Mamuhgee_
ZafafaBiyar
BlackMoneyLove
Littafin da labarin Ameenatou Wanda ni mamuhgee na rubuta gabaki dayansa sadaukarwa ne ga irreplaceable Besty na AMEENAH ABDULMALEEK (Meenal Maleek)🤍💋
1
BismillahirRahmanirRaheem.
Kaman yanda yake a tabbacen zance Salati baya hana ɗaukar rai, Hakama Ƙasar kabari bata shuka sedai ta binne binnanne,
Itadai ƙaddara yashi ce ko an dunƙulata bata dunƙuluwa,
Rayuwa da kaddara a tare suke tafiya tamkar Yan uwa Daya sbd haka kowace rayuwa take tafe da tata kalar kaddara duk wanda ka gani yau to yabiyo ta jiya.
****Cikin tsananin sauri da rawar jiki me tsananin gaske dattijuwar dadahnsu ta fito daga dakin da suke ba tareda ta damu da tsananin ruwan saman da akeyiba masu karfin gaske da iska ga Kuma duhu me.
Runfar madafarsu ta girki ta nufa tareda Saka hannuwanta duka biyu ta share ruwan Dake sauka kan fuskarta sbd ta Gani da kyau.
Madafar data gama jiqewa tsaf ta zubawa idanuwanta da sukai jajir cikin nauyin zuciya da tashin hankali Amma Kuma halinda suke ciki a yanzu ya wuce taji radadin baqin ciki ko wanne iri Dan haka ta qarasa inda murhun wutarsu yake ta fara kokarin gyara Yan sauran itatuwan Dake gurin tana hada kansu Dan hura wuta kota Yaya duk da ruwa da iskan da ake zubawa me karfin.
Motsi taji a bayanta sedai Bata iya juyowa ba sbd kokarin hada wutar cikin sauri dan tasan ba kowa bane face babbah mahaifin ‘yayan nata mijinta.
Zagayowa yayi ta gefenta Shima a jiqe kayansa na tsiyayar ruwa sosai hakama rawanin Daya zagaye kansa dashi sbd ruwan Shima ya jiqe sosai Yana tsiyayar ruwa.
Duk ruwan Nan da akeyi akansa aka farasu Yana tsaye kofar dakin da suke Tin safiyar ranar har zuwa yamman sallah kawai ke matsar dashi daga kofar dakin har hadarin ya Hadu Yana tsaye duk karfin iskan da aka fara aka fara ruwan Yana tsaye a gefen dakin Yana jiran tsammani ya zauna ya tashi tsaye,yaje farkon Bango ya dawo Babu abinda yake fata Se Allah ya kawo musu wannan lamarin a cikin sauki ko Dan jarabawa da kaddarorin da suka ringa haduwa dasu a rayuwar Nan.
Tayata hada kan itatuwa gurin da hura wutar yafara kokarin yi Yana Dan rife idanuwansa dasuka manyanta sosai tsufa yafara saukar musu sbd ruwan Dake shiga cikinsu,
Ita kanta dada kokarin kunna ashana takeyi amma ruwa da iska Baya bari Amma takasa Dena kokarin kunnawar hannuwanta na kakkarwan sanyi da mutuwar jikin damuwan Dake dabaibaiye da ita Mai hade da tsananin tsoro.
Shi kansa babba dayake tayata kare iska da ruwan da hannuwansa Dan ta kunna wutar yasan wura wuta a wannan lokacin ba abune da zai taba yiyuwa ba har abada sbd ita kanta ashanar tsiyayar ruwa takeyi Amma dukkaninsu sun kasa yarda da sallamawa sbd Babu Wanda zuciyarta take a daidai da tinanin nutsuwa a cikinsu abu Daya ne a ransa shine bazasu iya rayuwa ba idan wani abin ya samu wadda ke cikin dakin gurin haihuwar abinda yake cikinta,
Itace duk wani karfin zuciya da karfin halin dasuke dashi na ci gaba da rayuwa bayan masifun dasuka ringa shiga,
Babba shine shugaban gidan Kuma gatansu Wanda ya kasance jigonsu,shikuma babba itace hasken zuciyarta Kuma nasa jigon Dan idan Babu ita baida jarumtar cigaba da zama shugaba a cikin Iyalin nasa.
Hannuwansa Dake Dan rawa Shima ya miqa ya karbi ashanar hannun nata yafara kokarin tayarwa Amma kwalin ashanar narkewa ma kawai yafara yi a tafin hannunsa sbd ruwan Daya gama jiqasa..
Qurawa tafin hannunsa idanuwansa dasukai jajir yayi Yana kasa motsawa bare cewa komai zuciyarsa na daukan wani irin nauyi da dumi a lokaci Daya.
Dadah ma da jikinta ke mutuwa dagowa tayi da jajayen idanuwanta ta kallesa zuciyarta na yankewa da ganin yanayinsa,
Yanda yake tsananin son mahaifiyar Ameenatou da Ameenatou haka take tsananin sonsa Dan haka bazata bari ya sake dandana radadin rashin da yayi a Baya ba na rashin ganawa da Rabin jikinsa Dan haka jikinta na rawa ta juya ta nufi inda tasan akwai wata ashanar ta dauko tafara kokarin wura wutar da idan har gawar Dake Rami zata fito tayi magana to tabbas tashin wuta a wannan lokacin zai yiyu.
Ahankali babba ya Bude idanuwansa dake rintse ya Kalli dadah Daketa aikin abinda bame yiyu bane Amma taqi denawa Se qarawa takeyi kaman batasan ruwane ke tsiyayar daga shanar ba.
Nice
Allah ya Kara basira
Godiya
🙏🙏🙏🙏🙏
Thanks for everything
Allah ya qara basira
Ameen ya Allah