SANDAR DUKAN UWARGIDA
GIDAN ABDUL Mace ce wacce a ƙiyasi za a iya ba ta shekara talatin da biyar, tana tsaye a falo tana kaiwa da kawowa, hannunta riƙe da wayarta, wacce a yau take jinta tamkar maƙiyiyarta saboda yau ɗin ta kasance ‘yar aiken da ta kwaso mata labarin da ta kira shi da baƙin labari, wayarta ƙawarta ce amma a yau dai ba…
