Karshen Zalunci
Wata mace yar kimanin shekaru ashirin da uku dauke tsohon ciki a jikin ta sanye da tufafi kayan fata riga da wando,
Zaune take abisa kan wani ingarman doki baƙi, tafiya take a cikin wani irin daji mai tattare da sarkakiya, kwazazzabai, da duwatsu.
Kallo daya zaka yiwa matar ka fahimci cewa tana cikin mawuyacin hali.
Kaico tana cikin wannan hali ne sai taji alamun naƙuda sun bijiro mata, kawai sai ta ja linzamin dokin ta tsaya cak sannan ta kama ta sakko kawai sai ta taka da kyar ta durfafi kofar wani kogon dutse,
Kafin ta isa sai ta yanke jiki ta faɗi kasa, a cikin wannan hali ne naƙuda ta kamata ta haife abinda ke cikin ta .
Cikin matukar farin ciki maras musaltuwa ta dauki abinda ta haifa domin taga mene ne,
Ai kuwa sai taga wata santaleliyar yarinya ce kyakkyawa ta gaban kwatance,
Duk da cewar tana cikin wannan hali na laulayi bata san sa’adda hawayen farin ciki suka zubo daga idanun ta ba, a daidai wannan lokaci ne kukan jaririyar ya cika dajin baki daya,
Cikin azama ta ɗauki wani itace mai kaifi ta yanke cibiyar jaririyar.
Tana cikin wannan hali ne kwatsam Sai ta hango waɗan su dakaru sun durfafo inda take a bisa dawakai,
Kafin tayi wani yunkuri ɗaya daga cikin dakarun ya ɗame kibiyar sa ya harbe ta a gadon bayan ta,
Saboda tsakanin zafi da zugin da tayi a gadon bayan ta bata san sa’adda ta kurma wawan ihu ba ta sulale kasa sumammiya jaririyar ta na ci gaba da tsala kuka.
Har badakaren ya sake dame kibiyar ta sa karo na biyu na nufin ya sake harbin matar.
Kwatsam bazato babu tsammani sai aka ga wata murgujejiyar zakanya tayo fitar burgu daga cikin wannan kogon dutse dake dajin, ta dako wawan tsalle ta bangaji dakaren a kirji.
Saboda karfin bangazar sai da badakaren da dokin sa su ka yi sama tamkar an janye su da ƙungiya, sannan daga bisani suka faɗo kasa matattu ko shurawa ba su yi ba.
Nan fa aka fara kallon kallo tsakanin zakanyar da mayakan.
Daga can sai zakanyar tayi gurnani gami da hargagi sannan ta dako sufa kan mayakan .
Koda ganin hakan sai dakarun su ka daga makaman su suka yi ihu da kururuwa mai firgitarwa suka yi ɗauki kanta a kacame da azababban yaƙi mai matukar muni ban tsoro daban al’ajabi.
Wohoho! Hakika yaƙi shi ne matattarar dukkan bala’i kuma idan gwani ya haɗu da gwani JURIYA DA BAJINTA suka game waje guda, dola ne artabu ya zamo abin tsoro,
Nanfa zakanyar ta wanzu tana hallaka dakarun,yazaman cewa duk inda ta sanya gaba sai dai kaga dakarun na zubewa kasa matattu.
A inda zakaga ta mako badakare Daga kan dokin sa ya bisa ta turmu
A duk sa’adda dakarun su ka kaiwa zakanyar hari sai kaga ta wurkila haɗe da zame wa ta kaucewa saran.
Kafin badakare ya sake daga takobin sa zakanyar ta dako tsalle sama ta sanya fatatan ta ta tsire masa idanu, ruwan cikin idanu ya tsiyaye, take badakare zai sulale kasa daga kan dokin sa yana mai kurma ihu. Kai wasu lokutan idan ta daki badakare a wuya sai kaji wuyan nasa ya karye yayi kara ruƙus!! Ƙasa! Ya faɗi kasa matacce, ko shurawa bai yi ba.
Hakika waɗannan dakaru suna ganin tashin hankalin da basu taba ganin irin sa ba.domin kafin cikar rabin Sa’a zakanyar ta kashe fiye da rabin su.
Nanfa karafniyar karafa da ihun mazaje, haniniyar dawakai haɗe da gurnanin zakanyar ya cika dajin baki daya, kura ta turnuƙe sararin samaniya saboda yadda Dawakai ke yin turmutsutsu, kofatan su na kartar ƙasa,
Wohoho tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce wuya koda magani ba daɗi, kuma wuya mai sa dole,
Hakan ya faru ga sauran dakarun domin koda suka ga cewa a koda wane lokaci zasu iya baƙuntar barzahu sai suka cika wandon su da iska domin tsere wa,
Sai zakanyar ta dunga kure musu gudu tana make su suna faɗuwa kasa matattu. Kafin wani lokaci ta zubar da gawarwakin su a kasa.
Kawai sai ta juya ta durfafi inda wannan mata da jaririyar ke kwance a kasa tana fitar da wani irin gurnani.
Lokacin da wannan zakanya ta ruga izuwa inda suhaimat da jaririyar ta ke kwance,yayin da taga halin da take ciki sai ta ruga izuwa bakin wata korama ta guntso ruwa a baki ta dawo izuwa inda suhaimat take ta fesa mata ruwan a fuska,
Faruwar hakan keda wuya sai suhaimat taja dogon numfashi gami da sauke nannauyar ajiyar zuciya, idanuwan ta suka buɗe tartar ta wartsake daga suman da tayi,kawai sai ta mike zaune,
Yayin da tayi arba da zakanyar sai razana taja da baya tana mai ɗaukar jaririyar ta ta ƙanƙame ta a kirji.
Koda ganin halin da suhaimat ta shiga sai zakanyar ta juya ta ruga izuwa cikin wannan kogon dutse dake dajin,
Cikin matukar farin ciki suhaimat ta mike tsaye taje bakin wannan korama ta yi wa jaririyar ta wanka,ita ma ta tsafta ce kazantar da ke jikin ta,
Sannan ta dawo izuwa karkashin wata bishiya ta zauna ta shiga sharar da jaririyar nono tana mai shafa gashin kanta, zuciyar ta cike da matukar farin ciki maras musaltuwa.
Kuma ta shiga tambayar kanta a cikin ranta tana cewa,
Shin Wane ne ya kashe waɗannan dabaru? Ko kuwa wannan zakanya ce.
Amsar tambayar da ta kasa bawa kanta kenen,tana cikin wannan hali ne zakanyar ta dawo gare ta bakin ta rike da wata jakar fata, ta ajiye a gaban ta,
Bisa mamaki a wannan karon sai suhaimat taji ko kaɗan bata tsora ta da ganin zakanyar ba,
Bata re da fargabar komai ba suhaimat ta ɗauki wannan jakar fata ta buɗe ta,
Ai kuwa sai taga ashe nau’ikan kayan marmari ne a cikin ta,
Dangin su Ayaba da inibi, kawai sai ta shiga cin kayan marmarin har sai da ta ƙoshi,
Sannan ta fasa kwakwa ta shanye Ruwan cikin ta,
Zakanyar na tsaye na tsaye a gefe guda tamakar mai jiran umarni,
A sannanne suhaimat ta lura cewa jikin zakanyar akwai alamun jini take ta fahimci cewa ita ce ta kashe waɗannan dakaru domin ta ceci rayuwar ta da jaririyar ta,