BACCIN SO
Cike gidan yake makil da jama’a, kana ganin yanayin tsarin ginin gidan kasan irin gidan masu dan rufin asiri ne daidai gwargwado, babban compound ne mai dan madaidacin girma dakeda wata yar kodaddiyan milk gate dayake a bude sabida jama’a dake shiga da fita. Yammata ansha makeup ansha anko, sun zagaye wata yar budurwa dakana ganinta kasan itace Amaryan sabida yanayin tufafin jian gaban…
