar dani gaskiya dan ina lure da abinda yake faruwa a gidan. Bana son in yi managane dan kar aka dan ku yaran yata ne ina tare muku. Hamma ne ya bigeki?”
Hawaye ya zubo mun shar_shar ga raɗaɗin jiki, ga raɗaɗin zuchiya, ga raɗaɗin abinda ya faru da dabbobina nayi asarar dukiya mai yawa. Amman nayi tawakkali ina fatan Allah yasa wata musibace da zata sauka a kaina ta sauka a kan dabbobin.
E Yafendo shi ya dakeni” Salati ta soma tana tattafa hannayenta.
“Wannan yaron ne ya dokeki, yaushe ya zama lusari ni ban sani ba, a kanki dukan zai soma? Nasan wannan baya rasa nasaba da Hama nayi imanin tana da sa hannu akan wannan dukan, da mutuwar shanunnan naki. Bafa komai bane face baƙin ciki. Abinda dai nake so dake shine kiyi haƙuri kinji am? Ki zama mace mai juriya da ɓoye sirrinta. Hamma wankine, kuma nasan yana matuƙar sonki fiye da Hama. Itama kuma tasan haka ba zata barki ki zauna lafiya ba. Jabu kishi da fulatanar daji ba sauƙi. Da zan baki labarin irin wahalar da mahaifiyarki da Ai’i Yafendonku suka sha a hannun kishiya da zukatanku sai sun fashe. Ki duba irin yadda su Yusufu suke a ɗofane su da gidan ubansu duk sabida sharrin kishiya. Mai Nagge yaso Daso sosai mu munfi kyautata zaton asiri kishiyarta tayi ta farraƙa tsakaninsu, inaga irin asirin da Hama tayi a tsakaninki da wannan yaron kenan tunda har wannan yaron ya iya cire hannu ya dokeki.” Fasali ta ja. Ni kuma tuni ƙwaƙwalwata ta lula tunanin kenan nima haka zan rayu irin rayuwar da Dada tayi a gidan mai nagge, yarana suma haka zasu kasance kamar yadda su Yusufu suke kenan, ciwon zuchiya da hawan jinine zai yi ajalina daga ƙarshe, koma Hama ce zata kasheni ta huta? Ya Allah ga baiwarka bata da kowa bata da komai. Allah kaine gatana ya Allah ka karkato mun da hankalin mijina ya dawo zuwa gareni muci gaba da shimfiɗa rayuwa kyakkyawa mai albarka. Maganar Yafendo ce ya dawo dani cikin hankalina.
“Amman mai haƙuri shi ke dafa dutse har yasha romonshi. Na haɗaki da Allah kar neman mafita ko tudun dafawa ya kaiki ga bin malaman tsubbu Jabu. Ki dogara da Allah, zan dage in tayaki da adda’a. Bana son wannan maganar dukan da canjin Hamma ya je kunnen Adda Daso. Itama Baɗɗo da Amaduyal zan ja kunnensu.”
Muna cikin haka sai ga Baffa Musa ya shigo duk a ruɗe. Ɗankwalin kaina nayi maza na cire saina yafa kamar mayafi na rufe fuskata. Shi yama ɗauka kuka nake yi sai ya shiga rarrashina.
“Tashi jeki Jabu” Cewar Yafendo.
A hankali na fice na koma ɗakina, daɓas na shirgu a kujera saida ta yi ƙara tsabar ƙiba.
Tunani na shiga yi. Kaddarata ta wannan karon ta muguwar kishiyace, jahilar kishiyar da ko alwala ba daidai take yi ba. Na tsallake siraɗin uwar miji da ƙyar, na sake faɗowa tarkon kishiya.
Idanuna da nake ji kamar zasu faɗi na lumshe wasu hawaye masu zafi suka zubo, ina tuno sanda Yaya Hamma ya dunƙule hannu ya naushi idona, wanda hawayen daya tarwatse a cikin idon ni na ɗauke tsiyayewa idanun ma yayi. Tun ina jiyo hayaniyar matan gidan har na dena jiyosu, Baɗɗo dai yau bata je tallenba ɗan uwa abun wuya. Ita taimun duk aikina hatta abincin rana ita ta dafa mun ta raba, jikina ko ina ciwo yake yi, ciwon bayan dana kwaso a bautar gidan larabawa shima ya tashi sosai bayan har tururi yake yi mini. Zuwa yamma lis Amaduyal ya kawo mun kuɗin shanun daya yanka an siyar. Na buɗe adaka na ɗebo kuɗi masu yawa.
Ka riƙe ka ba Baffa Musa a hannunshi a siyo wasu shanun. Ka ɗauresu a gida kawai a hakan. Wannan ragunan da kajin ka kaɗasu ka mayar dasu gida”
Shiru Amaduyal yayi da kuɗaɗe a hannunshi yayi jimm
“Adda wannan kuɗin ba kuɗin da kike juya kasuwanci bane, kuma naga kayan sun ƙare anata nema. In aka siyo shanun ke da wanne kuɗin zaki juya?” Murmushi nayi mishi.
Babu komai akwai ragowar kuɗaɗe a hannuna. Uwani zata cikace mun zan saro kaya kar ka damu, a soma kashe wannan wutar tukunna” Kai ya gyaɗa kawai, har zaice wani abun sai kuma ya fasa, abincin Dada na bashi ya kai mata. Na koma na kwanta Baɗɗo kuma na sallar la’asar ina kallon abun mamaki dan ba daidai take yin Allah ba.
Baɗɗo ba daidai kike sallah ba subhanallaah. Ki shirya da zaran na warke dake da su Cubu zan kafa muku makarantar dare zan koyar daku ɗan iya abinda na sani game da addini, kuma mu dinga karatun Qur’ani”
Jikinta a mace mutus ta amsani da to. Ita tayi girkin dare ta raba ta fitar dana kowa, hatta ruwan wanka ita ta kaimun jiki yaƙi daɗi.
Ina zaune na gama kai kukana ga Allah sai na jiyo sallamar Yaya Hamma. Ba shiri na miƙe tsaye ina mishi sannu da zuwa, banza yayi mun ya nemi waje ya zauna.
Ina wuni barka da dawowa Yaya Hamma” Na durƙusa har ƙasa da ƙyar gani dama ba kaɗan ba. Hanci naga ya toshe naci wani ciwo a zuchiyata.
“Jabu ɓera ne ya mutu a ɗakinne?’ Yayi maganar da zafi.
A’a wari ɗakin yake yi ne?” Na bashi amsa a taƙaice tare da mikewa na zauna a gefenshi.
Kamar na soka mishi allura a takashinshi haka ya miƙe tsaye yana matsawa baya harya fita daga ɗakin.
“Bazan iya zama a cikin wannan warin ba. Kema kije ɗakin Dada ki kwanta gobe ki duba abinda yake warin”
Labulen ɗakin ya saki, sai naji kamar zuchiyata ta rushe dan bala’i. Kwanana ya miƙa ma Hama inaji ina gani. Kishi zai yi ajalina, duk da a cikin fishi da taka tsantsan nake dashi, amman duk bala’i gara ya zauna a ɗakin, ni na gwammaci ya kuma dukana daya kai kwanana ɗakin kishiya taga wallena. Baza ku gane ba nasan, wannan kishin da jiin zafin ya shafi mai kishiyane kaɗai, da waɗanda suke cikin takalmana ma’ana da matan da aka taɓa yima fin ƙarfin kwana suna ji suna gani. Tuttura tuwon da Baɗɗo tayi na dingayi na danne tuwon da madarar shanu, na haɗiyi fanado dama ina dashi da rana ma na haɗiya sanda Baɗɗo ta damamun fura.
Duk ciwon da nake ji, da ƙagewar da bayana yake yi, a wannan daren saida na hautsine ɗakinnan na birkitashi. Illahirin ɗakin banga komai ba, ni ƙamshi ma nake ji a ɗakin dan ni ma’abociyar ta’amali da turarukane mada’in ƙasashe daban_daban. Duk iya bincikena dana binciko banga komai ba. Na kwanta ina nishi gami da tunanin to me ke faruwa kenan, ko dai tsabar Yaya Hamma yana son tozartanine yasa ya tsiro da zancan warinnan? Ni dai kwana nayi cur ina tubkewa in warware abuna, abin duniya yabi ya dameni ga idanu ya matsamun lamba abinda yafi komai tayar mun da hankali shine kafin gari ya waye ba sai idona me ciwon naga kamar ya dena gani ba? Sai insa hannu in doɗe mai lafiyar, shi marar lafiyan kuma yana buɗe sai duhu da ɗan ƙyallin tocila kaɗan nake gani
Innalillahiwa’innailaihilrajiun na dinga ambatawa. Tada kabbarar Sallah nayi ina sallah ina hawaye ga wata ƙaddara kuma ta kuma samuna.
Washegari
A gurguje na sake kayan jikina, na buɗe adaka na ciro kuɗi na cusa a jaka na fito.
Hama na ƙofar ɗakinta tana kwashe Manshanun data gama burgawa yanzu na iso. Baddo ma na ƙofar ɗakinta tana aikin burga.
Hama dan Allah inaso kiyi mun magana da Yaya Hamma ne?”
“Dan jaraba da wannan duku_dukun zaki zo neman min miji. To baya nan bai shigo gidan ba”
Kafin in ja numfashi in saki sai gashi ya iso inda muke.
Yana isowa ya toshe hancinshi yana ƙoƙarin shigewa ciki.
Dan Allah inaso zanje asibiti Yaya Hamma”
“Sai kin dawo” Ya bani amsa a taƙaice.
Hama na kalla, na kuma kallonta da kyau nace.
In kinfi ƙarfina baki fi ƙarfin Allah ba.
Baddo yima Yuguda magana zaki rakani asibiti”
Hama ta cokaro ɗaurinta gaba bata ce dani komai ba. Baddo ta bar abinda take yi ta shiga ɗaki, bata jima ba ta fito goye da diyarta. Ɗakin Yafendo muka je na sanar mata abinda ake ciki. Nera dubu biyu ta miƙo mun.
“Ungo ku riƙe a hannunku, Allah ya ƙara sauƙi bazan hanaki zuwa asibitiba a birni kika rayu shiyasa, amman babu irin maganin da babu a gargajiya. Nima zan fita da hantsi inje in karɓo miki maganin idon, da tofi”
Kudin Baɗɗo ta karɓa mu ka yi mata Sallama.
Baɗɗo kina jin wari a jikina dan Allah?” Hawayen daya zubo mata sanadin tambayar dana yi mata ta share.
“A’a Adda. Ina tunanin asirin warin jaɓa Hama tayi miki dan ta rabaki da mijinki. Jiya muna tsakar gida muna hira ai ya baro ɗakinki yazo ɗakinta. Shine take tambayarshi me yazo yi ai ba kwananta bane. Shi kuma buɗar bakinshi yace warin jaɓa kike yi mishi, dake da ɗakin. Shine nake tunanin irin asirin da Lanti tayi ma kishiyarta kenan, ita kam baiwar Allahn mutuwa ma tayi daga ƙarshe. Sai da mijin ya shekara biyu tim baya shiga ɗakinta, baya cin abincinta, baya ko kallon inda take. Wannan baƙin ciki shi yai sanadinta.
Ƙaƙa sara ƙaƙa kundai ji halin da Jabu Iyabo take ciki.
Ina mai ba masoya wannan littafin haƙuri domin ba zaku jini ba kwana biyu ciwon idanu ya matsamun lamba, gashi bani da lafiya ma duk ni kaɗai na yauma dauriyace kawai.
Kuy mun haƙuri da zaran na warware zaku jini in sha Allah.
Masu promo kui ma Anty Zee magana.
Waɗanda ba ƴan kano bane akwai number wayoyinku a jikin kayan za’akai muku tasha in sha Allah. Nagode sosai sai kun jini.
Ƴan nijar da mutan Saudiyya ina godiya sosai.
MRS BUKHARI
Part 7
NAMA YA DAHU…
ROMO ƊANYE
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
LITTAFI NA UKU (7)
Maraɗi.
Gwadabe:.
Dariya yayi ma Hadiza ya kalleta yace.
“Hadiza duniya, fitinarki yawa, kin iya tada zaune tsaye. Ayi magana kice anci miki fuska.”
Haɗe rai tayi tace.
“Wai ni kam tsohuwar matarnan taka dame tafi sauran matane, da har yanzu ka kasa daidaita sonta da namu? Ƙila ma ta mance dakai ita sam a rayuwarta tana tare da mijinta ya kankare ka a zuchiyarta da ƙwaƙwalwarta”
Haɗe rai yayi ƴar fara’ar da yake take ta tsaya. Dama tayi ne dan ta kunna mishi wutar kishi, ko babu komai ranta sai yayi fes.
Washe gari Gwadabe ya bata kudi ta shiga kasuwa tayo ma ƴan takai tsaraba, har turamen atampa ya bata ta siyo mishi, da kayan yara na yaran Bara’u, da yaran Tamu. Baba Fhatsima itama ta haɗa musu nata tsarabar, ɗan kayan kwance Anti Badi’a ta tarkata tace a kaima Sakina. Malam da daddare yasa akai mishi kiran Gwadabe ya sameshi a turakarshi dashi da matanshi duka anata shari’a Sabitu ya daki matarshi har tayi yaji. Shigowarshi yasa Malam sallamar kowa sai Baba Fhatsima da take dashi ranar.
“Gwadabe naji a bakin Gyatumarku kunason zuwa Takai ko?”
“E Malam gobe in Allah ya kaimu zamu tafi harna yankar mana tikiti.” Malam yayi jim.
“Toh Gwadabe bazan hanaka shiga Takai ba ko dan Bara’u da matarshi su kaɗai sun isa ayi tattaki akai musu ziyara. Amman akwai abinda na ɓoye maka. Ga Fhatsima ita tasan komai Jamilu da yayi mun rakiya shima yasan komai. Babala tace Allah ya isanta nononta daka sha in har ka shigo Takai ka shiga gidannan. Sannan ta yanke halaƙarka da ƴan uwanka Allah ya isanta in ka je musu gida. Babu abinda bata faɗa ba. Dan haka sai ka guje ma Allah ya isanta kar ka kuskura ka shiga cikin gidanku. Hadiza da Shafa zasu iya shiga su nuna mata yara in Allah ya bata ikon ganinsu to, in suma ta korosu sai a haɗu duk ayi haƙuri. Iyatu da Hambali ke zuga uwarku akanka nayi iya tunani da hangen nesa namu na manya mahaifiyarku tana da son abin duniya, shi yasa take ɗaukar duk maganganun da Hambali ya ɗaurata akai. Da ace Allah zai ɗaga darajarka a duniya ka samu arziki zaka sha mamakin yadda komai zai wuce kamar bai faru ba. Gwadabe ka daɗa haƙuri kaji ko?”
Kan Gwadabe ya ɗaure, amman baiyi mamaki ba. Murmushi yayi ma Malam kawai yace babu komai ya gode, kuma zai kiyaye in sha Allah zaiyi yadda take so ɗin.
Washe gari asubar fari motarsu ta ɗaga sai Kano.
Tafiya mabudin ilimi sun fito shiddan asuba basu suka shiga Kano ba sai shidda na yamma. Gwadabe na sauke ƙafarki a garin Kano yanayinshi gabaki ɗaya saiya canja, tunaninshi ya sauya, yana hasko irin rayuwar da suka gudanar shi da IYABO a garin Kano. Har Hadiza ta soma zargi kunsan bakinta baya haila cewa dashi tayi.
“Hala tunanin tsohuwar matarnan taka kake yi. Naga duk ka sauya?” Baiko kalleta ba ya soma nema musu motar da zata shiga Takai. Sun ko taki sa’a motar akwai wajen mutum ɗaya daga ita kuma mota ba zata sake barin tashar ba sai gobe. A haka suka shiga Gwadabe ya zauna a injin shi.
Wajajen tara da ɗoriya sai gasu a Takai abuka da ƙauye garin a cike yake dam da matasa gungu_gungu, da magidanta a ƙofar gida wasu na hira wasu rediyo suke saurare, ga yara ratata a waje sunata wasansu cikin kwanciyar hankali.
Suna tafe zuwa gidan Bara’u da kici_kicin kayansu suka zo wucewa daidai ƙofar gidansu. Gabanshi ya yanke ya faɗi ras. Yau shine zai wuce gidan da aka haifeshi yayi rarrafe da wasan kasa a cikinshi, gidan da a ciki aka birne mahaifarsa. Wasu siraran hawayene suka gangaro mishi ya wuce gidan da sauri. Hadiza dai sai jejjefa kafarta take yi, babu wuta garin yayi duɗum dashi. Gaba da gidansu kaɗan anan majalisar abokan gwadabe take abokai irin na wasan kasa. Ai kuwa ilai Bara’u na wajen anata fafata musun da suka saba.
“Sannunku sarakan musun tsiya” Cewar Gwadabe, da fara’arshi dan ganin tsoffin abokanshi. Nan suka soma sowa da hargowar murna. Bara’u yace.
“Hadiza barka da shigowa Takai ta kawo ta saba da saukar baƙi.” Murmushi tayi aka gaggaisa.
Gwadabe ya gabatar da’ita ga abokanshi. Suka sake gaisawa da’ita.
“To bari mu karasa inna ajjiyeta zan fito muyi hirar yaushe gamo.” Ila yace.
“Akwai babban labarin abokinku kai da Bara’u Zilƙifulu.” Baki Gwadabe ya buɗe yace.
“Zilƙi fa kace, ya dawo daga yawon duniyar kenan? Shegen kaya bari in fito gaskiya a darennan ma ni sai naga Zilƙi”
Bara’u ya tayashi ɗaukar kayan shi da Ila, Ila iyakarshi dai zaure. Sakina da yara suna tsakar gida zafi kamar zai kashesu suka jiyo sallamar baƙi. Suna shigowa Sakina ta riƙe baki.
“Ah_a_a_a manyan baƙi mutanen nijar. Hadiza maraba lale. Gaskiya Bara’u muna da manyan baƙi yau”
Sakina tayi maza ta kunto Ummi daga bayan Hadiza.
“Ga tabarma Hadiza zauna dan ɗakin baya shuguwa, kun shigo lokacin zafi sai sanƙarau aketa yi da kwalara.” Zazzaunawa suka yi, nan aka shiga gaisuwa yaran kuma duk suka ruƙunƙume Gwadabe suna ga Baba ga Baba.
“Shafa anan gidan ta wuni yau cur. Abba yayi wayau sosai, danma ƙurajen zafi duk sun fesuo musu har uwar wallahi” Cewar Bara’u. Ita kuwa Sakina tana kitchen taje hado abinci, Ummi tana hannun Bara’u”
“Sakina ki bar tuwonki. Bari inje wajen Nalanjin in karɓo musu gashasshiyar zabuwa suci su more” Da dariya Sakina ta fito
“Kaga Shinkaface da miya yau muka dafa ba tuwo ba sabida Shafa.” Bara’u yayi Dariya yace.
“Kice yau Toye ya cika cikinshi har ya gaji?” Itama dariya tayi tace.
“Ɗan jakar uba ba. Gwadabe Toye baya son tuwon masara sam yaronnan. Dana zubo tuwo sai ya kama kuka harda birgima fa” Dariya suka fashe dashi. Gwadabe yayi ma Toye yarbanci, kafin yace da Sakina.
“Dake bamu fiye yin tuwon masaraba sai Amala, ko sakwara, ko tuwon farin albo shiyasa bai saba da tuwon masarar ba”
. Bara’u yace.
“Allah sarki tsuntsun soyayya. Ni ko Gwadabe kana jin labarin Iyabo kuwa? Ya kamata ko ba komai ayi zumunci bai kamata muyi fatali da Iyabo ba baiwar Allah guda da bari.” A_ido_a_ido Gwadabe ya kalli Hadiza, saida ta kasa jurewa ta sauya fuska. Sakina tace.
“Ko da suka shigo cikin gidannan sai da Iyabon ta fado mun. Ban dakko zancan bane sabida kar Hadiza taji babu daɗi”
“Hakane kuma uwargida a gafarcemu, ai yanzu kambun sarautar a hannunki yake. Gwadabe tawo muje mu siyo mata gashasshiyar zabuwa”
Ficewa suka yi nan suka bar Hadiza da dariyar yake ta ciki na ciki.
GWADABE
“Gwadabe Yaya Hambali ya zama babban mai kuɗi, yana ɗaya daga cikin manyan masu kuɗinmu na Takai. Da azuminnan daya wuce, yayi rabon abinci na ban mamaki. Sunje sun sauke farali har su Fodiyo ya biyama. Kai kaga inya shigo Takai yadda ƙofar gidanku yake cika kuwa? Hmm abun ba’a cewa komai. Babala kuwa tana dai shigowa Takai duk wata tayi sati guda ta koma Kano. Hambali ya ɗauketa kacokan daga Takai, kuma kasan Hambali ya auri Laila kuwa?” Gwadabe da bakinshi yake buɗe dan mamaki, ai saiya sake buɗe bakinshi.
“Ya auri Laila fa kace, ita auren nata kuma mutuwa yayi ne?”
“Mutuwa kai. Laila ai a kotu ma alƙali ya raba auren. Gagarumar sata taima mijin na akwatin kuɗi guda. Taita facaka da dukiyarshi shi bai sani ba, lokacin fa Laila ta shigo gari. To su Yaya Hambali ne suka tsaya mata lokacin ana kes ɗin, duk zaman kotun bai wuce ni ba. To bayan Yaya Hambali ya biya shi mijin kuɗin da Lailan ta sace, sai suka nemi a raba auren kawai.
To kai kasan Baba Iyatu idonta idon kuɗi nan taita naci da kuke kuken dole a cikin yaran Babala a samu ɗaya ya auri Laila ko dan a rufa mata asiri. Shine Hambali ya daki ƙirji ya aureta. Kai kaga bikin da muka sha a ƙauyannan? Ba’a taɓa yin biki irin nasu ba ni dai a iya tasowata” Kai Gwadabe yaita jijjigawa har suka siyo zabuwa suka juyo, Gwadabe ya kasa cewa komai dan mamakin abubbuwan, da mamakin yadda ya zam bare a cikin ƴan uwanshi cikin ummanshi.
“Kaji labarin Zilƙi a wajen Ila ko?” Ajjiyar zuchiya ya sauke, Bara’u ya lura Gwadabe ya lula duniyar tunanin yadda dangi sukai watsin ruwan tsarki dashi, shi yasa ya kawar mai da tunani da zancan Zilƙi.
“Wai ashe Zilƙi zai dawo ƙauyannan? Nifa na ɗauka ya manta da kowa” Dariya Bara’u yayi yace.
“Sai gashi ya dawo abinshi. Kuma kasan abin mamakin? Shine charman na nan Takai. siyasa ya faɗa ka’in da na’in kasan Charman ɗinmu daya sauka na nan Takai abokinshi ne, shima dake saida shima ya je ya gama yawon duniyarshi ya dawo ya faɗa siyasa. To wallahi shi ya tsaya ma Zilƙi akaita shige da fice, dani akaita yawon kanfen waje_ waje har dai Allah ya karɓa mishi ya zama Charman” Dariya da mamaki Gwadabe yayi ya buɗe baki yana murna.
“Charman Zulƙin? Iko sai Allah, Allah mai yin yadda yaso da bawa. Gobe zaka kaini gidanshi an daɗe ba’a haɗuba.”
“Ai kuwa shima sai tambayarka yake yi tun ma ana kan gangar siyasar. Kaci sa’a jiya ya dawo daga Abuja yaje taron wani semina. Gobe da sassafe zamu dirar mishi mu karya a tabkeken falonshi. Dariya du su biyun suka yi.
“Ya batun nomar bana Bara’u?”
“Asara kawai Gwadabe, Takai wannan karon anyi asarar dukiya noman bana babu yabanya me kyau sai dai godiyar Allah musamman mu masu noman gyaɗa har ɗan dama dama masu noman maiwa. Ya taka sana’ar maganin ka ce mun dai ka soma zuwa cin kasuwar ƙauyuka ya yanayin kasuwar to?”
Sai da Gwadabe ya jajanta ma Bara’u kafin yace.
“Kasuwa Bara’u babu abinda zance sai hamdala wallahi. Duk kasuwar ƙauyan dana ziyarta dana baza magani na soma yehuwa zaka ga an lulluɓeni. Bara’u fatana shine Allah ya bar abokarmu har yaranmu su gajeta. Ɗazu kayi maganar Iyabo, tunda muka rabu ban sake sa Iyabo a idanuna ba gaskiya. Amman in sha Allah inna shiga Kano ko a tasha ne zan ajjiyesu in nemi gidan Uwani. Ko kuma in barsu a nan Takai ka rakani mu nemi Uwani inji labarin Iyabo. Ko gidan naje mutuncina zasu ci har gaban abada ƴan uwanta ba zasu ƙaunaceni ba” Bara’u yayi murmushi yace.
“Baiwar Allah mai wuyar wucewa. Muma muka kasa mance halacci da Alkhairan Iyabo balle kai da dominka muka santa. Abinda za’ayi shine in ka huta zamu shiga mu nemo duk inda Uwani Tabalbalin take muji labarin Iyabo, mu ajjiye mata saƙon gaisuwa. Zancan abota Gwadabe tunda zamu haɗa yaranmu aure ai zumunci zai ɗore, fatana Allah yasa kar silar auren zumuncin namu ya samu tangarɗa.” Haka dai hirar wannan abokai ko Aminai yaƙi ƙarewa, gida suka shiga suka kai musu naman da suka siyo Hadiza da Sakina sai hirarsu suke gwanin sha’awa. Su kuma suka ɗauki abincinsu suka fita dashi waje yara suka kawo musu tabarma da fululluka dan a ƙwar gidan zasu kwana.
Washe gari.
Da safe Gwadabe yasa Hadiza ta cicciro tsarabobin da yayi ya cire na Sakina da yara, ya cire na Bara’u. Na gidansu Shafa ma ya cire ya ajjiye a gefe.
“Wannan in Sakina zata kaiki gidansu Shafa sai ki tafi musu dashi ko, wannan kuma na gidanmu ne”
“Dama nice zanje ni da nazo garinsu? Aina ɗauka itace zata zo ko?” Ƙur yayi mata da’idanu su biyu ne a ɗakin ta gamama Ummi wanka kenan tana mata nabkin.
“Kiyi abinda nace miki a matsayina na mijinki. In kuma ban isaba to sai ki zauna. Kar Sakina ta kaiki gidanmu tukunna dan su Babala basa nan.” Baki ta zunɓuro tace.
“Amman ai ita…..”
“Ya’isa haka Hadiza. In baki bi umarnina ba zan saɓa miki mai taurin kan tsiya marar jin magana baki da aiki sai ƙorafi mtwssa
Yaja tsaki ya miƙe ya fice.
“Gwadabe munga tsaraba fa Allah yasa a mizani, Allah ya bar zumunci”
“Sakina kenan baki da dama. Bara’u muje ko?” Bara’u yace.
“To muje. Sakina gidan Zulƙi zan kai Gwadabe yaushe rabon da’a gana”
“Allah sarki, sai kun dawo kwa gaishesu. Muma da mun kammala zan zazzagaya da Hadiza duk gidan daya dace dai. Gida kuma Babala bata nan inta dawo wannan aikin naka ne banma isa na kai Hadiza wajen Babala ba”
Da haka sukai sallama zuwa gidan Zulƙi. A harabar tabkeken gidan nashi suka zauna a wasu fararen kujeru me gadi ya shiga sanar mishi da zuwan na Bara’u. Bara’u ba baƙon gidan bane an saba ganinshi hatta ƴan sandan dake tsare lafiyar Zulƙi sun sanshi.
“Rigiji gabji lallai Zulƙi yafa samu duniya ji gida ma malam, ji ma’aikata da masu tsaro, ga motoci har uku.”
“Bafa kaga komai ba Gwadabe bari dai mu shiga cikin falon ka gani”
Me gadine ya ƙaraso inda suke yace.
“Hajiyar gidan tace a muku iso zuwa falonshi. Bacci ya tashi yanzu wanka yake yi zai zo ya sameku inya fito”
Tiryan_tiryan suka bishi har zuwa masauƙin baƙinshi inda anan yake zantawa da baƙinshi irin masu unguwa, mai gari, da hakimai, da dakatai”
Masu aikin girki suka kawo kulolin abinci da filas na shan shayi da kofuna. Gwadabe sai karema falon kallo yake yi. Yana mamakin wai wannan gidan na Zulƙi ne” zamansu baifi da minti talatinba sai gashi ya shigo yana saye da shadda wagambari ɗinkin tazarce. Baki ya buɗe ya nuna Gwadabe da yatsanshi yace.
“Gwadabe yau kaine a gidana, to yaushe ma ka shigo garin?” Da sauri Gwadabe ya miƙe suka tafa da Zulƙi suna dariya gami da farin cikin ganin juna yaushe gamo.
“Ranka shi daɗe ashe rai kanga rai?” Zulƙi yayi dariya suka zazzauna yace.
“Bara’u kaji ɗan iska waini yake kira da ranka shidaɗe. Ni Gwadabe kaida kake tare mun faɗa nine ranka ya daɗen?” Dariya suka saka Bara’u yace.
“Ai Zulƙi ba zaka canja ba. Wai kai baka mantuwane dan Allah?”
“Ba komai ake mancewa ba Bara’u. Gwadabe ai mutumne harda ɓari kai ka sani da sauran abokanmu da muka taso tare. Gwadabe wanne aiki kake yi? Bara’u dai ya tsokatamun matanka biyu kuna zaune a nijar gidan Baba Magaji wan Babala” Gwadabe yace.
“Hakane matana biyu. Sana’a anata buga_buga inayin haƙon zinare. Ina tallar magungunan karfin maza na gargajiya dana bature. Kaga irinsu”
Gwadabe yasa hannu a ajjihu ya ɗauko wani ƙullin magani guda biyu, dana bature sacet ɗaya. Baki Zulƙi ya buɗe yace.
“Kusun uwa tafi da gidanka kenan. Gwadabe kaine ka zama mai siyar da maganin maza?” Sunfi minti koma sunata ƙyalƙyala dariya kamar waɗanda suka ga wawan zama. Gwadabe yace.
“Wannan in ka zuba a tuwo kaci yajinnan Zulƙi ko kakai shekara saba’in saika dawo ɗanyen jini a wannan ranar, da miyar yauƙi ake ci. Wannan kuma na baturene shayin maza ne. Ka juye a kofin shayinka ka shanye ranar ba’a magana. Gana dattin mara, amman shi yana sa gudawa sassafe kafin aci komai ake dafawa a shanye da tuƙarshi. Ka jarraba amfani dashi zaka samomun kostoma” Bil haƙƙi Gwadabe yake musu bayani. Su kuma sai kwashewa da dariya suke yi.
“Ikon Allah kenan. Gwadabe zan jarraba in naga kyanshi niko zan haɗaka da manyan mutane”
“Yauwa ni dama abinda nake son ji kenan. Ya batun iyali Zulƙi, kuma wai ina katafi yawon duniya ne?”
“Iyali sunanan an tara. Na jima da yin aure yaranmu shida da matar dana aura a bariki ƴar garin bayalsa ce, tana da yare. Sai bayan na hau kujerar mulki saina auri yarinyar ƙanwar Babarmu, sun matsa ni bama sonta nake yi ba, dan Jenifa ta taimakeni sosai a rayuwa. Can Bayalsa na yada zango. Dakone kwasar shara, kwata. Gwadabe babu sana’ar da bamba har Allah yasa na auri Jenifa to mahaifinta ɗan siyasane babba. A wajenshi na koyi harkar siyasa shi ya wanke mun kai yace ai zan iya komawa ƙauyanmu in shiga takarar chiyaman tunda ina da takaddar gama sakandare. Shine ƙashin bayana, Rabo kuma chiyaman daya sauka saiya tsayar dani na zama ɗan jam’iyyarsu kaji abu kamar wasa ko?” Kai duk sukaita jijjigawa, dan shima Bara’u yaune yake jin wannan labari” Gwadabe yace.
“Yaya kake fama da Jama’a amma?” Sakkowa yayi yace.
“A zuba abinci muna ci ina baku labarin wahalar dake cikin kujerar mulki.” Dariya su ka yi. Sunsan Zulƙi tun yana yaro da zaran rana ta take lokacin cin abinci yayi ake nemanshi a rasa.
Bara’u ya bude kular abincin ya juye masar dake ciki dukka a faranti, ya kwarara miyar masar akan masar ya yaryaɗa musu man shanu isasahe. Duk yayi muku komai suka tsoma hannu, saida Zulƙi ya kai noma biyar kyawawa kana yace.
“Kujerar mulki bata da daɗi Gwadabe sam. Hakkin al’ummar yankunku akanka kai shugaba ya rataya. Kowa jira yake kahau ya kawo maka buƙatarshi, kuma fa dole yake nufin wannan buƙatar ka biya mishi. Yanzu tafiyar da nayi akan yadda za’a samun hannu a takaddar tallafama manoma da taki ne. Satina fin nawa ina sunturi, masu ruwa da tsakin sunƙi sa hannun.” Ya dinga basu labaran yadda abubbuwan suke tafiya, da yadda haƙiƙanin siyasa take. Sunfa jima suna hira a wannan gida basu ankara ba suka soma jiyo kiran sallar azahar. A banɗakin falon su kai Alwala sun fito harabar gidan Zulƙi ya shiga ya kira yaranshi maza uku suka wuce masallacin dake manne a jikin gidan ta waje.
A cike masallacin yake sosai kundai san jama’armu basai an karashe ba. A cikin masallacin Sai ga ƙafa da kafaɗun Gwadabe manne dana Yaya Hambali. Duk su biyun basu lura da hakan ba har saida gwadabe ya kalli ƙafar ya gane wannan ai kafar Yaya Hambali ce. Da sauri ya ɗago ya kalleshi a lokacin har an yi kabbara. Idanu suka haɗa wani irin kallon tsana Hambali yake jefo ma Gwadabe idanunnan nashi cike dam da farin kwalli kamar yadda ya saba, a yanzu ma yafi rambaɗawa sabida ya samu wadata. hannu yasa ya jawo wani saurayi daga sahun gaba ya sashi a gurbinshi, shi ɗin ya koma sahun gaba. A sanyaye Gwadabe ya ɗaga hannu yace.
“Allahu Akbar” Jikinshi sai rawa yake yi dai, haka gabanshi yake ta faɗuwa har aka idar da sallar. Kallon saurayin dake kusa dashi yayi sai yaga Ashe Nazifi ne babban yaron yaya Hambalin. Sauke kai kawai Gwadabe yayi baya ma so ya kallesu zuchiyarshi ta idasa karyewa.
Shi dai yana gefe a zaune Zulƙi yanata gaggaisawa da jama’a. Ya jima sosai kafin ya samu kanshi ya ƙaraso inda su Bara’u suke jiranshi. Gwadabe yana ganin yadda Yaya Hambali yake ta girmama Zulƙi. Yayi ƙiba ya sake kyau na musamman, fatarshi ta murje shi da Zulƙi suka saje. A gaban idonshi suka fita shi da Nazifi.
“Kuyi haƙuri na barku. Haka muke fama da jama’a, kuma dole kabi dasu inba haka ba sai zagi da cin mutunci. Kuzo muje can gidansu Baba mu gaishesu*
Dunguma suka yi gidansu Zulƙi aka gaggaisa akai zumunci. To su dai a gidan suka rabu dashi akan sai Gwadabe ya kawo matanshi sun gaisa.
Suna tafe suna tattauna abinda ya faru a masallaci sai gasu a ƙofar gidansu. Babala na daga ta cikin ƙofar gidan, Yaya Halima da Yaya Hambali suna daga ta waje. Gabaki ɗaya sai guiwowinshi suka sake ya tsaya cak shi bai jeba shi bai wuce ba. Kallon kallone ya shiga tsakaninshi da Babala na wasu sakanni. Ganin Babala ta ƙurama waje ɗaya idone yaja hankalinsu Hambali suka juya. Daidai lokacin da Bara’u yake jayeshi.
“Ka daure kayi ƙoƙarin cinye jarabawarka Gwadabe”
“Daya daure da kar ya daure duk ɗaya. Tsiniwace a kanshi ai inya tako mana gida. Tuni muka tsame matsiyaci a cikin zuriyarmu. Karka sake matanka ko wata banzar tsarabarka ta shigo gidannan. Dan naga Sakina na zagaye da iyalanka” Cewar Yaya Hambali kenan, cikin ihu da ɗaga murya yake maganar tashi. Kuka Gwadabe ya fashe dashi Bara’u ya jashi suka koma gida babu ma kowa a gidan a tsakar gida suka zauna jigum_jiugm sunata jimantawa juna. Har akayi kiran sallar la’asar babu wanda yace da wani uffan har suka fito daga masallaci. A gindin bishiyar mangwaro suka zauna akan kututture.
“Gwadabe kayi haƙuri ka ƙara. Uwa ba abun wasa bace, ka kiyayi Babala karka cuci kanka taima baki. Tunda bata son ganinka ni kam in dan ta mune karka sake kawo mana ziyararma wallahi mu mun yafe Gwadabe ka zauna zamu dinga zuwa duk ƙarshen shekara “
Gaga_gaga haka wunin ya kasance musu. Sai yamma suka samu shiga gidansu Shafa a tsakar gida suke a zube Abba sai kuka yake yi sabida zafi. Shafa tun rana take sa ran zuwan Gwadabe abincin rana ma data girka ma su Hadiza saida ta ɗebar mishi ta adana da taga har an ɗaura sanwar dare bai shigo bane ta cinye abincin.
Gaggaisawa akayo da matan gida, Shafa ta miƙo mishi Abba dake ta raraka kuka
“Kukan zafinne haka? Ga ƙuraje duk sun feso mishi, me kike shafa mishi to?” Gwadabe ya tambayi Shafa.
“Hodar moju nake barbaɗa mishi, bari in ɗakko a kuma shafa mishi” Ta tashi taje ta ɗakko hodar Gwadabe da kanshi ya shafe jikin yaron da hodar, baifi minti huɗu ba yayi baccinshi a jikin Baban. Matan gidan sai suka tashi suka koma zaure dan cikin ɗaki gaskiya baya shiguwa. Tuwo Shafa ta kawo musu suka taɓa dan sun san su Sakina ma suna can suna jiransu da abinci.
“Gwadabe dama ranar da muka zone saina shiga gida wajen Babala. To gaskiya abinda ya faru ya mugun ɗaure mun kai. Yadda Babala taci mutuncinmu, har Abba bata ƙyale ba dan ashe an faɗa mata sunan Baba yaci. Wai bata yafe ba da kasa sunan Baba.
“Ya’isa Shafa. Kuma kar in kuma jin bakinki akan wannan maganar.
To fa wata sabuwa su Babala manya.
MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI.
Part 8
NAMA YA DAHU…
ROMO ƊANYE
BADI’AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
LITTAFI NA UKU (8)
IYABO
Zuchiyata sai naji tana wani irin fusga. Labarin da Baɗɗo take bani ya jijjigani tsoro ya sake shigata sosai, ni dai har muka isa inda zamu hau acaɓa ya fitar damu jere bonyo bance komai ba. A lokacin kawai na riga da nayi saranda na yarda Hama ta ruguzamun rayuwata. Muna isowa jere muka soma cin karo da matan ƙauyanmu masu nono. Nan ƴan gulmammakinmu na mata ya soma tashi, har a bayan akori kura wata ƙawar Hama saida ta kasa haƙuri ta tambayi Baɗɗo.
“Baɗɗo hatsari yayarki tayi ne naga fuskarta a kumbure idonta ya tara jini baƙi ga bakinta a fashe?” Ɗagowa nayi na dubeta, na dawo da kallon nawa zuwa ga Baɗɗo.
“Zamewa tayi a bayan gida shine taji mummunan rauni asibiti ma zamu je”
“Asibiti a cikin ƙauyannan ana zuwa asibiti dama?”
Ni dai takaina nake yi, dan ni a lokacin wallahi ji nake kamar kaina zai faɗo, ga wasu jijiyoyi da suka ɗaɗɗaure a kaina sai nake jina wani iri haka. banma dawo hayyacina ba har saida naji motarmu ta kawo kan iyaka mun iso Girei.
Da ƙyar na sakko jiki duk ciwo, ko ina yayi tsami ga ciwon baya ya far mun. Mun jima a titi kafin muka samu bus ɗin da zata shiga gari. Wayata na zaro a jakata na kunna a lokacin rawar ɗari ma nake yi. Muna shigowa Adamawa kafin ma mu sauka na danna kiran wayar Uwani. Nako taki sa’a ringi biyu ta ɗauka.
“Kaga Amarya ƴar gaban goshi, shalelen Hamma, yau an fito birni kenan?” Idanuna na lumshe hawaye suka zubo mun da ƙyar na ɗan saisaita nutsuwata nace.
Uwani ki roƙi Hafizu dan Allah ya barki kizo. Wallahi ina cikin matsala, abubbuwa da yawa sun faru yanzu haka mun shigo garine Baɗɗo zata kaini asibiti, zaiyi wuya su sakeni in koma gida ma yau.” Sai na fashe mata da kuka duk na tashi hankalin Uwani.
“Shikenan Iyabo. Yanzu zan shiryo in tawo, zamu dinga waya har in iso. Kiyi haƙuri koma menene zanzo zamu samu mafita in sha Allah “
Wayar na datse ina share hawayena wasu na zubowa.
Ni hama zata sama wari a jiki, ta rabani da Hammana, to dama shi kishin haka yake, ko kuma a ƙauyen haka suke nasu kishin na azaba? Ya Allah ka ɗauke mun wannan lalurar warin da aka ɗauramun Allah ka bi mun kadina” Idanu na runtse zafin idon daya tara jini har tsaƙiyar kwanyata babu shiri na buɗe. Motarmu ta sauke mu a bakin tasha, acaɓa muka tare zuwa bakin asibiti. Muna bakin asibitin Uwani ta kirani motarsu ta baro kano.
Mu kuma muka shiga ciki, Baɗɗo ta zauna mun a layi ni kuma na buɗe fayil na yanki kati. Akwai layi bana wasaba haka mukaita bi. Saida wata mace tazo wucewa ta ganmu a layi ta dubi idona tace.
“Likitan idanu kuke son gani, dan naga idanunki suna ciwo sai ruwa kuma suke zubarwa?” Nace da’ita.
E likitan ido nazo gani”
“To ku biyoni, nan ba ɓangaren masu lalurar idanu bane. Kuzo muje” Haka duk uban layinnan da muka bi ya tashi a tutar babu. A baya mukaita binta har ɓangaren masu lalurar idanun. To mun kuma yi latti, da ƙyar wannan matar dai ta samu a layi dan taga idanun ya matsa mun. Mune har bayan azahar bamu shiga ɗakin ganin likita ba, sai wajajen uku saura aka kirayi sunana. Baddo na barma jakata da wayata na shiga ofishin likitan idon. Izinin zama ya bani, ya ɗago ya dubi idon da kyau kana yace.
“Me ya sameki, dukanki akayine, ko me ga idon yanata zubar da ruwa?”
Faɗuwa nayi a banɗaki shine na faɗi idona da bakina suka daki gini” Girgiza kai yayi yace.
“Ashsha, Allah ya kiyaye gaba. Ga gado zo ki kwanta inason duba lafiyar idanun”
Bayan na hau gadon sai yaga jikina na wani irin ɓari, ni kaina ɓarin da jikin nawa yake yi saiya tsoratani. Ba shiri ya taɓa jikina yayi wani irin mugun zafi, ni dai nasan inajin gadon dana kwanta yana juyi dani. Daga haka ban sake sanin abinda ke faruwa ba.
Ban sake samun kaina ba sai farkawa nayi naga ledar ƙarin ruwa a hannuna. Baɗɗo na zaune a ƙasa, Uwani na zaune a kan gadon da nake sun ƙura mun idanu.
“Ta farka Baɗɗo. maza jeki ki kirawo likita. Iyabo sannu yaya jikin?’
Uwani har kin iso ashe?” Da faɗar haka saita soma share hawaye, murmushi nayi nace.
Ki dena kuka, tawa jarabawar ta wannan auren kishiyace Uwani. Wai yau nice a gadon asibiti, namijin da nafi sonshi fiye da kowa shi ya dokeni, banda wari da matarshi ta saka mun. Jarabawar da girma Uwani. Amman akwai Allah “
Shiru Uwani tayi ta kasa cemun uffan. Niko wani tawakkaline naji ya shigeni ainun, lammurana suna ga Allah.
“Tun jiya muke asibitinnan Hamma baizo ba, matar tashi ma bata zo ba ko leƙe. Surukarki dai ta zo jiya sai wajajen magriba ma tabar asibitin. Dada kuma basu san halin da kike ciki ba,haka Baffa Musa, saidai Amaduyal ya sani. Kinga shi ya kawo mana abinci jiya, da safennanma shi ya kawo mana. Iyabo na tausaya miki. Amman wallahi kinsan Allah saina rama dukan da Hamma yayi miki a jikin figaggiyar matsiyaciyar matarshi?. Ƴar iska ke da zaki zage ki ci ubanshi ko da asiri da kin matseshi gobe bazai tunkaroki da duka ba. Jibi yadda ya nakasaki fa Iyabo . Taya zan tsaya wani ɗan ƙauye jahili yaimun irin wannan dukan, wallahi ko ya fi karfina da cizo, da yakushi saina kwaci kaina, in haɗa da hauka.”
Idanu na lumshe kafin in buɗe likita ya iso shi da Baɗɗo.
“Sannu Jabu. Yaya yanayin jikin naki kike jinshi?”
Ko ina ciwo yake yi mun. Kaina kuma yana matsanancin ciwo, ga wata jijiya da tai tsaye ta saman idon ciwo take yi mini”
“Ki nane idonki mai lafiyar marar lafiyar ki barshi a buɗe”
Umarninshi nabi, amman me koda na toshe idona mai lafiyar na bar marar lafiyar a buɗe dishi_dishi kawai nake gani”
“Kina iya tantance kalar kayan jikina?”
A’a gaskiya baƙi nake gani babu kala” Sai naji kuka na shirin kamani.
“To to Shikenan sake hannunki, ki biyoni zamu je ɗakin gwaji, domin musan a wanne mataki ciwon yake. Karin ruwan dake hannuna ya cire mun” Uwanice ta taimakamun na sakko akan gado.
“Baddo ki zauna ki jiramu, zan rakata” Cewar Uwani kenan. Tare da’ita muka shiga cikin ɗakin gwajin. Abubuwa mataki_mataki akaita bi. Har Abcd aka nuna mun a allo akace in karanta, in ban iya karatunba in ina ganinsu da kyau in sanar. Aka sakamun tabarau a idona, asa wannan a cire wannan, harda tocila saida aka haskamun idona likita sai tambayoyi kawai yake yi mun ina bashi amsa.
“To Shikenan zaku iya komawa. Ƙila zamu sallameta zuwa anjima ko kuma gobe da safe” Jijjunanmu a mace murus muka dawo ɗakin jinyar. Muka tarar da Yafendo ta zo.”
“Jabu sannu da jiki”
Yauwa Yafendo sannu da zuwa, ai da kin yi zamanki”
Na zauna akan gadon kaina a ƙasa.
“Ban isa in zauna ba, wallahi jiya ko baccin kirki ya kasa zuwarmun.” Uwani tace.
“Haura ki kwanta Iyabo sabida yanayin jiki”
Sai data taimaka mun na kwanta, suka gaisa da Yafendo, ta tambayesu yanayin jikin.
“To kusan dai zamu ce ido kam ya samu matsala, dan inuwa take gani dashi. Yanzu haka daga ɗakin gwaji muke. Sai dai muce Allah ya bata lafiya ya bata haƙuri dan matsalar idanu tana daga cikin manyan matsaloli kusan zamu iya kiranta mutuwar tsaye. Sannan fa Yafendo har yau Hamma ko matarshi babu wanda ya leƙo asibitinnan. Ni cewa nayi sun san Iyabo bata da lafiya kuwa?” Salati Yafendo ta saki tana tafa hannaye.
“Uwani kina nufin Hamma baizo ya duba jikin Jabu ba?” Uwani tayi ƴar dariya tace.
“Baizo ba wallahi, kinga dai tun jiya nake asibitinnan”
Shiru Yafendo tayi ta kasa cewa komai harna tsawon muntuna masu dama. Har wata ma’aikaciyar jinya tazo ta mayar mun da ƙarin ruwa, aka diga mun magani a idona. Har zuwa lokacin Yafendo bata ce komai ba.”
“Jabu, cuta ce an riga an cutar dake tunda kome za’ayi a matsayin ɗaukar fansa ba zai goge wannan lulurar data sameki ba.
Amman ki sani wannan yaron bashi da laifi yi mishi akayi. Ita kuma Hama zan ɗauki mummunan mataki a kanta matakin da hatta iyayenta bazai musu daɗi ba. Dan Allah kiyi haƙuri kuma a rufe wannan sirrin bana so Daso, da Baffa Musa, da su A’i suji. Mu haƙa daku mu burne. Shi kanshi Hamman a hakan zaiga fishina da ɓacin raina. Ina zuwa zanje wajen aikinsu in sameshi”
Nayi juyin duniya Yafendo ta bari karta je wajen aikin su Yaya Hamma, ko saurarena batai ba ta fice a cikin fishi tea Uwani ta haɗamun.
“Tashi ki sa wani abun a cikinki. Ai gara ki bari taje ɗin. Duk da ana zargin farraƙu akayi musu, baya nufin za’a zuba ido. Narantse da Allah idona idon Hama saina sabautata na nakasa wani shashe na jikinta in da daɗi sai taji” Baɗɗo tace.
“Koni ɗazu dana koma gida da safe saida mukai rikici sosai da’ita. Yuguda ne ya jayeni zuwa ɗaki naso in daketa ne, amman ban samu dama ba. Na barota a gidan ita da Daso tsohuwar munafuka, ita take kaita wajen bokaye tun kina Makka lokacin”
Ni dai ina zaune ina shan shayi, duk wacce tayi magana in kalleta. Sun ɗauka da zafi. Ni inata gwada musu abi komai a hankali abinda haƙuri bai bayar ba, tashin hankali bai isa ya bayar ba. Ina gama shan tean Uwani ta zubo mun jallof ɗin shinkafa mai bushasshen kifi. Loma biyu kawai na iya turawa na danne da ruwa. Ruwan hannuna na ƙarewa aka ciremun saina fita nayi alwala ina daga zaune a dadduma na soma rama sallolin da ake bina. Ban idar da sallar ba saiga Yaya Hamma Yafendo ta tasoshi gaba sunzo. Suka gaisa da Uwani ba yadda suka sababa, dan a daƙile yake magana, kuma ya cusa hancinshi a cikin rawanin daya naɗe kanshi dashi. Uwani kuwa sai harara take zabga mishi tana mai kallon wulaƙanci.
Ina sallamewa na ɗago na dubeshi, sai naga ya sake mun kyau. Shima idonshi yana kaina bai ɗauke ba.
“Sannu yaya jikin naki, ashe baki da lafiya?” Nan Yafendo ta shiga yi mishi faɗa da yare, sai ruwan faɗa take yi inaji tana ambaton Hama dai. Shuru yayi baice mata komai ba. Uwani da Baɗɗo sai haƙuri suke bayarwa, ni dashi munyi shiru muna kallon juna, ina hango tausayina a cikin ƙwayar idanunshi. A cikin kallon ƙudan da muke yima juna a zuchiyata ina roƙon Allah ya karya mugun asirin da Hama tayi mana domin mu samu zaman lafiya”
Ana cikin haka likita ya shigo da takaddar sallama ya miƙama Hamma. Jiki a mace ya fita. Likitan ya dawo da dubanshi gareni.
“Jabu mun sallameki. Amman duk bayan kwana talatin zaki ci gaba da zuwa muna duba lafiyar idanun naki. Zamu ɗauraki akan maganin ɗigawa safe, rana, dare. Sannan ki guji gasken rana, kuma karki dinga jagwalgwala idanun. In sha Allah karku saka damuwa a zuchiyoyinku idon zai warke, ba mutuwa yayi ba, matsalace kawai amman indai muka ɗaurata bisa magani zai farfaɗo da jijiyoyin idanun da suka sandare. Wannan taruwar jinin ita kuma ba wata matsala bane da sannu zai washe” Haka dai wannan likita yaita ƙarfafani da bani shawarwari.
Yaya Hamma yana dawowa daga biyan kuɗin sallama, ya miƙo ma Baɗɗo ledar magunguna, suka harhaɗa kaya muka fito. A mota ya ɗauramu ya biya kuɗin. Mu muka kama hanya, shi kuma ya koma bakin aikinshi.
Ga ciwo ga rashin kyan hanya. Bamu muka isa jaɓɓi ba sai yamma sakaliya. A tsakar gidan duk muka samu matan gidan dawowarsu daga talla kenan. Hama na wanke_wanken kwanukan tuwon jiya tana ganinmu ta wani taɓe baki. Uwani na riƙe dani wallahi ban ankaraba naga kan Hama a cikin bokitin ruwan wanke_wanke Uwani ta dulmiya mata. Da ƙyar Hama ta samu ta kwaci kanta dambe ya kaure na tashin hankali tsakanin Uwani da Hama. Matan gidan sun kasa raba wannan faɗa dan Uwani ta mahaukaci tayi musu, duk wanda yazo kusanta saita gabɗa mishi kwano. Saida fa maƙota suka cika gidan wannan faɗa ya rabu da ƙyar. Duk Uwani ta fashe ma Hama Baki, har nono uwani ta riƙe ma Hama kamar zata tsige mata shi, Hama sai ihu take faman yi. Ita kuma Hama ta gama yakushe ma uwani fuska sai jini suke zubarwa.
“Wallahi tun wuri kije ki tone asirin da kika ma Jabu. Shegiya muguwa mai baƙar zuchiya kawai, bagidajiya. Ku kuma munafukai ƴan iska ƙyaleku Jabu tayi wallahi dani nake aure a gidannan duk saina saisaita muku zama.”
Hama dai babu bakin Magana sai haki take ta famanyi. Dan iyakar dakuwa wallahi ta daku ainun. Da ƙyar matan unguwa suka tunkuɗa Uwani ɗakina. Yafendo ta dubeni tace.
“Jeki Jabu ki kwanta ki huta. Ke kuma Hama ki tattara ki koma gidanku. Kuma kiyi gaggawar karya asirin da kika yi mata. Ki sani Jabu ɗiyatace ko a gidan wani take aure sai inda ƙarfina ya ƙare wajen ƙwatar mata hakkinta. Balle kuma ɗana take aure. Kece bare a cikinmu dan haka kiyi gaggawar ficewa a gidannan”
Ni dai naji daɗin dukan da Hama tasha, kuma raina yayi fari da hukuncin da Yafendo ta yanke. Ɗaki na shiga na samu Uwani sai fito da kayan ɗakina take yi.
“Iyabo ga kujera a tsakar gida ki zauna akai ko ki kwanta. Saina caje ɗakinnan tsab na zaƙulo abinda aka ajjiye a ɗakin.”
Zama nayi a kujerar ina kallonsu ita da Baɗɗo sai zaƙule zaƙule suke yi, amman fa an fitar da gabaki ɗaya kayan ɗakin babu komai. Uwani ta miƙo mun fulo, kafin in amsa sai naga ta cire fulon a riga. Hmm mutum abun tsoro saiga fulo a ɗan farke. Uwani da ƙarfi ta kama fulon ta yage saiga jar laya a ciki. Ba shiri na miƙe na shiga ɗakin bakina a buɗe”
“Kingani ba Iyabo. Lallai wannan kishiyar taki tsinanniyace. Ya tabbata ita tayi asirin rabaki da Hamma harya dikeki haka. To Alhamdulillah asirinta ya tonu, kuma na rama miki dukan da tai miki itama yanzu zanje in kuma cin ubanta”
Zabura uwani tayi, nayi saurin tarota da ƙyar uwani ta yarda ta haƙura ta bar Hama haka.
Uwani yanzu yaya zamu yi da wannan layar to?”
“Buɗewa zamu yi, mu ƙona komu jefata a masai” Baɗɗo tace.
“A jefa a masai kawai basai an buɗeba, ni tsoro nake ji. Amman a nuna ma Yafendo tukunna” Nayi carab nace.
A’a kar a nuna mata. Hankalinta zai tashi da yawa. Kuma ƙila hakan yasa ta tursasa Hamma ya sau matarshi”
Wata uwar harara Uwani ta bini dashi tace.
“Au ke kinfi so ku zauna tare, an ganota ta nan taje ta kuma ƙullo sabon asirin da bakisan ma ko rayuwar zata rabaki da’ita ba. Wai bake kika ce mun kinsha kama garukan magani a ruwan wankanku, ko banɗaki ba, bake kika faɗamun ko abincinta ran girkinta taki miyar sai an barbaɗo miki magani ba. Iyabo anya kinsan ciwon kanki kuwa?”
Uwani tabalbalin kenan ƙawar faɗa da daɗi. Murmusawa nayi ina hawaye.
Uwani bawa mai cikakken imana yadda yake da ƙaddara imma mummuna, imma kyakkyawa. Na daga cikin sunnar rayuwa, rayuwa bata taɓa tafiya face sunyi kafaɗa da kafaɗa da matsaloli tari daban_daban. Ni bazan so in kashe auren Hama ba in ɗauketa daga kan yaranta ba. Duk mummunan halina bazan so Hama ta fitar dani a gidana ba. Wallahi in halinta ne dama ki rubuta ki ajiye zata kuma. Watarana shi shaƙundun ɗinne zai kamata da idonshi. Anan yana da damar zama da’ita ko rabuwa da’ita.”
“Ahh haba dan Allah? Ai kamata yayi a mayar da layar cikin fulon kawai. Kinga watarana Hamman da kanshi zai gano layar” Dariyar dole tasani, itama duk da a cikin ɓacin rai take saida ta dara. Miƙo mun layar tayi da bismillah a bakina na karɓa na jefa a masan gidan. Alwala nayi a bakin rijiya na wuce bukkar Yafendo na yi sallar magriba da Isha. Nasha magunguna, na ɗiga na idon. Yafendo ta dure mun tuwo tace.
“Maza ki daure kici tuwon Jabu. Sai kiyi kwanciyarki, in bacci ma ya ɗaukeki sai ki kwana abunki.
Ina tsaka da cin tuwon Yaya Hamma, da Haruna mijin Safiya suka shigo. Gabaki ɗaya hankalin Yaya Hamma a kaina yake gaba ɗaya.
Zama yayi yana fuskantata, ɗagowa nayi muka haɗa idanu. Kallon da yake yi mini mai cike da fassarorine masu dama, saƙone daga zuchiya zuwa ga zuchiyar da ake so da ƙauna.
“Yaya jikin naki, ki cire hannu a tuwon bari in siyo miki nama ki ci” A jejjere yayi maganar cike da kulawa tsantsa. Idanu na lumshe a raina nace.
Tsarki ya tabbata ga Ubangijin daya kuɓutar da Annabi Yusuf daga cikin rijiya. Kuma yasa wuta ta zama ni’ima ga Babanmu Annabi Ibrahim.”
“Dada bari inje yanzu zan dawo zan kawo ma Jabu nama ne” Ya fice da sauri ba tare da yaji me Yafendo zata ce ba. Murmushin farin ciki naga tana yi. Niko farin cikin da nake ciki bazaima musaltuba sam, sai ajjiyar zuchiya nake saukewa. Yaran Hama ne suka shigo. Mai sunan Yafendo riƙe data goyen, ta tsakiyan na biye dasu ashe Hama bata tafi da’ita ba. Karɓarta Yafendo tayi ta goya su kuma ta zuba musu tuwo suka zauna suna ci.
“Assalamu alaikum. Yafendo sannunku.” Cewar Uwani kenan tana daga bakin ƙofa.
“Yauwa am Uwani. Kun gama kwalimar ne?”
“E mun gama shine nazo kiran Jabu ta kwanta”
“Gaskiya ne. Jabu kije ki kwanta, kar ki tayarma da mijinki wata maganar ɓacin rai. Kibi dashi kamar babu abinda ya faru. Sauran ki barmun a hannuna. Tashi kije Allah ya ƙara karewa” Kaina a ƙasa nace.
To Shikenan Yafendo saida safe, Haruna saida safe” Haruna dake zaune tunda ya shigo baice komai ba yace.
“Allah ya ƙara sauƙi, ki yi haquri da abinda ya faru. Bamu da shaidar dukan mace a gidannan. Akwai dai wata maƙarƙashiya a ƙasa, kinsan sha’aninku na mata sai haƙuri. Na dawo tun daga hanya aka tareni ake faɗamun wai anyi dambe gagarumi a gidannan wai dake da Hama. Yaya Hamma ma an bashi labari har tafiyar Hama gida duk yaji.” Murmushi nayi nace.
Nagode Haruna. Sai da safe” Nai musu sallama nabi bayan Uwani har zuwa ɗakina. Sun kuma sake ma kan gadon nawa wajen zama. Kwanciyata ke da wuya muka jiyo sallamar Yaya Hamma ya shigo tare da abokinshi Baɗejo. Waje Uwani ta basu suka zauna.
“Ga wannan naman Uwani kuci ke da Jabu.” Uwani tasa hannu ta karɓi ledar. Mayafi na sako na fito daga cikin labulen da gadona ke ciki muka gaisa da Baɗejo. Shiru ya ɗan biyo baya can dai Baɗejo yace.
“Jabu, ni bansanma ta ina zamu soma baki haƙuri ba. Amman duk da haka kiyi haƙuri abinda ya faru dan Allah ki ɗaukeshi kamar ba’aiba. Ni wallahi da badan Hamma da bakinshi ya labartamun abinda ya faru ba. Alƙur’an da duk wanda ya faɗa mun wannan maganar bazan yarda ba. Shi kanshi yace baisan sanda abun ya faru ba. Kiyi haƙuri ki mishi afuwa dan Allah. Ki dubi girman ƴan uwantaka da soyayyar da Hamma yake yi miki kiyi haƙuri. Sannan naji labarin iftila’in daya afka ma daddobinki. Allah yasa da abinda ya tare. Munji labarin faɗan daya ɓalle a tsakanin Hama da ƙawarki Uwani. Uwani ayi haƙuri dai dan Allah koma me ake tunani bazai wuce zargiba. Ita kuma Hama koma me zata yi a wannan gaɓar bazai wuce kishi ko zigazigin ƙawaye ba.” Baɗejo ya daɗe yana tausata. Mai gayya mai aikin yayi tsamo_tsamo duk kunyata ta lulluɓeshi. Ni dai nayi ɗan guntun murmushi nace.
Babu komai Baɗejo wallahi na yafe. Kuma wannan abun daya faru bai rage son da nake yima Hamma ba saima ƙaruwa da yayi. Tunda har yasan yayi laifi ya kuma ɗakkoka dan kawai a bani haƙuri na haƙura. Batun dabbobi kuma Allah yasa da abinda suka tare” Naja bakina na tsuke. Ajjiyar zuchiya Yaya Hamma ya sauke a sirrance. Shima haƙurin ya kuma jaddamun dai, nace komai ya wuce.
“To komai ya wuce Hamma. Ina mai baka hakuri a bisa dukan da naima matarka. Dokin zuchiyane yasa har abinda zai faru ya faru. Saimu haɗu mu yafi juna” Cewar Uwani kenan. Yaya Hamma yace.
“Ai babu komai daliline nasan dole yasa faruwan hakan.”
Nan Baɗejo yayi mana sallama, Yaya Hamma ya tafi rakashi yace mun daga nan zai je yaba Yafendo haƙuri akan laifin da ya aikata. Kuma ya bata haƙuri Hama ta dawo ɗakinta. Ruwan tea Uwani ta dafo mana muka baje tsirannan.
“Iyabo naga akwatin aurenki a mugun yashe. Nace kyautar da kayan kika yi, kome kikayi ke ko da su?” Nadai san kala huɗu kika bani in dinko miki, kuma na tawo dasu ma an daɗe da ɗinkawa.
Mamaki dam fuskata na dubeta. Bance komai ba na miƙe naje na buɗe akwatunan kusan rabin kayan babu. Da hanzari na buɗe sib na ɗakko akwatin ƙarfen da kuɗina suke ciki. Dama tunda na ɗakko naga kwaɗon a ɓalle gabana ya faɗi. Babu ko ficika a ciki. Salati kawai na shiga jejjerowa ina jijjiga kai Hama naga halama so take ta sabauta mun rayuwata.
Uwani ce ta iso inda nake da sauri.
Uwani harda kuɗaɗena masu yawa duk kinga an kwashe mun. Wallahi nasan kuma Hama ce zata yi mun wannan aikin. Har kayan akwatinma itace zata kwashe. Illar rashin ƙofa kenan. Dole Yaya Hamma yaimun ƙofa gaskiya. Yanzu Shikenan fa ta kassarani gabaki ɗaya jarina ya ruguje murus” munfi minti talatin a Zazzaune muna jimami. A cikin wannan halin Yaya Hamma yazo ya samemu, cikin tashin hankali yake tambayar meke faruwa. Uwani ta miƙe ta nufi hanyar waje.
“Matarka zata maka bayanin abinda ke faruwa. Ni kam saida safenku.”
Tana fita ya dawo kusa dani, ganin duk ya ruɗe na fashe mishi da kukan baƙin ciki wanda ya sake sukurkutashi. Sai kuma ya mugun bani tausayi har sauya launi idonshi yayi.
“Jabu kiyi haƙuri in akan abinda nayi miki ne. In akwai wani abun ki sanar dani dan Allah” Nan cikin kuka na faɗa mishi satar da akaimun. Kai tsaye ban halaƙanta satar da matarshi ba. Kai ya girgiza yace.
“In dan akan wannan ne kike wannan kukan gashi ke ba cikakkiyar lafiya ba. Kiyi shiru ni zan biyaki kuɗin da aka sace miki, da kuɗin kayan da aka sace mikin Shikenan in anyi hakan kukan zai ƙare? Ko nawa aka sace miki kuɗinki bazai yi ciwon kai ba zan biyaki”
Faɗawa nayi ƙirjinshi ina share hawayena tare da kuma shigewa jikinshi. Danna lura saifa nayi da gaske zan iya zaman aure a ƙauyannan. Jibi yarinya ƴar ƙauye duk ta hautsina mun lissafi, ta kwance mun notukan kayina.
A wannan daren ni naga soyayya da tattali ra’ayul aini.
To anan nake cewa sai Allah ya kaimu ranar Talata kuma dan ranar monday akwai hutun maulidi oga na gida ba zaku samu posting ba sai ya koma aiki talata.
MRS BUKHARI
ramlex266: Ina mata da suka amsa sunan su ba Muna mata ba….
Ina macen da take so ta zamo tauraruwa a gidan mijinta,itace uwargida itace amarya…
ramlex266: Uwargida ko Amarya shin minene matsalar ki a wajen miji?
Rashin dandano ko ni’ima?
Bushewar farji qayau kamar busashen ciyawa?
Rashin samun gamsuwa a wajen maigida ko rashin sha’awar ce ga baki d’aya?
Budewar farji kamar kofar wambai ko qarni/wari ke damunki
ramlex266: Kina so ki zama tauraura kuma sarauniya a wajen oga a rasa gane sirrin naki? Ki zamo yar gaban goshi sai yanda kika ce wato kin mayar da oga mijin kafin ta ce? Ba boka ba malam gyaran shimfida kawai Hajiya to ki nemi hjy ramlex domin qarin bayani
Part 9
NAMA YA DAHU…
ROMO ƊANYE
BADI’AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
LITTAFI NA UKU (9)
Takai:
Ba shiri Shafa ta bar zancan ganin yadda Gwadabe ya ɓata rai.
“Munga tsaraba an gode Allah ya ƙara buɗi. Duk an rarraba ma kowa. Sannan kaima Yaya Bara’u godiya tunda muka shigo Takai kullum sai an aiko su Toye da ƙunshin tsire ko balango” Bai amsaba ya miƙe tsaye.
“Bara’u muje ko? Zamu tafi sai da safe. Gobe zanyi wata ƴar tafiya amman a goben zamu dawo, ina buƙatar adda’a ” Ya ciro kuɗi a ajjihunshi ya bata.
“Ga wannan nasan ba zaki rasa abun saye ba. Gobe kije gidan Sakina ki wuni tare da Hadiza, itace baƙuwa a garin” Nan sukai mata sallama, kai tsaye masallaci suka nufa suka sallaci magriba. Sai gasu a majalisar abokai nan akaita hira zuwa isha, da sukai isha suka shiga gida da ƙumshin nama, Bara’u ya aiki yaro ya kaima Shafa nata kason. Gwadabe fa tun haɗuwar da yayi dasu Babala har yanzu ita ke yawo a kanshi. Sukuku haka ya shiga gidan ya tarar da su Sakina da Hadiza da yaran duk anata cin abinci. Shinkafa da miya harda latas suke ci.
“Gwadabe wannan nisan kiwo haka. Tun fitar sassafe ko abincin ranar ma baku shigo kunci ba. Kai ku ba iyayenku waje, ku dawo tanan” Yaran suka dawo inda Sakina ta nuna musu, iyayen kuma suka zauna a wajen. Hadiza dai taga mijinta duk ya canja abunka da mace mai shegen kishi sai zuchiyarta take raya mata dan yaga Shafa da Abbane, shine ita da ummi ya sharesu. Tunda tace mai sannu da zuwa bata kuma tankawaba. Gwadabe kuwa da ƙyar yaci abinci loma biyar, a hakanma Bara’u ke ta janshi da hira.
“Gwadabe nace naga kayan da Anty Badi’a ta aiko mun dashi. Nagode sosai Allah ya bar zumunci. Hadiza ma ta gwangwajeni da kayan mutan nijar, Allah dai ya bar wannan zumunci har gidan aljanna”
“Ameen Sakina babu komai. Wata rana haka zamu zama surukan juna kinga an sake curewa an zama abu ɗaya” Ɗan darawa akayi Hadiza tana zaune kamar dutse ummi harta soma kuka taƙi kulata ga yarinyar a cinyarta, sai cin abincinta take. Gwadabe da dama a hasale yake wajen saukewa yake nema yace.
“Kinaji yarinya duk ta cika mana kunnuwa da kuka ki bata Mama mana ta tsotsa” Da fishi Hadiza tace
“Nima fa abincin nake ci kana gani. Yarinyarnan yanzu tasha ni babu wani nono da zan bata” Dama Hadiza tayi ne akan ramuwa, batasan kura ta kwanto ma kanta ba. Duk da bai kulata ba face miƙewa da yayi idandunanshi suka kaɗe.
“Sakina zanje in kwanta kaina ciwo yake yi. Gashi gobe zamu shiga Kano”
A razane Hadiza ta kalleshi ya daka mata harara yayi ficewarshi ya ɗaura mata tention shi kanshi yaga hakan.
Sanyin bishiyoyi masu kaɗawa da ƙamshin korayen ganyayyaki ne yasa Gwadabe wani lafiyayyen bacci, duk da ranshi da zuchiyarshi a jagule suke.
Washe gari sassafe su ka yi wanka. Suka karya da alala da kunu mai zafi Gwadabe ya mike yace.
“To Hadiza, Sakina mu kam zamu ɗau hanyar Kano sai in Allah yayi dawowarmu. Shafa zata zo ta wuni tare daku anan. Dan Allah Sakina ki shiga dasu gidan Zulƙi. Ko kuma su jira inna dawo sai in gaisu in gabatar dasu”
Har sun fito ƙofar gida ya jiyo muryar Hadiza.
“Gwadabe dan Allah bani minti biyu” Murmushi yayi yasan za’a rina. Yana zuwa ta sauke murya tayi kalar tausayi.
“Jikina yana bani gidan tsohuwar matarka zaka je. Wai dan Allah sai yaushe Iyabo zata barmu mu mori mijinmu ne? Jiya na kasa runtsawa sabida tunani, duk da ba yau Iyabo ta taɓa sani nai asarar darena ba. Amman abun ya haɗemun harda canjin dana gani jiya a wajenka sabida kana zumuɗin ganin Shafa da Abba”
Kallonta yake tayi tun sanda ta soma Magana. Da dariya ya fashe da yaga kuka take ƙoƙarin yi.
“Hadiza Matata ta kaina. Iyayen kishi su da kansu. Yafa kamata ki dena yadda da duk abinda zuchiyarki zata rayo miki gudun faɗawa tarkon dana sani. Iyabo ta tsone miki idanu da yawa naga ko Shafa dake ainihin kishiyarki abokiyar gurzawa bakya kishinta rabin yadda kike kishin Iyabo, ya kamata ki kama muguncinki, karki bari ki sire mun. Mu zamu tafi karmu makara”
A tsaye a ƙwar gidan ya barta bata shige ciki ba har saida suka ƙule ta ja jiki a sanyaye ta shige hantar cikinta sai kadawa take yi”
Kano:.
Saukarsu Gwadabe ke da wuya a garin Kano suka wuce unguwarsu Iyabo gidansu Uwani. Mahaifiyar Uwani Hajiya ce ta fito.
“Au Gwadabe shine kuka tsaya a waje sai kace baƙi bismillah ku shigo”
Dole haka suka kutsa cikin gidan. Hajiya ta shinfiɗa musu tabarma suka zauna aka gaisa a nitse.
“Dama Hajiya gidan Uwani muke son yaro ya rakamu.” Hajiya tace.
“Allah sarki ai kuwa kunyi saɓani Uwani ta tafi Jaɓiɓi wajen Aminiyar tata Iyabo acan take aure, to tafiyar ta gaggawace ma dai. Kuma tunda ta tafi ba mu yi waya ba, yaranta ma suna nan tare dani”
Tashi ɗaya Gwadabe ya koma kalar tausayi. Ba baƙin ciki yake da auren Iyabo ba. Ba kuma baiji daɗin jin tana gidan aure bane. Kishine na zahiri wanda bashi da masarrafarshi. Sai yaji ƙirjinshi yayi mishi nauyi.
“To Hajiya ko zan iya samun lambar wayar Uwanin ko ita Iyabo ɗin?”
“To gaskiya ni babu waya a hannuna. Yara da zasu baku lambar gashi duk kowa ya fice. Sai dai in gobe zaku dawo sai in sa yara su rubuta lambobin a takadda” Bara’u yayi carab yace.
“A’a ki barshi Hajiya. Nanda sati ɗaya ma dawo kafin lokacin Uwanin ta dawo sai muzo a kaimu” Hajiya tayi jim tace.
“Amman Allah dai yasa lafiya ba wani abun bane ba ko? Naga kamar kun matsa lallai sai kunga Uwanin” murmushi Gwadabe yayi yace.
“Babu komai wallahi Hajiya. Dama dai labarin Iyabo muke son ji a bakin Uwani. Baya ga wannan babu komai” Dariya Hajiya tayi irin ta manya tace.
“Allah sarki. Ai indan wannan ne ba dole sai kun nemi Uwani ba. Iyabo dai tayi aure a dangin mahaifiyarta. Dan kamar Uwani tace mun da gyatumar yaron da ita Iyabo ta aura. Da gyatumar Iyabo ya da ƙanwa suke. Sun jima suna son junansu tun su Uwanin da IYABO suna Saudiyya. Auren bai jima ba da akayi shi.”
Sai kallon kallo tsakanin Bara’u da Gwadabe. Gashi babu damar su matsama Hajiya da tambayoyi. Saidai abubuwa da yawa sun cunkushe kan gwadawa. Na farko shine Saudiyya da yaji Hajiya tace tun suna can. Na biyu jin a irin dajin da Iyabo taje tayi aure. Yasan labarin ƙauyen a bakinta amma bai san komai baya ga labarin bakinta ba.”
“To Shikenan Hajiya mun gode. Mu zamu koma, a isar mana da saƙon gaisuwarmu wajen Uwani dama Iyabon.” Cewar Bara’u kenan. Shi kam Gwadabe yana cikin dabaibayi.
“Zasu ji. Ya yaran duk suna cikin ƙoshin lafiya dai ko?” Bara’u yace.
“Suna lafiya. Suna karatunsu arabi da boko. Hajiya mu zamu wuce to” Bara’u ya zaro jaka biyar ya ajjiye ma Hajiya. Sukai mata sallama suka fito.
Suna zaune a motar Takai Bara’u yace.
“Wannan shirun yayi yawa Gwadabe me kake nufi ne. So kake IYABO ta zauna babu aure ko me? Naga kai mata biyu ka aura rana ɗaya” A fusace yace.
“Na auresu ne a bisa tayin aurensu da akayi mun. Waɗanda sukaimun tayin sun fi ƙarfin komai a wajena. Iyabo itace rayuwata Bara’u “
“To itama saika ɗauka umarnin mahaifiyarta tabi tunda ai kaji ance ɗan uwanta ne ta aura. Ni na ɗauka ma Debisi ne zai aureta wallahi”
“Hakane Bara’u. Ina tayata farin ciki da auren data yi. Sai dai ina tayata jimamin zaman ƙauye. Dan a yadda take bani labarin ƙauyan ƙauyene ƙayau, gasu da ƙauyanci da ƙarancin addini. Ko asibiti babu fa, balle wutar lantarki, kaga babu ruwa babu kwalta, babu makarantu.” Jim Bara’u yayi yace.
“Sanin da ba. Kasani ko sun samu tallafin gwamnati. Ita kanta sau ɗaya fa kace ta taɓa zuwa tun tana yarinya. Inka lissafa daga lokacin da taje zuwa yanzu ƙila sun samu ci gaba. Ko shekara biyar baya ka kalli takai ai kasan an samu gagarumin ci gaba ko? Ni batun zuwansu Saudiyya ita da Uwani shi nayi tunanin zaka yi nazari akai ma” Kai Gwadabe ya dafe tare da lumshe idanunshi. Baice komai ba, tunani da lissafe lissafe yake ta faman yi har Allah ya dawo dasu Takai lafiya.
Cikin gidan ma daya shiga wani tarin tulin takaici ya tarar. Hadiza sai kumbura take yi kamar kwaɓin gurasa. Sakina da Shafa su kuma sunata faman hirarsu da nishaɗi. Gefe guda Gwadabe ya zauna jigum.
“Bara’u Gwadabe ba lafiya ne?” Bara’u ya amsa ma Hadiza da cewar.
“Kanshi ke ciwo ga hanya mun shawo” Shafa sai tabar abinda take yi ta koma wajen mijinta ta kai musu abincinsu. Lamarin daya sake zugunɗuma fishin Hadiza ta sakei hawayen da take riƙewa kenan. Ta kullace wannan wulaƙancin da Gwadabe yake yi mata dan yaga ya kawota garinsu.
Da yamma liƙis suka dunguma gidan Zulƙi sun ko yi saɓani Zulƙi da iyalanshi basa nan sun tafi wani taro na masu kujeru a hannu a Abuja. Gwadabe ya kwashi su Hadiza harda Bara’u da Sakina suka je. Kwanansu biyu a gidan Tamu. Ayashe itama ta tarbesu tarba me kyau sosai. Nan da aka haɗu dole saida labarin Iyabo ya ratso ta cikin zancan. Hadiza tana mamakin irin tasirin Iyabo a cikin rayuwar Gwadabe da duk makusantanshi. Wai shin wanne irin kirkine da Iyabo, wannan irin kawaici da juriyane da’ita? Hadiza taima kanta tambaya. Kishi na rugurguza zuchiyarta d gangar jikinta. Saita tsinci kanta cikin son zama kamar Iyabo badan komai ba sai dan kishin mijnta da son mantar da Gwadabe Iyabo. Wannan dalilin nata yasa ta cakaloma Ayashe da Sakina zancan Iyabo. Sai dai me da suka soma zana mata Iyabo sai taji e lallai takai macen da dole ta tsaya a zuchiyar ɗa namiji. Sai taji a madadin ta zauna kishin Iyabo ya hanata jituwa da Gwadabe ai gara ta ari rigar Iyabo ta yafa. Amman me a daren ranar Hadiza ko runtsawa takasa yi. Sai jujjuya al’amura take yi a zuchiyarta wata zuchiyar tace da’ita.
“Ashe baki cika mace ba in har sai kinyi koyi da halayen tsuhuwar matar mijinki. Kenan ke ba zaki iya juyarma da mijinki hankali ba sai kin zama irin matarshi? Ai kamata yayi kema ki ɓullo mishi da sabon salon tarairaya da tattalin daya doke na beyerabiyar matarshi ba ki tsaya kina bin diddigin halayenta ba” Ai sai ta hau kan shawarar zuchiyarta tayi ɗare_ɗare.
Haka dai suka gama kwanakin da zasu yi suka tarkato suka baro Takai da tarin tulin tsarabobin da Sakina da Bara’u sukai musu ƙunshi_ƙunshi. Motarsu tana gudu a hanya. Hadiza zuchiyarta na gudu da tunanin mafitarta itafa tana ji tana gani ba zata bari Gwadabe ya sauya mata ba ta zama itace ma bare ba. Jibi Shafa tun shigowarsu motar take ta janshi da hira ya sake sai amsata yake yi sunata nishaɗinsu. Ajjiyar zuchiya ta sauke haƙiƙa ta fahimci Gwadabe ya gundura da ƙorafinta da saurin fishinta. Ta daɗe tana lura ita Shafa irin matannanne da kamar basu san ciwon kansu ba, kuma ba komai ke ɓata musu raiba. Da ire_iren wannan tunanin bacci yai awon gaba da Hadiza ɗiyarta na rungume a jikinta itama baccin take yi.
Juyowa Gwadabe yayi ya kalleta ya lumshe idanu. Hadiza tana da wani matsayi mai girma a zuchiyarshi yana sonta. Sai dai ɗabi’unta na ƙorafi, yawan fishi sun kaishi maƙura shi yasa a wannan karon shima yayi watsi da lamarinta. Ummi ya zare a hannunta hakan yasa ta farka da sauri tare da sake cabke ɗiyarta.
“Nine ba wani ba. Kawota ki samu kiyi baccinki”
Miƙata tayi ta koma baccinta ba tare da tace dashi komai ba.
Sai dare suka isa gidan sosai. Sun jima sosai suna buga ƙofar gidan kafin Mammada yazo ya buɗe musu.
“Sannunku da dawowa mutanen najeriya kune da tsohon darennan Gwadabe?” Matan ciki suka yi, Gwadabe ya tsaya suka gaisa da Mammada kafin ya ƙule ɗakin Shafa.
Hadiza tana kwance sai juyi take yi fitowarta daga wanka kenan. Tayi tsammanin Gwadabe ko babu komai zai leƙo yai musu sallama ai. Amman sai taji shi shiru a ɗakin Matarshi.
Washe gari ma ta jima sosai tana jiran ya shigo su gaisa da taji shirun yayi yawa dole ta goya ummi ta fito ta nufi ɗakin Shafa dan a ƙofar ɗakinta aka jibge tsarabar.
“Shafa Gwadabe yana ciki kuwa?” A kitchen ta samu Shafa tana zuba abincin da zata ci. Ita sai lokacin ma ta tuno ashe ko karyawar batai ba. Sai da Shafa ta gaisheta tace.
“Da wurwuri ya fita zaije cin kasuwar Damagaram. Ko ya shiga ɗakinki kina bacci ƙila” Wannan abu ya daki Hadiza sosai, sai dariyar yaƙe tayi tace.
“Babu mamaki kam dan ban jima da tashi ba. Bari in kunce tsarabar zan shiga ma da su Baba nasu’
“To Yaya gasu nan. Nima inna gama karyawa zam shigo cikin gidan “
Hadiza dai zuchiyarta na tafasa ta yi cikin gida da tsaraba. Saida ta mikawa matan malam nasu tsarabar kafin ta nufi ɓarayin Baba Fhatsima.
“Zafine a garinne Hadiza naga dul kin rame, ga ƙuraje duk sun feso miki?” Cewar Baba Asshi dake duƙe tana dauraya. Baba Suwaiba tace.
“Takai fa ƙauyene sosai. Ni nasan ƙauyan da jimawa dole su rame ai” Hadiza dai bata ce komai ba tayi murmushi tasan abune mai wuya ƴan gidan su canja halinsu. Tana shiga ta samu Baba Fhatsima na shan fura. Yaya Tasi’u yana zaune a gefe yana cin ƙwadon zogale.”
“Hadiza kaddai kune jiya da daddare kuke ta faman dukan ƙyaure?” Cewar Yaya Tasi’u kenan. Murmushin dole tayi mishi tace.
“Mune Yaya Tasi’u shigowar dare muka yi. Ina wuni yasu Safara’u, da Anti Badi’a?”
“Basa nan sunyi tafiya shekaran jiya suna da biki”
“Baba ina kwana mun sameku lafiya?” Abunka da uwa tuni ta gano Hadiza na cikin damuwa ga idanunta sun farfaɗa.
“Lafiya lau ya mutanan Takai, inasu Sakina da Toye?” Sai Hadiza ta ɗan sauke kanta sai hawaye shar_shar. Yaya Tasi’u ya miƙe tsaye yace.
“Sakara bata da aiki sai shirme. Baba ni zan wuce wajen aiki saina dawo” Baba Fhatsima tace.
“To a dawo lafiya. Kar ka manta da maganarmu akan Balaraba kayi tunani ina sauraren amsarka daga yau zuwa gobe” Bayan Yaya Tasi’u ya fice Baba Fhatsima ta mayar da hankalinta akan Hadiza.
“Wani abunne ya faru a Takai ɗin. Ko ke da mijinkinne, ko kuma abokiyar zaman taki ce? Ki nutsu kiyi mun bayani” Cikin shessheƙa Hadiza tace.
“Baba Tunda muka shiga Takai Gwadabe yaga Shafa da ɗanta shikenan ni da Ummi ya juya mana baya. Sai fishi yake yi, kuma fa har gidan tsohuwar Matarshi a Kano saida abokinshi ya rakashi suka je. Ni fifikon da yake nuna mun ya isheni” Baba Fhatsima tayi shiru cikin karantar yanayinta tace.
“Hmm Hadiza ho. Wallahi in kika yi saken da Gwadabe yaga wallanki to wallahi kin shiga uku zaman bazai miki daɗi ba. Hala kin isheshi da ƙorafine, ko kuma wata damuwar ke damun ranshi har kika ga ya canja. Ko kin tambayeshi dalilin canjin nashi?” Hadiza ta girgiza kai halamar a’a”
“Kinji irin shashancin naku ai yaran yanzu. Yanke hukunci ba naku bane, zaunar da miji zakiyi cikin kulawa da nuna damuwa da sannu saiya warware miki cikinshi. Da haka mace take zama sirrin mijinta abokiyar shawararshi. In kikayi sake Shafa ta samu wannan kambun bake ba. To abubbuwa da dama zasuita faruwa da mijinki, ƙalilan daga cikine zaki iya ji. Masu yawan yaci ya birne da abokiyar zamanki. Hadiza namiji wawane, kuma sauƙin sarrafawa garesu Wallahi. Abinda yasa na kira namiji da wawa shine. Shifa kulawa da tarairaya, sai ladabi da biyayya,iya girki, iya kwalliya, tsabta iya ɗauke lalurarsa. Shine fa namijin kuma shine zaman auren. Ana mallakar miji da kissoshi sunfu kala saba’in bari in jero miki kaɗan a cikinsu.
Akwai kirsar magana
Akwai kirsar tafiya a gaban miji, ko kishiya
Akwai kirsar rauni, yawan kuka
Akwai ta shagwaba
Akwai kirsar nuna ma miji ke kullum bai isarki a shinfiɗa
Akwai kirsar shimfiɗa
Akwai kirsar sa sutura
Akwai kirsar iya girki
Akwai kirsar ciyar da miji abinci a baki
Akwai kirsar yima miji wanka
Kirsoshin suna da yawa, ko wanne guda ɗaya kika ɗauka zaki zama ta daban. Kuma zaki zauna daram a zuchiyar mijinki. Shine zakiji yana faɗin alkhairin Allah ya kaima wance. A gaban matarshi zai iya yabon matar data mallakeshi da Tata kirsar namiji ba kunya gareshi ba. Ko kiji yana da wancece da yanzu tayi mun kaza, ko tace kaza. Namiji ya barki da sakakken baki. Su basa raina sauyi, ko jin daɗi duk ƙanƙantarshi. Abubuwa da dama mun ɗauke kanmu akai bamu ɗaukeshi da mahimmanci ba, shigowar boko duk ya wanke muku kanku kun dena biyayya. Mu a zamaninmu a wani gari da Malam ya taɓa kaini muka zauna lokacin sana’ar Malam sai da gishiri da manda ne. To gidan da muke haya akwai wata Fatu bafulatanar Gombe ce. Akan rashin sa ruwa a buta mijinta ya saketa sai garinsu ta koma. To wani akan shara zai iya rabuwa da mace. Wani duk waɗannan ƙanunun abubbuwan harma da manyan bai dameshi ba babu ruwanshi.
Amman kinsan babban abinda maza suka wasa shine tsananin kishi, zargi, ƙorafi, bin diddiginsu dan ganin laifinsu, ƙazanta. Waɗannan abubuwan dana jero duk halinki ne banda ƙazantar shi yai silar mutuwar aurenki na fari.
Ke ba zaki zama mai kawaiciba, ki gani ƙiri_ƙiri ki nuna baki gani ba. Kiji ki toshe kunnenki. Dole sai anayi ana haɗawa da halin ko in kula, koda hakan zai dameki.
Hadiza ki kiyaye abinda zai maisheki bora, Gwadabe fa yana haƙuri dake” Hadiza taci kukanta mai isarta. Baba Fhatsima batai yunƙurin hanata ba har saida tai shiru dan kanta kana tace.
“Sai ki kiyaye. In ranar kwananki ya zago saiki bashi haƙuri a bisa kusakuranki da kinfi kowa saninsu. Kuma cikin lallami ki doki cikinshi ya baki labarin matsalarshi. Ke kuma saiki magance mishi damuwar. Inta adda’ace kice zaki taya shi da adda’a. In kuma na shawarane ki bashi shawara, inma na nasihane ki mishi. To zaki ga ko farin cikin ya shiga kece ta farko. Ke namiji sauƙin kai gareshi in baki kwaɓeshi ba sai kiga har asirin kishiyarki ya fasa miki shi babu ruwanshi. Tashi ki koma ɓarayinku”
Sallamar Shafa ce ta katse musu hirarsu. Baba Fhatsima ma ce ta amsa mata ta shigo suka gaggaisa.
“Malam baya nanne Baba? Shafa ta tambaya”
“Bayanan sun tafi taron biki cikin Zinder sai da yamma zai dawo. Ya kika baro mutun Takai dana Habuja?” Murmushi Shafa tayi tace.
“Duk suna lafiya Baba. Ga wannan turmin zanine wana yace in kawo miki”
Ta miƙa ma Baba wannan turmin zani holan. Baba Fhatsima taita godiya. Anan dai ta tafi ta bar Hadiza dan saida taci ragowar zogalen da Yaya Tasi’u yaci ya rage, ta kora da fura kana ta tafi.
Tana komawa gidan ta samu suna abinda suka saba. Wannan karon da matar Mammada da matar Sabitu ne. Dan kaf gidan bada wanda matar Sabitu batai faɗaba shima ɗaure mata baya yake yi inya dawo ta faɗa mishi ƙarya da gaskiya saiya fito tsakar gida da gajeren wando bako riga yaita fitsara. Har Hadiza ta wuce ganin da matar wanta ake rikicin saita tanka.
“Haba matar Mammada wannan ai ba halinki bane kiyi haƙuri ki rabu da’ita sharrinta zai koma kanta” Tsautsayi da ba’a saka mishi rana. Buɗar bakin matar Sabitu sai tace.
“Ai sharri a jininku yake yawo. Tunda mahaifiyarki ta kakame komai gani take ku kaɗaine ƴaƴa. Kamar yadda Mammada ke da gado, haka Sabitu yake dashi shima. Ina ruwanki da wannan faɗan?” Hadiza tayi kasaƙe tana jin ikon Allah ga Shafa tana tsaye tana jin duk abinda ke faruwa. Hadiza tana juyowa ta cukume rigar Matar Sabitu dambe saiya kaure. To Hadiza ƙaƙƙarface sosai, nan ta guggurje bakin matar Sabitu. Duk da itama ta taɓuka tunda ta gwara kan Hadiza da bango har saida wajen ya fashe.
“Shegiya mai haƙoran mayu” A guje Hadiza ta bita Shafa tayi carab ita da matar Auwala suka riƙeta
To dama Hadiza kunga a cikin yanayin da dama take wuni tayi tana zage_zage da mita a tsakar gida, tana faɗin.
“Daidai nake da ko wacce shegiya a cikin gidannan ” matar Sabitu ta leƙo tace.
“Harma kina da bakin magana ke da saida aka roƙi Gwadabe ya taimaka ya aureki. Shi yasa aka haɗa auren da Shafa dan itace zaɓin ranshi. Wooo anji kunya anyi bandaro an kasa auruwa” Hadiza sai da tayi ɗan daka ce bata kula matar Sabitu ba, dan ta ɓarar mata da gari a gaban kishiya. Tunda ta shige ɗaki shikenan tayi ƙus. Shafa kuma tayi dariya ta shige ɗakinta itama.
To ko da daddare da Gwadabe ya dawo bai fa leƙo Hadiza ba. Tsarabar lemu da ayaba da balangu ya aiko Shafa ta kawo mata. Tana zaune sai jujjuya maganar matar Sabitu take. Gani take kamar gaskiya ne abinda ta faɗa akan aurenta da Gwadabe
Fitar Shafa ba daɗewa sai ga Sabitu ya buɗe labulen Hadiza rai a ɓace harda bulala fa. Batai tsammaniba ya shigo ya soma carbaɗa mata.
Gwadabe yana cin abinci ya jiyo karan tabka da ihun Hadiza ba shiri ya fito a fusace. Ganin yadda bil haƙƙi Sabitu ke dukan Hadiza Gwadabe yayi kukan kura ya dira a wuyanshi. To gaskiya Gwadabe ba ma’abocin faɗa bane, kuma ko a sifa Sabitu ya fishi jikin ƙarfi zuga Gwadabe yayi da ƙasa yaje ya shure jeren kwallayen Hadiza duk murafen suka rikito mishi.
Wannan ƙaran ɓarin kwanukanne ya fito da su Mammada. Auwala ya tari Sabitu ya dinga aika mishi naushi Babu shiri Sabitu ya fito a ɗakin Hadiza da gudu. Ya bangaji Yaya Tasi’u da shima hayaniyar ce ta fito dashi suka faɗi tim a ƙasa tare.
MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
Part 10
NAMA YA DAHU…
ROMO ƊANYE
BADI’AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
LITTAFI NA UKU (10)
Iyabo:.
Duk da ba lafiya ishasshiya gareni ba bada kai nayi bori yahau. Muka raya wannan dare cike da aminci. Washe gari zuchiyoyinmu wasai kamar ma ba mu ba.
Bayan Yaya Hamma ya karya yana shirye tsab yace.
“Bari inje wajen Baɗejo in karɓo kuɗinn da nace zan biyaki na kayanki da kuɗaɗenki da aka sace. Sai dai baki faɗa mun nawa ne kuɗin ba. Shagwaɓe mishi na kuma yi tunda na fahimci shagwaɓe na daga cikin abinda ke kunna shi. Fuskata ya shafa yace.
“Anya yau zan iya fita aikin ma kuwa ba zama zanyi inyi jinyar matata ba?” Da naji ya faɗi haka saina sake matseshi a jikin kujera na soma mishi wasannin da baisan dasu ba sai haɗuwata dashi. Nan muka sake lulawa duniyar ma’aurata.
A wannan ranar dai Yaya Hamma saida na roƙeshi ya yarda ya fita. Bayan ya caskemun kuɗin kayana da kuɗin da aka haɗa aka sace mun. Ya ƙaramun da Nera dubu ɗari da hamsin. Ya ƙwaɓeni sosai akan ka da in sake kowa yasan labarin kuɗin daya bani, dan Saniya ƙatuwa ya siyar ya bani kuɗin dukka. Naita mishi godiya na rakashi har ƙofar gida. A tsakar gida naci karo da Uwani.
“Uhm Tattabara Uwar soyayya har an shirya da halama komai ya dawo kan seti kenan?”
Hannunta naja muka koma ɗakina na danƙa mata wannan kuɗi a leda na labarta mata yadda muka yi ya bani kuɗin.
“Kin kyauta ko babu komai kaɗan zaki cika ki ɗakko dila kasuwancinki yaci gaba. Wannan karon me zaki saro to?”
To ina ganin kayan yara ma sun wadatar na maza da mata. Tunda ya farfaɗo mun da jarin kinga Shikenan. Uwani tace.
“Akwai dubu talatin ɗinki a hannuna kuɗin hayar gidanki du ɗakuna ukun an zuba haya. Kinga bama saina ara miki ko sisi ba. Dana koma Kano zan kira Faty muyi magana, zanje hajj kam in tura mata kuɗin. In kayan sun iso zaki ganni ni da kaina zanzo in kawo miki. Amman Iyabo me zai hana ki shiga ɗakin Hama ki dubo turamen zannuwanki ki kwashe. Mitsiyaciyar dai nasan da kuɗin zata tafi rugarsu”
A_a Uwani tunda dai Yaya Hamma ya biyani kuɗin komai harda ƙari bana son in kunno wata fitinar”
“Bari kiji Iyabo gobe zata iya miki satar da ta fi wannan muni, sai kiyi yaya kenan in tun yanzu baki ma tubka hanci ba?”
Nisawa nayi nace.
Idan ta kuma zata gane kurenta kinsan Allah inna zauneta saita amayar da ƴan hanjinta.”
Nan muka taɓa hirarmu ta yaushe gamo, saida Yafendon tazo tayi mun ya jiki sannan na tuno da ciwo ashe nake. Da safe dai nasha magani, Yaya Hamma ya ɗigamun na idanun yana ta faman yi mun sannu ni kuma inata langwaɓewa. Da yamma na sa mayafina muka je gidan Dada ni da Uwani. Hmm kunsan ƙauye da gulma ashe Dada ta riga da tasan duk abinda akayi sarai, bata shiga zancan bane sabida tasan Yafendo ba zata bari a cutar dani ba, haka shi kanshi Hamman bazai cutar dani yana cikin hayyacinshi ba. Nasiha da ban haƙuri ta dinga yi mun, tare da jajanta mun bisa asarar data hauni. Da yamma sakaliya muka koma gida muka tarar ƙanwar mahaifiyar Hama tazo an turota jin ba’asi. Su Baɗɗo suna tsakar gida suna aikace_aikacensu muka wuce, matan gida kuwa in banda Safiya babu wacce taimun ƙaƙa jiki, mazajensu dai sunzo sun dubani, amman dake su a bayan Hama suke shi yasa haushina ma sukeyi. Washe gari sassafe Uwani ta kama hanyar Kano. Wannan karonma ta sari man shanu a hannun Baɗɗo mai yawan gaske.
Gaga_gaga soyayyarmu ni da Yaya Hamma ta ƙara burunƙasa matsawar da Hama tayi saita bamu damar sake shaƙuwa da junanmu, mukaita ragargazar amarci. Yaranta kuwa a cikin kwana biyar da tafiyar uwarsu harsun sauya. Na tsefe musu kansu na wanke musu tas, na musu kitso, kullum saina musu wanki tare da Babansu da Yafendo. Gari ya ɗauka amaryar da Hamma ya auro a birni ta mallakeshi ta rabashi da Matarshi. Shima har tareshi akeyi a hanya ana mishi magana akan ya daure ya dawo da Hama. Abu ɗaya yake faɗa musu Yafendo ce ta koreta ba shiba, bashi da damar tsallake maganar mahaifiyarshi. Ni dai a cikin sati biyu da tafiyar Hama har wani haske da ƙiba nayi, kullum Yaya Hamma sai ya riƙo mun kayan daɗi yake shigowa, ga wani irin tattalina da yake yi. Roƙonshi nayi akan inaso in soma koya ma Baɗɗo da Safiya karatun Qur’ani a tsakankanin magriba zuwa isha. Babu musu ya amince mun nake koyar dasu a tsakar gida. Abu kamar wasa ba sai har matan maƙota suka soma shigowa ɗaukar karatu ba. Ya zamana ina koyar da mata ashirin karatun Alkur’ani da kuma abinda ya danganci tsarki, da alwala. Abun mamaki da yawansu basu iya wankan tsarki ba, ƙalilan daga cikinsune suka iya sai gyara da akayi musu. Ina jin daɗin ɗalibaina suma suna jin daɗina. Wannan makarantar daren saita sake debe mun kewa, ya zamana kuma an sanni sosai a ƙauyan.
Wata ranar juma’a da rana babu kowa a gidan ina kwance ina karanta littafin Hausa mai suna Allurar cikin ruwa na Bilkisu funtua . Bayan na gama bitar fassaran hadisin da zamu yi da ɗalibaina. sai kawai naga an wangale mun labude. Ɗagowar da zanyi sai naga Hama ce riƙe da labulen. Duk ta rame idanunta ya zurma.
“Kinci nasara a kaina gaki ga gidan Hamma. Ni zan bar miki gidan baki ɗaya kayana nazo kwasa. Amman ki sani babu ke babu kwanciyar hankali sai kin fita tsirara a haukace daga ruggarnan”
Ta saki labulen tana wata dariya. Jikina sai naji ya mutu murus na rasa kataɓus. In yinƙura in tashi na kasa, inaji Hama nata kwaramniya a tsakar gida. Ashe kayanta ta kwashe tsab saida Yafendo ta dawo muka gani, ko tsinke Hama bata bari ba. Da Hamma ya dawo da daddare ya sameni a ɗakin Yafendo ta labarta mishi hama ta kwashe kayanta. Duk saiya shiga damuwa ainun ina lure dashi. Ko da muka koma ɗaki kasa cin abinci ma yayi, ƴar hirar da muka saba ma yau babu.
Yaya me zai hana kaje kayo bikon matarka ta dawo tunda kana son matarka ga yara a tsakaninku” Anan naji abinda ke cikinshi. Cemun yayi.
“To ya zanyi Dada taƙi fur. Kullum inna shiga saina roƙeta akan tayi haƙuri ta yafe ma Hama ta dawo ɗakinta ko dan sabida yara, maganar gaskiya nima inason ta dawo. Sai tace a’a” Shiru nayi ina kallonshi da mamaki bil haƙƙi a cikin damuwa yake. Saina sanya salama a zuchiyata nasan lafiya lau yake zaune da matarshi kafin zuwana, har tatsar nono tare suke yi, tare suke duba dabbobi marasa lafiya. Bazanyi tsammanin ya soni fiye da Hama ba. Miƙewa nayi zuruf. Yayi saurin kamo hannuna muka ƙurama juna idanu, kishin sai neman ingizani yake yi, nifa sai naji nama tsaneshi ni kam, kamar in dira a wuyanshi haka nake ji.
Ina zuwa yanzu zan dawo”
Na furta a raunace. Idanu ya lumshe ya miƙe tsaye ya shige jikina ya ƙanƙame ƙuguna ƙam. Runtse idanu nayi kawai kishi nata ɗawainiya dani, sha’anin maza akwai munafurci a ciki. Babu mamaki acan ɗakin Haman haka yake mata irin wannan soyayyar koma fin hakan. Ai da wannan tunanin ya bijiro mun saina sa hannu bibbiyu na ɓamɓareshi a jikina na fice, inaji yanata kiran sunana ko tankashi bamba. Ɗakin Yafendo na shiga har tayi shirin bacci.
“Jabu lafiya kuwa”
Tsugunnawa nayi nafi minti talatin ina bata baki akan ta yi haƙuri Hamma ya dawo da matarshi. Ta dinga kwatantamun in bari kawai tunda Hama da kanta ta yanke hukuncin haƙura da shi. Na kafe akan ta dai yi haƙuri.
“Shikenan Jabu jeki Allah yayi miki albarka”
Ameen Yafendo nagode, sai da safe”
Sallama nayi mata na fita. Ina zuwa daidai bakin ƙofar ɗakina sai naji kamar wani abu ya shiga jikina haka. Nayi saurin runtse idanuna ina karanto duk adda’ar da tazo bakina, har saida na samu nutsuwa. A sanyaye na shiga ɗakin inaji tsigar jikina na tashi.
A kan gado ɗare_ɗare na samu Yaya Hamma idanunshi biyu amman ya shiga zurfin tunani juyo kai yayi muka haɗa idanu. Hannuwanshi biyu ya miƙo mun halamar inzo in shiga jikinshi. Basarwa nayi na samu jefen gado na zauna. Hannayena duka biyu Yaya Hamma ya riƙo yana murzasu yana daga kwance, suna ratsani sosai. Da wata murya sassanya yace.
“Ina kikaje kika barni ni kaɗai cikin kewa” Idanuna na lumshe a zuchiyata nace.
Lallai kishi aikine ja, banga laifin Hama ba da taita hauka lokacin da za’a auroni. Bansan sanda nace.
Kewar uwar ƴaƴanka data bar gidanka ko?” Da sauri ya miƙe zaune banyi aune ba ya soma aiko mun da saƙon kai tsaye, tun ina gane yaren har na dena gane komai ya fahimci raina ya ɓacine da damuwar daya nuna akan matarshi a gabana, sai ya zage ya dinga mun abubuwan da yasan inaso sosai. Sai da komai ya lafa kishin yaci gaba da nuƙurƙusata. Shi fa gogan yama yi baccinshi niko idanuna biyu ina kallon hawa da saukan numfashinshi. Ina aiyanawa a raina, ko wanne irin kalami yake ma Hama oho, gashi ya iya soyayya mai sanyi da tsaiwa a rai. Nina ɗauka irin wannan soyayya sai mutanen birni, ashe abun baiwane daga Allah. Sannan ya danganta da yadda namiji yake son mace. Su fulani Allah yayi su da iya soyayya da son mace sosai. Sai Allah ya basu basirar iya tattalin macen gashi dai rayuwarsu a ƙauye, mazan kuma rabin rayuwar a jeji ma suke yi. Wannan dalilin yasa matan fulani sunansu yai shura wajen kishi da yima kishiya mugun asiri. Ajjiyar zuchiya nayi na shafi fuskar ɗan fulanina ina murmushi. A haka bacci ya kwasheni. Amma me zai faru ina cikin bacci sai naji kamar ana tsaye a kaina. A razane na tashi zaune dafe da ƙirjina, hakan yasa Yaya Hamma ya tashi shima, yana riƙe dani ni kuma na runtse idanuna Wannan inuwar tana saitina. A zahiri ina ganin inuwa, a cikin jikina kuma ina jin halamar mutum a tsaye a kaina. Yaya Hamma yana tambayata menene, ni dai adda’a nake yi babu ƙakƙautawa da ƙyar na buɗe idanuna sai naga wayam babu wannan inuwar. Ajjiyar zuchiya na sauke na kwantar da kaina akan ƙirjinshi. Hannu yasa yana shafar bayana mai cike da tsoka yana mun raɗa a kunnena.
“Menene ya tsoratamun ke Jabu, mafarki mummuna kikayi?” Ni dai sai ajjiyar zuchiya nake saukewa, a hankali ya kwantar dani yana shafar kaina. Ni dai harya koma baccinshi , idanuna biyu. Dana rufe idanu sai wannan inuwar ta dawo, dana runtse idanu nayi adda’a inna buɗe sai inga babu, gashi babu tsarki a jikina ƙaƙa_sara_ƙaƙa. Babu damar yin sallah. Adda’a inna kamo wannan sai in faɗa waccan cikina ya duri ruwa sosai da sosai. Daren yayi tsayi kafin garin ya waye. Ko da na shiga bayan gida yin wankan sallah ina tsaka da yin wankan sai naji kaina na juyawa tsigar jikina na tashi. A lokacin ji nake yi kamar in fito tsirara dan tsoro da firgici. Da ƙyar da ɓarin jiki na gama wankan, na fito na tarar Yaya Hamma ya tafi masallaci. Ina ganin ɗakina amma wallahi na kasa ɗaga ƙafata in shiga. Dana gaji da tsaiwa da ɗaurin ƙirjin kamar mahaukaciya sai gani a ɗakin Baɗɗo. Ko ita data ganni saida ta tsorata.
“Adda lafiya kika fito haka, ko wani abun ya sake haɗaki da Yaya Hamma ne?” Sai naji hawaye na zuba a idanuna.
Babu komai ke dai jeki ɗakina maza ki ɗakkomun kayana in saka zanyi Sallah “
Baɗɗo tayi maza taje ta ɗebo mun kayan nawa nasa nayi Sallah a ɗakinta. To a gaskiya a wannan lokacin nayi sallar ne, amman bana ce ga abinda na karanta ba. Inyi adda’a na kasa sai naji zuchiyata tayi wani irin mugun cunkushewa. Sai kawai na saki kuka. Baɗdo na shirin fita na kirayi sunanta.
Karki kira Yafendo, ki riƙe mun sirrina Baɗɗo. Ke dai ki taya ni da adda’a dan auren ya isheni ya fice mun aka zaman ƙauyannan.” Shiru tayi kamar ruwa ya cinyeta. Ni kuma sai kuka kawai nake rerawa a haka Yuguda ya shigo ya iskemu. Ya tambayi Baɗɗo wani abun ya sake faruwa ne. To itama ba sani tayi ba, juyawa yayi sai gashi ya dawo tare da Yaya Hamma, sai suka fita suka bamu waje, suna fita na faɗa jikinshi na ƙara fashewa da kuka. Ƙanƙameni yayi wallahi ina jiyo dukan da zuchiyarshi take yi, jikinshi har rawa yake yi. Ya kasa cemun komai bai hanani kukan ba, sai bayana yake shafawa. Da yaga bani da niyyar yin shirune ya ɗagoni muka haɗa idanu idanunshi sun zama kamar gaushi, fuskarshi ta dawo kalar tausayi, ga soyayya muraratan ina karantawa a idanunshi, fuskarshi, dama gangar jikinshi. Muryarshi a dakushe yace.
“Menene ya faru, me akayi miki kike kuka haka, bakya jin tausayinane, ko dan kinga bana son kukanki ne shi yasa kikeyi dan ki horani?” Idanu ya lumshe ya buɗe su a kaina.
Yaya Hamma wallahi ina sonka, Allah ya gani inason zama dakai, ina son ƙare rayuwata dakai. Amma…..” Da ƙarfi ya mayar da kaina ƙirjinshi numfashinshi yana hawa da sauka. Banyi aune ba ya ɗagoni ya zura bakinshi a cikin nawa, tsabar ina sonshi haka na dinga shan wannan yawun mai ɗan bashi, dukda yana goge bakinshi kafin yaje masallaci. Ni ko goge bakin nawa banyi ba. Mun daɗe a haka kafin ya dubeni, nima shi nake kallo sonshi na sake ninka kanshi a zuchiyata.
“Mu tafi ɗakinmu Kar muyi abun kunya a ɗakin ƙanne”
Ba musu na bi bayanshi. A ɗakin Yafendo muka yada zango muka gaisheta.
“Dada yau batai ɗumamen safe ba, jiya mun kwana bata jin daɗi. Amman zata ba Baɗɗo ta dumama kafin Amaduyal yazo ɗaukar abincin Dada”
Kaina na sunne. Yafendo tace.
“Ayya sannu Jabu Allah ya ƙara sauƙi”
Kaina na ƙasa na amsa mata da ameen.
A wajen na sulale na fito na barshi. Baɗɗo har ta shiga ɗakina ta fito da ɗumamen ma. Tana tsaye da Amaduyal suna tattaunawa na isa wajen ina ƙaƙaro fara’a.
Me ake tattaunawa ne Amaduyal?” Dariya yayi yace.
“Adda jiya da daddarene Yusufu yazo yake faɗama Dada wai yau za’a ɗaura auren Cubu. Ya bada aurenta ma abokinshi Baffa Modibbo” Idanu na zare.
Abokin Baffan naku akaba Cubu yarinya karama da’ita. Ita za’a ba tsoho?’ Baɗɗo tace .”
“Hmm ai tunda Baffa ya faɗa babu makawa. Damma Baffa Modibbo dattijon arzikine. Sai dai Hajaru ƴarshi aminiyar Cubu ce, tare suke zama a wajen saida Nono.” Shiru nayi lamarin duk yabi ya dameni ya addabeni. Ga matsalar data tunkaroni, ga kuma wannan matsalar. Ajjiyar zuchiya na sauke.
Dada me tace da taji wannan labarin? Na tambayeshi.
“Babu abinda tace face fatan alkhairi. Ai aurenta yafi zaman gidan. Dan ke bakya zuwa gidanne da in kika ga irin rayuwar da sukeyi sai kinyi musu kuka. Gidan Baffa Modibbo kuma abinci me kyau suke ci. Kuma matanshi basa tallar Nono yana da yawan shanaye, kuma sha’awar haɗa iri dasu akeyi.” Shiru nayi ina hango cutarwar da hakan zai haifar. Amman yana iya, babu har sai naji ta bakin manya, duk da suma da halama babu abunda zasu iya. Ɗan daɗin da naji mata bai wuce na barin hannun matan ubaba, da kuma samun ƴanci daga gantalin zuwa tallar nononnan. Ita kanta Baɗɗo da sannu zan hanata wannan tallar nono, ta kama sana’ar yi. In kasuwancinta na man shanu ya kankama da Uwani shima zai rage wani abun. Dan Uwani tace ta dinga soyawa tana tara mata ko na nawa ne in tazo, ko inni zanje a tafi mata dashi. Amaduyal yace.
“Dama Yafendo nazo faɗama. Baffa Musa yace mu je duka mu sameshi a gida har daku. Bari inje wajen Yafendo” Ya tafi ya barmu. Na dubi Baɗɗo nace.
Kar ki faɗama kowa halin dana shiga Baɗɗo. Babu kuma abinda Yaya Hamma yayi mun ke dai ki tayani da adda’a kawai” Murmushin jin daɗi tayi tace.
“To Shikenan Adda, Bari in ɗunduma tuwo in kawo muku naku”
To
Kawai nace, na wuce. Ina zuwa ƙofar ɗakina ai sai na doge, tsigar kaina taci gaba da tashi. In shiga na kasa tsoro nake ji. A wajen Yaya Hamma ya sameni. Hannuna ya riƙe muka shiga bayan nace.
A’uzubillahi minal shaiɗanun rajim.
Ina sauke ɗayar ƙafar a cikin ɗakin sai naji abu ya kuma shiga jikina. Take sai ɗakin ya shiga jujjuyamun. luuu nayi na tafi zan faɗi, Yaya Hamma ya taroni, amma tare dashi muka faɗa kan kujerar nayi mishi nauyi bazai iya taroni ba. A zabure ya miƙe yana jijjigani. Ni kuma na kasa buɗe idanuna dan ɗakin jujuyawa yake yi dani. Adda’a kawai nake yi ina girgiza kai ina hawaye. Nafi minti goma a wani hali wanda bazan iya fassarawa ba da ƙyar na dawo daidai. Na faɗa ƙirjinshi ina kuka.
Ni Allah bazan zauna a ɗakinnan ba sai dai ka canja mun ɗaki. Ko kuma in tafi Kano”
Kanshi kawai ya ɗaga sama yama rasa me zaice. Sallamar Baɗɗo ne yasa ya sakeni ya tashi.
Tiran hannunta ya karɓa ya shigo dashi.
“Sakko ki karya. Sai in kaiki gidan Dada ki zauna. Inna dawo aiki zan biya in ɗaukoki hakan yayi miki Jabuna kafin mu nemi mafita?”
Kai na gyaɗa mishi halamar yayi mun. Hakan kuwa akayi muna gama cin abincin muka fito tare, ya bani dubu ɗaya yace in yi girki acan in naje muci Yafendo bata nan ma ta tafi kiran Baffa musa, Baɗɗo ke faɗa mana. Saina dubeshi nace.
To kaje aikinka zamu je gidan Baffa Musa ni da Baɗɗo. Zan tafi da yaran sai mu wuni acan gidan Dada” murmushi yayi mun yace.
“To Shikenan. Ki kula dan Allah. Saina dawo, ku gaishe da Baffa Musan. Amman me akeyi acan gidan nashi da ni ban sani ba?”
Baddo sai ta bamu waje, ta haɗa kan yaran suka fita. Ni kuma na labarta mishi abinda ake ciki da ƙin auren da nakeyi sabida hakan ka iya cutar da lafiyar Cubu. Shi kuma ya nuna mun ai babu komai kuma ba’a kanta aka soma ba, kuma gidan da zata shiga gidane mai daraja gidan arziki. A haka dai mukai sallama shi ya tafi aiki, mu kuma muka nufi gidan Baffa Musa.
Acan tattaunawa kawai akayi akan gudunmawar da zamu haɗa, bawai akan auren dole da tsoho da za’ayi mata ba.
To kayayyakin ɗakina da sukai saura suna gidan Dada nasa an ajjiye mata harda kujera 1_1. Na ware mata dogayen riguna da zanin gado har kala uku masu kyau, ta samu kular zuba abinci mai tsada da tire harda plate da tsokali. Ni duk wata gudunmawata na ajjiyeta tuni. Nan muka gama tattaunawa mukai ma Baffa Musa sallama muka tawo gidan Dada harda su Yafendo A’i. Daga nan suka shirya dan zuwa gidansu Cubu, amman ni ban dani, ni sai zuwa gobe in an kaita ɗakinta sai inje ayi yinin biki dani. Bodi ( keken shanu) suka tafi da kayan zuwa can gidan Mai Nagge. Ni da yarana kuma mu kai zamanmu a wajen Dada.
Wankinta na tattaro na fito dashi tsakar gida, na soma wankewa. Mai sunan Yafendo kuma na kirata na aiketa siyo kayan miya da garin tuwo. Ina gama wankin Dada na shiga aikin kwalime mata ɗaki, ga miyar kuka harna kaɗa na maida ruwan tuwo.
“Jabu sai yaushe kayanki zasu zo ne, maƙota suna yawan shigowa neman kaya sai dai Kari tace musu kayan suna hanya” Ninkin kayan na ɗan dakatar nace.
Dada suna hanya. Da zaran sun iso zaki ga Uwani zata kawo mun. Gobe ma inaso zan shiga gari gidan matar ogan Yaya Hamma in dubosu. Zan kira Uwanin a waya muji.”
Kai kawai Dada ta gyaɗa mun. Na ci gaba da aikina sai da mukayi sallar muka zuba tuwo da zafinshi muka ci muka ƙoshi dam. Dama har dare nayi tuwon dan inna koma gida bazan yi girki ba. Tsiren da ya zamema Yaya Hamma jiki wajen siyo mun, shi zanci in sha tea abuna. Ƴan biki sai magriba suka dawo niƙi_niƙi da tuwon biki an kawo ma Dada nata. Yafendo A’i tace.
“Jabu har yanzu baki tafi gidanki ba?” Murmushi nayi mata nace.
Yace in ya dawo zai biyo mu tafi. Sannunku da dawowa” Suka shiga ciki. Baɗɗo ta tsaya a wajena tace.
“Adda dama a wajen bikine adda Daso take faɗan wai Hama ta kusa dawowa. Kuma kullum sai Yaya Hamma yaje wajenta. Yanzu haka ma tace ba zata dawo ba saiya sake mata kayan ɗakinta kab. Sai garashi take yi sunata cin kuɗinshi” Jim nayi ina nazarin maganganun Baɗɗo. Kullum sai yaje wajen Hama? Maza mutananmu kenan. A zahiri nace.
“Ita Dason dawa take wannan hirar?”
“Da Sadiyan Yafendo A’i suke hira. Har tana faɗa mata wai hatta dukan Hama da Adda Uwani tayi ashe sai da Yaya Hamma ya ba Hama dubu goma wai kuɗin magani” Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
Hmm wannan a wajen namiji ba komai bane Baɗɗo. Babu komai. Ina mamakin yadda Daso ƙiri_ƙiri ta zama maƙiyiyata akan kawai Yaya Hamma.”
Zuwa bayan Isha su Baɗɗo duk suka watse bayan sunci tuwon biki, yaran ma Yafendo ta kama hannunsu suka tafi tare Tuwon da nayi ma sai dai su Dada su ci da safe dan ko buɗeshi ba ai ba, sun samu na gidan biki mai nama. Ni dai ina tsakar gida jigum nayi zurfi a cikin tuntuntuni sai ga sallamar Yaya Hamma. Ɗagowa nayi na kalleshi, shima ni ɗin yake kallo. Sai wani murmushi yake yi mun. Ni kuwa haushi murmushin ya ƙaramun.
Sannu da zuwa” Iyakar abinda na ce dashi kenan. Sai ya sha jinin jikinshi, ya fuskanci raina a ɓace yake.
“Dada fa?”
Tana ciki, yanzu ta shiga” Sai ya kutsa kai cikin ɗakin. Ya daɗe a ciki kafin ya fito yace in taso muje.
Sallama nayi musu na bishi muka tafi. Tun fa a hanya yake magiyar in faɗa mishi menene ya ɓata mun rai. Amman amsa ɗaya nake bashi cewar babu komai. A haka har muka iso gidan. Matan gidan suna tsakar gida, tare da matan maƙota da nake ma karatu. Suna ganina suka soma murnar ganina. Haƙuri na basu akan sui haƙuri sai gobe zamu yi karatu, duk na sallamesu suka tafi gidajensu. A ɗakin Yafendo na samu Yaya Hamma tana mishi maganar Hama. Da naji haka saina gaisheta na fice abina na jirashi a ƙofar lungunmu harya iso muka shiga.
Ina shiga ɗakin sai gabana ya yanke ya faɗi haka. Cikin dauriya muka sha tea da balangu da masa dai mu kai shirin kwanciya. Baccin da bai yiwu ba kenan fa. Irin na daren jiya sai abinda ya ƙaru dan ɗakin har jijjiga naji yanayi ƙasa na zubowa.
Wannan yanayi sai ya zame mun jiki, ni da bacci sai na rana, kuma sai dai in wuni a tsakar gida ko wajen Yafendo dai. Mu’amalar aure ba sai ta gagara ba.
Sai mun haɗu zuwa gobe kuma✍🏻
Mrs Bukhari
Part 11
NAMA YA DAHU….
ROMO ƊANYE
BADI’AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
LITTAFI NA UKU (11)
IYABO:.
Ba sai ina tare da nutsuwa bane har zamu iya mu’amalar aure ba? Banfa mance da furucin Hama ba yananan daram a raina. Ban ɗauka zata iya mun komai ba face abinda yazo a zanen ƙaddarata shi yasa.
Haka dai nake ta gurgura rayuwar watana guda cur a cikin wannan yanayi marar daɗi. Amman in fa gari ya waye na baro ɗakin Shikenan zanci gaba da harkokina. Ga ɗalibaina da suketa ƙara yawa yanzu harda ƴan mata. Ganin sunyi yawa saina sanya musu nera ashirin ashirin duk sati kuɗin laraba. Daga koyarwa ba saina soma buɗe musu karatun yadda zasu kula da kansu ba? Karatu kunga ai ya ƙara armashi. Ranar dana koma asibiti karɓar maganin ciwon ido, wanda duk wata ba fashi ina zuwa, duk da idonma yanzu ko inuwar bana gani ya riga daya mutu mus wallahi, kuma duk inda Yaya Hamma, ko Yafendo suka ji mai maganin ciwon ido sai sun karɓomun, amman dai ido ya riga daya mutu mus, nace ma bazan sake komawa asibitin ba. Saina kira uwani nace in zata zo ta shiga kurmi ta saromun magungunan mata ta tawo mun dashi, dasu turare ɗan ɗuri, da janbaki, hoda, gazal, kayan dai kwalliya a jimlace, da su yari.
Wannan matsalafa tana damuna. Wata ranar talata muna kwance Yaya Hamma yana murƙususu yana buƙatar mace, gashi bansan dalilin rashin tarewar Hama ba. Sai nace dashi ina kuka.
Ka taso muje ban ɗaki in biya maka buƙatarka. Ko muje garken Shanu”
Kallona yayi sai yayi murmushi.
“Ke da kike fama da lalura yaushe zan kai ki banɗaki. Nayi magana da Baɗejo gobe ke da matarshi zaku je gidan magani” Hawayena ya shiga sharemun. Ya ja hannuna muka fita, ina biye dashi sai gamu a ƙofar ɗakin Hama.
Yaya Hamma me zamu yi anan?” Ya kalleni da runannun idanunshi wanda suke sani kasala a kunnena yace.
“Duminki kawai nake son inji. Ina kewarki fiye da tunani”
Idanuna na lumshe a zuchiyata ina roƙon Allah ya kawo mun mafita. Adda’a inayi babu dare babu rana wallahi.
A.a ni bazan shigar mata ɗaki ba. Duk da babu kayanta a ciki. Amman ai ɗakinta ne, koni kayi ma haka na samu labari bazanji daɗi ba.”
Baice dani komai ba ya jani zuwa garken shanunnan. A tsakankanin shanu muka gudanar da soyayyarmu, ina kwance a cikin kashinsu. Kuma ya bani kulawa sosai ga kewar juna dama munayi sosai.
Me zai faru, wallahi sai ga bacci. Watana ɗaya da kwana goma cib baccin dare yafi ƙarfina kaina kamar zai buga. Shi kuma jin daɗin nayi bacci yasa sai ya gyaramun kwanciyata, shima yayi kwanciyarshi. Gamu a tsakankanin Shanu suma suna kwance. Kiran sallar assalatu ne ya tashemu.
Kunga ya tabbata a cikin ɗakina matsalar take kenan. Gashi Bama son kowa yasan matsalar dake faruwa a tsakaninmu
Mu kai wanka, shi ya wuce masallaci ni kuma na wuce garke wajen tatsar madara.
Matan gidan duk suma suna wajen ko wacce tana aikin dake gabanta. Sai wani habaici da sokiburutsun zantuka na jahilci da rashin wayewa suke yi. Wanda ya zame musu jiki. Dan ni kam a tsakaninsu dani ko ga miciji bamayi. Haka Baɗɗo ta zama saniyar ware a cikinsu. Suna gani ina koyarwa, amman ɓakin hali da gabar da suke yi dani yasa suna son makarantar, amman ba damar shiga. Gashi sai cika ake kuma yi. Yafendo ma tace a gina mun rumfa sabida lokacin damuna ruwa bazai barmu yin karatunba.
Da rana ina tsakar gida ina wanke_wanke sai ga sallamar Uwani. Ga wasu matasa a bayanta ɗauke da dilar kaya. Itama ga jakar kayanta a buhun Kano ta ɗau zafi tanata faman kici_kici.
Da sauri na wanke hannuna tsab naje na amshi buhun Kano ta ɗau zafin a hannunta. Yaran kuma na nuna musu ɗakin Baɗɗo a ciki suka sauke mun dilar. Na basu tukuici suka fice suna godiya.
Sannu ta balbalin kin shawo rana”
“Ke dai bari Iyabo. Ana kwanɗa rana da zafi. Bari mu gaisa da Yafendo tukunna.”
Ta wuce wajen Yafendo. Ni kuma na shinfiɗa mana tabarma a barandar kofar ɗakin Hama. Na cika mata ruwa da kofin sulba ruwan na randar ƙasa mai sanyi. Na zubo mata jallof ɗin shinkafar manja mai bushasshen kifi. Itace farkon zuba ma, dan yanzu na sauke. Na zuba na Yafendo na miƙa mata, muka fito tare da Uwani.
Ga tabarma can a inuwa kije ki zauna kisha ruwa mai sanyi, zan zuba ma yara abinci sai inzo”
“Iyabo ko laulayin ciki kikeyi ne, kinga yadda kika zuge kuwa?” Hawayene ya cika gurbin idanuna tab. Da ƙyar na saisaita kaina nace.
Tabalbalin akwaiki da wutar ciki. Inma cikinne dani duk zaki ji ai. Ina zuwa”
Kitchen na wuce, ita kuma taje ta zauna a wannan shinfiɗa da nayi mata. Ina zuba ma yara abinci saiga matar Baɗejo ta leko.
“Malama sannu da aiki. Kin ganni sai yanzu. Wallahi wanki nayi ne shi yasa”
Duk ɗalibaina da malama suke kirana. Ɗagowa nayi nace.
Ayya babu damuwa. Dan Allah zuwa wajen maganin mu bari bayan la’asar baƙuwa nayi daga Kano. Bari in zuba miki abinci ko yara kya ba suci.
Na cika mata ɗan china da shinkafa taita godiya. Suka gaisa da Uwani ta fice. Saida na sallami yaran nazo na zauna a kusa da Uwani “
MARAƊI
Tare suka faɗi rakwatsam a cikin bokatai. Sabitu yana kan burgujejen tumbin Yaya Tasi’u.
Hadiza kuma duk zafin dukan da Sabitu yayi mata bai hanata yima Gwadabe dariyar mugunta ba. Data kalleshi a tsakiyar kwallaye tsamo sai ta kuma tuntsurewa da dariya. Shi kuma kunya duk ta lulluɓeshi ji yake inama ƙasa ta tsage ya faɗa ko ya huta. Haka ya yunƙura ya bi bayan su Auwala ya bar Hadiza a ƙasa tana dariyarshi.
Da sauri Sabitu ya ɗaga Yaya Tasi’u. Sai da Mammada ya taimaka ma Yaya Tasi’u kafin ya iya tashi abinka da mai jiki.
“Meke faruwa, duk me ya kawo wannan rikicin?”
Yaya Tasi’u ya tambaya yana zazzare idanu. Hadiza ce ta fito ta bashi labarin sale_salin rikicin, da zuwa zaneta ta yayi har ɗaki”
“Bazan lamunci wannan iskancinba. Rashin darajar matarka yayi yawa da kowa faɗa take yi. Ka sani duk ranar da matarka ta sake takalo rigima irin wannan a gidannan to daga kai har ita ba zaku ji daɗi ba. Akanme kuma zaka bi Hadiza har ɗakinta ka daketa sabida matarka, kuma shima Gwadabe har ka tureshi. Mace na nema ta mayar dakai sususu shashan banza.”
Nan Yaya Tasi’u yaita ruwan faɗa yana hargagi.
“Duk kuje ku kwanta. Banason jin wannan maganar a cikin gida a kiyaye lafiyar malam. Zan saɓama duk wanda ya shigar da labarin gida har yaje kunnen malam. Gwadabe kayi haƙuri. Kema Hadiza kiyi haƙuri, kuma ki kiyaye kinsan Sabitu dashi da matarshi duk ƴan hau ne tuburarrune”
Nan Yaya Tasi’u ya kashe kes ɗin, kowa ya shige ɗakinshi.
Ko washe gari Gwadabe bai leƙa ɗakin Hadiza ba balle yaga yata kwana, kuma ya gani ko Sabitu yayi mata rauni.
Itama da damuwar abu biyu ta kwana. Damuwar rashin haɗin kan gidansu, da damuwar maganganun matar Sabitu. Waɗannan abu biyu su taita tubka a kansu tana warwara. Ta wayi gari da baƙin cikin fishin da Gwadabe yake yi da’ita wanda a yanzu tayi imani Shafa tasan fishi yake yi da’ita.
Yau monday dukkansu ficewa wajen aiki suka yi
Hadiza na dawowa ta ɗaura farfesun naman kan rago data siyo. Ta jiƙa shinkafar tuwonta dan lafiyayyar masa take so tayi musu suci da romon ganda. Da ɗan dama ta jiƙa shinkafar dan tana son ta miƙa ma Malam shima tasan yana son waina.
Sai ta shiga aikin ƙalƙale ɗakinta
A zahiri Hadiza irin matannanne da zaku ga komai na ɗakinsu ƙal filin tsakar ɗakinsu sai kaga kamar ba’a takawa. Badai kaga datti, ko ƙura ko ƙasaba. Komai kuma yana zaune a muhallinshi. Shafa na da nata irin tsabtar amman ba irin na Hadiza bane, dan irin su Hadiza har cewa dasu akeyi masu aljanun tsabta, in tsabta tana yawa to tasu tayi yawa ma. Data gama ƙalƙale dakinta ta fito ta shiga gyaran kitchen. Shafa na barandar ɗakinta a zaune tana wasa da Abba sai dariya yake yi. Daga haka sai Hadiza ta jiyo kakarin aman Shafa a bayan gida.
Da sauri ta iso ƙofar bayan gidan tana tambayarta me taci, ko dama bata da lafiyane?
A galabaice ta fito ta zauna.
“Lafiyata ƙalau Yaya, kuma ni banci wani abu da zai tayar mun da zuchiya ba. Tun safe nake jin jikina wani iri haka dai. Sai jiri da nai ta ɗan ji a wajen aiki. Amman inaga gajiyar hanya ce.
Shiru Hadiza tayi tana karantar yanayinta. A cikin zuchiyarta tace
“Shafa dai ƙarfi da yaji itace uwargidan Gwadabe. Ni dai nawa uwargidan sunane. To mi ya rage, ta haifi ɗa namiji gashi babba. Yanzu daga dawowarmu har Gwadabe ya ɗirka mata wani cikin zata kuma rigani haihuwa, ni shikenan na zama ƴar kallo. A zahiri kuma Hadiza tace.
“Bazai wuce gajiyar ba. To Allah ya ƙara sauki. Bara inje gida zan aika almajiran malam sui mun markaɗe inna gama gyaran gidana” Shafa tace.
“To sai kin dawo. Ni kam banji duriyar ummi ba tunda kuka dawo ko kukanta ban jiyo ba?”
“Ummi iyayen rigima tanata bacci. Yanzu sai dare yayi mu ta hanamu baccin ” murmushi kawai Shafa tayi. Hadiza ta ƙarashe gyaran kitchen ta kwanke banɗakinta, ta ɗauro alwala. Sai da tayi salla kana ta fice ta bar ganda akan gawayi a hankali gawayin yake ci babu yawa tasan ƙila ma mutuwa zaiyi nanda ɗan wani lokacin. Hadiza dai harta gama tuyar masarnan tana ta aikin tunani duk ta shiga damuwa. A sanyaye ta miƙa ma matan yayunta masa, tasa mayafi ta kai ma Baba Fhatsima tace ta ba Malam.
Zuwa taran dare saiga Gwadabe ya shigo. A lokacin tana tsaye taci kwalliya da riga da wando, ga kanta yasha kitso. Ummi na bayanta tana jijjigata sai ƙananan kuka take yi.
“Sannu da zuwa” Ta faɗa tare da karɓar ledojin hannunshi ta ajjiye a gefe.
Akan daddumar data jera kulolin abinci da duk abun buƙata ya zauna.
“Yauwa. Meya sameta ta hanaki zama” dukkansu babu yabo babu fallasa a fuskokinsu.
“Rigimace kawai” Murmushi yayi yace
“Kuntota, kije ki kirawo Shafa muci abinci yau a mugun gajiye nake sosai” Umarninshi tabi ta kunto ƴar ta bashi, taje ta kirawo Shafa suka tawo tare.
“Sannu da dawowa” Sai ya washe bakinshi yace.
“Yauwa Shafa ya gidan, ina Abba?” Hadiza tana zuba abinci tana kallon yadda Gwadabe yake mata fara’a tana jin ciwo.
“Bacci yake yi, yana kan kujera a falo”
Tana faɗar haka zuruf ya miƙe ya ajjiye ummu akan kujera ya fice. Hadiza ta kalli ummi data canyara kuka, ta dubi Shafa taji wani abu ya riƙe mata maƙonlatonta. Sai ga gwadabe da Abba a kafaɗarshi. Hadiza ta ɗauki ƴarta ta goya ranta ya bala’in ɓaci sai taji abincin ya fitar mata ma aka.
Allah ya taimaketa tana goya yarinyar sai tayi bacci. Suna tsaka da cin abinci sai Shafa ta fita a guje amai yazo mata. Da sauri gwadawa ya bita da Abba a hannunshi. Hawaye suka zubo ma Hadiza a kumatunta ta yi maza ta share hawayen ta rurrufe kwanukan abincin ta wanke hannunta ta shigewarta ɗaki tayi kwanciyar rub da ciki ummi na bayanta. Tuƙuƙin kishi zai murɗa mata yake yi. Gwadabe yafi awa guda kafin ya shigo.
“Hadiza daure ki ɗan dafa ma Shafa tea sai ki haɗa da balango a cikin ledar dana shigo da’ita in kai mata”
Namiji tuwon ƙaya miyar allura
Tean ta haɗa ta kawo mishi da naman ita bata rabo da ruwan zafi a filas, nanma saida yafi minti talatin kafin ya dawo.
Ya tarar Hadiza ta kunce ummi ta mata shinfiɗa itama tana kwance tayi shiru tana zubar da hawaye. Kwanciya Gwadabe yayi a kusa da’ita ya jawota jikinshi ya haɗa bakinsu waje guda. Daga nan labarin ya canja salo. Tsakanin mata da miji sai Allah. A daren Gwadabe ya wanke laifukanshi. Sukai baccinsu mai daɗi, da asuba ma bayan ya dawo masallaci ya jawota jikinshi suka koma ruwa.
Shikenan fa maganar ta ƙare.
Hadiza sai ta dena ƙorafi sam, duk abinda ta gani saidai ta cinye damuwar abun na cin ƙasan ruhinta.
Laulayin dai ciki ya tabbata bil haƙƙi akan Shafa cikinne dai da’ita. Cikin irin mai shegen laulayinnanne Anty Badi’a sun dawo daga tafiya suka tarar da Shafa babu yadda take. Ko me taci amai take yi farfesun kifi ne kaɗai take ci ya zauna mata. Tama dena girki kwata_kwata farfesun kifinma indai ita tayi bata iya ci, sai Hadiza ta ɗauke mata.
Shi kuma goga gwadabe fa ganin canjin da aka samu a wajen Hadiza sai ya zamana ya ƙara sonta, ya ƙara zagewa wajen kulawa da’ita. Kuma ya mata godiya sosai akan canjawar da tayi dan yaji daɗi gaya.
Ita kuma matar Mammada Allah bai bata haihuwarba ita kaɗaice a cikin matan gidan bata haihu ba, duk matan gidan goyo suke yi, sai ita kaɗai da ko ɓatan wata bata taɓa yi ba. Ga Shafa ta samu ciki tana jin yayi wuri dama bata samu ba. Ga matar Mammada tana dama itace Shafa. Haka Allah dama yake yin ikonshi.
A cikin gidan malam ta ɓangaren matanshi yawan faɗa da yawan rikici yayi sanyi sosai. Sai dai fa ko wacce ta ciki na ciki. Sunyi haƙurine sabida yanayin jikin Malam, da kuma sakin Baba Suwaiba da yayi. Wannan yasa Baba Asshi ta sassauta faɗanta dama itake haddasa yawanci fitintinun gidan. Tayi zuchiyar dena zuwa turakar Malam ma a tunaninta zaita binta yana rawar ƙafa akanta. Irin yadda yaima Baba Fhatsima data dena zuwa turaka, sai taga saɓanin haka. Ba shiri ta watsar ta koma akaci gaba da rabon kwana da’ita. Matar Malam kuma ciki gareta tana fama da laulayi, yau an bata gado a asibiti, gobe tana gida, yau amai, gobe yawu dai. Yaran matan da akaima aure, Malam ya kafa musu dokar dena zuwa mishi gida barkatai, sai matsalolin cikin gidan ya ragu. Sai matsalolin can gidan wanda wannan Yaya Tasi’u da Yaya Jamilu ne akai. Malam yama dena sanin meke faruwa.
Ta ɓangaren Baba Fhatsima kuma ta roƙi Yaya Tasi’u ne akan ya auri Balaraba tunda ta lura har gobe suna son junansu. Ta bashi kwana biyu yayi tunani. Ya dawo bayan kwana biyun yace mata ya amince.
To a halin yanzu hidimar haɗa kayan akwati akeyi. Harma an fitar da lifaran (ankon biki) Anty Badi’a ko da Yaya Tasi’u ya tareta da maganar ƙarin auren. Sai tayi mishi fatan alkhairi tare da yi musu adda’ar zaman lafiya. Jin daɗin hakanne yasa ya biya mata Umara. Ta tafi da kwana ɗaya aka ɗaura auren. Bikin daya tara ƴan uwa da abokan arziki. Amarya Balaraba ta tare a ɗakinta, akaita amarci. Saida suka cinye amarcinsu kafin Anti Badi’a ta dawo. Kafin ta dawo tazo ta tarar Yaya Tasi’u ya sake mata komai na ɗakinta, tayi mishi godiya, ta kuma rungumi Balaraba suke zaune lafiya, sai ɗan abinda ba’a rasawa. Wannan dalilin ya ƙara ɗaga daraja, girma, da kimar Anti Badi’a a wajen iyayen Yaya Tasi’u dama ƙannenshi ƴan ɗakinsu.
Ta bangaren matan Gwadabe kuma rayuwar tana ta buɗe musu, Gwadabe yana ta samun ciniki. Kwatsam ranar wata Juma’a sai ga kiran Zulƙi yana sanar da Gwadabe akwai taron manya da za’ayi a garin Abuja ranar monday. Yana so gobe yaje Takai ya sameshi sai su wuce taron tare ya tafi da maganinshi.
Ai kuwa hakan akayi shadda kala biyu Gwadabe ya ɗinka, ya sai takalmi mai tsada da hula. Ya ɗauki akwatin magungunan shi yaima matanshi sallama sai Takai. Kwananshi ɗaya a wajen Bara’u ranar Lahadi suka shiga Abuja. Washe gari Gwadabe yabi Zulƙi zuwa wajen taron. Kamar wata ƴar liyaface aka haɗa na Gwamnoni, da ƴan majalisu, da Chiyamomi, harda sarakuna.
Alkhairi da Gwadabe ya samu a wajen wannan taron bana wasa bane. Saida ya saida maganinshi tas ya dafe kuɗaɗenshi. Suka sake kwana a Abuja. Washe gari Gwadabe ya dawo Nijar, Zulƙi ya wuce Takai.
Cikin dare Gwadabe ya shiga gida, a ɗakin Hadiza yake harta yi bacci sai gashi. Yayo musu tsarabar sutura, da kayan kwalliya da turare. Kuma yai musu ihisani da kuɗi mai ɗan tsoka. Sukaita shi mishi albarka. Shafa kuma ya bata kuɗin siyan kayan jariri ta soma ajjiyewa duk da cikin watanshi ukune kawai, ganin ya samu kuɗine yake ganin bari a soma ragewar dai, tunda shi ɗinne dai zai siya.
MRS BUKHARI
Part 12
NAMA YA DAHU…
ROMO ƊAÑYE
BADI’AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
LITTAFI NA UKU
12
IYABO
“Wai Iyabo laulayi kike yi ne, ko ciwo kika yi mun yi waya har sau biyu dake baki sanar mun ba? Anya kina kallon mudubi kuwa? Kin ƙare kin lalace ko dai babu zaman lafiya tsakaninki da Hamma ne.
Ga ɗakin kishiyarki na leƙa sai naga wayam.
Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
Uwani halin da nake ciki yafi ƙarfin duk wannan lissafin naki. A cikin dabaibayi nake, cikin rijiya mai gaɓa dubu.” Wasu siraran hawayene suka gangaromun nayi sauri na share su. Labari naba Uwani na halin da nake ciki. Saida ta zubar mun da hawaye bayan ta gama saurarena.
“Yanzu kina cikin irin wannan halin mawuyaci kika kasa sanar dani Iyabo? Kuma sai yanzu kuka yinƙura neman magani ma?”
Uwani ina kai kukana wajen Allah shine zai mun maganin duk abinda ke damuna. Ni ko gidan magani da Yaya Hamman yace muje yau bana son yi mishi musu ne kawai shi yasa zanje. Amman da shawartata yayi da kukana zanci gaba da miƙawa wajen Allah yana sane dani bai mance dani ba. Ni garinne ya fitarmun akaina, auren ma ya fice a raina, sai inji kamar in yi ficewata in tafi ma kawai.” Uwani ta dafani tace.
“Komai yai tsanani sauƙi na nan zuwa. Duk abinda yai farko dole yai ƙarshe Iyabo. Amman kam kishiyarki ce tayi miki asiri ko kin ƙi, ko kinso tunda ai ta faɗa miki sai zaman gidan ya gagareki, kuma sai kin fita tsirara. Rashin bacci ai somi_ somin haukane. Amman muje wajen mai maganin muji me zaice mai kuma zai bamu. Kinga tashi kawai muje gidan matar abokin Hamman kawai mu wuce.”
Ko abinci Uwani bata ci ba, ta dai sha ruwa. Allah yasa abincin dana dafa tazarce nayi har dare na cika babbar kula na dare. Sallama naima Yafendo nayi mata ƙaryar zamu je gidan Cubu Uwani ta gano ɗakin.
Muna fita sai gidansu Baɗejo, dama matarshi a shirye take goyo kawai tayi muka wuce wani ƙauye gaba damu sosai, munyi tafiya a mashin mai nisa kafin muka iso. Malamine sak ba boka ba, dama Yaya Hamma yayi mun bayani. Sai naga zahiri harda almajirai gasu a gabanshi. Amman layi ma ake bi ga mata da maza anata layi. Mun daɗe sosai kafin ma layin yazo kanmu. Ni kaɗai na isa wajen nai masa bayanin dalilin zuwan nawa tsab, da duk yadda nake ji, harda furucin da Hama tayi a kaina. Kai ya girgiza da lalatacciyar hausarshi yace.
“A lalle haukatakin taso tayi, tunda ko runtsawa bakya yi, ƙarfin adda’ar da kike yi ne yasa burinta bai cika ba a kanki ba. Amman Allah ya fita. Yarinya ni ba boka bane, bana ba da laya. Sai dai zan rubuta miki ayoyin Alkur’ani in rubuta a allo in wanke miki. Sannan zan miki tofi da zaki dinga shafe jikinki, da habbatus sauda da zaki dinga turare ɗakin ki dashi. Ba asiri ba ko sammu akayi miki da izinin Allah saiya karye. Amman sai zuwa gobe zaki dawo, sannan ki dena kwanciya da janaba, ki dinga alwala kafin ki kwanta. Allah ya ƙara sauƙi gobe uwar haka sai ki dawo”
To Malam Nagode sosai. Nawa zan bayar abun sadaka?” Murmushi yayi yace
Sadaka bata kaɗan bata yawa, abinda Allah ya hore miki ajjiye ki tafi, inma baki dashi zanyi miki dolena.”
Nera dubu guda na ajjiye ina godiya na samu su Uwani muka kama hanya. Sai la’asar sakaliya muka shigo, a lokacin matan gidan duk sun daddawo anata aikace_aikace. A ɗakin Baɗɗo duk muka zube, muka yi Sallah. Baɗɗo suka gaggaisa da Uwani ta fita ta bamu waje
“Iyabo wani tunanine ya faɗo mun. Kin tuno da wannan adda’ar ta karya sihiri wadda na baki akayi yima Gwadabe mai ganyen magarya? To yau ba sai gobe ba kiyi” Idanuna na lumshe tare da yin hamdala ga Allah. Na mance da wannan maganin karya sihirin in banda yanzu da Uwani ta faɗamun. Ai babu wata wata na aiki Baɗɗo ta ɗebo mun ganyen magarya a ɗakina guda bakwai, ta kawo mun ruwa a bokiti na tottofa duk ayoyin ban mance komai ba. Na adana bokitin anan ɗakin.
Uwani wallahi na sha’afa da wannan magani na karya sihiri, daga yanzu in Allah yaso ya yarda bazan sake rabuwa dashi ba, lokaci zuwa lokaci zan dinga wanka da sha, tunda jarabawar gidannan ta kishiya mai asirice.”
“Wannan shi ake kira nama ya dahi romo ɗanye. Uwar miji a gidan auren fari ta hanaki saƙat. Wannan gidan kuma kishiya na neman rayuwarki. Ga kaya duk na siyo miki komai tashin hankali ya hanamu maganar kayan ma” Dariya nayi mata nace.
Ke dai bari ana takai wa yake ta kaya? Bari inje in samu in watsa ruwa me gidan yana hanya. Ga kiraye_kirayen sallar magriba anayi.”
A ɗakin Yafendo nayi Sallah, kana na fito na raba abinci, ina kan rabawa Yusufu yazo karɓa musu na zuba musu nasu da nasu Dada.
“Adda ance in faɗa muku Cubu bata da lafiya tana kwance a gida” Da sauri na ɗago na kalleshi.
Meke damunta Yusufu?” Yace.
“Ban sani ba dai, amman ance ciwon sosai ne” kwanukan abincin na miƙa mishi.
Allah ya bata lafiya, gobe zanje in dubata. Ku kara haƙuri kunji ko Yusufu? Kaine babban kanka a yanzu kayi ƙoƙarin kulawa da kan ka. Duk abinda kuke buƙata kazo ka sanar mun kaji ko?”
“To Adda, bari in tafi sai da safe” Yai mun sallama ya tafi. Ina fitowa Yaya Hamma na shigowa. Da sauri na ƙarasa na karɓi ledar hannunshi nayi mishi barka da dawowa. Daga ɗakin Yafendo kai tsaye masallaci ya wuce. Duk muna tsakar gida kowa na sha’anin gabanshi. Sai da naga wucewar Yaya Hamma ya nufi ɗakina na bishi ɗauke da tiren abinci.
Saida na jima ina addu’a kafin nasa kai na shiga ɗakin. Wannan tashin tsigar jikin dai saida naji, kuma sai inji anyi tsaye a kaina.
Shiru nazo na samu yaya Hamma ba dai yadda na saba ganinshi ba, kamar akwai damuwa a fuskarshi.
Yaya Hamma lafiya kuwa na ganka a cikin damuwa?” Ajjiyar zuchiya ya sauke ya dubeni yana dariyar yaƙe.
“Babu komai halin rayuwane, yau da gobe kinsan sai Allah. Ya jikin naki, kunje wajen maganin?” Ajjiyar zuchiya na sauke kana nace.
Munje harda Uwani ma, da rana sai gata tazo” Ya yi dariya yace.
“Uwani ƙawar amana kenan. Allah sarki. To yaya kuka yi da mai maganin?”
Na labarta mishi yadda muka yi, yana saurare yana cin abincinshi. Abincin loma biyu yayo ya ajjiye. Furarma kurɓa biyu yayi kawai ya rufeta. Ni gabaki ɗaya na kasa gane mishi. Na tambayeshi yace babu komai. Bana son in matsa mishi dole in barshi, sai dai in naga damuwar tafi haka yawa dole in kuma tambayarshi.
“Zanje wajen Baɗejo ba daɗewa zanyi ba. Kema nasan ɗalibanki suna tsakar gida suna jiranki.”
Tare muka fito, shi yayi waje ni kuma na ƙarasa wajen ɗalibaina mu kai karatun dai babu armashi yanayin yadda naga Yaya Hamma zahiri a cikin damuwa yake. Bamu kai lokacin tashi ba na sallamesu, na faɗa musu na kawo kayayyakin mata gobe kowacce ta kullo kudinta zan buɗe haja. Suna cikin murna Yaya Hamma yazo ya wuce mu. Da idanu na bishi jikinshi duk a sanyaye ba laka. Jikina a mace nabi bayanshi a kwance naje na sameshi yana kallon sama. Ƙur na ƙura mushi idanu ina nazarinshi.
Yaya Hamma dan Allah menene matsalarka ya kamata ka sanar dani damuwarka karka sani a wata sabuwar damuwar” Tunda nake magana yake kallona, hannayenshi ya miƙo mun halamun inje. Banyi musuba nabi umarninshi.
“Babu komai Jabu. Ki dena damun kanki bana jin daɗin jikin nawane yau shiyasa tun ɗazu a wajen aiki nake jina wani iri. Magani naje Baɗejo ya bani nasha.” Nan na shiga aikin yi mishi sannu. Wannan dare ya bamu wuya sosai dan har ji nayi kamar ana kiran sunana. Sassafe na yi amfani da wannan tofi, na sha na shafe jikina dashi tas. Abun da yafi komai bani mamaki a madadin Yaya Hamma ya tafi wajen aiki sai kawai na ganshi ya koro shanu ina duƙe ina wanke kayan yaranshi da nashi. Tsayawa yayi suka gaisa faram_faram da Uwani ya dubeni da sandarshi a wuya yace.
“Ni zan tafi kiwo ki mun addu’a Murmushi nayi nace.
Ubangiji Allah ya kareka da kai da shanun a shiga jeji lafiya a fito lafiya” Kallona naga yanata yi, ni dai saina tsinci gabana da faɗuwa. Harya fice a gidan na wanke hannuna na bishi.
Uwani ina zuwa”
Ina fita na sameshi a ƙofar gida yayi shiru yana kallon shanun, suma duk sun tsaya suna jiran shugabansu ya kirasu su soma tafiya.
Yaya Hamma yau baka da aikine zaka tafi kiwo?” Ɗagowa yayi ya kalleni. A madadin ya bani amsar tambayata sai yace dani.
“Ina sonki ina ƙaunarki duk runtsi. Wannan halin lalurar da kike ciki yana tayar mun da hankali tunda a gidana kika samu wannan lalura, ga rasa idanunki da kika yi sanadiyyar dukan da ni Hamma nayi miki kaicona, ina tsoron ranar da zaki gaji da wannan auren ki nemi barin rayuwata Jabu, ina tsoro da fargabar wannan rana. Akwai wani mai magani da aka kwatanta mun in an gwada na malamin da kika je wajenshi baiyi ba, zan ɗaukeki in Kai ki can wajen wancan. Kiyi haƙuri Jabu, kinsan dai ina sonki kuma lalurar ta dameni ko?” Ga murmushi a fuskata ga hawaye inayi. Ina bala’in son Yaya Hamma ku kunsan komai, kuma duk sanadiyyar aurenshi ne nake samun wannan matsalolin, inajin auren ya fice a raina, inajin ƙauyen ma ya isheni ƙarfin sonshi da nake yi ke riƙe dani a ƙauyen da ƙarfin adda’a. Amman a kullum sai in dinga ji kamar in zunduma ihu ko in fice a guje. Da zaran naji hakan ya bijiromun sai inta karanta la’ilaha’illah anta subhanaka inni kuntu minal zalumin, hasbunallahu wa’ni’imal wakil, la haula wala ƙuuwata illabillah. Sai inji dama dama.
Duk rintsi ina tare dakai Yaya Hamma. Bana fatan zuwan ranar da zan gujeka kasa a ranka zamu kasance har izuwa ƙarshen rayuwarmu. Soyayya ba ƙarya bace ina maka son so domin Allah ka yarda dani ka dena fargabar zuwan ranar da zan gaji da aurenka. Babu wannan ranar, bakasan girman matsayinka a zuchiyata bane.”
Murmushi yayi mun, nima na mayar mishi da murmushin ina share hawayena.
“Nagode Jabu yanzu kin ƙaramun kuzari, nutsuwata ta dawo jikina ni zan tafi kiwo”
To Allah ya tsare mun kai ya kareka. Inaso inna gama aikace_aikace zani gidan Cubu ance bata jin daɗin jikinta”
“Assha to Shikenan sai kin dawo, kya gaisheta”
Da haka mu kai sallama na koma cikin gidan. Ƴan tsurko sai kallona suke yi, ni ko bansan ma suna yi ba. Nazo na tarar Uwani ta gama wankin ɗauraya take yi. Tare mu kai shanya muka je ɗakin Yafendo muka karya.
“Jabu kwanannan ina lure dake bakya komawa ɗaki har sai wannan yaron ya dawo ko ƙarfe nawa zai kai. Ga rama kinata yi, inna tambayeki Jabu sai kice babu komai. Amman ni ko a fuskarki inna kalla sai inga damuwa ƙarara. Ki sanar dani abinda ke damunki Jabu, ni Mamanku ce baki da wacce zaki sanar ma matsalarki daya wuce ni, ko dai rasa idanunki guda da kika yi ne kika saka abun a zuchiyarki yake ta nuƙurƙusarki? Ki sani bawa baya wuce ƙaddarar da Allah ya ƙadarto mishi. Kuma har gobe bamu cire rai ba anata neman magani in da rabo sai kiga idon ya dawo kinci gaba da gani dashi.
Murmushi nayi kamar yadda na saba, kaina na ƙasa gudun karta gane ƙarya nayi mata nace.
Babu komai Yafendo. Wannan ramar ta canjin yanayi ne kawai, sai ɗan zazzaɓi dake damuna a tsaitsaye kuma ina shan magani. Rashin shiga ɗaki zafine kawai yayi yawa dake a cikin zafin muke.
Sai naga tana murna ƙila tana tunanin ko ciki ne dani. Au ai kuwa makon jiya ya kamata inyi jinin al’ada kuwa amman banyi ba. Na faɗa a raina”
“To masha Allah. Muga hannunki ” Saina miƙa mata, ta duba tafin hannuna sai tayi dariya tace.
“Sai ki dinga yin komai a hankali. Girkinma ki dena yi Baɗɗo in tayi ta zuba miki, ke dai kiji da kanki, wannan yaron abinci ba damunshi yayi ba dama” Duk sai kunya ta lulluɓe na fahimci dai Yafendo taga ciki ne dani. Sai naji wani farin ciki marar musaltuwa nake jina kamar wannan cikin shine cikin fari. Allah ya bani mai albarka, wanda zasu ji tausayina. A nan Yafendo ta fita ta barmu anyi haihuwa a maƙota zata shigar musu barka. Na sanar mata zamu shiga muma gidan barkan, daga nan kuma zamu je gidan matar Baɗejo.
“Ke baki san ma kina da ciki ba? Ni ko kinga ina ganinki ki kai mun kama da masu sabon ciki sabida naga kinyi haske. Amman da banji kince kina da cikin ba sai nake ganin ƙila sabida ramar da kika yine yasa kika yi fari. Nifa na mance ban faɗa miki ba Gwadabe yaje gidan Hajiyarmu nema na fa”
Take gabana ya tattake ya faɗi, zuchiyata ta tsinke jin an ambaci Gwadabe. Na yi jim ina tuno Gwadabe na, da irin rayuwar da muka gudanar duniya kenan. A duniya banyi tunanin ko a mafarki aurena da Gwadabe zai ƙare ba. Bayan ya ƙaren banyi zato ko tsammanin zan so wani ɗa namiji rabin yadda nake son Gwadabe ba. Ashe ba haka bane so da ƙaunar Yaya Hamma a zuchiyata ya dakushe tauraruwar Gwadabe a zuchiyata ta yanda ba’a iya hango ƙyallinta ko misƙala zarratan. Sai dai ina gani girma Gwadabe fiye da kowa, ina girmama ƙoƙarinshi a kaina. Yarana suka faɗo mun ai sai hawaye.”
“Au harda kuka Iyabo dan kawai na ambaci sunan tsohon mijinki?”
Gwadabe yafi ƙarfin kawai Uwani kema kin sani. Kar kiyi tunanin da ɓirɓishin son Gwadabe a zuchiyata alhalin da aure a kaina. Wallahi ko ɗaya, kuma nasan yin hakan laifine. Sunanshi da kika ambatane ya tuno mun da irin zaman da muka yi. Kukan da nayi kuma yarana na tuno kawai. Neman me Gwadabe yake miki, neman jin labarin inda nake ko? Gwadabe manya. Ina mishi adda’ar Allah yasa yana cikin aminci tare da yarana, ina mishi fatan samun macen da zata soshi fiye dani “
“Kamar kuwa kin sani. Har lambata yaso karɓa Hajiya ta hana tana gudun kar Hafizu ya zargi wani abun. Kinsan tunda na soma kasuwanci Hafizu ya soma mun baƙin ciki, da yaga maza sai ya koresu a shagona. Na kulle gidan na koma gida satina daya yaita sintiri kinsan ba zuchiya gareshi ba, ga talauci na damunshi a gidan nawane yake samun abinci me kyau ya kwanta a lallausan zanin gado. Nifa Allah auren Hafizu ya fita raina. Kuma a yanzu haka ciki gareni, amman inaga ko wata ɗaya baiyi ba ma To Hajiya dai ta faɗa mishi kina aure a garin da mahaifiyarki take. To sai dai tace ta mance bata tambayeshi yayi aure ko baiyi ba. Ta dai tambayi yaran yace suna cikin aminci sunata karatu”
Allah sarki Gwadabe nagode sosai. Inason ganin ƴaƴana in sha Allah inna shigo Kano zan ɗaukeki mu shiga takai ko tsirenine Babala sai dai tayi”
“A’a ki rufa ma kanki asiri. Mijinki kishinshi da yawa kiyi zamanki ni zanje in dubo miki su da izinin Allah. In kuma sun girma babu mamaki Gwadabe ya dinga kawo miki su su kwana biyu. Amman ki samu matsalolin da kike ciki su warware. Wato Iyabo idon naki ya mutu da guda ɗaya kike gani? Allah mai iko mata muna ganin jarabawa iri da kala a gidajen aure, sai dai muce Allah ya bamu mafita. Tashi mu je mu dubo Cubu, daga nan muje gidan Dada ko?”
Sai da mu kai wanka, Uwani ta shiga ɗaki ta ɗakko mun kaya nasa. Mu ka je ɗakin Baɗɗo ta tayani muka buɗe dila sabida ta cika ma Baɗɗo ɗaki, inaso in raga mu kai gidan Dada. Kayane gangariya na yara, mis dana jarirai masu kyau. Na jariran muka ware waje guda basu da yawa sai kawai nace ni da uwani mu raba tunda cikine damu.
“Aa ni na tara kayan jira jirai da yawa kin mance na saida dilar kayan yara? Ki ajjiye dai zasu miki amfani, tunda basu da yawa sai kawai ki ɓoyesu kinga in aka baki kuɗin kya yi wani abun dasu.”
Muka ware kayan kashi kashi. Muka ɗaubi ƙunshi biyu wanda zamu tafi dashi gidan Dada na ware ma yaran Hamma, da yaran Baɗɗo, da yaran Amaduyal, Safiya ma na ɗaukarma yaronta guda ɗaya, matar Baɗejo ma haka. Me jego da zamu shiga mata barka ma zanzo in duba mata kala ɗaya ranar suna in bata dan muna mutunci sosai ta kanyo zuwa na musamman wajena mu yi hira duk ranar da bata je tallar Nono ba.
Da muka fita gidan Dada muka soma zuwa sabida kaya da muka doro a ka ni da Uwani niƙi_niƙi muma muka saje da matan ruga. Daga gidan Dada ne bayan mun yi azahar sai muka tafi, na ba Dada ɗari biyar nace ta yi musu girki ga yaran Jatau ma suna gidan suna wasa.
Da Sallama muka shiga gidan Cubu. Kishiyoyinta suna tsakar gida ko wacce na aikin gabanta. Gidan a share yake ƙal suna da tsafta sosai ko bokatan gidansu babu kazanta a jikinsu labulayen bukkokinsu kuwa tas’tas haka jikkunansu ma tas.
“Sannunku Jabu anzo duba marar lafiya kenan?” Cewar kishiyar Cubu wacce acewarsu ita akaima kishiya tunda kafin zuwan Cubu itace Amarya, mata ta uku kenan. Na fahimci kamar tafi sauran guzumayen sauƙi dansu sunci sun ƙoshi suna da manyan yara gaisuwar arziki basa amsawa ni shi yasa ko kallonsu banyi ba. Na amsa ma kishiyar Cubu da cewar.
Wallahi kuwa nace dai bari inzo in dubata. Ina wuninku?”
In kun tanka sun tanka mu dai muka shige bukkar Cubu tana kwance ba yadda take duk ta bushe ta komaɗe, ga zafi amman tana ƙunshe a ɗaki tana fifita. Ganinmu ne ma yasa taji daɗi.
Cubu kina zaune ke kaɗai a wannan zafin ga matan gida a waje kowa na shan iska ba zaki fita rumfarki ki sha iska ba?” Cikin rawar murya tace.
“Adda inna fita sai suita zubar da habaici suna zagina wai Dadana ma taƙi zaman aure da girmanta amman aurenta ya mutu, mu bamu da tarbiyya muna ma kishiyoyin Dada rashin kunya. Dake kishiyata ta biyun ƙawar Baba Dije ce, ko ɗazu Baba Dije tazo wajenta. To Adda sai suita azabtar dani, kuma ranar girkina babu wanda yake taimakamun, ko da bani da lafiyannan basu ɗauke mun komai ba, kuma ina jin ƙaurin kara zanta hararwa”
Ƙuri muka zuba mata ido ni da Uwani. Kafin muyi magana sai ga kishiyarta da nono cikin ƙwarya yaji sikari da dambu ta ajjiye mana.
Cubu har wannan kishiyar taki da naga kamar tafi manyan kirki bata taimaka miki?” Sai Cubu ta ɗanyi murmushin da yafi kuka ciwo.
“Adda wannan matar muguwar makirace tunda nazo gidannan take ƙullamun makirci a wajen mai gidan. Bata so taga ya ambaci ko sunana” Uwani tace.
“Amman yaya tsakaninki dashi kuna zaune lafiya baya cutar dake?” Cikin kunya tace.
“Baya cutata, yana bani haƙuri kullum akan halayen matanshi shima sunfi ƙarfinshi ne. Kuma yana kawo mun nama da lemun kwalba a ɓoye, shi kaɗai nake iya ci”
Ajjiyar zuchiya muka sauke dukkanmu. Uwani tace.
“Komai zai zo miki da sauƙi tunda mai gidan baki da matsala dashi. Shawarata anan shine ki zage ki ƙwaci ƴancinki babu wanda zaizo ya ƙwatar miki ƴanci. Karki bari habaicinsu ya hanaki fita ki wataya, yadda kowa yake a zube a tsakar gida yana shan iska kema ki dinga fita. Yanzu lallaɓa ki fita mu gyaggyara miki ɗakin naga duk tarkace, in kin samu lafiya ki roƙi mijinki ya saki a makarantar dare da Iyabo take koyarwa kema ki samu ilimi.”
A darare Cubu ta fita, kai kawai na girgiza ina mamakin wannan rayuwa. Tas muka gyare mata ɗakin nata kayan wankinta Uwani ta haɗa tace zata tafi dashi ta wanko Yusufu ya kawo mata. A tsakar gidan muka sameta tanata sheƙa amai uwargidan tana kanta tana faɗa akan tana musu ƙazanta kamar a kanta aka soma ciki bayan ta shigo gidan ta gansu da ƴaƴansu. Ta inda matarnan take shiga ba tanan take fita ba. Mu dai bamu ce komai ba Uwani ta gyara wajen ta zuba ma Cubu ruwa ta wanke mata fuska ta kamota suka dawo tabarma ta saka mata fulo ta kwantar da’ita.”
Sannu Cubu. Zan yima Dada magana a turo miki ko Hassanan Hari ta ɗan dinga taimaka miki, tunda Jatau ya ba Dada ita ba’a barki ke kaɗai ba. Baɗɗo zata dinga zuwa dubaki akai_akai Allah ya ƙara sauƙi “
Mu kai ficewarmu ba tare dana amsa a sauka lafiyan da Kishiyar Cubu take mana ba. Muna tafe da Uwani munata tattauna matsalolin da mata suke fuskanta a gidan aure, sai dai muce Allah ya kawo mana ɗauki.
Da Sallama muka shiga gidan mai jego matan gidan ba kowa ko wacce ta tafi tallar Nono, sai wata tsohowa da inaga mai kula da mai jegonce.
“Maraba, ku shiga tana ciki me jegon”
Uwani ta ajjiye ƙunshin kayan hannunta muka shiga muka samu mai jego a zaune tana ba jaririyarta Nono.
“Ah malama sannu da zuwa. Kinga kuwa yanzunnan Hama ta shigo taimun barka ta fita” Zama mu ka yi a tabarma ta miƙo mana jaririyar. Jikina a mugun mace nace.
Allah sarki ta shigo kenan sannu mai jego”
“E yau ta dawo maƙota ma nata zuwa mata barka, ƴan tsurku ma suna yi maganganu sai yawo suke. Baiwar Allah ina wuni?” Ta dubi Uwani da fara’a ta gaisheta. Ita kanta uwani jikinta a mace ta amsa.
“Lafiya lau ya jiki Allah ya raya abinda aka samu” Ni dai gurum nayi ina mamaki Yaya Hamma yasan matarshi zata dawo shine bai sanar dani ba. Hmm maza ho halinsu sai su. Jaririyar na miƙa ma Uwani ina tambayar me jegon
Gobe ne sunan ko?”
“E gobe ne Malama. Naji anata labarin magungunan da kika kawo da kayan kwalliya nima dan Allah inaso malama tunda nima ɗalibarki ce.” Murmushin dole nayi nace.
To babu damuwa, gobe zan shigo da safe taya aikin abincin suna zan tawo miki dashi. Akwai ɗan kunne da sarƙa fella_fella in kina so”
MRS BUKHARI B4B
Part 13
NAMA YA DAHU…
ROMO ƊANYE
BADI’AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
LITTAFI NA UKU (13)
IYABO
“Inaso Malama a tawo mun dasu in zaɓa. Kuma inason jar hoda in akwai” Ta ƙarashe zancan tana Dariya. Nima dariyar nayi mata na miƙe.
To Allah ya raya zan tawo miki dashi Uwani tawo muje ko?”
Muna fitowa sai ga matar Baɗejo ta shigo barka.
“Ah Malama ashe kina nan, yanzu nake cewa in nayi barkar zan shigo miki mu samu muje mu dawo da wuri.”
Kinganni nazo barka, muma dama daga nan gidanki zamu je, shiga kiyi barkan muna ƙofar gida”
Shiga tayi mu kuma mu kaima wannan tsohuwa sallama muka fito.
Uwani ina cikin matsala. Matsalata ta dawo” Uwani tace.
“Hamma ya faɗa miki dama zata dawo ne?” Kai na girgiza mata halamar a.a ta kwashe da dariya tace.
“Maza mutananmu ɗan munafurcinnan ba’a rabasu dashi. Ni damuwata ɗaya wannan halin da kike ciki ke kaɗai zaki dinga kwana kenan? Bari inje in ajjiye wannan kayan wankin in fito tukunna.”
Ni dai har Uwani taje ta dawo ina tsaye kamar gunki ina tunanin yadda za’ayi in kwana ni kaɗai a wannan ɗakin. Bazanma taɓa iyawa bane wallahi sai dai Hamma yasan yadda zai yi dani ko mu haɗu mu kwana tare a ɗaki ɗaya ba.
“Iyabo harna dawo baki ma san na dawo ba. Almurar da danginta sunata shigar mata da kaya. Harda sababbin kujeru na gani a tsakar gidan irin marasa hannunnan. Sai wani bina suke da ido, inajin shegiyar tana musu yare nasan dai gulma ce.”
Fitowar matar Baɗejo ne ya hanani tankawa muka rankaya inda zamu hau abun hawa.
“Ashe Hama har ta dawo? Jiya inajin Baɗejo suna zancan dawowar tata da daddare da Hamma ya shigo. Akan maganar motar da zata je ɗebo kayanta” Namiji tuwon ƙaya miyar allura, duk yadda kake da namiji in yaso yin munafurcinshi sai yayi, shi da yace magani yaje ya sha a wajan Baɗejo ashe ƙaryace. Murmushi nayi nace.
E haka yake sanar dani batun dawowar tata nima.” Babu daɗi babu ragi naja bakina nayi shiru. Ina kan acaɓa ina mamakin maza har muka isa wannan ƙauye. Yau bamu tarar da layi sosai ba, malamin ya bani rubutu a gora, ya bani tofi shima a gora sai hayaƙin habbatussauda da yace dana ga dare yayi in banke ɗakina dashi, bayan na gama komai sai in yi alwala in sha wannan rubutu, shi kuma tofin in tsiyaya in shafe jikina dashi in sha Allah matsalata ta kau. Godiya nayi mishi sosai muka sake kamo hanya kafin mu iso magriba har ta kawo kai.
Ina saka ƙafata a ƙofar gidan ɗago ɗayar da zanyi in ajjiye a inda zan ajjiyen sai naga wani farin ƙyalle. Allah ya taimakeni ban taka ba sai nayi tsalle na shiga gidan. Uwani ta kewaye ƙyallen ta wuce. Allah al hakim wai wannan bala’in duk akan ɗa namiji akeyinshi wai shin me na tare ma Hama ne da take haɗa mun masifa da bala’i haka?” Uwani ce tai bismillah ta ɗauki ƙyallen muka shige. Ina jiyo surutun mata a kitchen anata shewa. Baɗɗo kuma fitowarta daga bukkarta kenan.
“Adda sannunku da dawowa. Ai kuwa yanzu wannan matar mai sarin kaya tazo nace mata bakya nan. Amman tace gobe da wuri ma zata zo dan nace mata kin kawo kaya.” Wallahi in yi magana na kasa sakamakon haɗa idanu da nayi da Hama. Taci uwar kwalliya ta sha sabuwar atamparta dal. Tayi wani irin kyau har baƙin ƙunshi tasha hannu da ƙafa, ga kitso an yarfa mata zai iya fin guda ɗari ya zuba kawai a kafaɗarta. Wani kishine ya tsargamun da ganin kyan da Hama tayi. Wanda yake da Hama banga abinda zaiyi da Iyabo ba, ba dai kyau na fuska dana fata ba sai dai diri da tsoka kawai za’abi. Ta gabana tazo ta wuce tana kwarkwasa da sabon filas dinta a hannunta.
Hama ashe har kin dawo tun ɗazu, da Yaya Hamma ya faɗamun nayi tunanin sai da yamma zaki dawo shi yasa ma ban ajjiye miki abinci ba, sannu da dawowa ” Da sauri ta juyo ta kalleni, nifa da ƙyar na danne kishina harna saurareta sai cemun tayi.
“Kinsan da dawowar kenan ya faɗa miki ke?” Ai sai naji wani farin ciki dana lura kura zan kunto mishi.
Kwarai na sani sosai ma. Ai dani akaita komai har zuwa wajenki da yake yi nice nace ya dinga zuwa, ya kuma dinga miki kyauta” Ina faɗar haka na yi shigewata ɗakin Baɗɗo na ajjiye kayan magungunana, nayo alwala muka yi sallar la’asar, muna kan sallah akayi kiran magriba. Na idar ina zaune a dadduma na yi tagumi Uwani fa sai magana take mun naƙi kulata.
“Adda akwai ruwan wanka a madafi a murhu ko zaki kwatsa ruwa?”
Zan watsa Baddo. Uwani wani tunanin na lula ina jinki ke dai bara in fito”
A gurguje nayo wankan haɗe da alwala. Hama fa sai giggiwa take yi kamar sabuwar bera. Murmushi nayi a raina nace.
Yau zaki sha mamakina wallahi Allah saina saki zubar da hawaye zan nuna miki bariki yau.” Ɗakin Baɗɗo na shiga nayi sallata a nitse duk ƙuncin da nake ciki ya yaye, na jawo bokitin wannan tofi na soma amfani dashi sannan na shafa na wannan malamin.
Uwani tawo muje ɗakina maci tuwon acan. Baɗɗo kiyi haƙuri in Yusufu yazo ki loda mishi wasu kayan ya kai gidan Dada na cika muku ɗaki da shirgi”
Hannun uwani naja muka fito, Hama na kofar ɗaki ta kafa ta tsare za’a amshi miji muka zo muka wuce da gaushina cike da kasko, da bismillah na shiga na lalubi tocilata a saman kujera na kunna haske ya game ko’ina uwani ta samu ƙasa ta bararraje da tuwonta.
Zauna kici tuwon yau za’aga jarfa a gidannan uwani ke dai zaki sha labari. Hayaƙi na zuba a gaushi na tafi sib ina nemo kaya ina addu’a tsigar jikina sai tashi suke kaina na buɗewa. Doguwar rigar gumama na saka mai baiyana shape gata da sulɓi ta sama ta kamani tayi caras a jikin nawa, ta ƙasa ya buɗe ta baya daidai mazaunaina rigar tayi ɗare_ɗare saman mazaunaina. Na fesa turaruka kala_kala harda wanda ma ban taɓa fesawaba na ɓaresu a kwali. Baɗɗo ce tayi sallama ta shigo da nono a hannunta ta dure a gaban Uwani.
“Adda ɗalibai sun gama cika fa ke muke jira yau naga harda sababbin fuska ma”.
To Baɗɗo Yaya Hamma nake jira har yanzu naji shiru na jiyo ɗuriyar su Nasiru amman shi har yanzu shiru” Ɗan murmusawa tayi tace.
“Ya dawo tun ɗazu fa Adda. Ya jima a cikin gidanma ai” Murmushi nayi mata na fice na barta nan. Karatun kanshi baifi na minti talatin akayiba hankalina na ɗakin su Hama da nake ta jiyo dariyarsu. Magunguna da kayan kwalliya dana fito musu dashi warwaso suka yi ma komai. Magani kam ya ƙare tas in banda wanda na cire ma kaina, da wanda na cire ma Baɗɗo, da me jego. Kayan kwalliyarne su kai ragowa nai musu bayanin da bai wuce minti ashirin ba na sallamesu. Ina zaune a turmi ni da uwani da Baɗɗo muna hirarmu, yaya Hamma ya fito suka gaggaisa da su Uwani yace
“Jabu ina ɗaki ina jiranki” Ya nufi ɗakina nabi bayanshi da uwar muguwar harara, na miƙe.
Sai da safenku Uwani ma ƙarashe gobe”
Na shiga na sameshi a tsaye yama kasa zama ina kallonshi ai saina danna ihu na rungumeshi ƙam na rufe idanduna ruf, basai na hau ɓarɓarɓar da jikina ba halamar matsanancin tsoro ba.
Gogan naku duk yabi ya rikice sai tambayata yake yi, wallahi naƙi bashi amsa saima wasu surutai da sokiburutsun zance dana shiga yi mishi kamar zautacciya.
Zan mutu Shikenan zan mutu in barka, ga danƙa a cikina ashe babu rabon zaka ɗauki ɗanka wanda nice uwarshi ka yafe mun”
Naita ɓarin zantuka ras fa nake nayi rantsuwar bai isa ya kwana a ɗakin Hama bane yau inaso in nuna mata shegen birni gaba yake da shegen ƙauye kuma shima duk bala’in kwaɗayinshi saidai ya haƙura.
Da ƙyar Yaya Hamma ya iya jana zuwa bakin gado muka faɗa gadon tare na wani sandare kamar na mutu.
Ai a guje ya danna a guje ya fita.
Idona na buɗe nace.
Kaɗan ai ka gani ma ba kai munafuki ba.
Bai jima ba sai gashi ya dawo tare da Yafendo, da Hama, Baɗɗo da Uwani.
Ruwa ya yayyafa mun nayi ajjiyar zuchiya mai ƙarfi, naƙi buɗe idanuna ma balle mu haɗa idanu sai kuka.
“Allah ya bata lafiya. Yanzu abinda za’ayi kai ka kwana tare da’ita kaita mata adda’a inaga wannan abun harda junnu. Gobe sassafe zanje in karɓo mata magani. Ku mu jenku. Jabu Allah ya tashi kafaɗa. Allah yasa ba sabida juna biyun dake jikinta bane aljanu ke son shafarta ba” yaya Hamma inaji yana tambayar Yafendo dama juna biyu gareni shi bai sani ba? To kunsan kunya irinta fulani sai ma ta fice a madadin ta kulashi sai Uwani ce ta bashi amsa.
“Juna biyu gareta ai Hamma. Dan Allah ka kula da’ita gashi gobe ni zan koma da sai in zauna da’ita. Duk da dai tafi bukatarka fiye damu. Baɗɗo muje ko” Suka fice, duk ina ganin komai na ƙanƙance idona duk ina kallonsu. Hama da Hamma ne suka rage a tsaye ta cika ta batse fam kallonshi tayi tace.
“Kana nufin a nan zaka kwana kenan alhalin kasan kwananane yau. Sannan kasan yaufa na dawo duk yadda kake cewa kayi kewata haka zakayi mun?” Ta ƙarashe maganar tana huci. Kallonta yayi ranshi a ɓace yace.
“Amman ba zaki tausayama halin da Jabu take ciki ba? Firgita fa take yi kina gani a gabanki fa na yafa mata ruwa ta farfaɗo zan tafi in barta a wannan halinne ga juna biyu a jikinta? Kuma a gabanki Dada tace ke kiyi haƙuri lalurace kema inya kamaki na tabbatar Jabu zata iya bar miki kwananta. Me yasa kike haka?” Tsaki ta doka tace.
“Munafurcin banza da wofi, akanta aka soma juna biyu ne Hamma, ko ba haihuwata uku da kaiba. Nii ban taɓa gani ko a cikina na fari kayo haka ba. Shikenan tunda abun rashin adalcine”
Ta fice fuu. Ni dai inata nunfarfashi, ban buɗe idanuna ba saida naji Yaya Hamma ya tattagoni ya rungumeni yana shafar kaina yana mun karatu a kunnena”
Lumshe idanuna nayi a raina nace kyaji in da daɗi ni da kikai mun a daren amarcina inaji ina gani. Rama cuta ga macuci ibadane”
A wannan dare ni dai dangane da matsalar dake damuna akwai sauƙi da canji gaskiya. Sai tambotsai da na dinga yima Hamma duk ya fice a hayyacinshi yanata faman yi mun sannu.
Karku mance banci abinci ba, wajajen ɗaya na dare sai nayi kamar irin abun ya lafa na laɓe a jikinshi da sanyin murya nace.
Yaya Hamma yinwa nake ji sosai”
Zaburar da yayi wajen tambayata abinda zanci saida ya bani tausayi na kanne nace.
Sha’awar taliyar Hausa nake ji ta manja da ɗanyan kifi” Ba shiri ya zare idanu yana kallona.
“Yanzu ina za’a samu kifi ɗanye Jabu? Taliyar Hausa dai naga Hama ta tawo dashi a cikin garar data dawo dashi, kifinne? Zaki ci haka ba kifin in tasota ta dafa miki?” Ai saina shige jikinshi na saki kukan kissa na sake tashin kanshi. Yaita rarrashi daga baya nace.
Haɗa mun tea kawai in sha kawai gobe ka karɓo mun taliyar uwani ta dafa mun” Ajjiyar zuchiya ya sauke ya tashi faka_faka ya hura rushona da bana rabo da kalanzir cike da tanki, bana rabo da kayan tea ma da ɗan kabin biskit ko in mishi sallahun biredi. Tea ya haɗa mun na sha da biskit sannan na kwanta riƙe dashi ƙam. Albishirinku a wannan daren ba ƙaramin bacci mai shegen nauyi nayi ba, dan garin ma saurin waye mun yayi, alhamdulillah sumul nayi baccina. Ai yana tashina da asuba saina zabura na soma rikeshi ina ni karya tafi masallaci tsoro nake ji”
“To naji zanyi sallar a gida. Kije ki ɗauro alwala kiyi sallah”
Sai dai ai ka rakani, gani nake yi kamar wani abun zai kamani”
Dole ƙanwar naƙi ya rakanu banɗaki tare fa muka shiga. Allah cikin amincewarshi muna fitowa muka tarar da Hama a tsaye a gefen banɗakin tana jiran a fito ta shiga bata ma san mu ne a ciki ba. Ga Hamma ya tallafoni hannunshi na ƙuguna ina dai jikinshi sosai. Wani dogon tsaki taja ta wuce banɗaki fu dariya ta kusan suɓucemun na dai kanne da ƙyar.
Tare muka yi sallah a takure yana gaba ina bayanshi. Juyowa yayi ya kalleni yace.
“Yaya jikin naki, kunje wajen mai maganin kuwa kun karɓo rubutun, ko jikin bai bari kunjeba?”
Munje harma nasha nayi hayaƙin duka” Fuskata ya shafa yana murmushi yace.
“Jabu nayi matuƙar farin cikin jin labarin cikina da kike ɗauke dashi zaki haihu dani mu sake zamewa abu guda. Ƴan ɓakin ciki su Ummu nabeeha, da M Farida Ammar, da Fadila Abdul, da masu mun fatan maciji ya sareni sai dai su mutu. Amman nasan su Khadija maidoki, Ramlex, A_A nafaɗa, da Mamanmu Hajara duk zasu taya mu murna. Nayi farin ciki sosai Allah yasa ki haifamun aboki da zai dinga tayani kiwo. Sannan ki dinga yin komai a hankali. Tunda Hama ta dawo zata taimaka miki” Idanuna na ƙanƙance nace.
Ashe kasan Hama zata dawo jiya amman ni ka kasa sanar mun, baka iya ɓoyema Baɗejo abokinka ba. In ka faɗamun ai ba hanata dawowa zanyi ba face in mata adda’ar dawowa lafiya. Hala shine dalilin da yasa jiya kaƙi sakewa dani abinci ma loma biyu kaya ka ture”
Shiru yayi yana kallona. Sai naga ya girgiza kai yana murmushi.
“Mata a barku da kishi. Yanzu Jabu fishi kikeyi dan ban faɗa miki dawowar hama ba? Gimbiyar mata aimun afuwa gani a gabanki kuiwa a ƙasa banyi tunanin rashin faɗan zai ɓata miki rai ba” Sai naga ya dena annuri ya ci magani halamar yana son yin magana mai mahimmanci dani.
“Jabu jiya a cikin damuwa nake ne. Sakamakon rasa aikina da nayi. Na saba da Alhaji mun kai shekara goma a matsayin masinjanshi, muna tare kuma yana kyautata mun tare da matarshi ma. Wannan shine dalilin da ya hanani sakewa inci abincin. Kuma wallahi Allah shine dalilin daya sha’afar dani wajen faɗa miki Hama zata dawo. Jabu ki yarda ni Hamma san da nake miki in zaki tara mazan duniya wallahi Allah ba zasu miki irin son da nake miki ba. A jiyan damuwace taimun yawa shi yasa”
Jikina sai yayi sanyi shi yasa akeson a ko wanne yanayi kaima mutum uziri, sannan ka bashi dama kaji ta bakinshi kafin ka yanke hukuncin da zaka yanke.
Meya faru ka rasa aikin ka Yaya Hamma, shine jiya ka ɓoye mun baka sanar dani mun haɗu munyi jimamin tare ba?” Hannayena duka biyu ya riƙe ya fuskanceni sosai.
“Ritaya me gidan nawa yayi, zuwa jibi ma zai kwashe iyakinshi ya tattarasu su bar ƙasar baki ɗaya. Kinji abinda ya faru. To sai naga ya dace in mayar da hankalina wajen kiwo, da damuna kuma in yi noman abinda zamu ci a shekara ko da bai kai harda wanda za’a fitar a siyar ba ko? Amman ke meye shawararki?” Kai na girgiza nace.
Wannan shawarace mai kyau. Allah sarki Hajiya ashe ƙasar zasu bari to Allah ya haɗasu da mutanen arziki a duk inda zasu koma. Amman ya kamata muje mui musu sallama ko?” Dariya yayi ya sauke ajjiyar zuchiya yace.
“Ke da kike fama da rashin lafiya ina ke ina wani fita gari, yadda hanyarmu bata da kyau dinnan ga karamun ciki a jikinki. Ni kaina yau a cikin ɗakinnan zan wuni ina kulawa dake” Idanu na zaro ina mamaki, shi kuma ya soma mun cakulkuli ina dariya ina turmusheshi. Sai ganin Hama mukayi a kanmu.
“Ai dama nasan babu ciwon dake damunki. Makirci ne jiya saida kika gama komai naki ni nama dawo gidan bakya nan, kina ganin Hamma kika narke. To ta Allah ba taki ba, kai kuma ka wuce muje ka karya.” Murmushi nayi mai cike da kirsa, inna kalleta sai in kalleshi amsar da zai bata nake jira kafin in koreta a ɗakina.
“Hama meke damunki haka wai, kar ki bari kishi ya sa ki aikata shirme fa. Kije zanzo inci abincin. Bai kamata kina shigowa ɗakin abokiyar zamanki sasakai haka ba. Musamman in ina ciki gudun kar kiyi gamo da abinda bazai miki daɗin gani ba. Kije ganinan”
Ficewa tayi bata tanka ba. Ni kuma saina shiga yi mishi abinda nasan bashi da juriya ta wajen. Fisgoni yayi jikinshi yanai mun raɗa.
“Zo muje a bani hakkina tunda abun hakane”
Uwar ɗakinmu na labule muka koma anan komai ya gudana cikin soyayya da kwanciyar hankali. Babu abinda ke mun daɗi sama da inga Yaya Hamma ya samu nutsuwarshi dani, kuma a fuskarshi ina ganin farin ciki da annashuwa. Rigarshi ya zura ya fice. Ganin fitarshi, sai matan gidan Yafendo tasa sukaita leƙowa suna gaisheni da jikina harda mazajen nasu. Can sai ga Yafendo da kanta ta shigo da kwano a hannunta cike da farfesun zabuwa ta dure mun.
“Jabu Yaya jikin naki da sauƙi ko?’ Cikin kunya nace mata da sauƙi miƙewa tayi tace.
“To Allah ya ƙara sauƙi ga nama nan ɗan romo romo kisha bakin ki yayi daɗi. Zamu je duba Cubu ni da Baɗɗo. In Yusufu yazo abincinsu yana madafi sai ya ɗauka” Tai mun sallama suka tafi. Suna tafiya na ɗaura ruwan wanka a risho yanayin zafi na juye na je nayo wanka na dawo, na ɗanyi kwalliya mai sauƙi ina zaune na kunna turaren tsinke ya cika ɗakin da ƙamshi sai ga Uwani ta shigo cikin shirin tafiya.
“Kaga masu ciki mata a gidan Hamma. Kin haddasa musu fitina gasu can sunata cin uwar sabada muryarsu har tsakar gida. Matan gidanku akwai munafurci duk sun nutsu suna saurarensu ƙauye garin su kare”
Dariya nayi muka tafa.
Uwani hankali kawai na koya mata matsayina na gwada mata a wajen mijin da take takamar ita ya soma aura. Sannan bansan ta ina zan iya kwana ni ɗaya ba. Uwani Alhamdulillah jiya na samu sauƙi sosai wallahi nayi bacci me kyau yanzu ma ɗakin Baɗɗo nake son inje in sha magungunan.
“To Alhamdulillah haka muke so, da izinin Allah wannan dai ya kau. Maza jeki kisha ba’a wasa. Kixo muyi sallama danni zan kama hanya. Na wanke ma Cubu kayanta tas in sun bushe a kai mata.
Zuwa nayi ɗakin Baɗɗo na sha rubutu na shafe jikina da tofin da nayi na fito. Har zuwa wannan lokacin Hama sai ihu take harda kuka, Yaya Hamma dai bana jiyo muryarshi. Matan gidan duk sun watse gidan kuwa kamar kitchen ɗin ƙazama sai tarin tulin ƙudaje sunata bin Nono da madarar da suka zuzzubar a ƙasa da kayayyakin da akayi aikin nonon.
Farfesun zabonnan na tarar Uwani na ci sanda na shigo. Nima na zuba inaci ina bata labarin yadda muka kwashe daren jiya. Uwani tayi dariya tace.
“Ko kefa in ka fiye shiru shiru sai a raina ka. Amman da zaran kana ɗan tabukawa wani abun ma ba za’aima ba. Ya batun siyan kayan mata Iyabo? Akwai mai motar daya shigo damu Girei daga tasha. Ya sanar mun shi ɗan ƙauyannan naku ne wai yaron gidan malam Idi ne mai shanu, ko kun sanshi?”
Kai na gyaɗa mata.
Na sanshi ƙanin Baɗejo ne. Sunan mahaifinsu kenan” Uwani tace.
“To bari Hamma yazo mu tabbatar. Ni da tunanina me zai hana in shi dinne kinga ai gidane, sai in dinga sa lambarshi a jikin kayanki in kaya suka iso Adamawa kinga shi za’a kira yaje ya karɓi kaya. Kinga zai kawo miki har gida. Ke kuma in kaya sun ƙare saiki fita gari kije ki samun kuɗi a banki, zan baki lambar account ɗina. To zamu yi waya kafin ki dawo ƙauyanku ki faɗamun duk abinda kikeso. Naga halama wannan kayan zaki samu alkhairai sosai.”
Haƙiƙa naji daɗin wannan shawarar taki uwani. Bari Yaya Hamma ya shigo muji. In akwai wasu kuɗaɗen ma a hannunshi zan ara a saro mun kayan da yawa in ajiye kinga guri ba kusa ba” muna cikin tattaunawa Yaya Hamma ya shigo.
“Kawayen juna anata hirar ne.” Yana daga tsaye a gefe suka gaisa da Uwani.
Yaya Hamma. Gidansu Baɗejo shine gidan Modibbo Idi mai Shanu ko?” Kai ya ɗaga mun halamar e, sai na kuma tambayarshi.
Suna da ƙani da yake tuƙun mota daga birni zuwa Girai ne Yaya?”
“Juma kenan. Me ya faru?” Uwani ta mishi bayanin yadda muka tattauna. Shima yayo na’am da hakan. Nera dubu hamsin na ara a hannun Yaya Hamma munyi zan bashi da zaran na soma saida kaya shi zan soma ware ma kuɗinshi. Na haɗa kan kuɗi masu yawa na ba Uwani. Yaya Hamma ya bata dubu biyar na mota. Tai mana sallama ta tafi da uban man Shanu data siya a hannun Baɗɗo.
Haka dai ranar ta zama ta tarihi Yaya Hamma yana gida tare dani, sai jefin azahar sai ga Yafendo da kayan magunguna ta leƙo ta bani tare da yi mun bayanin yadda zanyi amfani dasu. Godiya nayi mata.
“Wannan yaro yau baka fita kiwon ba ko? Ka kyauta gara ka zauna ka kula da’ita zuwa gobe ka fita Allah ya ƙara sauƙi”
Ni dai babu kunya na ƙunshe Yaya Hamma a ɗaki har sallar Isha a ɗaki yayi ta. A takaice dai sai washe gari Hama ta karɓi miji.
Alhamdulillah jikina yayi sauƙi a cikin kwana biyar komai ya zama tarihi, sai ciwon laulayi mai zafi. Duk abinda nasa a bakina sai ya dawo. Madarar shanu kaɗai nake iya sha itace abincina daga tatsota in shata da duminta ko dafawa bana so ayi.
Rayuwar tai ta shurawa, makarantata ta sake cika da ɗalibai, cinikin kayan yara har abun mamaki yake bani. Dan cikin ɗan ƙanƙanin lokaci kayan suka ƙare.
Ta bangaren Cubu laulayin nata yayi sauƙi sabida cikin ya tasa.
A kullum a hidima nake da Dada duk wani abun daɗi inaba Baɗɗo ta dafa akai mata tai ta sa mun albarka, ga sutura da nake dinka mata. Amaduyal kuwa ya tsaya tsayin daka wajen kulawa da kiwo har duka shanu biyun mata suna ɗauke da juna biyu. Tumakaina kuwa du biyun sun haihu, ɗayar mai laya ta haifi yara uku, ɗayar kuma farar yaro ɗaya ta haifa jal. Haka dai rayuwar tai ta matsawa, ina cikin dangina anata zumunci inata ƙoƙarin yin zumunci dasu. Daso ce sau biyu na taɓa zuwa gidanta, dan ita tana yawan kawo ma Hama ziyara. A haka ne Yafendo ta fahimci kamar Daso ita ke rura wutar rikici a tsakanina da Hama. Sai tai ma tubkaar hanci ta hanyar sanar da Yafendona halin da ake ciki. Ita kuma Yafendo taima Daso tas tunda dama ta san Daso taso Hamma sosai, sai ta saka mata dokar ba zata hanata zuwa gidan ba amman indai tazo iyakarta ɗakin Yafendo.
Gaga_gaga anata cuɗa rayuwar. Yau kwanciyar hankali, gobe akasin haka.
MRS BUKHARI
Part 14
NAMA YA DAHU….
ROMO ƊANYE
BADI’AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
LITTAFI NA UKU (14)
Hama irin kishiyoyinnane marasa dadin kishi. Gata da masifar bin bokaye. Duk tabi ta tashi hankalinta akan cikin dake jikina. Wata rana da rikici ya haɗamu har cewa tayi in sha Allah sai cikin ya zama ajalina in mutu uban kowa ya huta. Wannan furucin nata ya haifar mata da fishin Yafendo da Hamma daya ƙwallafa ranshi akan cikin. Yaya Hamma ya fi sati yana fishi da’ita. Ni ko ko a jikina domin da Allah kaɗai na dogara. Kuma Hamma na zuwa wannan ƙauye wajen wannan malami yana karɓomun tofi ina sha ina shafewa a jikina duk daren Allah.
Kasuwancin saida magungunan mata ya amsheni sosai a gaskiya. Sai kwana biyunnan dana lodo kaya sai naga yaƙi tafiya an barni da tulin kaya abinda bai taɓa faruwa ba. Abu kamar wasa ya zamana duk abinda na siyo saidai in yi asararshi. Hatta dilar kaya dana sake kuncewa wallahi sai kano na mayar ma Uwani da kayan banda asarar da nayi, ku har man shanu nake tarawa ranar kasuwa in kai ko za’a siya. Ba’a siya sai kace wacce ta kaɗe baƙar karya da baƙar mota. Sau biyu naje, zuwa na biyu harda kindirmon Nono naje mai kyau samanshi harda fatar mai kwance. Yaya Hamma bai ma fa san naje ba. Allah cikin ikonshi yadda na kai haka na jawo tsumman ƙafafuwana na dawo gida, abun bana lafiya bane A cikin watanni biyu da rabi saida na dawo nera biyar tawa wallahi bani da’ita babu da abinda na tsira sai shanu da awakaina wanda su kansu Amaduyal yace du basu da lafiya. Tunkiyata ma kasawa ta kusan yi aka saidata nera dubu takwas. Duka kuɗin na danƙama Dada nace ta ɗan dinga zara tana kashewa. Abinci dai suna samu tunda dama bani ke siya ba, ƙannena nice na zame musu makwafin Dada, dan sai ayi abu a cinye ma bamu faɗa mata ba, kanmu a mugun haɗe yake ga soyayyar juna. Abincin garata ya ƙare, zara bata barin dami. abincin mu kuma a ɗakin Hama yake kullum naje diba saita farfaɗamun maganganu da gorin abincin da nake bawa su Dada. Bana ko tankata ni takaina nake yi kuma da Allah na dogara. Yaya Hamma na roƙa ya gina mana rumbun da za’a dinga ajjiye abincin a ciki, banda rumbun iri da suke ajjiyewa, da buhunhunan masara. Allah ya taimakeni kuwa ya gina, sai na huta da hayagagar Hama. Sai dai tamun akan abinci da nake dafawa in kai gida.
Da cikina ya kai wata huɗu ranar talata ranar awo kenan saina tambayi Yaya Hamma inaso in soma zuwa awo tunda cikina ya soma motsi, dake a ɗakina yake ranar, yana shirin zuwa gonane damina ta soma har an soma share gonakai ana jiran ruwa ya tsaya a soma zuba iri. Ya ɗakko nera ɗari biyar ya bani.
“Kin ganta ita kaɗai ce a hannuna kiyi maneji dashi har kije ki dawo. Kudin cefanen da zan baki ma wallahi bani dashi dama ɗari biyar ɗince kaɗai ta rage mun.” Murmushi nayi mishi nace.
Dukkan tsanani yana tare da sauƙi. In sha Allah da zaran na haihu nima sai in dinga ɗaukar tallar nonon ina bin Baɗɗo muna tafiya. Babu komai”
Wasu hawayene suka gangaromun da gudu, a hakan ma ina fatan inna ɗauki nonon a siya. Duk abinda na taɓa lalacewa yake yi. Hatta koyar da ɗalibai na sauke ma kaina, da ɗaya da ɗaya suka dena zuwa. Ashe camfani akayi a ƙauyen kunsan ƙauya da camfe camfe wai ni mai rariyar hannu ce. Da naji ragowar ɗaliban da basu dena zuwa ba saina sallamesu.
“Ki dena kuka Jabu. Ba zata kai ga haka ba. Akwai alƙawarin dana ɗaukar miki da kikace mun kina da sharaɗi ke ba zaki yi tallar Nono ba. Ni kuma na ɗauki wannan alƙawarin. Daga gona zan shiga gari neman abunyi in sha Allah za’a dace ko na cefanan kwananki ake samu ina laifi”
Kafin in tafi awonnan nayi kukan da har saida idanuna suka kumbura. Yafendo naima sallama na fita. Kai tsaye gidan Dada na zarce naje ɗaukar Hassana tai mun rakiya. Dada ta ɗakko ɗari uku ta miƙo mun”
A’a Dada ni ban baki ba sai kece zaki ban in karɓa” Kallon tausayi tai mun tace.
“Babu komai Jabu karɓi”
Godiya nayi mata. Har munje ƙofar gida tace.
“Jabu. Amaduyal ya sanar dake halin da ake ciki kuwa akan kiwonki kuwa?” Gabana ya faɗi, a raunace nace.
A’a Dada wani abune”
“Kuje in kunje kafin ki wuce gida kizo ina nemanki zamu yi wata magana”
To
Kawai nace mata muka kama hanyar asibiti. Mun sha gwajab_gwalab haka dai muka isa. Layin mata masu awo har bakin babban asibitin Girei mai suna. Girei teaching hospital.
A lokacin kyauta ake raba kati komai ma daya shafi awo kyauta akeyi. Domin a hakanma ba wani zuwa asibitin daga cikin ƙauyuka akeyi ba. Sun gwammaci mace taita nakudarta har ta mutu ma akan su kawota asibiti. Ni dai ina zaune akan layi na yi tagumi ina tunanin rayuwa da irin halin da nake ciki. Sauƙina ɗaya babu abinda har yanzu ya canja daga so da kulawar da Yaya Hamma yake mun. Saima abinda yaci gaba, kullum a cikin rarrashina da ban baki yake. Ga rai daya ɗauka yasa akan wannan cikin nawa. Ɗan murmushi nayi na shafi cikin nawa daya fito sosai kamar wanda ya kai wata shida. Yanayin yana mun kama da yanayin cikinsu Taye da Kahinde.
Sai wajen azahar aka kira sunana na bi matar data kira sunana a baya, ta bani roba naje nayo fitsari na dawo mata dashi.
“Malama Jabu ai babu ciki a tattare dake. A text ɗin da mu ka yi miki na fitsari bai nuna mana kina da juna biyu ba. Amman bari mu miki text ɗin jini.”
Take jikina ya soma rawa zufa na keto mun. Ga motsin ɗa a cikina amman ace bani da ciki, ga ciki ƙato?
Allah cikin ikonshi wallahi anyi text ɗin jini maganar ɗaya ce ciki dai babu shi. Sai janaral asibiti Adamawa suka turani jibi inje za’aimun sikainin. Ta yi rubutu a wata takadda ta bani.
Da ƙyar na tashi na fito, cike nake da mamaki, fargaba da tsoro duka dai. Amman in naji motsin rai a cikina sai inga kamar dai basu iya aikinsu bane.
Anan Girai na sai kayan miya, da kuka, da maggi. Muka hau akori kura zuwa Jabbi lamba. Gidan Dada muka shiga da sallama
Amaduyal ma yana ciki da kuɗi a hannunshi yana ƙirgawa ga wasu ma a hannun Dada.
“Adda kun dawo” Cewar Amaduyal. Wani yawo mai kauri na hadiya, da ƙyar nace.
Mun dawo Amaduyal yau baka je kiwon ba?”
Shiru yayi baice komai ba.
Hassana ɗebo mun ruwa in sha ƙishi nake ji”
Hassana ta kawo mun ruwa mai sanyi cikin kofi na shanye, Dada sai kallona take a mugun firgice nake.
“Lafiya Jabu akwai wata matsalar ne?”
A’a Dada gajiyace da rashin kyan hanya ya galabaitar dani” Yanayinta bai nuna ta aminta da abinda nace ba,ta dai mun sannu, kafin tace.
“Jabu kinga wannan kuɗaɗe dubu ɗari biyu da sittin gasu. Kuɗin shanunki da awakanki ne. Kinga ga kaji can a bawo guda huɗu nasa an yanka su dan ko ba’a yanka ba mutuwa zasu yi. Ungo wannan kuɗin riƙe”
Hannu nasa na amshi kuɗin ina murmushi kawai.
“Jabu kisan kadarar da zaki siya ki ajjiye kar ki bari kuɗinnan ya lalace su kaɗai suka rage miki. Sannan inaso ki zama mace mai juriya da jajircewa, ki yarda Allah shi kaɗai yake iya ɗaurama bawa kaddara me kyau da marar kyau. Wata rana zaki huta. Kamar yadda kika sha wahala ni kika fitar dani a matsala. Kema in sha Allah zaki haifi waɗanda zasu fitar dake a matsala. Duk runtsi kar ki rabu da Hamma. Hamma yana sonki kuma zai iya zame miki garkuwa ko bayan raina. Kiyi haƙuri kar ki zargi kishiyarki hakan kar yasa ko bayan raina ki aikata mata wani abun a matsayin ramuwar gayya. Da sannu zata gurbe duk abinda ta shuka. Akan Hamma duk take wannan burinta ta fitar dake a ɗakinki. Ke kuma ki nuna mata kina ma Hamma son da sai dai mutuwa ta rabaku”
Hawayen dake zuba a idona na share.
Babu komai Dada, na kuma gode da wannan shawarar. Amman inaso zan ba Amaduyal ko da jari ne ya nemi wata sana’ar a cikin wannan kuɗin.”
“A.a riƙe kuɗinki ki nemi kadara ki siya. Zai yi noma kuma ya samu aikin tuƙa babur zai dinga jigilar shigar da mutane ƙauyuka”
Kuɗin na raba Uku na miƙa ma Dada fur taƙi karɓa, haka dole na haƙura na saka kuɗin a jakata. Na zari wasu daga ciki na ba Hassana tamun cefanan tumaturi ta auno mun shinkafar Hausa da Maggi. Suma su Dada nai musu cefane nace su yi girki na basu kaji biyu. Hassana ta rakani har gida da kayan cefanan.
Ina tafe kamar mahaukaciya har gidan namu na wuce tafiya fa kawai nake yi, sai da Hassana tace.
“Adda kin wuce gidan fa” Kana na juyo naga zahiri na wuce gidan. Da Sallama a bakina na shiga gidan. Yafendo tana tsakar gida, ita da Yafendo A’i.
“Jabu kin dawo” Cewar Yafendo A’i. Wajensu na nufa na zube a gabansu muka gaisa.
“Ai ɗazu mun shiga wajen Adda Daso ma take sanar mana siyar da dabbobinki da akayi basu da lafiya. Allah yasa da abinda suka tare. Kinsan ba kowa kiwo ya karɓaba shi yasa. Naji kuma sana’ar taki ma jarin duk ya karye miki shima. Jabu kiyi haƙuri jarabawace. Allah daya baki shi zai kuma baki wani, ki ɗau dangana.”
Suka haɗu sukaita ƙarfafani sai na ji sanyi a raina. A ɗakin Yafendo ma nayi Sallah na kwanta a ƙasa sanyin na mun daɗi.
“Ga madarar shanu ɗazu na tatso miki” Yafendo ta miƙo mun na karba ina sha suna hirarsu da fullanci. Allah yayi mun ƙwaƙwalwar saurin jin yare gaskiya. A halin yanzu abu ɗaɗɗayane suke faɗa wanda bana ganewa. Mayarwar ma inayi amman ba sosai ba dai. Sai da nayi la’asar na shiga ɗakina na gyara tas na fito. Kara naje nayo na hura wuta na wanke kajinnan tas na ɗaura a wuta. Na ɗakko dutsen niƙa na gwafe naita niƙa tumaurinnan dasu attaruhu nafi awa ɗaya ina abu ɗaya. Ni kaɗaice a gidan Yafendo ta tafi raka Yafendo A’i zuwa gidan Baffa Musa, daga can zasu je gidan Yafendona. Ni dai inata aiki jikina sukuku. Masu tallar nono an dawo sun sameni na gama suyar kaza na zuba a jar miya ina soya miyar. Ga shinkafa ina zaune inata tsinta da akwai ƙasa sosai.
“Kun dawo sannunku” Safiya da Baɗɗo ne dama kaɗai suke amsa sannu da zuwa in nayi musu. Ni dai inata aikina bayana da wuyana duk yabi ya riƙe gam. Sai magriba na wanke shinkafar na zuba. Naje nayo wanka nayi Sallah. Ina idar da Sallah na fito na raba abinci. Ɗaki_ɗaki saida na zuba ma kowa dake shinkafa abun ɗaukanice barinma mai miya da nama.
Ina ɗaki shiru ina sauraren motsin da cikina yake yi, idanuna a lumshe ina mamakin yama za’ace anyi awo bani da ciki. To in hakanne meye a cikina yake motsi?
Shigowar Yaya Hamma ne yasa na buɗe idona na yi saurin karɓar ledar hannunshi.
Kayan miyane a ciki da maggi.
Sannu da zuwa Yaya Hamma ya aikin. Wanka zaka soma ko cin abinci?”
Zama yayi a ƙasa ya jingina da kujera yace.
“Yaya jiki_jikin. Kin ga likita da kuka je asibitin?” Sai gabana ya faɗi. Amman saina jure nace.
Naga likita yaronka yana cikin ƙoshin lafiya” murmushi yayi yace.
“Allahu ya rabaku lafiya. Allah ya baki lafiya. Bari in soma wankan inzo in baki labari”
Ruwan wankan naje na juyo mishi na dawo.
Saina ga jini digo uku a ƙofar ɗakina. Gabana ya yanke ya faɗi wata fitinar ce kuma ake so in taka kenan?
Cikin gida na shiga na ɗakko tsintsiyar sharar tsakar gida da ragowar ruwan Baɗɗo dana gani a bokiti nazo da bismillah a bakina na wanke jinin tas, nayi adda’a na shige ɗaki ina mamaki.
Ina zuba mana abinci Yaya Hamma ya shigo ganin shinkafa da miya harda kaji yasa ya zauna yana kallona.
“A ina kika samu kuɗi haka Jabu?” Murmushi nayi mishi kawai nace.
Kai dai kaci zan maka bayani “
“A’a aimun bayanin tukunna dai. Kaddai zuwa kika yi kika ari kuɗi Jabu. Nasanki dai akwai ɓoye sirri bana jinki”
Da dai naga ya fara zargi saina sanar mishi abinda ake ciki. Na ɗaura da cewa.
Kuɗin yana jakata na adanasu. Amman dan Allah inaso sati mai zuwa ka yarje mun in je Kano. Inaso zan kaima su Iyaa Debisi ziyara, da Uwani” Shiru yayi kawai yana kallona irin kallon tausayi. Murmushi kawai nake yi dan murmushin yana kwarara mun zuchiyata.
“Allah yayi miki albarka. In sha Allah Jabu zan riƙeki da amana ni dai nayi miki alƙawarin ba zaki yi kuka dani ba. Batun zuwa Kano bazan hanaki ba. In lokacin yayi ki shirya kije. Amman meye tunaninki akan kuɗin me kike ganin zaki yi wanda kuɗin bazai rushe ba?”
To ka soma cin abincin tukunna muna hirar.”
Yana cin abinci yana santi, ina mishi dariya. In ina tare dashi yaye mun dukkannun damuwata yake yi. In ina farin ciki mancewa nake yi ina da damuww ma a rayuwa.
Gida nake so in siya ko me ɗaki biyu ne a zuba mun haya. Kasan ina da gidan dana siya a kusa da gidan Uwani, da ƴan haya ma a ciki. To ko ta kusa dasu na kuma samu sai in siya, ko kuma in sai fili”
Saida ya cika tsokar nama a bakinshi yace.
“Allah sarki bansan kina da gida a Kano ba yaushe kika siya?”
Bayan aurenmu. Lokacin dana shiga kano
A wannan lokacin Uwani taimun tayin wajen saina siya”
Kai ya girgiza yace.
“To ki sake siyan gidan ko filin kadarace babba musamman dake a birni ne, ba kamar ƙauye ba. Ga kayan miya na siyo miki. Na fita yau da ƙafar dama. Na samu gadi a gidan wani Alhaji a Girei. Daga takwas na safe zuwa shidan yamma zan dinga tafiya. Akwai wanda yake yin na kwana. Duk da nima yace inta kama zan dinga kwanan. Nera dubu huɗu a wata”
Nan na shiga murna tare da yi mishi adda’a. Da ƙyar naci naman kazannan ya zauna a cikina.
Da safe da nayi dumame kuma sai naji inaso naci da yawa.
Da Yaya Hamma zai fita na zari dubu Hamsin na miƙa mishi a hannunshi. Ya kalli kuɗin ya dubeni yace.
“Me za’ayi miki dashi?”
Nakane na baka kayi noma dashi. Dan girman Allah kar kace mun ba zaka karɓa ba. Dan girman Allah Yaya Hamma”
Murmushi yayi yace.
“Nagode Allah yayi miki albarka”
Ameen ko kai fa. Gobe ance in koma asibiti akwai gwaji da zasu sake yi mun. Nasan inka koma ɗakin uwargidanka bazan ganka ta daɗi ba.” Dariya yayi tare da girgiza kanshi yace.
“Allah ya nuna mana goben lafiya. Sai mu fita tare ai, ni in wuce aiki ke ki wuce asibiti.”
Hakan kuwa akayi Bakwai ma mun fice a gidan, har bakin asibiti ya rakani, ya wuce wajen aikinshi. Da naga ya ƙule na fito nayo babban titi na hau mota zuwa gari.
Allahu Akbar a babban asibitin ma magana ɗaya ce anyi duk gwaje_gwaje, da hoto, da sikainin amman basu ga komai ba. A zahiri ga ciki sun shaida kuma yana motsi, amman a awo babu ciki babu dalilinshi.
Tunda uwata tai sanadin zuwana duniya ban taɓa ji ko ganin abun almara irin wannan ba.
Halin dana shiga ya wuce gaban misalin da za’a musalta har ƙwaƙwalwar mai karatu ta ɗauka. Ku kwatanta da kanku, in kece wanne irin ruɗu zaki shiga? To irinshi na shiga nima.
Gaga_gaga na dawo gida. Na ja bakina nayi gum babu wanda yasan halin da nake ciki. Ai saina dena bacci, nice sallar dare, nice sadaka. Ko aikin girki nake bana rabo da ambaton Allah. Salatin annabi kuwa sai inyi a rana fin dubu biyu.
Da sati ya cika na shirya kayana a akwati na fito naima matan gida sallamar zanje ganin gida. Da ƴar tsarabata a buhu harda nono a jarka, da man shanu duka dai wata tsaraba data dace. Yaya Hamma bai bar tasha ba har saida motarmu ta bar tashar. Ko dana juya baya ina hangoshi ta tangaran ɗin motar yana ma motarmu odabo.
Wasu siraran hawayene suka sulalo a kumatuna, a hankali na lumshe idanuna, inata tunano abubbuwan da sukaita faruwa, lallai in haka kishiya take irin hama kishiya bala’ice, masifa ce. Hama ta wargaza mun dukkannin farin cikina, ta hanani sakewa da masoyina sam. Bata ƙaunar a zauna lafiya, in bata zageni, ko taci mun zarafi ba bata samun kwanciyar hankali. Amman ina tausayin ranar da zata soma girbe abinda ta shuka, ranar da zata zama abun tausayi. Dan ƙarshen mai biye_biyen bokaye ba ƙarshe bane me kyau. Macen data mutu akan wannan Gwadaben bata ba shiga aljanna, ba faɗata bace faɗar Allah subhanahu wata’ala ne. ( Jan kunne. Yake ƴar uwata ki sani bin bokaye shirkace. Allah baya gafartama wanda ya mutu yana shirka, kuma babu shi babu jin ƙamshin aljanna. Shin akan ɗa namiji kike son kai kanki ga halaka, kina mace kina zaluntar ƴar uwarki mace? Mace ta haukata kishiya, ta kashe kishiya, ta kashe yaran kishiya, ko ta kassara rayuwarsu. Sai kace munzo duniyane domun mu tabbata. Da muna tuna Allah, da azabobubshi, da muna tuna juma’ar da bata da ƙarshe, da muna tuna wuta, mu tuna aljanna wallahil azeem wasu abun ba zamu yi ba. Ke kina nan kina tabkama kishiya asiri, wata ƙila rayuwarki ma ba mai tsayi bace kije ki faɗi ki mutu Shikenan kin gama yawo. A duniya ba riba, a lahira ba riba, kizo a banza ki koma a wofi.
Allah ya ƙara tsare imaninmu ameen)
Bayan la’asar muka shiga kano Shigata kano ya famamun ciwukan da har abada ba zasu warke a rayuwata ba.
Allah sarki Gwadabe alkhairin Allah ya kai muku tare da yarana a duk inda kuke. Allah ya wadataka ya horema samun macen data kere Iyabo ta kuma”
Ni dai kai tsaye gidan Tabalbalin na wuce, nafiso saina gama da harkar asibiti kafin inje gida, kwana biyu rak zanyi a gida in koma. A shago na tadda Uwani tanata cinikayya da mata, ta buɗe dilar kayan jirarirai. Ga Hafizu a cikin shagon yanata rataye wasu kayayyaki a hanga. Shagon an sake gyarashi yayi kyau har doguwar kujera aka saka an sake yawan kantocin, an yi sabon fenti. Acaɓana na ajjiyeni a bakin shagon Hafizu ya iso ya sauke mun buhun kayana, da fantimoti na.
“Alaja kece a tafe, maraba” Cewar Hafizu. Murmushi na kakaro nace.
Wallahi nice Hafizu nace mutuniyar kwana biyu shiru ni bari in leko. An wuni lafiya ya Amarya da yarinyarta ko yarone?” Baki ya washe.
“Duk kowa yana lafiya, ai tama haihu jiya Wallahi an samu Uwani” Baki na kuma washewa. Saida na sallami mai acaɓa nace.
Ah ka kyauta. Uwani muka samu, wannan yarinya kace mafaɗaciyace”
Tare muka shiga shagon na Uwani, ta ko haɗe rai tamau. Ni nasan bazai wuce akan sunanta da akasa bane, ga cikinta ya fito sosai itama.
“Iyabo maraba. Jiya fa nayi mafarkinki kuma wallahi marar daɗi harma nayi sadakar ƙosai mai zafi. Ga waje ki zauna a karɓo miki lemo” Waje ta nuna mun na zauna. Ta ba Hafizu kuɗi ya siyo mun lemo da sakwara.
Hmmm Uwani damuwoyi sun yi mun yawa a kannan nawa. Ina tsoron kar in faɗi in mutu mutuwar farar ɗaya. A baya matsalata uwar mijice, sai facaloli. A yanzu matsalata Hama ce, haɗa miji da mace mai asiri bala,ine. Ni wallahi har gara in haɗa miji da makira. Ita duka biyu ta haɗa Uwani. Jibi ga ciki a jikina ga motsi, kuma yana girma. Amman gwajin duniya Uwani likitoci basu ga wannan ciki ba wai babu komai fa a cikin. Kaina ya ɗaure, bacci wannan bana iyawa. Banda bala’e_ bala’en daketa sauka akan dukiyata. To ta faru ma ta ƙare tunda yanzu komai nawa ya ƙare tas”
Hawaye na sharce bayan na ƙarashe maganata. Uwani kuwa kasaƙe tayi tana kallona kawai.
“Iyabo na shiga uku. Wannan tashin hankali har ina. Babu ciki likitoci basu ga cikin ba kikace. To mijin naki wanne mataki ya ɗauka akan hakan? Kinga jikina rawa yake yi Iyabo”
Hamma baisan abinda ake ciki ba sam. Na ɓoye mishi Uwani kar kiso ganin yadda ya ɗauki rai ya ƙallafa akan wannan ciki. Shi burinshi ya haɗa jini dani Uwani. Wallahi tsoro da fargabar me kaje kazo ne ya hanani ce mishi komai. Ina cikin tsaka mai wahalar fita.”
Kuka na fashe dashi, nayi shi ƙaƙas sai naji zuchiyata ta ɗan rage naunyi ni da kaina nayi shiru. Uwani bata hanani kuka ba. A ko da yaushe Uwani takance kuka shima wata hanyace ta rage nauyin zuchiya da cunkushewarta.
“Hmmmm ki kwantar da hankalinki Iyabo. Zamu zagaye asibitocin Kano. Kuma in sha Allah za’a dace. Akwai wani malami zan ɗaukeki muje zai taimaka miki.” Dawowar Hafizu ne ya katse mana hirarmu. Lemon montin dew ya ajjiye a gabana. Da kular sakwara.
“Hajiya tunda kinyi baƙuwa zan tafi. Sannan ki daure kije ki duba me jego da takwararki”
Uwani ta dubeshi sai naga tayi dariya, ta zuge lalita ta ciro kuɗi ta bashi.
“Ga albashinka nan” Yayi saurin cewa..”
“A’a ki riƙe a wajenki. A tsintamun kayan jaririya a cikin kwashe irin na ɗari_ɗari ko tsinke ban siya ba”
Kuɗin Uwani ta mayar tace.
“Gasu can ƴan ɗari_ɗarin ka ɗebi na iya kuɗinka”
Ni dai ina jinsu, Sakwara nake ci hannu baka hannu ƙwarya ga ganda sutu_sutu a miyar. Sai da Hafizu ya fita nace.
Uwani ki ƙyale Hafizu haka dan Allah “
“A’a fa Iyabo. Barni da Hafizu inda kika gammu. Nifa a haka nayi matuƙar ƙoƙari da kai zuchiyata nesa tunda har na iya ɗaukarshi aiki nake biyanshi duk sati yake samun naci da iyalinshi. Banyi ƙoƙari bane nifa nake ci da kaina da nawa yaran. A shago ina siya mai abincin rana. To me kike so, in goyashi in yi yawo dashi kome? Kinfa san komai duk ba akan Hafizu naje na afka bala’in da Allah ne yayi ina da tsayin rayuwa ba. A ƙarshe me yayi mun?”
Anan zan dakata sai ranar monday kuma
MRS BUKHARI.
Part 15
NAMA YA DAHU….
ROMO ƊANYE
BADI’AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
LITTAFI NA UKU (15)
“Ba aure yayo da kuɗinshi ba, abinda yayi ragowa ya cinye shi da amaryarshi ba? Wai ko so kike in danƙa mishi ragamar dukiyata ne, sai yadda yayi da’ita?”
Tabalbalin ta dinga faɗa ta inda take shiga ba tanan take ɓullowaba. Ni dai dana gama cin sakwara saina miƙe.
Bari in shiga ciki in ɗauro alwala inzo in yi sallah”
Ciki na shiga na kama ruwa nai alwala. Sai kawai ma nayi sallata tunda yaran suna ciki sai murnar ganina suke yi. Fitowa nayi shago na tarar da wata mata suna maganar filaye da Uwani.
“Kinga filin yayi sauƙi manyane dubu ɗari_ɗari aketa yankawa wallahi nan da shekara biyar wajannan cika zaiyi sosai. Shi yasa nace bari in sanar miki ko kina da buƙata ƙanina ne suke yanka wajan” Cewar wannan Mata kenan. Uwani tace.
“To zan duba kuɗaɗen wajena, ko kuma zuwa karshen mako akwai dashi da zan ɗauka kuma da kauri ko guda biyu ne sai in siya in haɗe ai” Ai sai nayi carab nace.
In babu matsala Uwani nima ai sai in siya tunda na siyar da shanuna kiwon yaƙi sai ciwo suke yi” Baki Uwani ta riƙe cike da mamaki. Numfashi ta sauke tace.
“To babu damuwa Halima da daddare zamu zo in Bellon ya dawo sai muyi magana ƙawata zata siya. Wannan ƙawatace tun muna yara tare muka je saudiyya da’ita. Zan siya sai a bamu kusa da juna”
Da wannan matar tai mana sallama akan sai ta ganmu zuwa daren.
“Wai kiwon ma Hama ta hanaki kiyi sabida bata son kiyi arziki? Hmmm kingani ko Iyabo kinsan muguntar mutumin ƙauye kuwa? Yanzu da ba dan kina da wannan gidan ba da haka kuɗin zasu haɗu su galgance jibi asarori da kika tabka. Ni da ace iyakar karayar jarine da yanzu na ɗoraki da yardar Allah. To ba’a siyan komai ne a hannunki baƙin asiri mitsiyaciyar tayi miki na baƙin jini. To ince dai bata da labarin gidan da kike dashi ko?”
Bata da labari, ko shi Hamma bai jima da sani ba. Hatta su Dada babu wanda yasan ina da gidannan. Wannan kuɗin dabbobinne ma Dada tace in samu in mallaki kadara. To Uwani kina ganin ko in siyar da ɗan kunne da sarkar da Saleem ya bani da wanda na siya a siya mun gida a sake zuba ƴan haya. Amman ke me kika gani. Inata ajjiye dasu su ba kawo mun kuɗi suke yi ba, ko babu komai hayar zatai mun amfani zan dinga karɓar kuɗina ina magance ƴan matsalolina. Amman meye shawararki?” Uwani tayi jim tace.
“Magana ta domin Allah in kin tawo dasu ai gara a haɗa a siyar dukka, mu haɗa da ƴan kuɗaɗen dake jikinki, shima wannan gidan a siyar sai a sai babba ko da gidan samane, me ɗakuna da yawa. Kinga duk shekara zaki samu kuɗaɗe masu kauri a hannunki, zakita jalautawa. A ƙauye in kinsa zinare ma waya sani babu. Ai gara ace ƙasa gareki itace babbar kadarar da babu asara a cikinta, yaranki ma sai su gada duk da dai fulanin gadon shanayen wahala ake bar musu”
Mun jima muna tattsunawa. Dab magriba Uwani ta kulle shagonta muka shiga ciki.
Tuwo ta tuƙa mana dama tayi miyarta ta ɗanyen karkashi yaji ɗanyan kifi tun safe, ga yajin daddawa mai daɗi da take siyarwa, ga man shanu shima soyayye da take siyarwa. Uwani fa ƙaƙas ta zama ƴar kasuwa. Bayan munyi Sallah muka ci tuwonmu munata hira, sai naji rabi da kwatan matsalata kamar ta kau. Sai da mu kai Isha Uwani ta ɗebi kayan jajirai muka tafi gidan kishiyarta barka.
Gidan duk ya fice a hayyacinshi yayi biji, biji.
Da Sallama muka shiga ɗakin. Jaririyar sai kuka take canyarawa. Ashe ba kowa ne a ɗakin, ko ina uwar oho sai wan jaririyar yana zaune da ƙaton ciki sai gyangyaɗi yake yi.
Uwani tayi haka zata ɗauko jaririyar a gado mai rumfa. Uwar jaririyar ta shigo da gudu ta riga Uwani ɗaukarta. Har tana sauke ajjiyar zuchiya.
Wai ashe haka kishi, da kishiya yake?.
“Tunda naji kukan yayi yawa nace ko wani abunne mugu ya sameta ashe kune. Sannunku da zuwa”
Ta ƙarashe zancan tana dariya.
Uwani ta dubeni, ta dubi kishiyar tata tace.
“Mune mugayen da muka kusanceta kenan shi yasa take irin wannan kukan? Yayi kyau baki da laifi”
“Lahh wallahi Innar Zainab ni ba haka nake nufi ba kar ki juya mun maganata dan Allah” Uwani zata kuma magana na taɓata ta baya. Wannan karon nako ci sa’a sai tayi shiru muka zauna. Ta bamu jaririya taƙi ta ƙanƙameta, daga ƙarshe saita cusama yarinyar mama. Wani shafaffen yanƙwanannen mama.
Hafizu ne yayo sallama ya shigo. Ganinmu ne yasa ya washe bakinshi.
“Iyabo ashe kun shigo. Ke basu jaririyar ki kawo musu abinci.”
“Tayi bacci ma” Ta faɗa. Uwani tayi dariya tace.
“Kinga kwantar da’ita in tayi bacci. Abinci kuma ki bar abinki. Iyabo Jeka lo ( muje)”
Miƙewa nayi, ledar dake hannun Uwani saita miƙa ma Hafizu tace.
“Ga gumama asa ma takwarata” Ya amsa yanata godiya. Mu dai nan muka fito muka barsu, ya suka ƙare oho musu.
Wai Uwani yadda kishiyarki ta ɗaukeki kenan baƙar muguwa? Kinji furucinta wai me yasa kishiyoyin kusan halayyarsu gudane, sai ɗaiɗaiku da suka rabauta?”
“Rabu da matsiyaciya. Baƙin ciki nan take Hafizu na aiki a ƙarƙashina, da kuɗina ake ciyar da’ita. Da bini_bini zata biyoshi har shago wai tazo ganinshi. Tasa na sallameshi da ƙyar na dawo dashi, da sharaɗin matarshi karta kuma zuwa nemanshi. Ko gidan biki ko suna haka na maƙota dana shiga sai ta sha jinin jikinta. Ni nafi ƙarfinta da ba dan haka ba wannan ƴar ƙauyan juyanu zata yi kamar waina. Shakkarta fa shi kanshi Hafizun yake yi, damma yasan ba kyau ba daɗi ni ɗin, shima da tsiyar zai tatamun ta su rijalu.”
Washe gari
Sassafe muka wuce asibitin murtala, bayan bin dogon layin awo. Bata fa sauya zani ba, magana guda ɗayace. Bani da ciki su basu ga komai ba.
Hankali saiya tashi fiye dana ko yaushe. Danni abinda nasa a raina shine a Adamawa akasi aka samu, bana jin asibitocin Kano indai dan ƙwarewa ne. Munbi asibitin kudi huɗu a ranar wallahi zancan ɗayane.
Kafin yamma idanuna ya faɗa na yi wata rama ta fatat ɗaya.
“Iyabo gobe zamu buga sammako zuwa lahadin makoli wajen mai maganin dana faɗa miki. Muje da izinin Allah zamu dace, kuma a dage da adda’a “
Kayya Uwani, ni ina ganin mu haƙura da zuwa wani gidan magani. A asibiti ba’a gani ba sai a wajen mai maganin hausa ne za’a gani? Allah yana ji yana gani shi zai bani mafita.” Uwani ta dafani tace.
“Bazan hanaki kuka ba. Wallahi nima dauriyace tasa ban zubar da hawaye ba. Amman fa Iyabo kowa yasai rariya yasan zata zubda ruwa. Ni dake a asibiti muka ga dunƙule magani a cikin abinci. Amman idanki ya rufe Hamma kawai. Alhalin ya kamata ace ki duba waye abokiyar zamanki shima yana da mahimmanci.
Matan katsina, Sokoto, zamfara, Maiduguri me yasa zaki ga in akaji dasu za’a haɗa kishi sai kiga an tashi hankali? Sabida waɗannan garuruwa dana lissafa sunyi ƙaurin suna wajen kassara kishiya, da mugun dumi suke ɗaukar sha’anin kishi. ( Kuyi haƙuri ba duka ake nufi ba, mafi yawancin ƴan garuruwan da aka ambata haka suke. Amman akwai da dama waɗanda ba haka suke ba. Kar a mance labarin na gaske ne ba ƙirƙirarshi akayi ba)
Iyabo mun kama laya a cikin fulonki, muka so ni da Baɗɗo a nuna ma uwar mijinku. Amman kika ƙi waike kaza ke kaza kar aurenta ya mutu. Ba gara aurenta ya mutu ba akan ta tarwatsa rayuwarki. Zuchiyar bafulatani fa tauri gareta basa jin kira. Yanzu jibi a cikin dare dubu ɗari da ɗayan data saki, baki mutu ba alƙiyamarki ta tsaya. Ga ciki yana motsi, yana girma amman ba ciki bane”
Kukana ne ya sake tsananta, ina ganin meye laifi danna zaɓi in rayu da sanyin idaniyata. Soyayyar da nake ma yaya Hamma ta wuce gaban kwatance, dan ko mayyace Hama bazai sa in janye aurenshi ba.
Ganin kukana yayi yawa ga dare ya raba Uwani taita rarrashina.
A daren ranar bacci banba, ni innaji cikina yayi motsi sai tsoro, dan bansan dame nake rayuwa a ciki ba.
Washe gari ni ko wanka banyi ba muka wuce, da ƙyar da suɗin goshi Uwani tasa nasha kokko da ƙosai biyu muka wuce.
Motar Karamar hukumar warawa muka shiga, daga warawa muka hau akori kura zuwa Ƙauyan Lahadin makoli. Daga lahadin makolinma saida mu ka yi tafiyar ɗari bibbiyu a Acaɓa. Tafiyar ɗari biyu a ƙauye bafa ƙaramar tafiya bace. Sai gamu a wata bukka da mata masu ciki zuzzube a ƙasa. Wasu cikinsu ya kusan haihuwa, wasu kuma cikin kamar dai nawa, wasu ma cikin bai kai nawa ba.
Layi Uwani ta kama mana, muka samu mu kai azahar, ta siya mana ɗanwake da mai da yaji. Ni bakina ma ɗaci yake yi da ƙyar dana sa ɗanwaken a bakina na haɗiye.
Uwani dan Allah ki rabu dani da abinci. Ki barni inji da damuwata” Murmushi tayi tace.
“Ki yarda da Ubangijin daya kuɓutar dake daga hannun larabawannan da suka nemi ranmu. Ki kuma yarda da ubangijin daya taimakeki kika auri Gwadabe a lokacin da duk wanda ya kalli alaƙar cewa yake bazai yiwu ba. Ki yarda da ubangijin daya ƙadarta miki auren Hamma har kika shiga wannan halin. Ki yarda zaki samu taimako daga gareshi. Iyabo nasanki da tawakkali da ɗaukar komai ba komai ba. Amman naga wannan lamarin kin ɗaukeshi da matuƙar zafi. Kici abinci kar ki kashe kanki”
Wallahi maganganun Uwani sai suka wanke mun kai. Wani tawakkali ya sakko mun. Murmushi nayi nasa hannu na karɓi ɗanwaken na cinye tas na sha ruwa. Na dubeta nayi murmushi. Itama murmusawa tayi. A haka har layi yazo kanmu. Mu huɗu muka shiga masu ciki, sai Uwani ta biyar. Ta farkon itace ta soma bayaninta, wanda ya gigita tunanina.
“Malam shekarata uku ɗauke da wannan cikin. Ni ban haihu ba, ni ban huta ba Malam. Naje wajen masu magani iri daban_daban amman ba’a dace ba Malam. Kishiyata ce ta biyun taimun baki a lokacin da mijinmu yake rawar ƙafar na samu ciki yana saka ran haifa mishi namiji. Shine tace, in dai tana doron ƙasa ban isa na haife cikinnan ba. Shekaru uku kenan har mijin ma ya gaji ya sakeni, ina gida da ciki”
Take zufa ta wankeni, jikina ya shiga ɓari. Malaminne ya soma magana da cewa.
“Kwantar da cikin akayi bazai yi gaba ba bazaiyi baya ba. Amman kin kawo kukanki gidan mutuwa
Akwai aljanin da zamu sa ya tayar miki da cikin. Zaki kawo baƙin raƙumi, da baƙin bunsuru, da ɓakar tunkiya, da baƙar mage. Wannan shine ladan aikin”
Zumbur na miƙe ina haƙi, tari ya kamani na nufi hanyar waje. Uwani ta biyoni tana riƙeni muka fita.
Uwani dama kina ta’amali da bokaye ban sani ba muke ta abota?” Na tambayeta raina a ɓace hankalina a tashe.
Ita kanta a cikin rudu tace.
“Wallahi Allah bansan boka bane. Kinsan Allah da girma yake Iyabo wajannan wata maƙociyatace ta taɓa zuwa, tana neman maganin haihuwa, ita ta kwatanta mun. Barni da Balbalin kema kin sani harkar shirka bana ciki. Mu maza mu bar wajannan danni gabana ma faɗuwa yake yi”
Ba shiri mka bar wajen, a ciki na baro takalmina warin ƙafar hagu.
Bamu muka koma gida ba sai wajajen sha ɗayan dare wallahi, gajiya, yinwa duk mun kwaso. Ni babbar damuwata bansan ko Allah zai amshi sallolinmu ba. Duk da shine masanin gaibu, munje wajenne ba tare da ilimin boka bane.
Ni dai a zarge na rama sallolina.
Uwani Allah yana gani zan koma gida muita adda,a da izinin Allah zai mun mafita. Bazan sake zuwa asibiti ko wani maganin gargajiya ba. Lokaci zaiyi halinsa, Allah zai nuna ma Hama ikonshi nayi wannan imanin Allah zai dubeni.”
Kwanana goma cib a garin Kano. Kwana huɗu a gidan Uwani, kwana shidda a gidanmu.
A kwanaki gomannan na siyar da zinaraina, Uwani ta sai gidana dake jikin nata muka gagganɗa kuɗin aka siya mun gidan sama mai ɗakuna goma sha biyar, da shaguna huɗu. Burodami Kokodeen da Burodami Debisi, da Uwani sune suka zama shaiduna, muka biya aka gyara takaddu da cike_ciken abinda ya dace, na kamo hanya na dawo, gida na hannun Uwani da Burodami Debisi su zasu saka haya su amshi kuɗin hayar.
Ƴan canjinan da suka ragemun, na siyo kayan aune, aune, da busassun kayan miya, da maggi dunƙule da fari, da dai abinda duk nasan ina buƙata. Iyaa Debisi ma tayi mun tsarabar doya, garin alba, garin amala, bushasshiyar gandane. Burodami Debisi shi kuma shinkafa da wake ya aunarmun mai yawa, ya kawo nama akaimun miyar stew soyayya mara ruwa ƙaramar robar fenti.
Uwani kuma kayan miya ta siya da yawa aka niƙo ta tafasamun ta duramun a jarka aka zuba mai a saman, yana daɗewa sosai bai lalace ba. Banda tarkacen su yajin daddawane, jan yaji ne. Tsaraba dai rigi_rigi na koma da’ita. A tasha na samu Yaya Hamma a tsaye kamar yadda ya saba yana jiran dawowata.
Da magriba matan gidan duk suna tsakar gida anata aikace_aikace sai gamu mun shigo da sallamata. Ga yara na bina da kaya rigi_rigi. Yaya Hamma shima yana riƙe da wasu kayan.
Hmm kunsan me? Da muka gaisa da matan gida saina nufi ɓarayin Yafendo na yada zango acan. Yaya Hamma kuma ya wuce masallaci, dan anata kiraye,kirayen Sallah.
Bayan na rama sallolina Baɗɗo ta kawo mun tuwo naci. Sai Yafendo take faɗamun mummunan abinda ya afku bayan kwana uku da tafiyata.
“Jabu ai bayan tafiyarki da kwana uku gobara ta tashi a lungunku. Da ɗakin Safiya, da Ɗakin Fatu ƙarama da naki. Ƙurmus suka yi babu abinda aka ɗauka. Gobarar daga ɗakin Fatu ƙarama ta tashi, anyi ruwa mamako saita shiga da gaushi ɗakin. Ashe ya kama zanin gadonta ita bata sani ba, cikin dare sai wuta ta tashi.
Murmusawa nayi idona na hawayen da suke shirin makanta ganina nace.
Allah yasa sa da abinda ya tare” Yafendo ta girgiza kai tace.
“Ameen. Bayin Allah duk sun kakkawo taimako anata kan karɓa kinsan mutanen ƙauye da haɗin kai.
Zamu kwana tare dake anan har zuwa a gyara miki ɗakin naki. Su Safiya duk suna gidansu.”
To Shikenan Yafendo mun gode.
Shigowar Yaya Hamma yasa Yafendo ta fice ta bamu waje.
Zama yayi yana fuskantata, ni kuma inata share hawayen da nayi yin duniya yaƙi tsaiwa, da kanshi yake hankaɗo kanshi.
Kallon tausayi yake yi mun, mai cike da tsantsar so.
“Kiyi haƙuri Jabu. Haka Allah ya ƙadarto mana. Daga wannan sai mu faɗa wannan. Aikin gadin dana samu ma ya kuɓuce mun. Matar gidan tasa an ɗakko ɗan uwan mijin a ƙauye an bashi aikin. Shanun da nake gadara dasu duk sun soma ciwo, yanzu haka Yuguda ya tafi dasu asibitin dabbobi. Annobar bace ta samu shanun. Waɗanda shanayensu basu kama ciwo ba, duk sun tafi ciranin dole, dan gujema annobar. To mu kam kusan rabin shanunmu ciwon ya kamasu, jikinsu duk kuraje. Kaɗan daga ciki da basu fi ashirin ba Jumare ya tafi cirani dasu.
Kiyi haƙuri zan sai miki kayan ɗaki gwargwadon halina.”
A’a Yaya Hamma. A halin yanzu bata kayan ɗaki ake ba. Mu yi adda’ar Allah ya kawo sauƙin wannan annoba data samu shanun kawai. Babu komai zamuita lallaɓawa”
Jigum_jigum muka yi. Kunsan dai bafulatani da Shanu. Baffa Musa ma ance yana kwance babu yadda yake a dalilin shanayenshi wajen bakwai sun mutu. An siyar da kusan goma. Jikin nashi yayi tsananin tsananta. Haka a daren muka je dubashi baya gane ma wanda yake kanshi. Mu dai gamu jigum_jigum su Dada sai sharar hawaye suke yi. Domin shi suke gani a makwafin uba a garesu.
Wannan kenan. Su Yafendo ne suka yanke shawarar data tashi hankalina cewar asubar fari Yaya Hamma ya kora shanun Baffa Musa ya tafi wannan cirani dasu.
Ai kuwa hakan akayi, a gidan Baffa Musa dukka muka kwana. Washe gari sassafe gun_gun matasa da magidanta suka haɗe kawunansu suka ɗau hanyar dokar daji, su kansu basusan a ina zasu samu garin da zasu yada zango su kafa tantinsu ba. Har waje nabi Hamma ina kuka. Ku dubi kunya irinta bafulatanin mutum amman gam Yaya Hamma ya riƙe hannayena yace.
Har abada soyayyarki ta dabance a zuchiyata bazan mance da halaccinki a gareni ba. Jabu ki tayani da adda’a ba zan fi shekara ɗaya ba ko dan inzo inga abinda kika haifa zan dawo. Bazan mutu ba har sai Allah ya sake ara mana lokacin da zamu sake shinfiɗa sabuwar rayuwa. Yara goma sha biyu zaki haifamun dukka maza in sha Allah.”
Ina kuka ina murmushi mu kai sallama yabi ayarin gungun fulani da gungun shanaye, suna tafe suna waƙar fullanci ta nuna jarumtarsu.
A ranar nayi kuka sosai. Sun tafi babu jimawa dan ko awa uku ba’aiba da tafiyarsu Allah ya ɗauki ram Baffa Musa sanadiyyar mutuwar shanunshi fulani da shanu ba dama ne.
A wannan shekarar anyi asarar dukiya anyi asarar rayuka sosai. Dan wasu da kansu suka kashe kansu, wasu kuma zuchiya suka haɗiye suka mutu.
Haka akaita zubar da gawawwakin dabbobi abin tausayi.
Wasu wannan ne yai silar karayar arzikinsu ciki harda Mijin Cubu, da mai Nagge mahaifinsu Baɗɗo, danshi kab shanunshi wayar gari akayi asa tarar sun mutu. Sai ya zama kamar wani zautacce_zautacce haka.
BAYAN WATA UKU
Ina zaune a ɗakina da wuta taci aka gyaramun na buga tagumi ina tunanin ko Allah zai sa mu sake ganawa da Yaya Hamma sai Allah. Ga cikina ya girma watanshi kusan takwas da kwana goma sha ɗaya. Yayi girma sosai, kullum fargabata yaya zanyi mu rabu da wannan ciki nake. Ƙila shine ajalina dan inaji a raina kamar ƙarshen rabuwata da yaya Hamma kenan. Yafendo ce ta leƙo.
Na ɗago na dubeta.
“Jabu kina zaune kina faman aikin tunanin kina da juna biyu? Maza fito ki sha iska ga magani na dafa miki kisha”
Da dabara na tashi, dan cikin ya girma sosai. A ƙofar ɗakinta ta shinfiɗamun tabarma na zauna ina haki. Maganin zaƙi ta bani cikin kofi na kafa kai na shanye, kasancewar ba magani mai ɗaci bane. Ta ajjiyemun lafiyayyen Nono yaji dambu shi kaɗai nake iya sha, bana gajiya. Sai in sha sau nawa. Gashi nonon ma wuya yake yi kasancewar babu shanun yanzu. Su Baɗɗo ma sai kwalba da madara suke ma ƴar dabara su fita dashi a matsayin nono, in ba a gabanka akayiba ba ka ce ba Nonon usul bane.
Yafendo sai jana da hira take yi har su Baɗɗo suka yo sallama suka shigo. Hama ma cikinta watanshi huɗu a jikinta tana ta dai gwalli ita namiji zata haifama Yaya Hamma daya dawo zai zo ya tarar da abin mamaki. Ni dai dama kunsan a mugun tsorace nake, ku kunsan komai.
Cikina a daren daya cika wata tara wajen sha biyun dare ina kwance a kasa a bukkar Yafendo naƙuda ta tashi. Dama kwana biyu dai inajin jikin babu daɗi a tsaitsaye dai nake yi.
Gobe ba zaku samu ba yauma dan nayi alƙawarine ayimun afuwa.
MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
Part 16
NAMA YA DAHU…
ROMO ƊANYE
BADI’AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
LITTAFI NA UKU (16)
MARAƊI:.
BAYAN WANI LOKACI.:
Abubbuwa da dama sun faffaru a cikin wannan shuɗewar lokaci. Ciki harda rasuwar Balaraba. Ta rasu wajen haihuwane ta haifi ɗiyarta mace sai aka mayar mata da sunan mahaifiyarta. A lokacin Anti Badi’a shayarwa take yi, sai ta ɗauki Balaraba ta haɗa da Saifullah taci gaba da shayar dasu. Duk matan gidan sun ƙara haihuwa banda matar Mammada da ko ɓatan wata bata taɓa yi ba. Hadiza, da matar Sabitu kuma suna turawa haihuwa ko yau ko gobe.
Malam ya samu lafiya sosai sai dai Baba Fhatsima tana cikin halin jinya sosai. Watansu kusan uku tana kwance a asibiti cutar ciwon zuchiya take yi. Daga baya Malam yasa aka sallamota suka koma yin na hausa.
Ta bangaren Gwadabe sai godiya dan a yanzu in ba’a kirashi hamshaƙi ba a kirashi mai kuɗi. Ya samu rufin asiri sosai da sosai. Ya ɗebo yaranshi ya dawo dasu kusa dashi. Toye yana hannun Hadiza, ƴan biyu kuma suna hannun Shafa dama sun saba. Rayuwa ta warware musu sosai. A ko da yaushe a cikin yi ma Bara’u aike yake. Damunan bana ya taimakama Bara’u da kuɗi yayi noman gyaɗa ya samu albarkar abun sosai da sosai.
Wannan kenan
Shafa ce tsaye a tsakar ɗakinta tana ta jijjiga yarinyarta mai suna Iyabo yar wata Takwas yarinyar akwaita da kuka, bacci ma basa iyayi. Gashi Allah ya jarabci Shafa da samun wani juna biyun na uku kenan, watan cikin biyu a jikinta sai ɗan karen laulayi ga fitinar Iyabo mai kukan banza. Ƴan biyu ne suka dawo daga makarantar yamma ta malam suna jaye da hannun Abba suka shigo da alawa a hannunsu malam ya basu.
Kamar daga sama Shafa ta jiyo kamar Hadiza na ƙwalo mata kira.
“Zo ku zauna Toye karku fito. Zanje ɗakin su ummi yanzu zan dawo.” Tana gama fadin haka ta fito da sauri. A falo ta samu Hadiza tana murƙususun naƙuda.
“Shafa kije ki kira mun Anti Badi’a dan Allah naƙuda nake yi.”
Da sauri Shafa ta nufi ɓarayin Anti Badi’a ta sanar mata halin da ake ciki.
“Abinda za’ayi Shafa ki shiga cikin gida ki karɓo rubutu a wajen Malam sai ki sanar musu halin da ake ciki.” Tare suka tawo Shafa ta wuce cikin gida, Anti Badi’a ta shiga wajan mai naƙuda.
Ciwon naƙuda har magriba haka su Gwadabe suka dawo suka tadda wannan lamari. Sau uku Malam nayo rubutu Baba Asshi na kawowa abu har bayan isha ana abu ɗaya.
Dole aka tafi da Hadiza asibiti a motar Yaya Tasi’u ranga_ranga. Tafiyarsu da kaɗan Allah yai ma Baba Fhatsima cikawa gida ya ruɗe aka fasa kukan mutuwarta. Su Gwadabe suna hanya Malam ya kira Yaya Tasi’u yana shaida mishi halin da ake ciki. Haƙiƙa anyi babban rashi a cikin wannan zuria. Rashin daya taɓa kab ahalin gidan, mutuwar data sauya zukata daga ƙiyayyar juna zuwa haƙuri da dangana. A rayuwa komai yana da mafari, kuma komai yana da ƙarshenshi.
Su Yaya Tasi’u suna shiga asibiti aka shige da Hadiza, amman likitoci sun bayar da sanarwar tiyata za’ayi mata. Gwadabe hannunshi na rawa yasa hannu a takaddar amincewa, da gaggawa aka shiga da’ita. Yaya Tasi’u ya matso kusa da Baba Asshi, da Gwadabe, da Anti Badi’a yace.
“Allah yayi ma Baba rasuwa muna fitowa. Ɗazu a mota kiran da malam yayi mun kenan. Tata ta ƙare Baba, sauran namu ya rage inma mu haɗe kawunanmu mu zama zuria ɗaya, imma mutuwa tai ta yi mana ɗauki ɗaiɗai”
Abun mamaki mutuwar Baba Fhatsima ta jijjiga Baba Asshi dan rikicewa tayi da kuka kamar ba kishiyarta ba. Yaya Tasi’u ya share hawayenshi ya riƙe hannayen Baba asshi yace.
“Ki yarda ki zame mana makwafin Baba. Ki amince a kawo ƙarshen wannan tashin hankali mutuwa ci take kamar rana.”
Baba Asshi yau itace ta sa kanta a ƙirjin Yaya Tasi’u tana kuka. Dukkansu a wajen kuka suke yi. Gwadabe abu ya rikice mishi ya haɗe mishi biyu, ga mata a wani hali, ga suruka kuma uwa ta rasu. Da Yaya Tasi’u da Baba Asshi suka koma gida, akabar gwadabe da Anti Badi’a sunata kaikawo idanunsu jawur kamar garwashi. Sai misalin ƙarfe sha ɗayan dare aka fito da Hadiza daga ɗakin tiyata tare da ɗiyarta macce zuwa ɗakin hutu. A lokacin ne Gwadabe ya samu sassauci daga tashin hankalin da yake ciki. A haka suka yi kwanan zaune asubar fari Gwadabe ya kama hanyar gida.
Yaje ya tarar ƙofar gidan Malam dafifin al’umma ne kawai suka cika ƙofar gidan, Malam na da jama’a sosai, haka Baba Fhatsima matace ta mutane kowa nata ne banda ɗan banza.
A cikin gidanma cike da mata anata koke_ koke kab yaran gidan sun zo, ko wanne ka kalla yana cikin tashin hankali marar misali mutuwar ta doki waɗanda ma ba,ai zato ba dan a kuka harda su Sabitu sai haƙuri ake bashi. Sabitu a tsakar ɗakin Baba Fhatsima ya gama rarrafenshi, goyo kuwa Tasi’u ne kaɗai ya fishi more bayanta, sai shi yazo a na biyunshi.
Gwadabe ya kutsa kai zuwa turakar Malam inda duk yaran gidan suke, matan guda biyu manya suna ciki ana ma Baba Fhatsima sutura.
Zama Gwadabe yayi yana sharar hawaye.
“Tasi’u kuzo ku fito da makarar zuwa falo kui mata adda’a a kaita makwancinta” Malam fa yana zaune babu yadda yake tsabaragen damuwa, ciwonshi ma tun jiya yayi tsanani ya bari a kaishi asibiti yaƙi yace shi zai sallaci gawar ƴar aljanna, ya sata a kabarinta.
Yaya Tasi’u da Gwadabe ne suka fito da gawar suka ajjiye a gaban Malam. Malam ya girgiza kai yace.
“Fhatsima Allah ya baki sa’ar tafiya. In dai sai miji ya ɗaga ƙafa ake shigewa aljanna to Fhatsima ke ƴar aljanna ce. Annabin Rahama yasan da zuwanki”
Yayi mata adda’a sosai. Sai yaran gida kowa yayi mata, sai su Baba Asshi da jiki yayi tiɓis tsoron Allah da nadamar abubuwan da suka faru ya shigesu. Cikinsu babu wacce batai nadama ba, domin babu wacce bata cutar da Baba Fhatsima ba. Banda zarginta da asiri da suke yi.
Yaya Tasi’u da Yaya Jamilu ne suka fito da gawar Malam na biye dasu sauran yaran suka mara musu baya. Nan gidan ya kaure da salati da kuka har aka fita da gawarta. Duk wanda zaiyi magana a kanta halinta nagari yake faɗa, duk wanda zaiyi magana zai ambaci mai yawan kyauta. Gardawa ma sun ci kuka domin uwarsu ce.
Tsabar al’ummar da Baba Fhatsima ta haɗa sai a ƙafa aka tafi da’ita zuwa makwancinta, gidanta na gaskiya. Daga haka jikin Malam ya rincaɓe dole akayi asibiti dashi cikin wani mummunan yanayi malam ya shiga, yanayin da dole a cire rai da tashin shi. Yaya Tasi’u da Amaryar Malam ne a asibitin. Su Yaya Jamilu da Baba Asshi suka ci gaba da karɓar gaisuwa. Ga Hadiza a kwance inda take ma bata sani ba. Abba da Toye suna wajen Shafa. Baba Asshi ce ta yafito Shafa ta zo inda take.
“Shafa maza kije ki haɗa kayan karyawa aba Gwadabe ya kai musu asibiti. Matar wanku tana can bata ci komai ba. Ki haɗa akaima wan naku ma nasu. Kuje da Zaliha maza”
“To Baba”
suka tafi da Zaliha ruwan tea suka dafa, sai suka yi tuwon shinkafa dama Shafa na da lafiyayyar miyar kuɓewarta mai kyau tasha naman rago da bushasshen kifi. Fitowa su ka yi da kayan Abincin. Zaliha taje ta kirawo ma Shafa Gwadabe yazo.
“Ga kayan abinci. Wannan Yaya za’a kaima. Wannan su Yaya Tasi’u za’a kaima. Yayan ta sauka ne?”
“E ta sauka tun jiya da daddare ta samu mace. Nayi waya da su Bara’u da Tamu tun cikin dare asussuba suka kamo hanya. Ance su Babala da Yaya Hambali ma suna hanyar zuwa baki ɗaya.
Shafa tace.
“To Allah ya kawo su lafiya”
Abincin ta bashi, ta koma cikin gida akaci gaba da amsar gaisuwa. Baba Asshi dawowa tayi ɗakin Baba Fhatsima da zama tare da su Ine. Dan duk wanda yazo gaisuwar ɗakin yake nufa. Surukan gidan aka wakilta ɗaura abinci a can gidansu. Domin baƙi daga nesa da zasu zo.
Amman maraɗi garine na karamci in anyi mutuwa fanteka_fanteka ake shigo da abinci har sai anyi bakwai.
GWADABE
Ya isa asibitin farkawar Hadiza kenan, tana kukan cikinta na mata ciwo”
“Dole zai miki ciwo ɗinki akayi miki Hadiza kibi a hankali.” Cewar Anti Badi’a. Suna cikin wannan maganar Gwadabe ya shigo shi da Mammada da abinci.
“Hadiza sannu da jikin” Cewar Mammada kenan. Gwadabe ya karasa kusa da gadon ya dubeta cikin so yace.
“Yaya jikin naki Hadizata, ya sabuwar Baby da muka samu? Wannan Baby ta bamu wahala sosai.
Sannu Anti Badi’a ina kwana?”
Ya ƙarashe maganar da gaishe da Anti Badi’a.
“Lafiya lau Gwadabe. Mammada sannunku fa da haƙuri”
“Yauwa Anti Badi’a. Sannu da kwanan asibiti.Ni zan leƙa Malam zan kai mishi abinci, ina zuwa dan ba jimawa zamu yi ba”
Hadiza bata gane me suke nufi ba sam dake a cikin zafin ciwo take. Ma’aikatan jinyar aka kira suka sake mata allurar bacci ta sake komawa bacci. Huduba Gwadabe yayi ma jaririyar da sunan Babala.
“Gata Anti Badi’a nayi mata huɗuba da sunan mahaifiyata Hauwa Ai mata alkunya da Mami. Ni zanje in duba malam daga can zamu wuce. Amman Shafa zata zo ta zauna dan lallai ana matuƙar buƙatarki a can gidan”
Jaririyar ya miƙa mata ya zaro kuɗi wadatattu ya ajjiye mata ya nufi ward ɗin maza.
Al’amarin jikin malam ya girmama ba’a buƙatar kowa ya shiga ɗakin ma da yake. Abun jawo numfashine a bakinshi, da wasu robobi da ma’aikatan aikin jinyane kaɗai zasu iya sanin menene ( Khadija maidoki ana magana) suke sagale a jikin malam. Kuma likitoci sun tabbatar musu malam ya shiga koma sai dai aita tayashi da adda’a domun ba lallai bane ya tashi. Amman aita mishi adda’a. Ba’a shiga ɗakin sai dai ka hangoshi ta taga yana kwance, lokaci guda Malam ya rame ya zuge saiya sake tsayi da haske sosai.
Jikin su Gwadabe a sanyaye hankali kuma a tashe suka bar Asibitin tare da Amaryar Malam suka tawo gidan tana buƙatar zuwa gida ƴan uwanta sunata kiran wayarta duk sun cika ɗakinta bata nan.
Zuwa yamma sakaliya sai gasu Babala da su Goggo Iyatu da Goshi, da Yaya Hambali, da Yaya Halima, sai Yaya Haula.
Jim kaɗan da zuwansu sai ga su Bara’u suma sun iso.
Abun mamaki a cikin taron mata Gwadabe ya kwashi su Bara’u suka je yima su Babala ta’aziyya. Babala ta yi maza ta fice a ɗakin ma baki ɗaya. Goggo Iyatu ce kaɗai ta amsa gaisuwarshi itama a wulaƙance.
Yaya Hambali kuwa ko da Gwadabe ya miƙa mishi hannu bai karɓi hannun ba. Yaya Tasi’u dake kusa dashi yace.
“Haba Alhaji Hambali menene yayi zafi haka shi ba wuta ba. Yanzu yaronnan ba zaku sarara mishi ya samu yaci gaba da zumunci daku ba, ina laifin wanda ya gaisheka ko da bare ne balle jininka?”
Murmushi Gwadabe yayi yace.
“Ai babu komai Yaya Tasi’u. Yaya Hambali kayi haƙuri in sha Allah bazan sake ba ma” Iyakar abinda Gwadabe yace kenan. Kunsan masu kuɗi da saurin hasala sai Yaya Hambali yace.
“Mitsiyaci kar Allah yasa ka sake. Kai ni inka kuma nuna ka sanni ma bazan yafe maka ba. Ɗan iska wanne irin baƙin ciki da tashin hankali ne baka sa Babala a ciki ba. Sanadiyyar baƙin cikinka har hawan jini saida ya kama mana uwa. Ɓace ka bani waje”
Bara’u ne ya ɗaga Gwadabe suka koma tabarma matasa irinsu, yayi jigum yama rasa ta cewa. Yana sha’awar yaga ya shiga cikin ƴan uwanshi ayi wasa ayi dariya tare.shin sai yaushe wannan lokacin zai zo ne? Shikenan shi bashi da damar da zai ko da gaishe da Babala ta amsa mishi, wannan rayuwa wannan tashin hankali da mi yai kamane?
Hadiza
Ba ita ta farka ba sai da yamma sakaliya ta buɗe idanunta, harta samu ta ɗan sha tea shima kaɗan. Tana cikin ciwo sosai.
“Shafa bani yarinyar in ganta”
Shafa ta matso da yarinyar Hadiza ta ganta harda murmusawa Allah sarki uwa ( na jinjinama duk wata uwa ta faɗin duniya)
“Allah ya rayata da imani. Shafa Gwadabe fa?” Shafa tace.
“Basu jima da fita ba. Su Ine da su Sadiya duk sun zazzo dubaki ma amman bacci kike yi sun jima kuma. Amman yanzu zan kira Gwadabe in sanar mishi da farkawar taki. Baki ga yadda ya damu ba”
Tana kai aya ta ɗaga waya ta sanar ma da Gwadabe farkawar Hadiza.
Ba da daɗewa ba sai gasu shi da su Bara’u.
Nan sukai mata ya jiki da kuma barka.
“Yaya Bara’u ashe kun ƙaraso, ina su Sakinan suke?”
Bara’u yace da Shafa.
“Mun karaso. Su Sakina suna gida.”
Basu suka bar asibitin ba har sai zuwa bayan Isha.
Sun leƙa Malam ma, jikinshi ba yadda yake gaskiya yana jin jiki sosai, sai dai ka hangeshi ta taga.
Tare da Hadiza Shafa ta kwana washe gari da sassafe Baba Asshi tasa Yaya Jamilu ya kawota asibiti, ance gara a sanar ma da Hadiza abinda ake ciki ba sai an dawo da’ita gida taga dandazon ƴan makoki ba. Ƙawayen Hadizan na wajen aikinsu duk sunje gidan, sanar dasu da’akayi cewar ita Hadiza bata san me ake ciki bane yasa suka kasa zuwa wajenta su dubata.
Hadiza tana ganin Baba Asshi da Yaya Jamilu jikinta ya bata akwai matsala, sai dai ko kusa ranta bai kawo mata mutuwace ba. Baba Asshi ta amshi jinjirar a hannun Shafa. Hadiza dai taga duk an gaggaisa cikin giirma da arziki, har Yaya Jamilu na tambayar ko akwai abinda take buƙatane, da mamaki tace mishi a’a.
“Hadiza inaso ki sani a rayuwa duk abinda Allah ya ƙaddara afkuwarshi babu makawa. Inaso ki saka aranki cewar dole wata rana duk daren daɗewa mu iyayenki saimun koma kushewa, ko kuma ku ku koma. Allah yana iya ikonshi akan jinjirin dake ciki a haifeshi babu rai.
Hadiza kiy haƙuri Allah ya amshi ran mahaifiyarku jiya mace mai haƙuri da yakana, macen da tun a duniya mijinta ya mata sitam na shiga aljanna. A iyakar zamanmu da ita alkhairi taita nufarmu dashi mu muna binta da sharri. A yanzu na gane gaskiya tashin hankali da rarrabewar kai ta kau.” Da sharar hawaye ta ƙarashe maganar.
Hadiza kuwa babu abinda take yi sai kuka.
Amman yadda da ƙaddara wajibine a wajen ko wanne musulmi. Dole haka ta ɗauki dangana. Ta kuma yi farin ciki a lokaci guda na sauyin da aka samu a cikin gidan. Sai dai kuma zukata suna cikin taraddadin halin da Malam yake ciki.
Haka akaita zaman makoki har zuwa bakwai. A wannan zaman an yi meeting kusan sau huɗu na haɗin kai domin manyan gidan so suke su samar da sauyi sosai kafin samun lafiyar malam. Kowa ya shiga tattayinshi. Ta bangaren yara mazan su da suka ɓata su akaba wannan ɓangaren suka tusa matansu gaba da zazzafan gargaɗi, da barazanar rabuwa dasu indai suka ƙi a zauna lafiya.
Har wannan lokacin su Babala sunanan. Amman daga Gwadaben har Shafa Babala bata amsa gaisuwarsu. Yaranma da Shafa tayi karambanin kwaso su ta kawo mata saita ɓige da yima Iyabo Allah ya’isa ganin Toye ya fama mata mikin da Iyabo ta ji mata rauni.
Ranar da akayi sadakar ukun a ranar aka sallamo Hadiza ta dawo gida. nan aka shiga tururuwar shiga gaisheta, haɗe da ta’aziyya, da kuma yi mata ya jikin Malam duk ita kaɗai. Hadiza da ƙannenta mata da yarta Zarah suka haɗa kansu sukaci kuka, a ranar sai mutuwar ta dawo musu sabuwa fil. Musamman da dangin Baba Fhatsima suka shigo yi musu sallamar zasu koma sai kuma sunzo sadakar arba’in.
Su Babala ma a ranar suka koma, su Sakina suma shirin tafiyar dai suke yi. Gwadabe yasa an tafi dasu Toye ya sanar dashi ya nemi Uwani ta rakashi ya kaima Iyabo yaran su ganta. Dan a kwanakinnan yana wasu irin munanan mafarkai akan Iyabo da bai gane ma hakan ba.
Kafin goman safe gidaje biyun ya zama iyakar iyalan gidanne kawai a ciki.
Hadiza tana kwance shiru Gwadabe ya shigo da sallama, ya nemi waje ya zauna idanunshi jawur. Dan yanzu Babala taci mutuncinshi ta zazzageshi harda dana sanin haihuwarshi ma saida tayi. Lamarin daya addabeshi, tsoro da fargabar makomar rayuwarshi ya ratsashi.
“Sannu da shigowa” Hadiza ta faɗa a raunane. Dubanta yayi dole ya danne damuwarshi, ya matsa kusa da’ita dab ta yadda suke jin saukar numfashinsu yana sarƙewa.
“Yauwa Yaya jikin, ya ƙarin haƙurinmu?”
Kukane yazo mata yayi wub ya tallafeta ya rungume matarshi tsam yana jin wani bala’in sonta na ratsa duk rassan jikinshi. Haɓarshi ya ɗaura a tsakiyar kanta ya lumshe idanunshi. Munanan furucin Babala na mishi kaikawo a ƙwaƙwalwarshi. A lokaci guda zuchiyarshi ke buga wasu irin tamburan tashin hankali.
Sun daɗe sosai a haka. Sallamar Shafa ce yasa Hadiza zamewa daga jikinshi, amman suna manne sosai da juna ta shigo.
Ganinsu a irin wannan yanayin sai ya ɗan daburta Shafa. Dama ruwan tea da faten dankalin turawane ta kawo ma Hadiza ta samu taci, tunda ance abu me ruwa ruwa zata ci gudun kar tiyatarta ta samu matsala.
A teburin dake gaban gadon ta ajjiye tiran .”
“Ashe ka dawo, sannu da dawowa. Su Yaya Bara’un har sun tafi?'”
A sanyaye take magana kuma sai satar kallon irin zaman da suka yi a manne take yi.
“Yanzu na shigo nazo duba Hadiza ne dama yanzu zan shigo.”
“A’a kayi zamanka kayi jinyarta har Allah yasa ta warware. Kaga a halin yanzu a cikin damuwa sosai take, barinta ita kaɗai akwai hatsari ni na yafeka har na tsawon wata biyu. Kuma zan dinga yin girki harna wata biyunnan”
Tana kai aya saita nufi hanyar ficewa abunta. Gwadabe kasa magana yayi dan mamaki.
“Shafa” Hadiza ta kirayi sunanta tana daf da fita. Cak ta tsaya a inda take ta juyo suka haɗa idanu.
“Nagode sosai Shafa Allah yaa saka da Alkhairi.”
Murmusawa tayi tace.
“La Yaya babu komai. Wannan shine zaman taren. Ummi ma tana wajena kinsanta da rigima duk saita dameku”
Fita tayi ta koma ɗakunta ta zauna a bakin gado, ta lumshe idanunta wasu hawaye masu ɗumi suka zubo mata. Ji take soyayyar Gwadabe kamar zata tarwatsa mata zuchiyarta. Amman ta jima da fahimtar hankalin Gwadabe, da soyayyarshi kacokam akan Hadiza yake.
Sallamarshi taji. Tayi saurin goge idanta. Ƙur ya ƙura mata idanu harya zo ya zauna dab a kusa da’ita bai dena kallonta ba. Tausayinta sosai ya hudashi. Juyo da’ita yayi ya fisgeta da ƙarfi ya mannata a ƙirjinshi ya mayar da hannayenshi ya nannaɗeta.
A tare suka sauke ajjiyar zuchiya. Wani kuka ta sake mai ƙaramin sauti ta kasa mallakar kanta.
MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI CE
Part 17
NAMA YA DAHU…
ROMO ƊANYE
GAWURTATTU UKU
BADI’AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
LITTAFI NA UKU (17)
IYABO:.
Salati nake yi a hankali ina shan yaji tare da karkaɗa ɗan yatsana. Kamar an tashi Yafendo ta taso ta’iso inda nake ta dafa mun kai.
“Jabu haihuwar tazo kenan? Alhamdulillah bari inje maza in taso Unguwar zoma tazo ta kula dake”
Tayi maza ta fita, bata jima da fita ba saiga Baɗɗo tare da Hama sun shigo. Ɗago idona da suka yi ja nayi nasa a cikin na Hama. Sai naga ranta fes tana tsaye a kaina tana murmushin dana kasa fassarashi. Sauke kaina nayi naci gaba da roƙon Allah akan ya saukeni lafiya yasa in haifi mutum ba wani abunba. Kafin Yafendo ta shigo ita da unguwar zomannan na gama jiƙewa da zufa sharkab. Da unguwar zomannan ta shigo sai tace.
“Ni a ƙa’idata bana karɓar haihuwa da mutane a ɗakin. Dan haka duk ku fice ku barmu daga ni sai ita”
Fita suka yi aka barmu mu kaɗai.
“Sannu Jabu ki saka dauriya zaki sauka lafiya. In baki ji nishi ba kar kiyi, hakan ke galabaitar da mata da yawa. Nishin zai zo da kanshi sai kiyishi iya karfinki nan da nan zaki haihu” Ni da unguwar zoma mukaita fama haihuwa dai tazo da tangarɗa kafin wayewar gari na fa galabaita bana ko motsin kirki.
“Kaɓoji aje a nemo mota a kai yarinyar mutane asibiti kar tazo ta mutu, ko abinda ke cikinta ya mutu. Ni tsawon shekaru Ashirin dana shafe ina unguwar zoma banma taɓa karɓar haihuwa irin wannan ba. Cikin yana sama bai faɗo ba, kuma naƙudar take yi”
Kafin Yafendo ta fita ta dawo jini ya ɓallemun. Baddo da Hama ne a kaina, in Hama ta faki idon Baddo saita danna mun cikina da iya ƙarfinta ni dama ganinsu sosai ma banayi.
A gurguje a acaɓa aka tafi dani asibiti ni ina tsakiya Yafendo na baya ta riƙeni tamau, su Baɗɗo na biye dani.
Ya ilayi ranar naga duniya, naga azabar da ko maƙiyina bazan mishi fata ba. A haka aka sake tarairayoni aka sakani a cikin akori kura zuwa cikin Girei
Duk motsin da motar tayi da wani shiga rami sai inji kamar hanjina zai zazzago dan azaba.
Muna shiga asibitin aka bani gado ma’aikatan jinya biyu suka rufu a kaina.
Can a waje anata yima su Yafendo faɗan damme zasu bari in galabaita haka.
Ni dai awana biyu a asibitin da kaina na haifo kyawawan yara maza ƴan tagwaye. Dishi_dishi nake ganin yaran ga gashi lub a kansu, gasu kamar yaran turawa da yaran a zuchiyata naji dif duhu ya maye gurbin hasken da nake gan.
Ban sake sanin inda nake ba sai washe gari da safe na buɗe idona naga ƙarin jini a hannuna, ga jariraina a gefena, yara tsabar kyau kamar na aro. Juyowa nayi na ɗaga kaina na dubi Baɗɗo, na dubi Kari. Na lumshe idanuna inajin tsantsar farin ciki da Allah ya ƙadartama wannan yara zuwa Duniya yaran da kusan asibitoci sama da huɗu suka duba basu gansu a cikina ba. Allah yayi ikonshi gasu sun fito duniya. Inama Yaya Hamma yananan yaga kyawwawan abokananshi masu tayashi kiwon Shanu. Murmusawa nayi a lokaci guda wasu zafafan hawaye suka zubomun. Na farin cikine kukan na tsallake siraɗi. Murmushin kuma na taya Yaya Hamma farin cikine burinshi ya cika ni dashi mun haɗe mun zama abu guda, jininshi ya tsaga ya fito ta jinina yaran kamar an tsaga kara da ubansu.
“Adda sannu yaya jikin?” Cewar Baddo ta yo kaina.
Murmushi nayi mats duk da jikina babu ƙwari amman zuchiyata fes take.
Da sauƙi jiki Baɗɗo. Sannunku, an sanarma Dada kuwa?” Dariya Kari tayi tace.
“Sannu Adda. Dada ta sani tun jiya. Yau kwananki ɗaya a asibiti”
Wata yinwace ta murɗa mun cikina da nake jin yanai mini ciwo_ciwo.
Baɗɗo yinwa nake ji sosai”
Da sauri Baɗɗo ta ɗauki kofi ta cikomun da kokko mai zafi. Kari ta taimaka mun na zauna, na jingina bayana da kan gadon. Ina shan kunun ina kallon yarana da aka lulluɓesu a cikin tawul ɗaya . Ma’aikaciyar jinyace ta shigo ward din tana bi gado_gado har ta iso gadonmu ɗakin duk masu jegone a kwance da jirajiransu abun sha’awa. Jinin da ake ƙaramin ta cire mun dama ya ƙare yanzu. Ta dudduba yaran dai haka, nima ta tambayeni ko akwai abinda ke damuna nace da’ita babu. Sai tace dani. Zuwa da rana zasu sallamemu ni da tagwaye muna cikin ƙoshin lafiya. Ta ɗauki yaran taita yabon kyansu dai haka ta ajjiyesu ta matsa gado na gaba.
Yaran na ɗauka na ɗaurasu akan cinyata ina kallonsu da kyau. Wasu siraran hawayene suka gangaro a kumatuna. Ni da kaina nayi musu kiran sallah a kunnensu. Na dinga musu adda’a ina tofesu dashi. Ina cikin haka sai ga Hama, Safiya, Daso sun shigo da kwanukan abinci niƙi_niƙi. Ko ranar da da aka kaini gidan Hamma a matsayin kishiyar Hama, banga ɓacin rai makamancin wanda take ciki yanzu ba a fuskarta. Dani da yaranma sai naga tana wani harararmu, idanunta sunyi ja kamar ma tayi kuka.
Safiya da Daso duk sukaimun ya jiki tare da yi mun barka. Wallahi babu abinda Hama tace dani. Anata kururuta kyan ƴan biyu tare da mamakin girma da kamanninsu da mahaifinsu. Funfurumfus Hama tayi ta zizarama idanunta kwalli taba banza ajiyarmu. Murmushi nayi cikin ƙarfin hali nace.
Baɗɗo miƙama Hama yaran ta gansu”
“A_a bassu bakya ganin nima ji nake yi da kaina.”
Murmushi nayi dama nasan ba ɗauka zata yi ba. Na gwadata ne kawai.
Baɗɗo jakar hannuna an tawomun da’ita kuwa? Inason in kira Uwanine, da Debisi in sanar musu” Jakar Baɗɗo ta miƙo mun daman. Na ciro wayata na kunna. Burodami Debisi na soma kira na sanar dashi haihuwar. Sannan na kira Uwani itama na sanar mata.
“Ai kuwa gara da kika sanar mun dan yanzu haka muna hanyar Adamawa tare da Bara’u abokin Gwadabe mijin Sakina”
Sai naji gabana ya tattake ya faɗi da jin sunan Bara’u.
Uwani ince dai lafiya dai ko?” Na tambaya a raunace. Hama idanunta ƙam a kaina tana karantata.
“Lafiya lau sai alkhairi ke dai sai mun karaso kawai”
Mu kai sallama na sauke wayata.
“Jabu ga fa abinci Hama ta dafo miki. Baɗɗo ki zuba mata ko?”
Cewar Daso kenan. Jin haka yasa nace.
A’a ta bar abincin bakina babu daɗi sam. Baɗɗo in kina jin yinwa zaki iya ci, ni kam ko zanci sai anjima. Na koma nayi kwanciyata yarana suna kan cinyata ina jiyo ɗumin abuna. Miƙewa Hama tayi da fullanci tace.
“To ni kam zan tafi gida, sai kun dawo”
Tana faɗan haka ta kara gaba, Daso tabi bayanta. Safiya ce taimun sallama cikin mutunci. Suna fita Amaduyal yana shigowa da kwano a hannunshi. Farfesun kazar hausane Dada tayi tace a kawo mun. Nako ci da dama nasha romon sosai shima take bacci ya ɗebeni bani na farka ba sai wajajen azahar.
Na farka ba da daɗewa ba aka kawo mana takaddar sallama da kuɗin da zamu biya. Baɗɗo ce taje biya dan Yafendo ta bata kuɗi daman ko za’a buƙata.
Ina zaune jigum saina hango Bara’u a gaba rike da Taiyo da kahinde, Tabalbalin na biye dasu ga Toye a gefenta.
Idanu na lumshe, Allahu Akbar naji daɗin ganin yarana fiye da tunanin masu karatu. Jina nayi kamar an tsundumani tsuungum a Aljanna.
“Tsuntsun soyayya ƴan biyun aka sake haifo mana? Masha Allah”
Miƙa mishi ɗaya nayi, Uwani ma ta amshi ɗaya.
Sakkowa nayi na rungume su Toye dukkansu.
Wato akwai ciwo rabuwa da yara, Toye ne kaɗai ya ganeni, su dai su Kahinde sunyi lub a jikina kawai. Naji daɗin ganinsu a cikin shiga mai kyau, da dukkan halamu Gwadabe ya samu rufin asari ba kamar yadda na sanshi ba.
“Iyabo ashe Allah yayi yara sun fito duniya? Kai masha Allah ji yara tubarkalla kamarsu sak da ubansu.”
Ɗan murmushi nayi ma Uwani tana fama da ƙaton ciki hancinta duk ya buɗe.
Bara’u barka da zuwa, yaya bayan rabuwa, yasu Sakina?” Dariya yayi yana jinjina kanshi.
“Duk suna lafiya Iyabo. Da fatan kin samu kai lafiya. Banga maigidanba ko a waje.” Ɗan murmushi nayi nace.
Sun tafi cirani kiwo kamar yadda akasan fulani da fita kiwo.”
Murmusawa yayi yace.
“Allah ya dawo dashi lafiya. Yara kuma Allah ya rayasu cikin aminci. Ga yara Gwadabe ya aikoni dasu tun daga Maraɗi yace a kawosu su yi wata guda, sai in dawo in ɗaukesu da yardar Allah.”
A Maraɗi kuma Gwadaben ya koma da zama?”
Na tambaya da mamaki.
” E Maraɗi yake da zama kusan shekara bakwai kenan. Gidan Baba Magaji wansu Babala. To yana auren Hadiza yarinyar Baba Magaji. Da Shafa ƙanwar Abokinmu Tamu, yaranshi huɗu ciki harda takwararki.”
Mamakine ya kamani. Gwadabe da mata biyu? Iko sai Allah, dama yana da ra’ayin mata biyu kena, ko bayan rabuwarmu ne ya samu ra’ayin?
Kafin in gama tantance fari da baƙi Bara’u ya miƙo mun hoton diyar Gwadabe takwarata. Nasa hannu na amsa na zuba mata idanu kyakkyawa fara da’ita.
Nayi farin ciki da Gwadabe yasa sunana ashe dai bai mance dani ba.
“Kin ganta wannan itace Iyabo. Shafa kanwarmu itace ta haifeta, shine yasa aka kaita gidan ɗaukar hoto aka ɗauketa dan a kawo miki ki ganta.”
Allahu Akbar. Naji daɗi sosai Bara’u Allah yabar zumunci”
Baɗɗo ce ta dawo daga biyan kudi. An gama komai sai tafiya.
Sallama nayi da matan ɗakin muka wuce. Tare duk muka rankaya zuwa gida. Baɗɗo nasa ta kai Bara’u gidan Dada, ni kuma aka wuce dani gida.
Wajajen bayan Isha can, bayan nayi wanka naci tuwo, Amaduyal yazo ya ɗauki abincin Bara’u da nasa akayi mishi, Da tsaraba Amaduyal yazo yace Bara’u ne yace a kawo mun. Su Toye suna ɗakin Yafendo ta janyesu.
“Iyabo na ƙosa ki bani labarin bayan rabuwa. Da ganin ɗakinki abubbuwa da dama sun faffaru. Naji kince Hamma ya tafi cirani. Meke faruwane, ga kishiyarki naga sai dukan yaranta take yi tana baloƙoƙo?”
Hmmm Tabalbalin meye ma bai faru ba?”
Nan na shiga mata labari daki_daki harna dire mata.
“Iko sai Allah Iyabo. Kina ganin rayuwa kekam iri_iri. Amman watarana fa duk sai labari, amman da kikayi gobara da saiki sanar mini kema kinsan zan turo miki da duk abinda kike buƙata, kuma zanzo ki ganni kiji daɗi. Baki ga yadda kika fita hayyacinki ba. Bara’u ma sai kallonki yake yi yaga duk kin lalace kin koma baƙauya fitik, jibi wata atamfa ruwan kwara_kwara a jikinki”
Banso inyi dariya ba amman ni da Uwani muka tuntsure da dariya. Sallamar Yafendo Jabu, da Dadane ya katse mana hirarmu.
Maraba Yafendona, Dada sannu da zuwa”
Tabarma na shinfiɗa musu a gefe suka zauna muka gaggaisa, Uwani ta miƙo musu yaran. Sai ga Yafendo dasu Toye da Baɗɗo sun shigo.
“Kunzo ganin mazajen naku kun kasa haƙuri sai gobe. Dada inyalli jam?”
Dada ta yi ma Yafendo murmushi aka gaggaisa, suka ga su Toye tare da shi musu albarka.
“Jabu wannan biyun naki macen naga sai ƙananun kuka take ɗanyi dai, tana ambaton Mama.”
Da yarbanci na kirata abun mamaki sai gata tazo na ɗaurata a cinyata nace.
Menene kike kuka Taiwo?”
Sai take ce mini ita gida zata tafi wajen Babanta.
Nan dai Yafendo tai mata dabarar ta bari sai gobe sai a kaisu.
Su Dada dai su kai mana sallama suka fita.
Ƴan biyu sai sheƙa baccinsu suke yi, ruwan nonona inaji yana zuwa.
“Iyabo ni ɗinnan fa a cikin damuwa nake sosai. Ni da ba dan wannan cikin ba, da kuma ina tunanin wahalar da yarana zasu sha a hannun matar ubansu ba. Ke da auren zan ajjiye wallahi in huta, na gaji matsaltsalu iri da kala.
Ko kinsan yanzu ni da Hafizu sai gani sai hange baya iya yin mu’amalar Aure dani abun baya yiwuwa. Tun yana so, harya haƙura. To daga baya ma aka dena lissafin wani rabon kwana, sai sanda yaga dama yake shigomun. Dama kuma na daɗe da korarshi a aiki, amman ya samu wani Alhaji ya sai mishi victira yana lodin ƙauyuka. To akan matarshi ya tare, ni dai da yarana sai dai fa in ciyar damu. Ɗan sauƙin dana samu ma kasuwancin Allah ya dafa mun mun haɗe shagunan ma duka biyu na zuba kaya sosai, na ɗauki su Ummi aiki tunda su zuchiyarsu ta mutu”
Ajjiyar zuchiya na sauke nayi ƙuri ina kallon uwani harta dire maganarta.
Rayuwarnnan bata tafiya face da tarin tulin matsaloli sune abokan tafiyar rayuwar. Ke ina ke ina wani barin gidan aure kina da gidanki, kina da sana’arki?
“A’a ni ƙuncine bazanta ƙunshewa ba Iyabo. Ke kinsan bani da daɗi. Rannan anyi haihuwa a salam layinmu. To mai haihuwar ƙawartace, ni kuma yarinyar kostomatace dan nina haɗa mata kayan haihuwa. Kinsan yarinyarnan saina shiga na taddata tana ba ƙawayenta labarin ai tayi asiri ta kashe na Hafizu gaba a gidana bashi da fus. Kaza_wa_kaza dai ni kuma sai gani.
Zagewa nayi na kirɓata wallahi, a daren kwana muka yi ni da Hafizu muna rikici. Ke nifa bazan mutu Lokacin mutuwar tawa batai ba.”
A lokacin dai sai haƙura da hirar muka yi, muka kwanta.
Washe gari da safe muka ɗaura.
Ina zaune fitowata daga wanka ban daɗe ba kenan. Yafendo Jabu ta gama ma yara wanka ta muƙo mun su, na zura musu nono suka hau sha. Baɗɗo ta shigo da tuwo a kwano yaji yajin daddawa da manshanu sharɓan.
Baɗɗo an kaima Bara’u abun karin da Uwani tayi mishi?”
“Ai gashi nan ma a tsakar gida fitowarshi daga wajen yafendo kenan. Yace in kiraki ke da Adda Uwani shi zai koma”
Yafendona tace.
“Jeki maza. Baddo ke kuma ki fitar da ruwan wankan da kayan yaran ki wanke. Ni sai in zauna da yaran”
Ajjiyesu nayi duk sunyi baccima, na saka takalmi da mayafi muka fito.
Bara’u wai harka fito sai tafiya?”
Taiwo na maƙale dashi gam.
“Wallahi ai naso asussuba ma in koma gaskiya. Iyabo Allah ya raya, ni zan koma sai nan da sati huɗu zan dawo ɗaukarsu. Ga Taiwo ta ɗaneni so take ta bini fa”
Kuɗi ya zaro nera dubu huɗu ya miƙo mun. Uwanice tasa hannu ta karɓa. Muka haɗa idanu da Hama wacce ta kafa ta tsare tana kallonmu
“A siyi sabulu ayi wanki. Ni zan koma. Allah bashi in mai gidan ya dawo a gaisheshi”
Godiya mai tarin yawa nayi mishi, na bashi manshanu soyayya da nono kindirmo cikin jarka, harda zakara nasa Baɗɗo ta kama aka ɗaure mishi. Nace ya kaima sakina. Godiya yayi ya fice, da ƙyar ya ɓanɓare Taiwo a jikinshi. Yarinyarnan tafi awa tana kukan banza harda birgima. Ina jiyo Hama na zage_zage a tsakar gida. Yafendona ce tai ta rarrashinta fa da ƙyar tayi shiru.
Can maƙota suka shiga tururuwar zuwa, tare da dangi na kusa gida ya cika tab da ƴan barka. Kunsan ƴan biyu akwai farin jinine. Haka aka dinga zuwa ganin ƴan biyu. Kab zuriyar su Dada babu wanda yake da ƴan biyu sai nice na kafa wannan tarihin. Irin baƙin cikin da Hama ta dinga nunawa abun ba’a cewa komai. A cikin ruwan wankan jariran tasan yadda tayi ta jefa allurai biyu, Yafendona tana sa Hassan allurar ta caki duwawunshi wajen ya fashe sai jini.
Dani da duk masoyana hankalin kowa ya tashi. Nifa tsabaragen ruɗewa fisge yaron daga hannun Yafendona nayi na shiga karanto mishi duk adda’ar da tazo bakina. Matan gida suka cika a ƙofar ɗakin kukan yaro har maƙota wallahi. Ana zubar da ruwan wanka saiga allura guda biyu. A masai Baɗɗo ta jefa alluran. Anata mana Allah ya kyauta, amman fa alkinkimar ko a tsakar gidanma bata. Sai sabon ruwan wanka Uwani ta ɗaura tayi zamanta har ruwan yayi zafi ta juyo ta kaawo ma Yafendona.
Kafin magriba ba sai jikin yaro ya saki ba, ga zazzaɓi ya rabkeshi.
“Iyabo ina zuwa. Bari kiga in koya ma matarnan hankali”
Da sauri najawo Tabalbalin nace.
Kul cikine da’ita kar a yi ta Hajiyayye da Yaya Uwa ( NA FAƊO DAGA BENE.. NA ZARCE RIJIYA)
Batta a niya bi a niya. Na tofesu da adda’a babu komai. Yaran da ko duniyar ba’aso suka zo ba.
Da Allah dai na haɗata har suka fito duniyar. Yanzunma na haɗata da Allah. Ammam in wani abun ya samu ɗana, ko kuma ya mutu baki ɗaya. Zanyi abinda ni da Hama sai dai mu yi mutuwar kasko”
Dawowa Uwani tayi ta zauna. Ni dai ina riƙe da ɗa ko nono yaƙi kamawa. Abu fa kamar wasa bamu runtsaba a gidannan sai jefin asuba dana tuno bari in mishi karatun Qur’ani a kunne.
na soma karanta mishi wallahi sai yaro ya sauke ajjiyar zuchiya, a_a ba sai bacci ba. Sannan ne hankalinmu ya kwanta. Ni dai dana soma baccin wahala saida na kai hantsi. A hakanma Cubu ce ta tasheni sunzo da yaran Baffa Musa.
Yafendona tace.
“Ai gara ki daure kije kiyi wanka. Me jego bata zama da yinwa a jikinta.
Wankan na daure naje nayo, abincinma tutturawa nayi babu dai daɗi. Har dai zuwa rana yaran suna lafiya ƙalau babu wata matsala. Baɗɗo da Cubu ne suka goya biyu aka kaima Dada su ta gansu dan ba zata iya zuwa ganinsu ba a kunya irinta fulani. Dawowarsune Baɗɗo take faɗamun wai taga mahaifinsu a wajen Dada yana rarrashinta ta koma.
Kafin in bata amsa sai ga sallamar gungun ƙawayen Hama sun shigo, harda ita da tun a tsakar gida da muka haɗu ban sake ganinta ba sai yanzu.
Uwani ta miƙa musu yaran suka amsa. Wata zabiya a cikinsu tace.
“Ba shakka yara sak ubansu, Amarya daga zuwa taci gida” Ta faɗa tana dariya kamar ba magana ta cusa mana ba. Uwani ta kalleta tace.
“Taci gida, taci miji ba. Saima kunga ta sake haifo wasu ƴan biyun ko ƴan uku du maza tukunna. Marasa mutunci fitsararru zaku zo har ɗaki kuna watsar mana da magana.”
Ƙwace yaran daga hannunsu tayi tace.
“Ku tashi ku fice mana da gani tatattun marasa tsoron Allah. Ke kuma Hama na dawo kanki da ba dan kina da ciki ba da saina miki ɗan banzan duka kafin in koma garinmu, Jabu ƙyaleki take yi kinsan karonmu ai babu daɗi”
Hama ta taɓe bakinta ta miƙe tsaye da ciki. Ƙawayenta suka tashi tsaye suma.
“Jabu kina ji ƙawarki na cin zarafin mutane kin kasa dakatar da’ita? Nifa ban gane me kuke nufi ba kuna dai son ƙalamun sharrine ni bani na saka allura a ruwan wankan yara ba. Kamar yadda kuma Jabu ta haifi maza ai nima abinda ke cikina kenan. Hamma kuma nawane kowa ya sani. Uwani ki bar ganin a baya kinci galaba a kaina ki rikeshi ya zame miki makani. A yanzu nafi ƙarfinki. Hafsatu mu fitar mata a ɗaki”
Ni dai da uwar harara kawai nabi bayanta naja dogon tsaki nace.
Jahilar mace wacce bata san kanta ba”
Harta fita suka juyo a tare ita da ƙawayenta.
“Ni kike kira da jahila? Oho dai da jahilcin nawa muka haɗa miji, mijin da yai miki gata harda uwarki da ƙannenki tunda shike ciyar dasu abun kunya”
Da sauri na miƙe tsaye na nufi Hama ni da Baɗɗo.
“Yayi kyau Hama sannunku da naimam fitina, ke dai kin kasa kwantar da kanki ku zauna lafiya ke da abokiyar zamanki, yanzu abun ya kai har Addan tawa kike zagi. Dan Hamma ya ciyar da’ita shine abun gori shi da yar mahaifiyarshi. Kul kika sake yinƙurin zagin Jabu a gidannan dan in ranki yayi dubu sai ya ɓaci wallahi.”
Yafendo ta ƙare mata tanadi tas, dalilin da yasa na koma ciki kenan. Ammam na ƙudure a raina na daina ragama Hama kwata_kwata a gidannan, in dai ta cakaleni zan mayar mata kamar yadda mudubi yake maida hoton fuska.
A cikin zaman bakwai ɗinnan ba fa ƙaramin rikici aka dingayi da Hama ba tata ɓurza babu wacce ba’aiba. Komai masifa ta takurama su Taiwo sosai ni fa sai gidan Cubu aka kai yaran dan tsabaragen fitinar Hama.
Ana jibi suna Uwani da Baɗɗo suka shiga kasuwa ranar kasuwa suka siyomun wasu kujeru marasa hannu dogaye biyu da wan_wan biyu, sai gadon katako waya goma sha biyu, da katifarshi. Uwani ta sai mun labule da ɗan abubuwan da baza’a rasa ba. Harda atampa kala biyu, sarƙa da ɗan kunne da takalmi daman uwani ta tawo mun dasu, da tulin kayan jarirai masu kyau. Dan ranar dasu Baɗɗo suka wanke kayan saida ya cika igiyoyin gidan kab. Ba Hama kaɗai ba fa har daga maƙota zuwa kallon kayan akeyi, dan basu taɓa ganin kayan jarirai masu yawan haka ba a cewarsu. Hama kuwa yi tayi kamar ta haɗiye zuchiya ta mutu.
Ko yau ma hakance ta faru da rana fatse_fatse Hama na zaune tana ma yaranta tsifa ta saki wuyan riga nono duƙui a waje, ni kuma na fito shanyar kayan ƴan biyu da Cubu ta gama wankewa dan itama ba daɗi take jiba.
Sai ga su Uwani suna dambe da kujeru. Bafa wasu kujeru masu kyau bane irinna ɗakinta ne amman wallahi sai kawai Hama ta fashe da kuka da kururuwa tayi ɗaki a guje.
Dariya muka kwashe dashi ni da Uwani kawai.
“Marar mutunci ni da nice kishiyarki tsirara zaki fice sabida duka, ƴar baƙin ciki, yara dai gasu Allah ya nufa sun zo duniyar, haka da zaran Hamma ya dawo zai sake ɗirka mata wani cikin ƴan biyun.
Cikin awa guda ɗakin me jego ya fito fes, har sabuwar leda suka siyomun komai yayi shar dashi, atampopim kuma aka kai mun ɗinkinsu maƙotanmu.
Washe gari Baɗɗo ta daddage ta yarfamun kitsona kaina ya fito shar dashi, su Dada da su Yafendo suma sai tasu hidimar suke yi. Da yamma saiga mijin Baɗɗo da raguna maza tiƙa_tiƙa biyu ya shigo. Baɗɗo dama tun bayan gama mun kitso ta tafi Girai ta siyo kayan miya da duk abun buƙata, shinkafa na bata kudi ta siyo mai kyau harda soɓo da kayan haɗinshi jallof muke so muyi da soɓo aci a more.
Da yamma sakaliya sai ga Amaduyal tafe da Anty Mulka, da Iyaa Beji, da Bose. Da kayansu na gara rigi_rigi abun sha’awa.”
Mrs Bukhari
Part 18
NAMA YA DAHU……
ROMO ƊANYE
BADI’AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
18
IYABO:.
Harda lemun kwalba kiret biyar suka tawo dashi da gararsu riƙi_riƙi. Buhun shinkfa, garin Amala, wake, doya, manja, harda soyayyar jar miya aka tawo mun da’ita. Ga suturu ɗinkakku da aka kawomun Burodami Debisi ne yasa duk aka ɗinkamun kayan tas, ga takalmi ƙafa biyu ga su ɗankunne da sarƙa, ƴan biyu ma sun sha kaya, ni dai dana gansu naga kayan da suka kawo sai kuka kawai
Anty mulka tace.
“Ki dena kuka Iyabo wannan shine zumuncin ai. Kinganmu har anko muka yi wanda zamu saka ranar suna. Sai dai kin rame kin mugun lalace sai kace ba ke ba, wani abun akeyi miki a gidan. Ko kuma matsalar miji, ko kishiyane?”
A jejjere tai mun tambayoyin duk sun kafeni da idanu suna son jin amsar bakina. Sai Bose tace.
“Dole fa kiga ta lalace a ruga fa take aure. Jibi a irin gida da ɗakin da take rayuwa, kuma ita ta zaɓarma kanta zaman” Hararar dana doka mata ne yasa tayi shiru.
Babu komai Anty Mulka nayi ciwo a cikinnan. Laulayin da ban taɓa yin irinshi ba nayi. Amman lafiya lau nake zaune da mijina, kishiya ita kuma zaman haƙuri akeyi da juna”
Su Taiwo da Kahinde ne suka shigo da gudu da yaran Kari. Iyaa Baji tace.
“Waɗanda ba yaranki na wajen tsuntsun soyayya bane? Harma yasan a inda kike aure kenan? Ahhh Ahhh Iyabo”
Uwani ce ta ƙwaceni ta hanyar mu su bayanin yadda akayi, shine suka barni na sarara. Babu laifi sun samu tarba mai kyau daga wajen Yafendo, Dada ma ta ƙuƙuta tayo musu farfesun kaza an aiko musu dashi. Maƙota sai zuwa gaishe da baƙi suke yi, anata zuwa gulmar irin kayan da suka tawo dashi. Hama ma ta shigo tako daɗe sosai a ɗakin tafi awa saida ta gama ƙarema kayan da suka tawo dashi kallo tas kafin tai musu sallama ta nufi madafi kuma.
Washegari ranar suna yara suka ci sunansu da suke zuwa dashi Hassan da Usaini.
Tun asussubar fari su Anty Mulka suka shiga hura murhu aka ɗaura tukwanen girkin suna. Maƙota suka cika gidan dam jama’ar su Baɗɗo da Dada, da jama’ar shi Yaya Hamma. Dan kab matan abokanshi saida suka shigo taya aiki. Ta ɓangaren mazan gidan suna daga gefe anata aikin fiɗar ragunan suna, Uwani tana bakin rijiya ita da Bose suna gyaran kayan ciki. Ni kuma ina daga ɗaki ina saka kaya. Farin lace ɗin da Iyaa Debisi tayi mun shi na saka ɗinkin buba da zani na fito shar dani gashi nayi muguwar rama ta mamaki hatta mazaunaina da nake gadara dasu sun sace kaɗan ya ragemun. Sai nayi haske fuskata tayi fayau da’ita ga kitso nasha ga lalle na salateb an rangaɗamun. Ina sanya ma su Hassan kayan da Burodami Debisi ya siya musu yace a sanya musu suci suna. Sai ga Yafendo ta leƙo ɗakin Safiya na riƙe da ƙaton bahun shaƙe da kayan dangin maza, saida sukaimun turamen zani ashirin cib, ƴan biyu kuma sunsha rigina masu hangar roba da masu hangar ƙarfe, omo da mandula da nabkin Kam mun samu da wasu wando me kala kala na yaran fulani. Da wata riga mai ruwan hoda, bulu, yallo. Nasan kun ganeta duk uwar da tayi renon ɗa shekaru ashirin baya ta san wannan riga da wannan wandon.
“Jabu ga namu kayannan babu yawa ayi haƙuri, yanayin garinne kinga anyi annobar Dabbobi an samu karayar arziki sosai”
Murmushi nayi . A raina ina tuno haihuwa biyu da nayi a gidan Gwadabe, a leda ake kawomun kayan dangin miji shima a wulaƙance.
Nagode sosai Yafendo mai yawan kenan ai. Dama yanzu nake son in gama a fitar da kayan da su Bose suka tawo dasu ma.
“Ki barshi in Adda Daso ta kawo na wajenta sai a saka a bawo biyu a fito dashi a shimfiɗa tabarma haka muke yi. Tubarkalla kunyi kyau ke da yaran. Naga yayyensu ma suna tsakar gida duk anci kwalliya”
Murmusawa kawai nayi ta saki labule ta koma ɓarayinta.
Ina gyara ɗaurin ɗankwalina saiga Kari da Cubu da kaya niƙi_niƙi a buhu sun shigo dashi, daga ɓarayin Yafendona suke saida aka kai mata sannan tace a kawo mini. Uwani ce ta shigo.
“Iyabo wannan man kamar bazai isa ai suyan kayan cikinnan ba gaskiya. Ahh cancaɗi kaga Amarya a gidan Hamma. Kai inama angon ƙarnin yananan zanso ganinshi a wannan rana”
Dariya nayi dan ta sosa mun inda yake yi mini ƙaiƙayi. Tun a daren jiya nake kewar rashin mijina a tare dani a lokacin da nafi buƙatarshi.
To kafinnan Uwani zo kiga abubuwan arziki da aketa samu. Sannan a sakasu a bawo a fitar tsakar gida kamar yadda suke yi a al’adance”
Nan Uwani sukaita jejjera kaya, ta ɓangaren Dada ma masha Allah ƴan biyu sun samu kaya sosai. Bawo uku aka fitar shaƙe da kaya. Nan maƙwabta akaita tururuwar zuwa ganin kaya. Da bakinsu suke labarin tunda ake haihuwa a rugar babu mai jegon data kaini goshi. Hama kuwa kamar zata haɗiye zuchiya ta mutu ta huta da baƙin ciki.
Jallof ɗin shikaface sai zoɓo da Amala da miyar ewedu da miyar tumatur da taji ganda. Dan tafi da gidanka su Iyaa Beji suka yi na bushasshiyar ganda, tun jiya da dadare aka jiƙata cikin bokiti da ruwan zafi.
Maƙwabta akaita bi da abincin suna, gidan sunan cike da yara da manya, kowa ka gani abinci da lemun kwalba yake ci.
Ina cikin matan abokan Yaya Hamma suna bani tasu gudunmawar, mai atampa, mai omo, mai kayan yara, masu miƙo kuɗi nayi sai ga Hama ta shigo babu ko sallama. Ganin na canja kaya nasa atampa me kyau dinkin ya zauna sosai a jikina saita sake ɓata ranta.
“Danginane abincin da aka bani bai ishesu ba. Ga kula a zubo musu. Mutum biyu basu samu lemun kwalba ba sai zoɓo”
Kular hannunta na karɓa na miƙa ma Uwani dake zuzzubama jama’a abinci. Babu musu ta cika mata kular tab da jalob ta ɗaura mata kayan ciki.
“Gashi lemun kwalba ne ba zasu iya samu ba. Kinga waɗannan lemun kwalbar da masu shi, suyi haƙuri da zoɓon da suka samu ma” Cewar Uwani kenan.
Hama dai ganin idanun abokan Hamma sai tace.
“Ai babu komai Uwani. Hakanma mun gode”
Ta karɓi kularta ta fita ɗaya daga cikin matan abokan Yaya Hamma sai kurantata take yi tana cewa tayi kyau wannan kwalliya haka.
Haka dai wannan suna ya gabata sai yamma lis kowa ya watse, akabar ƴan gida da wanke_wanke. Tare duk aka haɗu akayi wanke_wanken ragowar abinci daya rage kuma matan gida duk suka ɗebe ko wacce tana faɗin ta huta da ɗaura tuwon dare.
Sai bayan isha su Uwani suka kammala aikinsu tsab. Uwani ta shigo da banƙararrun ragunan da aka rataye a tsakar gida.
Waɗannan ragunan fa Uwani”
“So kike a bari a waje a sace? Uwargidanki tun magriba take sunturi a lungunnan kuma duk wucewa sai ta kalli ragunan taja ƙwafa na jima ina lura da’ita. Yanayinta kaɗai ya nuna ba mutuniyar arziki bace. Cewar Anty Mulka.
Dariya nayi nace.
Yanzu saita ɗauki rago to ta kaishi ina?
Uwar harara Uwani ta doka mun, nayi mata dariya kawai.
Washe gari duku_duku su Iyaa Beji suka tashi da suyar rago. Su Baɗɗo kuma sunata kiciniyar haɗa musu karim kumallo.
Yafendona ce ta juyo ruwan wankan yara, nima ta kai mun nawa.
“Maza Jabu je kiyi wankan kar ruwan ya huce”
Mayafi na ɗauka na fito. A ƙofar bukkata na tarda Taiwo da Kahinde suna zaune suna kuka.
Kallonsu nayi tausayinsu ya kamani, tsugunnawa nayi a kusa dasu. Na shiga rarrashinsu na samu su kai shiru nace su shiga ɗaki su kwanta a kan gado. Ai kuwa babu musu suka tashi suka shige.
Murmusawa nayi nabi bayansu da idanu. Hawaye suka taru a idanuna.
Wallahi barin yara a wani gidan babu daɗi. Kuma duk yadda mace takai sai yarannan sun mance da’ita kuma zasu kasance babu wannan shaƙuwar ta ƴaƴa ga mahaifiyarsu. A hakama Gwadabe yayi namijin ƙoƙari sosai da har ya aiko a kawo mun yaran.
Da ƙyar naja ƙafata na shiga wankan, ban jima ba na fito, na samu Yafendona tana yima ƴan biyu rawa sunsha fararen ovaroll sunyi kyau yara kamar yaran Turawa. Kan gadona na kalla Taiwo da Kahinde sunyi baccinsu sai ajjiyar zuchiya suke saukewa.
Haka aka soya namannan guda ɗaya surutum Yafendo tace a ciremun ɗayan ragon suka kasa kashi huɗu. Ɗaya nasu Yafendo da mutan gidan. ɗaya na Dada da ƙannena. Ɗaya na maƙota, sai ɗayan na dangin Babana. Yafendo tace in dibarma Hama a nawa, an kuma bata kai da ƙafan rago ɗaya, ɗayan da safe shi aka dafe mun naci.
A leda na ƙulla mata na tura yara suka kai mata. Nayi tunanin ba zata karɓama ma sai kuma ta karɓa. Na ƙarama su Iyaa Beji a nawa da Uwani.
Washegari su Iyaa Beji suka kama hanyar Kano. Uwani dama tace saita yi sati guda kafin ta koma.
Wata ranar alhamis muna zaune a tsakar gida ni ina wanki, Uwani na yi mun kwalimar ɗakina saiga Hama ta fito da jaka niƙi_niƙi da yara wai gidansu zata koma ita acan zata haihu taci gaba da zama har sai Yaya Hamma ya dawo.
Kai kawai Yafendo ta girgiza tace.
“A sauka lafiya. Ni bazan hanaki zuwa gidaba tunda wanda kike zamanshi bayanan. Amman ki ajjiye yara a gidansu suci gaba da zama a cikin ƴan uwansu.
Jabu ki karɓi yaranki kici gaba ds da riƙesu har zuwa sanda zata dawo.”
Bafa haka Hama taso ba. Cikin fishi ta ajjiye jakar yaran tayi ficewarta tana maganganu marasa daɗi.
“Allah ya shirya. Jabu kici gaba da haƙuri nima kaina haƙurin nake yi da Hama. Tunda dai aka auroki gabaki ɗaya kafatanin halayenta suka sauya.
Babu komai Yafendo. Ku kuma kuzo mu shiga ciki ko?”
Na tattare yaran muka shiga cikin ɗakina dasu.
Ana gobe Uwani zata tafi da daddare na tattaro mata kayana atampopi kusan kala goma cib nace duk ta ɗinka mun inna tawo sunanta sai in tawo dasu.
“Ki haɗo da waɗannan rigunan masu zubin ƴan ƙauye dukka sai in shiga kasuwa a yi canjin kasuwa in zaɓa musu masu kyau, tunda naga kin samu dayawa”
Ai kuwa kin kawo shawara me kyau.”
Tattaro mata nayi kusan duka kaɗan na rage.
Washe gari sassafe ta yi mana sallama ta kama hanya, kafin dai ta tafi ta faɗamun watannin daya rage haihuwarta sabida kintata zanyi in tawo tunda bamu da network.
Haka rayuwa taita tafiya su Taiwo sukaita bani wahala in wannan ya warke ciwo sai wannan ya kama, canjin ruwa da zaman ƙauye duk saiya sa suka rame ga ƙuraje caɓa_caɓa ya fito a jikinsu babu masaka tsinke.
Ranar da suka cika wata guda a ranar Bara’u ya tawo ya kwana a gidan Dada washe gari suka wuce. Na haɗama yaran goma sha tara na arziki. Taiwo Atampa biyu na bata. Na kulle atampa biyu daban na matan Gwadabe. Toye da Kahinde nasa Uwani ta sai musu kaya kala bibbiyu ƴan kanti duk da dai irin na ƴan ƙauyene amman dai na siya musu. Na siya ms Iyabo kaya itama.
Dada ta haɗa musu tsarabar ƙauye, hakama Yafendo, da su Baɗɗo. Aka dai haɗa musu tsaraba rigijib harda zabi huɗu aka haɗasu dashi wai suyi kiwo.
Kuɗi masu yawa Bara’u ya miƙo mun da kaya cikin babbar ƙatuwar leda yace wai inji Gwadabe yace a bani kuma yanayi mun barka.
Allah sarki Gwadabe. Dan Allah Bara’u kace nagode Allah ya saka mishi da Alkhairi “
“Babu komai ai tsuntsun soyayya. Naso mu tawo da Sakina ma amman tayi nauyine sosai haihuwa ko yau ko gobe. Amman wata rana kwatsam zaki gammu.”
Allah sarki Sakina Allah ya raba lafiya. Nima indai na shigo kano nanda wata ɗaya in sha Allah zan shigo Takai ɗin da izinin Allah.”
Da haka mu kai sallama ya tusa yaran a gaba suka tafi. Mu kuma rayuwa taci gaba da garawa damu. Shayarwa tasa nayi kyau na ciccika sosai. Hankalina ya kwanta sosai a tafiyar Hama gida har ga Allah ni dai saida nayi fatan inama karta dawo.
Gabaki ɗaya gidan da matan gidan duk sun sake. Ƴan biyu kuwa suna ganin gata a wajen Yafendo da ƙannen Yaya Hamma.
Haka dai naci gaba da shayar dasu cikin tsabta da lafiya. Abun mamki nayi ƙiba sosai baku ganni ba, sabida ƴan biyu suna da tsotso sai nima cin abincina ya ninka, dani dasu duk mukai ɓul_ɓul damu.”
Yau tun safe na tashi da shirin zuwa dubo Dada. Da wuri naima yara wanka nayi mana wankin kayanmu na shanya, na goya ƴan biyu na fito.
Ɓarayin Yafendo na nufa nai mata sallama inaso in je dubo Dada daga can zan leƙa Cubu dan ance bata ji daɗi ba.”
“Sai kun dawo ƙila anjima nima in leƙo gidan in duba Adda dan jiya ciwon kai ya sata a gaba” Ni banma sani ba sai yanzu da nake ji.
Ayya ai kuwa zan tafi mata da ƙwayar bature ta haɗiya. Sai mun dawo Yafendo”
Fitowa nayi duk inda na wuce sai na tsaya an gaisa sun ga ƴan biyu kafin in wuce. Ga rana sosai a garin zafi akeyi sosai safiyace amman har rana tayi zafi. Sai naji idona wannan marar ganin ya soma ciwo har yana zubar da ruwa.
Da sallama na shiga gidan Dada ina haki abunka da masu kitse.
A tsakar gida na samu Dada a kwance Yusufu na mata fifita Kari kuma tunda ban ganta a tsakar gidanba nasan bata nan an tafi talla.
“Jabu kune da safe haka? Saifa da nace da Baɗɗo ba sai sun faɗa miki ba shine saida ta faɗa”
Zama nayi a kan tabarmar, na sunto ƴan biyu da suketa kukan zafi. Yusufu ya karɓi ɗaya Dada ta tashi zaune itama ta miƙo hannu in sa mata daya.
A_a Dada kiyi fama da kanki Usaini nauyine dashi ga tumbuɗi”
Murmushi tayi tace.
“Kema lokacin da nake koyonki ai kin fishi girma da nauyi. Cika bayana dam kike yi. Duk inda na wuce sai an kalleni, har ciwon ƙirji saida ya kamani a goyonki. Miƙo shi”
Murmusawa nayi. Ni dai Allah ya jarabceni da tausayin Dada. Sanyin muryarta kaɗai ka iya cika idona da ruwan ƙwalla. Usaini na miƙa mata na tashi na ɗebo ruwa a randa na ɓalla mata fanadol biyu. Na bata ta sha ta kwanta.
Na samu Yusufu ya riƙe mun yaran nayi mata kwalima, na wanke mata tufafinta tas na share tsakar gidan.
Bani na bar gidan ba saida na yi mata miyar tumatur na aika Yusufu ya siyo mun nama da shinkafa. Sai wajajen biyun rana na nufi gidan Cubu.
Da sallamata na shiga cikin gidan abun mamaki kishiyoyinta da girmansu wasu da yaransu a gidan miji ma amman suka saka Cubu a gaba uwargidan ta zauna a ƙaton cikinta sai ihu take yi. Ragowar kishiyoyin suna ranƙwashinta.
Subhanallaah me zan gani kasheta zaku yi ko me?”
A firgice suka juyo suka zuba mun idanu. Hawaye suka gangaro a kumatuna. Cubu numfashinta sai kokuwa suke yi ita dashi”
Mrs Bukhari
Part 19
NAMA YA DAHU….
ROMO ƊANYE
BADI’AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
19
GWADABE:.
Ya daɗe yana shafa bayan Shafa amman ta kasa bama zuchiyarta haƙuri ta dangana. Zuchiyarta ta daɗe tana ƙunsan wannan takaicin na yadda yake kasa ɓoye soyayyar Hadiza a ko’inane ko kara baya yi mata. Sai dai ita tayi mishi kara ta tayashi son abinda yake so. Haka Hadiza ƙiri da muzu taƙi amincewa asa ma ɗiyarta sunan Iyabo. Amman ita tambaya ɗaya yayi mata ta amince mishi. Ko kusa bawai dan tana son sunan bane, tayi hakanne domin son abinda mijinta yake so. Duk kawaici na danginta saida saka sunan Iyabo ya taɓa ransu, Tamu ne yayi kinini a cikin lamarin ya hanasu tayar da zancan.
“Kiyi haƙuri Shafa koma menene ya saki kukan na roƙeki kukanki yana dafani?
Da sauri ta ɗago ta zuba idanunta a nashi a ƙoƙarinta nason ganin da gaske yake yi kukan nata na gasa ranshin kuma. Ja taga idanunshi sunyi harda maiƙon hawaye. A hankali ta sauke kanta a sanyaye tana sauke ajjiyar zuchiya.
“Inason sanin damuwarki da abinda ya sakaki wannan kukan. Ko dai ganin Hadiza da kikayi a maƙale danine ya zaburo miki da kishin ki uhm?”
Shiru tayi tana share hawaye. Niyyar tashi daga jikinshi tayi yayi wuf ya sake dawo da’ita jikinshi. Kyakkyawan riƙo yayi mata ya tallafo haɓarta tare da yima bakinta riƙon alewar yara. Wata duniya suka shilla ta masoya Gwadabe da Shafa sunma mance a duniyar da suke jin daɗin rayuwarsu kawai suke yi.
Labulen ɗakin suka ji halamar kamar a ɗage yake. Shafa ce ta yi saurin juyowa suka haɗa idanu da Hadiza dake tsaye tana hucin kishi. Gwadabe na zaune ko gezau baiyi ba balle yayi yinƙurin tashi.
“Lafiya zaki buɗemun labulen uwar ɗakina babu sallama balle neman izini, in da kinga abinda yafi haka kuma fa? Kinga hakan ai bai dace ba. Baban Abba tashi kuje Allah ya bamu alkhairi.”
“Ni kike faɗama wannan maganar, ashe ba har zuchiyarki kika sallamamun mijin ba? In ba haka ba daga zuwa yayi miki sallama zaku ɓige da soyayya ba kunya babu tsoron Allah. To yayi zamanshi anan wajenki ki bashi abinda yake buƙata. Namiji da kishiya duk amincinku watarana sai sun munafurceka”
Tana kaiwa nan ta saki labulen tayi ficewarta. Shafa ta dubi Gwadabe da taga yayi shiru baice komai ba, shi bai tashi ba, shi bai magantuba. Haƙiƙa taji ciwon maganganun Hadiza, ko dai dama ba yau ta soma yi mata ire-irensu ba, dannewa kawai take yi da ƙoƙarin a zauna lafiya”
“Shafa kiyi haƙuri ki daɗa zan kuma yima tubkar hanci danna fuskanci Hadiza zuma ce sai da wuta. Ni na ɗauka lallami zai bi da’ita ashe ba haka bane. Jeki shinfiɗe yara sai ki dawo”
“Kaifa ai ya kamata kaje ka rarrashi ƴar gwal ɗin taka da baka ƙaunar ganin ɓacin ranta.” Shafa ta faɗa cikin sigar kishi da muryar tausayi ainun. Kunya ta shigi Gwadabe dan tabbas yasan Shafa akwaita da kawaici da yakana.
“Ke dai jeki ki dawo, anan zan kwanta ke ba a gabanki tace in yi zamana ki bani abinda nake buƙata ba?”
Murmushi Shafa tayi kawai ta miƙe taje ta yima yara shinfiɗa ta dawo ta tarar har Gwadabe ya tuɓe yana kwance.”
“Baban Abba kayi haƙuri karka biyema tuburarriyar matarka in kayi la’akari da mutuwar da akayi mata da tiyatar da akayi mata. Inma kana son ɗaukar mataki a wannan karon na roƙeka ka daure. In dai Yaya ce halinta ne zata sake ai.”
Da ƙyar Shafa ta sha kan Gwadabe ya tashi ya mayar da kayanshi yai musu sallama ya fice. Hawayen baƙin ciki Shafa ta sake sharewa ta sake komawa wajen yaranta.
Da salllama Gwadabe ya shiga ɗakin fuska a turɓune, Hadiza tana zaune amman ko kallo bai isheta ba balle har ta amsa sallamarshi. Abinda ya sake ƙular dashi kenan, amman sai ya rabu da’ita ya haura gado ya kwanta yana shafar fuskar jaririyar da sai mutsu_mutsun somin kuka take yi. Ai kuwa kamar jira jaririyar take uban ya taɓata ta ɓalle da kuka. Nan ta shiga canyara kukan inya_inya Hadiza tayi funfurunfus taƙi juyowa ma balle ta san yarinyar na kuka. Shiko Gwadabe mamakine yasa ya kasa cewa da’ita uffan sai idanu da yake bin Hadizar dashi.
“Ke Hadiza wai baki ji yarinyarnan tana kuka bane koko Yaya?” Yayi maganar da kakkausar murya. Hadiza ta sake bama banza ajiyarsu lamarin daya fusata Gwadabe ƙarshen fusata, fusatar da bai taɓa yin irinta ba.”
“Wai shin ba dake nake magana bane Hadiza kina da hankali kuwa?”
Wallahi Hadiza ta sake yin watsin ruwan tsarki da Gwadabe harma ta yi kwanciyarta a gefen gadon ta juya mishi baya.
Miƙewa yayi da jaririyar ya shiga jijjigata dan baƙin ciki da ɓacin rai jikinshi har rawa yake yi, take kanshi ya soma sara mishi.
Shi kam ya gaji da matsalolin Hadiza. A yau yayi ɗan daka ce bai auri Hadiza ba ya rabu da’ita ta auri wani kamar yadda malam yace mishi. Lallai Hadiza mahaukaciya ce sosai. Kukan jaririyar ya karaɗe kab gidan harda ma can cikin gidan. Auwala ne ya tawo shi da matarshi suka shiga bubbuga kofar Gwadabe. Kafin yazo ya buɗe Sabitu ma ya fito.
“Ko lafiyar wannan jinjira wannan kuka ai yayi yawa Yaya Auwala”
Cewar Sabitu. Dubanshi Auwala yayi tare da jin sanyi a ruhinshi jin ɗan uwan nashi gudan jininshi ya kirashi da Yaya. Allah sarki rayuwa. ( Da ace mata zasu gane rarrabe kawunan ƴaƴa ba abu bane me kyau, ba kuma hanyace mai ɓullewa ba da sun huta. Ƴan uba ba abokan gaba bane. Ƴan uba abokan junane dangin junane.)
Gwadabe ne ya fito da jaririya a hannunshi tana shiɗewa.
“Wai lafiya Gwadabe Hadizan bata gidanne yarinya take irin wannan kuka na fitar hayyaci”
Auwala ya tambaya.
“Tana ciki taƙi karɓar yarinyarne kawai. Idanunta biyu tana ji. Iskanci da wulaƙanci take ji”
“Kaji aikin rashin hankali na Hadiza ko. Ku bani waje in shiga in ci ƙaniyarta wawuya kawai”
Cewar Mammada daya ƙaraso wajen. Ya amshe yarinyar yanata jijjigata. Allah sarki shi gashi haihuwar suke nema idanu rufe Allah bai basu ba. Ita Hadiza ta samu tana shirme.
“A’a Mammada banda duka kasan anyi mata tiyata abi komai dai a hankali.”
Cewar Auwala kenan. Auwala ya dubi Sabitu yace.
“Kaje shiyyar su Yaya Tasi’u ka taso su zata gane kurenta.”
Da sauri Sabitu ya tafi aiken da Auwala yayi mishi. Gwadabe ya nufi ƙofar ɗakin Shafa da jaririyar ya shiga aikin buga ƙofar Shafa.
Buɗe sakata tayi Gwadabe ya shiga da jaririya a hannu ya miƙa ma Shafa. Ba musu tasa hannu ta karɓi yarinyar.
“Ki bata Mama tasha, ki barta a wajenki tunda uwar bata sonta”
“To amman kafa…”
“A’a ni ban sanki da musu ba Ina girmamaki akan hakan. Ki sani nasan abinda nake yi.”
Haɗiye maganar dake bakinta tayi ta koma kan kujera ta zaro Mama ta zura ma jaririyar a baki. Nan ta soma tsotso tana sauke ajjiyar zuchiya”
“Allah yayi miki albarka Shafa nagode ƙwarai da wannan soyayyar. Matsayinki na musamman ne”
Yasa kai ya fice. Shafa ta girgiza kanta tana mamakin hali irinna Hadiza.
Fitowar Gwadabe daga ɗakin Shafa yayi daidai da isowar Yaya Tasi’u harda Anti Badi’a dake biye dasu. A falon Hadiza duk suka taru. Gwadabe ya basu labarin iyakar dalilin Hadiza na azabtar mishi da yarinya da tayi.
“Wallahi Yaya Tasi’u haƙurina ya kusan ƙarewa akan sha’anin fitinar Hadiza. In taso in kai ƙarane bazan iyaba. Ni wannan matsalar sabuwace a cikin rayuwata. Ni wallahi tsohuwar matata kafin ince tayi take yi. Haka ma Shafa take yi mun.
Amman fa Hadiza ita kullum a ƙoƙarin ganin laifina take duk iyakar kyautatawar da nake yi mata.”
Hadiza tana tsakankanin yayyenta kanta a ƙasa sai jijjiga kanta take yi da dukkan alamu dai maganganun bakin Gwadabe suna dukan ranta in akai la’akari da Iyabo da Shafa da shi Gwadabe ya ambata. Gyaran murya Yaya Tasi’u yayi yace.
“Allah ya kyauta. Ni na ɗauka wani gagarumin abune ya shiga tsakaninku ma da wallahi bazan ko sakko daga gadona akan wannan shirmen ba ko Auwala ya isa yaba Hadiza kashi.
Kaga Gwadabe kar ka bari ƴan uwantaka ko zumunci ya hanaka gyara gidanka. Kai kasan komai akan abinda yaita gudana a baya a cikin gidan Malam. Duk da muna fatan komai ya zama tarihi tunda ga Sabitu abun sha’awa a zaune a gabana a ɗakin Hadiza kuma.
Ke kuma Hadiza ni zan fi so ki kashe aurenki ki kima cikin gida ki dinga kallon rayuwar tsohon mijinki da tsohuwar kishiyarki. Ku kuma ku tashi kowa yaje ya kwanta.”
Ai nan Hadiza ta ɗago kanta ta dubi Gwadabe duba na wulaƙanci, ta maida dubanta kan Yaya Tasi’u tace.
“Wallahi Yaya Tasi’u Gwadabe ba adali bane. Yafi fifita Shafa da yaranta dan kawai tana da maza a….”
“Tas tas Yaya Tasi’u ya mari hadiza. Auwala ya zuba mata ranƙwashi a tsakiyar kanta, Sabitu ya zubo mata harara. Mammada da Gwadabe ne suka kwaceta dan Auwala zagewa yayi yana neman dukanta sai da Anty Badi’a tayi saurin shiga tsakani.
“A_a Baban Sailuba karfa kuyi kisan kai fa. Yarinyarnan ɗanyan jego take yi, aiki kuma akayi mata. Ke Hadiza tashi ki shiga ɗaki kinji. Gwadabe ka kawo mata jaririyar tata.” Da gudu Hadiza ta shige ciki Sabitu ya bita da mangari Allah ya sota bai sameta ba.
“Wawuya shashasha in baki yi sa’a ba gobe zan sa Zara ta daka mun ke a gidannan”
Cewar Yaya Tasi’u kenan a tare suka fice Gwadabe kuma ya kulle ƙofa yayi kwanciyarshi a doguwar kujera yana tubka yana warwara. Cin mutuncin da Babala da Yaya Hambali suka yi mishi sai dawo mishi yake yi. Yana mamaki ainun ace uwa ta tsugunna ta haifi ɗa ta dena sonshi. Duk da Yaya Hambali shine kanwa uwar gami a tsakaninsu. Mafi yawa_yawan lokaci Yaya Hambali ke zuga Babala ya harzuƙata ta hasaka har ta dinga furta mishi kalaman da basu dace ba.
Wayarshi ce ta shiga kuka ya zaro a ajjihu yaga Bara’u ne.
“Kayi haƙuri ban kiraka naji kun sauka lafiya ba sai kaine ka ɓige da kirana. Ina fatan kun sauka lafiya?”
Bara’u yace.
“Lafiya lau ka gammu a tsakar gida ma da yaran du. Zuwa jibi sassafe zan kwashi yaran muje Kano gidan Uwanin. Inma bamu je wajen Iyabo a jibin ba tunda ba zaman kanta take yi ba. Zan bar yaran a wajenta in tasa mun lokaci sai inje mu je ” Ajjiyar zuchiya Gwadabe ya sauke.
“Allah ya nuna mana. Ina fatan ku sameta cikin aminci in sha Allah. Sannunku Allah ya bar zumunci a huta gajiya”
Da haka suka yi sallama ya ajjiye wayarshi sai ga Hadiza firit ta fito tayi tsaye a kanshi tana jijjiga.
“Burinka ka kaso auren tsohuwar matarka dai kai ka sake aure abinka. Ta dai tabbata Iyabo dai asiri tayi maka. Bata ƙarƙashin inuwar aurenka ma adda’ar aminci kake yi mata. Allah zai saka mana mugu azzalumin banza”
A fusace Gwadabe yayo kanta gadan_gadan dan idanunshi sun rufe hannu yasa ya tureta ta faɗi. Da dukanta ma yaso yayi tausayinta yake ji ga tiyata a jikinta, ga rashi babba da akayi mata.
“Wayyo Allah ka kasheni a kan tsohuwar makirar tsohuwar matarka.”
Da sauri Gwadabe ya juyo me zai gani Hadiza face_face a cikin jini tana riƙe da wajen da akai mata tiyata.
Ranga_ranga suka nufi asibiti a motar Yaya Tasi’u. Tun daga gida Yaya Tasi’u yake faɗa har suka isa asibiti. Kuma Hadiza yake ma faɗa duk da a sume ma take.
Gwadabe kuwa ya shiga tashin hankali mai zurfi. Hadiza ta riga data kaishi maƙura shi gani yake yi zai sauwaƙe mata kawai ya huta gudun kar watarana tasa ya aikata aikin dana sani. Yanzu jibi baƙin kishinta abinda ya ja. Suna isa asibiti aka karɓeta Dr sai faɗa take yi akan ya za’ayi irin wannan saken ɗinkin da akayi mata ya warware.”
Ɗakin sabuwar tiyata aka shige da’ita ga jini data zubar sosai.
Wajen Malam duk suka ɗunguma suka je. Yana kwance kamar mamaci ko motsi bayayi. Duk mai tausayi inya kalli ɗakin da malam ke ciki sai ya zubar mishi da hawaye.
Sun fi minti talatin a wajen kafin Yaya Tasi’u ya shiga wajen Dr ɗin Malam su kuma su Gwadabe suka koma ƙofar ɗakin tiyata.
“Yanzu duk faɗan da akaima Hadiza bata ji ba sai da ta sake takalarka da wani jidalin? Wannan yarinya dai bata ji. Amman fa Gwadabe sai ka zama tsayayye sosai a gidanka kar ka kuskura kayi saken da kan yaranka zasu rabe. Wallahi matsawar haka ta faru Shikenan ni dai na faɗa maka. Kaduba gidanmu sai yanzu ne yake shirin farfaɗowa a haɗe kai. Tun su Yaya Tasi’u suna ƙananu ake abu ɗaya yau shekarata ni kaina nawa? Mata basa taɓa tsufa da kishi shine matsalar balle kace zasu watsar dan kansu. Barinma irinsu Hadiza masu zafin kishi. Itafa tun tana yarinya haka take da wannan baƙin kishin. Duk abinda aka siyo mana sai Hadiza tayi kuka in dai ba da ita za’a siyo ba. A makaranta akwai yarinyar da hadiza ta tsana kasan dalilin?” Auwala ya tambaya.
Ajjiyar zuchiya ya sauke kana yace.
“Sai ka faɗa”
“Sabida yarinyar a ko da yaushe ita ke zuwa na farko a ajinsu. Daga ƙarshe sai da Hadiza ta ƙwace wannan ragamar ta hanyar nacin karatu da dena bacci sannan aka zauna lafiya. Kai itafa tafi kab ƙawayenta kyau bata ƙawance da wacce tasan ta fita dan masifa.
Kai Gwadabe yake ta karkaɗawa yana sauraren Auwala tare da tunanin yadda zai shawo kan lamarin Hadiza. Lallai akwai gagarumin aiki a gabanshi to zaima iya gyara Hadiza kuwa, ko dai rabuwa da’ita shine a’ala a gareshi?
Idanu ya lumshe kanshi na yi mishi zafi.
A haka Yaya Tasi’u ya dawo ya tarar dasu jikinshi a mugun sanyaye da irin yanayin da yaga jikin malam ɗin. Shi kam ma har ya fitar da rai da tashin Malam. Almajiran malam kullum a cikin yi mishi sauka suke suma suna cikin wani hali.
Likitane ya fito daga ɗakin da aka shiga da Hadiza a lokacin wajen biyun dare. Yaya Tasi’u da Gwadabe ne suka bi bayanshi har zuwa ofishinshu, ya basu waje suka zazzauna.
“To mun samu nasarar sake yi mata ɗinki sabo. Tana buƙatar ƙarin jini dan ta zubar da jini sosai. Dan Allah a rinƙa kiyayewa koma menene dai ya faru a lura da’ita sosai tana buƙatar kulawa”
“Doctor mun gode sosai. Zamu iya zuwa du mu biyun a gwada jinin namu in yayi to, akwai ƙaninmu a waje ma in namu bai kai adalilin abinda ake buƙata ba.”
A gurguje dai Hadiza kwananta biyu kafin ta samu ta farka hannunta ɗaure da ledar jini. Yaya Zara tana gefenta a zaune, sai Amaryar Malam.
“Yaya Zara ina ƴata?”
Da abinda ta soma kenan. Da sauri Amaryar Malam tace.
“Zara maza kirawo likita. Sannu kinji Hadiza kai Allah mun gode maka”
Yaya Zara ce ta miƙe ta je ta kirawo Dr suka tawo tare. Ya duba jikin Hadiza tare da yi mata tambayoyi”
“Ku kula kar a bata abinci, sai tea ko kunu zuwa kwana biyu a kula. Sannu Allah ya ƙara lafiya’
Idanu Hadiza ta lumshe hawaye suka zubo mata tana mai cike da nadamar yadda da auren Gwadabe. Data sani tun wuri ta fita sabgarshi yaje ya auri Shafa ita kuma ta auri wani mijin da yafi mata. Da Yaya Zara, da Amaryar Malam, da Hadizan ko wanne cikinsu da damuwar dake damunsu. Ɗakin ya ɗauki shiru na lokaci mai tsayi sosai kafin isowar Isuhu da matarshi da yara.
“Isuhu kune a tafe?”
Baiwar Allah ga waje zo ki zauna”
Zama matar Isuhu tayi da ɗan goyonta a bayanta.
“Sannu Hadiza ya jikin, ya kuma ƙarin haƙurinmu na Baba, ya jikin Malam? Ai daga can wajen malam ɗin muke kafin Auwala yai mana kwatancen nan ɗakin shi da maigidanki”
A daƙile da wulaƙanci Hadiza tace.
“Jiki da sauƙi. Haƙuri mun gode Allah “
Yaran nata ta kalla daga kwance sun wani canja sun yi kyau sosai. Isuhu ne yace.
“Amadu kuje ku gaishe da Mamanku. Hadiza sannu da jiki.
Yaranne suka isa bakin gadon Hadiza ta riƙe hannun mai sunanta gam tana kallonta fes da’ita cikin kaya masu tsada. Gaisheta da jiki suka yi, tare da ta’aziyya. Su gwadawa ne suka shigo ɗakin.
“Gwadabe kun dawo? Sannunku. Zara muje daga waje mu basu waje ko? Amadu Hadiza ƙarama kuzo muje”
Amaryar Malam ta riƙe hannun yaran suka fice. Ɗakin ya rage daga Isuhu da matarshi. Sai Gwadabe da Auwala da Hadiza da take kwance.
“Kiyi haƙuri ban kawo yara sunyi ta’aziyya ba. Bama nanne munje umara. Shi yasa, jiya muka shigo Maraɗi muka tadda labari shine muka tawo. Ga yaran su miki kwana biyu Furare zata zo ta ɗaukesu. Zan sa a kawo musu kayansu. Auwala yayi dariya yace.
“Kako kyauta Isuhu sosai muna godiya da wannan zumuncin, baka duba halin gyatukarsu ba dan da an daka ta tata da zumuncin lalacewa zaiyi” Isuhu ya sosa kai yace.
“Irin riƙon da Malam yayi mini shi kaɗai ka iya riƙe igiyar wannan zumunci ko da ban taɓa shiga rayuwar Hadiza ba. Mu kam zamu wuce Furare muje”
Hadiza zamewa tayi tamkar mutum mutumi dan mamakin kuɗi da Isuhu yayi harda zuwa Umara. Yanzu yaranta sun taka ƙasa mai tsarki kenan, tare da ƙazamar Furaren data raina? Daman hausawa sukance ɗan hakin daka raina shike zamema gagara gasa.
Auwala ne ya takama su Isuhu Gwadabe ya ƙaraso wajen gadon yace.
“Yaya jikin naki Hadiza?”
Banza tayi mishi ta tafi duniyar tunani dan batasan ma Gwadabe na tsaye a kanta ba. Shiru yayi kawai yana karantar yanayinta. Can Hadiza tace.
“Tabb wai Isuhu ne ya je Umara shi da Furare, kuɗi yayi kenan?”
Wannan zancan zuchiyane ya fito fili. Ringing ɗin wayar Gwadabe ne yasa ta juyo da sauri ta ganshi tsaye bisa kanta.
“Bara’u kaddai har kun isa garin su Iyabo tsuntsun soyayya?” Da sauri Hadiza ta dubi Gwadabe shima ita yake kallo.
“Gwadabe kai kaga irin ƙauyen da tsuntsun soyayya ya kai Iyabo kuwa. Haƙiƙa wannan tsuntsu bai mata adalci ba. Iyabo ta ƙare ta komaɗe ta zama bagidajiya sak. Yanzu haka ma tana asibiti ta haifi yaranta biyu du maza”
Turus Gwadabe yayi yana sauraren Bara’u dake mishi bayani. Idanu ya lumshe a gaskiya baiji daɗin jin labarin Iyabo a haka ba.
“Kana ji yarannan in aka barsu a wannan ƙauyen akwai matsala fa”
“A’a Bara’u kar kace haka ka barsu kawai”
Yana faɗar haka ya juya ya fice ya samu gefe guda suka gama tattsunawa da Bara’u. Daga nan ya fice a asibitin ma ya koma gida. Shafa na zaune tana hutawa Gwadabe ya shigo da sallama fuskarnan tashi cike da damuwa. Kwanciya yayi kawai yana kallon sillin damuwa da tunani sun caza mishi kai.
Da sallama Shafa ta shigo hannunta riƙe da ruwan sha a kofin silba.
“Jikin Yayanne kuma? Yanzu na gama girki kenan nake son zamu je ni da matar Mammada da matar Sabitu”
Kuyi haƙuri gobe ba posting sabida akwai aiyukan turaren amare da aka bani kwangilar yi har show glass biyu manya, to kunga aikin da yawa.
Masu son turare su tuntuɓeni ranar asabar zan turo kaya arewa nagode
MRS BUKHARI
NAMA YA DAHU….
ROMO ƊANYE
BADI’AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
LITTAFI NA UKU
20
ajjiyar zuchiya Gwadabe ya sauke nannauya ya karɓi ruwan hannun Shafa tare da miƙewa ya kafa kai ya shanye tas ya sauke ajjiyar zuchiya.
“Nagode sosai da kulawa Shafa. Jikin Hadiza da sauƙi harta farfaɗo tayi magana ma.
“To Allah ya bata lafiya Alhamdulillah. In zubo maka abincinne?”
“A’a bar abincinnan bakina babu daɗi sam. Ku hanzarta kuje ku kaima su Yaya Zara abincin.” Shafa tace.
“Da nace ko zan tafi da yarinyarnan a mayar da’ita wajen gyatumarta tunda ta farfaɗo?
“A’a yarinyarnan ki ci gaba da shayar da’ita na baki ita halak malak horon da zanyi mata kenan.
Idanu Shafa ta zare sai kuma tayi dariya kawai ta bar zancan jin sallamar matar Sabitu a ƙofar ɗakinta. A zuchiyarta ta tafi da niyyar bama Hadiza ɗiyarta.
Ko da suka shiga sun tarar Yaya Zarah sai faɗa take yi ma Hadiza ita kuma sai hawaye take yi. Ganinsu ne yasa tayi shiru. Take jikin Hadiza ya sake rincaɓewa dole Shafa ta sake dawowa da wannan jaririyar.
Kwanan Hadiza goma cib a asibiti aka sallamota da yammar ranar litinin sai gasu da kayansu sun shigo cikin gidan. Nan aka shiga yi mata sannu_sannu. Gwadabe kuwa tun ranar da Bara’u ya labarta mishi halin da Iyabo take ciki da irin rayuwar da take ciki bayan ya dawo Takai. Sai ya shiga damuwa mai tsanani. Ita dai Shafa a tunaninta sabida ciwon Hadiza ne. Amman sai take ganin abun yayi yawa, data tambayeshi sai yace mata kewar yara yake yi ne, kuma baya jin daɗi kwana biyu.
A ranar Malam ya farka ya buɗe idanunshi sai dai baiyi magana ba. Ba shiri maza_mazan da matan Malam suka rankaya zuwa asibiti da surukan gidan matar Jamilu da matar Yaya Tasi’u.
A asalin ɗakin jinya suka tarar da Malam idanshi biyu sai likitoci dake aune_aune a kanshi. Da idanu malam yake bin iyalinshi kawai, saida ya buɗe idanu ramarshi ta sake fitowa. Tasi’u ne ya matsa kusa gareshi sosai. Sai yaga bakin Malam na motsawa.
“Tasi’u kamar fa Malam magana yake yi ko?” Cewar Baba Asshi. Jin haka yasa Tasi’u kara kunnenshi a bakin Malam.
“Fhatsima ina Fhatsima take?”
Abinda Malam yake furtawa a hankali kenan. Likitan malam yace.
“Malam yana buƙatar hutu. Zaku iya fita tunda kun ganshi. Mutum ɗaya ya zauna dashi, ku ku fita.’ Hutawa yake buƙata kar ayi hayaniya a kanshi. Kar kuma a lamince mishi yin doguwar magana dan Allah a kiyaye”
Kai yasa ya fita. Iyalin Malam suka marama Dr baya. Tasi’u ne ya zauna a gefen Malam yana ta shafa sumar kanshi wanda hakan ba ƙaramin daɗi yake ma Malam ɗin ba.
Da ɗaya da ɗaya iyalan gidan Malam sukaita shigowa suna duba jikinshi, a hankali cikin rashin kuzari yake amsawa daya gaji sai ya soma amsawa da ka. Hatta Hadiza saida ta zo ta duba Malam ta koma gida.
Tana dawowa ta soma aikin girki, Shafa tace.
“Yaya ke da baki da lafiya meye naki na yin girk? Ga abinci na kammala haar dake fa”
“A_a riƙe abincin ki kiyi ta ci. Ai na warke ya kamata in karɓi miji ko Shafa?”
Murmushi Shafa tayi tace.
“To Allah ya ƙara sauƙi Yaya. Bari in miƙo miki yarinyar” Hadiza tayi mata wani banzan kallo kana tace.
“Ai da kin barta wanda ya baki inya dawo sai ya karɓota ya kawo mun. In kuma ya bar miki itane huta roro, kinga na huta dama ke ya raina kece wahalalliya a wajenshi”
Haɓa Shafa ta riƙe ita dai bata ce komai ba, dama wanki take yi taci gaba da wankinta. Ragowar yaran suna can cikin gida suna wasansu.
Haka Hadiza tai ta kiciniyar girki. Matan gida duk wanda ya fito yaga tana girki sai yayi mata magana tare da cewa da’ita me yasa bata bari ba. Murmushi kawai take yi dan in tace zatai ta basu amsa zuchiyarta zata iya mata bindiga abubbuwane a zuchiyarta goma da ishirin. Tana zaune a gaban miya tana juyawa Shafa ta fito da jaririyar Hadiza ta ajjiyeta akan cinyarta tana bata nono tana kaɗa miya.
“Kusun uwa, me zan gani haka Shafa ƴata naga kina bama wannan ƙazamin nonon naki gantalalle?” Shafa ta ɗago cikin dariyar cusa haushi tace.
“Wallahi kuwa, ai mai gidanne ya bani ita halak_malak au wai baki ma da labari, ai ta riga ta cika cikinta dam da ƙazantaccen nono amman amintacce ingantacce a wajen mahaifinsu. Dan wallahi Gwadabe na ji da waɗannan nonuwan kasancewar ƴaƴanshi dashi ne kaɗai suka mayar da nonon haka. Ta ƙarashe tana dariya kamar ba magana ta faɗa ma Hadizan ba.
Tana dasa aya taja dogon tsaki ta shige ɗaƙi tana ƙananun mita tare da cewa.
“Mata sai jarabar tsiya ta hanani sukuni ta hana miji sukuni, wallahi yau ina daidai da ko wacce ƴar iska”
Hadiza kuwa status ta zama tana tsaye sororo hannunta a sama a yadda ta nuna Shafa da hannun a haka Shafa ta barta. Karab kuma ta jiyo furucin Shafa.
“Ke kika ƙyaleta kije ki rufeta da shegen duka ta gane akwai bambamci a tsakaninku” Cewar wani shashe na zuchiyar Hadiza.
Ai kuwa ba tare da duba me kaje me kazo ba ta faɗa ɗakin Shafa da sauri.
Karfa ku mance ga ɗinki sabo a jikin Hadiza yau aka sallamota daga asibiti.
To mu tara a littafi na huɗu inda anan zan naɗe taburmar labarin in sha Allah.
Shima fa akwai turka_turka me yawa a cikinshi mu dai je zuwa. Sannan kar ku mance akwai hutu kafin mu ɗaura da littafi na huɗun wanda zai zo muku da abubbuwan ban mamakin da zato bai zace su ba.
Nagode ƙwarai.
Gashi page ɗin yau babu yawa jiya na sanar muku ina aikin turaren amere show glass har biyu.
MRS BUKHARI
NAMA YA DAHU…
ROMO ƊANYE
BADI’AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
Book 4
(1)
MARAƊI
Asibiti:.
Tasi’u yana zaune a gefen malam hannun su yana cikin na juna tamkar abokai. Malam na ji da Tasi’u fiye da duk wani ɗa daya haifa, haka yake ji da Baba Fhatsima fiye da duk matan duniya, yake kuma jin tausayin Hadiza fiye da sauran yaranshi.
“Allah ya jiƙanki Fhatsima. Tasi’u!”
Malam ya ja sunan, Tasi’u yace.
“Na’am Malam akwai abinda kake da buƙatane?”
“Gani nake yi kamar baƙin cikin gidana da baƙin cikin matanane yayi sanadiyya Fhatsima, ji nake kamar ni nayi ajalinta”
“A’a Malam ko ɗaya kai da gidanka ba zaku iyayin ajalin Baba ba. Lokacin mutuwarta ne yayi, kayi haƙuri ka kwantar da hankalinka. Sannan Malam babban albishir shine yanzu abinda keke nema da mafarkin faruwarshi ya samu. Ahalinka sun haɗe kawunansu kowa yana zaune da ɗan uwanshi da zuchiya ɗaya mun haɗe kawunanmu mutuwar Baba Fhatsima ta ratsa zukatan ahalinka Malam. Shin ko da iya wannan ba zaka kwantar da hankalinka ba ?”
Idanu Malam ya lumshe zuchiyarshi sai yaji ta ɓangare guda tayi sanyi, ta ɗaya ɓangaren kuma sai mutuwar matarshi ta sake dawo mishi sabo fil.
Hadiza:.
Shafa na zaune taga Hadiza ta shigo da sauri. Tana isowa kusa da’ita sai kawai ta rufeta da dukan da yaba Shafa mamaki.
Jin kafafniyar dukan da Hadiza take yima Shafa ne da faɗin “kar ki je ɗinkinki ya sake ɓallewa Yaya” Yasa matan gidan fitowa kusan mutum huɗune suka shigo ɗakin suka jaye Hadiza tana haki. Duk da sun sha dambe Hadiza ta doku da kyau a hannun Shafa, take Shafa jini ya soma bin ƙafarta halamun ƙaramin cikin dake jikinta ya zube. Duk da haka bata bar Hadiza ba
“Wallahi sai kinyi nadamar wannan faɗan da kika takalo. Na dena ragar miki tunda dai ke jahilace mai kishin hauka wawuya marar tunani”
Wannan furuci yafi komai ɗaga hankalin Hadiza ainun. Yau ita Shafa ta kira da suna jahila?
Jan hannunta matar Mammada tayi ta mayar da’ita ɗakinta. Sai ita ta ƙarashe mata girkin nata ta shigar mata dashi ciki. Ciwo ya dawo mata sabo
Ita dai tana kwance ta mugun ƙurama silin idanu, damuwa sun ƙara cunkushe mata zuchiyarta. Ga a Irin wadatar da ta ga Isuhu da matarshi abun ya sosa mata ranta, bawai baƙin ciki take yi mishi ba, ba wai finta matarshi tayi ba ko ɗaya itama tasan mijin da take aure babu raini. Ga Gwadabe yanzu shigar shaddajo masu tsada yake yi sabida yana harka da manyan masu kuɗi sosai, sana’ar magungunanshi tana mugun kai mishi sosai.
Ajjiyar zuchiya ta sauke da jiyo muryar Anty Badi’a ta shigo da yaranta suna biye da’ita.
“Hadiza ashe ke dai baki da hankali ko? Wallahi kibi lamarin kishi a hankali. Akan Gwadabe dai kike wannan wautar kuma kinsan bazai goyi bayanki ba sai ma yin Allah wadai da abinda kika aikata, gashi a garin shirmenku cikin Shafa ya zube. Kika sake yayunki suka ji abinda kika aikata ranki ne zai ɓaci kinsan Sabitu duka zai yi miki sakarar kawai. Yaran ta barma Hadiza ta yi ficewarta ganin yaran yasa Hadiza haɗiye yawu ta haɗiye damuwarta tace.
“Kuzo ku zauna mana ko guduna kuke yi? Babban yace.
“Mu gida muke son a mayar damu wajen Babanmu mu ba zamu zauna ba” Gaban Hadiza ya faɗi data ji abinda yaron yace. Ta kuma tuno da roƙon da Isuhu ya dinga mata akan lallai ta tafi da yaranta taƙi fur a ƙoƙarinta na ƙuntatama Amarya tare da kawo musu cikas a cin amarcinsu. Ashe batasan cikinta ta daɓa ma wuƙa ba ita bata sani ba. Ajjiyar zuchiya ta sauke tace.
“Kuyi haƙuri kunga dare ya rufa gobe za’a mayar daku gidanku. Kai usmana kaje banɗaki ka yi alwala maza kaje waje kayi Sallah. Ke kuma inya fito sai kije ki ɗauro alwala kiyi sallar anan sai in zuba muku abinci kuci.”
Ficewa Usmanu yayi, yana fita sai ga Ummi ta shigo ɗakin anyi mata wankan yamma Abba na biye da’ita.
“Kai maza jeka ɗakin uwarka karka kuskura ka zauna mun a ɗaki ɗan iska mummuna mai ƙaton kai irinna ubanshi”
Abba ya fashe da kuka ya nufi hanyar waje. Ashe Gwadabe na tsaye a bakin ƙofar ɗakin a kunnenshi duk tayi wannan zagin. Abba ya raɓa ya wuce uban da gudu. Kallon kallo ne ya wanzu a tsakankanin Hadiza da Gwadabe. Kai ya girgiza kawai ya saki labulen ɗakin ya dawo falo. Ledar hannunshi ya ajjiye a gefe yana shirin fita usmana ya shigo. Yaron yabi da idanu harya shige uwar ɗakin, har ya sa ƙafa sai fita shi kuma daga falon sai ya dawo dai. Labulen ya sake ɗagawa Hadiza na tsaye tana zirga_zirga tana naushin hannunta.
“Yarannan kafin in dawo su bar ɗakinnan dan ban amince su zauna mun ba suna da gidan uba dan ubansu a mayar dasu In kuma kina sha’awar komawa kan ƴaƴanki ne ƙofa a buɗe take zaki iya sanar dani kinga gashi yayi kuɗi”
A tsorace Hadiza tace.
“Me kake nufi danine?
“Bala’i da masifa nake nufi dake. Ke baki sanni bane amman zan nuna miki wallahi nafi ƙarfin gidana kuma ni gidana bazai zama sansanin yaƙi da ƴan ubaba ki sani. Na fiki iskanci da bariki, baduniye ne da kike ganina. Da irin faɗa da tsawar da Gwadabe yake magana ya tsorata Hadiza dan tayi imanin na tsakar gida ma na iya jiyo sababinshi balle Shafa da ga_ ɗaki ga _ɗaki. Labulen ya sake a zafafe ya fice. Yana zage_zage
Haka dole Hadiza ta kama hannun yaran ta kaisu ɓarayin Anty Badi’a tare da mata bayanin abinda ke faruwa”
“Ai yayi kyau dama mai haƙuri bai iya fishi ba, maza dai ki turkuɗe auren naki ki huta kinga sai a buga miki tambarin ga wacce kishi yake hanawa zaman aure. Kuma Malam kinsan zaifi fishi dake ainun. Ga Sailuba nan ta kula dasu ni asibiti zanje in kaima Babansu abinci in sake dubo Malam ance jikinshi da sauƙi har yana magana.”
Ajjiyar zuchiya Hadiza ta sauke a sanyaye tace.
“Allah ya bashi lafiya dorarriya kya gaisheshi da jikin in kika je.”
A daddafe Hadiza ta koma ɗakinta ta shiga ta tadda Gwadabe zaune yana cin tuwon Shafa yana ba Abba da Ummi a baki. Ko kallon inda Hadiza take baiyi ba, itama wucewa tayi abunta ciki bata sake fitowa ba sai washe gari da asuba.
A falon ta tadda shinfiɗar bargon da take da tabbacin na Shafa ne harda matashin kai. Kai ta girgiza kifiyar kishi ta soketa.
Cikin wannan gaba har kwana huɗu Gwadabe na abu ɗaya baya cin abincin Hadiza, baya kwana a ciki sai falo ko gaisuwarta baya amsawa, ga yawan waya da yake yi da Bara’u akan Iyabo harda kuɗaɗen da Gwadabe yace aima Iyabo siyayya Hadiza ta sani, a ranar kasa bacci tayi sai juyi kawai ta riƙa yi har gari ya waye, ta kuwa tashi da ciwon kai mai tsanani, abu ya haɗe mata goma da ashirin. A haka har aka sallamo Malam daga asibiti ya dawo gida ya tarar da abun farin ciki yau ga yaranshi kawunansu a haɗe har an zauna zaman meeting na lumana na farko tare da sake ma juna ta’aziyyar Baba Fhatsima. Yaya Zarah dai da aka gama komai sai ta yi ma kowa sallama ta tattare yaranta suka koma. Hadiza har zuwa wannan lokacin a cikin faɗa suke da Gwadabe ɗiyarta dai tana hannun Shafa, ta kasa tambayar Gwadabe ɗiyarta, ga wajen da akai mata tiyata sai ciwo yake yi mata.
Da dai taga abun Gwadabe bana lafiya bane ranar daya dawo ɗakinta ta fito da zummar yi mishi magana ta riskeshi yana waya da Bara’u Sakina ta haihu.
“Ah masha Allah to Shikenan zamu tawo kafin suna ko da ni da Shafa ne Hadiza jinya take yi kaga ba tayi doguwar tafiya ba. Kace ina ma Sakina sannu, kaga in muka zo sai mu tawo dasu Toye”
Sukaita hirarsu Gwadabe ya dinga jan hirar dan ya baƙantama Hadiza daga ƙarshe dai dole sukai sallama.
“Dama dan Allah nazo in roƙeka gafarane a bisa abubbuwan da sukaita faruwa. Sharrin shaiɗanne kuma hakan ba sake faruwa zaiyi ba ni wannan fishin ya isheni”
Ƙur Gwadabe yayi mata da idandunanshi yana wani ƙanƙancesu, ita kuwa kanta a ƙasa tana jiran me zaice.
“Hmm Hadiza kenan sai yaune kika ji kina son kizo ki bani haƙuri, ai nayi tunanin kinfi jin daɗin zamanki a haka? Harni zaki cema yarona mai ƙaton kai kamata dan iskanci da wulakanci, kina so tun suna yara ki cusa musu mummunar aƙida. Sannan kika dubi tsabar idanuna kika kirani da azzalumi mayaudari mai bibiyar matar Aure “
Da sauri Hadiza ta runtse idanunta tare da katse Gwadabe ta hanyar cewa.
“Yaya ni dai dan Allah ka yi haƙuri banda tashin tashina”
“Rufa mun baki saina gama tsab”
Dole ƙanwar naƙi Hadiza ta rufe bakinta ruf Gwadabe yaita tambotsai kafin daga bisani yace ya haƙura amman fa ba har cikin zuchiyarshi ba.
“To yarinyar kuma sai yaushe za’a dawo mun da’ita?”
Dariya yayi yace.
“In dan sabida a dawo miki da yarinyane kika zo ban haƙuri kinyi gwari Hadiza. Yarinya ai kin nuna bakya sone shi yasa kika so ta mutu ki huta. Aikin banza aikin wofi”
Ya faɗa tare da tashi yayi ficewarshi sallar Isha. Har gwadabe ya dawo Hadiza na ciki tana kuka, ko daya dawo bai ko nuna ya damu da ganin Hadiza a wannan yanayin ba. Amman a ƙasan zuchiyarshi ya tausaya mata, ga rashin uwa, ga ciwo a jikinta, amman daya tuno halin jarabarta sai yaji haushinta.
“Har yanzu baki dena wannan kukan ba wai Hadiza, ko dukanki nayi ne, wannan wanne irin buyagine?”
Hadiza ta jima tana ƙoƙarin haɗiye kukanta yaƙi haɗiyuwa sai dai da taci nasarar karya zuchiyar Gwadabe. Hannu yasa ya ɗagota ya mannata da ƙirjinshi ya shiga shafan bayanta. Sun jima sosai a haka ji yayi sonta na ratsa jikinshi. Amman a kashi ɗari na sonta saba’in ya zube tas
“Ya’isa haka bani abincin to inci.” A kunne yayi mata raɗar, murmusawa tayi taje ta ɗakko mishi abincin ta kawo mishi, kanta na kan cinyarshi yana cin abincin yake cewa.
“Gobe zan shiga Damagaran akwai wani babban mutum da aka haɗani dashi zan kai mishi maganin ƙarfin maza yana da rauni ta fannin gamsar da iyali, kuma yayi maganin harma ya gaji. Ga arziki amman babu mace ko ɗaya a gidan duk sun kama gabansu. Shine akayi mishi hanyata gobe zanje sai ki saka ni a adda’a kwana biyu zanyi a gidan nashi akwai dafe_dafen magani da zanyi, in dai yasha da izinin Allah sauƙi zai samu, ki taya ni da adda’a”
Murmushi Hadiza tayi tace.
“Yana son ya zama jarumi kamarka kenan?”
“Au ni jarumine bani da labari?” Ya tambaya yana shafa sumarta.
“Me abu da abunshi kura da kallabin kitse. Kullum fa saika ɗibgi magani muna gani”
Dariya yayi sosai ya kawar da zancan da cewa.
“Sakina ta samu kai yau ta samu ɗiyarta mace. To ana gobe suna in jikinki ya sake yin kyau sai mu rankaya dukka, in kuma baiyi ƙwari ba sai muje da Shafa da yaran duka. Su Toye ma sun dawo daga wajen Gyatumar tasu suna Takai saiki soma shiri ko?”
“Allah ya nuna mana lokacin”
“To Ameen “
Daga haka dai faɗa ya ƙare washe gari Gwadabe da hannunshi ya ɗauko yarinya daga wajen Shafa ya damƙama Hadiza ita, yai musu sallama ya tafi.
Kafin ya tafin saida ya ba ko wacce wadataccen kuɗin tsaraba, ya shiga ya duba Malam yai mishi sallama ya kama hanya.
Nan su Shafa suka shiga shirin tafiya. Tsakanin Shafa da Hadiza gaisuwace kawai itama gaisuwar bata girmamawa kamar yadda Shafa ta saba Yaya sama Yaya ƙasa ba, ana dai gaisuwar a hakanma Gwadabe ne yai ta tausarta. Ita kanta Hadiza tasha jinin jikinta dan hatta su Yaya Tasi’u basa amsa gaisuwarta kuma suka sanarma Malam abinda Hadiza ta aikata. Ya dirar mata da faɗa Baba Asshi da Baba Suwaiba, da Amaryar Malam duk sukai mata faɗa akan kuskurenta. Malam yasa akai mai kiran Shafa ya bata baki ya bata baki sosai.
“Babu komai Malam wallahi ya riga daya wuce”
“To Allah yayi miki albarka Shafa’atu, ina su Abba?”
Ɗan murmushi tayi tace.
“Suna ƙofar gida makaranta”
Sallama tayi mishi ta komawarta gida, ta shiga aikin girki, Hadiza ma aikin girkin take yi na tarbar Oga, matan gidan ko wacce na aikinta anata zuba hira abun gwanin ban ƙawa.
Daf magriba sai ga Gwadabe ya shigo da niƙi_niƙin kayan tsaraba. Daga ƙofa ya zunguri Shafa da ledar lemo da ayaba.
“Riƙe nan inna dawo sallah ki sameni a ɗakin Hadiza mu tattauna”
Ta amsa tayi godiya, ta ajjiye ledar ta shige banɗaki, shima alwalar yayi ya tafi masallaci a gurguje dan har an tada Sallah.
Sai da Shafa ta sake gyara kwalliyarta dan yanzu a fice take ta ɗauki shawarar wata ƙawarta abokiyar aikinta data ziyarceta washegarin ranar da Hadiza ta bita har ɗaki.
Ba iyaka Gwadabe Shafa ta ɗaga ma hankali da kwalliyarta ba harda Hadiza dan kusan tafi Gwadabe firgita. Ga gashinta sai sheƙi yake yi, gashi dai shi ba yawa ba amman ta gyare abunta tsab gwanin sha’awa. Zama tayi a gefen Gwadabe jikinsu na gugar juna, Hadiza na daga ɗaya ɓangaren.
“Barka da dawowa ya hanya, da fatan abinda akaje nema an samo? Barka da gida umman Ummi”
Saroro Hadiza tayi tana kallonta tama gagara amsa sannun da take yi mata ta bita da idanu kawai.
“Sannu Shafa Irin wannan kyau haka. Ina Iyabo kika barota ?”
“Iyabo tayi bacci shine na shinfiɗeta a kusa da Abba”
Da yanga take magana.
“A_a _a_a je ki ɗakkota inta farka tana neman nono fa? Maza jeki ɗakkota bana son abinda zai taɓa Iyabo”
Har Shafa ta fice ta dawo tsakanin Hadiza da Gwadabe babu wanda yace komai.
Shinfiɗe Iyabo Shafa tayi a kujera.
“Hadiza zuba mana abincin yau dai muci tare sai in rarraba muku tsarabarku data yaran ko?”
Fuska a turɓune Hadiza ta zuba musu lafiyayyen tuwo da miyar bushasshen karkashi wanda yaji naman ragon suna da kayan ciki.
Tsakankanin Shafa da Gwadabe ne kawai suke ta hirarsu har aka kammala cin abincin dai.
Atampipi da leshi ya zaro a ledarshi ya ajjiye a tsakar ɗakin.
“Wannan naku ne da zaku dinga kuyi fitar sunan Sakina. Gashinan kala uku_ukune ke Hadiza tunda kece babba ki soma ɗauka”
“Itama babbace ta ɗauka ta bar mun nawa”
Shafa tasa hannu ta zaɓi ta darje tace.
“Mungode Allah ya ƙara arziki”
Leda ya miƙoma Shafa yace.
“Wannan nasu Abbane gashinan kinmun ƙorafin Abba bashi da wanduna kwanaki, to ga wannan a ƙara mishi dashi. Hadiza kema ga na su Ummi, wannan kuma na sabuwar jinine.
Hadiza ta karɓa tana bin manyan laidojin da Gwadabe ya bama Shafa. Ta kalli ta hannunta ta gyaɗa kai kawai. Tace angode wallahi ta kasa dan wani ƙududune ya tokareta a wuya. Shafa kuwa sai adda’a take yi mishi. Ya haɗa musu da dubu shida_shida.
“Wannan kwa yi dinki. Ragowar kayannan Hadiza ki ajjiyesu a wajenki na Sakinane sai ku ƙara da taku gudummawar. Ke Shafa ɗauki Iyabo bari in ɗebar miki kayan in rakaki”
Hakan kuwa akayi, suna fita Hadiza ta wuce ciki fu tayi kwanciyarta. Ko da Gwadabe ya dawo yayi mata magana tayi watsin ruwan tsarki dashi, shi kuma yayi tunanin ma bacci take yi.
Gaga_gaga har ranar tafiya Takai yayi sukai ma jama’ar gida sallama suka tafi.
Da daddare suka shiga Takai Bara’u na ƙofar gida ya gansu.
“Gwadabe kune a tafe? Maraba lale da zuwa. Hadiza, Shafa bismillah ku shiga ciki’
Bayan an gaggaisa sai suka wuce ciki Gwadabe kuma yayi zamanshi wajen amininshi tunda yana jiyo muryoyin mata a gidan.
“Ya bayan rabuwa Bara’u. Ya labarin Iyabo da rayuwar gidan aurenta?”
Dariya Bara’u yayi yace.
“Kai Gwadabe maimakon ka soma da tambayar yara da noma kamar yadda ka saba sai ka somamun da batun Iyabo? Nasan ana binka sallah ga buta yi alwala kayi Sallah.
“Haram munyi sallolinmu dukka a hanya. Kai dai bani labari”
Ajjiyar zuchiya Bara’u yayi fuskarshi ta sauya. Yace.
“Labarin tsuntsun soyayya babu daɗi. Ga wani babban al’amari daya faru a gidanku wanda duk garinnan na Takai anata tsogumi akan abun Gwadabe. Nasan baka sani ba Gwadabe. Yanzu haka Babala tana asibiti rai a hannun Allah. Tashin hankalin da take ciki ya kai.
Mrs Bukhari ce
Ayi haƙuri da wannan idanun nawa bai warke ba.
Sannan dan Allah ba kullum zan dinga posting ba sau uku a sati zaku dings samu sakamon idanuna daya matsa mun da ciwo nasan zaku yi mun uzuri in ku kai la’akari da ni bana wasa da typing sam.
Nagode.
Ku taya ni jaje Allah yayi ma magena rasuwa mai suna Sameer jiya.