Bismillahir Rahmanir Rahim
Cikin mamaki tace”but jiya fa an Aiko min da flower Kuma a jikin flower an rubuta to my heartbeat Rahma Kuma nasan babu Wanda zaiyi min haka sai Kai bana son Wasa”
Hade rai amir yayi ya juya Mata baya yace”watoh har kina da wani da zai aika Miki flowers baby yaushe kika fara kula wasu”
Itadai mamaki take because this is not the first time da ake yi Mata aike Wanda a tunaninta Amir ne but ji take ta tambayeshi ne ko tayi shiru gudun kar ranshi ya b’ace”
Zuwa tayi gaban shi tace”baby wallahi babu Wanda nike kulawa kaima kasani ka yarda dani baby please “
Kallonta yayi da jajjayen idonshi ya Kama hanunta ya Kai saitin kirjinshi dake mugun bugawa yace”baby ki ji fa wallahi in kika kula wani mutuwa zanyi baby Ina kaunar ki dan Allah ki rufamin asiri karki gujeni”
Rungumeshi tayi tare da fashewa da kuka tace”wallahi my amir hakan bazai faru ba Allah ya jarrabe ni da mugun sonka please karka sa damuwa a ranka bana jin zan iya rayuwa babu Kai please karka zargeni”
Kama fuskarta yayi yana mata kallon cikin ido cikin karyewar zuciya har hawaye yakeyi yace”baby bansan meyasa wallahi hankalina ba zai kwanta ba sai na ganki a gidana”
Murmushi tayi ta Haye saman desk tace”ka ji ka da wata magana aini in ba mutuwa ba auren Kamar an gama ne saura fa sati d’aya”
Zama yayi yace”thanks aina sani Kuma in so samu ne mu mutu tare”haka fa Suka cigaba da Hira cikin nishadi
B’angaren Aayan kuwa bayan ya gama waya da jabir ya fara zirga-zirga ya kasa Zama ya kasa tsaye
Sake dialling number jibrin yayi yace”kana Ina?”