Page 3
……………Shuuuu yazo ya wuce sai jikin glass ɗin wata motar bus.
Saurin kallon wanda ke riƙe da hannuna nayi, gabana yay masifar faɗuwa saboda cin karo da nai da fuskar da ban taɓa tunanin gani a wajenba ko tsammani, ya sake fisgar min hannu muka duƙe bayan wata mota saboda tahowar wasu harsasan huɗu kanmu.
Cikin matuƙar fusata ya girgizamin hannu yana faɗin, “K shashasha ki dawo hankalinki!!”.
Yanda yay maganar da wata firgitacciyar muryace ta dawo dani duniyar mutane, amma hatta da kunnuwana da sun doɗe baki ɗaya ko ƙarar harbin banaji.
Ya jefamin wata bindigar a jiki, cikin zafin nama na cafeta.
Sosai Jawaad yaji mamakin salon na bilkisu, sai dai babu wannan lokacin a garesa yanzun, dan haka ya maida hankalinsa akan abinda ke gabasu.
Wajen ya sake hargitsewa da musayar wutar harbe-harbe, kowa burinsa ya kare kansa, mutane kam bamuda tabbacin halin da suke ciki a yanzu.
Bazan iya tantance muku halin dana tsinci kainaba a ciki a wannan lokacin, amma ni kaina nasan na zama jaruma mai ban al’ajabi..
Kowa ya jigatu a wajennan. Bagamu jami’an tsaronba baga ƴan ta’addaba, balle kuma jama’ar gari da suka fimu shiga ruɗani da tashin hankali. Sai dai abin farin cikin shine mutum biyune suka haɗu da tsautsayin harbi a farar hula, ɗaya a ƙafa ɗaya a hannu, amma Alhmdllh babu wanda ya rasa ransa sai a cikin ƴan ta’addar da aka harba a ƙirji. Mun sami nasarar cafkesu baki ɗaya, su biyarne, ɗaya ya mutu, ɗaya naji masa ciwo a hannu, sai raunika da sauran suka samu da wasu a cikinmu harda ni da gilashin wata mota ya yanka a hannu.
Comment
INA ALFAHARI DAKU